You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*🫆🐾🦚



_Our strength lies in Dedication_🤍




_ Pending Amarya 32_
Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta wanda hakan yayi dai - dai da fitowar Hydar tare da
Abbuh saboda bayan yaje office ɗin ya dawo gidan rasuwar da rana saboda mayar da Abbuh wurin
aiki.......




Wani kalar kallo ya watsa mata sannan ya kalli Abbuhn da bai ma lura da wa'yanda ke tsaye ba suka
wuce cikin motar nasa.



Hararan gefen ido ta wurga masa sannan ta cigaba da magana da Sultan ɗin dake ta faman yi mata
magana, amma tasa kanta gefe guda tana wasa da zara-zaran fingers ɗinta.



''Ka gama?, nace ka gama?, ban hanya na wuce.''

Daga haka ta bi ta gefen sa haɗe da shigewa cikin jeep ɗinta.



Acikin motar ma kasa driving ta yi ta rasa mai ke mata daɗi kawai Unaisah ta bawa car key ɗin domin
taja motar dan a halin yanzu babu abin da take tunawa kalar rayuwar ta da Sultan and she ended up
marrying his elder brother.



''Ya subhanallah.'' ta faɗa a fili.
Sannan ta jinginar da kanta a jikin kujerar motar, kawai tunanin yadda suke soyayya take, the kisses, the
hugs, yanzu ai da kunya ta buɗi ido ta ganshi a matsayin ƙanin wanda take aure.




*NOTE.*

_Ƴan mata masu sakarwa samari ragamar jikinsu ku bi a hankali because baku san ya ƙaddara zata
kasance da ku ba._




Za ta ji nauyin zuwa gidan surikanta ma bama Sultan ɗin kaɗai ba, Allah yasa ma surutu irin na Sultan ɗin
babu wanda ya faɗawa kalar haukan da take yi da shi.



Har Unaisah ta iso gidan bata sani ba sai da ta yi horn, sannan horn ɗin ya fargar da ita daga nisan
tunanin da ta lula.



Ko ina na gidan tsaff Salima ta gama gyara ko ina dan yanzu har wajen 4 ta gauta.

Ƙamshin turare ya gauraye ko ina ga wani sanyi da ɗakin ya ɗauka.



Salimah na zaune cikin falon jikinta sanye da hijaby tana wayarta hankali kwance.

Shigowar Liyanar ne ya sa ta katse wayar tare da faɗin ''Aunty Liya sannu da zuwa.''



''Yawwa, mai kika girka?."



''Dambun jollof ne.''



''An bar miki kayan ki, dafa mana pasta kafin mu fito please.''
''Toh Aunty.''



Daga haka suka bar falon ita kuma Salimah ta shiga kitchen domin dafa musu pasta ɗin.



Shigarsu saman ma komai tsaf - tsaf da shi sai ƙamshi yake mai bada nutsuwa.



Sai a lokacin ta kunna wayarta haɗe da faɗawa Lily rasuwar da aka yi musu.



''Hello lily.''



''Bae what's app nah.''



''Wallahi normal.''



''Bae tun safe ake cigiyar ki a online, wai first in history ƴar Nabil tayi offline for 2 hours.''



''Wallahi My Grandpa just japa recent.''



''Jehooovaaaa, how comes wetin come happen?."

''Person no go die again?."



''Dalla bae am surprised ne ai ta ya Jiddah zai mutu haka?."



''Thunder go fire you, bastard."
''Ahh bae mai na yi kuma?."



''Ba Jiddah ba fa papi.''



sun daɗe suna hirar sannan ta katse wayar.



Kaya kusan kala goma ta ɗiba da hijjabai biyar sai slippers biyu, sai laptop da kuma charger da brush da
soson wanka da sabulanta da kuma mayukanta na jiki.



''Wannan kayan fa hajiyata.'' Unaisah ta faɗa tana ƙafe Liyanar da eyes.



''Na gidan rasuwa ne mana.''



A daidai nan Salimah ta yi sallama haɗe da shigo da pasta ɗin daya ci crab fish da gasasshen kaji, sai
ƙamshi yake.



''Ga abincin nan.''

''Godiya muke hajja Salimah.'' Liyanar ta faɗa tare da janyo plate ɗin.



Salimah bata ce komai ba ta fita daga ɗakin.

Abincin suke ci hankali kwance suna hirar su gwanin burgewa.



