You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannun

"Hero yi bacci ka ji,saboda abin da kake son aikatawa bai dace da lafiyar ka ba right now ka bari har ka
kuma warwarewa okey"??ta lankwasar da wuya sai yayi wani dariya yana kallom ta..

Ya saka ta a duhu har ta rasa me zata ce da shi sai ta cigaba da kallon sa har ya tsagaita dariyar nasa ya
kalle ta yana mai kai hannun sa saman bakin sa

"My girl ɗazu ɗazu fah kika gama shafe ni kina romancing ɗi na kina faɗin kin ji kewa ta kina kan jin
kewar ma har yanzu duk kin gama tattaɓa ni kin saka ni cikin halin da kike ciki sannan yanzu dan zan
taimaka in taya ki quenching thirst ɗin ki shine kike wani noƙewa kike son ƙaryata zamcen da na zo maki
da shi?haka kike dama baby"!???..

"What"?ta faɗi a bayyane sai ya ɗage kafaɗar sa alamun oho sai ta shiga girgiza kai tana mai son
kwanciya dan zancen nasa kamar wasar yara yake a kunnuwar ta..

"In kika kwanta zaki ja ma kanki"!!cak ta dakata haɗe da ɗagowa tana kallon sa fuskar ta babu alamun
wasa ta ce
"Zaid baka da lafiya,kana buƙatar kuzarin jikin ka ko so kake ka cigaba da zuwa asibiti a ko da yaushe
kullum muna hanyar asibiti duk dan saboda kai haka kake so?uhum?me ya sa baka son fahimta ne wai?
in ka ƙara haƙuri kamar yanzu ne dan baka huta da ni ba Zaid hakan ba yana nufin baka isa bane,,a'a
yana nufin kai ma ka damu da lafiyar ka kana son samin sauƙi..amma kawai dan kana son kayi proving
min kai ɗin jarumi ne da har zaka tafi kowani length just to show me sam baya birge ni bana son
hakan,na fi son ka natsu mu taru mu samar maka da lafiyar ka ingantacciya har ka wake in ya so duk
wani abin da zai faru sai ya biyo baya ta hakan ai zamu fi mayar da hankali mu yi komai cikin lumana da
jin dadi hade da kwanciyar hankali zai fi armashi Zaid baka tunanin haka"??shiru yayi yana sauraron ta ya
san gaskiya take faɗi dan sam bai wani jin kuzari amma so yake ya isar mata dan kar ta mai kallon lusari
marar jarumta..

Ɗago ƙwayar idanun sa yayi ya zuba cikin nata sai ta kai hannun ta kumatun sa tana shafawa ta ce

"Trust me hero,kai ɗin jarumi ne ni zan faɗi haka can you believe it,?rounds huɗu muke yi a single night
kuma baka gajiya hasalima ni ce mai nuna gajiya ta ni ce marar jarumtar ba kai ba Hero dan haka ka ƙara
haƙuri kamar yanzu ne highest ba zamu ƙare honeymoon ɗin nan ba tare da mun yi resuming duty ɗin
mu ba sanin kan ka ne hakan ai ko"?fuskar sa kamar wani ƙaramin yaro haka kamar zai yi kuka ya ce

"Amma ni so na ke in isar maki babes,bana so ki zauna cikin thirst ɗi na alhalin ba rasa wanda zai yi
quenching maki kika yi ba i don't wanna let you all alone shi yasa na ke son fitar da ke daga ƙishirwar da
kike ciki"murmushi tayi tana mamakin hali irin na Zaid ita kam Allah ya haɗa ta da miji

"Na sani hero shi yasa nake kiran ka da hero dan kai ɗin hero ne babu wanda ya isa ya nuna maka
jarumta ta ko ina miji na na yarda da dalilin ka amma mu ƙara haƙuri duk mai wucewa ne wataran sai
labari hmm"??gyaɗa mata kai yayi yana mai bin ta da kallon sha'awar ta dake damin sa sai dai kamar
yadda ta faɗi ne lafiyar sa na gaba da komai a gare su su duka dan haka lallaɓa sa tayi yayi bacci ita kuma
ta tsura mai ido tana kallon sa tana kallon erection ɗin sa sai ta girgiza kai dama mutumin da yake ji da
ƙarfi da bajinta ba ko wani lokaci yake iya jure rashin abu mafi muhimmamci a rayuwar sa ba...

