You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗauke da park na wasanni chan
suka nufa tun daga nesa take son fara jan sa da magana sai dai hakan ya ci tura dan bayan kallon gaban
sa da yake yi baya kallon ko ina gashi fuskar kamar an mai dole.

Daurewa tayi dai ta ɗago da maganar

"Ni kam Zaid in tambaye ka mana"cikin taushin murya tayi maganar wanda ƙaryan mutum musamman
ɗa namiji ya ce an mai magana ta wannan siga bai ji shi har cikin tsokar jikin sa ba amma da yake Dr Zaid
Maher is almost back to his Dr Zaid Maher sai yayi pretending bai ji abin da ta ce ba and so she have to
ask again

"Zaid na cein tambaye ka mana"!! Sai a nan ya ce

"Uhhhnn"irin ina jin ki ɗin nan tsabar jin haushi bata san lokacin da ta ce da shi

"Damuwar ka"ba abin sai ya so bashi dariya amma ya mazge kamar dariyar bata taso mai ba saboda out
of frustration tayi maganar ba tare da ta san zai fito da sautin haushin da ta ji ba.



Sai da suka yi nisa a takawar sannan ta ji sassaucin abin haushin da ya mata har ma ta tuna da abin da
ta yi mai na demonstrating ɓacin ran ta a gaban sa.

Bata ce da shi komai ba ta ƙyale sa kamar dai yadda yayi shiru shima.

Da suka ƙarasa cikin park ɗin ne suka nemi wun zama ta bar sa a nan ita kuma ta ƙarasa zuwa ciki wun
masu saida kayan sanyi dangin su smoothies,icing,vinegar icing,ice creams,da dai sauran su ordering
vinegar icing tayi ma kanta shi kuma ta karɓo masa smoothie,master card ɗin ta ta miƙo masu suka yi
transferring haɗe da miƙo mata card ɗin ta ce da su thanks.

Daga nan wun masu siyar da kayan ciye ciye ta nufa inda akwai abubuwa da dama kamar su
cookies,spring rolls,sandwich,hot pizza,hamburger,da sauran easy chops.

Hamburger ta karbawa kanta shi kuma ta kaeɓo mai cookies though bata sani ba ko yana ci ko baya ci.

Nan ma transferring aka yi aka miƙo mata card ta juyo ta nufo inda ta bar shi tana ɗan murmushi dan
tunowa da ranar da suka haɗu a theater room yana surgery babu assistance sai anaesthetics ran nan a
haɗe ita kuma ta rantse ba zata taimaka mai ba dan bai nemi taimakon nata ba gashi babu wasu likitocin
kaf suna off ranar ma emergency surgery ne ya taso ita kuma ta zo duba patient ɗin ta sai ta ga yana
buƙatar taimako amma rashin tambayar alfarma daga gare ta ya sa ta shiga surgery room ɗin tayi zaman
ta tana kallon sa har ya gama da taimakon anaesthetic nurse yana gamawa tayi tafiyar ta shi kuma ya
rinƙa bin ta da kallon takaici.



Tana isa kusa da shi annurin fuskar ta ya kau ta zauna haɗe da miƙo mai abin da ta siyo mai karɓa yayi
ya ajiye a gefen sa sai ta juyo ta kalle sa ta kalli gefen da ya ajiye abin da ta kawo mai sai ta juyar da kai
ta ce

"Uhumm"daga haka ta fara shan ice vinegar ɗin ta tana sipping kaɗan kaɗan babu wanda ya ce komai a
cikin su shi ya zuba ma park idanu yana kallon wasannin yara dama ƴaƴan turawa da rashin ji in an ce su
bari basu bari,wani ɗa ne ke faman throwing tantrum kawai saboda an hanasa shiga cikin anaconda na
wasa da ke park ɗin, uwar tayi tayi ta rarrashe sa amma ya ƙi jin ta sai kuma uwar ta koma bashi haƙuri
madaɗin yayi shiru sai ya ƙi yin shirun ya saka mata kukan banza



Duk event ɗin nan a kan idanun Bilkisu da Zaid ake yin su,gajiya Zaid yayi da kallon rashin ta ido irin ta
ɗan sai ya miƙe a hankali ya shiga takawa har ya isa gaban su a hankali ya durƙusa ya riƙe hannun ɗan
yana kallon sa yana son sanin damuwar sa

"Hey kiddo whats up"sai yaron ya kalle sa idanun sa cike da hawayen shagwaɓa ya ce

"Momma doesn't wanna let me play with the anaconda she didn't allow me to play with the cobra all
my buddies are there play with the anaconda but momma isn't listening to me she doesn't want me to
play around i just wanna go home"..

