You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da duba coffee maker ɗin domin haɗa coffee, ganin coffee akan kitchen
island ne ya sanya shi kallon kitchen ɗin dan ganin ta inda za ta ɓillo.
''Kina ina?, za ki fito daga bayan ƙofar nan ko sai na ba ki dirty slap wanda za ki ga kan ki a gidan ku.''



A hankali ta fito daga bayan ƙofar kanta a ƙasa ta na wasa da hannayenta, wani shegen kallo ya bita da
shi tare da faɗin ''Sau nawa ina faɗa miki ki daina haɗa min coffee a gidan nan?."

Fashewa ta yi da kuka haɗe da ɗaga hannayenta ta na ma sa alamar biyu.

''zan kwashe ki da mari idan ba ki min magana yadda na miki ba.''

Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Sau biyu yau ne na uku.''



''Alright, tun da ke naga ba kyau jin magana is like ba kya son rayuwar da babu punishment, ki zauna
kayan ki ba tare da kin shiga harkokina ba ke ba kya jin daɗi, ya'r tusai ba kwarjini, i command you ki
wuce ki gyara min ɗakina, ko da wasa kika min abin da ba shikenan ba yau ɗinnan na lahira sai ya fi ki jin
daɗi, oya!."



Ya yi maganar tare da yi mata pointing ƙofar.



Jikanta a sukwane ta nufi hanyar corridor ɗinsa idanunta na fidda hawaye, a hankali ta buɗe ƙofar ɗakin,
falo ne mai kyau sosai babu tarkace kallo ɗaya za ka masa ka ga luxury living room, it looks rich and
elegant, parlourn bai yi wani datti ba sai wani kalar zallar ƙamshin turarensa dake tashi kamar ya na cikin
ɗakin.



A hankali ta fara tattare falon duk da ba wani lalacewa ya yi ba, kawai tsabar tsafta ce irin na Hydar
amma ai babu abin da falon ya yi hakan ya sa ta kawai mopping ɗinsa ta yi sannan ta shiga master room
ɗinsa da ko ina yake tsaf tsaf, standing mirror ne kawai yake ɗan hargitse daga shi babu komai a ɗakin da
za'a gyara, dan alamu sun nuna kullum sai ya gyara ɗakinsa da kansa.



Mirror ɗin ta nufa tare da ɗaukan glass cleaner da towel ta fara goge mirror ɗin, mistakely jikinta ya gogi
turaren da aka ajiye shi ba dai-dai ba, hakan ya sa turaren faɗuwa a ƙasa tare da fashewa, wani kalar ihu
ta saki wanda a garin juyowa shima kansa madubin ya biyota ya tarwatse a ƙasa, kalar mirror ɗin nan ne
wanda ake jingina shi akan standing ɗinsa.

Wani kalar kakkarwa jikinta ya fara yi wanda hakan ya sanyata fashewa da kuka tare da tisa mirror da
turarukan agabanta ta na kallonsu.
Ta ma rasa wani kalar addu'a za ta yi, hakan nan ta tsinci kanta da faɗin ''La 'ila ha illa anta subahanaka
inni kuntu minal lil zali min.''

Haka tai ta nanatawa ta na kuka.




Ganin ta kai kusan hour ɗaya har yanzu ba ta fito ba ne ya sanya shi hawa saman a fusace tare da tura
ƙofar ɗakin, zaune ya ganta agaban mirror ɗin dake zube a ƙasa duk dakin ƙamshi ya baibaiye shi wanda
hakan ya bashi tabbacin cewa turarensa ne suka fashe.



Kallonta ya yi sosai tare da faɗin ''Gyara na ce ki yi ko ɓarna?."

Cikin shashsheƙar kuka ta ce ''Dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri, wallahi ban san ya akayi ba sharrin
shaida'n ne.''

Ta ƙarashe maganar ta na kneeling da ƙafafuwanta hannunta ta na alamun pleading da shi.''

Kallonta ya ƙara yi da kyau tare da kaudar da kan sa gefe haɗe da faɗin ''Kina da zaɓi biyu, na ɗaya, za ki
bi ta kan glasses ɗinnan ki wuce ki fita, na biyu kuma za ki frog jump za ki zagaye compound ɗin gidan
nan sau goma.''



