You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

''Dan girman salatin Annabi kar ka dake ni.'' ta yi
maganar ta na ɗan ja da baya zuwa wajen stairs, wani kalar sulɓi ne ya kwasheta kanta ya buge da
benen farko wanda hakan ya sanyata sakin wani kalar razananniyyar ƙara....



Takowa ya yi har wajen da take a yashe, tare da zuba hannayensa cikin aljihu, a hankali ya tsugunna a
wajen tare da faɗin ''I don't care about kin faɗi ko kin ji ciwo, all I know is that sai kin canza change over,
and right now not later.'' ya ƙarashe maganar haɗe da hankaɗe ta da ƙafafunsa ya na mai ball da ita.



Wani wahallalen kuka ta saki haɗe da dafe kanta tare da yunƙurawa ta tashi domin zuwa backyard ta
kunna solar.



A daddafe ta kunna solar sannan ta dawo cikin falon, inda Allah ya ceceta ma kanta kumburi kaɗai ya yi
ba ta ji ciwo sosai ba, direct kitchen ta nufa tare da ɗora tukunya dan har ga Allah ba ta san mai za ta
dafa ba, kashe gas ɗin ta yi tunawa da conflakes da ta yi.



Komai na conflakes ɗin da za'a iya amfani da shi wurin shan shi ta zuba a resin tray, haɗe da jera shi akan
dinning table ɗin.

Wanda ta jiƙa ma kasa sha ta yi dan ba ta wani jin yunwa.



Hydar kam ya na shiga ɗakinsa ruwa kawai ya watsa tare da jona phones ɗinsa a charge, sallolinsa ma
acikin ɗakin ya yi su dan a lokacin har an fara kiran sallahr isha.

Wayarsa ce ta fara ringing wanda hakan ya sa shi sakin wani ɗan gajeren tsaki dan ya tabbatar ƙila
Abbhi ne, dan wayar Liyanar na hannunsa har yanzu, tun ɗazu Abbhin yake kiran wayar daga ƙarshe ya
kasheta gaba ɗaya.




Ko da ya ɗauko wayar nasa ma Amir ne ke kiransa hakan ya sa shi ɗaga wayar a hankali, tare da faɗin
''Assalamu alaikum, Amir what's wrong ka yi min booking ɗin?.''
''Wassalamu alaykum, Man an ɗan samu matsala babu jirgin da zai je China direct.''



''Fucked up, yanzu sai yaushe?, ɗaga meeting ɗin zan yi kenan?."



''I think soo Man, ka ɗaga meeting ɗin, wannan ACn da ka turo min ita ake son ka ƙera a companyn ka?."



Sai da Hydar ya ɗan ja numfashi sannan ya ce ''Yeah, na ma rasa wani suna zan saka mi shi.''



Dariya Amir ya yi sannan ya ce ''Toh ka saka sunan matarka ma na .'' ya yi maganar ya na gimtse
dariyarsa.



A take muryarsa ta canza cikin wani kalar salon rashin mutumci kalar na Hydar ya ce ''Soo ka na son Ac
ɗin ya ƙi samun karɓuwa ko ajanye offer ɗin Almost 70 billion dollars, kar ka sa raina ya ɓace da daren
nan please.'' daga haka ya kashe wayarsa tare da jan duvet ya na mai kwanciyarsa.



Jin shiru bai fito bane ya sanyata shigiɗa akan kujerar parlourn tare da duƙunƙune jikinta wuri ɗaya, dan
har a lokacin ba ta san asuba ta yi ba. Cikin shirinsa na masallaci ya kalleta kan kujera takure waje ɗaya
ta na baccinta hankali kwance, direct kitchen ya wuce haɗe da buɗe fridge tare da ɗaukan goran ruwa
mai sanyi, da sauri ya ɓalle bottle ɗin haɗe da juye ma ta shi gaba ɗaya a fuska wani kalar wahallalen
ajiyar zuciya ta sauke, haɗe da tashi a zabure ta na mitsitsika ido.




Da ga haka ya fice i zuwa masallacin, ta shi ta yi haɗe da nufar stairs ta na mai nufar ɗakinta.



Sai da ta yi wanka haɗe da brush sannan ta yi sallar jikinta duk agajiye.



