You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

usual muje zuwa.....




> KAR KUJI HAUSHI NA SABODA RASHIN UPDATE KOMAI A HANKALI NAKE BI BANA RUSHING😭😭



> PENDING AMARYA'S BOOK CORNER EXTRAORDINARY EVERYDAY
https://whatsapp.com/channel/0029VbAyucH7j6g0IDCpPi2V



THE REGRET

(Dana sani).




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




The Noble Writters 🦚

Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 24 _



Ita kawai so ta ke ta nunawa Abbhin ta samu strawberry ice cream da ta daɗe bata sha ba wan da ba ta
wani lura da mutanen dake ɗan cunkoso a wurin, wata matashiyyar budurwa ce ta ɗan bige ta ta yi baya
zata faɗi wanda hakan yasa ta rufe idanunta gamm, har ta sadaƙar zata faɗi sannan ta jita ajikin wani
faffaɗen ƙirji, Ƙamshin turarensa na Armani Georgia haɗe da Valentino da Baccarat duk sun cika mata
hanci wanda a hankali ta fara buɗe lumsassun idanunta tare da sauke su akanta.........''
Wani kalar waro ido ta yi tare da ɗaure fuskar ta a lokaci ɗaya, shi ma ganinta da ya yi ba ƙaramin ɓata
masa rai ya yi, sun kalli fuskar su na some seconds sannan a hankali ya sake ta ta faɗi a ƙasan wurin,
wani ɗan ƙara ta saki wanda hakan ya sa attention na wasu daga cikin mutanen ya ɗan dawo kansu.



Ficewa ya yi daga wurin gaba ɗaya, Liyana kam a hankali ta tashi tare da kakkaɓe jikinta, Sandy ce ta zo
kusa da ita tare da ce mata sannu tare da kamo hannunta.

Fincikewa ta yi tare da dalla musu harara, har ta ƙarasa wurin Abbhin.




Ta na ɗan ɗingisawa, sannan a hankali ta kamo hannunsa a cikin nata.



Juyowa ya yi tare da yin sallama da Dr Hafiz, hawayen da ya gani shaɓe shaɓe a kan kuncinta yake bi da
kallon mamaki, sannan a hankali ya ce ''Day maker what's wrong?." Cikin Wani kalar marayan murya ta
ce ''Abbhii.'' tare da fashewa da kuka dan daman a jogane take.

''Subhanallahi daughter mai aka miki?, wani acikin ku ya mata wani magana ne?." Ya faɗa tare da kallon
su Ilham.



''Mun ganta a ƙasa mu bamu san mai ya faru ba ma.'' Classy Reeda ta faɗa tare da ƙafe Liyanar da eyes.



Abbhin bai ce komai ba kawai ya ɗauke ta suka mara mai baya sannan suka ɗauki hanyar gida.

A motar ma wani kalan kuka take wanda ita kaɗai ta san na menene.



Bayan sun zo gidan ma a ɗakin da yake masu yanzu ya ajiyeta.
Kallonsa ta yi tare da faɗin ''Abbhi ba zaka min tsifan ba?.'' ''Babyn Abbhi dare ya yi kiyi bacci da sassafe
zan zo na miki tsifan sannan muje saloon ɗin da ake miki kitso kin ji?." Gyaɗa kanta ta yi kamar sokuwa,
sannan a hankali taja duvet ta rufe iya ƙafarta ta na duba wani ɗan saƙo da Sultan ya turo mata wani ɗan
video ne nasu a mota, ba zata manta ranar ba hijab ne jalibab a jikinta black color da ya amshi fatarta
_"Did you remember this day."_ shi ne abin da ya rubuta a ƙasan videon .



A hankali ta yi clicking tare da fara kallo, wani biscuits ne a hannunsa chocolate biscuits mai tsada ne
sosai, ta ce ya bata ya ƙi ba ta shi ne ta fara mai waƙan Fire boy Dml ta na faɗin _" if I leave you nah you I
go run back to, I go run back to you, e sure for you baby am going no where, your love is true I know you
will always be there, no one could love you like I do no body......_




Dariya ya yi sosai a videon sannan ya ce ''Na wash yaudara ne wallahi.''