Ƙura mai idanunta ta yi na ya'n daƙiƙu, sannan a hankali ta fara tunanin gwanda ta jewa zaɓi na biyu,
akan ta yi jinya kuma dole ne ta yi aikin gidan.



" I choose the second punishment." Ta faɗa a sanyaye.

Press ɗinsa ya buɗe tare da ɗaukan wani bulalar fata mai baki biyu, wanda ya siye shi da daɗewa.

Zaro idanunta ta yi waje ba tare da ta yi magana ba ta bi bayansa ganin har ya fice daga ɗakin.



A lokacin har sha biyu ta gota wani kalar rana ake yi mai zafin gaske.
*****



Ɓangaren Abbhi kam tun bayan da suka yi waya da Liyanar sa yake jin wani kalar farinciki, dan Rufy ji
take kamar ta mauje shi, dan sam - sam ba ya barin su su wataya a gidan sanadiyyar shaiɗaniyyar
yarinyar da yake kira favorite, ita matsalar ta ɗaya yadda doctor ya ce mahaifarta ba zai iya ɗaukan ciki
ba, shi ne babban damuwarta a yanzu.



Da sassafe ya fara shirye-shiryen zuwa gidan Liyanar saboda suje shopping ɗin da suke yi duk shekara
idan birthday ɗin waninsu ya zagayo a gidan, wani black color tissue yard ya saka wanda suka masa
mugun kyau na fitar hankali.

Cikin shigarta na Abaya Ammi ta shigo ɗakin na sa tare da ajiye ma sa break fast cikin sanyin muryarta ta
ce " Abbhinsu Happy Birthday, Allah ya ƙaro shekaru masu albarka unlimited money in your account."

Sai da ya ɗan kalleta sannan ya yi ɗan murmushi da suka tsaya a iya lips ɗinsa tare da faɗin ''Amin Iki
dear, Finally yanzu kin girma, da wannan breakfast ɗin da kika kawo da kin sha ranƙwashi, kin taɓa ganin
na sha hollandia yourghurt ba strawberry hollandia ba?." Ya yi maganar ya na kallonta sosai.



A hankali ta ce ''Ayi haƙuri Yallabai strawberry ɗin ne ya ƙare shiyasa, amma bari a mayar.''

Ta yi maganar tare da kai hannunta kan tray ɗin.

A hankali ya ce ''Just leave it I will manage.''

Murmushi ta sakar ma sa mai kyau tare da faɗin ''Your wish is my command sir, thank you Sir.''

Daga haka ta baro ɗakin.



Till date ta na matuƙar son Nabil ba ta son wani abu da zai ɓata mata ransa.



Bayan ya gama breakfast ɗin ma sai arround 12 ya fito domin zuwa gidan Liyanar, Ammin na ma sa a
dawo lafiya.



A hanyarsa na zuwa gidan Liyanar ma sai da ya biya ta Boutique ya mata siyayya sosai, daga kan palazzo
trousers da jeens skirts, da boots, da shirts babu abin da ya manta, sosai ya mata shopping, dan so yake
ya ga murmushi a fuskar mafi soyiwa a wajensa.
Ya ɗan sha wahala wajen gane gidan Liyanar saboda ko ranar da yazo shi da Ilham, da daddare suka zo
gidan, kuma Ilham ce ta yi driving ɗin motar dan zuwan bazata ya mata, kuma a time ɗin da ita yake
waya, shiyasa da ƙyar ya gane gidan.



A hankali ya fara horn a daidai luxury gate ɗin, ganin ya ɓata kusan mintuna biyar ba'a buɗe ma sa gate
ɗin ba, ganin small gate ɗin a buɗe ne ya sanya shi canza shawara haɗe da yin parking ɗin motar ta sa a
wajen gidan.



Fuskarsa ɗauke da ɗokin ganin ɗiyar ta sa ya buɗe motar haɗe da fitowa daga cikin motar hannunsa riƙe
da ledoji wanda ke cike da kayayyaki na alfarma.



Unguwar shiru take babu wani hayaniyya abin ka da unguwar masu hannu da shuni, a hankali ya ƙarasa
bakin gate ɗin tare da buɗe ƙofar a hankali.