Hijabyn jikinta ta zare tare da saukowa ta na mai nufar kitchen ɗin, chips kawai ta soya da ƙwai sannan
ta ɗaura coffee a coffee mixer, tare da ɗaukan flask ta tari ruwan zafi a dispenser.
Ƙarar shigowarsa ta ji wanda hakan ya tabbatar ma ta da ya dawo daga masjid, hakan ya sanya ta ɗan
gyara kitchen ɗin dan ta san zai shigo ɗaukan coffee.



Kayan da ta jera a tray ta ɗauko tare da nufar dinning room ɗin ta na kallon cikin tray ɗin da ta ga wani
ƙwaro na yawo aciki, karo ta ci da shi da yake kallon waya wanda alamu sun nuna kallon wasu abubuwan
yake masu muhimmanci acikin wayar.



Abincin dake cikin tray ɗin ne gaba ɗaya suka zube ajikinsa wayarsa dake hannunsa kuma ya yi flat a
ƙasa.

''Inna lillahi wa inna ilaihir rajiun, am dead, wallahi tallahi billahillaxi la ila ha illahuwar - rahmanu i didn't
do it intentionally, ka ji rantsuwar Musulunci kenan.''

Ta yi maganar hawaye na zuba a idanunta. ''Thank God kin san kuɗin wayar da kika fasa right?.'' gyaɗa
kanta ta yi sannan a hankali ta ce ''Is 4 million plus.''

Murmusawa ya yi tare da faɗin ''Smart girl, oya miƙo min wayata before I turn your face to blue black.''
ya yi maganar a tsawace.



Durƙusawa ta yi da niyyar ɗaukan wayar wanda hakan ya sata jin saukan wani kafirin duka a bayanta.

Runtse idanunta ta yi tare da ƙarasa ɗaukan wayar tare da miƙo ma sa idanunta na zubda hawaye.

Sai da Aliyu ya sa ta gyara gidan ga ba ɗaya tsaf sannan ta huta, still kuma he didn't gave her, her phone,
duk hakan ya sata shiga wani hali.




***_____***




Da sassafe kamar yadda ta ɗan saba a kwanakin nan ta tashi tare da yin iya abin da za ta iya, glass
cleaner da mooper da kuma towel a hannunta ta nufi kan dinning domin goge area ɗin .
She was surprised to see her phone akan dinning table and also shocked at the same time, ''Ahh wannan
halittan ya manta wayar yau anan kenan, ɗan ƙwal uba.'' ta iddasa maganar haɗe da ajiye tarkacen dake
hannunta ta na mai ɗaukan wayar, screen ɗin wayar a kunne yake picture ɗinta da Ammi da Ilham da
kuma Abbhi ne agaban wayar,wanda da alama dai hoton last year eid ne.



Kallon wayar ta yi haɗe da faɗin ''One big family." Ƙwalla na ɗan zubo mata.

''Uban mai kike da wayar hannunki?." Wani kalar bugawa da zuciyarta ta yi sai da ta tsorata, wani tsawa
da ya daka ma ta sai da wayar hannunta ta faɗi aƙasa.



''Hasbunallahu wa ni'imal wakil, my phone, innalillahi wa inna ilaihir rajiun.'' ta iddasa maganar ta na
fashewa da kuka.



''Idan ba ki rufe min baki ba za ki gane shayi ruwa ne.''

Da sauri ta yi shiru haɗe da cigaba da goge dinning ɗin ta na kallon wayarta dake yashe a ƙasa.



Sai da ta gama gyara gidan duk da bai wani gyaru ba, sai arround 3 i clock sannan ta ci abinci shi ma
abincin bai ma ta wani daɗi ba, noodles ne sai hollandia strawberry da ta haɗa da shi.

***_____***




Sosai ya canza turarensa ya mai da shi shumuk luxury scent ba Valentino da Baccarat ko Georgia armani
ba, dan sosai shumukh ya take su wajen tsada, mazubin sa ma abin kallo ne.



Shi da Amir ne suka je shopping sai da suka biya ta gidansu Liyana da Neneh har gidan Mami da kullum
take cigiyar Liyana.



