You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




The Noble Writters 🦚

Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 29_




Ganin wanda ke tsaye gabanta ya mugun ɗaga mata hankali, amma sosai ta dake haɗe da murguɗa
bakinta tare da faɗin "kai kullum duk inda zan je sai ka bi ni ? are you for real?." Ta faɗa tare da ƙara
murkuɗa masa bakin.




Shanyayyun idanunsa dake nuna alamun basu daɗe da tashi a barci ba ya zuba mata su sosai wanda
hakan ya sa cikin ta ya yi wani mugun kaɗawa............"
A hankali ya buɗe bakinsa ya ce "I will be the one asking you this spoiled brat, duk inda naje kina sane
da ni da rayuwata, kina yawan satar kallona, this should be the last time da zan ganki arround me, if
not." Bai ƙarasa ba kawai ya yi ƙwafa.




"Ƙarasa karta kashe ka."




" I don't have time ga wa'yannan kalan matan, for the last time don't you dare show your face again, get
lost!."




Sakin baki ta yi dalala har ya ɓacewa ganinta bata sani ba, ga baƙin cikin ɓakar maganar da ya sakar
mata, wai wa'yannan matan?.

Karuwa fa kenan yake nufi.

"Kam balasti."

Ta faɗa a fili kafin tayi wani harraman binsa har Abbhi ya iso inda take.



"Abbhi yunwa."
"Da ƙwandala ake cin abinci fa anan."



"Abbhi manaaa, Allah yunwa nake ji ba wasa nake ba."




" Sorry babyn Abbhi." daga haka yaja hannunta suka ƙarasa wajen wurin order abinci kafin suka fara ci.



Sai da ta shiga ruwa suka yi yawo sosai, sai ƙarfe goma sannan ta nufo hanyar gidanta dan sai da Abbhi
ya ajiyeta a gidansu ta ɗauko kayan da Abbhin ya siya mata da motarta, shima Ammi kamar ta kasheta
da faɗa.



Da wani mugun speed take sharara gudu a saman titin da babu kowa sosai sai manyan motoci haka tayi
ta overtaking mutane.



Wani kalar birki taci sanadiyyar karon da suka yi da wani mota ƙirar Lexus LC 500.



Wani kalar matsiyacin duka ta kaiwa sitiyarin motar tare da daka wata uwar tsaki ta fito daga cikin
motar ta.



Babu mutane sosai a unguwar, a hankali ta duba motarta tare da leƙa wanda suka ci karo.

Yana zaune ahakimce ya na ma waya.



Ganin hakan ne ya sanya ta komawa cikin motarta da niyar tada motarta ta ƙara gaba.



Still motar a buɗe ta barta dan sai ta gama tada mota sannan take kulle ƙofar ita haka tsarin ta yake.
"Kamar saukar aradu taji muryar mutum a kunnenta unexpectedly wanda saboda hakan ya sanya ta
firgita a take dan Liyana akwai tsoro.




"Can't you say sorry?."



Dake babu wani haske a motar yasa bata ga fuskar ba buh the voice sounds familiar amma wannan ya na
da sanyi not wanda ta saba jin sa a fusace.



A hankali ta fito daga cikin motar wanda hakan ya ɗan sa shi ya ɗan ja baya.



A nitse ta fara magana " You will be the one to kace min sorry ai, saboda kana waya kana tuƙi which is
not allowed."

Ta faɗa tare da fara ƙoƙarin komawa cikin motarta.



"Wayarsa daya mayar gaban aljihunsa tun lokacin da ya gama waya ne ya fara kawo flash alamun kira.

Wanda hakan ya hasko masa fuskar wadda take cikin motar.



Sai da ya ɗan ja baya kaɗan sannan ya ce " at this time daman sai mata Irinku ke shawagi a titi."

"Whaaaat! How dare you?."



Ta faɗa tare da cire glasses ɗin ta.



"Don't you dare ki yi min magana son ranki."



A hankali tayi shiru tare da mayar da hankalinta kan gaban motarta tana kallon titin da babu kowa,
sannan a hankali ta ƙara faɗin " ja gefe zan kulle motana."
Tsaye yayi bai motsa ba awurin.



"What's all this wai, ko kaine ka siya min motar?!."




Ta faɗa a hasale.