Cikin muryarta na sakalci ta ce ''Kaiiiii."



''Toh ga shi kina faɗin No one could love me like you do, ina kika bar Mami da Abbuh?."

''Toh na ce ka yi comparing da wannan soyayyar ni dan Allah ka bani biscuits ɗin yawu na ya tsinke.''

''I No dey give.''

''Please.''

''za ki iya aure ki barni ita kuma Mami ba zata iya barina ba.''



''Kai kullum cikin negative vibes kake, why?." Ta ƙarashe maganar kamar zata yi kuka.



''That's the reality.''

''Toh ni bana son reality ɗin bani biscuits.''



Bai mata magana ba ya ci gaba da ci, a hankali ta fakaice shi ta wawushi na hannun sa ta lunƙume a baki,
a haka sukai ta kokawa, then at the end she had her first kiss a wurinsa anan kuma videon ya yi cut.
Cilli ta yi da wayan tare da fashewa da kuka, why THE HEART BREAK this is BEYOND HEART BREAK
wannan ya fi karayar zuciya.



ta raini son shi for almost 3years yanzu kuma ace wani zata aura, aranar dai Liyana kasa bacci ta yi
tunanin Sultan yaƙi barin ƙwaƙwalwarta.




Tun su Ilham na rarrashi har suka tattara suka rabu da ita.




Washegarin ranar da ta tashi fuskarta a kumbure, ta yi jaa sosai, bayan sun gama breakfast Tun da kusan
kowa na gidan dan su Ammi ma basu koma ba, arround 10 O'clock Abbhi ya zo bayan sun gaisa, ya zauna
ya na yiwa Liyanar tsifa.



Wuraren biyu kuwa ya wuce office, Liyana ita dasu Sandy ne suka tafi aka yi mata washing and setting,
sai yamma liƙis suka dawo gida, dan ba kitso zata yi ba.

Huge hair ɗinta a pake duk ana zaune a na ta hira.




Suna daga zazzunen suka ji sallama, cikin wani kalar siririyar murya, Rashanda da Classy Reeda suka ta
shi a million, suna rungume wannan ƴar matashiyyar budurwar da ta shigo, tsayinsu zai zo ɗaya da
Liyana amma tafi Liyana kawrin jiki.




''Hey cousin sisters karku karya ni manaaa.'' (shegen iyayi 😌😂).

''Babu maganar karyawa we really miss you mis chubie.'' duka suka haɗa baki wurin faɗa.
Cikin falon suka ƙarasa aka yi ta hira da ita ita ma Liyana ta ajiye girman kai aka fara hira da ita amma still
ba ta gane wacece ba. A hankali ta ce ''Sandy please can I know her more.'' a hankali Sandy ta ce ''ai
sunan mamanta kika ci gado ƴar yayan Uncle ce da ta rasu (Abbhi).




''Okay na gane Allah ya jiƙan musulmai.'' ''Ameen suka amsa gaba ɗaya.''



Washegari da sassafe suka kama hanyar zuwa legal dan acan za'a yi lallen lallen, Liyana ya yi maroon
sosai sannan ya yi kyau dukkannin su yayi kyau amma na Liya yafi.



On monday za'a fara events, da ball za'a fara a _La Sultanah_ za'a yi events ɗin REAL MADRID LOVER'S.



Tun safiyar ranar aka fara shiri. Liyana kam wani dakakken Palazzo trousers jeens ta saka sai rigan
Madrid, daga ganinsa zaka san mai mugun tsada ne all the way from Switzerland.



Sannan ta ɗaura wani black jacket mai ɗan laushi mai kama da water jacket akai an rubuta _The Bride_
sai kuma farin booth, sai kuma ta ɗauki wayarta ƙirar iphone fourteen promax.



Jersey veil ta yana tare da ɗaura wani butterfly sun shade mai mahaukacin kyau.



Dukknnin su kayan Madrid ne amma na Liyana ko a ido yafi tsada.

Lilian ma ta yi kyau sosai.

Sultana ce ta zo ƙanwar Aliyu da sauran cousins ɗin Aliyun suka nufi wurin taron arround six pm.



