You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba beelove"abin mamaki ya ba wa Bilkisu sai ta kasa
furta komai sai zancen zuci yanzu wai ta zama matar wani kenan fah!ikon Allah.

Suna tsaye a wurin Hakim ya zo wucewa dan kwaso sauran kayayyakin Zaid da ba'a gama kwasowa ba
sai ya hango su dan haka ya kira Bahajjatu ta ce da shi tana zuwa har sai da ta gama maganar ta da
Bilkisun sannan ta nufi inda yayan nata yake

"Ya aka yi ne yaya Hakim"!?ta tambaye sa sai ya ce mata

"Is about askin da za'a yiwa yaya Zaid ke kin san in har Abba ya gano cewa ba'a mai gyaran fuskar nan ba
ke kin san akwai damuwa"sai ta ce

"Ai yaya ka san umarnin Ammi ne hakan kuma Abba ba zai taɓa yin rigima akan abin ba kawai dai ga
matar sa since she is now his life partner i guess zata yi resuming duties nata kuma zata fara ne da
gyaran fuskar ko ya ka ce"??murmushi yayi kafin ya ce
"Yayi baby sister kin kawo shawara mai kyau"..

Daga nan ya wuce zuwa ɗakin Zaid na da dan kwaso abubuwan da aka manto su chan ita kuma ta nufi
hanyar fita dan kayan ta da zata fara arranging saboda tafiyar su ma washegari.



Itakuma ɗakin ta ta nufa dan bata jin zata iya shiga nasa ɗakin at that moment.tunane tuname take ta yi
in su Umman ta suka tafi suka bar ta daga ita sai shi ya zata kula da shi,ire iren tunanin da ta ɓata
lokutan ta tana yi kenan har ta cinye rabin ranar dan in iyayen nata sun shigo duba ta sai tayi pretending
tana bacci sau biyu suna duba ta dan haka suka rabu da ita su dai burin su ya cika an yi mai kankat.



A halin ɓoye ɓoyen ta kai har dare sai dai tana muradin ganin sa but she can't she feel she can't see him
at that moment dole ta bari har sai sun tafi.a haka ta kwana ta tashi ba tare da ta saka sa a idanun ta
ba,da yake jirgin wuri zasu bi ita kuma tana bacci lokacin sai Ammi ta bar mata note suka yi tafiyar su



Ko da ta farka bata lura ba sai ta yi harkokin ta na yau da kullum but ta saka a ran ta cewa dole ne ta
gan sa ko da kuwa suna nan dan ta gaji tun shekaranjiya rabon da ta saka sa a idanun ta.she dress in an
alluring way shiga mai kyau tayi ta ɗan yi makeup kaɗan ta saka flat Zara pams ta nufi ɗakin sa dama bai
da nisa da nata dan haka da zuwan ta shiga tayi kai tsaye ba tare da tunanin maybe iyayen nasu na ciki
ba.

Zaune yake a kan gadon ana bashi abinci sai ta ƙarasa zuwa inda suke tana kallon mai bada abinci sai ta
ga baturiyar mace ce sai ta mai da idanun ta kan sa ta ga yana kallon mai bashi abincin ai tuni ta ji ran ta
ya ɓaci ta fara tunani marar kyau a kan mai bada abincin gashi ta ga dai matar yake kallo sai ta zuciya ta
karɓe abincin daga hannun matar haɗe da saka fake grin ta ce da ita

"Thanks you may leave please"baturiyar sai ta maida mata da murmushin sannan ta fita.

Zama tayi a kujerar da ke kallon gadon sa ta shiga ƙoƙarin bashi abinci sai dai ya girgiza mata kai dan
dama ɗazu da yake kallon matar nan nuna mata yake son yi akan ya ƙoshi sai dai ita bata gane ba.ita
kuma Bilkisu ganin ya nuna alamar ya ƙoshi bayan ta ga yana ta karɓa a wun waccan baturiyar sai ta ji
ran ta na suya dan haka cikin ɓacin rai ta ajiye abinci ta tashi da nufin fita ta bar mai ɗakin in yaso Ai ko
Baha ko ma ita baturiyar su zo su basa since he doesn't need her help.

