You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

how comes?, mai ya kawo ta gidan sa wa tazo nema? Ba
dai ƙawar wannan j'airar aka aura ma sa ba.

Kwata -kwata zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa wani kalar tunani suke basa, ga zuciyarsa wani kalar tafarfasa
yake, tunaninsa da hankalinsa sunƙi ba shi nutsuwa, haka nan kawai yaji ya tsinci kansa da shiga
ɗakinta."



A hankali ya tura ƙofar ɗakin tare da shiga ciki, wani ƙamshin turare ne ya daki hancinsa a take ya ɗan
lumshe idanunsa.



Ɗakin kaca - kaca yake, kwalin pizza na kan gado, sai kwalin hollandia, ga wani ɗan container kamar na
milky donut shima akan gadon, sai kuma wani bra dake yashe a ƙasa wanda tun shigowarsa ɗakin shi ne
abin da ya fara masa sallama, duk ɗakin kaca -kaca.



" Daman nasan tsaftar biri ne, just look at."
Ji yayi kamar amai zai taso masa har zai fita daga ɗakin, sai a hankali idanunsa suka sauka kan wani
picture dake bedsides na Ilham, jalbab ɗin himar ke kanta har ƙasa, tayi folding hannunta tana murmushi
dimple ɗinta ya loɓa.

Sai kuma ɗayan su biyu ne ita da Liyana, still dai hijab ne ajikinta, ita kuma Liyana palazzo trousers da
corset top tayi alamun kiss da bakinta.



A hankali ya ijiye frames ɗin tare da faɗin "might be the one in hijab in shaa Allah."

Daga haka ya fita daga ɗakin.



Ko a mota sai da ta kira Salimah akan lallai idan taje gidan ta gyara mata ɗakin dan jinta take wani iri da
ta bar ɗakinta kaca -kaca, dan abin da bata saba da shi ba kenan."



A school ma lecture ta ɗau daɗi, bayan sun fito sai da ta biya gidan Lily ta yi rayuwarta sannan ta kamo
hanyar gidanta.



Gidan sai ƙamshi yake dan Salimah sai da ta mata girki ta gyara gidan tsaf ta saka mata turaren wuta.



"Aunty Liyana sannu da zuwa." " Yawwa Salima, mai kika dafa?." " Cous cous ne da sauce."

" Serve me please."



"Okay Aunty."



Daga haka ta shiga kitchen ta zubo mata abincin, sai da taci sannan ta haura sama, shima fess ko ina.



Kayan bacci ta saka tare da feshe jikinta da turare masu tsadar gaske, sannan ta fito dan taya Salimah
hira.



Sai kusan Arround 10 O'clock sannan ta haura sama ita ma Salima ta shige ɗakinta na downstairs.
Arround twelve O clock ta tashi tana jin ƙishin ruwa wanda sai da ƙyar ta sauko downstairs dan tsoron
gidan take ji, kitchen ɗin ta shige tare da kunna switch ɗin kitchen ɗin, wanda a take idanunta suka gane
mata bayan wani faffaɗen mutum mai tsayi, jikinsa sanye da pyjamas white color wanda alamu sun nuna
tea yake haɗawa.

Wani kalar razananniyyar ƙara ta saki dan a tunanin ta aljani ne ko ɓarawo.(Ɓarawo da haɗa tea😂).



Shi ma a kiɗime ya juyo dan ƙarar har kwanyar kansa ta ratsa, a hankali ya sauke idanunsa akan............




Let's meet tomorrow



Thanks for reading 🤗🦋🤌



THE REGRET

(Dana sani).




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




The Noble Writters 🦚
Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 27_




Arround one O clock ta tashi tana jin ƙishin ruwa wanda sai da ƙyar ta sauko downstairs dan tsoron
gidan take ji, kitchen ɗin ta shige tare da kunna switch ɗin kitchen ɗin, wanda a take idanunta suka gane
mata bayan wani faffaɗen mutun mai tsayi, jikinsa sanye da pyjamas white color wanda alamu sun nuna
tea yake haɗawa.

Wani kalar razananniyyar ƙara ta saki dan a tunanin ta aljani ne ko ɓarawo.(Ɓarawo da haɗa tea😂).



