You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda zai kular mai da ita shi ya sa yana idar da
sallar ya nufo gida lokacin har gari ya fara wayewa haske ya fara bayyana sai ya ɗan ƙara saurin sa ya iso
gida,gaisuwar su da mai gadin sama sama ne burin sa ya isa ciki ya tayar da ita dan lokacin sallah na
tafiya kuma ya san har in ba tayar da ita aka yi ba ba tashin zata yi dan bacci mai nauyi ne ke ɗaukar ta..



Kamar ya sani,yana shiga ɗakin tana gyara kwanciyar ta dan cigaba da baccin sai da ya bar ta ta sami
mintuna biyu a haka sannan ya zo har saman gadon ƙafar sa ɗaya dogare da gadon ta ƙasa ɗaya kuma ya
ɗora bisa kan gadon ya duƙar da kan sa ƙasa kaɗan ya yaye blanket ɗin ta wuyan ta ya kai lips ɗin sa ya
manna a wuyan ta ba kiss ya mata ba amma ya ɗau lokaci da lips ɗin sa a nan tun tana share abin har ta
ji ba ta iyawa dan dole ta buɗe idanun ta ta juya zuwa direction ɗin sa cikin kula ya kalle ta ya ce

"Lokacin sallah yayi baby tashi ki yi"!!shiru tayi na wasu seconds kafin ta fara yunƙurin tashi jikin ta duk
ciwo yake mata dan baccin da take yi ba na daɗi bane kawai dai ba yadda zata yi dan duk lokacin da ta
kwanta baccin dolen a takure take yin sa sai ta tashi duk jikin ta ya rinƙa mata ciwo tana jin zafi but tana
da niyar zuwa asibiti a duba ta dan ita ta kasa yiwa kanta diagnosis mai ma'ana at first ta yi tsammanin
tunanin Zaid ne da ta sakaea kan ta sai ta rage tunanin amma still babu wani canji sai ta canza diagnosis
ta ce maybe zaman wuri ɗaya ne dan in ba wani aiki ne ya taso da za'a kira ta yi ba shima da ta kammala
take komawa gida,bata yin komai but still abin sai ya girme mata fiye da tunanin ta dan haka ta yanke
shawarar zuwa ganin wani likita maybe zata sami lafiya..



Tana dire ƙafar ta ɗaya ƙasa yayi saurin zagowa ya riƙo ta yana ce mata

"Easy...slowly"!duk hankalin sa ya koma kan ta sai taka tsantsan yake yi da ita abin sai ya saka ta
wondering me yake ta damuwa da ita har haka,ta san dai ba sauraron sa tayi ba but why all the caring
stuffs..

Hannun ta cikin nasa ya ɗaga ta ta tashi da ƙafafun ta sai ta zame hannun ta ta wuce ciki ta yi brush
haɗe da yin alwala tun kafin ta fito har ya ɗauko mata hijabin sallah ya shimfide mata sallaya ita kawai
yake jira.

Wow is this guy for real!?tambayar da ta wa kanta kenan ganin yana ta abubuwa so gentile ta manta
shi ɗin haka yake dama chan yanayi ne da rashin fahimta ya sa ta kasa gane hakan sai yanzu da aure ya
haɗa su ƙarƙashin inuwa ɗaya..

Tana hawa kan sallayar ta yi kamar zata tsugunna ta ɗau hijabin sai ya riga ta ya ɗauko ya miƙo mata ta
karɓa tana mamakin sa sai dai bata iya cewa komai ba.

Tada sallar tayi shi kuma ya ɗan kishingiɗa yana kallon ta har ta idar da sallar tayi addu'ar da zata yi
idanun sa na kan ta tana gama addu'ar kawai ta kwanta nan ta cigaba da baccin ta dama ba isar ta baccin
yayi ba gajiya ne ya saka ta farkawa.
A ɗan hanzarce ya tashi ya ƙura mata ido me ke damin ta ne wai haka?baya jin tsetse fly na yawo a
gidan bare yayi tunanin baccin ta na da nasaba da cizon sa toh anya kuwa lafiyar ta ƙalau...

