You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi, ta na mai ɗaure fuska ta nufi kan cushion ɗin ɗakin Mamin da jakarta ke ajiye a wajen.



Ɗaukar wayar ta yi tare da kallon sunan Lily da ke yawo akan fuskar wayar , wani kalar tsaki ta ja tare da
ɗaukan wayar haɗe da faɗin ''Hello.''

''Yes dear, ba za ki shigo school ba, yau lectures ɗin Sadauki ne wallahi, ya kamata ki shigo, ten marks zai
ba da.''



Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce ''Okay on my way.'' daga haka ta katse wayar.

Mami ce ta shigo cikin ɗakin hannunta riƙe da tray ɗin dake shaƙe da pepe soup, sai kuma wani ɗan
bread daga gefen plate ɗin dake cikin tray ɗin.



''Daughter you're awake, zauna ki ci abinci, kin ji.''

Sai da ta yi ƙasa da kanta, dan har ga Allah ta ji kunyar ganin Mamin da abinci, kuma wai ita aka kawowa,
ita ta rasa ta ya ma ɗan iskan baccin da ta rasa dalilin yin sa ya kwasheta, dan ba ta san lokacin da baccin
ya sureta ba.
''Mami na ƙoshi, yanzu wai lectures za'a yi a school, idan na dawo daga school ɗin zan biyo kafin na wuce
gida.''

''Noo ta ya za ki tafi da yunwa, zauna ki ci kayanki kin ji.''

Murmushi kawai ta yi tare da faɗin ''Tom Mami na gode.''



Daga haka ta zauna ta fara cin pepe soup ɗin.

Ba ta wani ci sosai ba ta wuce ta yiwa Mami sallama tare da wucewa school ɗin.



><><><><><><><>




Zaune yake akan office chair ɗinsa, jikinsa sanye da wasu suits masu tsadar gaske sky blue color,
gemunsa na gyare tsaff da kyau, tsintsiyar hannunsa na ɗaure da agogonsa na Rolex explorer ll wanda
ya saba sanyawa fararen hannun na sa.



Wa ta Chinese Lady ce ta shigo cikin office ɗin, kayan dake jikinta shi zai ba ka tabbacin cewa ita ɗin
clearner ce.



''Good day Sir.''

Chinese ɗin ta faɗa da muryarta da yake na zallar Chinese.

Gyad'a kansa kawai ya yi tare da fara duba wasu documents ɗin da ta kawo ma sa tun safiyar ranar. Cikin
muryarsa da ke da ɗan ɓacin rai ya ce ''Kira min Manager's.''

Da ga haka ya cigaba da scrolling ɗin cikin apple computer ɗin dake gabansa, agogon hannunta ta danna
tare da yi musu magana ta agogon, sannan ta fita daga cikin office ɗin Hydar ɗin.




Turo ƙofar office ɗin aka yi, dukkaninsu suka shigo atare jikinsu sanye da baƙaƙen suits dake ɗauke da
logo ɗin companyn.
Zama suka yi a wajen da suka saba tattaunawa a office ɗin nasa, sannan kuma a hankali ya fara magana.




''Mai ya faru da 500 billion ɗin da suka fita last upper month?."

Shiru suka yi na ya'n daƙiƙu sannan Manager ya fara cewa ''An siyi business jets ne saboda yiwa
mutanen wasu ƙasashe delivery.''

''Eh haka ne Sir.'' Assistant manager ya amsa da hakan, kallon wasu daƙiƙu ya yi musu tare da faɗin ''Ina
jets ɗin suke?."

Ajiyar zuciya Manager Yhu ya sauke haɗe da faɗin ''An yi banning compayn daga ƙere-ƙere.''




Wani kalar baƙin ciki ya haɗiya sannan a hankali ya ce ''10 million will be deducted daga cikin albashin
ku, har sai kun gama biyan 500 billion ɗin, and no more allowances, daga yau na yanke wannan, next
time kuyi abu ba tare da kun shawarce ni ba.'' daga haka ya tashi ya fice daga office ɗin, suma suka bi shi
jikinsu babu ƙwari.




Ko da ya fito direct basement ya nufa tare da ɗaukan motarsa ya bar compayn gaba ɗaya, ya nufi hanyar
gidan nasa.