Kwata kwata yaron ba zai wuce 5years ba a shekaru kuma daga dukkan alamu yana da tsiwa da rashin ji
sai ya murmusa ya shafa kan yaron yana cewa



"Common cobra tell me when momma says you shouldn't play and stops you from playing what does it
signifies"??sai yaron ya ƙurawa Zai ido kafin ya ce

"It signifies that something dangerous is there"cikin gamsuwa ya tari yaron ya ce

"Good cobra,that's it momma have seen something bad and that is why she didn't allow you to play
there with your friends"sai yaron ya kyaɓe fuska ya ce

"But i wanna play buddy"abin dariya one sided smile Zaid yayi sannan ya ce

"Tell me kiddo are you sure you not scared of anything"??sai yaron yayi shiru yayin da mahaifiyar ɗan
ke kallon su cikin admiration dan dai ta san wannan stranger ɗin ba ɗan ƙasar su bane but yana da kirki
gashi har ya fara gano matsalar ɗan nata da ita kanta ta kasa rarrashin sa but ga wannan yana ta jan sa
da hira shiru ta yi tana kallon su tana murmushi.
Amsar da ɗan ya bashi ne ya sa ya ji tausayin yaron

"Buddy am scared of darkness"sai ya ce da shi

"And i think the anaconda is dark what did you think"??a rikice yaron ya ce

"Yeah the anaconda is dark"sai ya ce

"And you are scared of"?? ai a mugun tsorace yaron ya ce

"Darknesssss"da gudu ya shige bayan mahaifiyar sa yana ɓoyewa tsabar tsoro sai ya shiga cewa

"I don't wanna go i hate darkness i hate anaconda"sai Zaid yayi murmushi cikin ruwan sanyi yayi
handling abin da mahaifiyar ɗan ta kasa yi wai dan ma ɗan turawa ne in ba dan haka ba da da iron hand
zai yi handling ɗin sa dan shi ya tsani rashin kunya kuma that is exactly what the boy is doing kuma uwan
na kallon sa imagine..



Miƙewa yayi ya juya zai yi tafiyar sa sai mahaifiyar yaron ta dakatar da shi ta hanyar ce mai

"Thank you young man,my son Andrey is having a disorder he have claustrophobia he get scared easily
and that is why i don't allow him to play all alone his friends are used to playing alone and they might
forget him while playing he can get into harm i don't hope for that"sai ya gyaɗa mata kai alamun ya gane
sai ya ce da ita

"I understand Ms... "?sai ta ce

"Mcsantos am Elina Mcsantos nice meeting you"sai ya ce

"Me too"da murmushi ya juya zai tafi ta kuma dakatar da shi

"And you are"sai ya ce

"Call me Zaid"sai ta ji abin banbaraƙwai dan haka ta ce

"Just Zaid"?da murmushi ya ce

"Dr Zaid Maher"cikin amusement ta ce

"Wow nice name but i will address you by Dr ZM did you like it"??sai ya ji mamaki kamar an sanar da it
ɗaya sunan sa da aka saba kiran sa da shi a asibiti sai ya ce

"Sure"da fara'a a kan fuskar sa ya juya zai tafi sai ta kuma ce mai

"That beautiful lady..is she your spouse"??abin sai ya ɗaure mai kai ya manta shaf wai ta gaya mai shi
ɗin mijin ta ne sai ya rasa me zai ce ma Ms Mcsantos ga ta da surutu ta ya ma aka yi tambayar ta ta kawo
wannan gaɓar ya ma aka yi ta hango baby doctor sai ya ji bakin sa ya mai nauyi me zai ce wa matar dan
shi kam bai yarda da zancen baby doctor ba wai ita matar sa ce haka kawai kai tsaye ake yin aure.