Ja yayi da baya yana ƙare mata kallo da kyau wani kalar matsiyacin kallo ta masa duk da duhun haɗe da
tsaki sannan ta tayar da motar ta wuce.




Tun bayan da suka rabu da ita a joint ɗinsa sai da suka yi yawo sosai da Amir sannan ya kamo hanyarsa
na dawowa gida domin ya huta, still a hanyarsa sai da ya haɗu da wannan shaiɗaniyyar yarinyar.




Har yanzu mamakin kalar iyayen da suka yi raising ɗinta yake.



Gaskiya sun yi sakaci da yawa.



To eleven ace ƴar ki bata dawo ba kuma ba zaki iya neman inda taje ba.



Dubi yadda take ta'amali da tsofaffi duk sugar daddies that girl is a fitina to society gaskiya.




Sai tsaki yake ta jaa, dan Hydar na da mita sosai.
Murza motarsa ya yi ya cigaba da tafiya har ya ƙaraso gidan.




Liyana kam ranta fess she didn't even care about rashin ɗan idon data masa duk da bai bata fuskar
hakan ba.



Bayan ta dawo ɗinma sai da taci abinci ta yi wanka ta sauko parlour cikin shigarta na pyjamas wandon ya
tsaya mata a dai-dai gwiwa.




Rigar ta lafe luf - luf a jikinta.



Duk da uban daren da ake tsalawa sai da ta kunna waƙa a TV haɗe da ƙure volume.



Ga home theater da sai amsa kiɗan suke.



Koda ya dawo cikin gidan ma tun a parking lot yake jin kiɗa na tashi na ban mamaki.




Shigowarsa keda wuya ya tarar da ita tana tweking kamar wadda take a club.

Waƙar Ayra Starr Bloody Samaritan ce ke tashi a living room ɗin.



With all her body take girgiza ko ina na jikinta ko ina ta na malƙwayashi haɗe da lanƙwasa shi dai-dai da
salon kiɗan.
Baki sake ya tsaya kallon wadda yafi tunanin cewa ita ce matar tasa sannan a hankali ya ƙaraso living
room ɗin haɗe da ɗaukan remote ɗin Tvn ya na mai kashe tvn.



A tunaninta ko Saleemah ce hakan ya sa ta juyowa a fusace wanda hakan ya yi sanadiyar haɗa idanunsu
a daidai inda ya duƙa zai maida remote ɗin mazauninsa......."




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).
~PENDING AMARYA CE~




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*

*(J.W.A)*




_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi._




With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.




*THE NOBLE WRITTERS TEAM.*

_Dedication is Our Strong_




_ Pending Amarya 30_




A tunaninta ko Saleemah ce hakan ya sa ta juyowa a fusace wanda hakan ya yi sanadiyar haɗa idanunsu
a daidai inda ya duƙa zai maida remote ɗin mazauninsa......."
Da wani kalar speed ta ja baya sannan ta ƙara matsowa sosai haɗe da murza idanunta ko gizo suke gane
ma ta, da ta ga dai da gaske idanun na ta ba su mata ƙarya ba hakan yasa ta daddage ta runtuma wani
uban ihu wanda duk wani na kusa da ita idan ya ji zai ji shi ne har dodon kunnensa.



''Salimah! Salimah! Na yi gamo da aljani, innalillahi wa inna ilaihir rajiun!."



Jikinta sai rawa yake dan ganinsa da ta yi ya yi mugun ɗaga mata hankali.




Ƙwalama Salimah kira take amma babu alamun zata fito ma, kuma mutumin sai ƙara dosota yake, itama
ta na matsawa baya.



A hankali ta tafi tare da zurawa a guje zata haura saman stairs teddy slippers ɗinta ya faɗar da ita a
ƙasa.



A hankali ta ƙara yunƙurawa ta tashi daga ƙasan haɗe da tsayawa ta na ƙare masa kallo.



Salimah dake kwance ta na waya da boyfriend ɗinta ce ta fito a kiɗime jin kiran da Liyanar ke kwaɗa
mata, "Aunty Liyana what's wrong?."



Idonta ne ya sauka akan Hydar dake tsaye ya ƙafe Liyanar da eyes ɗinsa.
''Laa Ya Hydar sannu da zuwa.''