Shi ma a kiɗime ya juyo dan ƙarar har kwanyar kansa ta ratsa, a hankali ya sauke idanunsa akan
kyakkyawan shape ɗinta na baya data juya da gudu domin nemawa kanta mafita, dan wannan baya ma
kama da mutum, bare ma ace ɓarawo ne ko what soo called her fucking husband.




Ko upstairs bata nufa ba ƙasan ɗakin Salimah ta bubbuga da ƙarfi, a firgice Salimah ta buɗe ƙofar ta na
tambayarta mai ya faru?.

Ko kallonta Liyana ba tayi ba ta shige cikin bargon Salimahn ta kwanta tana maida numfashi.



''Aunty Liyana lafiya?."



Tsaki taja haɗe da faɗin ''Lafiya ce tayi sanadiyar shigowata ɗakin ki ai tun da penthouse ne ɗakin naki.''
ta ƙarashe maganar haɗe da shigewa cikin bargon.




''Allah ya ba ki haƙuri Aunty.''
Ko kallonta ba tayi ba ta kwanta wani wahallalen bacci ya kwasheta.



Da safe ma bata yarda ta fita ba komai Salimah ke zuwa ɗakinta ta ɗauko mata.

Dan yau babu school ɗin da zata iya zuwa.



Zama tayi a parlourn tare da da kallon Salimah da ta gama kwashe kwanukan da suka yi break fast ta ce
'' Salimah ɗauko min hand bag daga sama please, sai ki haɗo min da veil black color, da kuma slippers.''



''Toh Aunty.''

Da sauri ta hau saman tare da ɗaukan abin da ta aiketa sannan ta dawo mata da su.



Shiryawa ta yi tsaf daman already jeens trouser da long sleeve shirt ne ajikinta black color amma
wandon fari ne.

Sai kuma slippers baƙi, sai baƙin mayafi da jakarta ƙirar Gucci, chewing gum ɗin dake kan center table ta
ɗauka haɗe da cilla shi a baki.



''Salimah shirya muje mu dawo.''

''Aunty kuma a haka za ki fita.''



''Bana son shishshigi, yaushe muka fara wannan dake, je ki ciki ki shirya mu wuce dallah.''



Sum- sum Salimah ta shirya ta saka wani zumbulelen hijab har ƙasa ta fito.



''Wa za ki bi a haka, nifa ba gidan mutuwa zanje ba kika wani saka hijab kamar za ki tafi musabaƙa.''



''Toh Aunty Liya ban da mayafi.''
Tsaki taja sannan ya kuma faɗin '' sai ki taho muje dan ba zan shiga sama ba.''



Daga haka ta wuce wurin dinning room ta ɗauki mukullin motar ta a inda ta bar shi jiya da ta ci abinci,
dan tsarin gidansu kenan, idan kana goge - goge, ka ga abu ka bar shi a wurinsa.



Ta nufi jeep ɗinta, tare da sanya seat belt ɗinta. Taja motar ta bar gidan.

Bata zarce ko ina ba sai rijiyar zaki gidan Neneh.



Shigowarsu ma Neneh da fadila ne a zaune ƴar aikinta suna hira.




''Ni Ajiddeh matar Aliyu na ga abin da ya kai min wuya.''



Ko kallon Nenehn bata yi ba ta nufo falon tana ƙoƙarin zama a parlourn.



'' ke kam rainon Nabil bai miki kyau ba, mai wannan?, dubi ki ga yadda nake hango ƙasusuwa, duk kin
bar Lami a buɗe.''



''Neneh ke ko missing mutum ba kya yi kya bari na zauna kafin ki fara halin naki ai.''



Matsowa ta yi sosai kusa da Liyanar tare da faɗin.

''Kin haɗu da Khairatu a waje ne?."



''Wace hakan?."

''Ashaa, Uwar mijinki mana.''

''Ni ina da mijina?, ko akwai wanda ku ka yi da shi zan aure sa?."
''Na yarda bayan tsalle tsalle harda shaye shaye a tattare dake, tun da Allah ya jeho ki sai ki zo muje can
bachirawa wai Ummaru ba lafiya.''



''Subhanallahi, Tsohon manyan ne ba lafiya?."



''ni fa iyayinki ke haɗa ni dake, ba komai ba, kice Babi, kawai kin tsaya wani kalacen jaraba.''