Tasowa yayi ya zo inda take kwancen ya tattare mata hijabin ya gyara ta yadda zai rufe ta da kyau shi
kuma ya ɗan raɓa ya kwanta a gefen ta yana kallon ta sai sharar bacci take yi.,hannun sa ya sagala da
nata hannun yayi creating interlock ymda yatsun su ya kuma matso da fuskar sa kusa da nata ya kwantar
da kyau ta yadda duk wani abin da zai yi zata jiyo sa itama haka..baccin ne dai ya kuma ɗauke su.



_8am_

Sai yanzu suka farka daga baccin daga ita har shi sai da jikin su ya gaya masu kwanciya a ƙasa bayan
sanyi ga ƙarfi da rashin taushi dan ma da darduma kenan,ganin sa kwance kusa da ita sai ya kuma bata
mamaki ta kasa gane shin gaske ne ko faking yake yi..

Ita ta riga sa tashi tana miƙa shi kuma daga kwancen ya ƙare mata kallo ba komai miƙar ta ke haddasa
masa ba illah sha'awar ta amma ba halin manifesting dan sai tayi tsammanin dama dan hakan ne ya ke
mata abubuwa yake kuma bata kula..



Tana sauke hannayen ta hamma ya biyo baya sai yayi saurin ce mata

"Hungry"!?gyaɗa mai kai tayi sai yayi saurin tashi yana faɗin

"Ina zuwa ki bani 15minutes okey don't go anywhere"!!da kai ta amsa mai yana gama faɗin haka ya
tashi yayi waje ita kuma ta tashi daga saman sallayar tayi cikin toilet dan yin wanka sai dai babu wasu
abin buƙatar ta dan haka sponge ɗaya da ta hango da shi tayi wankan ko cikin bathtub ɗin bata yi gigin
shiga ba dan ta san tana shiga bacci ne zai ɗauke ta.

Cikin kwanciyar hankali tayi wankar ta ta saka rigar wankar sa dan ya fi ƙarfin ta lulluɓe kan ta tayi da
towel ɗin sa ta fito kan ta tsaye bata yi tunanin ganin sa cikin ɗakin ba sai dai what shocked her shine
tana turo ƙofar ɗakin ta gan sa tsaye babu riga sai boxer da yake sanye da shi,tun daga ƙasa ta fara
kallon sa tana kallon ƙafafun sa da ke ɗauke da suma kwance har wani gazar gazar suke yi wanda ta ji
tsigar jikin ta ya tashi at once,kaɗan kaɗan ta rinƙa kallon sa har ta kawo jikin sa ta rinƙa kallon bare
chest ɗin sa da ke a ɗan buɗe ta kalli right and left side na ribs ɗin sa ta ga ABS packs ɗin sa sai ta tsaya
tunanin ita ce ta ɗauki nauyin sa a daren rannan?she can't believe it ta san in aka bar ta da shi a rightful
senses ɗin ta toh lallai zata mai kuka wataƙil har da shessheƙa dan shi ɗin ba na wasa bane..

Yana kallon ta tana ƙare mai kallo yana bin ta da ido har ta gama ta sauke idanun ta ƙasa ta shiga
nemawa kan ta hanyar tafiya bai yi gardama ba ya ja gefe ya bata hanya,raɓawa tayi ta gefen sa ta wuce
sa shi kuma ya shige toilet ɗin dan yin wanka..
Da wani irin full force ta zauna bisa gadon tana maganganu da iya gaskiyar ta

"Toh kuma menene na cire kayan jikin sa alhalin ya san ina ciki kuma ma ni ba ce mai nayi ina buƙatar
kallon jikin sa ba in ina son kallon jiki ne ga nawa jikin ba sai in kalla ba mtsw"ta ja tsaki sannan ta hau
dube duben inda zata ga cream dan ga dukkan alama nan ɗin ba ɗakin ta bane nasa ne saboda babu
kayan gyara irin na mata,.

