You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shawarar kar ta yarda wani abu ya shiga tsakanin su muddin bata
gama amfani da kayan da aka saba bata ba ta sanar da ita unda ta ɓoye mata su cikin trolley ɗin ta ne da
ke waldrop na ɗakin chan cikin ma'ajiyar ƙarshe a nan ta ɓoye mata..

Da ta gama karanta wasiƙar sai ta nannaɗe ta nufi waldrop haɗe da budewa ta ajiye papern a back zip
ɗin jakar sannan ta mayar ta rufe ta ɗan ƙara kallon kan ta a wayar ta sannan ta nufi hanyar waje,tunani
ne fal a ran ta dan sai yanzu ma ta tuna wai bata sanar da shi matsayin ta a gare sa ba ko ya zai ɗau
maganar Allah ne ya sani..



Da fargaba ta doso ɗakin tun daga ƙofar ɗakin take kallon sa ya jingina da pillow idanun sa a buɗe yana
kallon gefe ɗaya so she felt awkward abin da ta mai bai dace ba shi kaɗai ta bari tayi tafiyar ta ba tare da
ta tsaya ta saurari damuwar sa ba what if he hasn't taken his drugs mr kenan tayi a matsayin ta na matar
sa ai wannan babban abin kunya ne a gare ta sai dai ta daure ta shiga ɗakin fuskar ta ɗauke da
murmushin ƙarfin hali she is feeling clumsy already dan ta san bata kyauta mai ba wai ma tukun me ke
damin ta ne haka she get confuse easily kuma duk saboda tunanin Zaid ne.

Tsaye tayi daga tsakiyar ɗakin ta ƙi ƙarasawa sai ya lura ya kira ta

"Bilkisu akwai wata matsala ne"??very calm and gentile yayi maganar and so he drove her crazy and
insane ita dai bata san ya zata yi da Zaid ba sam she doesn't feel comfortable in har ya kira sunan ta kai
tsaye haka kuma gashi yanzu kamar da gangan yake kiran sunan dan ya ga yana causing mata effect..



"A'a babu wata matsala dama so nake in sani ko ka sha magungunan ka na safe na ga har 11am na son
gotawa"!!

Na sha magunguna na na safe??strange ya faɗa a zuciyar sa shi so yake ma ya san a wace ƙasa suke but
bata yarda ta bashi opportunity ba hakan ba ƙaramin danuwa ya janyo mai ba shiru dai ya mata yana jira
ya ga iya gudun ruwan ta.

Jin bai ce komai ba sai ta ji ta tsargu dan haka ta bar shi a ɗakin ta nufi inda nursing personnel suke ta
masu kwatancen ɗakin sa haɗe da tambayar ko an yi serving masa morning drug nasa..

Dubawa suka yi suka tabbatar mata da cewa ba'a bashi ba dan bacci yake yi sai ta ji mamaki wani irin
bacci bayan ta san idanu biyu ta bar sa kuma ta dawo ta tarar da shi a jingine alamar dai ba baccin yayi
ba maybe he pretended to be asleep dan kar a takura shi,,umartar su tayi akan su zo su bashi ya farka
dan haka ɗaya daga cikin su ta bi ta har zuwa ɗakin sa a inda suka gansa kwance shiru fara harhaɗa
magungunan tayi har ta gama ta matsa zata nufe sa dan bashi ya sha ai Bilkisu bata san lokacin da ta
dakatar da ita ba cikin kakkausar murya



"Excuse me young lady,,no need for all the unnecessary care just give it to me i will make sure he take
the drugs hmmm"?babu ko tsilin fara'a a kan fuskar ta sai baturiyar nurse ɗin ta mata wani irin kallo irin
kallon are you okey at all ɗin nan ke kika kirawo ni sannan kina min wani irin kallo??sai dai bata furta ba
ta bar ma kana ta yi gaba abin ta tana tunanin anya yarinyar nan bata da matsala a ƙwaƙwalwar ta
kuwa..