Suna kallon ball suna nishaɗi, sannan suma suka shigo cikin stadium ɗin suna ball suna rawa, wani waƙan
Madrid fan na wannan mawaƙin _Elikia_ waƙar _Mentality_ .
She's very happy a ranar duk wani damuwarta nemansa ta yi ta rasa, saboda Liyana ba sai na faɗa ba
gwana ce a wurin sharholiyya.



Sai ƙarfe goma suka dawo gidan, duk sun gaji wanka suka yi kawai suka kwanta bacci dan gobe shima
akwai events.




Ɓangaren Hydar kuwa tun ranar da Maminsu ta dawo ma da aka nuna mai lefen bai wani react ba kawai
ya dai yi murmushi sannan ya bar living room ɗin dake jibge da boxes ɗin.



Ya wani cire damuwa a ranshi ya sa business a gaba.

Da yanzu ma ya na China Abbuh ne ya hana sa.



Bayan an kai lefen ma sai da aka cajesa kuɗin ɗinki two million sannan hankalinsu ya kwanta.

Sam babu wanda ya damu da shi ba ga dangin Mami ba ba ga dangin Abbuhn ba.



Kullum ya kanje ya sha yawonsa kafin ya dawo gida, ranar ma wani tsautsayi ya sa shi ya ji yana sha'awar
zuwa shawarma zone yaci shawarma with ice cream, ranar kam sai da ya haɗu da bad luck ɗinsa
acewarsa Liyana is a bad luck to him.



Lamarin Amir kam wurin zolayarsa ƙara gaba take yi, kullum cikin maganar shape ɗin Liyana yake shi
kam abin na mugun ɓata masa rai ba kaɗan ba.



Ranar Monday arround 11pm Sultana ta shigo ɗakinsa bayan sun dawo daga La Sultanah ta ce ''Yaya
sannu da hutawa, wallahi your wife is very beautiful, Kai ka ganta kuwa santaleliyya wallahi ka iya zaɓe,
ta yaya ma ka ganta har ka gayawa su Abbuh, abeg gist me, ni is like na taɓa ganin ta sau ɗaya a school.''
haka tai ta surutu.

Bai mata magana ba ya zaro slippers ɗin ƙafarsa sannan ya saita bakinta ji kake buff.
''Wayyo Yaya daga magana.''

Tashi ya yi tare da ajiye laptop ɗinsa ya sakar mata ranƙwashi, ''wayyo kaina.'' wani ya ƙara sakar mata,
sannan ya ce ''Duk magana ɗaya idan kika ƙara sai kin gane kuren ki.''

''Am sorry Yaya.'' yatsunsa na tsakiyya da na ƙarshe ya haɗe su tare da ɓalle mata baki sannan ya ce
''Not even sorry, motsi kika yi yau sai kinga ribar gulma. ''Yaya buh k........'' ɓalle mata baki ya sake yi.

Sultana kan data ga abin na zalunci ne yau da gudu ta tattara wandonta ta bar ɗakin.



Ajiyar zuciya ya sauke sannan a hankali ya cigaba da nazarin laptop ɗin da ke gabansa.

Amma tunanin yarinyar ya ƙi barin brain ɗinsa, wani iska mai zafi ta furzar haɗe da ajiye laptop ɗin yana
focusing akan chatting ɗinsa da Amir........




> GUYS SALO YA CANZA KUMA SAI KU CANZA ZAMA 🤭🚼



THE REGRET

(Dana sani).




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
The Noble Writters 🦚

Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 25_



Ajiyar zuciya ya sauke sannan a hankali ya cigaba da nazarin laptop ɗin da ke gabansa.

Amma tunanin yarinyar ya ƙi barin brain ɗinsa, wani iska mai zafi ta furzar haɗe da ajiye laptop ɗin yana
focusing akan chatting ɗinsa da Amir........




Washegarin ranar za'a yi Lifaya day wato shuwa Arabi day, tun safe aka fara shiri, abinci kala kala babu
wanda zaka nema ka rasa abin dai sai wanda ya gani.



Shima dai a Leena event center za'a yi, dan Jiddah ne ya ce baya son a tsawwalawa bidi'a da yawa
albarka kawai ake nema.