Bayan sun fito daga gidan Mami ma sai da ya biya restaurant ya yi take away ɗin fried rice and chicken
sannan ya sauke Amir shi kuma ya zaryo gidansa.
Ta na daga cikin falo a zaune ta ji an yi horn, da gudu ta tashi haɗe da saka slippers ɗinta tare da buɗe
masa huge gate ɗin.



Bayan ya yi parking motar na sa a wajen flowers ya tsaya ya na ƙare musu kallo, da ƙyar ta ƙarasa rufe
gate ɗin da ƙirjinta ke amsa nauyinsa sannan ta wuce shi da niyar shiga cikin gidan.



''Ke dan ubanki come back here.'' dawowa ta yi baya a hankali haɗe da faɗin ''Gani.''

Sai da ya mata kallon some seconds sannan ya ce ''Uban wa kika barwa watering flowers ɗin gidan nan,
abi na me you dey wait make i remind you tun da agidan ubanki ba ki saba ba?."



Ɗago kanta ta yi ta kalle shi ƙwalla na ziraro ma ta cikin sassanyar muryarta mai haɗe da kuka ta ce '' I'm
sorry.''



Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.....




Manage please b yawa🤗



*THE REGRET.*



Pending Amarya ce ✍️



JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION.

THE NOBLE WRITER'S TEAM 💎
*** Pending Amarya 40***




''Ke dan ubanki come back here.'' dawowa ta yi baya a hankali haɗe da faɗin ''Gani.''

Sai da ya mata kallon some seconds sannan ya ce ''Uban wa kika barwa watering flowers ɗin gidan nan,
abi na me you dey wait make i remind you tun da agidan ubanki ba ki saba ba?."



Ɗago kanta ta yi ta kalle shi ƙwalla na ziraro ma ta cikin sassanyar muryarta mai haɗe da kuka ta ce '' I'm
sorry.''



Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.....




Da ga haka ta nufi backyard domin ɗauko abin da za ta yi watering flowers ɗin.

Direct ɗakin shi ya nufa ya na mai shirya turarukkansa akan standing mirror ɗin.




** After 3 weeks**
Zaune take akan kujera ta na kallon TV ɗin ɗakin amma sam hankalinta ba ya kan kallon da take, yau sati
uku kenan da fashewar wayarta da har yau bai ba ta ba, ga rashin chatting da Abbhinta da su Rashidat
da ke ta ɗawainiyya da ita.



Tunanin kalar halin da Abbhi zai shiga idan ya kira ya ji wayarta a kashe ta ɗinga yi, duk ta rasa abin da ke
ma ta daɗi, yaushe rabonta da ta ci abinci mai nauyi yau kusan wata biyu kenan tun barin Salimah daga
gidan nan.




Cikin takunsa na ƙasaita haɗe da aura ɗinsa ya fito cikin shigarsa na manyan kaya black color wanda suka
ma sa kyau matuƙa, ƙamshin sabon turarensa da ya canza ne ya fara ratsa ƙofofin hancinta, kafin ta kai
kallonta garesa.



Sosai ya mata kyau girarsa da ta kusan haɗewa ta mugun tafiya da zuciyarta, lips ɗinsa da ɗan ƙyalli
kamar wanda ya sanya lipstick.

Har ya ƙaraso inda take ba ta sani ba ta na aikin kallonsa, cikin muryarsa mai amo ya ce ''Biyo ni.'' still ta
ƙafe shi da ido dan har ga Allah kawai lips ɗinsa ta ga ya motsa wanda suka ƙara narkar da zuciyarta, dan
ta kasa dawo da kanta hayyacinta ita dai kawai ta tafi duniyar imagination.



Kallon 3 seconds ya mata ganin da gasken gaske ba ta san ma ya na wani magana ba ya sanya sa shinfiɗa
ma ta wasu lafiyayyun ranƙwashi har guda biyu, wanda hakan ya sanyata dawowa hayyacinta.

''Za ki sanya hijabin ne ko za ki tsaya min halinki na biye - biye anan?." Ya faɗa tare da murtuke fuskarsa.



Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Na rantse ban ji ba.''