A tsugunne take idanunta na fiddar da zallar hawaye, fararen ƙafafunta babu slippers, hannuwanta na
kame da kunnuwanta, wanda dukkan alamu sun nuna frog jump take.

Tsayawa ta yi da niyyar hutawa, hakan ya sanya shi ɗaga bulalar hannunsa, haɗe da zula ma ta shi a
gadon baya, wanda hakan ya sanyata sakin wani ƙara haɗe da wani kalar nishin wahala, ka na ta saki
kuka mai mugun cin rai.



A hankali aka turo ƙofar haɗe da shigowa cikin compound ɗin gidan, idanunsa suka ma sa mummunar
gani, ganin Liyana acikin rana, shi kuma Hydar ya na zula ma ta bulala kamar an jefo shi.



Take Abbhi ya saki ledar hannunsa wanda hakan ya jawo hankalin Liyanar da Hydar ɗin suna mai kai
duban su wajen gate ɗin.



Cikin muryarsa mai amo ya ce ''Abbhi ina wuni.''

Cikin wani kalar murya wadda ba ta fita sosai Abbhin ya ce ''Riƙe gaisuwarka ba na buƙatar ta, Liyana
kwaso kayan ki mu tafi.''
Cikin wani kalar murya wadda ba ta fita sosai ga wani kalar kuka da take ta ce ''Abbi kayi haƙuri bazan iya
rabuwa da mijina ba ko da ka d'auke ni gangar jikina ka d'auka sabida my heart and soul will be left in
this house, Just pray for me Abbhi ka faɗawa Amminah I really need her prayers.'' ta yi maganar haɗe da
goge hawayenta, ta na mai kallon Abbhin da ya matso dabb da ita.



''Are you out of your mind?, ta ya kike tunanin zan barki acikin wannan gidan a kuma halin da kike ciki,
anya ba ki fara zarewa ba?.''



Cikin murya mai sanyi ta ce ''Abbhina ni ina son mijina, ba zan iya barinsa ba, and I know what I'm doing,
Abbhi just go and seek Ammi's forgiveness, na san duk abin da ta fuskanta acikin gidanka, akwai wani da
ga danginta da suka zo suka ɗauketa?, ka tafi kawai na girbi abin da ka shuka, my hope and prayers shi
ne punishment ɗin ya tsaya a kaina kar ya taɓa min Ily, just goo and pray for me.''



Ta ƙarasa maganar tare da tashi tsaye.



Murya a sanyaye Abbhi ya ce ''Daughter please.''



''Abbhina not now, yaushe muka fara arguing?, just goo okay, I'll be fine, ai wuya ba ta kisa.''



Jiki a sanyaye Abbhin ya fice daga gidan tare da tayar da motarsa ya bar unguwar idanunsa na zubar da
wasu hawaye masu zafin gaske.



Ita ma tun fitar Abbhinata take wani kalar kuka take mai tsuma zuciyar mai sauraro.



Wani kalar bulalan da aka zula ma ta ne ya dawo da ita daga nisan kiwon muzuran kukan da take.



''Shhhhhhhh.'' ya faɗa haɗe da yi mata alaman da tayi ma sa shiru, haɗiye kuka ta yi tare da ziraro da
wasu kalar hawaye masu zafin gaske.
A hankali ya ajiye bulalar dake hannunsa a ƙasa tare da ɗaga wayarsa dake ring da sunan Amir ke ta
yawo akan screen ɗin.



''Assalamu alaikum Man.'' Amir ya faɗa ta ɗayan ɓangaren.

''Wassalamu alaykum Bud buddy.'' Hydar ya amsa ma sa.



''Man flight ɗinka is tomorrow in shaa Allah, sai ka fara shirye-shirye, amma sai ka je Lagos first thing in
the morning, because babu jirgin direct daga kano har yanzu.''



Wani kalar tsaki Hydar ya ja tare da faɗin ''Okay Buddy, buh you told me, kayi min suggest na sunan Ac
ɗin nan, i want anything to be intact before morning.''

Wani kalar dariya ya yi tare da faɗin ''Yeah..... Yeah we are still on it ai, karka ji komai kawai, yanzu ma
ina hanyar zuwa Barakat ne zan biyo ta gidanku, how's Amar.....''