Ko da ta juya dan fita a zuciye sai ta ji deem voice na sa na kiran sunan ta

"Bilkisu come back"!!sai yayi shiru itakuma ta ƙame a tsayen bata juyo ba bata fita ba ta rasa me ke
mata daɗi is it her name that he called?or the care he puts in while calling the name?ko dai kawai
unique feelings ne?sai ta tsinci kan ta tana mai annashuwa haka kawai...
*_S,Ibraheem_*

Follow@siyamaibrahim

*⚜BWA*



_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers}_



👄 °°° °°°👄

°°

°



*🎀IYA RUWA FIDDA KAI*🎀

_{the love saga}_



*#Hot love*

*#Romance*

*#allegation*

*#Epic*

*# Arrogance*

*#Pains*

*#Regrets*

*#Obscure and more*



*SIYAMAIBRAHEEM* Wattpad@siyamaibrahim



*19*
A hankali ta juya ta yi ƙasa da idanun ta ta shiga takawa a hankali har ta iso kusa da shi sai ta tsaya ba
tare da ta ce da shi komai ba sai da ya kuma yin magana

"Bilkisu zauna"!!sai ta zaunan tana mai kallon ƙasa shi kuma ba hakan yake so ba so yake ta kalle sa dan
ya mata tamnayar da yake da niyar yi sai dai sam ta ƙi yarda su haɗa idon sai da ya kuma furta wata
maganar

"Ki kalle ni mana"!!sai ta ji saukar maganar a tsakiyar kan ta itama bata san me yasa ta ke shakkar haɗa
ido da shi ba ita da ta daɗe tana muradin ganin farfaɗowar sa dan dai ta haɗa ido da shi sai gashi yanzu
da ya farfaɗon ta kasa kallon sa cikin ido.

Bai san menene dalilin ta na ƙin son kallon sa ba sai ya mata shiru ba tare da ya kuma ce mata komai ba
har sai da dan kanta ta ɗago a hankali ta sauke idanun ta a kan fuskar sa tana son haɗa courage ɗin
magana da shi,dama ya juyar da kan sa gefe sai ya ganta ta gefen ido sai da ya ja lokaci sannan ya juyo ya
zuba mata deem eyes ɗin sa da har yanzu basu gama dawowa normal ba sakamakon jinyar da yayi.



Sarƙewa idanun su yayi a na juna,doguwar lokaci suka ɗauka suna kallon juna wanda kallon nasu cike
yake da ma'anoni kala daban daban wanda su kaɗai suka san ma'anar sa sun daɗe a haka shi bai cire
idanun sa ba ita ma bata cire ba dan kasa cirewar tayi ta rasa dalili.

Ba su suka daina kallon juna ba har sai da aka turo ƙofar ɗakin aka shigo haɗe da faɗin

"Good morning"da fara'a a kan fuskar wanda ya shigo,ita ta riga sa ɗaga kai ta kai duban ta ga wanda
ya shigon sai ta ga Dr ne dan haka ta tashi tana tambayar sa

"Morning anything"??amsa mata yayi da

"Yeah i want to check his system to assess his body function"sai ta girgiza kai cikin gamsuwa ta matsa
mai ya matso kusa da shi yana gaida sa haɗe da tambayar sa ko da akwai wani abin da ke damin sa amsa
ya basa da a'a illah son sanin blockage da ke kunnen sa a nan doctorn ya rasa abin faɗa mai dan bai
shirya wa tambayar tasa ba kuma dama shi dai duba sa ya zo yi ba wai shine main doctorn Zaid ɗin ba.

Sai ta ba Zaid amsa ta hanyar amfani da yaren hausa ta ce da shi

"Zan faɗa maka dan ba shine ainihin likitan ka ba zuwa yayi duba ka in ya tafi zan maka bayani"!sai ya
tsura mata ido hakan kuma creating mat wani abu yake yi wanda bata iya withstanding sai ta kawar da
idanun ta ta mayar ga likitan

"Is okey i will explain to him"jijjiga kai yayi ya cigaba da dube duben sa kafi daga bisani ya mai fatan
ƙara samin lafiya ya fita ya bar ɗakin sai ta koma mazaunin ta ta zauna ta yi ƙoƙarin danne hawayen da
ke cike a ƙwayar idanun ta sakamakon tunowa da tayi da matsalar da Zaid ya ke da shi wanda yayi
necessitating masa zama da ear device ɗin for a long period of time ga final healing and recovering stage
da ke jiran sa a nan gaba wanda alƙawari ne ta ɗaukar wa kanta babu yadda zata sanar da kowa ita kaɗai
zata yi handling komai thank goodness yanzu ita ɗin matar sa ce so ko ma me ta yi ta san is for their own
good.kallon sa tayi ta ga shima ita yake kallo sai ta ji ta kasa daurewa dan haka t bar hawayen suka zubo
wanda ya saka sbi cikin duhu dan bai san ma'anar kukan nata ba sai ya ce da ita

"Menene kike kuka"??muryar sa ƙara saukar mata da tausayin sa yayi sai ta rasa ta ina zata fara kamo
zaren bayanin da take son yi mai a kan rashin lafiyar sa..



