You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin ta ɗiyar ta na kwance sama da sati biyu bata ci
komai ba ina ta ga ƙarfin cin wani abin.

Sai da prof yayi dagaske kafin ta chakwalkwala abincin ta ce ta ƙoshi ta matsar gefe.ce mai ta yi ita sallah
zata yi kafin su koma asibitin ya ce toh shima bari ya tafi dan yin sallar dan haka kiran Dr Maher yayi a
waya akan ya zo su tafi sallah,sai da ya kwantar mata da hankali sannan ya fita daga ɗakin ta tayar da
sallah shi kuma ya sauko ƙasa dan jiran Dr Maher.



Da lallaɓa da encouraging words ya samu ta haƙura ta yi shiru ta daina kukan har zuwa lokacin da kiran
prof ya shiga ya sanar da ita sallah zasu tafi ta mai Allah ya kiyaye hanya bayan tafiyar sa ne ta yi sallar
itama ta zauna roƙon ubangiji da ya ba ma ƴaƴan su lafiya ya ta da kafaɗun su ba dan zunuban su
ba,sosai ta masu addu'a dan watanni uku zuwa huɗu da aka ɗebar ma ɗan ta akan adadi lokacin tashin
sa ba abu mai wuya bane a wun ubangiji...



Da ta idar ne ta nufi ɗakin su Hajiya Zeenat a inda suka zauna zaman jimamin conditions da likitan ya
zayyano masu game da farfaɗowar Zaid but sun yi realising cewa komai shall be possible da yardar
Allah.ba jimawa suka shirya dan tafiya asibitin inda tare suka fito suka tarar da taxi na jiran su ba ɓata
lokaci suka shiga ya wuce da su zuwa asibitin,ko da suka tafi sai suka tarar da Bilal ne kaɗai suka
tambaye shi inda Afzal ya tafi bai ɓoye masu komai ba ya sanar da su cewa ya koma Nigeria but ya ce
Hakim zai zo dan saboda akwai ayyuka da suka taru da yawa a hospitals ɗin iyayen su and there is no
one to take care of them sai shi kaɗai,



Abin ya ɓatawa Ammi rai har ta fara bambamin cewa aiki ya fi ƴan uwan sa muhimmanci a gare sa
kenan in ba haka ba ana wannan hali har wani aiki mutum zai je yi but Hajiya Zeenat ta yi calming nata ta
ce dole ne ya kula da wani fannin since there is no one to do it da haka dai ta yi shiru not because ta yi
niyar yin shirun sai dan kar ta janyo magana a hospital premises.



Ƙarasa shiga cikin ɗakin baby doctor suka yi inda suka ganta kwance tana bacci kamar dai yadda suka
bar ta this is 3 hours da barin su asibitin but bata tashi ba abin ya dame su sai suka koma chan gefen Zaid
dan ganin ko an sami improvement but shima still a nan gwiwowin su ya fara sagewa shi Bilal mai kukan
ne dai ya ƙarfafa masu gwiwa dan shima jiran zuwan Hakim ya ke yana son komawa gida yayi resuming
aikin sa maybe kafin sati ya wuce zai ji an ce da shi an sami improvement dan zaman sa a nan ɗin gani
yake kamar abubuwan basu cigaba..



Zaman jiran farfaɗowar baby doctor suke yi dan sun san shi kam Zaid ba tashin yanzu yanzu bane.. Cikin
hikimar ubangiji kuwa zaman su babu jimawa suka ji kira daga ofishin likita da suka tafi hints ya basu
akan yanda zasu kula da ita yanzu da ta farfaɗo dan gudun kar ta kuma collapsing kamar yanda ta yi ɗazu
godiya suka mai suka fita suna murnar ta farka..



She is awake and cool dan a zaune jingine da bed cradles suka riske ta an saka mata soft pillow ta bayan
ta tana sipping wani abu da basu san ko menene ba a tea cup rufe da murfi sai straw da take sipping da
shi wanda ya ke ta saman kofin..