''Yawwa!, Sannu!, who's she!?." Ya amsa gaisuwar nata haɗe da jefo mata tambaya akan Liyanar da
itama ta ƙuresa da firgitattun idanunta.




Sai da ta tsaya yi musu kallon mamaki sannan a hankali kuma ta ce ''Matar ka ce mana Yaya.''

''You can go.''



''Toh Yaya.''

A hankali ya fara ta ko ƙafafunsa zuwa inda take tsaye a fusace ta ce ''Kar ka matso kusa dani ko da
wasa!.''



Bai kula ta ba ya cigaba da matsowa kusa da ita.

''Don't you dare come closer, you dog!."




Jikinsa har wani kalar huci yake, idanunsa na canza kala dan ya sha faɗa ya tsani mace mara tarbiyya da
kuma mara kunya a rayuwarsa.




Da sassarfa ya ƙaraso wurin da take haɗe da ɗauke ta da wanni kalar gigitattcen mari sannan a hankali
ya ce ''wannan na ranar da kika faɗar min da waya ne, kin tuna ranar?, nasan ba za ki tuna ba.''
wani marin ya ƙara mata wannan karon sai da ta ga stars kalar na duniyar mars (😂😅).



'' Wannan na ranar da kika bige min mota ne.'' sannan ya ƙara mata wasu twins ɗin mari making four
''wannan na marin da kika min ne saboda lack of tarbiyya da iyayenki suka ba ki.''



Hannu ya ɗaga zai ƙara sakar mata wani marin wanda bai kai ga marin ba ta bangaje hannun nasa tare
da hawan kan stairs da gudu cikin shashsheƙar kuka ta fara magana ''Ai ba jaka aka kawo maka ba da tun
safiyar Allah kake marina mugu kawai, lack of tarbiyya kuma wannan kai za'a kira da shi, banza kawai
mai dukan mata lusari!.''



Da gudu ya biyo ta zai dake ta wanda hakan ya saka ta arce a guje.



Ko da ta shiga ɗakinta ma faɗawa ta yi akan gadonta ta fashe da wani sabon kuka, a haka har bacci ya
kwasheta.



Ɓangaren HYDAR kam marin da ya mata ma a ganinsa bai huce ba, dan laifukan ta sun fi yadda ya lissafo,
ga yawo da samari da aurensa akanta, ai wannan ma sam - sam ba matar aure bace, ya sha ganinta a
joints kala - kala, musamman da ya ke gina joint ɗin shi da yake duba kalar wa'yanda ake da su anan
kano ɗin.



Ƙwafa ya yi tare da faɗin ''kaɗan kika gani, zaman gidan nan ma sai ya gagare ki.''



Daga haka ya shige toilet domin watsa ruwa sannan ya sanya kayan baccinsa tare da kwanciyarsa, sai da
ya ɗan duba laptop sannan ya gyara kwanciyarsa bacci mai daɗi ya kwashesa.



Washegarin ranar ma Liyana ko da wasa ba ta fito ba rayuwarta kawai take a sama Salimah na kawo
mata abin da take so.



Shi HYDAR ma ko ta kanta bai bi ba, duk da ya ga abinci jere kan dinning buh he prepared ya ci na
siyarwa because shi yanzu komai na gidan ya fice masa a kai, ga tsanar yarinyar na ƙara fizgarsa.
Fitarsa ke da wuya a gidan wayarsa ta fara ringing ko da ya duba ma Abbuh ne ke kiransa a wayar ajiyar
zuciya ya sauke sannan a hankali ya ɗaga.



''Assalamu alaikum Abbuh.''



''Wassalam, har ka fita ne?."

''Eh Abbuh.''



''Kana ina toh yanzun?."



''Ina hanyar zuwa gida ne."

''Gidanka?."

''A'a Abbuh gidanmu, naka kai da Mami toh.''



''Yayi maka kyau, ka zo ka sameni a office yanzun nan.''

''Wanne a ciki?."

''Na takalma.''

''Toh sai na iso Abbuh.''



"Okay, alright.''



Ajiye wayar ya yi haɗe da fuzgar da iska a bakin sa sannan ya juyar da kan motar tasa zuwa can office
ɗin.
Liyana sai da taji fitar motarsa sannan ta fito falon fuskarta duk shatin mari dan har lokacin shatin na
nan.