Miƙewa tayi ta sauko ta nufi hanyar toilet tayi alwala ta fito ta fara sallar nafila,zama tayi tana tasbihi
har shabiyu da rabi ya gota sai tayi estimating time kasancewa awowi biyu ne tsakanin Dubai da Nigeria
sai ta yi concluding kiran Umman ta dan yanzu su suke kaiwa 10pm saboda shawarar ta take nema cikin
gaggawa dangane da zancen da Zaid ya mata akan Asma'u dan ita sam abin bai kwanta mata a ran ta ba
wai su nemo ainihin bakin zaren ta fi ganin a share zancen kawai shi zai fiye masu dan ita ba wai son
kuma haɗa ido da yarinyar nan take ba...



Tashi tayi ta ɗauki wayar ta dake saman side drawer ta dawo saman sallayar ta zauna tayi dialing
numbern Umman nata ta tsaya jiran ayi picking,ba jimawa aka ɗaga wayar sai ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Umma ina yini"!!cikin ɗaurewar kai Hajiya Zeenat ta ce

"Lafiya ƙalau Bilkisu lafiya cikin tsakar daren nan kika kira ni"??ajiyar zuciya ta kuma saukewa kafin ta ce
"Lafiya Umma amma ba lau ba"!!tashi tayi daga kwancen da take tana faɗin

"Me kuma ya faru Bilkisu ba dai jikin Zaid ɗin bane"?girgiza kai tayi kamar tana gaban ta kafin ta ce

"A'a Umma ba shi bane"sight na relieve Hajiya Zeenat ta sauke sannan ta ce

"Toh ina jin ki menene"??jujjuya maganar take a ran ta ta faɗa ne ko kuma tayi shiru ne saboda a wani
fuskar abin yana mata kamar sirrin su ne ita da mijin ta bai kamata ta bayyana ba sannan ta wani fuskar
tana ganin ya kamata ta faɗawa mahaifiyar ta dan wannan zancen ba wanda zata iya sanar da Bahajjatu
bane kasancewar ta ƙanwa ga mijin ta dan in a matsayin aminiya zata faɗa mata maganar toh ba laifi
amma tana matsayin ƙanwar Zaid bata jin abin zai dace maybe ma Bahan ta rinƙa kallon yayan nata da
wani irin ido ita kuma ba kasafai ta fiye son ana raina mata miji ba dan haka sai kawai ta yanke shawarar
sanar da mahaifiyar ta kawai at least zata iya bata shawarwari more than Baha..

"Bilkisu ina jin ki dare fah yayi bacci zan yi kika hana ni yi"!!shiru tayi kafin ta buɗe baki ta fara yi mata
bayani

