You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gate ɗin a fusace suka shige ciki aka mayar aka rufe.



Shigar ta falon kenan ta tarar da su suna abin da suka saba yi ita dai Allah ya bata kyautar iyaye a ko da
yaushe kamar wasu yara suke yanzu ma dai umman ta ce cikin shigar fitted gown an sha kwaliya an zubo
suman nan har gadon baya she is just looking perfect kamar wata wacce bata manyanta ba yayin da
Abban ta ke cikin shigar ƙananan kaya kamar ba shi yazo hospital ɗazu ba cikin shigar manya duk sai
suka koma mata wasu teenagers



"Prof na gaya maka baby ba zata tafi wannan outreach ɗin ba muddin ba tare da company ɗin wani ba i
can't risk that"tana maganar ne tana wani mammatsewa yayin da shi kuma cikin son impressing ɗin ta
ya ce



"Haba no heart she is not going alone tare da zaid zasu tafi that is in kin amince amma in bai maki ba sai
a yafe tafiyar"kamar wani wanda yake bauta mata haka yayi maganar ga mamakin sa sai ta saka dariyar
manya ta ce

"Common are you serious"? Cikin jin daɗi yayi impressing ɗin ta ya ce

"Yes of course"ta rungume shi tana cewa
"Na amince zaid is a good boy zai kular min da baby na"daɗi ya ji sosai inda ganin abin na su ba mai
ƙarewa ba ne ya sa ta gyara murya wanda hakan ya dawo da su daga jubilation ɗin da suke yi da sauri
suka gyara zama murmushi ta masu ta ce



"Good evening love birds"hararar wasa mahaifiyar tata ta mata ta ce

"Baby me yasa kike da son yi mana shishigi ne wai kin dawo instead ki tafi apartment ɗin ki sai kuma kika
tsaya kallon mu gashi kin hana mu ƙarasa hirar mu ko prof"? Ta ƙarasa tana kallon direction ɗin shi inda
yayi saurin girgiza mata kai.



Dariya kawai ta masu ta wuce tana jin daɗin ganin farincikin iyayen ta ko da kuwa sun ɓata mata rai ne
da zarar ta birkice masu zasu sauko su fara rarrashin as if ita kadai ce ƴa a gidan tana alfahari da su duk
da ma dai Abban ta na yi wa umman ta total obedience kamar wani wanda bai girma ba ita kuma
umman ta na ruling gidan according to her desire sai dai ta san duk a cikin soyayya ce dan da babu
soyayya duk hakan ba zai faru ba.karasa haurawa tayi tana fatan wataran in ta shirya neman abokin
rayuwa ta sami kamar Abban ta dan a tarihin gidan su irin rayuwar da ya gabana kenan she just pray that
the epic will repeat it self a kan ta...



Shima da shigar sa kenan ya tarar da iyayen shi zaune bakin swimming pool an sha ƙananan kaya ana
zuba soyayya ko ba'a faɗa ba a nasu fannin dai kusan abin da ke faruwa a gidan su bany doctor ke
faruwa a nan dan mahaifiyar shi ce ke faman bayar da command akan abin da za'a kawo masu in suka
tambayi mahaifin sai ya ce duk abin da ta zaɓa ya mai alhalin bai da niya amma dan gudun ɓacin ran ta
sai ya basar girgiza kai yayi ya nufo su ya tsaya masu a kai kamar soldier sai da mahaifiyar ta sa ta juyo ta
lura da dawowar shi cikin sauri ta miƙe tsaye tana cewa



"My boy yaushe ka shigo ban sani ba me za'a kawo maka kafin ka yi wanka"? Instead ya bata amsa sai
ya haɗe rai kamar bai iya dariya ba ya ce



"Ammi sau nawa nake hana ki ke da Abba yin irin waɗannan shigar?ban ce maku in zaku yi ku bari sai ba
mu nan a gidan ba"? Ya ida maganar cikin sanyin murya

Cire hannun ta tayi daga kan kyakyawar fuskar sa wanda yake nan exactly irin nata ta juya ga mahaifin
sa ta ce
"Only ka ma ɗanka magana yana mana shishigi a rayuwar mu da yawa in bai son ganin soyayyar mu me
zai hana shi zuwa ya samo tasa matar ta yadda ba zai rinƙa ganin namu soyayyar ba"ta ida tana batsewa
a dole ya ɓata mata rai cikin hanzari ya miƙe tsaye dan cika mata umarnin ta ya ce