Da harara ta raka bayan nurse ɗin kafin ta sake tsaƙi ba tare da ta san ya kufce mata ba kafin ta kai inda
ruwan shan maganin yake tayi ƙwafa ya fi a ƙirga shi dai da ido yake ta bin ta dan shi kam yau ya ga abin
mamaki daga gare ta as smallish as she is amma ta iya yiwa matar nan rashin kunya what did she mean?
mr mme actions ɗin ta ke nufi?he have to ask her.
Kyaketa yayi ta gama zuba ruwan ta matso haɗe ce mai

" tashi ka zauna sai ka sha maganin"bin umarnin maganar ta yayi babu musu ko jan magana ya zauna ta
miƙo hannun ta ta ce mai ya buɗe bak,buɗewar yayi ta zuba mai haɗe da bin maganin da ruwa ya haɗiye
sannan ta gyara mai pillow ta mayar da kofin ruwan ta ajiye.

Dawowa tayi ta zauna ttana tunanin tambayar sa ko yayi wanka amma hakan ta daure ta tambaye sa
cikin sanyin murya

"An maka wanka ne"??sai ya ji abin banbaraƙwai dan haka ya bi ta da idanun sa wanda ya saka ta yin
ƙasa da nata idanun tana tsoron kar ya zarge ta akan abin da ba shine ba.

For a While sai ta ji sautin muryar sa

"A'a han yi ba me ya faru"??faɗuwar gaba ta ji sai ta kasa cewa komai har dai ya gaji da shirun ya ce

"Me ya faru na ce ban yi ba"!!cikin fargaba ta ce

"Toh dama zan taimaka maka me in ba zaka damu ba"da mamaki ya kalle ta ya girgiza kai ya juyar da
kan sa grfe sai ta ji ba daɗi dan haka ta ce mai

"Zaid taimakon ka zan yi ka yi wankan ka ga Hakim baya nan duk sun koma please let me help me dan
ka sami bacci mai daɗi humm"??shiru ya mata yana kallon ta ita bata son yadda yake kallon ta sam dan
haka sai ta kaear da fuskar ta gefe shi kuma ya ce da ita

"Kina so ki taimake ni saboda kina wa kenan"cikin tsoro ta ce

"Zaid am your wife and am here to help you get bath ka ga har chanza kaya na nayi dan in kaika wajen
building ɗin nan saboda ka yi saurin farfaɗowa gabaɗaya am not here tk harm you daga ni sai kai ne
kawai a ƙasar nan kuma saboda ina matar ka ne yasa aka bar ni tare da kai dan in kula da kai please Zaid
let's get you clean up dan mu fita ka ga waje ka ji"??ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba yayin da take maganar dan
saura kaɗan tayi fainting masa a wurin sakamakon yawan faɗuwar gaban da take ta samu yayin yin
maganan da shi ƙasa ma taje kallo dan ba zata iya cigaba da kallon sa ba..



Wani irin kallo ya ke mata wanda ya saka ta jin akwai idon wani a kan ta sai ta ɗago suka haɗa ido ta ga
irin kallon da yake binta da shi irin kallon nan can only mean one thing oh ya salam what did she get
herself into?ita da ke son dagewa dan kar ta yi ƙasa saboda ta taya shi farfaɗowa amma yake mata irin
wannan kallo haka?ya zata yi ina zata kalla ta sami sauƙi dama ta sani za'a sami matsala amma wannan
kallon da yake mata duk ya fi hargitsa ta da tsorata ta dan ita kaɗai ta san ma'anar kallon..




*_S,Ibraheem_*
Follow@siyamaibrahim



*_I heart u all masoya na 1 luv💋_*

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*20*



Cigaba da aika mata da kallon ɗaure jijiyoyin jik ya ke yi sai ta rasa ya zata mai bayanin itama ba da son
ran ta aka masu auren ba sai dan dalilai da dama kuma a yanzu ita bata son ya ji abin da zai ɗaga mai
hankali ko ya firgita sa dan bai kamata yana ƙoƙarin warkewa ba sannan ta ƙara danƙwafar da shi ba.

Tunowa tayi da maganganun yayan ta na fara ɗabbaka responsibilities ɗin Zaid a kan ta sannan tayi
resuming wifely duties nata ba tare da ɓata lokaci ba dan kula na musamman yake nema daga wun
makusancin sa wanda babu wani makusancin da ya fita a yanzu dole ko zai cigaba da yi mata wannan
murɗaɗen kallon sai ta yi abin da zai faranta mai.



"Zaid baka amsa min ba ka yi shiru..."!ƙarfin hali tayi har ta mai tambayar sai bai ce mata ƙala ba ya
cigaba da kallon ta.