Share hawayen ta tayi tana saka murmushin dole ra ce

"Babu"sai ya juyar da idanun sa alamun bai yarda ba sai ta ɗan yi dariya dan dai kar ya mata tambayar
sai ta mai bayanin dalilin ta yin kuka,saidai da yake shi ɗin ɗan boko ne bai bata opportunity na gujewa
wayon da take son yi mai ba,kuma yi mata magana yayi ya ce

"Ban yarda ba ki gaya min dalilin ki na kuka"!a hankali ya mata maganar sai taji tsigar jikin ta ya tashi at
the same time ta ji kamar sanyi sanyi na shigar ta hakan ya bada gudunmawar ƙin ba shi amsar tambayar
sa dan haka ta shiga rera kuka ba ji ba gani shi kuma sai ya ruɗe gashi kan sa na banging kamar me sai ya
shiga bata haƙuri

"Am sorry ban san tambayar tawa zata ɓata miki rai ba ki daina kukan"sai ta ji wani iri mijin ta na bata
haƙuri akan laifin da bai sani ba sai tayi saurin ce mai

"A'a Zaid ni ya kamata in baka haƙuri dan ni na maka laifi,tambaya ta kayi na ƙi baka amsar tambayar na
shiga yin kuka am very sorry am so sorry please forgive me"ta haɗe tafukan hannayen ta wu ɗaya ta
shiga ba sa haƙuri tana zubda ƙwalla.



She is acting strange but why?ya ma kansa tambayar dan sarai ya san halin ta ba mai saurin karaya
bane amma me ya sa take kuka haka dan ya tambaye ta kuma sai ta ƙara yawan kukan nata abin ya
ɗaure masa kai sai dai bai ce komai ba dan baya son tursasa ta akan lallai lallai sai ta mai bayanin dalilin
kukan ta zai bar ta har sai ta ji kan ta daidai kafin ya tambaye ta,ga tambayoyi da yawa da yake son yi
mata sai dai bai san ya zata ɗau tambayoyin ba wannan ɗaya kenan amma ta shiga yin kuka.

Shiru yayi yana kallon ta tana kukan har dai ta tsagaita ta kalle sa tana jimamin lamarin ko in ta mai
bayanin dalilin kukan ta zai kalli bayanin da fuskar fahimta kokuma zai ƙi amincewa Allah ne masani

Ta san yana da tambayoyi da yawa da yake son yi mata dangane da zuwan su nan,wani wuri ne nan
ɗin,a wace ƙasa suke,me ya same sa,ina family ɗin sa and she knows maybe a ƙarshe yayi tambayar
ina....a zafaffe ta ce

"No way"bata san ta furta shi a zahiri ba har ma ya isa kunnen Zaid sai ya kalle ta da kyau yana mamakin
halin da take demonstrating dan bai san ta da wannan halin ba me kuma ya dame ta har take magana ba
tare da ta san ta furta ba??
Dawowa hayyacin ta tayi sai ta ji kunya ta kama ta bayan ta san a zahiri ta yi maganar da ta yi a haka ta
warawre gyalen ta ta ja ta rufe har dai idanun ta suka ɓuya ƙarƙashin mayafin.

Shi dai kallon mamaki yake mata ya kasa furta komai dan abin nata ya fara zarce tunanin sa why is she
covering her face?ya tambayi kan sa.



