You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su karba a haka.



"Is okey is a very visible reaction it occurs it happens it's actually normal and you need not worry about
the months because we operated directly in the brain and for the brain to heal up completely it need a
gradual healing process for it to be able to transform back to it normal functioning state and so i urge
you to help the patient in it's recovering process"..su dai kallon shi suke ta yi bai sanar da su amsar
ƙarshen ba dan ko ya faɗa ba zai sami attention ɗin su ba dan basu hayyacin su sai ya ce da su

"I guess that's all for now you may see the patient in the next 4 hours".



Godiya iyaye mazan suka masa dan matan kasa cewa komai suka yi sai hawayen da ya ciko masu idanu
dan haka ɗaga su suka yi suka fito ko hanyar ɗakin basu bi ba suka wuce zuwa masaukin su a inda sai a
lokacin suka sharɓi kukan su sosai a nan suka tuno ma da source of all this problems dan haka Hajiya
Zeenat ta fara haukacewa prof akan ita fah ba zata yarda ba sai an koma Nigeria an san yadda za'a yi da
ɗan iskan yaron da ya janyo ma ƴaƴan su wannan fitinar ita ba yafewa zata yi ba an ɗauko hanyar halaka
masu ƴaƴa daga taimako shi dai rarrashin ta yale yi dan a cewar sa ɗaukar fansa duk bata taso ba ta ƙara
haƙuri har su sami kan ƴaƴan su.mai hali baya dainawa dan haka sai da ta gwada mai iko dan kuwa
balbale shi tayi wai dan ba shi ya ɗau cikin ƴaƴan ba bai san azaban da suka ji a lokacin da suke ɗauke da
cikin ƴaƴan ba shi yasa zata ce a kamo masu ɗan iskan yaro ya ce a'a,in banda haƙuri babu abin da yake
ta bata dan ya san ya takalo kenan maybe ma ta daina sauraron sa har sai yaran sun farfaɗo dan haka ya
je ya haɗa mata warm water dan tayi wanka banza ta mai ta ce ba'a yi shi kam dariya abin ya basa dan
tun da abin ya faru bata sami natsuwar ta ba sai yau kuma madaɗin ta ɗan samar ma zuciyar ta hutu da
sukuni tunda sun ji outcome na komai sai kuma ta ɓige da wani rigimar su kam Allah ya basu mata.



A chan apartment ɗin su Dr Maher kuwa rasa abin faɗa Hajiya Madina tayi game da abin iya magana Dr
Maher yayi amma bata bashi amsa ba ƙarshe ma da ya ishe ta sai ta ce



"Dr"ya amsa mata da

"Na'am Hajiya"..

"So nake ka sa a kamo min yaron nan"ya ɗan yi shiru na wasu lokutan kafin ya ce

"Hajiya wani yaro kuma"a ɗan fusace ta ce
"Dr yaron nan yaron ƙauyen nan da ya lahanta mana yara yaron nan da ke son ya kashe mana yaro shi
nake son a kawo min shi in gan shi da idanuna dan in tantance ko ya kai matsayin laying hannayen sa aka
ɗa na ina son sanin ko he is worthy enough to cause this calamity to my boy did you understand me"!??
ta ƙarasa a tsawace bursting into tears of pains sai ya rungume ta yana jijjiga ta shi kansa yana son a
hukunta yaron but for now lafiyar yaran su shine major priority ɗin su..

Afzal da ke da niyar shigowa dan sanar da su cewan shi zai koma Nigeria ya turo Hakim dan akwai
ayyuka da dama da suke asibitocin iyayen nasu wanda ba mai iya kula da su because Dr Aslam baya nan
Kuma jigajigan doctors ɗin duka na nan suna jinyar doctors biyu,jin abin da suke faɗa ya sa ya fasa shigan
sai kawai yayi waya da Bilal da ke asibitin ya ce da shi ya cigaba da kula da iyayen su da patients ɗin ya
mai bayanin komai,ya mai fatan alheri dan a ranar yake son komawa tsoron sa ɗaya idan Hakim ya zo ya
ga yanayin su tun ma na yayan shi it will be hard in bai ɗau law a hannun sa ba dan yaron na da mugun
zuciyar tsiya da basu san inda ya ɗauko shi ba shi da Bahajjatu..