"Umma kin ga Zaid ne,,,har yanzu fah bai rabu da zanven wannan Asma'u of a girl ɗin nan ba,sai cewa
yayi ma wai mu tafi mu samo asalin zancen har fah ya fara ganin laifi na wai bana fahimta ce min yayi
baya jin yarinyar na da laifi akan allegations da nayi laying mata is like yana goyon bayan ta ne ko
menene ban gane mai ba ni kuma gaskiya Umma hankali na sam bai kwanta da wannan shawarar nasa
ba kwata kwata bana son sake haɗa ido da yarinyar nan i don't know why kawai bana son ta ne bata
kwanta min a rai ba kuma Zaid sai nanata min kalmar in ba dan ita ba da baya existing yanzu da haka
does that mean that ni baya recognizing nawa ƙoƙarin da nake mai dan ganin ya samu lafiyar sa ya dawo
dai dai yadda yake a baya?Umma ni na gaji da halayyar Zaid babu abin da yake min da bana so illah abu
ɗaya shine kiran sunan wannan yarinya da yake yi ba wannan kaɗai ba har kare ta da yake yi ba son sa
nake ba ni na gaji ma da jin zancen ta ɗazu ya ke ƙara tambaya ta akan amsar da tambayar da ya min
gameda maganar yarinyar da ya kawo min i have to take his moment duk dan kar ya kuma yin maganar
saboda ban da tangible response ma tambayar nasa shi ya sa na ce zan sanar da ke Umma in kina da
alternative please engage me in it dan Zaid yana pushing ɗi na so hard akan zancen Asma'u of a girl ɗin
nan"!!!duk ran ta ya gama ɓaci yayin da take maganar ita kuma Hajiya Zeenat bata yi interrupting mata
maganar ta ba har ta dire..

Idan akwai abu da zata cire cikin zancen Bilkisu toh abubuwa guda biyu kacal jiga jigai zata iya cirewa
cikin zancen nata wato kishi da rashin fahimta dole ta fitar da ita daga cikin wannan duhun tunanin da
zargin dan kishi dai irin na Bilkisu bata taɓa ganin sa ba ko a baya da tayi irin tata kishin akan gaskiyar ta
tayi ta ba akan zargi da rashin fahimta ba..



"Bilkisu kina ji na"?amsa mata tayi jiki a sanyaye

"Eh ina ji Umma"
"Da kyau toh,,ki saurare ni ki kuma fahimce ni da kyau dan abin da zan sanar da ke ƙila ba zai maki daɗi
ba amma dole ni ɗin ce zan sanar da ke..,Bilkisu kina fama da matsananci kishi mai duhun gaske sam
babu haske cikin kishin ki wanda shi ya janyo maki rashin fahimtar mijin ki kwata kwata kin kasa gane
abin da ke gaban ki sakamakon baƙar kishin sa da kika ɗorawa kan ki Bilkisu,ban ce kar ki ji ko kar kiyi
kishin sa ba amma ana sara ana duba bakin gatari shi fah Zaid namiji ne mijin mace ɗai ɗai har huɗu
kenan bayan ke yana da ikon ƙara wasu har uku dan ya cike gidan sa,baki da hurumin taso sa gaba kina
nuna mai aon ra'ayin ki akan dole shi zai hau ya zauna duk dan kar ya ɓata maki rai...,kija sane yarinyar
nan da za'a bar sa auren ta zai yi dan shaƙuwar da ta shiga tsakanin su a baya bugu da ƙari yana mata
kallon yarinyar da ta taimake sa saboda wannan dalili kawai Zaid na iya auren ta kuma babu tambayar
hakan dan so dama yakan faro ne da tausayi toh a naki case ɗin sai kika tausaya masa fiye da yadda shi
yake tausaya maki wanda ya saka ki zurfafawa da yawa cikin son sa da ƙaunar sa har ma kike kishin sa
fiye da yadda mutum zai iya misaltawa kwata kwata baki ganin abin da ya dace da wanda bai dace ba
iyakar wanda hankalin ki ya kwanta da shi shikenan shi zaki yi which is totally wrong,,namiji ne fah Zaid a
ganin ki kin isa hana sa ƙaro mata ne?ko gani kike son da yake maki zai rinjayi faranta ran sa?namiji ba
zai taɓa sakewa da ke ba muddin kika zaɓi ki rinƙa canza hanya da shi ta yadda in ya kawo maki magana
sai ki nuna cewa baki tare da shi duk saboda wani dalili chan na ki toh kuwa in kika nuna mai haka dole
ya fara janye jikin sa da ke daga haka sai ku nesanci juna abubuwa su ta faruwa a tsakanin ku amma baki
sani ba rashin fahimta ta shigo tsakanin ku duk sakamakon laifin mutum ɗaya amma in kika nuna mai
kina tare da shi ko da kuwa hakan bai maki ba ba ƙaramar ƙima zai ƙara maki a idanun sa ba dan zai rinƙa
counting on you zai ga yana da strength bai da wani fargaba saɓanin ture sa da ingiza sa shi da damuwar
sa kawai dan baki yi na'am da shawarar sa ba...wannan kishin da kike ganin sa Bilkisu nayi fah,na yi shi a
lokacin da yake da riba ba yanzu ba da in kika yi wuya zaki sha dan mazan zamanin nan ba'a nuna masu
baƙar kishi tuni suna jin kan su suna ji da kuɗi da ganin zamanin su ne sai su sauya ki,,.. Babu abin da ya fi
ƙarfin addu'a i was very prayerful da ƙarfin addu'a Allah ya yaye min kusan 85% cikin kashi ɗari na kishin
da nake fama da shi..na daɗe ina maki addu'ar nan taAllah ya sa kar ki yo gado na ta fannin kishi sai dai
ban san me ya sa ba sai gashi kishin ki har yana son ɗare nawa kishin,