Hango cream ɗin tayi saman abin shafe shafe sai ta kai hannun ta ta ɗauka ta matso ta shafa a ƙafar ta
tana shafawa tana tuno jikin sa da ta gani ba kaya wani bin tayi tsaki wani bin ta girgiza kai..

Shafe jikin ta tayi da cream ɗin sannan ta koma ta zauna tana jiran fitowar sa dan ya kai ta inda zata
sami kayan sakawa,.

Abin dariya tana kwantawa kawai sai bacci wannan abu ya ba Zaid mamaki ba kaɗan ba dan yana ta
kiran ta akan ta kawo mai towel amma bai ji amsbi ba sai ya keƙi da kansa only to see her
sleeping,ƙarasa fitowa yayi ya duba ya ga towel ɗin gefen gadon a ƙasa ɗagawa yayi ya ɗaura sannan ya
goge jikin sa da ƙaramin towel da ke hannun sa,..



Shirya kan sa yayi cikin kaftan grey colour ya fito da ƙwarjinin sa fili matsalar ɗaya ce rashin gyaran
fuskar da bai yi ba kuma shi ba wannan ne damuwar sa ba damuwar sa shine Bilkisu ta cigaba da zama
da shi kar ta ce gida zata tafi dan tana faɗin hakan zasu ɓata because he won't let her go home..



A yau ɗin ma abincin da ya saka a haɗa masu ɗakin ya shigo da shi ya ajiye bisa wata madaidaiciyar
table dake ɗakin sai ya fita ya koma ɗakin ta ya binciko mata wata native,atamfa ce mai zanen tsuntsu
an mata ɗinkin doguwar riga hannun ta dogo amma an tsaga daga bakin hannun har zuwa tsakiya jikin
rigar kuwa a riƙe yake wato straight gown wuyan rigar kuma ta ɗan sauka ƙasa kaɗan off shoulder kalar
mai fuhu ce sai ya haɗo mata da mayafi mai kalar zanen tsuntsun ya haɗo mata da kayan kwalliya da
accessories da zata haɗa da kayan..

Jan ƙofar yayi ya rufe ya dawo nan ɗakin ya gan ta still baccin take yi sai yayi murmushi kawai ya wuce
ta ya ajiye kayan sannan ya shiga tayar da ita

"Hey....sleeping beauty..,wake up"yana gama faɗin hakan kamar an tsungule ta ta buɗe idanun ta dan
dama baccin ba nisa yayi da ita ba.

Cikin miƙa ta tashi tana hamma sai ya ƙura mata idanu so yake ya duba wani abu a jikin ta dan bai yarda
da yawan baccin nan da take faman yi ba tun jiya har yau a ƙalla sau uku kenan tayi bacci a yau ɗin nan
cikin safiyar nan what could possibly be the reason..

Zuba masa ido tayi tana girgiza kai irin me kuma ɗin nan.,a ɗan firgice ya ce
"Your clothe...,gashi nan ki saka in mun karya zamu fita ina so ki raka ni wani wuri ne please"abin da ta
lura da shi shine yawan amfani da kalmar _Please_da yake yi kamar wanda yake ƙarƙashin ta yana
nemar amincewar ta,bata ce mai komai ba ta saka hannu ta karɓi kayan sai kuma ta kasa tashi tana jiran
ya matsa shi kuma da yake ɗan duniya ne sai yayi ignoring irin bai gane ma'anar zaman ta har lokacin
ba,abin ya harzuƙa ta so tayi ta hukunta sa by not talking to him for 72hours dan ta tabbatar ko da gaske
ya yarda da auren su kokuma pretending yake yi amma yadda yayi kunnen kurma sai ya saka ta haɗe
girar sama da ta ƙasa dan kar ma ya fara tunanin raina ta

"Ina buƙatar sirri"!!..sai ya shiga jujjuyawa yana kallon gefen sa wai so yake ya ga baren da yake ɗakin
apart from the two of them,tsayar da fuskar sa yayi a daidai nata fuskar sai ya saka silly face ya shiga
kaɗa mata kai yana faɗin

"Sirri"???kallon sa tayi ta gyaɗa kai sai ya ce

"Amma ai babu stranger a nan daga ni sai ke...wani sirri kuma kike nufi"??sarai ta san ya gano abin da
take nufi amma dan shi ɗin ɗan rainin tunani ne sai ya sakankance yana nuna shi bai gane me take nufi
ba..