Jiyo muryar ta yayi cikin fushi tana cewa

"Yes am his spouse you have problem with that"??ta faɗa tana mai zaro mata rikitattun idanun nan nata
da suka fara canza launi dan ɓacin rai sai matar ta tsorata ta ce

"No..i don't but you got a good and caring husband"cikin gundara da maganar matar da gajiya da kallon
mummunar fuskar ta kamar dai yadda ta laƙaba a ran ta ta ce da ita

"I know"da murmushin haushi ta bi matar sai matar ta tsorata da irin kallon da ta bita da shi sai ta ce

"Just complimenting"a harzuƙe ta riƙo hannun sa suka fara tafiya tana mai ce ma matar

"We don't need your compliment"a haka suka tafi sai bambami take yi wai matan turawa basu da
kamun kai da mazajen su but da zarar sun ga wasu mazan jikin su ya shiga ɓari kenan ko abin da ta siyo
masu bata bari sun ɗauka ba ta ja shi suka koma asibitin yana binta da kallon mamaki why is she
behaving so strange in ta gan sa tare da mata...



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*
*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*22*

*_First move_*




_Next morning_

_*8:45am*_



Shigar white Burberry slim-fit shirt ne da wandon Calvin Klein baƙa sai takalmin Jason of Beverly hills
mai silver white colour hannun sa saƙake da agogon Daytona Rolex baƙa wuyan sa kuwa saƙale yake da
muffler baƙa sai hular sanyi da ya saka na kamfanin Balmain kalar ta ɗaya da takalmin ƙafar sa idanun sa
sanye cikin black goggle,ga doguwar jacket mai kalar ƙasa da ya riƙe a hannun sa daga dukkan alamu dai
sakawa zai yi in ya fito,tsaf ya fito cikin shirin fita yawon zaga gari wanda shi dan kan sa ya haɗa fitar ba
tare da sanin taba dan kamar abin shammaci zai mata sakamakon alkhairan da take mai tsakanin ta da
Allah wanda ya san ko da wata nashi ce ta jini iya abin da zata mai kenan dan haka da wannan ƙudirin ya
kwana a ran sa sai dai bai nuna ba bare ya sanar da ita.



Kwance take ɗaure da towel orange colour mai ɗan girman kan ta lulluɓe da hular wanka,komai bata
saka a jikin ta ba dan tun da ta fito ta kwanta a nan a ƙalla ta kai awa guda tana kwance kamar bata
ɗakin tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa lokaci zuwa lokaci.
Bata ankara ba ta ji an turo mata ƙofar ɗakin a 360° ta yi wani juyin masa ta jawo bed sheet ta naɗe kan
ta a ciki tana ta faman zazzaro idanu waje dan ta san babu wani mai shigo mata kai tsaye daga ita sai shi
ne a apartment ɗin in ba shi zai shigo mata ba babu wanda zai yi barging mata kai tsaye haka.

Tana kai duban ta ga ƙofar ɗakin tayi arba da shi cikin shigar da ba kasafai yake yin su ba sai lokaci
lokaci.

Wani ihu ta tsala dan ganin yadda ya kafe ta da ido alamu dai ya nuna ya gama kalle ta tun ɗazu bata
sani ba dan ya sakankance ne a yayin da ya zuba mata idanun sa abin da ya tada mata hankali kenan har
ya sa ta sake ihun dan a wun ta kamar ta cutu ne kallon ta da yayi kusan gakf naked babban abin cutuwa
ne a gare ta.



A rikice cikin rasa abin yi ya ja dabaya haɗe da turo mata ƙofar yana panting kamar wanda yayi tsere
yana mamakin dalilin ta na yin ihu ana zaune lau anya lafiyar ta ma ƙalau kuwa.??



Kuka zata yi ko hauka ta rasa toh shima me ya kawo sa ɗakin ta kai tsaye babu alama ko sallama,ita bata
taɓa yi mai shigar kai tsaye ba gudun kar tayi tozali da abin da bai kamata ba amma shi ya shigo kai tsaye
kuma ai ita ta saba zuwa duba sa ba shi ba dan me zai mata shigowar bazatta?ya gama da ita...

Wani zuciyar ke sanar da ita ai ba laifi bane dan ya gan ki a haka kin manta shi ɗin mijin ki ne kuma ya
halasta ya gan ki a halin da ya fi wannan??sai kuma ta ji kunya da haushin kan ta why did she react in
this way..

Haushin kan ta taji sosai dan ba girman ta bane at least she is 25 ai ta san do and dont's na ma'aurata
dan ta sha gani haka zalika tana da ilimi da hankalin tantance fari da baƙi..