"Haba zaid ya zaka na saka Ammin ka da ni a gaba kamar kai ka haife mu tare fah ka gan mu ta yaya
kake son raba abin da Allah ya haɗa?toh kar ka sake ka jini ko"? Ya gama maganar yana mai signal irin
yayi haƙurin nan murmusawa yayi dan yasan Ammin sa ce ruler ɗin gidan dan haka Abban sa has no say
sai abin da ta ce well duk a cikin soyayya ce ya faɗa a ran shi yayin da ya juya ya fara tafiya ya tsinƙayo
muryar ta tana cewa

"Ni wai only yaushe yaron nan ka ce zai yi tafiya ne"?



"In the next 10days kuma tare dababy doctor zasu tafi ai yayi ko"? Cikin murna ta ce



"Kana nufin da ɗiya ta zasu yi tafiyar"? Cikin murna ya ce

"Eh tare zasu tafi"

"Ohh Allah ya kai su lafiya i have to call hajiya Zeenat dan mu raba wannan farinciki tare miƙo min waya
ta"ya miƙa mata yana farinciki shima yace

"I have to call prof mu raba farincikin mu"hararar wasa ta mai ta ce

"Whatever ni damuwa ta ma yaron nan ya tafi ya bar mu mu sake"



Murmushi kawai yayi ya wuce zuwa ciki dan iyayen shi are always behaving so childish bai san yadda zai
yi da su ba.........




_Toh ya kuka ji takun farkon?mu cigaba ne ko dai mu dakata? yawan amsoshin ku da sharhunan ku su
zasu bada cikakkiyar amsoshin ku da amincewar ku_



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim
#vote

#comment

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*




*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim
*2*



Dr Zaid Maher Mahmud shine cikakken sunan sa ɗa ne ga Dr Maher Mahmud retired Dr mammalakin
asibitoci biyu da ɗan sa ke running wato Dr Zaid,ya kasance babban ɗa ne ga Dr Maher Mahmud wanda
ya ke da ƙanne uku Afzal wanda ya ke aiki a Canada da wani babban asibiti a inda mahaifin sa ya matsa
akan sai ya dawo nan ƙasar Nigeria amma ya ƙi a cewar sa tunda yayan sa na kula da asibitocin sa na nan
no need ya dawo haka ya ƙyale shi kasancewar mahaifiyar su ta saka bakin a bar shi har sai yayi deciding,

Hakim shine ɗa na uku wanda ya ke kan yin masters ɗin sa a science and technology a ƙasar Qatar sai
autar su Bahajjatu wacce ita ce sa'ar baby doctor kuma babbar aminiyar baby doctor tun yarinta
kasancewar tare suka taso har rana ita yau amintakar su na nan tana running babban fashion company
na kan ta wanda mahaifin ta ya buɗe mata.



Gidan su ya kasance strict free home very simple and unique home babu takura da hantara na kasa na
girmama na gaba da shi akwai ginanniyar ƙauna da shaƙuwa a gidan tsakanin su ilimin addini da na
zamani daidai gwargwado akwai fahimta mai ƙarfi a tsakanin iyaye da ƴaƴan na su.



Dr Zaid da ya zama babban ɗa a gidan ya lashe gurbin babban yaya a gidan kuma babban ɗa very simple
and jovial brother and a son bai haɗa ƙaunar kid sis ɗin sa da na kowa dan haka ma duk mai neman wani
abu a wun shi a cikin ƴanuwan na ta ke bi ta wurin ta dan ita ce ƴar gwal ɗin sa since she is the only girl a
gidan she is just 24years amma a hakan a wun shi a ƴar 5years yake ɗaukar ta ta yadda yake zuba mata
sharuɗɗan irin saurayin da zata saurara a haka kuma ta ke bi dan duk hutu da arziƙin ki muddin ka zo
mata da abin da baya cikin sharuɗɗan yayan nata toh ta haƙura da kai kenan sai dai ka nemi wata dan
yadda yayan nata ke ji da ita haka ma ita kanta..