A haka har suka gama cin abincin sannan ta shiga toilet ta yi wanka haɗe da shiryawa cikin simple dress
mara hayaniya.



Ta yi kyau sosai ga yamma ta yi dan an fara kiran magriba.
Key ɗin ta ɗauka haɗe da trolly ɗinta sannan ta fito parlourn Salima na zaune ta na kallo.



''Mai kike yi tun ɗazu haka a zaune ba ki shirya ba?."

''Aw!, wai Aunty da ni za ki tafi.''



''Malama ba zan tsaya dogon turanci ba, taho mu tafi.''

''Toh.''



Daga haka Salimah ta shiga ɗakin ta in less than two minutes ta fito da wani ɗan kit.



daga haka suka fita daga falon tare da nufar motar Liyanar.

Wani kalar gudu take shararawa wanda ba'a jima ba suka iso ƙofar gidansu Ammin dai-dai kiran sallar
isha.



Gidan kowa dai shiru babu mai tankawa kowa Unaisah da Salimah ne suka kamo mata trolly ɗinta suka
kawo mata shi har cikin ɗakin.



Sannan ita ma ta mara musu baya.



Yusrah ce zaune kan gadon dake ɗakin Sandy Rash da Classy Reeda na zaune kusa da ita duk suna hira
sama- sama.

Shigowar Unaisah da Liyana ne ya sa su farinciki haɗe da baƙin ciki duk a lokaci ɗaya.



Sannan kuma suka fara hira.



ILY ce ta ƙaraso cikin ɗakin haɗe da ajiyewa kowa abincin sa sannan kuma ta zauna tare da ƙurawa
Liyana ido.
''Aunty Liya ko ki neme ni.''



''Sannu Ikimat, ko nace sannu Nabil.''

Matsowa ta yi kusa da Liyanar ta ɗan dake ta sau uku a ƙirji tare da faɗin ''Blood.''



''Sai dai period ba blood ba.''



''Ke dai da bak'ar magana, ance ki je ki ɗauki abincin ki.''



''Wa ya dafa?.

''Mama Fatuh ce.''



''Ill!, never!."

''Mai kike nufi?."



''Ba zan ci ba wallahi.''



Yusrah da tun lokacin da Liya ta shigo take jin wani kalar baƙin ciki na lulluɓe ta ne ta ce ''za ki ci kaza
kazanki.''



''Toh mai kike ci na baka ba falling down.'' Liya ta faɗa haɗe da murmusawa.



''Uwarki za'a kwaɗan ta min naci.''
''Ahh wallahi kin yi kala da mayu daman, ni nafi ƙarfin na yi dake sai dai nayi da uwarki, dan haka ki aiko
min ita da ita zan yi.''



''Bara uba........''




To be countinue tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*
(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️




*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



This page is dedicated to UNAISAH (Miss chubie)🌕



Barka da jummah my lovely fans 👥🫂



•°•°• Pending Amarya ce 33 •°•°•




''Ahh wallahi kin yi kala da mayu daman, ni nafi ƙarfin na yi dake sai dai nayi da uwarki, dan haka ki aiko
min ita da ita zan yi.''
"Bara uba......."




''Bara uba, dani kike?."

''Ba ki ji mai nace ba da uwarki nake.''



Kafin Yusrah ta ƙara wani maganar su Rashanda da Unaisah suka fara bada haƙuri da haka dai kowa ya yi
shiru.

Sai tsaki dake tashi a ɗakin different types of sounds.



Hayaniyya ke ta tashi a tsakar gidan wanda ke nuna alamun wani ne ya ƙara zuwa a cikin dangin.



Kowa ya shirya cikin kayan baccinsa, banda Liya kaɗai dake zaune ta na aikin chatting da wata ƴar class
ɗinsu ta secondary school da suka haɗu ta IG (Instagram).



Sai da ta ga 11 ta ɗan gauta sannan ta kama cire kayanta haɗe da ɗaura towel ɗinta domin ta ɗan watsa
ruwa.



Cikin ƙanƙanin lokaci ta fito ɗaure da towel haɗe da goge jikinta tare da sanya kayan baccinta, haɗe
shafe jikinta da turarenta na Almiski wanda ta saba shafawa.