''Munafuki.'' shine kalmar da ta faɗa haɗe da zama akan kujerar dinning ɗin ta fara cin abincin da ta
ganshi a jere a kan dinning ɗin.



Salimah ce ta fito daga cikin ɗakinta fuskarta da dan damuwa tazo wurin Liyanar ''Aunty Liyana, kin tashi
lafiya?.'' ajiye spoon ɗin hannunta ta yi tare da faɗin ''lafiyar ce ta saka kika ganni da shatin mari à
fuskata algunguma!.'' ta ƙara jan tsaki haɗe da kwaikwayon Salimahn.



''Laa Yaa Hydar sannu da zuwa baka sani ba matarka ce ai.'' ta ƙarashe maganar da tsaki tare da faɗin
''Rubbish.''



Sannan ta cigaba da cin abincin ta .

Har Salimah ta fara kwashe warmers ɗin Liyana ta ƙara faɗin ''Shi ko menene sunan da kika kira ma, ko a
ina kuka haɗa dangi har ya zama yayan naki oho.''



''Aunty Liyana dan Allah ni kiyi haƙuri, ki barni haka.''



''Ni kauce min a hanya, mtsww laa ya hydar.''

Ta faɗa sannan ta ƙarasa up stairs da gudu.

Miss call ɗin Lily ta gani hakan ya saka ta bi wayar.

Ring biyu ta ɗaga a hankali suka fara magana because test ɗin jiya shine jigon exam ɗinsu na first
semester a level 400.



''Lily yaushe za ki zo?."

''Bae i think next week zan zo buh kinsan ni wallahi am not good a zuwa gidan friends unless idan zamu
haɗu a Hydar's palace and garden.''
''Ai sai dai kar mu haɗu wallahi.''



Haka suka cigaba da hira har ƙarfe biyu sannan ta yi sallah.

Bayan ta idar ma fitowa dinning room ta yi domin cin abincin rana.



''Aunty Liyana kin fasa zuwa Saloon ɗin ne?."



''Kin saka an yi min damaging fuskar zan fita a hakan?."



Parking ɗin mota Liyana taji a compound wanda a take ta saki spoon ɗin hannunta haɗe da arcewa da
mugun gudu.



Salimah kawai da idanu ta bita.



''Assalamu alaikum jama'a.''



Muryar Neneh ta daki kunnen Liyana da saura ƙiris ta ƙarasa buɗe ɗakinta.



Juyowa ta kuma yi a million ta fara saukowa da gudu jikinta daman tun mini skirt ɗin yau da safe ne ba
ta yi wani wankan ba.

Sai wani crop top mai kyau milk color ƙafarta kuma sanye da slippers ɗin Gucci.



Kanta ba kitso tayi parking a tsakiya santala santalan cinyoyinta na ta sheƙi kamar kullum.



''Sannu da zuwa my Neneh.''
''Subhanallahi, Fatima ko fitina? , maza dallah je ki saka tufafi kin bar su lantana a buɗe haka?."



Ɗago kanta tayi a ta kai dubanta wurin Neneh, amma idonta bai sauka kan kowa ba sai wanda ke sanye
cikin shigar manyan kaya kansa na sanye da hular nan ta zanna bukar............




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."




*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️




With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*🫆🐾🦚



_Our strength lies in Dedication_🤍




Am back to who I'm 🤝

A baya nayi sanya amma yanzu na ajiye son jiki agefe, akan kawo ƙarshen wani abu domin fara sabon
abu.



Dan haka na kawo karshen sanyin jikina domin cimma nasarata.

Kafin na cimma nasarata sai na ajiye son jiki agefe.



Am Soo sorry everyone.



Pending Amarya as usual 😌
But not like before 😌 🥀🙌💎
_ Pending Amarya 31_




Parking ɗin mota Liyana taji a compound wanda a take ta saki spoon ɗin hannunta haɗe da arcewa da
mugun gudu.



Salimah kawai da idanu ta bita.



''Assalamu alaikum jama'a.''



Muryar Neneh ta daki kunnen Liyana da saura ƙiris ta ƙarasa buɗe ɗakinta.



Juyowa ta kuma yi a million ta fara saukowa da gudu jikinta daman tun mini skirt ɗin yau da safe ne ba
ta yi wani wankan ba.

Sai wani crop top mai kyau milk color ƙafarta kuma sanye da slippers ɗin Gucci.