Tsaki ya ja kawai sannan ya wuce zuwa compound ɗin gidan, daman abaya ce ajikinta, mayafinsa kawai
ta yana akai tare da shafa lipstick a saman laɓɓanta haɗe da zira slippers sannan ta fito zuwa compound
ɗin.
Ya na zaune cikin motarsa ya yi balance ya na jiranta for almost 1 minutes.



niyar shiga motarsa take ƙoƙarin yi hakan ya sa shi ɗaga kansa haɗe da kallonta, cikin wani kalan tune ya
ce ''What are trying to do?, ko ba ki san aikin ki ba?."

''I'm sorry bara na buɗe.'' daga haka ta nufi gate haɗe da buɗe shi gaba ɗaya, fita ya yi da motar tare da
yin parking a ƙofar gidan sannan ya fito daga cikin motar, kallonta ya yi da kyau kafin ya cillo ma ta key
haɗe da faɗin ''Kulle ki same ni à mota.'' da toh ta amsa tare da rufe gate ɗin da saka masa pad lock.




Bayan ta gama kullewa cikin motar ta shige tare da kulewa a hankali, da mugun gudu ya figi motar basu
zarce ko ina ba sai rijiyar zaki, gidansu Aliyun.




****_____****




Acikin motar ma shiru ne ya ratsa motar, sannan a hankali ya ce ''Kin ga yadda za mu je gidan nan, You
better behave yourself, Kuma kar kiyi min kauyanci ki yi ta pretending kamar kina jin tsorona, wallahi
kika min haka ubanki za ki ci, ki min magana normal yadda kike wa samarin ki na da, idan ta kama You
can touch my hand, ki min magana kuma in form of biyayya, wallahi kika min iskanci sai kin koma gida a
ƙafa, kuma idan na riga ki zuwa gida ki sa ran ƙarewar rayuwarki na har abada, am I clear?." Nodding ɗin
kanta kawai ta yi ba tare da ta kallesa ba idanunta na zubar da ƙwalla.



Horn ya yi mai ƙarfin gaske wanda hakan yasa mai gadi buɗewa da sauri, bayan ya faka motar a parking
lot, saukowa ya yi ta na biye da shi jikinta sukuku, har suka ƙarasa babban falon gidan da gaba ɗaya
family ɗin suke zaune, Sultana na chatting da wayarta, yayin da Mami da Abbuh suke kallo a tashar
Aljazeera, shi kuma Sultan ya na kan dining ya na aiki da laptop ɗinsa.
Color fatarsa ya yi kyau sosai, ya yi fresh kayansa, jikinsa sanye da combat sai wani polo shirt ash color,
ta ma sa kyau sosai ma shaa Allah.



Assultanah ce ta fara an karewa da su , hakan ya saka ta yin cilli da wayar hannunta haɗe da rungume
Liyana da hannunta ke maƙale da na Hydar, da take ta ɗaɗɗari da shi.



Murmushi ta saki mai kyau haɗe da rungumeta ita ma, sannan ta kama hannunta suka ƙarasa cikin falon,
har ƙasa ta durƙusa haɗe da gaishe da Mamin tare da Abbuh zuciyarta na wani kalar bugawa kamar zai
fashe.




Bayan sun gama gaisawar Abbuh ya kira Aliyu dan akwai taron da zasu je, za'a bawa companyn Abbuh na
takalma award, Soo zasu je amsa.




Tun shigowar Liyana Mami ta fuskanci yarinyar duk ta yi wani kalar rama idanunta duk sunyi zuru zuru,
kamar mai shan wahala.



Kallonta Mamin ta yi da kyau tare da faɗin ''Fatima ki yi haƙuri ban samu time mun yi magana yadda ya
dace ba a wancan ranar, sai kwanaki muke maganar da Neneh take faɗa min abin kusan dole ne, soo am
sorry da yadda aka ɓillo miki da lamarin, hope kuma za ki zama good wife the way da kike ganin
mahaifiyyarki na zaune da mahaifinki, we are all sorry rayuwar aure sai haƙuri, idan ba'a yi haƙuri da
juna ba zaman ba zai taɓa yuyuwa ba, sai anyi haƙuri akan cimma nasara, gazawar haƙurin kuma kan
haifar da mummunar ciwo na har abada, na san Hydar na da wuyar sha'ani most times, ki ma sa biyayya
za ki ci moriyarsa, ki shanye duk wa ta muzanta ko ƙasƙanci da yake cikin rayuwar aurenki, Fatima.'' ta
iddashe maganar tare da kiran sunanta.