<><><>><>><>>><><>



A school ɗin ma da ƙyar ta samu ta iya yin lectures saboda baccin da take ji, around 4pm suka fito daga
cikin school ɗin, duk da ba ta wani biyewa Lilyn ba ta dawo gidan Mamin.
Sosai ta hana idanunta bacci ta taya ya'n aikin gidan aikin bayan sun sanar da ita Mamin na kwance tun
bayan fitarta.



Sai ƙarfe tare ta dawo gidan nata, shima kamar jiya haka ta tarar da pizza da ice cream akan dining table
ɗin.



Murmushi ta yi mai kyau dan na jiya ma mantawa ta yi ba ta tambayi Salimah wanda ya kawo ba, amma
ta na gani ta san wannan aikin Abbinta ne.




Yanka ɗaya kawai taci ta ji gaba ɗaya ya gimsheta, hakan ya sanya ta tashi a hankali ta nufi hanyar
ɗakinta dan wani kalar bacci ne a idanunta.

Ko wanka ba ta iya yi ba balle cire kayan jikinta, tare da abayar ta kwanta bacci mai daɗi ya sureta.




Kwance yake yana kallon yadda take baccinta hankalinta kwance, he's missing her badly, ya na son ya
ƙara kasancewa da ita, ko wannan kukan na ta da take, missing komai na ta yake.

Wayarsa ce ta yi ringing hakan ya sa shi kallon wayar domin ganin wanda ke kiran na sa, ganin Amir ne
ya sanya shi ɗaukan kansa ya na mai maida hankali wajen kallon laptop ɗinsa.



Sai da Amir ɗin ya jera ma sa miss call kusan guda uku sannan ya ya bi kiran na sa.

Ring biyu wayar ta yi Amir ɗin ya ɗauka.

''Assalamu alaikum Man." Amir ya faɗa daga kwancen da yake shima

Sai da ya ɗan ja wa Amir ɗin aji kaɗan sannan ya ce ''Wassalamu alaykum Dude.'' Hydar ya faɗa ransa
aɗan ɓace.

''Mai na maka, da idan na kira ka ba ka ɗagawa?, ko ka fara shaye - shaye ne?.'' Amir ya iddashe
maganar tare sakin dariya kaɗan.

Wani kalar haushi abin ya ƙara bawa Hydar dan ya tsani a masa laifi kuma a ɗinga ma sa dariya.
Cikin Wani kalar murya ya ce ''You're mad Amir, how could you?, you spoiled all my plans on that girl
Amir, ka ɓata komai Amir, wallahi idona idon ka a Nigeria ba zamu kwasa da daɗi ba.''



Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?."

Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business."

Da ga haka ya kashe wayar na sa.......




''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂
*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

The Noble Writers Team.




**Pending Amarya 47**



What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧



Not edited 🌟💔🥹



****




Wani dariyan Amir ya ƙara kwashewa da shi tare da faɗin ''Ka yi, ko ba ka yi ba?."

Wani ɓakin cikin Hydar ya haɗiya tare da faɗin ''That's not your business."

Da ga haka ya kashe wayar na sa.......
After 2 weeks.




Sosai ta maida hankalinta kan lafiyar Mamin, dan yanzu kam baccin da take yawan yi ya ɗan sake ta, ta
na ɗawainiyya da ita sosai.



Yau ɗin ma kamar kullum ta shirya cikin wani dark purple color hijab, sannan ta ɗaura da wani farin
classic booth white color, sai kuma wani white designer bag na companyn dior.



Wayarta na hannunta ta fito tare da zama akan kujerar dinning ɗin ta na mai ɗaga tafasasshen madarar
da ta saka Salimah ta dafa ma ta haɗe da kaninfari.



Ta ji daɗinsa sosai hakan ya sanyata shan kusan rabin mug ɗin, sannan ta fice daga gidan.

Sai da ta biya gidan Mami ta ga lafiyar jikinta wanda Alhamdulillah ta samu sauƙi sosai, sannan ta wuce
school.




Bayan an gama lectures ɗin ma Lily ce ta nemi rakiyar ta hakan ya sanyata tashi haɗe da bin bayanta
suka bar school ɗin acikin motar Lilyn.