Kyaɓe fuska tayi ta saka fuskar cat tana faɗin

"Ni dai ka fitar min dan sarai ka fahimce ni ka san me nake nufi"!!shagwaɓe muryar ta tayi sai ya riƙe
dariyar sa ya ce

"You are funny,,sirri??where??here??just the two of us and you still need privacy or what"??ɓata fuska
tayi tana shirin yin kuka ta ce

"Ni dai ka rabu da ni i never intended talking to you but you made me did it"ta ƙarasa tana mai juyar da
kan ta gefe sai ya tsinci kansa cikin yanayin son raha da tsokanar ta dan haka ya wani matso kusa da
kunnen ta yayi ƙasa da murya kamar mai jin bacci ya ce

"Na fah san komai,,na taɓa nan,na taɓa nan,na yi wasa da nan,kuma kema kin ji daɗin hakan,har ce min
kike _Zaid taɓa nan,Zaid taɓa min nan_ kika rinƙa nuna min inda zan taɓa tun bana so har kika saka ni yi
shine kuma yanzu zaki ce kina buƙatar sirri?me ya rage ban gani ba ban kuma sani ba?huhh"?tun da ya
fara maganganun sa ji tayi kamar an tsoma ta cikin Electric Convulsive machine an kuma saka vibrating
speed ɗin as high as 200/300,zirr zirr ta rinƙa ji madaɗin ta ji haushin maganar nasa sai tayi ending up
falling for him again,bata tashi jin haushin sa ba sai inda ya ce tana ce mai ya taɓa nan ya taɓa nan,ita
yaushe aka yi hakan da ita..

A zuciye ta ɗauko mini trow pillow dake saman gadon ta mare shi da shi haɗe da jefa mai,..

Burin sa ya cika ya saka ta hawa kan hanyar da yake son saka ta dan haka da dariyar sa cikin son cigaba
da tsokanar ta ya ce

"Common baby doctor,ai ba ƙarya na yi ba a hakan ma fah ban sanar da ke ire iren noises da kika rinƙa yi
ba kenan"ya buɗe baki dan cigaba da magana sai ya ji saukar hannun ta saman bakin sa tana mai girgiza
mai kai da fuskar yayi haƙuri yayi shiru sai ya tsaya ya ƙura mata ido yana jin wani abu game da ita,ya
shagala da kallon halittar ta yana yaba kyakyawar fuskar ta da ƙwayar idanun ta da yake roƙon Allah ya
sa ƴaƴan sa su yi gadon sa dan ba kaɗan ba yake admiring eye balls ɗin ta,da ta ga yayi shiru yana bin ta
da kallo sai ta ji ta tsargu har ta kasa cigaba da kallon sa ta cire hannun ta daga bakin sa cikin sauri ta
juya mai baya tana faɗin

"Am sorry"!!. synchronously ya tako har daidai space dake tsakanin ta da shi ya cike space ɗin ya kai
hannun sa yayi grabbing waist ɗin ta yayi wrapping hannun sa biyu daga waist ɗin ta zuwa ta gaba lower
abdominal region ɗin ta ya janyo ta baya ta haɗe da jikin sa sai suka lumshe ido at the same time suka
sauke ajiyar zuciya,gaban ta ne ya shiga yin gudun tsere kamar gudu tayi,saka fuskar sa yayi ta gefen
wuyan ta ya sauke haɓar sa daidai clavicle bone ɗin ta ya shiga brushing slowly yana lumlumshe ido,taya
sa sauke ajiyar zuciyar tayi wanda suka ɗau mintuna biyu suna a haka sai shine ya tambaye ta cikin
sanyin murya

"Don't you like and enjoy this moment"!?shiru ta mai tana jin touch ɗin nasa na shigar ta ga nishin da
yake yi daidai kunnen ta kawai rasa inda zata saka kan ta tayi sai ta kawo hannun ta ta ɗora saman nasa
hannun tana son cire hannun amma ya ƙi barin ta ta cire..