abu ɗaya ne ya kasa hana ta shine amintakar su da baby doctor dan kuwa ya buga ya buga har fushi yayi
da ita sai dai haka ya haƙura ya bar ta dan ƙarshe shi ya koma rarrashin ta as strong head ɗin ta in ya
motsa baya jin lallami shi kuma bai iya ɗaukar fushin da take yi da shi he just doesn't know how amma
jinin shi ne kawai bai haɗu da na baby doctor ba dan tun yarintar su yake ganin taurin zuciya irin na ta
kwata kwata when it comes to him ba ta da sauƙi ko kaɗan bata raga mai in ya ce 'a' sai ta mayar mai
since they are all neighbours kusan a gidan su take yini dan mahaifiyar su Hajiya Madina na bala'in
ƙaunar ta saboda ƙaƙƙarfar friendship relationship da ke tsakanin ta da mahaifiyar baby doctor wato
Hajiya Zeenat,ganin hakan ya sa ya ke raga mata but in da ta shi ne yarinyar ta daina kusanci da ahalin
shi but unluckily for him hatta mahaifin shi na ji da ita being his best friend only girl child ga ƙannen shi
na son ta saboda hazaƙar ta da ilimin ta tunda both houses ɗin gidan boko ne sai relationship ɗin su ya yi
ƙarfi daɗin ƙarawa irin career ɗin iyayen su suke yi sai abin ya burge iyayen har ma suke fatan wataran
ala'ƙar su ta karfafa ta fi haka fatan su kenan amma ga su waɗanda ake ɗorawa hope ɗin ba haka ba ne
dan a kulliyaumi idan zasu haɗu da juna toh babu alkhairi is either a rabu da juna ana dasa ma juna
magana ko kuma a rabu ana aikawa juna mugayen kallo,



Dr Zaid ya kasance mutum ne shi mai son girma da kamun kai hakan ya samo asali ne sakamakon zurfin
karatun da yayi a ƙasar balarabe wato Dubai dan sanin mutunci da ƙimar ɗan adam ya ƙare a ƙasar
larabawa sai dai ɗaiɗaiku da ba za'a rasa ba masu ɓata ƙas, rayuwar sa a chan ya sa ya yi adopting
halayyar su dan fah shi bai cika son raini ba bare shishigi a al'amurar mutani over 12years yana ƙasar dan
ko da ya kammala karatun sa da su ya fara aiki until his momma mounted pressure on him kafin ya dawo
ƙasar shi ko da ta ga abin na son repeating kanshi akan Afzal sai bata wani damu ba since her boy is close
to her kuma shi Afzal ɗin ya nuna mata bai da niyar dawowa yanzu shi yasa ta sa mahaifin su ya bar shi
kawai tunda bai ra'ayi.



Kwata kwata bai wuce 33years ba very young gentile and hard working guy dan shi ke handling
hospitals ɗin iyayen na shi da na mahaifin shi da na aminin mahaifin nashi wato Dr Muhammad Sulaiman
dan duk ƴaƴan shi babu wanda ya karanci medical line ganin haka ga shekaru na ja ya sa Dr Maher
Mahmud bashi shawarar ɗora Zaid akan wanda za kular mai da asibitocin sa har kafin baby doctor ta
kammala karatun ta ya ko ji daɗin shawarar dan haka ya tuntuɓe shi da maganar akan in babu takura sai
dai ya ji daɗin amsar da ya bashi na ce mai da yayi ai shima ɗan shi ne dan haka duk yadda ya ga ya dace
a wun shi ba matsalar komai tun daga lokacin ya cigaba da kular mai da asibitocin sa +na mahaifin sa it
wasn't that easy for him gashi ɗan uwan shi yaƙi dawowa sai lokacin da baby doctor ta dawo sannan
abubuwan suka mai sauƙi but still wannan baƙar tambarin ƙin da ke tsakanin su ya sa instead of them to
be close and work hand in hand with each other sai suka kuma tsanar juna because shi yana nuna mata
ya rigata zuwa system ɗin muddin girman kan ta ba zai saka ta saukowa ta nemi assistance ɗin sa ba toh
kuwa sai dai ta rinƙa yin abubuwan ta ita kaɗai dan shi ba zai taɓa saka hannun sa a abubuwan ta ba
hakan ba ƙaramin ci mata rai yake yi ba ganin ita da asibitin mahaifin ta amma ana mata iko da mulki
gashi mahaifin nata bai shirya ganin abin da ke cikin duhu ba mahaifiyar ta kuwa bata son jin negative
side ɗin Dr Zaid sanar da ita abin da ke faruwa is a total waste of time.