Da yamma misalin ƙarfe shida aka fara harraman zuwa can wurin occasion ɗin.



Liyana ce cikin wani kalan dakakken lifaya da kuɗinsa kaɗai sai ya cire mutum daga talauci na wucin gadi.



Lifayar fari ne ƙal sai stones golden color da aka yi mai wani kalar classic design, sai wani kalar gucci hills
da ya ƙarawa shigarta kyau, sai gashinta da aka yi mata kitson gaba ƙato gudan ɗaya, tun kafin ka iso
kusa da ita zaka ji sanyayyar ƙamshin turaren nata ya fara maka marhaban.
A hankali wasu tsofi guda biyu suka kamata suka saka ta acikin motar da na musamman Abbhi ya siyo
dan kai ta wurin events ɗin nata.



In ban da rawan Al ragaba (rawan wuya)babu abin da suke yi suna yi suna cilli da hannu, ga kuma
turaren wuta a ɗayan hannun ya na tashi a hall ɗin.



Ko ina waƙan Roua Na'eem ke ta shi waƙar nan nata mai taken _Habibi_.



Anci an sha sannan aka dawo gida, shi ma duk jikanta a gajiye, da daddare misalin ƙarfe 11, yunwa ke
nuƙurƙusan cikinta hakan ya bata daman fitowa kitchen dan samawa cikinta abin da zata ci.



Bayan ta shiga kitchen ɗin ma Pepe soup ɗin kan rago ta gani an ɗan buɗe shi ya sha iska Dan kar ya
lalace, shi ta ɗiba tare da bread ɗin da ta gani saman toaster, ta shigo ɗakin ta na ci idanunta a lumshe
saboda bacci take ji sosai.



Da haka har ta gama ci ta wuce ta kwanta a tsakiyar su Unaisa (mis chubie).



Washegari ma da sassafe, mutanen gidan suka fara hada -hada amma ita Liyana sai da ta korawa kowa
jawabin kar wanda ya tashe ta.



Da yamma aka yi mother's day, Liyana cikin wani dakakken Abaya duk ya ji stones masu kyau sosai,
mother's day ɗin dai a compound ɗin gidan akayi inda aka kira wannan mawaƙin boys kiddo ya waƙe
Ammi da wannan waƙar na shi na Mama.



Haka Liyana da Ilham suka rungume Ammi suna ta kuka har aka tashi daga taron.



Da daddare ma hira suka ɗinga yi a tsakanin su, wanda Liyana babu zato babu tsammani ta fashe da
kukan da bata san dalilin sa ba.
Su Classy Reeda da Sandy Rash da Mis chubie har da Lily suka yi ta bata baki har tayi shiru bacci ya
kwashe ta.

Ko da Abbhi ya shigo da ya tambayi Liyanar cewa aka yi bacci take yi.



Bai sa an tashe ta ba ya wuce ya koma Hotoro.



Washegarin ranar aka yi Father's day, idan kaga Abbhi da Liyana sai ka rantse shi ne zai aureta, baƙin
yard ya saka itama wani baƙin material da aka yi mata ɗinkin corset gown, da ya bi shape ɗinta ya lafe.




She looks hot sosai, haka suka yi ta rawa da ƙawayenta Abbhi na mata liƙi.

Ta yiwa Abbhi baitoci sosai sannan aka tashi daga event ɗin Abbhi ya maida ta gida sannan shima ya
koma Hotoro.



Washegarin ranar aka yi sisters day duk sunyi kyau sosai cikin shigar su na abaya's, anyi games da dama.




Rana bata ƙarya yau ne kamu wanda aka gayyaci manya -manyan malaman Musulunci, irinsu sheik
Tijjani Guruntum da ma sauran malamai irinsu sheik Gadon ƙaya.




Anyi wa Liyana wa'azi sosai akan haƙƙoƙin miji da ma sauransu, jikinta duk a sanyaye yake ta sha kuka
bayan taro ya watse sosai, rayuwarta kawai take tunawa bayan auren nan ko ya zata kasance? Ko ya
mijinta yake?. Wani kukan ta fashe da shi mai tsuma zuciya.