Zaune suke babu wanda ya kuma furta komai har tsayin lokaci sai ta yanke kawai is better ta sanar da
shi a wuce wurin dan haka ta yi ƙarfin halin riƙe hawayen ta ta gyara murya

"Zaid"bai ce komai basai idanun sa da ya zuba mata sai dai ta daure bata cire nata idanun daga cikin
nasa ba



"Abin da ya faru da mu ba yin mu bane haka zalika ba wai mun fi ƙarfin faɗawa a ƙaddarar ubangiji
bane..sai ta ja fasali kafin ta ɗora da,satin ka kusan huɗu kana unconscious sakamakon abin da ya faru da
mu a ƙauyen koma ban sani ba ko ka tuna da abin da ya farun but bana fatar ka tuna dan ba abu mai
daɗin ji bane ina so ka sani ba da gangar na bari aka kai maka harin da ya illata ka ba kuma ina so ka sani
am always ever ready dan kare ka daga wani harm ba'a fata but i promise never to let any harm come
your way again,,,a last two weeks aka maka cerebral surgery wannan shine dalilin saka maka ear device
da aka yi saboda accident da ka samu ba a iya cerebral region ɗin ka ya tsaya ba yayi affecting maka
pineal gland wanda ya tilastawa kunnuwan ka amfani da device ɗin nan dan taimaka maka wun rage
shigar sharp and lousy noises amma doctor ya sanar da mu cewa akwai tsawon period da amfanin shi zai
yi elapsing sai a cire maka and you will be back to normal but before then please kar ka sakawa kanka
damuwa da yawa in ka ga ba zaka iya ɗaukar damuwar kai kaɗai ba ka yi sharing da ni am at stand by
now and always kuma dama doctor ya ce ba nan kusa zaka farfaɗo ba sai ka kai 3-4months but ikon
Allah sai ka farfaɗo in less than 2weeks ka ga kenan tunda har ka iya farkawa kafin expected time
wannan ear device ɗin ma ana iya cire sa kafin lokacin da suka ƙiyasta ka ga ba sai ka shiga damuwa ba
dan am here and our parents are also here to help us da fatan ka fahimce ni and please don't react i
know you will get well soon and all these minor pains will be done and over with just trust me"!!ba
ƙaramin dauriya tayi ba a yayin da take sanar da shi dan kuka ne ke ta son taso mata ta sani it won't
sound superb a kunnen sa dan ba abu mai daɗin ji bane a ce da kai ga abubuwan da suka same ka kuma
yet baka gama warkewa ba especially ga wanda shine ya saba sanar da wasu sai a ce yau ana sanar da
shi abin babu sauƙi definitely ta san he will be hurt amma gwara da ta sanar da shi tun yanzu dan bata
san me zai faru ba in aka ɓoye mai asalin abin zai iya jin zafi in aka jinkirta sanar da shi but yanzu ta san
ta sauke wani ɓarayi na nauyin da ke damin ta a zuciyar sa but inda gizo ke saƙar shine ta yaya zata sanar
da shi matsayin ta a gare sa as his wife will he wacce or reject her bata sani ba kuma bata san lokacin
sanar da shi ba har da ma dai tana tunanin by now either Bahajjatu,Hakim or Ammi must have inform
him but a yadda yake yi sai take gani kamar bai da masaniya.
Ko da ya gama jin jawabin ta sai ya tsinci kan sa da son sanin cikakken labarin dan ya san ba duka labarin
ta ba sa ba saboda je can sense phobia da ke damin ta dan har a muryar ta hakan ya nuna,he barley
remember what happened that night but ya san ko ma dai menene it must be awful and ugly dan tsoro
ne taf a tattare da ita sai ya yi interrupting tunanin da take yi ta hanyar kiran ta

"Bilkisu ba duka labarin ba kenan,ina son sanin cikakken labarin"!!dumm ta ji gaban ta ya faɗi dama
zagaye ta mai dan ta tsani ta kai kan gaɓar labarin inda Asma'u came to play dan sam bata so ya tuna da
yarinyar saboda ba ƙaramar hatred take da shi ma yarinyar ba and she thinks bayan hatred akwai wani
abin da take ji game da yarinyar wanda bata san ko menene ba.




sauke idanun ta tayi ƙasa dan tsakani da Allah sai dai yayi fushi da ita amma ba zata taɓa gaya mai
gaskiya ba..

"Ka ga Zaid ka daina sakawa kan ka damuwa saboda wannan labarin da na baka iyakar ta kenan babu
wata believe me"tana gama faɗa ta tashi ta yi hanyar waje tana jin sa yana kiran ta amma ta ƙi dawowa
dan bata shirya sanar da shi ainihin labarin ba sai dai peripheral ɗin.