Ko da ta kai dubanta kan gadon ma har kowa ya yi occupying wurin kwanciyyar, duk sun fara bacci
amma ban da Unaisah da take latsa laptop ɗinta ta na haɗa wani rahoto da zata bayar a gobe.
''Toh ni à ina zan kwanta?." Ta faɗi hakan tare da kai dubanta zuwa wurin Yusrah data baje a kan gadon.



Unaisah ce ta gyara zaman glasses ɗinta sannan ta kalli Liyanar haɗe da faɗin ''Ki ce musu su gyara
kwanciyyarsu because ni ina gamawa a ƙasa zan kwanta ke kuma naga you're not a fan of kwanciyar
ƙasa.''



''Ba zan iya kwanciyya a ƙasa ba just tell this girl to shift for me, duk ta cinye wurin.''



''Ni fa Liya karki ce za ki yi faɗa da daddaren nan idan ma falo ne kije ki kwanta a coach ɗin palo ko ki kira
mijinki ya zo ya ɗauke ki ki koma gidanki.''



''Babu wanda zan kira a ɗakin nan zan kwana no matter what wallahi.''



''Ai shikenan.'' daga haka ta cigaba da danna laptop ɗinta.



Fincike filon da Yusrar ke kwance ta yi wanda ba shiri ta tashi daga barcin, wanda hakan ya saka faɗa a
tsakaninsu, Neneh ce ta shigo cikin ɗakin tare da mutan gidan, su Rashidat da Faridat duk sun tashi daga
barcin, Ilham kuma daman a wurin su Ammi ta kwanta duk tare suke da su Nenehn.




''Mai ya faru haka da ba zaku bari muyi bacci ba shima Umaru ya samu salama a inda yake kwance eh?."



Yusrah ce ta doka wani ɗan banzan tsaki haɗe da hararar Nenehn.



''Ai ba dake nake ba cangali tsone, da jiƙata nake.''

Rashidat ce ta yi wiƙi - wiƙi da ido tana kallon Nenehn sannan kuma a hankali ta buɗi baki ta ce ''Neneh
bacci muke hayaniyar su ce ta tashe mu.''
''Duk yadda aka yi Ikimat kin ci zabi da cikin ƴar nan, taho muje can ɗakin Maimun ki kwanta acan ki
ƙyale wannan kayan wankin mana.''




Liyana ce ta kalli Nenehn haɗe da faɗin ''Wallahi Neneh babu inda zani, kuce mata ta matsa min na
kwanta tun da ba na ubanta bane.''



Yusrah ce takalli mutanen ɗakin kafin kuma ta murmusa tare da faɗin ''A gaban ku dai take zagina kuna ji
kuna gani ko?."



Ilham da tun ɗazu abin ke sosa mata rai ne ta fincike Liyanar daga ɗakin.

''Ily ki cika ni kafin na wanka miki mari.''



Ko kallonta Ily ba ta yi ba ta shigar da ita ɗakin nasu, sannan a hankali ta fara magana ''Wai ke ba za ki
nutsu ba fisabilillahi, kullum akan ki Ammi ke kukawa, ki tsaya mana ki duba lamarin nan, ke idan ta miki
magana ko ta tsokane ki ba za ki iya over looking ba kawai ki barta, dole sai kin shiga harkokin ta?, haka
jiya da yamma Sultan na waje kuka yi ta dambe haka maƙota ke ta yayatawa, just ki barta please.''



Ta ƙarashe maganar haɗe da miƙa mata ruwan sanyi domin ta sha.



Nannauyen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce ''Naji amma wallahi aka min sai na rama.''




Daga haka suka kwanta haɗe da yin bacci.



Washegari da safe ma ko kallonta bata yi ba kuma Mama Fatuhn ce ke raba abincin safen fankaso da
kunu, bata bi kan abincin ba ta sa Salimah komawa can gidan ta yo mata girki ita da su Unaisah suka ci
kafin ta tafi aiki.
Ko ina na gidan shiru dan Liya baccinta ta ɗinga shararawa.



A haka rayuwa ta cigaba kewar Alhaji Umaru na yaɗewa a zukatan su yayin da yau ake sadakar bakwai
na marigayin.



Tun safiyar yau Jiddah da Abbhi ke zuwa gidan marayu da talakawa marasa ƙarfi ake ta rarraba musu
kayan abinci haɗe da tallafawa masallatai.

Gidan ruwa da ake siyarwa da masu ga-ruwa ruwa sai da suka rarraba musu kuɗi sosai domin al'ummar
musulmi su amfana a kuma raba musu shi kyauta.