A ranar ya bar ƙasar germany ya dawo ƙasar Nigeria shi Hakim ɗin ya zo ya ɗauke sa ya tambaye sa abin
da ke faruwa shiru ya mai sai da ya dame sa akan ya mai bayani dan ya matsu ya san halin da suke ciki da
fari ya gaya mai yanda likita ya gayawa iyayen su akan surgery was successful har ya fara samin natsuwa
kafin daga baya dai ya daure ya sanar da shi gaskiyar maganar yana jan motar ne ya ja wata irin wawan
burki da yayi sanadiyar tsorata yayan nasa Afzal da ke zaune a gefen sa dan har mai achaɓa da yazo
wuce su sai da achaɓar ta ƙwace masa shi kuma ya juyo a firgice ya cire glasses ɗin idon sa ya zuba yayan
nasa idanun sa da suka rikiɗe zuwa wani kalar shi ja shi ba ja ba babu abin da Afzal ke iya hangowa in
banda masifa da bala'in da ke yawo a idanun ɗan uwan nasa.. Tabɗijam akwai sauran rina akaba Hakim
hmm....................




*I love u my wattpadians muahhh💋💋💋_*



_Enjoy the chappy huh😍😍_



*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

#vote

#comment

*⚜BWA*
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*




*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*13*



Tun kafin ya furta wani abin Afzal yayi saurin dakatar da shi ta hanyar riƙe mai hannun sa ya ce
"Hakim calm down calm down please"amma bai ko tsaya sauraron sa ba dan ya gama zuciya a wani irin
tune mai nuna tsantsar ɓacin rai da fushi ya wani ynƙuro ya damƙo kwalar long sleeve da ke jikin Afzal
ɗin ya fara maganganu

"What are you saying..tell me what are you saying?huh?my brother?my brother is unconscious?kana
son sanar da ni cewa yaya Zaid na chan bai san inda kan sa yake ba har yanzu?aren't you a doctor?can't
you make him recover quickly?did you need money?name your price zan biya ka kawai ka farkar min da
ɗanuwa na if not..if not Dr Afzal i will sue you..i will sue you..ya ɗan dakata na second ɗaya ya
cigaba,,who was that bastard?who is he?who are his parents?huhh?waye iyayen sa a duniyar nan baki
ɗaya?wa ya bashi izinin saka filthy hands ɗin sa a jikin yaya na?tell me am asking you"? Ya ida yana mai
fitar da hawaye a nan ne idanun sa suka rine ainihin rinewa na kalar ja..



Riƙe hannun nasa Afzal yayi da niyar sauke su daga wuyan sa sai dai bai saki ba instead ya kuma
damƙewa da kyau a zuciye ya ce

"Ina tambayar ka wanene banzan da ya taɓa min ɗanuwa na"a ɗan zafafe Afzal ya mayar mai da
martani shima

"Who knows kid brother!i don't know kar fah ka manta nima yaya Zaid ɗanuwa na ne na jini we all
share the same bloodline a jikin mu why don't you understand anything in ka yi fushi ne wai?baka ganin
halin da yake ciki ne?addu'ar mu kaɗai yake buƙata ba revenge ba ko ɗaukar law a hannun mu ba did
you get it"?saurin katse shi yayi ya ce

"No!no Dr Afzal i don't get you"!!a yanayin da yayi maganar one can tell that a sigar da ake kira da
gatse yayi maganar shi Afzal ya san da hakan sai kawai ya rikice mai shima ya shiga balbale sa