Hamdala suka yi na ganin ta cikin sukuni har ma tana iya shan abu tana iya riƙewa da kan ta.ƙarasawa
ciki suka yi a nan aka shiga tambayar ta me ke damin ta ina ke mata ciwo ita dai murmushi kawai ta rinƙa
yi har suka yi shiru ta ce da su

"Am fine am absolutely fine you all can see that am good"!!ta faɗa tana masu murmushi dan hankulan
su ya kwanta sai suka faɗaɗa fara'ar kan fuskar su.tambayar su ta yi



"Ya jikin na sa"?a nan suka ɗan yi jimm sai ta kalle su haɗe da ajiye kofin ta ce
"Is okey kar ku damu zai tashi nan ba da jimawa inshaAllah"daɗi suka ji lallai tana da ƙarfin zuciya ita da
yanzu ta farfaɗo but har tana da ƙarfin reassuring nasu as a doctor,rungume ta Ammi ta yi ta ce

"Allah ya maku albarka ya kuma kare mana ku daga yau sai yau babu ku babu outreach ko da a nan
asibitin ku ne ba ku kuma yi"!a halin jimami ake amma sai da maganar ta ya saka kowa darawa kaɗan
ciki kuwa har da Bilkisun dan a nan ta fara tunanin shine fah ya natse na maganar outreach ɗin nan ita
kuma shegen girman kai ya hana ta ƙin yarda akan ba zata bi shi ba shi dan ya hukuntata ya shirya
tafiyan but at the end of the day abin sai ya juye masu he end at the receiving end ohh Allah ka bashi
lafiya,,a zuciyar ta ta yi wannan analysis ɗin..



Ranar murnar iyayen baya misaltuwa dan haka a nan ɗakin na ta suka kai har dare ta ce da su zata tafi
ganin shi suka ce a'a ta bari har washegari bata gama farfaɗowa ba dan haka ta haƙuran Bilal ne ya taya
ta hira har dare wuraren 11 sannan ya mata goodnight ya tafi dan hutawa yayin da Ammi da Hajiya
Zeenat suka kwana a nan dan a daren aka so yi mata wanka ta ƙi ta ce zata iya da kan ta har tsiya suke
mata wai in bata yarda an mata yanzu ba ma ai akwai na jego dole ma ta yarda jin su ta yi amma ko za'a
haɗa ƙasa da sama ba zata yi wannan wankan jegon miyatar da ake yi ba haka kawai ta janyowa kan ta
matsala.

Da ƙyar ta yi wankan aka saka mata rigar bacci mai kauri da hula abinci ta ce sai washegari dan ta sha
energy booster kafin su shigo haka suka ƙyale ta ta kwanta suma suka kwanta. Oh rayuwa wai su ne ke
jinyar yaran su biyu a asibiti asibitin ma ta wata ƙasa lallai yaron nan ya guji haɗuwar su da shi...




************

Kwanaki biyu aka ɗauka ana koya mata tafiya dan joints ɗin ta duk na mata ciwo sakamakon doguwar
kwanciyar da ta yi a course of minor exercise ɗin ne ta yi saloli wanda ya taimaka mata ta kuma jin jikin
ta ya sake mata har take fatan Allah ya sa anjima su fita dan ta samu ta yi sneaking zuwa ɗakin Zaid
because tunanin sa ya zame mata obsession tun da ta farfaɗo su kuma sun ƙi kai ta dan ganin sa..




A yammar ranar ne jirgin su Hakim ya iso dama Bahajjatu ta hana kar a sanar da Bilkisu zuwan su she
want to surprise her dan Hakim ya sanar da Ammin su tare da Bahajjatun zasu taho har da faɗan kar ya
kawo mata ita ta zo tana portraying masu madness a asibiti but sai ya mata bayanin ai ta shiru ƙyale shi
kawai tayi..
It was a big surprise to her dan ta ga babbar ƙawar ta da zata iya sharing damuwar ta da ita.

After all the oyoyo and everything sai suka keɓe ta sanar sa ita damuwar ta dama ƴar taya ɓera ɓari ce
sai ta nemar mata hanyar fita kamar ɓarayi ta yi directing nata zuwa hanyar office ɗin doctor kamar dai
yadda Bilal ya nuna masu da suka zo dan bai bari sun ga Zaid ba dan gudun tashin hankalin da zasu shiga
a ce da zuwan su sun riski matsala irin wannan bai kamata ba..