Ɗago kanta ta yi tare da faɗin ''Na'am Mami.''



A hankali Mamin ta ƙara faɗin ''Babu wani aure da babu ƙalubale acikin sa, kowa sai da ya sha wahala
sannan ya samar da gidansa, go ask everyone da kika sani yake da aure kafin ya zauna da ƙafafunsa
acikin gidansa sai da ya fuskanci ƙalubale, even me ban cire kaina ba, though I don't know about your
mom's side, buh kowa sai da ya fuskanci ƙalubale, ldan kika zama mace mai haƙuri, kin yi fice a wajen
mijinki.'' ta ƙarashe maganar tare da gyara zamanta sosai.



Liyana kawai bin Mamin take da kallo ta na ya ba wayewarta, no one has ever told her this before, ita dai
she lives her life ne kawai, ta yi duk wani badaƙalar da take so,.money is available for her, her dad is
available for all her need, soo she don't panic.




''I think lokacin sallah ya yi daga nan sai ku ɗaura girkin dare, ma za Sultanah kuje ku yi sallah ku mana
girkin dare kafin Abbhu ya dawo.''



Ta ƙarashe maganar ta na kallon Sultan da ya zuba mu su idanu, wani harara Mami ta maka ma sa tare
da faɗin ''ka wani tsare mu da ido ba zaka wuce ka fita wurin da ya aike ka ba sai ya dawo.''



''Mami fa har yanzu am heart broken à ɗinga lallaɓa ni.''

''ƙanin ubanka Wanda Qassim da zuwaira ba su haifa ba suka mutu, leave my presence, oloshi.'' ( Ashe
yaya Alih anan aka samo leave my presence 😂😂😂).




''Sorry Maa.'' daga haka ya ɗauki laptop ɗinsa da car key sannan ya fi ce daga falon, ita dai Liyana ko
kallonsa ba ta yi ba, dan ta na kiyaye eye contact da shi a yanzu.




Hannunta Sultanah ta ja suka nufi kitchen ɗin tare, in less than 30 mins suka dafa lafiyayyan cous cous
jollof da ya ci hanta da kaza, sai pepe soup da fruit salad da suka yi, duk da Sultana ce jagaba wajen
ayyukan.



Sosai gidan ya ɗau ƙamshi y'an aikin har sun gama gyaran gidan sosai.
Mami ce ta fito sanye cikin wani Adire gown maroon color ta yi kyau sosai, a time ɗin har sun kammala
komai akan dinning table ɗin.



A daidai lokacin kuma suka ji parking motoci a cikin compound ɗin, cikin minutes suka shigo shi da
Abbhu hannunsa riƙe da award ɗin mai form of takalmin wanda aka kera shi da glass, amma kallo ɗaya
zaka ma sa ka san cewa da diamond aka yi shi.



Bayan sun yiwa Abbhu sannu da zuwa, basu zauna ba suka wuce masallaci da Abbuhn da kuma Hydar,
after 20 mins suka dawo gidan, suka ci abincin gaba ɗayan su amma ban da Sultan da har time ɗin bai
dawo ba.



Sosai ta buɗe cikinta ta ci abincin, ƙarfe tara na dare ya ce da ita ta shirya su koma gida.

Lokaci ɗaya wani kalar baƙin ciki ya ziyarce ta mara misaltuwa, dan har Mami sai da ta yi noticing ɗin
halin da take ciki.



''Fatima ba kya son komawa gidan na ki ne ko ƙaƙa?."

''A'a Mami, ban leƙa gidan Neneh ba ne kuma gashi har zamu tafi.'' taƙarashe maganar hawaye na zuba
a idanunta.



Ga mamakin Mami sai kawai ta ga hawaye a fuskarta ta na gogewa.

Ita tun shigowar su daman yadda ta ga yarinyar wani iri duk a rikice ta san ba lafiya ba, kamar yarinyar
ba ta jin daɗin gidan Aliyun.



