You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

riga mayafin da matar ta yana akanta da ya ƙara mata kyau kuma ya fito da siffarta na
uwa sannan baƙin mayafin ya ƙara fitar da colorn fatar ta ruwan ƙwai.




Cikin sassanyar muryarta ta ƙara yin wani sallama a karo na uku, sannan liyana ta amsa tare da faɗin
"Sannu da zuwa Maa, ina wuni." Tare da yi mata alamar zama akan ɗaya daga cikin kujerun masu kyaun
gaske.



Murmushi mai kyau matar ta sakar mata tare da amsa mata da " Lafiya lau ƴammata, ya kike?."

" Lafiya lau Maa." " Neneh na ciki?." "A'a ba ta nan ta fita tun safe." Mai aiki ce ta zo tare da faɗin"Aunty
Liyana mai za'a kawowa Mamin?." " Bar shi zan zo na haɗa ma ta."

Daga haka ta shige kitchen ɗin tare da haɗa mata abubuwan motsa baki.
Table ta janyo tare da ajiye tray ɗin a kai. Godiya matar da mai aiki ta kira da Maami ta mata sannan ta
ce " Ina Nenehn ta je?." " Ai tun safe ba ta ji daɗi ba shi ne mijinta ya kai ta hospital." Ɗagowa matar ta
yi, Liyana tai sauri ta ƙara faɗin " Jiddah kai." Murmushi matar ta sake yi sannan ta ce " Subhanallah,
Allah ya sa kaffara ne, in ta dawo ki ce ma ta na zo amma zan dawo in ta dawo gida, ki ce mata Mamin
Sultana ce ta zo, ya sunanki ƴammata?." Cikin sanyin muryarta ta ce " Fatima." Ma sha Allah fatiti." Sai
da ta sha ruwan sannan ta ce mata ta tafi ta kula da kanta.

Toh kawai Liyana ta ce ta na jin matar ta kwanta mata a rai, ga nutsuwar matar mai ratsa jini, dan ita
kam matar ta yi mata kwarjini sosai.........✍️




Akwai ƙura faa a gaba 😂😂
> THANK YOU FOR READING 💜




To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.

Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.

See you in the next chapter of our journey.



With love,

Pending Amarya 🦋




> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋



> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.




Pending Amarya as usual 🦋 🫠




I really love you readers 💎
> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday

> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> Pending Amarya's book corner
Extraordinary Everyday 🦋 posting channel 👇




https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



The Noble Writters ✊

Dedication is our strong



THE REGRET 🙆



when love meets temptation who survives?
Na saba da ke 😉
na aminta da ke soyayya da ke zaƙi
😪 kamar rake 🤫 Baby buɗe min ƙofa na zuciyarki
nuna min hanya na zo gabanki😩 na lura kece ruhinaaa burina a kawo ki ɗakinaaaa😅😉




BOYS KIDDO DUNIYA NE 😂
THIS PAGE IS DEDICATED TO HIM 😂




The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko
ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!




Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂




Mallakar Pending Amarya ce_




NDA DUBDO🦚

My Maiduguri ppl
CHAPTER NINE : HYDAR & LIYANA 🦚💎

LONG CHAPTER ✍️




_PENDING AMARYA _




Page 18




Toh kawai Liyana ta ce ta na jin matar ta kwanta mata a rai, ga nutsuwar matar mai ratsa jini, dan ita
kam matar ta yi mata kwarjini sosai....
Ko da yamma da Nenehn ta dawo Liyana ba ta yi mata maganar matar da ta shigo ba sam.

Sai ma biyewa Nenehn da ta yi su ka cigaba da hira ta na ba ta labarin zamaninsu yadda maza su ka yi
rubibinta, sannan Allah ya sa ta zama rabon Jiddah a yadda ta ce dan ita ba ta yarda da maganar Neneh.




Sai wurin goma sannan su ka shiga ciki sai da su ka yi waya da Sultan sannan ta kwanta.