She just hate the way he stairs at her bata jin sauƙi a zuciyar ta,bata ƙara second ba ta tashi ta shiga
toilet ta hau neman abubuwan da zata haɗa mai dan ya sami warm bath,bathing lotions ɗin sa ta
harhaɗa tayi regulating mai ruwan wankan a right temperature dan har sai da ta nemi bath
thermometer ta gwada ruwan wankan sannan ta shiga haɗo abin guaran fuska kama daga shaving
cream zuwa liquid face cleaners da su shaving stick,face mask da ake mannawa bayan an gyara fuska
saboda ya taimaka wun smoothening fuskar,mirror da cucumber paste duk ta haɗe su a cikin ƙaramar
tray da ke ɗakin wanda a ciki ake zuba kayan datti kamar sachet na magunguna da su kwalayen drips

Fitowa tayi da su sannan ta koma ta ɗauko warm water a bowl haɗe da ƙananan towels biyu ta dawo.

Ɗarɗar take ji amma ba zata iya cigaba da kallon sa yana son losing appearance ɗin sa ba kawai saboda
yana kan jinya a gadon asibiti ko ba komai ai shi ɗin mai matsayi ne a gare ta tunda har hukuncin Allah
ya sa ta zamo matar sa..

Ko kallon kwayar idanun sa bata yi ba ta shiga mixing abin buƙata har ta kammala sannan ta ce mai
cikin tsare gida

"Zan maka gyaran fuska ne kafin ka yi wanka please cooperate"..bin ta da ido yayi kamar wanda bai da
bakin magana sai ido,haɗa ido tayi da shi ko second bata ƙara ba ta cire nata idanun daga nasa haɗe da
cewa

"Let's begin"bata tsaya jiran sa ba ta hau ɗeban shaving cream na kamfanin aloe vera ta zo dab da fuskar
sa tana tsoron kar ya dakatar da ita sai dai ga mamakin ta sai ta ga ya ajiye mata fuskar ba yabo ba
fallasa hannun ta na ɓari ta kai kan fuskar sa wanda ba ita kaɗai ba har shi sai da ji electrification da ya
haɗe a yayin da hannun ta ya taɓa fuskar sa.
Kasa janye hannun ta tayi sai ta bar shi wu guda tana kallon sa yayin da shima ita yake kallo,kallon kallo
suka tsaya aikawa juna har suka ɗau lokaci mai tsayi ba tare da sun sani ba,bata farga ba sai da ta ji
sautin muryar sa cikin gajiya ya ce

"Auchhh"!!a nan ta tuna cewa ta bar hannun ta mai ɗauke da cream a kan fuskar sa a wu ɗaya,cikin
sauri ta cire hannun bakin ta na ɓari muryar ta na karyewa ta shiga ce mai

"Am...a...m...amm so.oo..rrr...yyy"kallon ta yayi ita kuma tayi saurin ɗaukar hand towel ɗaya ta shiga
hoge mai part ɗin da ta bar hannun nata,ko da ta kai towel ɗin da nufin goge cream ɗin sai ta ga har
suman wurin ya karye yayi laushi sai ya fita,cire towel ɗin tayi daga kan fuskar sa tana kallon towel ɗin
shima towel ɗin ya ƙurawa ido,at the same time suka ɗago suka zubawa junan su idanu sai chan ta cire
nata idanun daga nasa tayi ƙasa da idanun cikin in ina tace

"Kayi haƙuri ban lura bane"..

Ci kanki bai ce da ita ba sai ya kawar da fuskar sa dan haka ta bi sa ta direction ɗin da ya juyar da fuskar
sa ta kai hannun ta cikin tsantsene da hikima ta shafa mai cream a fuskar,a hankali ta shiga murza mai
cream ɗin tana yi tana kallon reaction na sa dan tana gudun kar ta kuma maimaita abin da tayi earlier
on.

Da ta tabbatar cream ɗin ya bi ko ina a fuskar sa sai ta koma kan suman kansa da ya taru har ya wuce
misali,in bata manta ba gyaran suman sa yayi shige ne da na boys scout mai fasali na zamani dan haka
tayi picking scissors da ta ɗauko musamman dan gyara mai sumar.