Tun jiya ma kiran Sultan take amma shegen yaƙi ɗagawa. Tsaki taja haɗe da yaye gadon data kwanta ta
shige toilet haɗe da yin wanka da ruwan turarenta dan bacci take ji.
Ko ina kuma a social media maganar bikinta ake har jira ake aga ta hau online, shi yasa ma wayar ajiyesa
tayi a gefe data ga zai takurata, dan ƴan comment section har izgili suke mata, har yau basu ga mijin
Aunty Carrier ba. Dan a cikin followers ɗinta akwai masu ce mata Aunty Carrier. (Ko mai sa oho).



Rana bata ƙarya sai dai Uwar ɗiya taji kunya yau Sunday ranar da dumbum jama'a ke ƙoƙarin shaida
wannan babban rana ga Fatima Nabil Aliyu Ibrahim Shuwa Arabi da kuma Aliyu Ahmad Qassim Kyari.

Ƙarfe goma dai-dai aka ɗaura aurensu akan Sadaki Naira Dubu ɗari biyar lakadan ba ajalan ba.



A take street ɗin ya ɗauki busawar Algaita, da kuma hayaniyar jama'a.

Amir ne kaɗai ke ta washe baki kamar shine angon.



Bayan labarin auren ma yaje masa ji ya ɗinga yi tamkar ya zunduma ihu.



Dan Amir yasa yaje ya masa leƙe, bayan auren kam, Sultan da Amir ne a parlourn Hydar suna ta kallon
yadda yake ta huci kamar wani zaki.



Amir ne ya yi gyaran murya tare da faɗin ''dama tashi kayi ka shirya da ya fiye maka wannan fake
emotions ɗin naka dan class mates ɗinmu babu wanda ban gayyato ba.''

Sultan ya amshe da faɗin ''Ko kai ma ka faɗa Amir, da ni ne ake min maganar anyi min mata ajiye wadda
muke soyayya da ita zan yi a gefe in amsa hannu bibbiyu daga ƙarshe na ƙaro ta ana biyu.''



''Shege.'' Amir ya faɗa da ɗan barkwanci.



Bai ma kallesu ba balle su saka ran amsa ya cigaba da danna wayarsa.




Ɓangaren Amarya Liyana kuwa tun da taji an ɗaura zuciyarta ke duka uku³ ta rasa yadda zata yi.
Kuka zata yi ko dariya bata sani ba.

Wani mahaukacin shadda da ya lalace da ɗinki ta saka wanda alamun kayan ma kaɗai kasan ba ƙaramin
shadda bane sannan ba ƙaramin tailor ne ya ɗinka sa ba.



Ɗinkin yafi kama da na ƙasar Gambia dan aɗinke yake a cikin lefenta.



Shaddar milk color ne sai aka yi design da coffee color thread, sai aka yi mai ruwan stones, sai kuma
wani coffee heels dan sam bata sa ka zani ba kamar sauran amare.




Duk da ba kwalliya tayi ba, amma wannan hasken na amare ya karaɗe fuskarta, duk ɗakinta ayarin
cousins ne and all of them are very classy.




Rashanda da Classy Reeda da Unaisa da Ilham sun saka kaya kala ɗaya har da Lily.



Farinciki a wurin Ammi baya misaltuwa, ta aurar da headache ɗinta a rayuwa.

Rufaidhat kam ranta a ɓace yake yadda ta ga kowa ya yi banza da ita.

Kamar mayu sai da suka je shan ice cream ɗin, dan Liyana ma bata ci komai ba sai ice cream ɗin data
sha.



Misalin ƙarfe shida na yamma Aka yi mata wanka da ruwan lalle sai da aka ƙara dafa ta, sannan aka sa
mata wani lifaya purple color da ratsin white color aka saka mata sai da aka turara mata jiki gaba ɗaya
sannan aka kaita wurin Jiddah ya mata Nasiha, ita ma Neneh aka kai ta ta mata tare da faɗin ''Ni dai
Fatima aure ne an riga an miki rashin kunya, da waƙe -waƙe sai ki ajiye tun da dai Davido ba ƙanin ubanki
ba ne ba, in kunne ya ji jiki ya tsira daga azabar Allah, akai ta wurin Salamatu ta ja mata Aya.''