Bilkisu Muhammad Sulaiman shine ainihin sunan ta wanda aka fi sani da baby doctor,ita ce ɗiya ta uku a
wun iyayen ta su biyu aka haifa lokaci guda ita da twin brother ɗin ta mai suna Bilal akwai babban yayan
ta mai suna Jamil wanda yake age mate ɗin Dr Zaid kuma aminin sa but shi ya yi aure har ma da baby ɗin
su Zarah kuma shi ɗin navy ne tun fari mahaifin shi ya so ya karanci medicine amma ya nuna interest ɗin
shi ba a nan yake ba shi yasa ya rabu da shi,mai bi mai shine Lukman mai aiki da Nigerian custom shima
haka mahaifin sa ya so ya bi medical line amma ya ki,abin ya dami mahaifin na su dan shekarun sa sun
fara ja but babu mai jan ragamar asibitocin sa not until lokacin da Zaid ya fara tafiyar mai da abubuwan
sa ganin haka ya sa yayi ƙoƙarin ganin ɗiyar sa ta dage a medical line ɗin dan dai ta zama mai share mai
hawayen shi wani abin dole sai naka daman toh a nata ɓangaren ma haka ne she dearly loves her dad
dan haka ta tashi da ƙudirin maye mai gurbin da yayyen ta suka kasa because even her twin brother bai
amince ya hau medical line ɗin ba instead ya je ya karanci banking ita kaɗai ce ta bi line ɗin mahaifin ta
shi ya sa ya fi fifita son ta akan yayyen ta bugu da ƙari sunan mahaifiyar Dr Muhammad gare ta.



Yarinya ce ƴar shekaru 24 wacce ta sami takardar zama cikakkiyar likita at early age yarinya ce mai kaifin
basira da ilimi wanda ilimin nata ya ke zame mata makamin yaƙar samari masu kawo mata hari da
farmaki dan duk ilimin ɗa namiji muddin ya kawo mata shiriritar wai son ta yake toh tun daga lokacin ya
zama marainin wayon ta dan fah ita maza sam ba su layin ta as for now tana da burin farantawa
mahaifin ta dan haka batun saurayi bai gan ta ba.



Fitinannen da ya addabe ta ya ishe ta a rayuwa kuma bai da niyar rabuwa da ita duk wulaƙanci da cin
kashin da take mai amma ya naniƙe mata shine Dr Aslam yaro ɗan gatan Mama da Baban shi shi kaɗai
suka haifa a duniya dan haka suka yi over pampering ɗin shi abin da yake so shi za'a mai in fact bai da
self discipline a haka ya taso a gidan su yayi karatun sa a ƙasar barure ƙasar London ya taso da ratuwa
irin ta masu jajayen kunne bai san wannan abin yayi ba mo a'a bai yi ba in dai shi ya mai toh
shikenan.dawowar shi ƙasar ya haɗu da baby doctor a wani medical conference meeting wanda zallan
doctors ne suka haɗu dan ƙarawa junan su ilimi a inda a nan ya ji kawai ta mai he thought it would be an
easy task since shi ɗin ɗan gidan manya ne not knowing that ita ɗin men headache ce yayi yayi ko
friendship ne su haɗa ta mai banza ƙarshe dan fitina sai da ya san yadda yayi ya sa mahaifin ta ya bashi
gurbin zama ma'akaci a asibitin da take running actually shi kan shi mahaifin nata ya ji mamaki
kasancewar ya san shi kuma ya san irin gata da daular da yake ciki toh dan me zai zo neman alfaar yin
aiki a ƙarƙashin shi.