Da kuka ta ƙarasa ɗakin ta kuka mai tattare da cin rai take yi dan pains da agony da ke zuciyar ta bata
iya riƙewa kanta ita kaɗai gashi bata so ya san abin da ke damin ta dan kar ya gane cewa maganar da ta
sanar da shi ba cikakkiya bace.

Tana tsaka da kukan ne ta ji ƙarar wayar ta sai ta yi kamar ta share amma wata zuciyar na bata ta ɗau
kiran sai ta kai duban ta ga wayar cikin saurumi ta ɗaga kiran ta kara wayar a kunnen ta tana mai sakin
wani kukan

"Yaya Zaid zai fasa min zuciya ta da son sanin abin da ni kaina nake kan binnewa tun kafin yanzu,sai
tambayoyi yake min i can't withstand it na gaji please yaya help me am too young for all these
problems"ta fashe da kuka mai tafe da shesheƙa sai yayan nata da ya kira dan yi mata congrats saboda
jiya wayar ta a kashe take kowa ya kira sai a ji wayar a kashe toh yana gwadawa ya ji ya shiga sai ya saka
a speaker dan tare da Bilal,Lukman da Zainab matar Jamil ɗin suke da fari ma video call yaso yi sai dai ya
chanza ra'ayi ya kira kawai,jin abin da ta furta sai yayi saurin cire wayar a hands free ya tashi daga inda
yake zaune yayi isolating kan sa a waje ta gefen pool side cikin natsuwa ya kira sunan ta



"Bilkisu calm down talk to me and stop crying me ya faru"??cikin kukan ta ce da shi

"Yaya tambaya ta yayi in gaya mai abin da ya faru and i narrated everything bayan na gama ya ce bai
yarda ba sai na sanar da shi komai,,,yaya ba zan iya ba akwai ugly parts da ba zan iya sanar da shi su ba
amma ya natse sai na gaya mai Yaya i have to leave him all alone in that room dan ba zan iya cigaba da
kallon sa yana cikin pains ɗin da ya shiga ba but i know by now su Ammi sun ba shi haƙuri na san zai
haƙura in suka mai magana kaima in ka mai magana zai janye son sanin labarin please yaya help me na
kasa composing kai na"!!tausayin ta ne ya kama sa dan duk a halin ruɗani take maganganun gashi bata
da labarin dawowar iyayen nasu dan daga dukkan alamu bata san cewa sun kamo hanyar dawowa
ba,daga ita sai Zaid a ƙasar germany babu wani ɗan uwa ko aboki dole su yi tolerating juna haɗe da
nunawa junan su kulawa har Allah ya sa Zaid ya sami lafiya su dawo gida.

"Baby kina ji na"??ta ansa da

"Eh ina jin ka yaya"!!sai ya ƙara sassauto da mutyar sa ta yadda zata ji komai cikin sauƙi



"Baby kin ga su Ammi sun kamo hanyar dawowa gida already yanzu a ƙasar nan babu kowa naku daga
ke sai shi kuma kin san shi ɗin ba lafiya ce da shi dole ya rinƙa samin kula daga gare ki dan ke kaɗai ya
sani bai san kowa ba duk wasu lalurorin sa da ɗawainiyar sa sun komo hannun ki daga jiya har izuwa
ƙarshen rayuwar ku kin chanza daga abokiyar aiki,makwafciyar sa kin zamo matar sa abokiyar shawarar
sa abokiyar rayuwar sa,,nauyi ne ya ƙaru a kan ki ba kaɗan ba dan haka ina so kiyi concentrating wun
bashi kula dan sai kin bashi isashiyar kulawa ne zai sami natsuwa ya warke yadda ya kamata ba tare da
an sami mishkila ba,kar ki damu da individual differences da ke tsakanin ku duk waɗannan zaku iya
mending nasu in har kuka cigaba da zama tare dan haka ina so ki sani in har kika saba mai da rayuwar
ƙarya tun yanzu a kan sa zai ginu in ma na gaskiya ce duk a haka zai ginu so i guess tun yanzu ki sabar
masa da faɗin gaskiyar lamari ko da kuwa ba zai mai daɗi ba gwara ya sani daga gare ki than ya ji daga
wun wani ko outsider da fatan kin fahimci maganganu na baby sis"??ƙamewa tayi a zaunen dama sun
tafi ne ba su sanar da ita ba??yanzu ita ya zata yi da Zaid?yaushe ta gama kula da kanta har da zata fara
kula da Zaid all alone?me yasa suka mata haka ne yanzu ko Baha bata tsaya ba suka tafi suka bar ta ita
kaɗai tayi nursig kanta sannan tayi nursig Zaid??ta ina zata fara?..