Ɓangaren Mamin Sultana ku wa tun da ta koma ta sa Sultan ya je ya siya mata fresh fruits domin haɗa
fruit salad, sai kuma snacks saboda Hydar na da son waɗannan ƙananan abunawan.



Abinci su ka haɗa na alfarma, tun da shima Yallabai be daɗe da dawowa daga can ba. Shirye shirye su ke
a gidan kamar biki, kuma ba shirye-shiryen wasa ba.




Gida ne da ya amsa sunan sa gida, domin gidan su Liyana ba komai bane ba.

Ga faɗi, ga kyau, uwa uba komai na gidan looks zamanious().😂Komai na gidan is rich and elegant,
babu wani tarkace na ƙyale -ƙyale, komai is neat and luxury.

Ko da Sultan ya dawo waya maƙale a kunnensa. " Maƙale mata ƙarfe nawa jirginsu yayanka zai sauka?."
Sai da ya katse wayar sannan ya ce " sorry Mami arround 6 O clock in the morning In Sha Allah." Allah ya
kaimu toh, so na ke na shiga wurin Neneh kuma ga shi dare ya yi, wai naje ɗazu wai ba lafiya." "Ayya
Allah ya ba ta lafiya."

Daga haka ya shige ɓangaren sa.
Mami wasu daga cikin masu aiki ta bawa ordern su gyara ɗakin Baban gida Hydar.

Tun cikin daren su ka ci ƙarfin aikin na su tun da saukan sassafiyya ne zai yi.

Ko da Alhaji Kyari ma ya dawo hira su ka dasa tsakaninsu banda Sultan da Assultanah da ke ɗaki ta na
karatunta na final exam.




Su Ammi na ta fama da Abbhi kullum cikin kiran Liyana ya ke ya ji zance amma kullum maganar ɗaya ne
ba ta gama plan ɗinta ba.



Itama Ammie ba ta zaman gidan sai dai ta bar Rufaidhat da Abbhin saboda ta buɗe wajen siyar da hijabai
da kuma kayan kwalliyan mata ba ki ɗaya, sannan ta kan je gidansu wani sa'in dan in ta biye wa Nabil
tsaf sai ta daina hulda da mutane.




Liyana da ke zaune cikin shigarta na kullum wato palazzo trouser da long sleeve shirt white color, sai
hulanta da ke kanta da gucci slippers ɗinta purple color.



Salimah ce ta kawo mata hollandia strawberry ɗin ta sai kuma milky donut, tana zaune ta na daddana
wayar hannunta tare da sipping ɗin yourghurt ɗin da ke cikin transparent glass cup ɗin ta yi crossing
ƙafafuwanta ɗaya kan ɗaya.



Neneh ce ta sauko cikin shigarta na lifaya white and golden color, "isasshiya, dubi yadda ki ka zauna
jibge kamar kayan wanki ba aikin fari ba re na baƙi, in kin yi aure naga mai miki ai, kya bari bakwai ta yi
kafin ki fara ciye-ciye, mutum ba auki sai ci kamar gara, gafara dallah in zauna." Nenehn ta faɗa tare da
zama kusa da Liyanar.



Ba ta tanka mata ba ta cigaba da abinda ta ke yi.
"Ni ina da ke ai ba zan ma bari Abbihna ya ɗaukar min house maid ba, ki ka sa uniform irin na Salima ai
ba ƙaramin kyau za ki yi ba, tun da kuma gidan kakannin ki ne sai ki zo ki bani time ɗin cin abinci."



" Ni ki daina ambatar min wannan uban na ki a gida kar Mala'ikun rahama su daina shigo min."



"Kya ji da shi kuma."




Ɓangaren gidan Alhaji Kyari tun ƙarfe shida su ka nufi filin jirgin saboda tarban Hydar ɗin, ko wannensu
ya ci ado cikin shiga na alfarma, sannan kuma na mutumci sakkowa ya ke cikin aura ɗinsa da ya gama bin
jikinsa, ya doso wurin da ya hangin sanyin idaniyarsa ma'ana mahaifiyyarsa, a hankali ya ja LV trolly ɗinsa
duk gajiya a tattare da shi, Assultanah ce ta fara ganinsa ta tafi da ɗan gudunta ta rungumesa, shi ma
rungumeta ya yi sannan ya sakar murmushin sa mai kyau.