Kanta ba kitso tayi parking a tsakiya santala santalan cinyoyinta na ta sheƙi kamar kullum.



''Sannu da zuwa my Neneh.''
''Subhanallahi, Fatima ko fitina? , maza dallah je ki saka tufafi kin bar su lantana a buɗe haka?."



Ɗago kanta tayi a ta kai dubanta wurin Neneh, amma idonta bai sauka kan kowa ba sai wanda ke sanye
cikin shigar manyan kaya kansa na sanye da hular nan ta zanna bukar.......




Ta ma rasa mai ke mata daɗi, tana tsaye ta kasa gaba ta kasa baya.



Neneh dai neman wuri ta yi ta zauna tare da faɗin ''Mai kike wani gwaggwale ido kamar kin yi wa sarki
ƙarya.''



Duba wurin da Sultan ke tsaye Neneh ta yi, ta ga babu alamar sa, kallon Liyana ta yi tare da ƙara faɗin
''Kin aike sa ne naga baya nan.''



Shiru Liyana ta yi sannan kuma cikin sassanyar muryarta ta ce ''waye shi Neneh?."




''Ke nifa ba tambaya nazo ki min ba, zuwa na yi na sanar miki Umaru ya mutu murus, yanzu daga wurin
gaisuwa muke zanje kwaso kaya na na koma can ɗin, Ita kuma Maimu ƴar daɗi miji ta na can tana,suma
ita ala dole mijinta ya mutu.''



''Innalillahi wa inna ilaihir rajiun!, Neneh kiji tsoron Allah.''



''Toh yo tsoron ki zanji, ku zubo min abin da ku ka dafa in ci,abinci ko wahala?, abicin gidan rasuwan duk
yaji sai kace a gidan yarabawa, toh ina fama da gyanbon ciki ina Ajiddeh da cin fara da mai.''
Liyana ba ta tsaya jin shirmenta ba ta haura ɗakinta haɗe da sanya simple abaya mara kwalliya haɗe da
himar sannan ta zira slippers tare da ɗaukan car key.




Ta sauko da ɗan gudunta.



''Ke dai Fatima ba ki da imani, a sanar dake mutuwa amma ko ɗigon hawaye babu balle kuka.''



''Dan kin sanar dani mutuwa sai na kama birgima a ƙasa tun da sunana Ruth?."



''Kar ki zagen.''



''Kyaji da shi kuma.''



Daga haka ta fice daga falon tare da faɗin. ''Salimah ki kula da gidan, ke kuma Neneh idan kin taho ki
haɗo min da kayana.''



''Ba ni aka kawo miki yar aiki ba ai.''

Bayan fitar Liyanar kallon Salimah ta yi sannan ta ce ''Wai Salimah da ta tafi da izinin wa ta fita?."

''Neneh dai tare muke anan fa."



''Allah ya kyauta kowa dai fitsararre ne.''




Ko da Hydar yaje office ɗin Abbuhn ma tare suka je gidan rasuwar.
Sannan Abbuh ya ce masa ya kula da harkar komai na office ɗin tun da Sultan ke na Hydar ɗin.



Gidan ya yi maƙil da jama'a saboda Alhaji Umaru mai son jama'a ne sosai.



HYDAR bai iya zama gidan rasuwar ba saboda tausayi matan dake kuka ke basa, ga matarsa sai suma
take tun da ya zo aka nufi hospital da ita, amma da rana zai dawo ɗaukan Abbuh.



Liyana kam gudu kawai take shararawa a titi har ta ƙarasa bachirawan, ko ina shiru a unguwar a hankali
ta sauko daga motar idanunta duk ƙwalla babu wani alamar tsiwa a tattare da ita, a hankali ta tako har
cikin gidan.



Ko ina maƙil yake da ƴan uwa da abokan arziki, kowa nata jimami Ammi na zaune kusa da Fatima yayarta
da suke da uba ɗaya tare da ƴarta Yusrah, ƙarasawa tayi kusa da Ammin tare da faɗin ''Ammi ya haƙurin
mu?."

''Da godiya.'' ta bata amsa a taƙaice.



''Ammi ina Ilham da Mama Maimu?."