Amir bai ƙarasa ba ta yi ƙit ya kashe wayar.



Wani banzan kallo ya dalla ma ta fusakarta har a sannan ba ta daina hawaye ba.



A hankali ta fara motsa baki kamar mai shirin magana, bai barta ta faɗi abin da ke ranta ba ya ce ''Za ki
tashi ki wuce ciki ko saina bubbuge miki baki?."



A hankali ta tashi jikinta ba lakka, ta na mai jan ƙafafunta da suka ma ta tsami.



Direct ɗakinta ta nufa ta na mai shiga toilet haɗe da haɗa ruwa mai zafi a jacuzzi.



Ta fi kusan 30 mins a ciki sannan ta fito daga banɗakin, goge jikinta ta soma yi tare da shafa mai, muryar
Abbhi na mata ringing bell a kunne.

Wani kukan ta fashe da shi, tare da ƙarasa shiryawarta.
***______****



Bayan Abbhin ma ya koma gida bai zame ko ina ba sai ɗakin Ammi dake yiwa Ilham kitso, da hawaye a
fuskar shi, ya ƙaraso cikin ɗakin, ganin hakan ya sa Ilham fita daga cikin ɗakin, kansa ya ɗaura akan cinyar
Ammi haɗe da fashewa da wani kalar mahaukacin kuka.

''Subhanallahi, Abbhisu what's wrong?."

Atake wani kalar zazzaɓi ya kama sa hakan ya sa shi fara kakkarwa atake, paracetamol ta na sa tare da
lulluɓe shi, wanda hakan ya sanya shi bacci a take.




Cikin shigarta na normal abaya mara kwalliya ta fito ƙafarta sanye da slippers, kanta sanye yake da
normal hula.



Dubanta ta kai tsakiyar falon da yake zaune cikin wani jeens trouser mai kyau da T- shirt white color, sai
wani soft slippers dake sanye da ƙafarsa, hannunsa riƙe da mug ɗin coffee.



Ajiye mug ɗin ya yi tare da kallonta tare da faɗin ''Muje.''



Duk da yunwar da take ji hakan bai hana ta binsa ba, backyard ya nuna ma ta, hakan ya sa ta ɗaukan
kayan aikinta ta fara gyara flowers ɗin gidan haɗe da musu ban ruwa.

Horn aka danna a ƙofar gidan hakan ya sa shi kallonta tare da faɗin ''Heys, je ki buɗe ƙofar nan, and be
fast don't keep him waiting.''



Da sauri ta nufi hanyar gate ɗin da buɗesa ya zame ma ta jiki, tare da buɗe shi da ƙyar.

Da gudu Amir ya shigo da motarsa ƙirar BMW cikin compound ɗin gidan tare da parking ɗin sa a kusa da
water fall ɗin gidan.
Saukowa ya yi cikin yadinsa na white color tare da ƙarasowa wajen da yake tsaye, rungume junansu suka
yi tare da kuma yin musabaha duk a lokaci ɗaya.



Kallon Liyana ya yi tare da faɗin ''Uwargida agidan Hydar." Murmusawa ta yi a hankali tare da faɗin '' Ina
wuni, Ya Amir.'' ''Lafiya lau, mai kike ba wa abokina ya yi wannan ƙiba haka kamar wani bons.''

Kafin ta bayar da amsar Hydar ya caɓe tare da faɗin ''Ita wannan ɗin, sai aka gaya maka wife material
ce?, ke get us something liquid dallah kika tisa mu agaba kamar sa'annin ki.''



Wani ƙwalla ne ya taho ma ta ta yi sauri ta share tare da wucewa cikin building ɗin.



Cikin wani resin tray, ta zuba musu coke haɗe da Hollandia, sai kuma wani chips ɗin leda da ta zazzage
acikin bowl.



A hankali ta fito tare da nufar cikin wani ɗan rumfar shakatawa dake cikin gidan ta na mai ajiye musu shi
akan table ɗin da yake a wajen.



''You see barb, ka ga abin da nake ma ka complaining kenan, yanzu da ta kawo wannan abun da mai za'a
sha, kee where is the glass cup?."



Cikin sassanyar muryarta ta ce ''Ya na ciki kitchen.''

''Wuce ki ɗauko, before I hose you slap.''