Tun da ya sami aikin nan ya rinƙa ɓarin ƙafa since he is from a free home babu wanda ya takura ko ya
tsaurara wa decision ɗin sa tunda ya ce yana jin daɗin aikin da zai fara so let it be suka yi supporting ɗin
shi a gefen baby doctor kuwa abin bai mata daɗi ba sai dai da yake ta kasance ƴa ce mai biyayya ga
umarnin mahaifin ta sai ta amince amma ba wai dan ran ta na muradin hakan ba..haɗuwar su ta farko a
office da shashancin ya tunkare ta ta ɗaga mai ƙafa thinking that he will change amma haka abin ya
cigaba da repeating kanshi sai a wani faithful thursday da ta kwance mai notice ɗin bala'in ta ya ga fah
muraran fitinanniyar kan ta ne sai ya ɗan yi sanyi madaɗin ya fita harkar ta sai ya cigaba da bibiyar ta ita
kuma mutunci mahaifin ta da take gani ya sa bata kuma warware mai tsakanin zare da abawa ba dan ko
na farkon da ta mai an kai ƙararta wanda take da tabbacin Dr Zaid Maher ne dan shine mai liver ɗin
kwashe stuff ɗin office ya mayar gida ma mahaifin ta gashi he knows that her dad is her weakness bata
iya jayayya da shi.toh fah tun daga ranar da ya ga ya kira ta da Beelove bata yarfa shi ba sai ya cigaba
wataran ya ce mata Beelove wataran ya ce mata baby abin na baƙanta mata rai dan dai ita ta san babu
inda zata kai shi dan waɗanda suka fi shi tsari,fasali da hankali ma ta watsa su bare shi da ba cikakkiyar
ilimin addini gare shi ba.
Wani abu da ke harzuƙa Dr Aslam shine ganin irin special attention da mahaifin baby doctor ke bawa Dr
Zaid dan komai ya taso sai ya ce a nemi Dr Zaid ko Dr Bilkisu da ke ɗiyar shi bai wani cika kiran sunan ta
ba sai Dr Zaid ganin kusancin su yayi yawa gaahi shi kuma so yake ya share wa kan sa hanya a wun Dr
Muhammad Sulaiman dan ya amince ya bashi auren baby doctor amma ya ga hankalin sa ya karkata ga
Dr Zaid sai ya fara kishi marar dalili da Dr Zaid duk a tunanin sa hala akwai wani hidden relationship ne
tsakanin Dr Zaid da Dr Bilkisu wanda ya sa Dr Muhammad ke karkata akalar shi zuwa ga Dr Zaid kuma
abin da ya kasa ganewa shine babu wata kyakyawar jituwa da fahimta tsakanin Dr Zaid da Dr Bilkisu a
haka yake masu kallon kamar masoya ne su saboda tsabagaren girman kai da izza da ke ɗawainiya da su
su biyun da haka yake ƙoƙarin ganin ya ƙure Dr Zaid a komai tun daga dressing har kwarewa a aiki sai dai
ya makaro dan duk moves ɗin shi Dr Zaid ɗin ya gano da yake shima ɗan kan shi ne sai ya bar shi a haka
ya ta wahalar da kan shi ya mai biris kamar bai ɗago komai ba shi haushi ma yake bashi ganin wannan
ƙanƙanuwar yarinyar yake ma wannan haukar yarinyar da bata ma san da zaman shi ba abin da yake
saka shi sakar mai maganganu kenan a duk haɗuwar da zadu yi amma da yake sakarai ne bai wani
ɗaukar abin chan ciki.



Sunan ta na baby doctor kuwa ya samo asali ne daga mahaifin ta wanda shi ya laƙaba mata shi
kasancewar ta very smallish and young and she was able to acquire a doctorate qualification at a very
tender age she tressure and value the name sosai hakan ya sa tun mahaifin ta ke kiran ta da sunan tana
amsawa har ya kai ga sunan ya bi ta ko a gida ne,family ɗin su ne,neighbours ɗin su har office da sunan
ake kiran ta dan fah ko fushi take yi aka kira ta da sunan takan huce dan tana respecting sunan sosai shi
yasa da Dr Aslam ya gane ya ke mata abu son ranshi dan ya gano makarin ta sai dai still in tana jin
zazzagar ta bata ɗaga mai ƙafa ko da kuwa sau dubu zai yi bitar sunan ta a bakin shi ba sassauta mai take
ba sarai ta san tarihin shi abin da yake daɗa ƙara mata ƙarfin wulaƙanta shi kenan wai ko zai yi fushi ya
rabu da ita amma ya ƙi dan jaraba ƙarshe fita a harkar shi ta yi ko da theater take da shi bata kiran shi
yayi assisting ɗin ta yadda bata gayyatar Dr Zaid sai dai in dan kashin kan sa ya zo ya mata tsayuwar
sojoji toh haka shima wannan yadda ya zo ya saka hannu haka zata share shi babu uhm ko uhuhm illah
in ya harzuƙa ta da zarar sun fita ta balbale shi ta wuce abin ta haka zai rinƙa bata haƙuri kamar marar
zuciya abin ba ƙaramin ƙona ran Dr Zaid yake yi ba shi yasa ya ji ya ƙara ƙin baby doctor gashi ya rasa ta
inda zai ƙuntata mata dan ta dawo cikin hayyacin ta ta daina wulaƙanta maza ta rigada ta siye imanin
family ɗin shi baki ɗaya dan kamar wasar asiri duk babu mai son jin laifin ta they believe that she is a
genus dan haka sun fi alaƙanta rashin jituwar Dr Zaid da baby doctor a matsayin rashin fahimtar junan
da basu yi ba ne dan shi ya kasance irin natsatsun mazan nan masu hankali da sanin ya kamata haka
Itama ta kasance quite simple lady marar son jayayya da maganr manya especially iyayen ta in akwai abu
na farko da Hajiya Madina ke matuƙar so shine respect wanda tuntuni ta hango hakan tattare da baby
doctor shi yasa ta aminta da abotar su da ɗiyar ta Bahajjatu tun yarinta har yanzu again silently she is
praying for a special day that will come da zata haɗa zuri'a da ahalin Dr Muhammad Sulaiman bata san
cewa iyaye mazan sun riga iyaye matan yin wannan tunanin ba tuntuni dan haka itama Hajiya Zeenat ta
gama haɗa nata tunanin suka sanar da juna murna suka yi sosai ganin tunanin su ya zo ɗaya sai dai basu
bari mazajen su sun sani ba wai tunda su ke juya su su zuba masu idanu kawai dan jin me zasu ce in sun
tuntuɓe su da batun auren ƴaƴan separately akan in amsar bai zo masu yadda suke so ba sai su juye
maganar sun san dole su amince da su a kan wannan yarjejeniyar suke..