''Ke wacce kaliyar sha³ ce da ba ki da hankali sannan kuma ba ki da tunani?, kina ganin halin da suke ciki
za ki wani kama tambayar banza da wani wofi.'' inji cewar Yusrah dake zaune kusa da mahaifiyyarta y'ar
gidan yayar Ammi ɗin her half cousin sister.



''Karki saki ki ƙara zagina tun da dai ba uwarki na tambaya ba!."



''Bara uba uwata kika zaga?!."



Kallonta Ammi tayi tare da faɗin ''Fatima kar na sake jin bakin ki anan.''
''Ba zan sake magana ba Ammi amma wallahi ta zagan sai na rama.''



Dariya Yusrah ta yi tare da faɗin '' banza kawai mara tarbiyya.''



''Da ni dake idan makaho ya shafa ya san mai tarbiyya da mara tarbiyyar ai, tsohuwar kilaki.''



''Ni kike kira da karuwa?."



Tashi Liyana ta yi haɗe da cire himar ɗinta sannan ta ce ''An kira ki ɗin, ki yi duk uban da za kiyi, ko zan
daku ne?."

''Liyana I said ki daina cacar bakin nan ko?." Inji cewar Ammi.



''Ammi can't you see ita ta fara takalata ko uwar ta bata gani da zata hanata faɗe.''



Ammi bata ƙara kallonta ba ta cigaba da lazumin ta.



Yusrah ce ta kawo wa Liyana mari ita kuma ta sa hannu ta kare, kamar ba gidan rasuwa ba haka suka
fara dambe a tsakaninsu kamar wasu karnuka.



Yusrah ce ta samu nasarar kama gashin Liyana hakan ya sa ta saki ƙara.



Sannan a hankali Liyana ta gartsa mata cizo, Mama Fatu ce ta zo ta fincike ƴar tata tare da faɗin ''Ke ba
kida hankali da za ki biyewa wannan.'' ta faɗa haɗe da fincike Yusrah a hannun Liyana, tun da gaba ɗaya
a bedroom na yaran gidan suke.



''Kar ki sake wallahi Mama Fatu ki ƙara zagina, karki ƙara cemin wannan.''
''Kull cire Maman nan kira ni Fatuh mara ɗaha kawai mai suffan shegu.''



''Suffar shegu kam kina ganin ƴar ki kinsan ta fi ni suffar shegu har da na shaiɗanu ba ki ɗaya, ki kalle ni
daga sama har ƙasa ban yi ƙari da komai ita kuma ƴar ki fa?."



Ƙanƙance idanunta Mama Fatuh ta yi tare da faɗin ''Ke da aka aurar dake saboda kuɗi fa?.''



''Da kema za ki samu ki aurar da ɗiyarki saboda kuɗi da kin fi kowa murna.'' Liyana ta ƙarashe maganar
da tsirawa Mama Fatuh ido.



''Ba dai aure ba?, mu zuba mu gani.''

''Shege ka fasa, in fitsari banza ce kaza ma ta yi mu gani, ƴa ta gama ruɓewa kin zo kina wage wawwaran
bakin ki duk kin hanani sukunin."



''LIYAANAA!." Ammi ta faɗa da ƙarfi.



''Ammi ki ƙyale ni.'' ta faɗa haɗe da cuno baki.




''Ikimat a gaban ki ƴar ki ke zagina haka ba ki ce komai ba.'' ta faɗa tana kallon Ammi.



''Ahh wallahi da sauran tarbiyya ta ni bake na zaga ba, aatoh kar ki kaini inda Allah bai kaini ba.''



Jiddah ne da yaji hayaniya ya fara yawa har matan dake waje sun fara shelantawa a tsakaninsu, hakan ya
sa shi shigowa cikin ɗakin tare da yiwa Liyanar magana ''Ya Zahra mai kuke yi haka?, ko kun manta wurin
rasuwa ne nan ɗin?."
Sassauta muryarta ta yi haɗe da basa haƙuri.

''Toh kar akuma."

''In shaa Allah jiddah.''

Daga haka ya futa daga ɗakin.

Sai data fakaici idon Ammi da Mama Fatuh data ajiye kanta kamar ta Allah, daman Yusrah nada kumatu
manya manyan nan, hakan ya sa ta kwaɓe mata fuska haɗe da faɗin ''Shegiyya.''