Sannan su ka ƙarasa wurin parents ɗinsa ya gaida su ci ke da girmamawa, Mami ce ta kallesa tare da
faɗin "Am proud of you Baamii, Allah ya sa Albarka." "Amin." ya ce sannan su ka shige motar da su ka zo
da ita har guda biyu.



Ko da su ka ƙaraso gidan sai da ya yi wanka ya rama sallolinsa sannan ya fito cin abinci shima snacks
kawai ya ci sai fresh milk, sannan ya shige ɗakinsa domin hutawa.




******



Liya na gama cin snacks ɗin komawa ta yi ta kwanta bacci dan sai ƙarfe 12 ta ke da lectures shi ma ba za
ta je ba wani birthday party za ta da Lilian.
12 dai-dai ta tashi tare da nufar toilet ta yi wanka tare da yin alwala dan har ƙarfe ɗaya ya yi, sannan ta
yi sallar ta haɗe da shiryawa cikin simple dress mara nauyi, because sai ƙarfe 4 za ta kama hanyar zuwa
gidan Lily because a Piccolo za ayi partyn.



Wani kalar yunwa ke nuƙurƙusan cikinta dan haka kitchen ta nufa tare da buɗe fridge ta ga Salimah ta
ajiye mata fruit salad, murmushi kawai ta yi tare da ɗaukan bowl ɗin ta fara shan fruit salad ɗin a hankali
kwance.



Neneh ce ta ƙara sakkowa amma wannan karan ta canza lifaya zuwa maroon, harara Liyana ta dallah
mata sannan ta ce " ke ba kya ta shi sakkowa sai mutum na cin abinci? Ni fa bana son kwaɗayi."



"Ni ba shi ya dameni ba Fatima, maza zira hijabyn ki mu je gidan Alhaji Kyari, kin ga ɗan nasa da na ke
gayamiki ya dawo."

"Babu in da za ni." Ta na faɗin haka ta cigaba da shan fruit salad ɗinta.




"Sanyi ya haifi zafi wannan haka ya ke, mai tarbiyya ya haifi mara tarbiyya." Daga haka ta sa kai ta fice a
falon.

" Za ki dawo ki faɗa min waye mara tarbiyyar ai, tsohuwa sai bala'in tsiya, mtsww."



Sannan ta shige ɗakinta tare da shiga app ɗin Instagram ta na duba wasu comments da aka yiwa
pictures ɗinta.



Wasu zagi ne wasu kuma zallar goyan baya ne daga followers ɗinta.

Gidan da aka rubuta Kyari's mansion Neneh ta kutsa kai ta shiga securities na ta gaida ta dan duk cikinsu
ɗauka su ke Nenehn mahaifiyyar Alhaji Kyari ce.



Gidan ya rabu kashi da dama, ko ina kuma cike ya ke da kayan alatu.
Ɗaya daga cikin ɓangaren da ke kallonta ta shige, Sultan ta fara cin karo da shi a living room ɗin, sai da ta
yi a' uziyya sannan ta wuce shi ya na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba daddagewa ya yi ya ce "toh yi
haƙuri ƴar tsohuwa zan auri jikar ta ki." A ƙufule ta juyo tare da faɗin " ai ba neman kai na ke da ita ba."



Dariya kawai ya yi sannan ya juya ita ma ta yi hanyar sashen Hajiya Khairat ɗin.



Shiga ta yi tare da zama, Assultanah ta shigo ta yi ta yi wa Nenehn tsiya.



Ko da Mami ta fito su kai ta hira, sannan ta kira layin Aliyu Hydar ta sanar masa Neneh na jiransa.



Bai ɗauki lokaci ba ya fito sanye da T-shirt da jeens trouser black color sai slippers da ya zira.