Thank goodness ta sami doctor ɗin but he was amused ganin ta bayan ya san cewa ita patient ce sai ya
ce ta zauna ta zauna

"How may i help you"ya faɗa feeling free da ita sai bata ɓoye mai komai ba akan tana son sanin komai
ne game da ɗayan patient ɗin ta kira sunan sa at first the doctor was like can he tell her everything
about the patient ko dai ya ɓoye ne da ta ga haka sai ta mai bayanin cewa daga ita har shi ɗin da ke
unconscious doctors ne har ta ɗan kawo mai scenario da ya faru da yayi sanadiyar zuwan su,a nan
hankalin sa ya kwanta sai yayi narrating mata duka findings ɗin su she was shedding tears but bata san
cewa crocodile tears take shedding ba real tears ba sai da ta ji ɓoyayyen solution da likitan ya sanar da
ita a nan ta yi zaman dirshan ta shiga risgar kuka ba ji ba gani haka ya rinƙa bata magana har dai ta tashi
ta tambaye shi ɗakin da Zaid yake ya mata describing bai da nisa da office ɗin sa ta fita tana haɗa hanya
da ba gama warwarewa tayi ba tana dafa bango ana kallon ta ana mata sannu bata amsa kowa har ta iso
ɗakin ta hango shi ta waje under control of machineries and devices ta tuna da final solution da likita ya
gaya mata sai kawai ta fashe da kuka tana yi tana jujjuya kai tana cewa

"Noo noo..Zaid please noo i can't witness that inalillahi wainaillaihir raji'un please Zaid don't accept the
defeat fight it please"...




*_I guess this chapter is somehow wow and somehow oh no u need not to worry just keep on following
sequentially you shall enjoy the love saga i bet you,catch yah tomorrow mi Amor_*




*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim
#vote

#comment

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*14*
Giftawar ta kawai bilal ya gani sai yayi saurin bin bayan ta a hankali ya rinƙa tracing hanyar da ya hango
ta har dai ya iso ƙofar ɗakin da take tsaye wato dai ɗakin Zaid,jim yayi yana kallon ta tana bashi tausayi
dan duk maganganun da take yi yana jin ta rasa abin faɗa mata yasa yayi shiru har dai ya ga abin na son
fita a kan dausayin mai hankali.

She was crying with great agony and pains haɗe da hatred na Asma'u dan ita gabaɗaya ta ta'alaƙa laifin
komai ne a kan Asma'u because if not for her babu ta yadda za'a ma Zaid wannan aika aikar dan haka
with each passing seconds of her life yana tafiya ne da tsananin tsanar Asma'u a ran ta tsana ce mai ƙarfi
wacce bata jin zata iya yafe mata saboda taɓa lafiyar Zaid da aka yi daidai yake da hukuncin takura mata
walwalar ta da sukunin ta a duniyar ma baki ɗaƴa.



Any word she speak out rhyme with her heart wishes she just pray that he wakes up at the right time if
not da akwai babbar tashin hankali a ƙauyen koma gabaɗaya ba ma gidan su Mudan da Asma'u kaɗai
ba..

Tana tsaka da kukan ta mai tsuma zuciya ta ji an taɓa ta sai ta dakata da kukan tana share hawayen ta
kafin ta juyo ta kalle sa sai ta ga Bilal ne ba amfani in ta ɓoye masa damuwar ta sai ta cigaba da kukan
tana nuna mai ɗakin Zaid tana kuka kamar ba ita ta farfaɗo daga jinyar sama da sati biyu ba jan hannun
ta yayi dan su bar wurin saboda kasancewar su a wurin ba komai zai haifar mata ba apart from more
heartache da increase hatred wanda is not good for her health.

Tana kuka tana fincikewa yana jan ta da kuka da fixge fixge suka koma ɗakin ta inda a nan ne suka yi
kiciɓis da Hajiya Madina dan dama daga neman ta ta fito ko da ta ga bata nan babu wanda ya fara zuwar
mata rai sai Bahajjatu dan ita kaɗai ce marar jin maganar da zata iya fitar da Bilkisun shi yasa ta rinƙa
trying line nata sai dai bai shiga dan ita ma Bahajjatun fita tayi dan neman apple ɗin ta because zuciyar
ta fes yake and she is praying for her big bro to wake up as soon as possible,suna cikin hirar ne sai ya ga
kamar gilmawar twin sis ɗin sa cikin tashin hankali sai yayi saurin biyo ta inda yayi discovering abin da
take kallo har ya saka ta kukan da take yi shi ya sa ya ja ta suka bar wurin gudun kar Bahajjatu ta gano
ɗakin da yayan ta ke ciki because he is sure ahe will definitely create a scene dan bai san dalilin da yasa
Afzal ya bar ta ta biyo Hakim ba alhalin duk sun san halin ta.