Daga wajen ya ɗan ɗaga murya ya ce



"Good morning"!!!bata amsa ba sai ta ce

"Uhmm"what?ya tambayi kan sa dan mamaki ta ba shi sai ya kuma cewa

"In kin gama ki fito zamu tafi wani wuri ina jiran ki"

Sai tayi kasaƙe tana tantaman anya daidai kunmuwan ta suka jiyo mata Zaid na faɗin in ta gama ta fito
wani wun zasu?da wa?da shi?sai tayi shiru bata sauko daga kan gadon ba tana nan nannaɗe da zanin
gadon kamar dai tana ganin sa a ɗakin har lokacin.
Shiru shiru bata fito ba ya kai duban sa ga agogon hannun sa ya duba ya ga mintuna ashirin da shida
sun wuce kuma bai ji alamun ta ma sauko ba bare ta shirya sai ya tashi daga inda ya zauna zaman jiran ta
ya nufi ƙofar ɗakin ta ya shiga danna mata alarm bottom.

Cikin firgici ta ɗago ta mai da idanun ta kan ƙofar tana jin faɗuwar gaba take huɗubar Ammi ya dawo
kan ta inda take sanar da ita wai kar ta yarda Zaid ya san ta a ƴa mace sai har ta kammala shan
magungunan ta dan Zaid ya iya tsara zance muddin akan abin da ya gani yana so ne.

Wannan huɗubar ne ya kuma ruɗa ta da tunanin ta har dai tayi making mind ɗin ta akan in ta kuskura
ta biye mai toh ba shakka zai kai ta ya baro dan haka ta mai banza sai da ta ji ya kuma pressing bottom
ɗin sannan ta ɗaga murya ta ce

"Zaid i can't come with you....,,just go alone am sick"jin ta kira sunan sick a kalaman ta sai ya turo ƙpfar
gabaay ya shigo yana nuna alamun mamakin rashin lafiyar ta dan lafiya ƙalau suka rabu jiya toh me
kuma ya same ta hala shi yasa ma bata zo ta tashe sa da asuba ba.

Ko da ta ga ya bankaɗo ƙofar sai ta tsala ihu ta shiga masife shi tana cewa

"Zaid get out...out...how can you be barging into my room without my permission...get lost....you
wanna see me naked or what...arrrrggg..ka fitar min a ɗaki nace bana zuwa ba zan je ba just go out"!!!da
matuƙar fushi ta ƙarasa maganar wanda ya ɗan yi shaking nasa kaɗan sai dai bai biye mata ba instead ya
tsaya clearing kan sa a wurin ta ta hanyar faɗa mata shi bai gan ta ba ko ɗazu da ya shigo amma ina ta
tuɓure ta ƙi yarda ta kafe akan lallai lallai ya gan ta shi kuma na natse da rantse mata a kan bai gan ta ba

"I swear i didn't see you"ya faɗa with sincerity a idanun sa sai ta natsu bata ce komai ba har sai da ya
kuma nanata mata sannan ta ce

"And now?ka ganni"??sai ya kuma zama serious kafin ya ce idon sa cikin nata alamun assurance



"Not at all baby doctor...ban gan ki ba"!!sai ta cigaba da kallon ƙwayar idanun sa kafin ta ce

"Ka tabbata baka ganni ba"??cikin gaskiya da gaskiya ya ce

"I swear".....



Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyin gaske wanda ya bashi mamaki toh me na ɗaga hankalin ta dan ya gan
ta?sai yayi bouncing maganar ma ya ce

"It's her perception and hallucination"a zuciyar sa yayi maganar yana mai furzar da iska.
Kusan mintuna uku suna a haka ya fita bai fita ba ta tashi bata tashi ba sai daga bisani tayi gyaran
murya haɗe da ce mai

"Excuse me"!!cikin sauri ya ce

"Sure"!!amma me?sai bai tashi ba ya cigaba da maintaining eye contact da ita sai da ta kuma nanata

"I said excuse me Zaid"da ɗan ɗaga murya ta yi maganar wanda ya saka shi dawowa hayyacin sa sai ya
tuna ashe fah hide and seek puzzle ake yi shi kuma ya zauna..

Tashi yayi cikin daburcewa yana in'ina yana faɗin



"Errrmmm..so...sorrry..ina jiran ki a waje sai kin fito"!!ya fita cikin sauri,ko kallon sa bata yi ba dan a
takure take da zarar yana kusa da ita shikenan natsuwar ta ya kau haka ma tunanin ta ya tsaya har sai ya
bar wurin..

Halan ba sai ta tafi wun psychologist an duba lafiyar ƙwaƙwalwar ta ba kuwa?..