Shigowa ya yi tare da sallama tare da bayyanar da murmushinsa akan fuskarsa.



Bayan sun gaisa da Nenehn su ka ɗan taɓa hira sannan ya ce " zai ɗan fita ya ga gari ya dawo, sannan
Sultana za ta kawo mata tsarabar ta." Sannan ya sa kai ya fice daga gidan.




Mami ce ta kalli Neneh tare da ɗan gyara zamanta ta ce "wallahi Neneh wa ta fulawa na gani a gidan ki
in da hali na kamawa Babana ita." Ta ƙare zancen da murmushi.



"Ki ganar da ni mana uwar Alkhairi, fulawa ai da yawa a gidana, yanzu in sa uzaifa mai gadi ya tsinko miki
duk wadda ta miki."



Murmusawa ta yi sannan ta ce"Neneh kenan, wannan ƴar budurwar ce wallahi da na ganta a gidan ki
kuma ta burgeni shine na ce in ba'a mata miji ba ina son Hydar ya aureta."
"Kamar ki na raina khairatu , wallahi ri ga ni faɗa kawai ki ka yi nima abin da ke raina kenan ai ko sun yi
mata mijin sai sun since, in dai Hydaru ne, amma kin gayawa kyarin ko?."



" Eh shi ya ce na tunkare ki da zancan."

"Toh Ma shaa Allah ina zuwa zan sanar da Rafiƙ komai sati biyu masu zuwa ma ai sai a ɗaura aure tun da
tuwo na mai na za'a yi."



"Exactly, Allah ya tabbatar da Alkhairi." Daga haka su ka cigaba da hira har Nenehn ta koma gidanta.




Ko da Neneh ta dawo daga gidan da wasu tsadaddun lifaya ta dawo, ta kalli Liyana ta ce "kin ga harkar
arziƙi, wannan kwarɓaɓɓen saurayin na ki mai ya taɓa kawo min, kullum cikin wayar tsiya."



"Ke abin duniya ya dama ai."



Jiddah ne ke saukowa a hankali cikin jallabiya black color mai tsantsi ya kafa kansa da hula fara mai kyau,
hannunsa riƙe da walking stick ɗinsa.

"Jiddah! , ta faɗa tare da ƙarasowa wurinsa ta rugumesa, ta na kuma gaida sa duk a lokaci ɗaya.

Ƙarasowa su ka yi su ka zauna ku sa da Neneh, cikin muryarta mai cike da manyantaka ta ce "Lale
marhaban ya Rafiƙ." Murmushi ya yi tare da gyaɗa mata kai alamun ya na jinta......
Sorry da bana update kwana biyu yau da zafi na na taho 🥹💎




THANK YOU FOR READING 💜




To everyone who took the time to read The Regret, you’ve just held a piece of my heart in your hands.

Kuna daga cikin dalilin da yasa zan ci gaba da rubutu.

See you in the next chapter of our journey.



With love,

Pending Amarya 🦋
> Pending Amarya's book corner Extraordinary everyday 🦋



> Share for more pages in sharing ɗinku ya yi yawa zan ƙara typing da yawa.




Pending Amarya as usual 🦋 🫠




I really love you readers 💎



> Pending Amarya's book corner Extraordinary Everyday

> Mondays to Fridays from 8am to 12am follow for more 🎊🫂📚> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER
EXTRAORDINARY EVERYDAY POSTING LINK 👇




https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪



:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::



The Noble Writters ✊

Dedication is our strong



THE REGRET 🙆



when love meets temptation who survives?




THIS PAGE IS DEDICATED TO MY FRIENDS🫵



Rufaidhatah 💔 Afnan (My Khaldun). Rashanda, Princess minal, Fatimatuzzahra (K. M. A).

Assultanah 🦧, Besty ss, My Hafsy Dear.



Umty luv 🥀,, Sis Mansura. And so on.
This page is dedicated to you guys. I love you all 🤫🌚




The Regret Mallakar pending amarya ce ban yarda a sauya min labari ba ta ko wani siga, idan hakan ko
ta faru kotu ne zai rabani da ke!!!!