Sosai suka kashe kuɗi akan sadakar bakwai ɗin yau.




Mama Maimu kuwa a hospital results sun nuna da cewa hawan jininta ne ya yi mugun tashi, domin sai
yau ta farfaɗo.

Tun da ta farfaɗo ɗinma kuka kawai take Neneh na bata haƙuri, amma sai ya ɗan ƙara warware wa zata
dawo gidan.




Mr Ali namu kuwa shima wurin bada nashi gudunmawa ba'a barshi baya ba dan sosai ya turawa Jiddah
kuɗi a account ɗinsa.



Ga kullum Mami sai ta takurasa akan ya kawo mata Liyanar yanzu almost wata uku da auren basu zo ba
in banda shi da yake sintiri, idan Sultana ta ce za taje kuma sai ya ce zai karya ta idan ta taka zuwa gidan.



Yau dai kam su Liyana sai ƙasa ƙasa ake da kai dan su Mami da Abbuh zasu zo gaisuwa har ma da Hydar
ɗin.
Ita wani kalar kunya take har addu'a take Allah ya sa kar azo da Sultan.




Ammi ce keta bawa Salimah da Ily order su ɗan dafa abinci saboda baƙin da za'a ɗan yi.

A hakan dai har suka gama girkin.

Ƙarfe sha biyu dai-dai su Mami da Abbuh da Hydar da Assultanah suka hallaro.



Gidan da ɗan hayaniya amma ba sosai ba.




A haka har suka shigo cikin gidan, palon Umaru ɗin da ake tarban baƙi.



Basu wani jima ba Ammi da Neneh suka shigo haɗe da gaisawa dasu Mamin, shi dai tun da ya kalli Ammi
sau ɗaya ya siddar da kansa a ƙasa, bai yarda ya sake ɗagowa ba.

Ita ma ta lura da hakan yasa suna gama gaisawa ta ce musu zata aiko musu Liyanar sannan ta yi
ficewarta.




Neneh kam in banda bada labarin rasuwar Umaru ba abin da take yi.



A haka har ta shigo cikin parlourn cikin siririyar muryarta mai kama da busawar sarewa tare da yin
sallama wanda ya amsa ilahirin ɗakin.



''Yawwa ƴar halal ta ƙi ambato.''

Neneh ta faɗa haɗe da kallon Liyanar.
Aƙasa ta durƙusa haɗe da gaida su Mami da Abbuh ɗin.

Amsawa suka yi haɗe da shi mata Albarka sannan suka yi mata ya haƙuri.



babu abin da suka ci a abin da aka kawo musu.



Bayan shiru ya ɗan ratsa falon, kanta aƙasa tana wasa da diamond ring ɗin hannunta, shikam Hydar ko
kallonta bai yi ba ya na ta operating wayarsa ne kawai.




Cikin sanyin murya Sultanah ta ce ''Aunty you're soo beautiful Ma shaa Allah.''

''Thanks little.'' Liyana ta amsa mata a taƙaice.



Gyaran murya Mami ta yi tare da faɗin ''yanzu daughter yaushe za ki zo mana?."

Murmushi kawai ta yi mai sanyi ba ta amsawa Mamin ba.

Neneh ce ta amshe da faɗin ''dake ake mai farin fuska kike ta nannoƙewa kamar ta Allah.''



Hararar gefen ido ta sakarwa Nenehn akan idon Hydar da ya ɗan gyara zaman sa.



Sannan kuma a hankali ta ce ''Mami shi ya hanani zuwa.''

ɗago kansa ya yi tar- tar akan kyakkyawar fuskar ta sannan kuma ya ɗauke kan nasa daga kanta.



''Nasan za'a rina ai.'' Mamin ta faɗa, shi dai bai tanka musu ba a haka har suka shi musu albarka, haɗe da
ficewa a ɗakin har da Neneh.

Mamin da Sultana cikin gidan suka ƙarasa, shi kuma Abbuh cikin yan makoki ya shige abinsa.



Gajiya ta yi da zaman hakan yasa ta tattara hijab ɗinta ta tashi da niyar fita daga parlourn.
Cikin Muryarsa mai amo da daɗin sauraro ya ce ''Da izinin wa kika fita?." Turo ɗan ƙaramin full lip ɗinta
ta yi tare da faɗin ''Oho."