Ganin Bilal tare da ita ya sa Ammi sauke ajiyar zuciya kafin ta ce

"Bilal ina ka kai ta ka san bai kamata ta rinƙa fita mai tsayi ba ba tare da guidance na kowa ba kuma ka
fi kowa sanim halin da take ciki i see no reason why you should take her out of the room"!!ita fah
magana take yi ba tare da ta lura da cewa ita Bilkisun kuka take risga ba sai da ta fara wata maganar
sannan ta lura
"Ni har na fara targeting Bahajjatu thinking ita ce ta fitar da ita daga ɗakin nan ashe ba ita ba ce kai
n...."a nan kalmar ta maƙale mata sakamakon fitinannen kukan da ta fashe da shi wanda daga cikin
zuciyar ta kukan ke fitowa sai ta yi hanzarin riƙe ta ta shiga tambayar me ya same ta a nan Bilal ke sanar
da ita abin da ya faru sai ta yi mamaki kenan dama ranar da ta mata bayanin komai bai shige ta ba kenan
ya ɓace mata a memory na ta but kamar wannan kukan ba akan ganin Zaid a halin da yake ciki bane
kawai is like there is something hidden beneath the tears but what could it be?rashin samin amsa ya sa
ta zaunar da ita a kan gadon ta fara rarrashin ta tare da bata magana ita duk a tunanin ta ganin halin da
Zaid ke ciki ne ya saka ta yin kukan though tana suspecting akwai ɓoyayyiya but since she refuse to say a
word sai kawai ta ƙyale ta after all bai kamata ta shiga damuwa ba da farfaɗowar ta haka da
wuri..rarrashin ta ta ke yi sosai har da gaya mata ai yadda ta farfaɗo ba tare da sun yi tsammani ba haka
Zaid zai farfaɗo shima akan ta dai yi mai addu'ar samin lafiya,sauraron Hajiya Madina ya zame mata dole
shi ya sa take sauraron ta ba wai dan maganganun ta na tasiri a zuciyar ta ba dan kuwa babu magana ko
ɗaya nata da ke shigar ta ko kaɗan har ta kai ayar maganar ta kuka kawai take yi daga ƙarshe dai kiran
doctor aka yi ya zo ya mata abin da zai yi seducing ɗin ta ta zamo calm..



Hakan aka yi dan allural anti depressant aka bata wanda babu jimawa bacci mai nauyi yayi gaba da ita sai
a nan suka sami kwanciyar hankali,Bilal dai ya kasa ganewa wannan murɗaɗɗiyar al'amari dan shi a iya
sanin sa babu wata jituwa tsakanin brother In-law da twin sis ɗin sa kafin su tafi outreach ɗin nan kuwa
he can swear that sam ba da niyar ta aka yi tafiyar ba but what later happened bayan tafiyar su?did they
manage to get closer to each other?did they understand each other in the course of their outreach?toh
wa ma zai ba shi amsa?babu dan haka ya ƙara ba ma Ammi haƙuri akan fitar da ita da aka yi ya sanar da
ita shi ke da laifi ba Bahajjatu ba dan sarai ya san halin Ammin sai ta balbale masa apple which he hate
more than anything,faɗa ta mai akan ya kiyaye fitar da ita anyhow saboda she is still in convalescence
stage bata da damar yin abubuwan da ta saba yi a baya sai a hankali zata mayar da jikin ta,haƙuri ya bata
kafin ya mata sai da safe dan yana son tafiya harhaɗa kayan sa na komawa.



Fitar sa babu jimawa Bahajjatu ta shigo ɗakin duk a ɗan ɗarare dan tsammanin ta Ammi ta san ita ce ta
fitar da Bilkisu har fitar ya janyo mata collapsing she thought Ammi is just waiting for her to give her a
sound slap dan Ammi bata tolerating shirme hatta da Hakim da ke babba da ita in ya nemi ja da yawa da
Ammin sai ta mare shi babu abin da ya shafe ta sai dai in abin ya lafa ta bi shi ta ja shi a jiki a nan zata
mai faɗa da nasiha sannan ta ɗora da rarrashi..