Ana zaune ƙalauya ƙirƙiro da wani tafiyar outreach har zuwa Adamawa a Adamawar ma chan cikin
yankin Koma inda ya san babu wanda ta sani a chan dole shi da ya ƙirƙiro tafiyar shi zata na bi a lagwas
har su gama su dawo wanda da biyu yayi arranging ma tafiyar na farko shine ya haɗu da sanyin idanuwar
sa na biyu kuma ya saita baby doctor kafin su bar ƙauyen.



Ko da ya sanar da iyayen shi akan outreach ɗin sun jI daɗi ƴaƴan su sun yi kaifin basira dan shi ce masu
yayi decision ne that was made between the two of them da labari ya isa kunnen ta rasa abin cewa ta yi
dan dai the last time she checked ba su taɓa samin conversation mai ma'ana a tsakanin su ba na good
2minutes sai dai yaɗeyaɗen maganganu na ban haushi toh ta yaya zai mata wannan saurin shiga haka
and she can't say no to her dad bayan albarka da ya gama duldula mata but in har tafiyar ta tabbata lallai
zata gwada mai taurin kai irin nata dan komai ba zata yi ba har su gama su dawo a haka ake wanda duka
ƴanuwan su ke murna thinking that sun fara jituwa ne especially Bahajjatu da Bilal waɗanda ke tsokanar
su da cewa wataran wannan rashin jutuwar tasu na iya rikiɗewa ya koma soyayya sai dai ta ji su ta kyale
dan tana da wannan ɗabi'ar ta kyale mutum in yana mata magana..



Despite all this her attitude tana da disability ɗaya she is cold blooded saboda tana da chronic
pneumonic patient ce ita for so long tun da ta cika shekaru shida a duniya abin da ya ɗaga ma iyayen ta
hankali da yayyen ta dan shi twin brother ɗin ta ma har kuka yakan yi akan shi a dawo mai da rashin
lafiyar as a young child back then bai san komai ba sai da suka girma a nan ya dage akan kula da ita har
wasu lokutan takan tasa shi gaba da masifar ta akan he is being overprotected kamar shine Prof ɗin
gabaɗaya bai biye mata sai dai ya rarrashe ta as she is the eldest shine hussainin ta haka ta ke mai big sis
stuff kamar ta bashi wasu shekaru ne..



Yayin da ƙiyayya ke ruruwa tsakanin Dr Zaid Maher da Dr Bilkisu Muhammad soyayya ce ke gudana
tsakanin Bilal twin brother ɗin baby doctor da Bahajjatu ƙanwar Dr Zaid babbar aminiyar baby doctor
daga gida wun iyayen su Bahajjatu an san da labarin soyayyar su dan haka ake jiran ranar da za'a saka
bikin su at first abin banbarakwai ya ma baby doctor but tunda ta ga ita kanta

Please Login or Register in order to submit comment