Ƙyale sa tayi tana jiran ganin iya gudun ruwan sa dan abin yana mata daɗi kawai fushin da take yi da shi
ne ya sa take shasshare sa da duk wani abin da yake mata..

Ita shiru shi shiru a tsayen da take har ta fara jin wani jiri jiri domin kuwa bacci ne ke son yin awon gaba
da ita amma ta kasa sanar da shi ta mai shiru tana jiran ganin ko zai daina ko ba zai bar ta ta saka kayan
ba.



Kamar wasa kuwa tun tana iya hana kan ta har ta kasa ba haƙura bacci ya fara ɗaukar ta dama idanun sa
a lumshe suke yana sauraron numfashin ta sai ya ji kamar numfashin ya fara canzawa saurin buɗe
idanun sa yayi ya leƙo fuskar ta sai ya ga abin mamaki "wai bacci tayi kuma"??ya ma kansa tambayar sai
yayi saurin juyo ta ta ɗan buɗe idanun ta tana son daidaita su amma ta kasa dan haka luu tayi ta faɗa a
jikin sa bacci ya shiga next stage ta cigaba da sheƙa baccin ta..



Over 60 seconds yana rungume da ita tana baccin kuma bata motsa ba izuwa yanzu kam abin ya fara
razana sa ya fara jin tsoro dan lafiyayyen mutum baya bacci haka kowani lokaci,ko dai bata da lafiya ne
take ɓoye mai..

Yin ƙasa da fuskar sa yayi yana kallon ta sai ya ga ba baccin kaɗai take ba har da riƙo rigar sa tayi tana
sauke numfashi a tsanake kamar ta daɗe bata yi baccin ba sai yanzu..

"What the heck,,why did she sleeps so fast"?ya tambayi kansa dama so yayi in ta shirya sai ya kai ta
asibiti a duba ta hala wata matsalar ce da ita amma basu damu ba..
A hankali ya nufi kan gadon da ita yana lallaɓa ta kar ta tashi,suna zuwa gadon ya kwantar da ita haɗe da
ɗaga ƙafafun ta ya ɗora bisa gadon yana mai kallon ta,zama yayi yana kallon ta kamar wata sabuwar
halitta abin na ɗaure masa kai ta yaya mutum zai rinƙa sharara bacci haka sannan in ya farka babu wata
alamar rashin lafiya tattare da shi,..



Riƙo hannun ta yayi cikin nasa yana ƙare mata kallo she is damn beautiful,innocent and so flawless me
yasa bai taɓa lura ba a baya sai yanzu da ta nesanta kan ta da shi ya daina ganin ta..

Baccin mintuna goma tayi yana monitoring nata time na cika ya hau susa mata tafin hannun ta yana yi
yana kiran ta

"Bilkisu,baby,..wake up..kin ji"!??kamar a mafarki ta ji muryar sa yana kiran ta sai ta ɗan buɗe idanun ta
ta sauke cikin nasa idanun,ɗage mata gira ɗaya yayi yana faɗin

"Let's eat abincin zai yi sanyi"!!nayar da idanun tayi ta lumshe sannan ta buɗe zata kuma rufe idon ya
tashi a 360 yana faɗin

"Not again baby not anymore tashi kar ki fara baccin nan kuma"!!kamar zata fashe da kuka haka ta tashi
dole ba dan ta so ba taya ta saukowa daga gadon yayi yana mai nuna mata inda zata zauna dan cin
abincin..

Zama tayi tana fushi tana faman kumbure kumbure kamar an mata laifi,shi dai ido yake bin ta da shi
dan abin nata gaba yake yi bacci fiye da ƙima ba alama ce mai kyau ba..