Sai ta ga akasin hakan sai ma ta ga Ammi tana tambayar ta ina ta shiga

"Baha ina kika tafi ga Bilkisu har ta famo rashin lafiyar ta Bilal ya fitar da ita ya kai ta ɗakin yayan ku now
she has collapsed ban san me yasa Bilal ya fitar da ita ba alhalin ya san halin da ta shiga i hate to see her
sleeping bana so it scares me"jin waɗannan bayanai na Ammi sai ta sami sauƙi a ran ta Allah sarki her
apple ya amshi laifin da bai da masaniya a kai duk dan yana gudun kar Ammi ta balbale ta.

Rungume ta tayi ta ce
"Is okey Ammi she will wake up inshaAllah zasu farka mu cigaba da yi masu addu'a kawai kin ji Ammi
na"?girgiza mata kai tayi suka kalle ta daga bisani suka fita suka ja ƙofar suka rufe mata dan ta sami
peaceful sleep..



************

A nan hotel apartment Hajiya Zeenat ce kwance tana kallon Dr Muhammad da ke ta faman bincike a
laptop dan ya kai kusan awowi uku yana faman binciken da ya ke yi wanda binciken ba akan komai bane
face akan remedy na rashin farfaɗowar Zaid Maher dan almost 4 days kenan ya fara research ɗin saboda
shi kwata kwata bai gamsu da 3-4months da doctor ya faɗa masu a matsayin period da zai yi spending
yana unconscious ba sam bai yi buying idea ɗin ba ya fi yarda da ya binciko makarin matsalar da kan sa a
matsayin su na iyayen sa dole su nemar mai lafiya dan wannan duk ba zai kawo masu kai ba time is
passing ba zai tsaya jiran kowa ba likewise if care is not taken they might loss him Allah dai ya kiyaye
baƙar ranar.wannan shine babbar dalilin sa na takura kan sa ba dare ba rana yana binciken abu mafi
sauƙi da zai samo masu hanya mai ɓillewa ba wai ya raina taimakon likitocin bane a'a but yana ganin
suna ɓata golden hours da suka samu dan su samarwa da Zaid lafiya shi yasa yake bincike binciken da
yake yi with the hope that in an dace Zaid na iya farfaɗowa within a month or less ba sai an cigaba da
jiran gafara sa ba'a ga ƙaho ba.

Yana tsaka da binciken sai ya ji hannun ta a kafaɗar sa tana mai massage kaɗan kaɗan,lumshe idanu
yayi kafin ya buɗe su ya ce

"Thank you so much"!!

Murmushi tayi da ta daɗe bata yi irin sa ba tace

"It's my pleasure my prof".

Ɗan shiru ne ya ratsa wurin kamar mintuna biyu sai ta ce.

"But prof me zai hana ka kwantawa ka huta in ya so anjima sai in ta da ka ka cigaba da research ɗin or i
might even help you you don't know"!!shiru ya mata dan shima ya san yana buƙatar hutun but he just
can't he have a task da dole ya ƙarasa dan haka ya ce

"Nahh sweetheart je ki kwanta zan cigaba i will join you later saura kaɗan in gama gabaɗaya ma
research ɗin dan mu sami hutu da sukuni dukkan mu humm"??ya zuba mata idanu amsa mai ta yi tana
mai jin tausayin sa na shigar sa madaɗin ta kwantan sai ta ta gyara kujerar kusa da shi ta zauna ya dube
ta da mamaki ya ce

"Baccin fah?kin san dai gobe ke zaki tafi asibitin nan dan ya kamata Hajiya Madina ta huta haka nan"!
amsa mai tayi ta ce

"I know but ba zan iya ba kin ga saura ƙiris in kammala dan Dr Maher bai da sukuni kuma kin ga after all
these hallacin da yaron nan yayi mana kafin Bilkisu ta amshi kwatan ragamar ayyukan nan namu ina
ganin kamar ta nan kaɗai zan iya saka wa mahaifin sa da family ɗin ma baki ɗaya i just need your prayers
and support"rungume shi tayi ta ce

"I know your purpose Dr na san dalilin ka kuma ina taya ka addu'ar samin nasarar wannan aiki da kaje yi
Allah ya ba su lafiya"da amin ya amsa daga haka suka cigaba da zaman shi yana aikin sa ita kuma tana
zaune beside him jefa jefa sukan yi hira.

Sallama suka ji an yi a ƙofar ɗakin sai ta miƙe ta nufi ƙofar,leƙawa tayi ta ga mai sallamar sai ta buɗe
haɗe da amsawa,bashi hanyar shiga tayi ya shigo ta mayar da ƙofar ta rufe suka ƙarasa shigowa parlorn
tare zama yayi ya gaida iyayen sa amsa mai suka yi kafin ya sanar da su dalilin zuwan sa akan komawa
gida fatan alkhairi suka mai haɗe da addu'ar kariya daga sharrin hanya da na ƙarfe..