Ɗazu da kike narrating min matsalar ki sai na gano wani abu is like you are lacking in your prayer
point,baki da ƙaƙƙarfar prayer point Bilkisu dan da a ce kin san falala da ƙarfin addu'a da kin damƙe sa
sosai dan shi kaɗai ne zai magance maki wannan tsantsar baƙar kishin ta ki da ya saka ki kasa fahimtar
mijin ki..

Bilkisu falalar addu'a mai girma ce dan ni zan faɗi hakan kafin ni akwai mutani da yawa da zasu bayyana
maki falalar addu'a kafin su akwai amintattu,Mursalai da addu'a haɗe da falalar ta suke magance masu
damuwar su kamar Annabi Ibrahim addu'a yayi Allah ya ƙetarar da shi daga sharrin mutanen sa da kuma
wutar da suka saka shi ciki,haka annabi Yunus shima yawan addu'a da tasbihin sa ga Allah ne ya sa Allah
ya fito da shi daga cikin kifin nan,ga Annabi Musa ma wanda addu'a yayi Allah ya raba sa da kaidin
Fir'auna da mutanen sa a inda ya buga sandar sa ruwa ya rabe shi kuma fir'auna ya halaka tare da
muƙarraban sa ciki,ga Annabi Nuhu wanda shima addu'a yayi Allah ya saukar da ruwar ɗufana a duniya
baki ɗaya,again ga annabi Muhammad S.A.W wanda shima addu'a yayi Allah ya halakar da Abujahil,Utba
da Abu-Lahab har ma da sauran mugayen kafirai maƙiya musulunci,,,kenan kin ga girman addu'a da
falalar sa in har mutum ya bi ƙa'idar sa kamar yadda Allah da mazon sa suka umarta,Bilkisu falalar addu'a
Allah kaɗai ya san sirrin da yake cikin ta dan haka duk wani damuwa,tsanani da tsaurin da bawa zai tsinci
kan sa a ciki addu'a ta ishe sa maganin wannan damuwa ta sa..

Muddin kika riƙe addu'ar nan da hannu bibbiyu Bilkisu wannan kishi naki na Allah ya kiyaye toh ina da
tabbacin babu wani magani da zaki sha da zai magance maki shi face falalar wannan addu'ar saboda
haka ina nan zan taya ki da addu'ar Allah ya yaye maki wannan kishi taki kema dole ki tasho tsaye da
addu'a sannan ki gyara halin ki kar ki ga kina mace wai kina da abin jan ra'ayin mijin ki wannan duk
shirme ne dan gidan auren da babu ƙaƙƙarfar addu'a a cikin ta kamar kwanko ne marar abu a ciki so you
need to buckle up and improve in your lapses ki gyara zaman auren ki ki rinƙa supporting mijin ki ko kina
so ko baki so ki nuna mai kina tare da shi hakan zai saka sa ƙara samin sakewa da ke dan haka kar ki ƙara
nuna mai cewa baki son ra'ayin sa always show him that you are with him and i bet you zaki ji daɗin
zaman gidan mijin ki and you will say it out to other women out there who are very tedious when it
comes to jealousy..