''Ke ta shafa ai, ban tambayi mijina ba babu inda za na je.''



''Aatouh mai ruwan Neneh uban uwarki ne dai.''

''Ba ubanki ba.'' ta faɗa tare da murguɗa baki.



''Fatima ni kike zagi?."

''La Salimah kuji Neneh za ta min sharri fa, dan Allah wannan zagi ne?."



Neneh baƙin ciki ma ya hanata magana, sai can bayan some minutes sannan ta ce ''Dan kaza kazanki zo
ki fitar min a gida.''



''Babu inda zani, Salimah ɗauko min Apple dan Allah.''



''Kizo ki fita ko na tuno miki ranar da Ikimat ke naƙudar ki a duniya.''



''Da naji daɗi.''



Sai misalin ƙarfe shida da ƴan canji Liyana ta bar gidan ta koma nata da ita da Salimah.
Aliyu kam tun da ya ga ta fita da gudu bai ma bi ta kanta ba dan shi a rayuwarsa idan aka ce menene
dislikes ɗin da kake da shi a rayuwarka toh mutum mara nutsuwa ne, he's an introvert sam wuri mai
hayaniya yana nisantar kansa da shi ne, idan yaji ihu ko wani abu makamancin disturb, ya kan ɗan tsinci
kansa da ciwon kai, shiyasa idan kana magana da yawa ma baya hulda da kai.




Bayan ya gama haɗa tea ɗinsa ya sha sannan ya yi sallah raka'a biyu haɗe da kwanciya.

Washegari ma da sassafe ya bar gidan ya tafi gidan Mami da kullum ba ta da magana sai na Liyana.

Shima Amir kullum cikin maganar zuwa yake shi da mamansa, amma kullum cikin hana shi yake duba da
yadda ko sanin yanayin yarinyar bai yi ba balle a kai magana kan kawo manyan baƙi.




Ya maida hankali kan business ɗinsa sosai, dan ko da wasa ba zaka taɓa ganinsa wai da sunan he's not
busy ba because shima ya san he's damn busy with his business, trying to achieve more goals, kuma
babu laifi managers na yin abin da ya dace.

Dan a iya month, sai a samu riba fiye da five billion tun da shi ɗin akwai factory waɗanda su ne suke
ƙerawa daga kan android, laptos tablets, fridge, etc sune suke samar da shi.



HYDAR na da mahaukatan kuɗi, idan yazo wurin spending ɗinsu he spends it roughly, because shi bai
yarda da wannan al'adar ta Malam Bahaushe wai a tara musu ba, A'a idan sun fito sun zo duniya sun kai
munzalin nema su nema su tara na kansu.




Shi a stage ɗin da yake yanzu mace da abin da ya shafe ta ba sa gabansa, he just want peace, like original
peace of mind.




Idan yana son shakatawa ya kan fita shi da Amir, su zagaye Kano sometimes har da wajenta, amma still,
ko budurwa ko wani abu he didn't care about them.
Saboda ɗaure fuskarsa ma ba kowacce kilaki bace ba ke kawo kanta da sunan seducing ko soyayya ba,
noo he didn't do that.




Washegarin ranar ma Amir ya kira dan kansa wani mugun sarawa yake, tunda yayi sallahr subhi ma bai
tashi a barci ba sai kiran Amir da yayi akan ya taya shi handling, kallon laptop ɗinsa, sannan yau zai yi
conference video call da su saboda CEO ɗin Adafar Ventures Adam Ayan Muhammad Ali Humaish Al
khaizaran ( Beyond heart break). yazo all the way from Singapore akan wani sabon ac da suka ƙera za'a
basa sari almost fifty thousand pieces, kuma akan hakan ne zasu yi magana.



Washegarin ranar ma da sassafe bayan ta shirya cikin shigarta na as usual, fruit salad kawai ta sha
sannan tayi packaging milky donut, da kuma hollandia strawberry yourghurt ɗinta.




Bayan ta gama packaging komai ta zira slippers ɗinta ta nufo hanyar da zata sada ta da balcony ɗin da
zaka shigo parlourn ta buge mutum dake sanye cikin jumper ox blood color da sauri ta ɗago ta kallesa
sakamakon wayar da yake amfani da ita wanwar a ƙasan wurin.