Miƙewa tayi ta nufi waldrop ɗin ta ta buɗe ta fito da wata Chloe top and trouser cream colour ta ɗau
ƙaramin gyale baƙa amma haɗe yake da hijabi ana iya yafa shi a naɗa kamar gyale mai hula.

ta ajiye a kan gado haɗe da ɗauko pins da zata kama gyalen da shi,takalmin boot na fata mai kalar ƙasa
ta ɗauko mai tsayi wanda ya kai har kusa da gwiwar ta mai siraran rope lace da ake ɗaura takakmin da
shi dan samin comfort a ƙasar takalmin kuwa tsini ne kamar dai hills haka yake,ɗaukar babbar Alexander
McQueen jacket mai tsayi har gwiwar ta ta haɗa da muffler cream colour.



Bayan ta gama saka inner wears ɗin ta ta saka kayan sai da ta yi rolling veil ɗin ta saka ta ciki sannan ta
ɗora jacket ɗin sai gyalen ya kasance yana rufe cikin jacket ɗin,naɗa muffler ɗin tayi a wuyan ta ta ɗau
ƙaramar side bag cream colour ta saka wayar ta da tablet a ciki sai room keys da ke hannun ta ba wani
make up sosai tayi ba kaɗan ne amma ta fito dan hidden angelic beauty ɗin ta ya fito a sihirce beauty ɗin
ta ke haskawa yana glowing a fizge..



Rasa yadda zata fito daga ɗakin tayi sai da ta gama juye juyen ta sannan ta yi shahada ta turo ƙofar ya
buɗu sannan ta fito kan ta a ƙasa kamar marar gaskiya.a yayin da take ƙoƙarin rufe ɗakin shi kuma yana
zaune yana jiran fitowar ta jin ƙarar buɗe ƙofar ne ya sa ya ɗago sai ya gan ta tana rufe ƙofar.

Ƙura mata ido yayi yana kallon ta dan gani yayi kamar ta sami process of hypertrophy saboda
transformation da ta samu dan ta ƙara weight compared to yadda take da in a baya tana weighing 50kg
a yanzu yana iya cewa ta kai 58-59kg dan ba kaɗan ba canjin ya nuna a jikin ta..
har ta gama rufe ƙofar sannan ta juyo kan ta a ƙasa ta ce da shi

"Na gama"!!sai ya miƙe tsaye ya tako a hankali har ya iso dab da ita sannan ya dakata ya matso da
fuskar sa kusa da nata a hankali wanda hakan ya janyo mata faɗuwar gaba tana tunanin Zaid ai babba ne
ba zai yi shirmen samarin zamani ba sai ga shi yana mata wani irin abu da bata san dalilin sa na yi mata
hakan ba.

Jin numfashin sa tayi yana sauko mata daga gefen fuskar ta sai ta ji intense obsession ya shige ta but
bata iya furta komai ba

Cikin ruwan sanyi da kama aji ya ce da ita

"Kin yi kyau and......you....smell..gooood"a haka ya jero maganar sai ta ji jikin ta na wani iri kamar yana
son programming ɓakon abin da ya kawo mata ziyara a lokacin da Zaid ke jero mata maganganun nan
dan ba a maganar kaɗai ya tsaya ba sai da ya haɗa da sauke mata numfashin sa wanda abin ya zo mata
out of the blue..



Jin muryar sa tayi yana cewa

"Shall we"sai ta ɗago ta kalle sa haɗe da yin murmushin ƙarfin hali ta ce

"Yes"...daga haka ta shiga gaba yana bayan ta har suka fito ya rufe ƙofar suka shiga takowa a hankali har
suka iso reception inda ya sanar da su cewa fita zasu yi ba yanzu zasu dawo ba da kyakyawar fahimta
receptionist ɗin tayi wishing nasu good day dan ta ga alamun kamar newly couples ne faɗa ne kawai
bata yi ba but tayi alƙawarin dhk dare in har suka dawo zata sanar da su how much she admire them ga
shigar su kusan iri ɗaya dan jacket ɗin su kala ɗaya ne because suna fitowa daga ɗakin ya saka nasa but
rashin kwanciyar hankali ya sa Bilkisu bata yi noticing ba but shi yayi tun lokacin da ta fito hakan ne ma
ya sa ya yi complimenting nata but sai ya ga bata yi responding yadda yayi tsammani ba kenan bata lura
cewa kaya iri ɗaya suka saka ba ko me ke damin ta ne haka bai sani ba...