Cikin tattausar murya Amir ya ce ''Hydar calm down mana.''



''Amir don't tell me to calm down, ba ta iya girki ba, ba ta iya magana ba, ba ta san wannan kayan na
cikin gidane ko na fita yawo ba, babu abin da ta iya sai rawa a social media, who does that, a haka kake
cemin na koyi sonta?, babu wannan qualities ɗin mace ta gari a tattare da ita, Amir ba'a tauye ni ba a
tunanin ka?." Ya iddashe maganar a zafafe tare da tashi tsaye.
Tun da ya fara maganar hawaye ke zuba a idanunta, kanta na ƙasa ta na wasa da hannunta.



Ajiyar zuciya Amir ya sauke tare da faɗin ''Ka ga ta fifita ka akan family ɗinta for the sake of the love
that she had for you, ta ci wannan alfarmar mana Man.''



''I didn't ask her to sercrifice them to me.'' ya yi maganar ya na ɗaura hannayensa kan kujerar wurin.



Kallonta Amir ya yi tare da faɗin ''Shige ciki, zan neme ki Okay.''



Cikin muryar kuka ta ce ''Na gode Ya Amir.'' da ga haka ta fara ƙoƙarin komawa gidan.

''Malama wajen aikin ki za ki koma." Ya faɗa a gadarance, nodding kanta kawai ta yi tare da wucewa
wajen favorite flowers ɗinta, wato tulip flowers.

Wani kalar tsaki Hydar ya ja tare da ƙoƙarin barin wajen, da sauri Amir ya dawo da shi ba ya.



''Wallahi Amir idan ba ka sake ni ba zan mare ka a wajen nan........"

*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️

JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

The Noble Writers team.




**Pending Amarya 42**



What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧
Not edited 🌟💔🥹




Cikin muryar kuka ta ce ''Na gode Ya Amir.'' da ga haka ta fara ƙoƙarin komawa gidan.

''Malama wajen aikin ki za ki koma." Ya faɗa a gadarance, nodding kanta kawai ta yi tare da wucewa
wajen favorite flowers ɗinta, wato tulip flowers.

Wani kalar tsaki Hydar ya ja tare da ƙoƙarin barin wajen, da sauri Amir ya dawo da shi ba ya.



''Wallahi Amir idan ba ka sake ni ba zan mare ka a wajen nan........"




*******




Cikin muryar kuka ta ce ''Na gode Ya Amir.'' da ga haka ta fara ƙoƙarin komawa gidan.

''Malama wajen aikin ki za ki koma." Ya faɗa a gadarance, nodding kanta kawai ta yi tare da wucewa
wajen favorite flowers ɗinta, wato tulip flowers.

Wani kalar tsaki Hydar ya ja tare da ƙoƙarin barin wajen, da sauri Amir ya dawo da shi ba ya.



''Wallahi Amir idan ba ka sake ni ba zan mare ka a wajen nan."



Murmusawa Amir ya yi tare da faɗin ''dake an gaya maka Liyana ce ni sai na tsaya ai ka mareni.''

Tsaki Hydar ya ja tare da zama akan kujerar wajen tare da faɗin ''Ina jinka ka faɗi abin da yake tafe da
kai.''
Sai da ya ɗan nisa sannan ya ce ''Yanzu tsakanin ka da Allah ace Assultanah ake yiwa hakan za ka ji daɗi?,
kwata -kwata wannan rashin girki dasu waye- waye, duk ba hujja ba ce, can't you teach her how to do
it?, ko ba ka iya ba?."



''Amir kayi maganar da ta shafeka ba na son third person acikin alaƙar dake tsakanina da mata ta.''

Wani dariya Amir ya sheƙe da shi tare da faɗin ''Awwww habaa...... Su third person manya, da kan ka za
ka zo ka same ni wallahi Aliyyu, zo ka raka ni please.'' Amir ya iddashe maganar tare da ɗaukar key ɗin
motarsa daga kan table ɗin wajen.



Tsaki Hydar ya ja sannan ya ce ''Ba ka faɗa min sunan da zan saka ba kuma a ACn.''

Sai da Amir ya duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa sannan ya ce ''Idan ka raka ni sai na faɗa
maka a mota.'' daga haka ya fice daga cikin rumfar domin shiga cikin motarsa.