Pending Amarya ni ce satellite ina haska su kamar ring light 😂😂




Mallakar Pending Amarya ce_




NDA DUBDO🦚

My Maiduguri ppl
🦚💎

LONG CHAPTER ✍️




_PENDING AMARYA _




Page 19




Ƙarasowa su ka yi su ka zauna ku sa da Neneh, cikin muryarta mai cike da manyantaka ta ce "Lale
marhaban ya Rafiƙ." Murmushi ya yi tare da gyaɗa mata kai alamun ya na jinta......




Kallon Liyana ta yi sannan ta kalli Jiddah da ke zaune, ya gane abin da ta ke nufi dan haka cikin sanyin
muryarsa ya ce "Ya Zahra." Ɗago da kanta ta yi because haka Jiddah ke kiranta, "Shiga ciki manya za su yi
magana." Nodding kan ta ta yi tare da ɗaukan wayarta ta nufi ɗakinta ba tare da ta tankawa Nenehn ba.
Matsowa ta yi sosai tare da kamo hannunsa ta ce "Rafiƙ, khairatu ce ta same ni da wata maganar da ta
faranta min rai sosai, ɗan wajenta Hydar dai namu da kuma Liyana ta ke son a haɗa aure, ai kaga
ɗaurewar zuminci kenan." " Liyanar ta ce miki ba ta da manemi ne?." "Ta doshi wata a gidan nan wallahi
ban taɓa ji ko da wasa ance ana sallama da Liyana ba." "Zan ji ta bakinta toh dan ba za'a mata dole ba." "
Toh Rafiƙ Allah dai ya tabbatar da Alkhairi shi ne kawai."



Bayan shigar Liyana ɗaki kuwa waya su ka kuma yi da Sultan.




Bacci ta ƙara komawa, ta yi baccin sosai, sannan ta tashi arround 4 , ta yi wanka tare da brush.sai da ta
tsane jikinta sosai sannan ta ta fara shiri because partyn ma anko su ka yi ita da Lilian.



Duk da ba wani tsada ne da kayan ba ta zaro su daga cloth set ɗinta da ke sheƙe da kaya saboda
shopping ɗin da ta ke yi, carton colored palazzo trousers ne sai normal hand long sleeve shirt coffee
color sannan ta ɗaura ɗankwalinta matar minister, gucci high heels masu kyau black color sai jaka shima
gucci black, latest phone ɗinta wadda ake ya yi iphone 14normal ta ɗauka tare da cilla fresh mint
chewing gum a baki sannan ta shafa lipstick a heart shaped full lip ɗinta, sai ya ƙara wa shigarta kyau da
kuma tsari, ba za ka so ka mata kallo ɗaya ka ɗauke kai ba.

Wani ɗan siririn eye glass da ke kama da medical glasses ta sanya amma kuma is for passion masu kyaun
gaske da ɗaukan ido, sai da ta ɗauki wayarta ta sakarwa Instagram reels sannan ta fito parlour da Neneh
ke ta kallon AIT NIGERIA.




kallon Nenehn ta yi tare da ɗauke kai, ta nufi Jiddah da ya ke a zaune ya na kallonsu.

" Jiddah! Dan Allah car key za ka bani." ta faɗa tare da siddar da kanta ƙasa,"ki amsa a wurin driver,
sannan ina za ki je ?." Ba za ta iya faɗan birthday za ta je ba Jiddah is very judgemental, zai iya hana ta
zuwa idan ta ce masa birthday za ta je.