Yana zama ta ce da shi

"Ina abincin"!?saurin serving nata yayi yana mai yi mata Bismillah,janyo plate ɗin tayi gaban ta ta shiga
cin abincin tana jin baccin na fizge ta daga sama so take tayi ta kammala da abincin nan ta kwanta,yayin
da take cin nata abincin shi kuma yana kallon ta,kwata kwata bai fi rabin kashin abincin da aka zuba
mata ba ta ci ta ce ta ƙoshi zai yi magana ta ce

"Enough please i wanna sleep na ci abinci ai toh me kuma ya rage"??ta mai tambayar tana mai ƙure sa
da idanun ta sai ya hau girgiza mata kai.

Tashi tayi tana maganganu ƙasa ƙasa tayi kan gadon ta kwanta,still rigar wankan ne a jikin ta bata sauya
ba.

Bin ta da ido yayi yana nazartar ta har dai ta kwanta sai yayi gyaran murya yana faɗin

"Fitar tamu fah?sai yaushe"?sama sama ta ji tambayar dan haka sama sama ta amsa mai tana fizgo
maganar
"Please Zaid stop causing me somnambulism just let me sleep i beg of you"tana gama faɗar haka bacci
mai ƙarfi ya ɗauke ta.jijjiga kan sa yayi yana mai yi mata dariya lallai baccin ba kaɗan bane in ba haka ba
me kuma haɗin ta da somnambulism tana kwance tana sharara bacci,wani dariyar ne ya kufce masa ya
yi yana biting lips ɗin sa yana kallon ta.

Girgiza kai yayi ya yi serving kan sa abinci yana ci yana kallon ta yana nazarin ta akan abubuwa daban
daban..

Shi ya kwashe kayan da kan sa sannan ya fito ya bar ta a ɗakin ya sauko ƙasa,canza wurin tafiya yayi
dan so yayi su ga likita sai su ɗan zaga gari amma copping with the situation sai kawai ya haƙura ya shiga
motar sa aka buɗe mai gate ya tsaya yayi warning gate man ɗin akan kar ya kuskura ya bari wani ya
shigo mai gida kai tsaye apart from their families dan matar sa na ciki na bacci bai son a dame ta,gyaɗa
mai kai yayi sannan ya fita ya ɗau hanyar tafiya gidan aminin sa Dr Hussain dan yana ganin in ya mai
bayanin abin da ke damin Bilkisu yana iya preferring masa solution..



Tafiyar mintuna talatin ne ya kawo sa Otako inda a nan gidan Dr Hussain yake,kiran sa yayi yana
tambayar sa ko yana gida ya sanar da shi cewa eh yana nan lafiya,kashe wayar yayi ya fito daga motar sa
ya taka da ƙafa har zuwa gate ɗin inda aka buɗe mai aka yi tambaya ya ce a ce Dr ZM ne ai kuwa Dr
Hussain na jin haka yayi saurin fitowa har gate ɗin yana mai nuna farincikin sa da zuwan Zaid ɗin,har ciki
ya kai sa suka zauna ya kirawo matar sa dan ta kawo mai abin taɓa baki amma ya ce ta bar shi he is okey
daga gida yake..

Kallon sa Dr Hussain yayi da ya gama ya fara yi mai tsiyataku kala kala shi dai shiru ya mai har ya gama
sai ya ce mai

"In ka gama sai ka saurari abin da ya kawo ni gidan ka har kake min magana son ran ka"dariya ya mai
sannan ya ce

"Dr ina jin ka"gyara zama Zaid yayi yana mai fatar samin mafita daga wun Dr Hussain ɗin.

Narrating mai komai yayi game da yawan baccin Bilkisu da unpredictable mood swings ɗin ta har da
sabbin attitude da take portraying wanda a iya zaman sa da ita a ƙasar germany bai taɓa ganin halayyar
ba sai yanzu..