Basu zarce ko ina ba sai gidan Lilyn, ba ta iya cin komai ba in banda wani milk shake da ta gani akan
bedsides kawai ta ɗauka ta sha tare da ɗan kishigiɗa.
''Ahhh, i just dey wonder your situation OOO, anya ba ciki ne dake ba?." Lilyn ta faɗa tare da kanne ma
ta ido ɗaya.



A zabure ta miƙe sannan kuma ta koma ta zauna tare da faɗin ''Ke kika yi min?, ni mai nayi ma da zan yi
ciki.'' Liyanar ta faɗa a rarrabe.



Wani kalar dariya Lily ta yi tare da faɗin ''Wallahi you're very funny, ko da ace Hydar dutse ne , ba zai
taɓa escaping hanyar da na sa ki ba.'' ta yi maganar tare da ɗaukan wani magani ta na mai watsawa a
bakinta.



Wani tsaki Liya ta ja tare da faɗin ''Your hanya wey lead me to hell, ni na ƙara ɗaukar shawararki over my
dead body.'' ta ƙarashe maganar tare da kunna datar ta.

''Jezz!, gist me wetin happen babe.?'' Lily ta faɗa tare da matsowa kusa da Liyanar.



A taƙaice ta faɗa ma ta duk abin da Hydar ɗin ya mata har da wani ɗan kukanta ta ce ''Lily if you see the
kind wahala wey that guy give me, ba za ki so na zauna a gidan ba wallahi.''

Wani kalar ajiyar zuciya Lily ta sauke tare da faɗin ''Then leave, kar ki saka kanki cikin rayuwar da ba za ki
iya ba.'' Lilyn ta ƙarashe maganar tare da shafa bayanta.

''Lily i can't leave him, kin san ina son shi, na tsani kaina idan na tuno rashin mutumcin da na yi masa, Lily
I'm dying wallahi, idan da gaske ne ina da ciki, da sai na fi ko wace ya' mace sa'a a duniya.'' ta ƙarashe
maganar tare da ɗaukan wayarta da jakarta ta na mai miƙewa.



''Where are you heading to.?" Lilyn ta faɗa tare da ta shi tsayen ita ma.



'' To the hospital.'' ta faɗa tare da zira slippers ɗinta.

''Let's confirm it first before taking any action babe, ƙila period ɗinki ne ya zo da hakan.''

''Noo Lily na fi tunanin cewa cikin ne, dan yau wata ɗaya da sati uku da ban ga period ɗina ba kenan.''
Ajiyar zuciya Lilyn ta sauke tare da nufar kan standing mirror ta ɗauki mukullin motar ta suka fi ce daga
cikin gidan.




After 5 hours 🦚🌟




Ko da aka yi test ɗin kuwa result ɗin ya fito da cewa ta na ɗauke da cikin wata ɗaya da sati uku da
kwanaki biyar, wanda hakan ya ɗirar ma ta da farinciki da kuma aka sin sa, duba da yadda course ɗin da
take karantawa ya shaida ma ta da zafin haihuwa.




Daga hospital ɗin ma makarantar ta koma tare da ɗaukan motarta ta koma gidanta.




><><><><><>><>>><><

Zaune yake a makeken falonsa, hannunsa riƙe da wani book mac ya na duba kayan da suke out of stock
domin a fara ƙera sabbi, da ma wasu colors ɗin.



Wayarsa dake gefensa ne ya yi ringing hakan ya sanya shi kai duba wajen da wayar ta sa ke ringing ɗin.



Sunan Abbhu ya gani akan screen ɗin wayar hakan ya sanya shi ɗaukan wayar tare da karawa a
kunnensa.



''Assalamu alaikum Abbhu, ina wuni.'' Hydar ɗin ya faɗa ya na jiran amsar da Abbhun zai ba sa.
''Wassalamu alaykum, Son ya aikin.?"

''Alhamdulillah, Abbhu.''

''Daman na kira ne na sanar da kai ba kai kaɗai bane ba yanzun, you should come back home saboda
matarka, ka ji ni.?" Abbhun ya faɗa ya na mai jiran amsar da ɗansa zai ba sa.




Wani ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin ''Eh Abbhu daman am planning na dawo next month in shaa
Allah, ya jikin Mami.?"