Dubanta ta kai akan kyakkyawar fuskarsa wanda abin da idanunta suka gane mata suka girgiza dukkanin
tunanin ta..............




Mu haɗu a next page 😤



The regret na baku ginger kuwa😭
*THE REGRET*



(Dana sani).




PENDING AMARYA CE




*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers
born to share powerful words.💪




Alhamdulillah it's Friday again 🙌.




*ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMAD, WA ALA AHLI MUHAMMAD KAMA SALLAITA ALA
IBRAHIM WA ALA AHLI IBRAHIM INNAKA HAMIDUN MAJEED.*



*ALLAHUMMA BARIK ALA MUHAMMAD WA ALA AHLI MUHAMMAD KAMA BARAKTA ALA IBRAHIM WA
ALA AHLI IBRAHIM INNAKA HAMIDUN MAJEED 🦋*
The Noble Writters 🦚

Dedication is Our Strong 🤝




_ Pending Amarya 28_




Washegarin ranar ma Amir ya kira dan kansa wani mugun sarawa yake, tun da yayi sallahr subhi ma bai
tashi a barci ba sai kiran Amir da ya yi akan ya taya shi handling, kallon laptop ɗinsa, sannan yau zai yi
conference video call da su saboda CEO ɗin Adafar Ventures Adam Ayan Muhammad Ali Humaish Al
khaizaran ( Beyond heart break). yazo all the way from Singapore kuma akan hakan ne zasu yi magana.



Washegarin ranar ma da sassafe bayan ta shirya cikin shigarta na as usual, fruit salad kawai ta sha
sannan ta yi packaging milky donut, da kuma hollandia strawberry yourghurt ɗinta.




Bayan ta gama packaging komai ta zira slippers ɗinta ta nufo hanyar da zata sada ta da balcony ɗin da
zaka shigo parlourn, buge mutumin dake sanye cikin jumper ox blood color tayi wanda hakan ya sanya
ta ɗago da sauri ta kallesa sakamakon wayar da yake amfani da ita wanwar a ƙasan wurin.



Dubanta ta kai akan kyakkyawar fuskarsa wanda abin da idanunta suka gane mata suka girgiza dukkanin
tunanin ta.............."




Cikin muryarta da yake breaking ta fara magana "SUL....TAAAN...... whaaaa...... What...... U ... Doing
here..?."
Kallonta yayi da kyau sosai sannan ya ce " i will be the one asking you this, for almost 3 weeks you're not
picking up my calls, na miki wani abu ne?." Ya faɗa tare da riƙe kafaɗunta, da sauri ta ƙwace jikinta
daga hannunsa, sannan ta ƙara kallonsa cikin ido ta ce" ka amsa min tambayar mana." "Liyana i missed
you, dan Allah babyn Abbhi ki daina ignoring ɗina, let me hug you ko na ji sanyi a rain......" Bai ƙarasa
maganar ba wayar dake ƙasa ta fara ringing.




"Damn it." Ya faɗa a taƙaice sannan ya ɗaga wayar da ya kwankwatse a ƙasa ya ɗaga wayar a hankali
tare da juya mata baya.

"Hello Big Brother, in the next ten minutes please." Sun kai kusan minti biyu suna magana da yayan
nasa sannan ya katse wayar.

Juyowan da zai yi ya tarar har ta shige Jeep ɗinta gate man ya buɗe mata gate ɗin har ta fita da mugun
gudu.



A cikin motar ma tunani take kala kala, ko dai Sultan ne mijinta?, ko abokin mijinta ne?, wata zuciyar
tace " Nooo it can't be, and it will never be." Ta faɗa tare da dukan stiring motar.




"Ya Allah Have some mercy upon me, yah rabbi what's all this happening."

Ta faɗa tare da juya kan motar ta yi hanyar hotoro gidansu kenan.




Tana isowa gidan wani kalar horn ta danna mai shegen ƙarfin tsiya, bayan mai gadi ya buɗe mata motar
ta shige gidan da mugun gudu.
Motar Abbih da na Ammi duk suna nan a parke alamun babu wanda ya fita cikin su, ko da ta shigo ɗin
ma, cacar baki Rufaidhat da Ammi suke.