Har ya kammala bayanin sa Dr Hussain na sauraron sa at the same time yana analyzing
maganganun,tambayar sa yayi wasu alamomi sai yayi shunning nasa dan shi kan sa ba sani yayi ba
tsakanin sa da Bilkisu dare ɗaya ne after that nothong happened how could he know the answers to his
questions.

"Yanzu baka san amsa ko ɗaya ba cikin tambayoyi na"??gyaɗa mai kai yayi sai kawai Dr Hussain yayi
murmushi yana jijjiga kai yana faɗin
"Yehyehyeeeeh"sai kuma ya saka dariya wanda ya ɗaurewa Zaid kai har ya jibya fara jin haushin Dr
Hussain ɗin a ƙarshe dai tsaki ya ja yana ma Dr Hussain ɗin masifa

"Ba laifin ka bane ni na janyowa kaina da na kawo maka damuwa ta dan ka min magani ko ka nuna min
mafita da ban zo ba da ba haka ba"sai da yayi dariyar sa mai isar sa sannan ya natsu ya dafa kafaɗar Zaid
yana mai yin murmushi ya ce

"Man you are about to become a father"daga sama ya ji saukar maganar sai ya ɗago kan sa ya kalli Dr
Hussain yana mai girgiza cikin ruɗu

"No..,ba haka bane,Bilkisu can't be pregnant no"ya rinƙa girgiza kai babu iyaka ƙarshe dai Dr Hussain
dafo sa yayi yana mai gyaɗa mai kai ya ce

"Me yasa kace haka"?sai ya girgiza mai kai yana cewa

"Because she....,,!!"sai kuma yayi shiru yana mai faɗin

"A'a wani abin ne daban ba wannam ba"ɗan murmushi yayi yana faɗin

"Calm down just relax anf think about this ideologically,yaushe mutum mace ma kuma likita ta taɓa
zama tana sharara bacci every now and then?sannan tana experiencing yawan fushi marar dalili again
bata son yin magana"??sai Zaid ya natsu yana nazarin maganar Dr Hussain.tashi yayi yana faɗin

"Am out of here Hussain thanks"tashi Dr Hussain yayi yana son dakatar da shi amma bai tsaya ya
saurare sa yayi tafiyar sa gida..



He arrived at exactly 12 noon yana tura ƙofar tana tashi daga kwancen da take kenan tun da safe da ya
bar ta bata farka ba sai yanzu toh ko dai maganar Dr Hussain gaske ne?amma is it possible for her to
conceive a karon farko da suka tara?.

observing nata ya shiga yi dan gasgata maganar Dr Hussain sai ya ga babu ko guda dan haka ya
shashantar da zancen ya ƙarasa ciki yana mai faɗin

"Kin farka sleeping beauty"da murmushi yayi tambayar sai ta amsa masa da kai tana mai ƙare mai kallo
da alama dai daga anguwa yake tambaya ta jefo mai

"Ina ka tafi"da murmushi saman fuskar sa ya ce

"Inda na ce ki raka ni kika ƙi"sai ta kyaɓe fuska tana faɗin

"Toh ba gashi nan na tashi ba"dariyar wayayyu yayi yana ɗage mata gira ɗaya sama ya ce

"Ba zan iya ba dan yana yiwuwa muna fita ki bige da bacci you see,,you will become a liability to me so
just don't worry another time"ko a jikin sa ita kuwa abin ya taɓa ta sai ta tashi tana faɗin
"Damuwar ka"tayi hanyar toilet.dariya ya raka ta da shi sannan ya shiga cire kayan sa yana tunanin
yadda zai rikita ta a yau ɗin dan so yake su dawo normal ba kamar baƙin juna ba..




_8pm_

Tun da ya dawo yake ta mata wasu alamomin nuna kulawar sa gare ta sannan ya hana ta baccin da ke
taso mata da ta kishingiɗa zai tayar da ita sannan yayi yayi ta zo su zaga gidan ta ƙi wayar ta ta nemi da
ya bata ta kira gida amma ya ce bai san inda wayar take ba ya ara mata

Please Login or Register in order to submit comment