Sannan find it in your heart to understand that girl and also know her reason for doing such dan duk
zafin da zaki ji a bayan na mahaifiyar sa ne dan ita ta san zafin sa ke tsintar sa kika yi baki san wuya da
wahalar da mahaifiyar sa ta sha a kan sa ba amma ita kan ta ta bar zancen ta dangana hakan da ƙaddarar
rayuwa ce wanda babu wanda ya isa ya tsallake sa bare ya canza sa but ke kin zurfafa da yawa cikin
maganar kin ɗau abin da zafi kina ta blaming yarinyar ba tare da kin sa dalili ba wanda hakan haramun
ne saboda na san kin sani dan kin karanta a hadisi inda ake gargaɗin mu da yin zargi aka ce _iyakuwa
zanna,fainna zanna,akhazabul akhihi_ wato fassarar sa shine Allah SWT ya ce _ina maku hani da yin
zato,domin ita zato,magana ce ta ƙarya_

You see,tunanin ki lies on this dan haka ku canza ki mai da shi kyakyawa ki rage ko ma ki daina
gabaɗaya zargin da kike yi dan wataran kina iya jin kunya akan zargin da ba gaske bane kuma na san ki
baki da hayaniya so it will be very bad of you a ce ana maki raddi sakamakon zargin da ba gaske bane
these are all minor minor things we ignore in our marriages kuma su ke dawowa su zama manyan
matsalolin mu dan haka i hope you will transform your perception into a negative one baby and i pray
Allah ya ƙara shiryar mana da ku ya daɗa kare mana ku ya ƙara maku fahimtar junan ku da haƙurin
zaman tare ya kaɗe duk wani mugun abu da zai shigo maku marar daɗin ji da gani a rayuwar auren ku
dan hankulan mu baya kwanciya matuƙar naku ba a kwance yake ba.Allah ya maku albarka"....



Nannauyar ajiyar zuciya Bilkisu ta sauke sakamakon jin wannan extensive exclusive sermon da
mahaifiyar ta ta mata wanda is in different form da ya haɗa da faɗa,wa'azi,wayar da kai,jan kunme and
most of all tunatarwar da ta mata akan rashin riƙe addu'ar da bata yi wanda shine kamar garkuwa a gare
ta ta san she is weak ta wannan ɓangaren dan bata taɓa zaman yin addu'ar Allah ya yaye mata kishin ta
ba ba ma ta tunawa da wannan until now da Umman ta ta tunatar da ita then she is lucky for having a
mother like Umma Allah ne kaɗai zai saka mata da alkhairi akan ƙoƙarin ta da take yi akan ta da su ƴaƴan
ta ma baki ɗaya..
jan numfashi tayi kafin ta ce

"Umma nagode Allah ya saka da alkhairi ban taɓa yin wannan tunanin har na ware lokaci na na zauna
nayi addu'a ta musamman akan sa ba sai yanzu da kika ankarar da ni Umma Allah ya baki lada kuma
Allah ya bar mana ke ya ƙara haɗe ki da Abban mu"da murmushi mai sauti ta ida maganar wanda ya saka
Hajiya Zeenat murmusawa itama tana faɗin

"Allah ya shirye ki Bilkisu kin mai da ni grannyn ki ko"?sai ta dara tana faɗin

"Ni na ma isa Umma"darawa suka yi kafin daga bisani ta kuma yi mata ƴar nasiha kafin su yi sallama ta
ajiye wayar ta juya ta kalle sa sai sharara baccin sa yake yi hankali kwance sai ta mai da duban ta ta ga
yadda lokaci ya ja har ƙarfe ɗaya da rabi ya gota..