"Come back to your senses Hakim,iyayen na chan basu da kwanciyar hankali,yaya Zaid da baby doctor na
kwance bamu dan lokacin da zasu farfaɗo completely ba baka jin tausayin su ne?baka ganin yanzu ba
lokacin ɗaukar fansa bane?baka ganin zai fi ma kowa armashi in aka yi reporting case ɗin to authority
kuma by then victims ɗin sun farfaɗo?a tunanin ka ni ban damu ba e?a jin ka cikin walwala nake na
ganin ɗanuwa na cikin wannan wahalar?gani kake kai kaɗai ka fi kowa son sa a duniyar nan?ce maka aka
yi Bahajjatu bata da zuciyar da zata iya kisan kai ne?amma bata yi ba dan ita kanta jiran farfaɗowar yaya
Zaid take yi saboda she believes in da hankalin sa komai zai zo da sauƙi wurin kamo wanda yayi wannan
abin..i never intended telling you this but saboda gudun kar ka tafi ka ga halin da yake ciki ka dawo ka yi
blaming mutani da dama ko ka yi creating scene a wurin nan shi yasa na sanar da kai but just look at you
look at your self Hakim duk ka bi ka haukace min har kake min iƙirarin in kuɗi nake so in yi naming price
ɗin are you insane?have you forgotten that i am your elder brother?da ina da remedy na matsalolin nan
kana ganin ba zan yi maganin sa tun kafin ya kawo nan ba?for God sake Hakim ka bani haɗin kai please
am the only one doing all these hustle i myself am tired am fed up already i can't handle and control it
all alone i thought i have someone that will understand me but i was wrong babu wanda ya shirya
fahimta ta ciki har da kai Hakim why"?kamar zai yi kuka yayi maganar sai jikin Hakim yayi sanyi bai san ya
furtawa yayan nasa waɗannan zafaffan kalamai ba dan in har ran shi ya ɓaci babu abin da bai furtawa sai
daga baya ya zo yana regretting wasu kalamai...



Rungume sa yayi ya shiga rera mai kuka yana faɗin

"Please forgive me brother,ka yafe min i failed to understand you feelings i was thinking cewa yaya Zaid
yaya na ne ni kaɗai na manta he have a mother a father a sister and brothers even loved ones out there
ka yafe min ɗanuwa na ka gafarce ni"hugging ɗin sa back yayi yana rarrashin sa dan shima ji yake kamar
yayi kukan dan da halin da ɗanuwan sa ke ciki gwara a ce cikin hayyacin sa yake kullum ana masa allurar
kashe zafi har ya farfaɗo gabaɗaya but bai da ikon yin komai dan babu komai da ke hannun sa he can't
do anything absolutely nothing especially when it comes to his family affairs he is weak baya iya
executing komai game da treatment sai dai ya sa a masu toh dama Zaid ne ke da wannan taurin zuciyar
na treating family ɗin sa dan shi baya iyawa gashi Zaid ɗin na kwance banbancin sa da gawa dai shine
numfashin da yake fitarwa..

Kuka Hakim ya zage yayi wanda ya yanke hukunci saidai ya barwa zuciyar sa dan inshaAllah ya yi niya
kuma baya jin zai iya haƙura dan ba halin sa bane ƙin cika abin da yayi niya sai dai in Ammi ce ta gano ta
hana sa amma ko mahaifin sa baya iya mai bare yayyen sa wannan hali na sa da Bahajjatu ya sa Dr
Maher nesanta sa da yara abokan wasan sa tun yana yaro da ya girma kuma ya yi ƙoƙarin nesanta sa da
abokai dan gudun kar ya ɗauko masu abin yaɗawa a duniya saboda ba dan shi ya haifi Hakim ba kuma
shi ya yi conducting delivery ɗin ba tsab yana iya cewa chanza mai ɗa aka yi toh sai abin ya zo mai da
sauƙi same attitude da yake yi shi Bahajjatu ke yi su biyun su suka fita zakka a gidan dan ba'a san inda
suka kwaso muguwar zuciyar da ke taso masu ba time to time dan Hajiya Madina dai bata da zuciya
iyakan zuciyar ta shine tsakanin ta da Dr Maher kuma nasu ne na ma'aurata wanda ya zama very visible
kowa ya sani shima Dr Maher ɗin bai da zuciya hasalima bai da damuwa he is gentile wanda ɗan sa Dr
Zaid kaɗai ya biyo sa a komai except kamannin da ya ɗauko na mahaufiyar sa dan ko Afzal ma a juye
yake wasu lokutan normal wasu lokutan subnormal wasu lokutan abnormal gane mai sai su ƴanuwan sa
amma bare sai ya iya cewa ko jinnu ne da shi masu juya shi but in aka haɗa su da Hakim sai a ɗauke sa a
bar Hakim though Hakim appear to be simple and quite amma ba hakan yake ba dan abu kaɗan zai
harzuƙa shi while Afzal happen to be someone with mood swing shi kan sa ya sani shi yasa baya
misbehaving a wuri kuma da zarar ya ga wannan mood swing ɗin zai fara mai sai yayi isolating kan sa
dan baya son affecting mutanin kusa da shi unlike Hakim da bai da control of his emotions and anger he
break it out bai iya ɓoyewa...