Wani ɗan gajeren tsaki Hydar ɗin ya ja tare da binsa cikin motar.

Ganin sun shige cikin motar ne ya sanyata saurin buɗe gate ɗin gidan haɗe da yiwa Amir waving ɗin
hannu alamun sai anjima.




Da sauri ta rufe gate ɗin tare da shigewa cikin living room ɗin, direct wajen dinning ta nufa tare da buɗe
warmers ɗin abincin, ta ga wayam babu komi, fashewa ta yi da kuka tare da ɗauko indomie ɗanya ta
soma ci ta na korawa da hollandia.




Sai da ta ƙoshi sannan ta yi sallar azahar tare da la'asar, sannan ta hau gyaran gidan da babu abin da ya
same sa.
*********




Bayan ya tashi daga baccin ta shigo cikin shigarta na koda yaushe wato classic Egyptian abaya, wanda ya
gaji da haɗuwa.



Ƙarasa shigowa ta yi ta ganshi a kwance, kamar yadda ta bar shi bayan ta ɗan watsa masa ruwa, a
hankali ta ƙaraso wajen da yake tare da fara kiciniyar ɗago shi daga kwancen da yake, dake Abbhin
ginannan jiki garesa hakan ya sa ta zubewa ajikinsa tare da ƙurawa kyakkyawar fuskarsa idanunta masu
bala'in tafiya da guntun imaninsa.



A hankali ya fara sauke idanunsa ya sauke su akan fuskar kyakkyawar black beauty ɗin matarsa, ƙarasa
buɗe shanyayyun idanunsa ya yi tareda sauke su akanta ganin gaba ɗayanta akan faffaɗan ƙirjinsa.



''Iki.'' ya furta cikin wata kaliyar murya wadda ta daɗe ba ta jisa da ita ba.



A hankali ta tashi a jikinsa tare da zama kusa da kansa ta na mai ɗora kansa akan cinyarta yadda za ta
kalli fuskar na sa sosai.



Ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin ''Naam Yaya, mai ke damun ka?."



Fashewa ya sake yi da kuka kamar wani yaro tare da faɗin ''Iki nah Ina yi DANA SANIN duk wani abin da
ya faru a shekarun baya, please and please, I'm Soo soo sorry, na amshe ki da hannu bibbiyu ki zame min
mata, ki haifa min yara maza, su cika gidan nan, wallah ina matuƙar son ki tun a baya, is just that you're
not how I expected, shi ne ya dagula al'amurran, Ni kuma na san ke nutsatsiyya ce, buh you see that lady
we called Rufaidhat is a devil, she ruin everything, wallahi ita ta ɗinga poison zuciyata na yi ta wulaƙanta
ki, dan Allah ki yafe min, Our daughter is now facing the same trauma, violence wanda ya fi wanda na
miki.''
Ya ƙarashe maganar ya na kamo kumatun ta daga kwancen da yake idanunsa na zubda ƙwalla.

Ita ma Ammin hawayen take sannan kuma cikin sassanyar muryarta ta ce ''Yaya, wallahi ni na yafe maka,
buh you know karma, bai damu da ita ɗin ya'ta bace, Yaya i loose my virginity ba da son raina ba I'm
ashamed to tell you people that I'm not a virgine and duba da yanayin zamanin mu banyi wayewa da
zance zan yi taking wani action ba, kuma is our principal,shi ne yayi min, i cried kamar babu gobe, kuma
har yau kukan nake ban daina ba, buh I later received a message that ya mutu, tun a ranar na yafe ma
sa, kuma kai ma na yafe ma ka.''

Ta ƙarashe maganar ta na fashewa da kuka.



A zabure ya sauko daga kan lallausar katifar dake ɗakin tare da kneeling da ƙafafuwansa haɗe da faɗin
''Na zubar miki da ciki har sau bakwai, na hana ki bacci dare rana kullum cikin takura miki, na hana ki
ƙarasa makarantar ki wanda har yau a grade6 (jss3) kika tsaya a school, na saka kowa ya tsane ki a
dangin mu, na sa ya'rki ta farko ta kasa sakin jiki dake, na kori dukkanin ƙawayen ki da suka zo gida na,
na mai da ke mai gadi, mai bawa flowers ruwa, mai wankin mota, mai wankin kayana da na yaran,
motsin kirki na hana ki acikin gidan nan, amma still Ikimat kika yafe min?." Ya ƙarashe maganar tare da
nuna kansa, hawaye sosai a fuskarsa.