"Shegiyya farar karuwa, ai ke ɗin a tafin hannuna kike, uban waye bai san ba ki shigo gidanki da
budurcinki ba, ko an gayamiki banda labari akai, shashasha kawai, kuma ƴar ta ki da kike ikirari da kin
aurar, ina ne bata karaɗe ba hotels kala kala babu wanda bata sani b......."




Rufaidhat ba ta kai ga ƙarasawa ba Liya ta sauke mata mari zafafa guda biyu tare da ranƙwashi mai rai
da lafiya.



"Idan kina tunanin mahaifiyyata ta na a tafin hannunki ni à ina kike tunanin zan saki, ƴar balaja'u."

"Ke kuma Ammi mai na biye mata bayan kin san ƴar ƙwayace, huh."




"Ke kuma Ilham mai kika tsaya yi, farar kura."

Liyana ta faɗa tana ƙafe Ily da ido.

"Liya Ammi ta ce nai shiru faa." Ta faɗa ta na ƙara sakin kuka.



"Ina Abbhina."



"Ya na ɗakinsa ciwon kai ke damunsa, since day before yesterday."



"What ?! and non of you call me, ku gaya min kuma mun yi waya da shi jiya bai gaya min ba."



Rufaidhat dake tsaye wajen stairs Liya ta hankaɗe tare da faɗin " Stupid hag."
Da gudu ta shige corridor ɗin ɗakin Abbhi wanda yanzu ta kai four months ba ta shigo shi ba tun ranar da
ta bar gidan.



Ya na zaune akan Sofan bedroom ɗinsa yayi stretching ƙafarsa akan center table ya na shan lemon juice
ta shigo ɗakin.

"Amarya." Abbhin ya faɗa tare da buɗe hannunsa da nufin tayi hug nasa.



Da gudu ta ƙaraso tare da rungumarsa nasa tana ƙarewa fuskarsa kallo.



"Amma ba kai kama da mai rashin lafiya ba."



"Rabu da su sun takura min da kawo ƙara ne wallahi, that's why kawai nace musu hakan na ɗan huta."



"Abbihhhhh."

"Naaaaam."

Ya kwaikwayeta.

"Buh ka sani cikin damuwa manaaaa."



"It's okay dear Am sorry dear, and yanzu ina za ki je ?."

"Am planning naje school akwai test yau buh na ma fasa, i wanna spend my time here with you."

Ta na faɗin haka tayi kwanciyarta anan kan coach ɗin.



"Ko za ki shirya muje Domino's Pizza?."



"Banda kaya ai anan Abbhina."
"Ina ta so daman ranar da zan zo gidanki na ba ki kayan da na siya miki amma tun da kin zo sai ki saka shi
ai, ragowan kya tafi dasu."

"I love you wallahi Babana."



"Love you more."

Daga haka ya miƙe ya buɗe tankamemen press ɗinsa tare da ɗauko wani leda mai kyau.

"Na san palazzo trousers ne favorite dress ɗinki soo I picked them for you." Ya faɗa tare da zaro wasu
tsala -tsalan palazzo trousers masu kyaun gaske.

Daga sama har ƙasan su wani kalar beeds ne ajikin su masu walƙiya sosai daga ganin kayan za ka san
kuɗi sun yi kuka .



"Abbhina you're the best ever, Allah ya ƙara buɗi."

Bata jira amsar sa ba ta shige toilet ɗinsa dake ƙamshi mai daɗin gaske haɗe da canza shigarta zuwa
kayan da Abbhin ya siya mata.



Ko da ta fito sai yabon kyaunta yake.



Take taji duk wani damuwarta na ganin Sultan a gidanta ya kau.



In less than ten minutes ta shirya cikin kayan da suka mata matsiyacin kyau.



Already daman slippers ne aƙafarta and her bag to is the same color with her slippers.




A hankali suka sauko shima Abbhi ya mayar da rigarsa na kaftan yadin nasa mai mugun kyau da tsada, sai
car key ɗinsa dake hannunsa ta benz ɗinsa, hannunta acikin na Abbinta.
Ilham dai ita kam abaya ce ajikinta tana lunch tana daddanna wayarta dan chatting take da Sultan da sai
magana yake mata akan changes ɗin Liyana da kuma ganinta da yayi yau buh he didn't tell her a inda ya
ganta.