''Is Okay daughter, Aliyu maza ka kaita wurin Neneh sai ku wuce.''

Da toh ya amsa tare da kama hannunta suka fice daga gidan gaba ɗaya.



***_____________***
Ɓangaren Neneh kam kullum sai sun yi hirar Liyana da Salimah, ta na ba ta labarin yadda Hydar ke kula
da ita.



Cikin muryarsa mai amo yayo sallamar hannunsa sarƙafe da na Liyanar suka ƙaraso cikin falon.

''Ɗan halak ya ƙi ambato, ku ce shegun kuna kusa, toh Allah yaso ni alherin ku nake faɗa ba sharrin ku ba
balle ku ɗebe min albarka." Nenehn ta faɗa ta na gyara zaman glasses ɗinta.



Har ƙasa ta durƙusa cikin sassanyar muryarta ta ce "Nda Dubdo Neneh."



Amsa gaisuwarta Neneh ta yi tare da faɗin.

''Yau kuma da wannan salon aka zo kenan.''

A fakaice Liyana ta dallah ma ta harara wanda hakan ya haɗa idanunta da Nenehn.




" A uzubillah, Fatima mai ya sami fuskarki ta yi baƙi haka kamar lantarki?, Aliyu a haka na baka jiƙata ko
zallar baƙin halinka ne haka?."



" Malama za ki tashi mu tafi tun da kin ganta, ko jiƙata za ki yi ki shanye?." Ya yi maganar tare da ɗago
kansa daga wayarsa da yake dannawa.



Kamar za ta yi kuka ta ce " Neneh sai da safe."




" Allah ya tashe mu lafiya, kai dai Aliyu ko a aljanna na ganka sai na tambayi sababi, dan har ga Allah
kallo ɗaya za'a yiwa jiƙata aga wani kalar baƙi da tayi kamar hadari, toh daman dai wajen ƙiba bana ce ka
ramar da ita ba saboda daman can ko skeleton ya fi ta ƙiba."
Cikin muryarsa mai amo ya ce" nifa Neneh kar ki jefa ni à bakin duniya, ciki ne da ita, laulayi take, sai ki
barni na huta ai ko?, ke kuma taso mu tafi.''



Daga haka ya finciki hannunta suka koma can gidan nasu, ko ledar da Sultana ke bata, ba ta bi ta kansa
ba ya wulla ta cikin motar tare da mata key suka bar gidan.



''Ke dan ubanki ba nace dake you should feel free ba, kiyi rayuwarki yadda kika saba ba?." Ya tambaye ta
ya na wani kalar zaro idanunsa waje, wani kalar karkarwa jikinta ya soma yi, sannan a hankali ta ce
''Please, ka bar ni ko fuskar iyayena na gani i don't think idan na cigaba da rayuwa da kai zan kai labari,
ban san tsoro ba, kai ka fara sanar da ni, ban san menene zubar hawaye ba a silar ka na san hakan,
please and please, for once ka barni na shaƙi iskar farin ciki arayuwata, honestly na gaji am tired please.''

''Okay ni da ke mun zama sa'anni da har za ki kalli idanuna ki gaya min magana san ranki ko, ko dan na
riƙe hannayenki yau a tunaninki shinfiɗa na haɗa dake?, is alright, za ki wuce ki buɗe gate na shigar da
mota ko sai na ɓaɓɓalla ki?."




Ba ta tanka ma sa ba ta ɗauki key ɗin tare buɗe ma sa haɗe da buɗe gate ɗin gidan, da gudu ya shigo
cikin gidan haɗe da parking motar a wajen da aka tanada.




Hannunsa riƙe da award ɗin da Abbuhn ya bashi ya ajiye a wurinsa ya fito daga motar, ya na kallon
yadda take kiciniyar kulle ƙofar.



Da ƙyar ta gama sannan ta wuce backyard ta kunna solar, haɗe da watering flowers ɗin gidan gaba ɗaya.