Duk a cikin zuciyar ta taje waɗannan tunane tunanen mantawa tayi da yayan ta na kan layi har sai da ya
kuma yin magana

"kina ji na kuwa Bilkisu"firgigit ta dawo daga tunanin ta ce

"Eh na ji yaya,,amma yaya su Umma basu kyauta min ba ta yaya zan fara kula da kaina in kula da Zaid
nima fah convalescence patient ce ba gama warkewa nayi ba ina buƙatar kula ta musamman daga wun
wani ta ina zan fara i can't...i just can't do it all alone brother please do something"...sai ya rasa abin faɗa
mata gashi sai kuka take yi

"Baby stop panicking stop crying komai zai zo maki a daidai da yardar Allah all ypu need to do shine ki
natsu kiyi studying Zaid da kyau ki san abin da ran sa ke so da wanda baya so sai ki fara exhibiting but
crying won't solve the problem ki natsu zaki iya handling komai baby sis you have to learn how to start
leaving alone dan zaki fara family ɗin ki ne so bai kamata ki fara da tsoro ba henceforth be back
completely dan Dr Bilkisu Muhammad Sulaiman da na sani is a conquerer despite the fact that her tittle
is Baby doctor but she is actually not a baby when it comes to fighting for her goal she ain't a loser she
always win humm dan haka ki daina faɗin wai ba zaki iya ba sure you can kin ji"??

Jan hanci tayi tana jin ta sami ƙwarin gwiwa..

"Nagode Yaya Allah ya saka da alkhairi you are special to me nagode yaya bari in duba shi dan ban san su
Umma sun tafi ba"

"Shikenan baby sis Allah ya shige mana gaba"

"Amin yaya nagode sai anjima"ta kashe wayar haɗe da sauke ajiyar zuciya ta kwanta da baya tana kallon
sama.tunanin maganar su da yayan ta take yi sai t ga gaskiya ƙarara a zancen nasa tabbas dole a kan
abin da ta ɗora sa zai ginu dan dama namiji da abin da ka sabar mai zai cigaba da gudanar da rayuwar sa.

A baya tayi tunanin jan jikin ta daga nasa ta so ne ta rinƙa guje mai ko da wani abin ne ya taso sai ta yi
sama sama ta nisance sa sai dai yanzu da ta ji babu wanda ke tare da su da zai taimaka mai akan
harkokin sa wanda ya haɗa da su lalurorin sa kama daga cin abincin sa kula da jikin sa shan maganin sa
hira tare da shi ta yadda zai ƙara mai kuzarin farfaɗowa gabaɗaya sai ta ga ya kamata ta rinƙa ɗauke
masa waɗannan abubuwan he have no one to do it sai ta ji tausayin sa na tsirga ta dan haka wuf tayi ta
tashi tana duba jakar kayan shafawar ta ta fiddo ƙaramar abin powder ta buɗe mirror ta ɗan yi touching
kwaliyar fuskar ta kaɗan dan bata so ya gane cewa tayi kuka sai ta ɗan shafa lip moisturizer ta kuma bin
jikin ta da turaren jiki mai sanyin ƙamshi sannan ta ta chanza kayan jikin ta zuwa riga da wandon Dior
pink colour ta ɗora after dress mai igiyar ɗaurawa black colour mai adon duwatsu ƙanana ta nemi
ƙaramar gyale baƙa ta yafa a kan ta takalmin valentino na mata ta saka mai ɗan tudu kaɗan sai ta kuma
bin jikin ta da perfs kala biyu kacal sannan ta ɗau wayar ta zata fita kenan ta hangi takardar da Ammi ta
ajiye mata sai ta koma ta zauna ta ɗau takardar ta warware tana duba abin da ke ciki cikin natsuwa.

Har ƙarshe ta karanta wasu kalmomin da Ammin tayi amfani da su sun mata nauyi har take jin kunya ita
kaɗai..

Most of the things contained in the later shawarwari ne akan zaman ta da Zaid haɗe da tunatar da ita
matsayin ta a wun Zaid ɗin sai kuma

Please Login or Register in order to submit comment