Ammi data fito da wani bowl ɗin fruit salad ce ta ce "Yallabai the lunch is ready." "Noo eatry muka nufa,
yau ɗin, since babu wadda ta damu dani a cikin ku."

Sidda kanta kawai Ammi ta yi sannan ta ce " Gimbiya mai ya kawo ki yau ɗin."



Fuska ta yi kamar mai son yin kuka sannan ta ce "nazo naga Abbhina ne faa Ammi."

"Is alright Allah ya kyauta ya kuma tsare."

"Am sorry Ammi ke nazo gani faa."

"Nooo da maganar farko ake amfani ai."

"Nope Ammi an wuce generation ɗin fa."



Kafin ta gama surutan ta har Abbhi ya wuce ya fita.

Rufaidhat ce ta zauna a living room ɗin tare da faɗin "su fanko har za'a tafi kenan, har an gama
barbaɗin."



Cikin wani kalar ɓacin rai Liya ta ce "Naji idan ma fankon da gaske ne ba ubana ne ya maida ni ba hakan
wasu kuma faaa?." Ily ta caɓe da faɗin "karuwan gidane idan an gama da iya sai adawo kansu."



Wani kalar tsawa Ammi ta daka musu.

Taɓe baki Liya tayi tare da faɗin " wallahi Ammi shiyasa ta rainaki, dama nice matar Abbhina da kin daɗe
da fita a gidan nan tsohuwar bazawwara."

Ajiye bowl ɗin Ammi ta yi tare da cire slippers ɗinta ta biyo Liyana, ai da gudu ta arce ta bar falon haɗe
da ƙwalawa Abbihnta kira.
Rufaidhat kuwa ta cika famm kamar zata fashe.

Sannan idanunta suka kawo wani ƙwalla mai mugun zafi tana dana sanin, sanin Nabil da ƴaƴansa da tayi.
Dama zamanta tayi a gidanta su cigaba da damawa da ita da Sufyan ɗinta.



Da gudu ta haura sama.



Koda ta shiga motar Abbih numfashi kawai take da sauri haɗe da dariya.



"Wallahi Abbhi matanka ba zasu kashe ni ba, muyi sauri ka ajiye ni a gidana."

Ta faɗa tare da rufe ƙofar motar.

A hanya ma kawai labarai suke ta yi, a hankali ta ce " Abbih ina ma muka nufa?."

"Wani sabon wurin shakatawa ne."

Bata bashi amsa ba ta cigaba da jin waƙar ta da ta jona da ear plugs ɗinta sabon waƙan da Davido ya saki
_Un Available _.




Basu wani jima ba suka ƙaraso Hydar's palace and garden, dake a titin hanyar minjibir wurin ya mugun
tafiya da tunaninta wurine dake cike da shuke shuke na ban mamaki na flowers mabanbanta tun daga
gate tulip flowers ke shinfiɗe a ƙasa ga mutane nata basu ruwa.

The place is damn beautiful.



Kallon Abbhi ta yi tare da faɗin "i love it, promise me every friday za ka ɗinga kawo ni nan please."

"Pinky promise dear."

Fitowa suka yi daga motan bayan ya faka motar.



Wurin ƙarshe ne wurin kyau amma gaba ɗaya wurin is artificial, komai constructing nasa aka yi.
"Kaɗan kika gani idan kinje VIP ɗin za ki riƙe baki."

"Abbhi dan Allah?, toh kai ya aka yi ka san nan ma bayan kana office kullum ko dai za'a wa Ammi ta
uku?."

ta faɗa tare da turo ɗan ƙaramin full lip ɗinta dake shafe da lipstick.



" Babyn Abbhi kina da matsala, oya let's goo."

Haka ta riƙe hannunsa suka wuce cikin wurin da ake biyan kuɗin.



Bayan sun shigo reception ɗin ma ce musu aka yi the boss is arround, ba zasu iya shiga VIP ɗin ba, indai
kuma suna don shiga sai dai 500k each person.



A haka ta matsawa Abbhinata sai da ya biya suka shiga wurin da idan ka gansa zaka manta Nigeria ne.
Kana ganin yanayin wurin ka san all the way from out side aka masa wannan aikin.