Ɗaga hannun ta tayi ta rinƙa kwararo addu'oi kamar ba zata tashi ba har dai ta shafa ta miƙe zuwa
lokacin har biyu yayi..

Naɗe dardumar tayi sannan ta cire hijabin ta ta dawo kan gadon ta kwanta haɗe da sagale yatsun su wu
guda tayi addu'ar bacci daga haka ta rufe idanun ta....



***********

Wasa wasa har suka cinye sati biyu babu wani abu na auratayya da ya shiga tsakanin su kuma dangane
da lafiyar sa yana samin kula kuma Alhamdulillah yana jin sauƙi sosai har ya fara bijiro mata da very soon
zai bi haƙƙin sa dan bashin da ta tara akan ta yawa ne da su ita dai dariya take mai dan huɗubar Ammi
kullum dawo mata yake yi a ranar da zasu koma Nigeria bayan sun zo dyba jikin Zaid da ta kira ta bayan
sun shiga taxi da zai kai su airport, inda tace da ita kar ta yarda su ɓallo liƙi dan daga gani Zaid baya ɗaga
mata ƙafa gashi sai mulka ƙiba yake yi alamun yana samin yadda yake so toh ta bijire mai har sai ta
gamsu da ya warware da kyau in ba haka ba zaman asibiti ya kama su su kuma ba su barin mazajen su su
zo jinyar ƙato saboda jarabar sa ta tsiya da ta saka sa kwamciyar asibitin...

Wannan gargaɗi kullum shi ke saka ta guje mai da zarar ta ga ya ɗauko hanyar nemar haƙƙin sa kuma
tun ranar da Umman ta ta mata magana da daren nan a washegari ta nuna mai ta amince in sun koma
zata raka sa su tafi ƙauyen koma a binciko ainihin labarin hakan ba ƙaramin daɗi ya ma Zaid ba har ya
kasa ɓoyewa ya nuna mata kuma addu'ar da take yi ya saka ta ta fara jin sa'ida cikin ran ta game da
azababben kishin da ke ɗawainiya da ita..

Duk wasu responsibilities ɗin ta na matar sa tana performing except of sexual acts wanda ita kuma
tanadi take mai har ya warke ras dan da kan ta take amfani da kayayyakin da Ammi ta bata kuma labarin
yawan baccin nan duk ya ragu mata ta yi tunanin yawan mating da suke yi zai yi affecting mata baby sai
dai bai faru ba dan har ta shiga second month dake cikin first 3months trimester ɗin ta yadda take kafa
kafa da shi shima haka yake yi da ita sam baya son wani damuwar ta ko rashin kwanciyar hankalin ta
izuwa yanzu kam an fara shopping babies wears shi ce mata yake yadda ya iya shooting nata a karon
farko toh dole ne ma da yardar ubangiji twins zata haifar mai ita kuma sai ta ce da shi ta san single viable
life baby ne a cikin ta duk lokacin da aka yi wannan argument ɗin da faɗa ake ƙare sa sai daga baya ya zo
yana bata haƙuri wai ita dole sai tayi accepting two babies ne a cikin ta ya ta iya da shi dole ta amince da
hakan..



Zaune take tana waya da Baha akan wedding plans ɗin ta

"Kin san fah bana son hayaniya Beelove amma dole bikin autar gida a san an yi biki a faɗin ABJ baki ɗaya
dan gaskiya ba irin taku bikin za'a min ba abu salam lami babu armashi"wani dariya Bilkisu tayi tana
ganin wautar Bahajjatu dan kamar ba so take ta gane bambancin auren da ba'a mai bidi'a ba da wanda
akawa bidi'a..