Sai wajen 12 na dare ta kwanta, kasa bacci ta yi saboda tunawa da Birthday ɗin Abbhi da ta yi, wanda
al'adarta ce ita ke fara yi masa wishes da gifts.
Wani kalar fashewa da kuka ta yi ta na mai ƙanƙame jikinta, murɗa handle ɗin ƙofar aka yi tare da
shigowa cikin ɗakin, wanda daman ba ta kulle ƙofar ba, dan ya sha mata warning akan kulle ƙofa, akan
hakan ma ya sha mata duka, jikinsa sanye da pyjamas white color ta janye sleep mask ɗinsa zuwa kan
gashinsa, hannunsa sanye cikin aljihunsa.

Kallonta ya yi cikin shigar kayan baccinta pyjamas purple color, buh wandon is short, kanta sanye da
hula, santala santalan cinyoyinta ya bi da kallo da sai wani kalar sheƙi suke, dan yanzu ba ta kwana babu
haske tun da ta na rashin waya.



''Am even regretting why ƙanwar ki ta ɗauki number na ta bawa mahaifinki, kusan kullum sai ya min 10
miss call I donno ko ba shida aikin yi ne.''



Ba zato babu tsammani ta ji kawai ta yi wani mugun fashewa da wani kalar kuka mai cin rai, ita
arayuwarta da a zagi Abbhi gwara a zagi Ammi, dubi filthy words da yake faɗawa mahaifinta fi sabilillahi.



Dailing number Abbhinata ya yi tare da miƙa ma ta wayar, ring ɗaya kamar jira ake ya katse kiran haɗe
da biyo kiran, ''Hello dear, kin wuni lafiya?."

Sai da ta kalli fuskarsa sannan ta ce ''Ina wuni Abbhi, ya gida, ya su Ammi da Ilham?."

Sai da Abbhi ya yi ƴan sakanni, because all his life Liyana ba ta taɓa gaida shi cikin ladabi haka ba, sannan
a hankali ya ce ''Lafiya lau, kowa lafiya, mai sa muryar ki ya yi sanyi haka rashin lafiyar ne har yanzu?, ga
shi kusan last 3 weeks kika ce za ki zo, ba ki zo ba?."



Ita ta manta da wani Hydar ma a kusa da ita cikin wani ɗan murya mai nuna zumuɗi ta ce ''Kaji Abbhi da
wani zance, Allah na tuba sai ka ce baka san gidana ba, kai ba zaka zo ba ni zan ta zuwa?.'' ta yi maganar
ta na wani kalar dariya haɗe da rufe bakinta da hannunta.



A ta can ɓangaren Abbhi ya ce ''Daughter kin manta birthdayn Abbhinki kenan?."

''Allah sarki Abbhin Liyana kar kayi fushi kana can cikin raina, wallahi riga ni faɗa kawai ka yi, toh Happy
Birthday,my rock, Allah ya kawo shekaru masu Albarka.''

''Yeah Daddy's girl.''

''Abbhi am a lady not a girl manaa.''

Ta yi maganar ta na turo baki.
''I will come tomorrow in shaa Allah, let's goo for our annual shopping.'' Abbhin ya faɗa ma ta tare da yi
mata sai da safe.



Wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce ''Sai in ga uban da zai fita gate balle yaje shakatawan.''
daga haka ya fice daga ɗakin.......




Manage please b yawa🤗

*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

The Noble Writers team.




**Pending Amarya 41**
What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧



Not edited 🌟💔🥹



****




Wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya ce ''Sai in ga uban da zai fita gate balle yaje shakatawan.''
daga haka ya fice daga ɗakin.



Da ido ta bi shi har ya fice daga cikin ɗakin, sannan a hankali tayi kwanciyarta haɗe da rungume jikinta,
bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.



*******



Washegarin ranar da sassafe ta tashi domin shirya abubuwan da za tayi ta koma bacci tun da har yanzu
bai barta ta koma makaranta ba, hakan ya sa lokacin ta a barci da aiki take ɓata shi.



Sai da ta gyara gidan tsaf sannan ta ɗaura chips da plantain da yanzu hannunta ya faɗa sosai a sarrafa su
a yanzu.



Bayan ta gama jera abincin a dinning table kitchen ɗin ta koma domin haɗa masa coffee kafin ya dawo
daga gym, ƙarar buɗe ƙofar da ta ji ne ya sanya ta rikicewa.

Direct kitchen ɗin ya nufo

Please Login or Register in order to submit comment