A daren dai sai after 2 na dare suka rintsa dan sai da ya tabbatar da cewa ya samo ainihin doctor ɗin
nan wato Dr Ruzu shaharrren herbal doctor ne wanda ya shahara a fannin magungunan gargajiya da
sarrafa kayan itatuwa da ganyayyaki wurin samin makarin cuta duk tsananin ta wanda ko da mutum ya
kai shekara ashirin yana fama da cuta muddin ya baka magani toh inshaAllah kai da wannan cutar har
abada,shine likitan da watanni uku da suka gabata gwamnatin ƙasar china ta miƙo masa gayyatar su
akan ya dawo ƙasar ya zama babban likitan gargajiyar su a fadar shugaban ƙasar china saboda ƙwarewar
sa da hazaƙar sa da suka ji suka kuma gani wanda a ƙasar germany ɗin ma an san da shi ta fannin bayar
da magungunan gargajiya masu inganci,toh a rashin sani aka kusa rasa sa a ƙasar sa ta gado wato Nigeria
dan saura ƙiris ya amshi gayyatar gwamnatin ƙasar china sai dai wani mai yaƙi da ha'inci,mai muryar
talakawa,mai bawa marasa murya murya,uba ga marasa shi kai har ma da masu shi,adali,zaƙaƙurin
shugaba mai taimakon al'uma wato Dr ordinary president Ahmad isah shugaba a gidan radion Abuja mai
suna *HUMAN RIGHTS RADIO AND TELEVISION* yayi nasarar ɓarar da katin gayyatar da ƙasar china ta
kawowa likitan ya hambaɗa masu hayaƙin tsohuwa ta hanyar yin kane kane wun hana Dr RUZU amsar
gayyatar haɗe da nuna mai muhimmanci sa a ƙasar sa da kuma illar tafiya chan dan dama a ƙa'ida bai
kyauta a ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi ba wanda a tarihi kowa ya san ƙasar china ƙasa ce da ta shahara a ilimin
sanin ganyayyaki da itatuwa masu muhimmanci wanda ya kasance ɗya daga cikin hanyar income na
ƙasar dan hikimar su wurin tantance magungunan gargajiya da sanin hanyoyin amfani da su wa marar
lafiya kenan in har ƙasar Nigeria ta yi rashin irin wannan babban likitan gargajiya da kafatanin ƙasar
china aka rasa wanda yayi nasarar zama likitan gargajiyar fadar shugaban ƙasa kama daga ƙasar har
zuwa ƙasashen ƙetare na fararen fata har aka tsallako aka zo ƙasar bakaƙe ƙasar Africa a African na
yankin ƙasar Nigeria toh lallai da an yi babbar rashi but with the awareness being created by the
ordinary president to the genius herbal doctor Dr RUZU sai aka sami cigaba daga watanni ukun da
duniya ta kuma sanin sa sosai sama da da zuwa yanzu an sami marasa lafiya masu fama da cututtuka
daban daban kama daga paralysis either unilateral or bilateral paralysis,Diabetes Mellitus,cases related
to long hospitalization that can lead to unnecessary comma(kamar dai condition ɗin Dr Zaid Maher) and
so many other illnesses da asibiti ta kasa maganin sa shi yana ƙoƙarin sa wurin bayarwa wanda ba shi
kaɗai bane ke wannan ƙoƙarin ba wasu lokutan great herbal doctor ɗin nan ma wato pharmaciest Zainab
Sharif mai bada nata gudunmawar a fannin magungunan gargajiya har da ma dai ta yi kwana biyu da
barin aikin but one of her daughter is on the line wato tana karantar fannin herbal drugs a ƙasar Dubai
duk ta hanyar shugaba ordinary president Ahmad isah aka yi exploring waɗannan great herbal doctors
namu wanda in banda addu'a babu abin da za'a sakawa wannan great man da shi _(ilimi kogi ne faɗi ne
da shi ƙaryar ka ka ce za ka ga ƙarshen sa ba tare da ka samo abubuwa kala kala ba ciki har da na ƙwarai
da akasin sa,komai na da sanadi kasancewar Dr Muhammad Sulaiman great and best

Please Login or Register in order to submit comment