Ajiyar zuciya ta sauke sannan cikin muryarta mai zaƙi ta ce "Jiddah akwai wani ɗan ƙaramin biki da aka
haɗa mana a school. Ƴan ajinmu ne suka shirya mana tun jiya bayan mun gama last paper na level300,
shine ake ɗan ƙaramin biki." "A ina za'a yi?." Ta ƙara tsintar muryar Jiddah a kunnenta.
" A can wani ɗan gidan abinci a nasarawa G. R. A." "Allah ya tsare, in kin dawo za mu yi magana okay?."
"Okay grandpa." Ta faɗa tare da bashi side hug. Ba ta kai ga fita ba Neneh ta ce " yadda ki ke rawan jikin
nan da ƙyar in gaskiya kika faɗa." "Bara inna dawo zan yi maganin ki young lady." Daga haka ta fice tare
da shigewa cikin Lexus LX 600 mai numfashi da tun ɗazu ta amshi car key ɗin wurin drivern Jiddah
Adnan.




Sai da ta ɗaura seatbelt sannan ta yi connecting waƙa cikin talent ɗinta na tuƙi ta cilla hancin motar kan
titin da ke shinfiɗe a street ɗin.



Tana jin waƙar ta na gyaɗa kai a daidai kwanar da za ta sha ta ɗauki hanyar kabuga ta bige wani ɗan
Lexus RX 350 da sam ba ta lura da shi ba.



Kuma parking ɗinsa aka yi ba tare da an lura cewa kan hanya bane ba.

Wani ɗan ƙaramin tsaki ta ja tare da parker motar ta fito ta na kallon motar Jiddah da babu abin da ya
sameta, sai wannan Lexus RX 350 ɗin da fitilarsa na baya ya ɗan fashe.




She didn't bother tun da babu abin da ya sami motarta har ta buɗe driver sit ɗinta ta zauna tare da fara
driving ɗinta.

Aliyu da ke cikin motar ya na jiran isasshen da ya buge mai mota ya zo ya basa haƙuri har ya ga an tayar
da motar.



Bayan an bashi fruit ɗinsa bayan motar ya bi ba wani delay.

Gudu ta ke shararawa, shima binta ya ke bai cimmata ba har sai da suka ƙaraso Piccolo, sannan ya yi
mata overtaking, wan da hakan ya sa taja birki ta tsaya.



A fusace ta fito tare da rufe ƙofar motar da ƙarfi, shima fitowa ya yi ya kalleta da kyau he was shocked
to see her again, ya na ganinta ya ganeta just ɗan girman da ta ƙara da kuma minor things haka, cikin
tafiyarsa da ke cike da izza da kamala ya tako ya tsaya a gabanta tare da nuna ta da ɗan yatsa tare da
faɗin ''haba no wonder, daman nasan wannan aikin sai mata irinku marasa tarbiyya da kamun kai,
waƴanda iyaye ba su isa da su ba, You hit my car and you can't even say sorry, that's pure arrogance,
kuma kika kaɗa motarki like nothing happened, is that a manner?.''




Tass ta wanke sa da mari, ya ɗago fuskarsa ya kalle ta sosai, wani marin ta ƙara wanka masa sannan ta ce
''baka sanni ba ba ka san ko ni wace ba za ka zo kai ta gayamin maganar da basu dace ba idan kasan
wata ba ka san wata ba, kuma na mareka sai na ga uban wanda ya tsaya maka, complementry card ɗin
Abbhi ta wulla masa tare da address ɗin gidansu, ta ƙara faɗin '' ga shi idan za ka kai ƙarar nawa wurin
waƴanda su ka bani tarbiyyar. Christmas goat.'' tare da jan tsaki ta shige motarta tare da yin reverse ta
bar wurin gaba ɗaya ta koma gidan Neneh.

Hydar da ya yi mutuwar tsaye,ya ji tsanar yarinyar ta ɗirar mai a zuciya a lokaci ɗaya.

Ya shige motarsa tare da kama hanyar komawa gida, dan yanzu haka he couldn't control his self. Dukan
mace ba halinsa bane ba da sai ya yi mata lilis kafin ta bar nan.

magana shi kaɗai '' amma yarinyar ta ci ni wasa ya tsani yarinya mara kunya a rayuwasa.'' so ya ke ya
tuno a ina ta faɗar mai da waya amma ya kasa, je must teach her a lesson, Allah ya ƙara haɗani da ke.''