"Can we go home now"cewar Afzal

"Sure brother"ya bashi amsa daga nan suka cigaba da tafiya har suka iso gidan buɗe ƙofofin motar suka
yi suka fito Afzal ne ya fara shiga ciki kafin Hakim ya biyo sa sam fuskar sa babu walwala ko kaɗan dan
haka ma masu aikin gidan sun lura suka kama kan su amma still sai da mai girkin ta fuskanci masifar sa
dan bata gama arranging abinci a kan dinning ba..



Jiki na ɓari ta rinƙa bashi haƙuri dan ba kasafai ya ke samin saɓani da ita ba bai ma cika shiga sabgogin
su ba ya fi yi da masu tsaftace gidan.yau ganin tambotsan sun motsa ta mai uziri Afzal have to calm him
kafin yayi shiru



"But brother kana fah gani bata gama shirya maka abinci ba kusan an hour aikin me take yi in fact ta tafi
she is fired bata da amfani"tarar numfashin sa Afzal yayi ya ce

"Common Hakim ina mun gama da maganar nan tun a hanya?ban ce magana ya wuce ba?why must
you start the unnecessary blame?kana ganin hakan shine mafita a gare ka?in har ba ka fara controlling
fushin ka ba Hakim i fear you won't get a wife trust me"ya juya ya fara hawa kan benen sai ya dakata ya
juyo ya ce da shi

"And apologize to her she is old enough to be your grand momma humm"?girgiza mai kai yayi bayan ya
gama haurawa ya juya ya ba ma matar haƙuri dan kam in bata yi sa'ar granny ɗin sa ba toh zata girmi
dad ɗin sa not even his Ammi shima ya san bai kyauta ba zuciyar taaa ce sai a hankali..




Haurawa saman yayi bai tsaya ko ina ba sai ɗakin Bahajjatu da ke zaune tana amsar reports akan
boutiques ɗin ta,abunuwan da ake buƙata ake sanar da ita akan an yi placing order sai dai sakamakon
bata nan ya sa wasu suka fara zuwa dan withdrawing order ɗin sai dai an basu haƙurin nan da sati ɗaya
komai zai daidaita,abin haushi kamar ta janyo kelita da ke mayar mata da zancen ta tablet ta gaggaura
mata mari take ji sai dai ba hali technology bai kai nan ba sai ta shiga masife ta

"When?when did i hired you to start selling me?when did i ask you to beg some stupid useless
costumers for me?when did i agree to pay you for that?huh"?kamar zaki haka ta koma kelita kam ta ga
tashin hankali da bata taɓa gani ba dama ma'am na da fushi haka but bata taɓa demonstrating ba tabb
ita kam me ya kai ta gaya mata gaskiyar lamarin da ma ƙarya ta mata ko ma juya zancen msybe da bata
sha faɗar har haka ba,tana tsaka da tunanin ta ta ji abin da ya girgiza ta



"You know what?just go you are fired because i hate working with cheap creatures".. Wani irin ihu kelita
ta yi ta tablet ɗin ta fara surutai
"Jesus christ madam please spare me don't do this to me i curse the devil that want to see me in hell i
reject it madam i beg you in the name of Allah almighty don't send me away because i have no where to
go"hanzarin katse ta Bahajjatu ta yi cikin takaicin sunan Allah da ta kira a gurɓace ta ce



"Go to hell go there i guess your parents are there waiting for you right?go and meet them right away
for calling my creator name with no respect i will have to sue you to court annoying thing get lost and
make sure you evacuate that office before i return mtsw"bouncing ɗin ta tayi ta kashe tablet ɗin ta yi
wurgi da shi sai a hannun Hakim dan ya ɗab jima yana sauraron conversation ɗin su a zuciye ya zo but
ganin itama ta zuciyan sai ya ɗan sassauta na sa fushin ya ƙaraso ciki yana son sanin ainihin matsalar ta.

Bata san ya shigo ba sai da ya kira sunan ta



"Baha"!!a firgice ta juyo ta ce

"Na'am waye"?

Ɗan murmushi yayi saboda tsabagen masifa wai da duka hasken da ke haska ɗakin amma bata iya
ganin sa har sai ta tambayi ko wanene..