Daman a wajen ƙarshen kujera yake ta wajen ƙofa, hakan ya sa ya saka mata ƙafa ta yi tuntuɓe haɗe da
faɗuwa a ƙasan.

Wani kalar ƙara ta saki tare da yarfa hannunta.



Manunin hannunsa ya saka akan bakinsa alamar ta yi masa shiru, sannan ya rage tsayinsa haɗe da
tsugunnawa har suna iya jiyo numfashin junansu.



''Bayan yawace -yawacen ki harda iya haɗa ɗa da mahaifanshi kika iya ko?."

Kanta ta matsar gefe haɗe da murkuɗa masa baki.

Hannunsa na tsakiya da na ƙarshe ya sa tare da ɓalle mata baki, wani ƙaran ta saki tare da yunƙurawa za
ta tashi hijab ɗinta ya ƙara faɗar da ita a ƙasa.

Shi dai bai ƙara mata magana ba ya ɗauki wayoyinsa haɗe da fita tsakar gidan da hayaniya ke ta tashi an
ɗaukewa Mama Fatuh kuɗinta har dubu ɗari biyu da hamsin, hakan ya sa take ta zage - zage kamar ta ari
baki.

Shi dai Hydar kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa haɗe da sa kanshi ya fice daga gidan gaba ɗaya.



Da ƙyar ta tashi daga ƙasan haɗe da fitowa tsakar gidan da akwatin ta yake a yashe a tsakar gidan duk an
mata fatali da kayanta.



Ilham ta tafi school Unaisah na aiki, su kuma su Reeda da Sandy sun tafi siyayyan komawarsu.

Umma Mansura kuma da Ammi na tsaye cirko -cirko yayin da Neneh ta tafi raka su Mami domin tafiya
dan bata san wainar da ake toyawa ba.
Wani kalar mari Mama Fatuhn ta ɗauke ta da shi haɗe da faɗa mata suna ɓarauniya da kuma baƙaƙen
maganganu ita ma Yusrah suka haɗe suna ta zagin Liyanar, har Umma Mansura zata shigo Ammi ta yi
saurin girgiza mata kai.



Wani kalar mari Neneh da shigowarta kenan ta wankawa Mama Fatuhn tare da faɗin ''Ke kinsan waye
mahaifinta wurin kuɗi, kin san kakanta wurin kuɗi, haka zalika kin san mijin da ta aura ba kaɗan bane ba
a wurin kuɗi kowa anan zai shaida Alhaji Ahmed Qasim Kyari, ke da kallo ɗaya za'a miki a gane talauci
gaba da baya sha ³ , so so so mai kama da biri.''




Baƙin ciki ma ya hana Liyanar magana sannan a hankali kuma ta cire himar ɗinta haɗe da jacking ɗin
Mama Fatuhn ta kanainayeta kamar macijiya.

Kowa sai dukan hannun Liyana yake amma taƙi sakin Mama Fatuhn ta wani kalar shaƙe mata wuya.



Idanun Liyanar ya yi wani kalar ja.



Jikin Neneh wani kalar rawa yake dan ita a tunaninta Liyana jinnu ta tayar.




Duk da hammatan Mama Fatuhn ta hana ta sakat amma haka ta cigaba da naniƙe mata.



Hydar da zuwan sa gida kenan daga mayar da su Abbuh gida ya ji wayarsa na ringing wani kalar tsaki yaja
dan atunaninsa Amir ne ko Sultan hakan ya sa shi yaƙi ɗagawa, sai da ya ga wayan na ƙara sosai hakan ya
sa shi ɗaukan wayan amma sai kuma ya ga sunan Neneh ajiki.



Bayan ya ɗaga a kiɗime ta fara magana ''maza ka juyo ka dawo gidan nan, fitinar matarka zai sa ta yi
kisa.''
Kalmar kisan da yaji ne ya sa shi ajiye wayar haɗe da ɗaukan key ɗin motarsa ya fara tuƙi a million.



Ko lokacin da ya iso har an samu nasarar ɓanɓareta daga jikinta dan Mama Fatuh sai da ta suma dan
wahala.

Liyana na zaune sai huci take.

Abbhi ne ya zo ya zauna a kusa da ita wanda hakan yasa hawaye zuba daga cikin idanunta haɗe da
rungumesa.