''Okay, Allah ya maka albarka, jiki da sauƙi matarka na kula da ita sosai yadda ya dace, ta samu ƙarfin
jiki, dan karaya ce ta samu a wajen ankles ɗinta.''

''Mami really try gaskiya, Allah ya bamu lafiya ba ki ɗaya.''

''Amin son.'' daga haka suka yi sallama.




><>><><>><><>><>><>
Gidan Ammi kam soyayya tsakaninta da Abbhi ba'a magana kafin ta faɗi abu har an yi ma ta shi,
Rufaidhat yanzu babu dare babu rana kullum ta na yawon neman maganin infection wanda zai yi curing
ɗinta.



Ko ta kan girls ɗinta ba ta bi, dan so take ta samu ta tara dukiya ita ma a gidan.




Zaune suke suna yin break fast a katafaran dinning table ɗin na su, Ammi na sanye cikin wani kalar abaya
mai tsadar gaske, Abbhi na kusa da ita cikin wasu ƙananan kaya farare da suka yi ma sa kyau sosai, ya na
shan wani fruit salad da Ammin ta haɗa ma sa.



Cikin muryarta mai sanyi ta ce ''Yaya yaushe ne family meeting ɗin.?" Ta tambaye sa tare da k'afesa da
idanun, ɗago kansa ya yi a hankali, hakan ya basu daman haɗa ido da Abbhin, kanne ma ta ido ɗaya ya yi
tare da faɗin ''I think is today, why are you asking.?"

Sauke kanta ta yi dan har yau ta na mugun jin nauyin sa.



Murmushinsa ya yi mai kyau tare da faɗin ''Ki daina jin wannan kunyar Iki, shekaru kusan 27 da
kasancewar mu tare ba fa wasa bane, atleast said it out ki na son ganin Liyana, amma wannan noƙe -
noƙen ki daina shi." Ya yi maganar ya na mai ƙafeta da idanunsa.



Gyaɗa kanta kawai ta yi tare da cigaba da shan water melon juice ɗinta.

Tsaki da suka ji a wajen ne ya basu damar juyawa suna mai kallon Rufyn da take ta doka wata uwar tsaki.



''Hajiyata ke ba za ki shirya ba ne, ko mu tafi ne.?" Abbhin ya faɗa ya na mai kallon Rufaidhat.

''Wllahi Nabil ka na ba ni mamaki, wannan abin da kake ka na nuna min banbanci, wanda hakan sam bai
dace da kalar rayuwar da muka tsara ba kafin ya'r ƙunar baƙin waken nan ta raba.'' Rufaidhat ta faɗa ta
na mai kauda kanta gefe daga kallonsu.



''Kar ya dace ɗin mana, damanta ne ki barta ta dama, kema da daman ki ya zo kin fi kowa zaƙewa ai.''
Abbhin ya faɗa tare da miƙewa dan a rayuwarsa ya na mugun son ya ga ya haɗa faɗa.



''Haka ka ce.?" Rufy ta faɗa tare da ƙafesa da manyan idanunta.



''Tsoronki nake ji ai, Mamma ta so mu tafi, ke kuma Ikimat zauna ta fasa miki kai kin ji.''

Daga haka ya sanya kansa haɗe da fita daga cikin falon.



''Shegiyya karuwa, wadda ba ta zo da budurcinta gidan mijinta ba, mai halin akuyoyi.'' in ji cewar
Rufaidhat da ta tashi ta yi hanyar fita daga falon.



''Ammi idan ba ranar da na ci uban matar nan ba, ba za ta saurara da kiran wannan sunayen ba.'' Ily ta
faɗa zuciyarta na ƙuna.



A zuciye Ilyn ta bi bayan Rufaidhat da ta nufi hanyar fita a falon domin zuwa wajen Abbhi, ita ma Ammi
da saurinta ta biyo ta ganin kamar yarinyar ta fita a hayyacinta.




Cimma Rufaidhat ɗin ta yi tare da wani kalar hankaɗeta, Rufaidhat har ta sadaƙar za ta faɗi Abbhi ya yi
saurin riƙe hannunta dan kaɗan ya rage maƙogwaronta ya caki wani ƙarfe da shi ya raba parking space
da garden ɗin gidan.