Zama yayi a saman couch da ke gefe kaɗan da gadon ta yayi crossing ƙafar sa ya miƙa mata tab ɗin
haɗe da cewa

"Me aka maki kike ta masifa bayan kin san na hana ki yawan saurin zuciyar nan"!sai a nan ta gane ko
wanene sai ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce

"Yaya Hakim can you imagine"??sai ya tsaya kallon ta ya ce

"Menene"?tsaƙi mai sauti ta yi ta miƙe tsaye cikin jin haushi ta ce



"Wai wannan banzar yarinyar mai fuskar shanu wai ita kelita ta je tana roƙan clients ɗi na akan sun ce
sun janye order da suka yi placing dan ban kawo masu akan lokaci ba?ta je tana siyar min da dignity a
wun waɗancan banzayen ƴan uwan ta masu fuskar shanaye?ni saka ta nayi?ko aikar ta na yi?hala gani
take biyan ta na yi na ɗauko ta dan ta rinƙa min iskanci da sunan customer care service provider,my
brother is unwell and yet those animals think that i have time for their useless order i have to deal with
her dan ta ma gama raina ni firing her won't satisfy me huuuh"!!ta furzar da iska daga bakin ta wanda
alama ce ta abin ya ƙuntata mata dan haka miƙa mata bottle water yayi wanda ya tsiyaya mata a glass
tumbler ya san ƙanwar ta sa ya san matsalar ta,matsalar yayan ta ne da na aminiyar ta ya sa duk kowa
take sauke mai fushin ta kuma shi bai ga laifin ta ba dan is normal a wurin sa
Amsar tumbler ɗin ta yi ta ƙwalƙwali ruwan sannan ta ajiye ta koma ta zauna ta na sauke ajiyar zuciya
kamar wacce ta yi race ɗin 50km,bin ta yayi ya zauna ya ɗan bata time dan ta dawo full senses nata,ta
ɗau lokaci kafin ta dawo hayyacin ta sai ta ce da shi

"Ina yaya Afzal ɗin"??kallon ta yayi yana jimamin sanar da ita abin da aka sanar da shi shima sai ya ce

"Yana ɗakin sa yana freshen up"sai ta girgiza kai ta gyara zama ta ce



"And them??are they alright"??tayi tambayar ne cikin tsoro shima ya sani sai ya amsa mata da

"Yeah suna cikin ƙoshin lafiya"bata yarda ba dan babu wanda zai gwada mata halin sa sai ta ce

"No yaya Hakim ban yarda ba ban yarda ba,ba kuma zan taɓa yarda ba tell me me yaya Afzal ya sanar
da kai akan su"?she is out of her conscious mindset already sai yayi amfani da hakan yayi narrating
exactly abin da Afzal ya gaya mai dan ya san ta nan kaɗai zai sami abin da yake so..



She was mad she was insane dan maganganu kala kala ta shiga yi wanda a nan yayi nasarar ingiza ta
har ta amince da buƙatar da ya zo mata da shi ita kaɗai ce zata amince da wannan buƙata ta shi amma
ba Afzal ba.



"Thank you baby sis kin gama min komai da kika amshu buƙatata no more cry no more worries from
now henceforth hum"?amsa mai tayi da kai tana share hawayen ta ce mata yayi ta tashi au tafi dinning
dan cin dinner,she wasn't hungry but saboda yayyen ta sai ta ji kamar ta ɗan sami appetite na cin
abincin.



Bin bayan sa t yi suna saukowa suna magana ƙasa ƙasa a nan ya ce da ita ta ma kelita haƙuri ta mayar
da ita bakin aikin ta dan yarinyar na mata ƙoƙari sosai jin sa kawai ta yi dan kamar ydda yake da kafiya
akan abu haka itama ke da kafiya as far as she is concern kelita is fired and that stay final in ba dan ma
shi da yake yayan ta ba ne kuma ta san halin sa ba da sai ta ce hala neman kelitan yake yi da ya nace da
batun a mai da ta bakin aikin ta,da haka suka ƙaraso dinning table inda suka yi zaman 5minutes dan jiran
Afzal kafin ya sauko yayi joining ɗin su,gaisuwa ta musamman suka yi shi da Bahajjatu ta mai sannu da
zuwa tare da tambayar sa masu jiki ya ce mata da sauƙi dan shi gudun sanar da ita gaskiyar lamarin yake
bai san she is aware of everything ba..