Yana kallon ta da idon sa kamar wani saƙago wanda aka sassaƙa sai an bashi umarni yake iya aiwatar da
abu,kaɗan gently ta fara bin suman tana yankewa a hankali dan kar wani wun ya fi wani wun tsayi ko
gajerta,a haka a haka har ta yi leveling suman zuwa desired look da ta gama ne ta dawo kan fuskar sa
tayi amfani da hand towel ta goge mai fuska sannan ta bi sajen sa ta yi amfani da brush ta rinƙa taje shi a
hankali har ta kammala sai ta ɗau face mask ta manna mai sannan ta koma kan suman kan sa ta shafa
mai wani exotic hair wash ta cuccuɗa tana gamawa ta cire mai face mask ɗin ta shafa mai cucumber
paste sama sama shi dai yana kallon ta ƙala bai ce da ita ba hakan kuma ya mata daɗi dan ta sami
ɗaukewar kashi casa'in a cikin kashi ɗari na fargabar da ta rinƙa samu kafin ta fara mai gyaran ga irin
kallon ƙur da ya rinƙa mata ɗazu sarai ta gane ko kallon menene sai dai ita kam tayi alƙawarin enduring
duk wani maganganun zafafa zuciyar da zai mata dan dole a matsayin ta na matar sa ta koyi shanye duk
wasu rigingimun da zai taho mata da su addu'ar ta ɗaya kar Allah ya bashi ilimin tambayar ta Asma'u dan
ji take kamar zuciyar ta zai buga a duk lokacin da ta tuno yarinyar abin da ya faru da su bai mata daɗi ba
ko kaɗan hakan ya sa ta ɗau tsanar duniyar nan ta ɗora shi akan Asma'u dama chan jinin su bai haɗu ba
bare yanzu da take ganin itace ummul aba'isin na janyo masu matsalar da suke ciki dan haka bata jin
zata iya yafe ma yarinyar so soon dan yanda take jin zafin abin da yarinyar tayi ko shi da ya aikata
ta'addancin bata jin zafin sa kamar yadda take jin na yarinyar..
Kusan tun da ta fara har ta ida a halin kurame suka yi gyaran fuskar sai da ta kammala ta mai kallon
tsanake ta ga ya fito a ainihin Dr Zaid Maher ɗin sa though akwai wasu tranaformational changes da ya
faru a jikin sa kamar ramar da ya ɗan yi alamomin jinya da ya nuna a fuskar sa sai gajiya da yake tattare
da shi..



Magana ta mai cikin ruwan sanyi ta ce



"Na gama duba ka gani in akwai wani wurin da kake so a ƙara gyarawa sai ka sanar da ni"!!kallon
mamaki yake mata dan maganar ta na kan yi mai yawo a ƙwaƙwalwa wai ita ɗin matar sa ce gaske ne ko
ko rainin hankali ne dan ta ga he is helpless.

Kallon sa itama take yi tana jiran jin amsar sa sai dai har ta gama ƙiyastin ta bai amsa mata ba ya ƙyake
ta kuma wannan guilty look ɗin yana nan yana bin ta da shi kasa jurewa tayi sai ta miƙe tsaye tana mai
gyara mayafin ta.

"Wanka zaka yi bari in taya ka ka shiga toilet"!!wani razanannen kallo ya bita da shi she must admit that
ta gigita da kallon saidai bata bari ya gane hakan ba ta ɓoye ta cigaba da abin da take yi

"Mu je kar ruwan yayi sanyi"!!kai hannun ta tayi ta riƙo nasa a hankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga sa with the
hope that zai taya kan sa tashi in yaga effort da take yi sai dai bai taya ta ɗin ba dan daɗa ƙara weight ɗin
sa yayi a kan gadon tayi tayi ya tashi ya ƙi sai ta ɗago ta haɗa ido da shi ta mai alama da ido akan ya
tashin mana amma yayi shunning nata sai ta gane ashe ba wai weakness ne ya sa ya kasa taimakon
kansa dan tashi ba a'a kawai ra'ayin sa me yin hakan sai ta haɗiyi wani abu da ta ji ya taso mata ta cigaba
da trying dan dai ya tashin amma ya ƙi.

Bai tashin ba ita kuma bata karaya ba ta cigaba da ƙoƙartawa dan kan shi ya tashin dan ya ga kamar ta
fara gajiya har zufa take yi,yana tashi tayi tanga tanga kamar zata faɗi sai dai ta yi saurin regaining
balance shi kan sa ya tsorata da ya ga zata faɗi sai dai da tayi regaining balance ɗin ya sami relief amma
bai nuna ba ita kuwa ko a jikin ta ta matso ta riƙe sa ta baya ɗaya hannun ta na riƙe da nasa hannun a
haka suka fara takawa har ta kai shi bakin toilet ta rasa me zata yi shin ta raka sa har ciki ne kokuwa ta
bar sa ne a bakin toilet.