Tare da janyota jikinsa, ''Mammah mai ya faru haka?, da za ki kasheta.'' ya yi maganar ya na tsare Ily da
idanunsa, ''Abbhi just let me, ka barni na koya ma ta hankali.'' ta faɗa idanunta na zubar da ƙwalla.

''Shut up, shiga cikin mota, matar ta wa za ki koyawa hankali, kamar wa ta sa'ar ki?, get in.''

Fashewa ta yi da kuka tare da shigewa bayan motar, ita ma Rufaidhat bayan ta shiga, sannan Ammi da
fitowarta kenan ta shige gaba.
><><>><><>><><>>><>><>><>><>




Bayan ta tashi daga baccinta sallah ta yi tare da yin miraja'a haɗe da azkar da ta sabawa kanta da su
ayanzu, sannan ta wuce kitchen suka fara haɗa breakfast ɗin da zasu sama cikin su.



Bayan sun gama karyawan ɗakinsa ta shiga, tare da goge shi tass haɗe da sanya turaruka masu ƙamshin
gaske, ɗakinta ta koma tare da shiryawa cikin wani abaya mai kyaun gaske, tare da sanya wani face mask
haɗe da saka eye glasses ɗinta, safar hannu ta saka wanda hakan ya sanya cikar kamalarta fitowa.



Wayarta ta ɗauka tare da saka shi a cikin jakarta na companyn channel, tare da ɗaukar key ɗinsa ta nufi
hanyar falon cikin gidan.



Ita ma Salimah a shirye take cikin abaya, daga falon kuwa compound suka wuce tare da ɗaukan motarta
suka wuce gidan Nenehn.




Horn suka danna wanda atake mai gadi ya buɗe musu gate ɗin tare da shigar da motar nasu, compound
ɗin dake cike da motoci na alfarma.




Wani kalar farinciki ne ya ziyarceta ganin motar Abbhinta a compound ɗin, dan ta san duk inda ƙarfe
takwas yake a gidan yake musu idan za'a yi taron family.




Har kusan tuntuɓe ta yi tsabar farinciki, da ɗan gudunta ta iso cikin falon tare da faɗawa ajikin Ammi
dake zaune cikin cousins ɗinta da suke sa'anni.
Gidan acike ya ke da jama'a, su Rashanda ne da su Unaisah da Classy Reeda suka fito da ɗan gudunsu jin
muryar Liyanar a falon.



Umma Mansura ce ta fito hannunta riƙe da wani bowl dake cike da sararran rake ta fito daga cikin
kitchen ɗin falon jikinta sanye da wani less mai kyau da tsada.



Da ɗan sauri ta saki Ammi tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta su
ɓare.

Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"

Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai
ƙyalƙyala dariya.......




''Ya Ubangijina ka basu daman share."



Allah ya yiwa fans ɗina masu sharing arziki fiye da Dangote ✨😤🌟

Ma ra sa share Allah ya kawo kuɗi na siyi mota na tada muku ƙura 😂😂



*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION
The Noble Writers Team.




**Pending Amarya 48**



What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧



Not edited 🌟💔🥹



****




Umma Mansura ce ta fito hannunta riƙe da wani bowl dake cike da sararran rake ta fito daga cikin
kitchen ɗin falon jikinta sanye da wani less mai kyau da tsada.



Da ɗan sauri ta saki Ammi tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta su
ɓare.

Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"

Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai
ƙyalƙyala dariya.......
Da ɗan sauri ta saki Ammin tare da faɗawa jikin Umma Mansurar da saura kaɗan raken dake hannunta
su ɓare.



Abbhi dake zaune ya na kallon ikon Allah ne ya ce ''Yau Daughter ni aka manta kenan.?"

Tsintar muryar Abbhi da ta yi ne ya sanyata saurin sakin Umma haɗe da rungume Abbhin, ta na mai
ƙyalƙyalewa da dariya.




''I can see you guys are all happy seeing me here right beside you, na yi farincikin ganinku sosai, Aunties
and Mummies, da ma ya'n uwana, barkammu da haɗuwa da junanmu.''



''Ma shaa Allah daughter ya kike ya mai gidan.?" Umma Mansura ta faɗa tare da miƙa ma ta bowl ɗin
raken hannunta.