A fusace ta ɗago kanta saboda yadda masifa ke cinta wayarta ƙirar iphone fourteen promax ta cillawa
Liyanar wanda hakan ya sa wayar ta fashe tare da yin blank.



''Wa ya gaya miki ana nufan ƴar gidan Nabil da sharri a wanye lafiya, U la la.'' ta ƙarashe maganar da
gwalo da kuma dariya mai cin rai sannan ta fice daga ɗakin.




Ammi ta ma rasa bakin magana ta rasa ya zata yi da lamarin Liyana, ta san wace Mama Fatuh ta san mai
za ta iya aikatawa ba ta ƙi ta lalata rayuwar Liya ba .



Tunani sun mata yawa akai berekete, ga mahaifiyyarsu bata farka ba har yanzu Neneh ma shiru bata
dawo ba.



Gasu Fati ƙarama har yanzu daga kai order kayan sadakan uku basu dawo ba da ita da ƙanwar Mama
Fatuh, Mansura ma bata iso ba ( Fati ƙarama ƙanwarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya, su biyu mamansu ta
haifa).



''Yaro bai san wuta ba sai ya taka.'' jiin kalmar da Mama Fatuhn ta furta shi ya dawo da ita daga dogon
tunanin data lula.
Liyana kuwa ko da ta fito daga cikin ɗakin a compound ta yi zamanta tana ƙwalla dan yanzu wani kalar
taƙaicin biye wa Yusrah take.



Ga wani tuna marigayi da ta yi, Idan ya na mata wasa tana masa shan ƙamshi idan yana kiranta matarsa
ashe dai ba zasu gana ba.

Ta takura kanta wuri ɗaya tana kukanta.



Sallamar da aka yi ta amsa tare da ɗago kanta tana kallon Unaisa da ta janyo wani ɗan trolly fuskarta duk
hawaye sakin trollyn tayi tare da rungume Liyanar ta na faɗin ''Papi is gone!.'' haka suka yi ta raira kukan
sannan suka kai kayan nasu ɗakin jikoki dake gidan.



''Ina Mama Maimu?." Unaisah ta tambayi Liyanar.



''She fainted kusan sau biyu, because a hannunta wai ya mutu.''



''Allah sarki ya rabbi I need this kind of love.''



Tsaki kawai Liyana taja tare da faɗin ''Zo ki raka ni gidana dan Allah.''

''Awwn kaga masu gida.''



''Y'ar iccar kawai.''

''na kai ki?."

Duk da suna cikin jimami hakan bai hanasu murmusawa ba.



Daga nan suka tashi tare da ɗaukan wayarta da car key ɗinta suka yo waje.
Ko da suka isa ƙofar gidan ma Sultan ke tsaye da Ilham wacce ke sanye da hijaby lemon green da ya
haska mata fata.



Kallo ɗaya ta yi musu sai taji ba zata iya tafiya ba hakan yasa ta bawa Unaisah car key ɗin haɗe da nufar
wurin da suke tsaye.



Cikin takunta na slay queens in hijaby (😂😂). Ta iso wurin da suke tare da faɗin ''Ilham mai kike a
anan.''

''Yaya Liyana tambayarki yake fa, yawwa Yaya Sultan here she is, amma fa as I said she's married, na
barku lafiya.''



Kallonta ya yi sosai haɗe da barin jinginar da ya yi wa motar ya dawo yana bawa gidan baya ita kuma ta
jingina da motar tare da folding hannunta haɗe da kallon sa da kyau sannan ta ce '' faɗi mai ke tafe da
kai am all ears.''



''Liyana how could you?....."



'' How Could I what?....huh.""

Ta faɗa tana hura iska a fingers ɗinta haɗe da ɗage girarta guda ɗaya.

" Got married without telling me?."

Murmushi ta yi mai sauti sannan kuma ta tsuke fuska kafin a hankali ta kuma faɗin ''As you be my
papa?."




Ta ƙarashe maganar da murmushi akan fuskarta wanda hakan yayi dai - dai da fitowar Hydar tare da
Abbuh saboda bayan yaje office ɗin ya dawo gidan rasuwar da rana saboda mayar da Abbuh wurin
aiki.......
To be countinue tomorrow in shaa Allah!!. babu sanya al'amarin pending amarya yanzu 😩




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah,

Please Login or Register in order to submit comment