Allah ne kaɗai ya kai Liyana gida, dan kawai tuƙi ta ke bata ko ganin gabanta, ranta ya ɓace sosai,ka
zageta da komai amma banda rashin tarbiyya tana cikin haka ta ji wayarta na ringing, ''Who's that
idiot?." tare da ɗaga wayar a ƙufule.

Lily cikin muryarta ta ce '' Liya it's time already kuma ba ki shigo ba har yanzu.'' ''I'm not coming.'' tana
faɗan hakan ta kashe wayar.

Wani kalar horn ta ja wanda ya sa mai gadi ta shi a guje ya buɗe gate ɗin a miliyan ta shigo gidan tare da
parker motar ta shigo cikin gidan Neneh na zaune ita da Salimah suna taɓa hira.



''ni dai wallahi a wurinmu da safe ake wannan, ya mutum zai shigo ba sallama kamar jiƙar bob Marley,
ayi mutum ba tsari Allah na tuba.''



''Neneh da na shigo gidannan ban miki magana ba ki bar ni da abin da na ke ji.''
''Ahaf ai sai haƙuri nima haka na yi ta fama da samari a zamanina wallahi, ai na ki mai sauƙi ne.''



Tsaki Liya ta ja tare da kulle ƙofar ɗakin da ƙarfin tsiya.

Cire kayanta ta yi tare da watsa ruwa ta shirya cikin kayan bacci mai tsantsi dan yau ana isha za ta
kwanta.

Salima ce ta shigo tare da kawo mata strawberry hollandia ɗinta ta ajiye mata a bedsides.

''Aunty Liyana Jiddah na kiranki wai a ɗakinsa.'' ''I heard you.''

Tana faɗan haka ta ɗauki wayarta tare da ficewa daga ɗakin.



Kallonta Neneh ta yi ta ce '' masu magana da yawun Queen Elizabeth, an fito kenan.''

''Wallahi Neneh darajar Abbhina da Jiddah ki ke ci a gidan nan, na bar Rufaidhat a gida na zo na huta
kuma ki tiso ni gaba, who does that huh.''

''Salimah maza ki je, can ƙarshen layi, gidan gonan Alhaji Kyari ki tsinko mata tsamagiyya ta mun duka
hankalinta ya kwanta.''



Kallon Nenehn ta yi sannan ta buga ƙafarta ta hau saman stairs.



''Ni na rasa mai Khairatu ta gani jikin wannan ta kamawa Hydar, dan wannan ta fi ƙanjamau illa.''



''Amma ai Neneh ke kika fara yin maganar kafin Mamin.'' Salimah ta faɗa ta na kallon Nenehn.

''yi aikin ki banason shirmen banza.''




Ƙarasawa ta yi ɗakin Jiddah da ke magana akan companyn sa da ake rulling na man gyaɗa a can Lagos.
Zama ta yi kusa da shi ta ce '' Jiddah da ma ina son maka magana da daɗewa.''

As usual he just smiled, sannan ya bata attention, '' Jiddah Please ka taimaka ka yafewa Abbhina abin da
ya maka, we are all humans, we make mistakes, we are not perfect, at times wallahi sharrin shaiɗan ne
ba komai ba, forgive and forget, you are a muslim, let bygones be bygones, please grandpa.'' ta ƙarasa
maganar da hawaye because ba ta ɗaukan abin mahaifinta da wasa.




'' Ya Zahra.'' a sanyaye ta ce ''Na'am.''



''ki ce mai ya zo ina neman sa gobe In shaa Allah, kuma kar ki ba ri Neneh taji am I clear.''

''Yeah grandpa, tomorrow is my birthday anything for me, kuma dama ya ce gobe zai kawo min birthday
gift soo no need na gaya masa ai.''



''Idan kika aminta da ni i promised you kujerar Hajji this year In sha Allah, Allah ya miki albarka za ki ji
saƙona ta wajen mahaifin na ki,

Please Login or Register in order to submit comment