Sai da Liyana ta ɗage abin lifayar ta dallawa Nenehn harara, wadda ta cigaba da surutun ta.
Daman ta saba kiran Ammi da Salamatuh that's why kawai wurin Ammi aka kai Liyanar, ita dai Addu'a ta
mata tare da mata fatan samun daidaito a rayuwarta ba ki ɗaya.




Daga haka aka kaita wurin Abbhi.

Rungume shi ta yi ta na kuka shima bai san lokacin da ya fashe da kukan ba dan har ga Allah ba zai iya
zama bai ga ɗiyarsa ba ace har sai wani ya bata izni yanzu akansa.



''Don't worry dear every friday zan ɗinga zuwa ganin ki okay?." Gyaɗa kanta kawai ta yi sannan aka wuce
da ita gidan su Mami sai da suka samu tarba mai kyau, itama Mamin ta mata nasiha sannan aka ɗauki
hanyar sharaɗa da ita dan acan gidan Hydar ɗin yake.



Duk ƙawayenta da kuma ƴan uwanta na jiki sai bayan one week zasu koma gidan Neneh dan al'adar su
ce hakan, wanda a yaren shuwa Arabi muke kiransa da Sabbayats.



Ko kaɗan bata daina kukan ba haka tai ta kukanta su Reeda da Unaisa na rarrashinta.



A haka har ta daina kukan.



Daga ƙarshe ma dai ta ware suka cigaba da hira tun suna jiran angwaye har suka kwanta bacci.

A haka har kwanaki bakwan da zasu yi ya ƙare.

Ranar da zasu ta fi babu kalar magiyyar da Liyana bata musu ba har diamond ɗaya ta ce zata basu da
dubu ɗari biyar su ƙara sati ɗaya amma suka ce su basu san zancen ba gida zasu koma.

Itama Ilham ta ce zasu koma makaranta Lily kam ita ma preparations tace zata koma ga fara dan next
week zasu koma.



Ta sha kuka sosai ahaka har suka gama shiri suka kama hanya suka ɓacewa ganinta.
Gidan wani kalar faɗi ne da shi na ban mamaki, dan gidane babba sosai, readers gidan Liyana sai a novel
babu shi a reality, because ya gama haɗuwa komai na gidan looks luxurious.



Ga marble tiles kaca -kaca, gidan dai soo Ma sha Allah.



Haka ta yi ta rayuwarta ita kaɗai ta girka abin da take so taci.

Shi ma Abbhi yayi ƙokari sosai wurin haɗa mata gara domin har da Hollandia strawberry ya sa mata her
favorite drink.



Kullum tana online ko Sultan ya mata magana bata basa amsa dan bata canza layinta ba.




Monday Morning 🫂




Yau ta kasance Monday yau kuma za'a koma makaranta tun safe ta shirya cikin shigarta na wani black
abaya mai mugun kyau da tsada sannan ta sanya Gucci flat shoes ɗinta black color haɗe da saka wani
ziconic leg chain mai mugun ƙyalli da stones ajiki green and red.



Ta yi mugun kyau sosai sam sam babu wani locality ajikin Liyana komai na ta mai kyau ne.




A hankali ta sanya hannu tare da ɗaukan one in town wayarta, da ta fara amfani da shi last week her
pink iPhone , sai da ta gama pictures sannan ta shiga dakakkiyar motarta mai numfashi da Abbhi ya siya
mata na gudumowar bikinta.
A hankali ta nufi wurin jeep ɗin nata da yake Black color mai ƙirar G_Box, ta masa wuta tare da barin
cikin gidan gaba ɗaya.



Wasa wasa har ta kai one month a gidan bata taɓa ganin wanda ta aura ba

Zata ji fitarsa da dawowarsa duk a kunnenta amma basu taɓa clashing ba ko da wasa.

Yau dai basu da lectures, wani kalar yunwa ke nuƙurƙusan cikinta dan haka ta fito dan nemawa kanta
abin da zata sa ma cikin ta.

Misalin ƙarfe biyu ne na rana, wani palazzo trousers ne mai kyau da kuma faɗi ajikin ta sai crop top
black color mai ɓulallen ƙirji.