''Lafiya lau Umma, ina su Rashidat?, ko ba'a zo da su ba.?" Liya ta yi maganar tare da ɗaukan raken da
ke cikin bowl ɗin ta na mai fara sha.



''Daughter suna dakin ki ai, tun safiya suke jiran zuwan ki.'' in ji cewar Umma Mansura.



Tashi ta fara harraman yi da niyyar shiga cikin ɗakin, hannunta na riƙe da raken tare da cire veil ɗin
abayarta mai ɗan faɗi da ya lulluɓeta sosai ta na mai miƙawa Abbhinata.
Ɗakinta na gidan Nenehn ta nufa, har ta kai hannunta kan handle ɗin ƙofar ta ji muryar Ammi cikin
kunnenta.

''Liya, dawo nan ki zauna.'' Ammi ta faɗa ba tare da ta kalli mutanen dake wurin ba.



''Saboda mai?, haka kawai ba ƙawayenta ba ne , ke dai Salamatu ki rage baƙin halin nan na ki.''

Neneh da take saukowa da ita da Jiddah ta faɗi hakan, jikinta sanye da wasu ox blood color lifaya masu
kyaun gaske.



Gaishe da Neneh da Jiddah ya'n falon gabaɗaya suka yi, Liyana kam jikinta har mazari yake taje wajen
Jiddahn haɗe da ba sa side hug.



Murmusawa ya yi tare da shafa kanta ya na mai faɗin ''Ya Zahra na same ku lafiya.?"

Wani kalar frawn ɗin fuskarta ta yi tare da faɗin ''Allah ni Jiddah na yi fushi ma da kai.'' ta yi maganar a
shawgwaɓe kamar yadda ta saba yi ma sa.



Murmushi kawai ya yi tare da zama akan kujerar da take a matsayin na sa wanda ko da wasa Neneh ba
ta barin kowa ya zaunar ma ta.



Zame jikinta ta yi daga falon tare da shigewa ɗakin na ta wanda duk a idon Ammi da ta kasa magana
saboda ganin idanun Neneh kurr akanta.



Ƙarasa shigowa cikin ɗakin ta yi ta tarar da su Rashanda da su Ilham da sauran counsins ɗinsu gabaɗaya
suna ta hira, Yusrah na zaune daga gefen wajen book corner ɗin ɗakin ta na chatting da wayarta forming
boss lady.

Shigowarta ya sanya su wani kalar ihu haɗe da murna kowannensu na ta shouting ''Awwn.'', ''Mrs
HYDAR.''

Basar da su ta yi tare da faɗin ''Wai na fito rannan kuma ban ganku ba.?" Ta yi maganar ta na ƙoƙarin
amsar coke ɗin dake hannun Ilham.
Tsaki suka ja a tare, sannan Unaisah ta ce ''Ai ni na manta, da wallahi babu wadda za ta miki magana
acikin mu.'' ta yi maganar tare da harar Liya.



''Wallahi Yaya kin ɓata min rai, har yau idan na tuno kamar na yi kuka.'' Ilham ta yi maganar kamar ta
kwashe Liya da mari.



''Wannan kuma matsalar ku ce, ai sai ku bar masu aure su shana, haka kawai da daddaren Allah ku wani
kwaso jiki, wai za ku kwana.?"



Liyanar ta yi maganar tare da tashi da niyyar fita daga ɗakin.

Yusrah da tun ɗazu maganar Liya ke shigar ma ta kaine ta ajiye wayarta tare da juyowa ta na faɗin ''Toh
dan ubanki sai ki aurar da waya'nda ba suyi auren ba.''

All of them were shocked, dan su har ga Allah sun manta da wanzuwarta a ɗakin.



Classy Reeda ce ta ce ''I don't understand, wani ya yi mention ɗinta a nan ne?, ko akwai sa'anta anan.?"
Ta yi maganar tare da ajiye pillown da yake kan ƙafarta.



''The thing wonder me OOO." In ji cewar Rashidat.



''Yaya dan Allah don't respond to her, ki ƙyaleta dan Allah.'' Ilham ta yi maganar ganin Liyanar ta fara
ƙanƙance ido.