Sassanyar murmushi ta yi haɗe da faɗin ''Yaya kenan, forgive and forget menene ma duniyar, dududu
yaushe ya rage a tasheta, let bygones be bygones, That's all, and focused on your way to achieve
something big in life, ni ban riƙe ka da komai ba Allah ya yafe mana kawai, amma ni yanzu you're free.''
ta yi maganar haɗe da murmusawa ta na mai lanƙwasar da kanta gefe.



Da sauri ya tashi haɗe da rungumeta tsam jikinsa, ya na mai shi ma ta albarka tare da faɗin ''Zo ki bani
twins yau ɗinnan.'' a take muryarta ta sauya cikin wani kalar murya ta ce ''Yaya ka manta ba nida
mahaifa?."

Ajiyar zuciya suka sauke a lokaci ɗaya tare da ƙara shi ma ta albarka.
*******




Sai misalin ƙarfe goma Amir ya sauke shi abakin gidansa, tun ya na cikin motar Amir, yake jin wani kalar
ciwo a wajajen ƙasan cikinsa, dakewa ya yi kawai, sannan ya matsawa Amir ɗin da ya juyo da shi gida,
dan wai kaisa zai yi wajen wa ta girl ɗinsa, dan Amir ya na zuba life dai-dai gwargwado.




Wani kalar mahaukacin bugu ya ke yiwa ƙofar wanda atake, sai da ta zabura, daman already ta shirya
cikin kayan baccinta waya'nda ba sa wani rufe ma ta jiki na arziƙi, da sauri ta zira slippers ɗinta tare da
buɗe ƙofar gidan, a tsaye yake hannunsa dafe da cikinsa, ya ƙarasa shigowa cikin gidan.



Da idanu ta bi shi tare da ƙarasa kulle gate ɗin da pad lock, sannan ta bi bayansa a hankali, dan kar ta yi
wani laifin.



Sauri ta yi ta shige gabansa tare da wani ɗan gudu, wani kalar ƙara ya saki ya na mai ƙara dafe cikinsa.



A take ta yi pause a wajen kamar wadda aka sawa remote, tare da waigowa ta na kallon yadda ya runtse
idanunsa dake hasken falon ya na reflecting wajen da suke.

Ɗago jajayen idanunsa ya yi tare da ƙafeta da su ya na ma ta wani kalar kallo da bai taɓa ma ta irin da
baa........




Love is blind 😌



*THE REGRET*

PENDING AMARYA CE ✍️
JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION

The Noble Writers team.




**Pending Amarya 43**



What goes around comes around ⏮️⏩



Try to be a good father to your children not a cowed 🤍 🫧 🤧



Not edited 🌟💔🥹1



****




A take ta yi pause a wajen kamar wadda aka sawa remote, tare da waigowa ta na kallon yadda ya runtse
idanunsa dake hasken falon ya na reflecting wajen da suke.

Ɗago jajayen idanunsa ya yi tare da ƙafeta da su ya na ma ta wani kalar kallo da bai taɓa ma ta ba.




Ganin hakan ya sa ta kuma arcewa aguje ba ta nufi ko ina ba sai cikin dakinta kuma a tsakiyar gadonta,
har ta so saka key a ƙofar ta tuno da kashedin sa na rannan.



Lafewa ta yi akan gadonta tare da rufe idanunta wanda atake bacci mai daɗi ya kwasheta.
*****




Ko da ya shige ɗakinsa da ƙyar ya samu ya yi wanka, tare da nufar dispenser dake ɗakinsa, ya na mai
tarar ruwan zafi acikin mug tare da buɗe fridge ɗin falonsa ya na mai matsa lemon a cikin ruwan, ji ya yi
ma kamar ƙara masa abin da yake ji ake, dan wani kalar kakkarwa jikinsa yake ma sa, a hankali ya dubi
wayarsa wanda agogon screen ɗin ya tabbatar ma sa da

Please Login or Register in order to submit comment