Serving ɗin su aka yi suka fara cin abincin peacefully ya ga har sun yi rabin plate bata ce ƙala ba suka
kusa gama cin abincin bata tanka ba sai ya fara suspecting ko dai an sanar da ita ne but me ya sa bai jiyo
hayaniyar madness ɗin ta ba daga ɗakin sa?ko dai ta gyaru ne ta daina masifar ta da ke yawo a jikin ta
ne?who knows maybe Allah ya shiryar da ita.sai ya basar shima bai ce komai ba har suka gama aka yi
clearing table zata tashi ta wuce ya kirawo ta

"Baha"!!tsayawa tayi ta ce

"Na'am yaya"!

"Zo ki zauna ina da magana da ke"komawa ta yi ta zauna kamar wace ba abin da ke damin ta sai da ya
gama nazarin ta sannan ya tambaye ta



"Wai kin kuwa san halin da yaya ke ciki shi da aminiyar ki"??jijjiga mai kai tayi tana share hawayen ta sai
mamako ya kama shi ya ce

"Wa ya faɗa maki"?ta ce

"Yaya Hakim ne"shiru yayi yana tunanin anya ba sauƙi daga Allah bane ya fara zuwar masu seeing that
yayi wa Hakim nasiha ɗazu ya ji yanzu kuma Bahajjatu ta san labarin abin da ke faruwa but yet bata yi
reacting ba?what a miracle yayi exclaiming kafin itama ya shiga yi mata nasiha ƙarshe ma haɗa su yayi ya
rinƙa yi masu nasihar dan dai ya kwantar masu da hankali daga bisani ya ce da su su je su kwanta su
huta.tashi suka yk suka sallame shi kowa yayi hanyar ɗakin sa shima ya nufi nasa ɗakin da relieve na
samin chanji a gidan na su daga wun ƙannen sa at least sun girma da zasu iya taya sa wurin taimakon
yayan su da baby doctor si yi recovering lafiya ƙalau,with this thought in his mind ya kwanta bacci dan
bai so a kira shi a fara tambayar sa dalilin sa na dawowa sai ya kaahe wayar gabaɗaya he believe Bilal
can handle everything kafin Hakim ya tafi dan shi a nasa ma in ya gama monitoring Bahajjatu ya ga eh
lallai ta yi hankali bata da zuciyar nan da ya san ta da shi sai su tafi tare da Hakim....



Kusan kwanaki biyu yana lura da ita babu abin da ya samo na ganin ido daga gare ta dan haka ya yanke
hukuncin yi mata albishir na tafiyar ta da Hakim zuwa ƙasar germany akan da dare in sun haɗu a dinner
zai sanar da ita dan da ya so su tafi tare da either Lukman or Jamil but dukkan su babu wanda ke
available sai dai in sun dawo daga tadiyar da suka yi.



It was in the morning da suka haɗu wun breakfast yana ma sauri zai tafi asibiti yake sanar da su cewa he
have a surprise for the both of them in ya dawo suka ce mai sun matsu ya sanar da su amma ya ƙi yayi
tafiyar sa.fitar sa babu daɗewa suma suka yi ficewar su..




_10:00pm_
Afzal,Hakim da Bahajjatu,zaune a parlor suna jiran jin me zai sanar da su amma yayi shiru sai chan ya ce

"Guess what"?turo baki tayi ta ce

"Whattt yaya kana ta ja mana rai"!!ɗan dariya yayi kafin ya ce



"Zaki bi Hakim ku tafi germany gobe dan komai naku is well set babu wani abu da ya rage"!!murna ne ya
kama su su duka har ta je ta rungume sa tana ce mai



"I love you yaya i love you so much thank you for allowing me to go visit them"murmushi suka mata
daga baya suka ma Afzal ɗin godiya ya ce da su su shirya tafiyar wuri za su yi,murna ne fal a ran su dan
haka cikin nishaɗi suka yi shirin su suka kwanta bacci....




*************

A chan germany kuwa da Hajiya Zeenat ta gama fushin ta sai ta haƙura ta tafi ta yi wankan ta abincin ne
dai bai shiga sosai ba dan bata jin zai sami masauki a

Please Login or Register in order to submit comment