Tsaki Liya ta ja tare da faɗin ''Ni nafi ƙarfin nayi dake kema kin san sai dai na yi da Fatuh mai warin
hammata.''

Daga haka ta fice daga ɗakin tare da rufe musu ƙofar da ƙarfi.

''Kutumar......., wallahi sai gidan nan ya koma na yaƙi.'' Yusrah ɗin ta faɗa tare da ficewa ita ma daga
ɗakin.



Su ma gabaɗaya suka mara musu baya.
Afalon su Mama Fatuh har sun fito daga backyard daga dafa abincin da suke yi a traditional kitchen ɗin
gidan, yan aikin Neneh da Salimah da ta zame ta tafi can tun bayan zuwan su, suna ta rabon abincin da
ya ji crey fish.




Yusrah ce ta zo ta tsaya akanta cikin fushi tare da faɗin ''Mama ki taso mu tafi ba zan iya ɗaukan
wulaƙancin kowa a gidan nan ba.'' ta yi maganar hannunta riƙe da ƙugunta.



Umma Mansura ce da abin ya ɗaure ma ta kai ta ce ''Yusrah ban gane wulaƙanta ki ba ?, wa ya
wulaƙanta ki ɗin toh.?"



Ko kallonsu ba ta yi ba ta ci gaba da yiwa Mama Fatuhn magana.



Ammi ce ta kai dubanta wajen Liyana tare da faɗin ''Hope nothing happened a tsakanin ku.?"



''Ammi zagi na ta yi na rama.'' Liyana ta yi maganar tare da miƙewa daga kusa da Ammin.



''Yusrah ki yi haƙuri ma na ki koma ki zauna.'' Ammin ta yi maganar a sanyaye.

Tsaki Yusrah ta yi tare da faɗin ''Ki ajiye kirkin ki na banza da na wofi a gefe, watarana za ta miki amfani.''



Daga haka ta ja wani tsaki tare da barin wajen.

''Idan kun san wata ba ku san wata ba, Ikimat ki gaya ma ɗiyarki da ta kiyayi ƙasar shuri, ko da kuwa ta
na cin ko wani ƙasa ta zauna lafiya.'' Mama Fatuh ta yi maganar tare da ɗaukan jakarta.



''Yaya wallahi, ni ban san mai ya faru ba dan Allah ki yi haƙuri.'' Ammi ta yi maganar kamar za ta yi kuka.
''Wallahi Aunty kika ƙara ba ta haƙuri sai na kira Yaya na sanar da shi wannan maganar, tun da ke ba kida
hankali, ta ya ana ƙoƙarin kashe magana ya'rta na wa mutane rashin kunya kuma ta na maganar a kiyayi
ƙasar shuri, ita ma ta kiyaye sa, ubanwa rigimar ta kashe, ita ma kanta ta san Nabil ya ji wannan maganar
ba a nan kaɗai za'a tsaya ba, daga can ki yi can.'' Umma Mansura ta faɗi maganar zuciyarta a ɓace.



Juyowa Mama Fatuhn ta yi tare da faɗin ''Ai ni ban yi dake ba Mansura, da ƙanwata nake.''



''Sai ki gayawa Awwalu maƙera na garin maraɗi.'' Mama Mansura ta yi maganar tare da ɗauke kanta
gefe.




''Mansura za ki ci kaza - kazan ki, dan ubanki.'' inji cewar Mama Fatuh dake tsaye ta na huci.

''Idan kare ya na haushi ba'a tanka shi ai.''



Wani uban tsaki Mama Fatuhn ta ja haɗe da barin gidan.



''Umma ina su Abbhin suka je.?"

Liyana da tun ɗazu jikinta ya yi sanyi ta tambayi Umma Mansura.



''Daughter sun fita da Neneh da Jiddah taron Y'an Maiduguri.'' Mama Mansura ta ba ta amsan haka.



''Ilham zo ki raka ni gidansu Sultana.'' ta yi maganar ta na zira slippers ɗin da ta gani a palourn.

''Wace Sultanah da za ki kwashi jiki, ki tafi.?" Umma Mansura ta tambayeta tare da ƙafeta da idanuwa.

Cikin inda-inda ta ce ''Gidansu .........Ya Aliyu fa, nan maƙotan Neneh.''

Please Login or Register in order to submit comment