Tsayuwar ya fara gundurar s sai yayi tsaki hakan ne ya fargar da ita har ta ruɗu bata sani ba ta cigaba da
tafiyan yana bin ta suna takawa ta kai sa har kan bathtub ɗin ya zauna dama komai ta tanadar mai
wanda zai baƙata ta kawo mai bath throb kusa da shi ta ajiye su sponge da bath liquids daga haka ta
kalle shi cikin tausayi ta ce

"In ka gama ka sanar da ni sai in zo mu fita"..
Wannan kallon baƙuwar ya bita da shi ita dai tayi gaba dan gani tayi kamar tunda ya farfaɗo bai da wata
ɗabi'ar da ta wuce na kallon ta dan ko sauran mutanin da ke kewaye da shi baya masu kallon da yake
mata takan rasa ma'anar kallon.



Dawowar ta ɗakin ne ta shiga gyara mai gadon sa ta canza bed linen ɗin ta share ɗakin da electric
cleaner ta biɗe waldrop ɗin sa ta shiga kallon kayan nasa dan tantance wannene zai fi masa sauƙi
sakawa,bayan dube duben da ta yi sai ta fiddo mai da Tom ford tuttle neck top ash colour ta haɗa da
black jeans,white singlet ta ɗauko,muffler ash colour ta haɗo da sai head warmer ash mai tuntu baƙi,
takalmin sneakers baƙa mai tambarin NBA da aka yi shi da ash colour gyara shoelace ɗin tayi daga yadda
aka saka shi zuwa wani iri ta yadda zai ƙayatar.mayar da waldrop ɗin tayi ta rufe ta dawo da kayan a
hannun ta a kan gadon ta zuba su daga nan side drawer ta buɗe ta duba kayan shafar sa ta fito da su ta
ajiye a saman drawer ɗin.



Zaman jiran alamar gamawar sa take yi time to time takan kalli agogon hannun ta dan ganin time in ta
haɗa duka time ɗin da yayi spending a toilet zata iya cewa ya sami kyawawan mintuna arba'in a toilet
ɗin nan wanda ta san ko da wani irin wanka ne wannan da yake yi ya ci a ce ya kammala but me yasa bai
yi alerting nata ba wata zuciyar ce ta bata amsa da cewa ta yaya zai yi alerting ɗin ki bayan ke kanki kin
san kallon da yake miki ba irin kallon ya gamsu da ke a matsayin matar sa bane sai ta yi tunanin in har
kuwa so take Zaid ya amince cewa ita ɗin matar sa ce toh dole sai ta yi mai abin da zai fahimci hakan har
ma ya gamsu da haka.



Wannan tunanin ne ya ingiza ta ta taka har zuwa bakin ƙofar toilet tana mai tambayar sa a hankali

"Zaid ka gama wankan ne"!!sai da ya ɗau lokaci sannan ya amsa da

"Uhum"kamar dai marar baki haka ya amsa mata.

Tura ƙofar tayi ta shiga kan ta a ƙasa har ta zo kusa da shi dan zaune yake a inda ta bar sa kafin ta fita
kenan bayan ya gama wankar ne ya koma ya zauna a gefen bathtub ɗin ɗaure da bath throb da ta bar
mai ƙafar sa sanye cikin slippers bath throb ɗin bai kai mai har ƙasa ba amma da kaɗan ya rage ya kai
ƙasan space ɗin da yake expose a ƙafar sa abin kallo ne dan suma ne kwance sakamakon ruwan wankan
da ya taimaka wun kwantar da suman fatar jikin sa sai glowing ƙafar ke yi.

Kai hannun ta tayi ta riƙe sa suka fito tare daga nan ta zaunar da shi a kan kujera ita kuma ta ɗauko
towel dan goge mai kai daga tsayen ta bayan sa ta riƙe towel ɗin ta shiga goge mai kan tana yi tana
massaging kaɗan kaɗan gently har ta gama sannan ta dawo ta zauna a saman gadon suna kallon juna ta
ɗauko body lotion da ta fito da su ta matsaa hannun ta ta murza tsugunawa tayi ta shiga shafa mai a
ƙafar sa ta dama ta ɗago ta kuma matsowa ta murza ta tsugun ta shafa mai a ƙafar hagu daidai inda
towel ɗin ya rufe da kaɗan wato gwiwar sa a nan take jan burki dan bazata iya shafa mai duka ba da ta
gama ta hau shafa mai a hannun sa shi kam abin na bashi mamaki ba dan komai ba sai dan farin sanin da
yayiwa yarinyar dan first class ce wun girman kai da izza amma sai gashi yau ya nuna mata attitude ta
hanyoyi daban daban duk dan ta san cewa shi fah ba yarda yayi da abin da ta gaya mai ba wai ita matar
sa ce amma bata nuna ko a fuska ba akan abin ya mata ciwo ko ya ɓata mata rai ba me yasa haka.