''Abbhinaaa ni ka kira min lawyer na, wallahi sai na kai wannan maganar ƙara, mai zan yi da 250k, let her
check my account balance kuɗina 2 million za'a ƙara ya zama 20 million, Abbhi 250k is a chicken change
a wurina wallahi."



''Is Okay, duk wanda ya taɓa min ke nayi alƙawarin bi miki haƙƙin ki daman ko waye shi, i don't care
about the closeness, zata fuskanci hukunci, dai-dai gwargwadon abin da ta aikata miki kinji.''



Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta kalli wa'yanda ke wurin ba.......




To be countinue on Monday in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩
*Durrah Hydar.*✍️




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️
*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



Pending Amarya 34




''Abbhinaaa ni ka kira min lawyer na, wallahi sai na kai wannan maganar ƙara, mai zan yi da 250k, let her
check my account balance kuɗina 200k (last page na samu typing error ban lura ba). za'a ƙara ya zama
20 million, Abbhi 250k is a chicken change a wurina wallahi."



''Is Okay, duk wanda ya taɓa min ke nayi alƙawarin bi miki haƙƙin ki daman ko waye shi, i don't care
about the closeness, zata fuskanci hukunci, dai-dai gwargwadon abin da ta aikata miki kinji.''



Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta kalli wa'yanda ke wurin ba..........
Neneh da sai yanzu jininta ya ɗan sauko ce ta ce ''Alhamdulillah ga Hydar ɗin ma ya ƙaraso, sai ka zo ka
ɗauki wannan fitinanniyyar matar ta ka, wallahi tun da Ummaru ya mutu, Liyana ba ta bar shi ya ji daɗin
mutuwarsa ba kullum cikin fitina take, ai wannan ba Fatima ba ce ba fitina ce wallahi.'' ta ƙarashe
maganar tare da direwa Hydar ɗin trolly ɗinta.



Murmushi kawai ya yi sannan ya durƙusa ya na mai gaishar da Abbhi dake kusa da Liyanar.

Babu yabo babu fallasa ya amsa haɗe da tambayarsa ya aikin.



Bayan sun gama gaisawar ya ɗauki trolly ɗin haɗe da sawa acikin booth, ko da ya dawo cikin gidan
Neneh na ce mata ta tashi ta bi mijinta ƙi tayi, wai ita alankatafir ba zata bi shi ba.




Sai da Abbhi ya lallashe ta haɗe da tura mata 5 million a account ɗinta sannan ta tashi jiki a saɓule, haɗe
da bangaje Mama Fatuhn da ta miƙe daga sumanta da ta farfaɗo, duk a gaban Hydar ɗin.




Bayan motar Hydar ɗin taje ta zaga ta zauna duk su Abbhi da Neneh suna kallonta, shi ma Hydar ɗin bai
yi magana ba ya shige gaban motar haɗe da yi masa key.



Sai da suka fita daga unguwar sannan ya juyo da fuskarsa zuwa inda take zaune ta na hawaye.




Parker motar ya yi cikin muryarsa mai amo ya ce ''Uban waye driver ɗin ki?."

Ko kallonsa ba ta yi ba ta cigaba da goge hawayenta da hanky ɗin da Abbhi ya bata.



''Ba kya ji ne?."



''Leave me alone tun da dai da na shigo motar nan ban maka magana ba.''
''Zan bubbuge miki baki idan ki ƙara min magana without a bit of respect, dawo front sit kafin na ba ki
correct slaps.''

Tsaki ta daka sannan ta buɗe motar haɗe da shigewa front sit ɗin.



Shiru ne ya ratsa cikin motar sannan a hankali ya juyo da kansa ya kai duban sa gareta tare da faɗin
''Amma wallahi ba ki da kunya, yanzu saboda rashin ɗan ido da mahaifiyyar ki kike faɗa harda bangaza?,
see the way she's shouting time ɗin da muka shigo, wallahi ina ganinta na san ita ce mamanki, ashe dai
tsotsa ki kayi a nono.'' ya ƙarashe maganar haɗe da fuskewa kamar ba shi ya yi ba.




Juyowa ta yi ta kallesa haɗe da haɗiye miyau sannan ta ƙara mayar da kanta gefe.



''Mai sa ba za kiyi magana ba?, sosai that lady deserve to be your Mom, gaskiya aje ayi DNA TEST
because albasa ba tayo halin ruwa ba, Dan dai kar nayi saɓo da nace samun ki a matsayin ya' da Ammi ta
yi shi ne jarabtar ta.''