Ko da ta shiga kitchen tea ta haɗa tare da futowa living room ɗin, ganin waƴanda ke falon ba zato babu
tsammani mug ɗin tea ɗin da yake hannunta ya faɗi a ƙasa ji kake tassss...........




Let's meet tomorrow in page 26 muji yadda zata kaya.



Pending Amarya ce ✍️



THE REGRET

(Dana sani).




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪
The Noble Writters 🦚

Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 26_



Ko da ta shiga kitchen tea ta haɗa tare da futowa living room ɗin, ganin waƴanda ke falon ba zato babu
tsammani mug ɗin tea ɗin da yake hannunta ya faɗi a ƙasa ji kake tassss...........




Cikin muryarta mai sanyi da kuma nuna tsantsar farincikin da take ciki ta ce " Ilham!, Farida, Rashidat,."
ai da gudu ta ƙarasa wurinsu tare da rungumesu gaba ɗaya, tare da fashewa da kuka.



Rungumeta suka yi tare da sakin ta Reeda ta ce " ashe za ki iya missing namu har haka."

Tsaki Liyana taja tare da faɗin kaɗaici ne kawai buh na rasa wa zan yi missing sai ku? Is impossible ai, dan
Allah ku tashi ku dafa min abinci am starving." Rashanda ce ta dalla mata harara tare da faɗin "Ily kaɗai
kika girma anan ba mu ba."



"Ni na ce ke ne?."

"Kin ma isa."
Reeda dake zaune cikin wani paper less mai mugun kyau ce ta ce "zaku fara ko?."



A haka suka yi ta hira har sai yamma liƙis sannan suka kama hanyar zuwa gidan Neneh shima da ƙyar
sannan ta barsu suka tafi.



Ɓangaren Hydar kam bai wani damu da ya ga what soo called wife ɗin da ake kirarin an masa ba shi dai
kawai yana rayuwarsa, daga gidan Mami sai gidansu Amir da kullum cikin tsokanar sa yake da yayi fresh
menene sirrin?.



Baya tanka masa balle ya sa ran answer.




Almost a month da bikinsu buh he didn't even bother ya ga wacece ko chanyar corridor ɗinta baya bi
balle idonsa ya kai ƙofar da yake sa ran nata ne.




Yau tun safe ta shirya cikin wani up and down masu kyau sai tayi ɗaurinta na matar minister sannan ta
saka gucci heels da kuma bag sai wani passion eye wear masu kyau, yau data yi waya da Neneh tace
mata zata aiko mata Salimah tun da ba Salimah kaɗai bace ba ƴar aikin Nenehn.

Hollandia strawberry kawai ta kwankwaɗe tare da fita daga cikin flat ɗin, ta shige mota haɗe da zuge
glasses ɗin motar ƙasa dan zata yiwa mai guard magana.



Bayan ta shige Jeep ɗin nata haɗe da sanya seat belt tare da yiwa motar key, kafin ta ƙaraso ma har ya
buɗe gate ɗin.



Parker motar nata ta yi tare da yiwa mai guard ɗin magana, cikin muryarta mai sanyi ta ce " Malam mai
aiki zata zo da anjima, ka buɗe mata gate, am I clear?, and......."
Bata kai ga ƙarasawa ba wani mota ƙirar Lexus RX ta kutso kai saura kaɗan motar ta shafi ta nata.



Bayan motar ta wuce sai da ta futo da kanta waje ta dallawa motar harara haɗe da kallon mai gadi tace "
da maƙota a gidan nan ne?." "Hajiya ke kaɗai ce ai da Alhaji a gidan nan, kuma ina fatan har abada daga
ke ba ƙari."



" Idan ya ƙaro sai ka fitar da ita ai, kaji bayanin dana maka?."

" Eh hajiya Allah ya bada sa'a."



" Tun da ance maka gasar kyau zanje ai."

" Allah ya ba ki haƙuri."

" Haƙuri kaya ne." Daga haka taja motar zuwa school.



Ko bayan ya dawo daga gym daya shigo gidan, idanunsa suka gane masa yarinyar da take cikin motar he
was shocked to see her for the fourth time, buh

Please Login or Register in order to submit comment