"Apple kina ji na ko,wato shi fah albarkar aure yayi laying ne akan ƙanƙantar sadakin sa haɗe da
albarkar da aka saka masa,all these parties showing up isn't gonna work for you check this out,an mana
aure ni da yayan ki duk muna cikin magagin rashin lafiya a haka muke har yanzu ba fah mu yi bidi'ar ba
kenan ina ga waɗanda ke ɗaukar bidi'a a komai nasu na rayuwa zaki yi aure kin dage sai kin yi kaza da
kaza da kaza what for?dan ki nunawa duniya ke ɗin wacece?ko dan ki nunawa duniya kina son mijin ki?
you don't do that in kika haƙura Baha am telling you the silent wedding is the perfect and most blessed
one wallahi zaki ji daɗin sa dan baki da fargabar ba'a gama haɗa maki reception ba ba'a kawo intensive
decor designers ba ba'a kawo most talk of the year cake ba blah blah blah all those things duk in kika
toshe kunnuwar ki wallahi zasu wuce kuma in kika so ma ke da mijin ki a ranar da aka yi bikin kuna iya
tafiya honeymoon ɗin ku from there sai ku yi duk wasu abin da zaku yi da baku yi ba during the
wedding"ajiyar zuciya Bahajjatu ta sauke tana faɗin

"Thank you so much Beelove gaskiya kin buɗe min idanu na at first ruɗin jin daɗi da claims sun gama
rufe min ido and i wasn't able to see the effects of waɗannan bidi'ar Allah ya bar min ke matar yaya
na"dariya Bilkisu tayi tana faɗin

"Amin and what are friends for dama if not for benefits"

"Haka ne kin ga dama chan yaya Afzal ba so yake ba ni ce dai na matsu sai ya amince but kin ga yanzu da
na gane ai shima zai ji daɗi"

"Haka ne apple Allah ya shige mana gaba ai 2 weeks to the wedding ma zamu dawo"

"Toh ban da ja Beelove Allah ya kawo mana ku lafiya muna jiran dawowar ku"sallama suka yi ta ajiye
wayar sai Zaid ya shigo dan dama a toilet yake yana wanka jiran ta ya rinƙa yi ta zo tayi joining nasa
amma ta ƙi shiga ta ƙyale sa...

"My girl da wa kike ta waya tun ɗazu"?ya faɗa yana goge sumar kan sa cikin murmushi ta taso ta karɓi
towel ɗin tana goge masa dan an daina saka masa bandage ɗin
"Da Baha nake magana"sai ya kalle ta ya ce

"Me take ce maki halan da har ya fi muhimmancin a gare ki sama da ki zo ki taya mijin ki wanka"?faɗaɗa
murmushin ta tayi tana faɗin

"Wace ni in zaɓi aminiya sama da miji na"janyo ta yayi zuwa jikin sa ya matse ta har sai da ta ɗan ɗaga
mai murya

"Zaid my baby"ta faɗa tana dariya sai ya ɓata fuska

"Babyn ma naki ne kenan toh wa ya baki babyn"?dukan ƙirjin sa tayi tana faɗin

"Who knows"dariya ne ya kuma kufce mata shi kuma ya ce

"Kar ki damu duk dan na ɗaga maki ƙafa ne amma yau na maki alƙawari ko kina gudun fanfalaƙi ne a
faɗin hotel ɗin nan sai na sauke maki gajiya dan kin azabtar da ni na gaji"daga jin haka sai ta fara ja baya
amma ya ƙi sakin ta ya daɗa matse ta

"Zaid my baby"

"Our baby"yayi interrupting nata ya cigaba

"I swear ba wasa nake yi ba ki shirya tarbon gwarzo kuma jarumin mijin ki any moment from now"kallon
kallo suka yi musaya sai ta ja jikin ta tana faɗin

"Yi ka shirya we might miss the show"tana gama faɗin haka ta juya ta canza kayan jikin ta waiting for
him to get done da shirin sa..

Ya

Please Login or Register in order to submit comment