''Ya kuma ishe ka haka."



''Shut up while I'm talking joor, sai shegen iyayi, kamar kina da wani wayewa bayan kaff arewa babu mai
daƙiƙanci kamar ke.''



''Ka na kai ni bango fa?."



''Kin manta ƙarshen duniya nake kaiki.''



''Hmm.'' ta faɗa haɗe da cije lips ɗinta sannan ta cigaba da girgiza ƙafafunta, alamar masifa na cinta.
Daga ƙarshe shiru ne ya ratsa motar fuskar kowa a tamke barimma na Hydar.



Ko da suka isa gidanma komai neat kamar suna gidan, sai a lokacin take tunawa da wata Salimah.



Tsaki taja tare da hawa stairs ɗin ta bar shi a falon.



Remote ya ɗauka haɗe da furta ''Ƙazama.''




Liyana bayan ta ƙarasa ciki ma wayarta ta ɗauka haɗe da kiran Salimah akan ta dawo gidan.

Wanka ta shiga, ta daɗe a toilet ɗin sannan ta fito haɗe da goge jikinta da towel sannan ta fara shiryawa
cikin mini skirt da kuma wani polo top.



Polo ɗin babba ne sosai dan kar ya takurata hakan ya sa ta tattara shi haɗe da kulle top ɗin sai ya tsaya a
dai-dai cibiyarta. Wanda ya ƙara fito da farin shafaffen tummy ɗinta.



Slippers ta saka white color, haɗe da ɗaura normal hula akanta.



Shigar ya mugun yi mata kyau sosai, sannan ta cilla mint chewing gum ɗinta a bakinta da ya sha lipstick
mai ƙamshin pineapple.



Neman wuri ta yi ta kwanta ta na daddana wayar hannunta dan yunwa take ji amma ta rasa ta ya za ta
shiga kitchen ɗin ko noodles ta dafa.

Gashi har an fara kiran sallahr asar.



Ganin zamanta haka yunwa zai hallakata ya sa ta tashi daga kwancen da take haɗe da fita parlourn.
Ko da ta fita ma baya falon hakan ya saka ta shigo da ɗan gudunta cikin kitchen ɗin.



Tsaye ya ke ya ɗaura noodles a transparent glass pot ɗin dake kan standing gas, ya yi folding ɗin
hannunyensa ya ɗan jingina da kitchen island ya na mai ƙurawa tukunyar ido.




Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa, ba kayan safe bane ba ajikinsa, wannan karon combat ne ajikinsa sai t
shirt milk color a gaban rigar an rubuta _NEVER STOP ROMANCE._ da black ink.

Kallon fuskarsa ta yi tare da ɗan ƙure sa da manyan idanunta, gaskiya guy ɗin ya haɗu ya na da pointed
nose, ga gemunsa baƙi siɗik, idanunsa manya ne sosai, ga wani ɗan baƙi yale - yale dake wurin idanunsa
da suka ƙara masa kyau.



Lips ɗinsa pink ne sosai musamman na ƙasa.



''What are you staring at?."



''Mai za'a kalla anan ɗin?."



Tana faɗin haka ta buɗe fridge haɗe da ɗaukan hollandia strawberry yourghurt ɗinta.....




Na gaji mu ƙarasa gobe in shaa Allah please
To be countinue on tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩




*Durrah Hydar.*✍️




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️




*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎



_Pending Amarya 35_




Kallonsa ta yi daga sama har ƙasa, ba kayan safe bane ba ajikinsa, wannan karon combat ne ajikinsa sai t
shirt milk color a gaban rigar an rubuta _NEVER STOP ROMANCE._ da black ink.

Kallon fuskarsa ta yi tare da ɗan ƙure sa da manyan idanunta, gaskiya guy ɗin ya haɗu ya na da pointed
nose, ga gemunsa baƙi siɗik, idanunsa manya ne sosai, ga wani ɗan baƙi yale - yale dake wurin idanunsa
da suka ƙara masa kyau.



Lips ɗinsa pink ne sosai musamman na ƙasa.



''What are you staring at?."



''Mai za'a kalla anan ɗin?."
Tana faɗin haka ta buɗe fridge haɗe da ɗaukan hollandia strawberry yourghurt ɗinta.




''Leave my presence.'' ya faɗa cikin Muryarsa

Please Login or Register in order to submit comment