Dan wani kalan rafi aka yi a wurin sannan aka zuba yashin sahara, da duk idan kaga wurin za kayi tunanin
ocean ne sai dai ocean is big and wider than what she's seeing right now.



Komai na wurin looks classy ga bishiyoyin kwakwa da suke a wurin just saboda passion.



She was like woow, wayarta ta ɗauko ta fara sakin reels in less than a minute ta samu like fiye da
1million because ta riga da ta tafi viral in everything akan social media sai dai fa ita bata facebook da
tiktok.



Ko ina yayi kyau ga wasu boats dake ta yawo kan ruwan because sai da akayi ramin almost 20 kilometer
sannan aka yi constructing rafin.



Ga wasu kujeru a wurin na shakatawa, turawa ɗaiɗaiku ne a wurin saboda is a VIP place sannan aNƙara
zuƙa masa kuɗi duba da boss na nan.
Ɓangaren Mr. Ali namu kuwa tun safen da ya kira Amir bayan ya ɗaga suka yi magana ya kira Sultan
domin ya duba masa abubuwan dan yana da buƙatar fresh air.



Bayan Sultan ɗin ma yazo jogana sa yayi da laptop ɗinsa suka fara meeting ɗin daya kamata da CEO ɗin
Adafar Ventures Adam Ayan Muhammad Ali Alkhaizaran.




Combat ne ajikinsa sai wani white designer polo shirt sai ya saka Gucci slippers masu kyau haɗe da
ɗaukan key ɗinsa suka wuce a motarsa.




Wurin shakatawar sa ya nufa domin ya samu bacci, dan baccin hotel da ban yake da na gida dan da
akwai hotel a wurin shakatawar nasa.




Arround 10 O'clock ya ƙarasa cikin ƙantamemen luxury Joint ɗin nasa wanda daga gani kasan an narka
wasu mahaukatan kuɗi a wurin gina shi.




Direct lift ya bi ya shiga dan idan yace ta ƙofofi zai bi QR code zasu masa wahalan snapping ga
thumbprint ma zai ba shi wahala.




Danna bell ɗin da zai sada shi da réception ya yi.
Wanda a take suka kawo masa breakfast ɗinsa.




A ɗakin ma Amir cika mi shi kunne ya yi da surutai berekete babu kai da ƙafa, da dabara ya sa shi yaje
wurin rafin domin ya shiga boat ya za ga wurare, ya yi race da polo with so many games dai arround 2 O
clock zai sauko, dake Amir ɗan sharholiyya ne babu ruwan shi dan shi he's an extrovert kowa ba shi ne.

A take ya amince ya bar ɗakin nasa.




Bayan fitar Amir ɗinma wani bacci mai mugun daɗi ya wuce da shi, wanda kuma babu wani ɓata time ya
basa haɗin kai.




Liyana kam daman tun da suka zo da ta ga one hour ne ya cisu zuwa nan tace masa after four zasu koma
gida.



Arround one thirty ta fara jin yunwa ga Abbhi ya na can gefen rafin ya na amsa waya da business
partners dan sabon engine na atamfa yake son siya.



Ga shi babu wani waiter dake wurin balle ta kira a kawo mata strawberry smoothie ta sha.

A hankali ta tashi daga kan kujerar dake wurin tare da fara tafiya a hankali towards Abbhi at the same
time pressing her phone in a comfortable way.



Bigewa tayi da mutum ta yi baya kamar zata faɗi sannan ta dawo ta tsaya da ƙafafunta.

Sai da ya ƙarewa jikinta kallo, sannan ya kalli fuskarta dake sanye da farin glasses.
Ganin wanda ke tsaye gabanta ya mugun ɗaga mata hankali, amma sosai ta dake haɗe da murguɗa
bakinta tare da faɗin "kai kullum duk inda zan je sai ka bi ni are you for real?." Ta faɗa tare da ƙara
murkuɗa masa bakin.



Shanyayyun idanunsa dake nuna alamun basu daɗe da tashi a barci ba ya zuba mata su sosai wanda
hakan ya sa cikin ta ya yi wani mugun kaɗawa............"




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



Allah ya haɗa mu ranar monday mu fara Posting steadily.😪



*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya
tunanin

Please Login or Register in order to submit comment