Da fitan su suka shiga cab da ke tsaye a wajen hotel ɗin dama basu ci abincin safe ba dan haka da mai
cab yayi tambayar inda zasu tafi sai ya ce da shi ya kai su nearby eatery sai mai cab ya ja suka yi tafiyar
da bata wuce mintuna ashirin ba ya ja ya tsaya ya yana mai ce da su sun zo.

Fitowa suka yi ya miƙo mai kuɗin sa ya ja yayi gaba su kuma suka shiga takawa har suka iso glass
translucent four sided sliding door ɗin eatery ɗin suka yi sliding yayi ciki da su a juyi na biyu wurin
madaidaici ne ba babba ba ba ƙarami ba ga wun regular nan a gefe ga vip a gefe nesa da wun regular sai
kuma vvip da ke saman upstairs.

A ran sa ya fi son su tafi saman wun vvip dan yana da sociophobia when it comes to eating in public
hakan na ɗaya daga cikin dalilin sa na ajiye ice da ta kawo mai the other day dan baya iya cin abinci a
gaban jama'a da yawa ko family ɗin sa ba kasafai yake son zama suna cin abinci tare ba dan baya taɓa
sami comfortability in yana cin abinci ana kallon sa ko ba'a kallon sa yana samin nervousness.

Dan haka yana gama ƙare ma wurin kallo ya mata alama da su haura sama,ita dai bata san dalilin sa na
cewa su haura saman ba dan ta ga akwai tables a ƙasa but ya ce su haura sama.

Gently suka haura saman inda ɗaya daga cikin host ɗin ta yi leading nasu har zuwa desired choice ɗin
Zaid dan shi ya nuna inda yake son su zauna.

Wurin rufe yake dan wanda yake zaune a nan fannin ba zai iya shaida wanda yake zaune a chan fannin
ba saboda yanda aka yi designing wurin an yi designing nasa ne cikin yanayin sirri privacy is ensured a
wurin sosai komai naka a tsare yake dama baturi na ba ma tsari haƙƙin sa sai wurin ya ma Zaid sosai har
yake tunanin for the main time of their staying a germany nan zasu na zuwa cin abinci dan wurin ya
birge shi sosai.

Round glaas table ne mai ɗauke da attracting bouquet a vase ƙanana ƴan gudil gudil sai light candles
dake cikin glass container gefe kuma sparking lights ne masu different colours suna walwal bayan
already akwai hasken farin wutar lantarki dake fitowa daga bulb dake sagale daga saman vvip ceiling
arena ɗin wanda shi kansa ado aka mai abin kallo dan glass ne mai kalar golden da silver yayi kamar oval
ta ƙasa sannan yayi curving daga sama kujerun na mutim biyu ne kawai sai dai in mutum na buƙata sai a
ƙaro wasu like in case of family eating outing treat..



Ba shi kaɗai ba har ita wurin ya birge ta har take tunanin sanar da shi ko nan zasu rinƙa zuwa cin abinci
kafin su koma because privacy na gaba da komai kuma su biyu ɗin na son privacy sosai..

Shi yayi gaba ya iso kan ɗaya daga cikin kujerun ya ja mata baya alamun ta zauna sai ta kalle sa da
murmushi a saman fuskar sa ya ce

"Ladies first"sai itama ta mai murmushi ta zauna a hankali tana wani basarwa kamar ba mamaki ne ke
damin ta ba sakamakon manly treats da yake ta mata tun da suka fito har zuwan su nan ba..

Juyawa yayi ya koma fannin ɗaya kujerar yana mai ƙoƙarin cire jacket ɗin sa kafin ya zauna.

Hanging jacket ɗin yayi a wani abin hanging kaya da ke bayan sa sannan ya kalle ta haɗe da ɗaga mata
gira ɗaya sama kafin ya ce

"You"??yana mai nuna jacket ɗin ta da chin ɗin sa sai girgiza kai alamun a'a

"Okey"ya bata amsa sannan ya zauna yana mai miƙo hannun sa ga host da ke tsaye a daga gefen sa dan
jiran ya nuna ordern sa kafin ta ba ma bBilkisu itama ta nuna nata sannan a kawo masu.



Bayan ya karɓa sai ya kalla kusan sau biyu sannan ya ɗago ya miƙo mata ba tare da ya ce komai ba sai
ta tambaye

Please Login or Register in order to submit comment