Jin muryar ta yayi tana ce da shi

"Na gama saura saka roll-on gashi saka"ta miƙa mai kallon roll-on ɗin yayi kafin ya kalle ta ta amsa mai
da kai akan ya karɓa ya shafa,karɓa yayi ita kuma ta shiga mayar da cream ɗin leaving a little gap da zata
mayar da roll-on ɗin in ya gama amfani da shi ko da ya gama shafawa bata jira sa ba ta karɓa haɗe da
miƙo mai fogg body spray ta ce

"Ungo ka fetsa"she behave gentile and kind it amuses him.

Karɓa yayi ya fetsa haɗe da miƙa mata ta ƙarba ta haɗa da roll-on ta mayar a drawer daga nan ta tashi
dan miƙo mai kayan sa da zai saka sai ta tuna bata ɗauko mai boxers basai ta koma ta buɗe ta hau
dubawa hangowa tayi an yi hanging nasu a wasu hangers sai ta ɗau ɗaya ta juyo da shi ta miƙo mai kan
ta a ƙasa.

Nan ma sai da ya mata kallon stranger sannan ya karɓa sai ta juya mai baya dan ya sami privacy ya saka
hankali kwance.

Da ya gama sakawa bai mata alamar ya gaman ba sai ya cigaba da saka sauran kayan ya saka inner wear
ya ɗau top ya saka ya ɗau jeans har ya fara sakawa sai ta ga kamar ya kamata a ce ya gama saka boxers
by now sai ta juyo dan miƙo mai rigar da zai saka sai dai tana juyowa idanun ta bai sauka a ko ina ba sai
kan jeans trouser da yake hannun sa ga rabi ya wuce rabin ƙafar sa sai tayi gaggawar runtse idanun ta
tana jin faɗuwar gaba oh ita me ya kai ta juyowa yana cikin halin nan har zata juya ya dakatar da ita ya
ce

"Get me a belt"!!

Da sauri ta isa gaban waldrop ɗin ta buɗe ga belts ɗin nan a gaban ta but abin mamaki shine sam bata
lura da shi ba sai da ta gama kalle kallen ta sai chan ta ga belts ɗin a gaban ta dan haka ta ɗau ɗaya daga
cikin belt ɗin ta ɗan tsaya gudun kar ta kuma yin gamdakatar da abin da ta gani ɗazu,



Ya san tsayawa tayi dan kar ta gan sa a halin da ta gansa ɗazu sai yayi gyaran murya.hakan ne ya bata
damar juyowa dan alama ce da ya gama saka kayan.

Miƙo mai tayi tana sinne kai ƙasa karɓa yayi ya shiga sakawa ita kuma tana kallon ƙasa da ya kammala
sai ta kwaso takalmin ta kawo mai kamar dai ta bar shi ya saka da kansa sai kuma ta fasa ta durƙusa ta
shiga saka mai takalmin da ta gama ta ɗaure shoelace na takalmin tana gamawa ta miƙo mai oud perf
mai ƙarfin ƙamshi ya fetsa sannan ta karɓa ta mayar muffler ta saka mai a wuyar sa ta ɗau head warmer
ta saka mai sannan itama ta gyara gyalen ta ta ɗau wayar ta da nasa ta riƙe a ɗaya hannun ta da ɗaya
hannun ta riƙe sa tunda ta ga kamar yana da ƙarfin jikin sa baya buƙatar much help haka nan tashi yayi
da taimakon ta daga haka suka shiga takowa har suka fito kamar kurame bata ce da shi a ba bai ce da ita
uffan ba da suka fito ta saka ma ɗakin security pin ya rufu sannan suka cigaba da takawan.



Ta baya suka bi suka fita daga asibitin baki ɗaya akwai wani garden mai

Please Login or Register in order to submit comment