You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai, nufuto ya fara yi hakan ya sa ta fara
janye jikinta ta na matsawa baya.

Daman tun da can a jogane yake zaune a falon tun cin farko da aka musu, Amir ya kira shi yake ta masa
dariya.

A zafafe ya ƙaraso wurin tare da faɗin ''You're laughing saboda an ci mu wasa right?."



''Noo wallahi am coughing ba dariya nake ba.''
''Za ki gane kurenki ne yanzu.''



''Dan Allah kayi haƙuri wallahi, fuskata kaɗan ya rage fatar wajen bai ɗaye ba dan zafi, please Yaya Alih.''



''Stop calling me with that stupid name da kike ƙoƙarin kakaɓa min.''




Sosai Liyana ta tsorata da lamarin Hydar.



Wani kalar ɓaci ransa ke ƙara yi, yadda take ba shi haƙuri at the same time take wani kalar murmushi,
abin da ya tsani Sultana ta yi.

Zuciya ce ta ɗibe shi hakan nan kawai ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga lafta ma ta kamar an aiko shi.



Dukanta kawai yake babu ji babu gani, Salimah da ta ji ihunta ta fito bawa Hydaar ɗin haƙuri, guda ɗaya
da Ya shauɗa mata a baya ba ta san time ɗin da ta shige ɗakinta ba haɗe da saka key.




Ga shi jikinta daman babu kayan arziƙi duk cinyarta sai da ya yi masa dukan lilis.




''Frog jump.'' ya faɗa a zafafe haɗe da cillar da belt ɗin hannunsa tare da shafa gemunsa.



''Ba ki ji abin da na faɗa bane!." Ya faɗa a tsawace.



Ta na layi ta tashi haɗe da faɗin '' Ni ban san yadda ake frog jump ba.'' ta ƙarashe maganar tare da
fashewa da kuka.
''Kin ga already Sallah ake kira, kafin na dawo daga masjid ki tabbatar kin fara frog jump ɗinnan, if not za
ki ga the worst side of me.''



Ya ƙarashe maganar tare da yin ƙwafa ya wuce masallaci da kayan jikin nasa.



Liyana cinyoyinta kawai take bi da kallo haɗe da yin da na sanin fitowar da ta yi, indai wannan ne aure
wallahi da ba ta yi ba, sanin miji ko iftila'i'.




Fashewa ta ƙarayi da kuka mai tsuma zuciya.



Ƙarar buɗe ƙofar falon da ta ji ne ya sanyata tashi da sauri ta na sharɓar majina haɗe da yin frog jump
ɗin.

Shigowa ya ƙarasa yi cikin takunsa na ƙasaita haɗe da faɗin ''Make sure kin zagaye falon nan sau uku.''



A tunaninta ko wucewa sama zai yi sai ta ga ya ma jawo ragowan fresh milk ɗinsa ya na sha.




Sai da ta zagaye falon sau biyu sannan ta ji ƙarar buɗe ƙofar ɗakin Salimah.



''Salimah ina za kije?." ''Yaya Hydar girki zan yi na ga dare ya fara yi.''



''Je ki huta yau ita za ta yi girkin, You over there."

Juyowa ta yi ta ƙafe shi da manyan idanunta.
''Ma za ki tashi ki shiga kitchen ki dafa min abatcha, Salimah akwai fresh cassava da na kawo yau a ina
kika ajiye?."



''Store ɗin ajiye potatoes yaya.''

''Mai kuma abatcha ɗin?." Ta faɗa ta na gwale idanunta.



Bai ma bi ta kanta ba ya wuce ya fara tafiya towards kitchen ɗin.



A hankali ta tashi dan ba ta son jikinta ya ƙara tsami hakan nan ta na ji ta na gani.

A hankali ta shiga ɗingisawa tare da bin shi a baya har suka ƙaraso cikin kitchen ɗin.

Bai zame ko ina ba sai store ɗin potatoes da doya, wasu manyan cassava's ya ɗebo guda uku tare da
ajiye mata su akan kitchen island.

''Start.''

''Wallahi ban san mai ne abatcha ba, please karka dake ni.'' ta faɗa haɗe da fashewa da kuka haɗe da
matsar da kanta gefe ta na mai gaucewa marin da yake shirin kai mata.

''Shut up.'' shiru ta yi tare da faɗin ''Toh ya zan yi?."

''Ɓare rogon tukunna.''

A hankali ta shiga ɓarewa slight mistake idan ta yi kuwa sai ya ranƙwasheta ko ya ɓalle ta da harara.



Wani bowl ne ya zame a hannunta, still ba ta damu ba ta cigaba da gurza cassava's ɗin.



Ranƙwashi ya sakar mata hakan ya sa ta ce '' zan kwashe idan na gama.''



''Who care's idan yaso ki fasa gaba ɗaya kayan kitchen ɗin in dai tiles ɗin ba zai samu karcewa ba am
okay, c'mon do something fast.''



''Yi nake faaa.'' ta faɗa hawaye na zubar ma ta, ta sa hannu ta goge.
Haka ya yi ta monitoring ɗinta a kitchen ɗin har abatcha ɗin ya zama done, wani ɗan wood plate ta
ɗauko ta zuba masa abatcha ɗin.




Bayan ya ga ta juye acikin plate kamar yadda ya umarce ta, wucewa ya yi ya zauna akan kujerar dinning
dake cikin kitchen.




A hankali ta shiga jan ƙafar har ta tako zuwa wajen da yake, ajiye plate ɗin ta yi a hankali sannan ta fara
ƙoƙarin barin wajen.



''Ina za kije?."

''Hutawa nake son yi kafin nayi sallah.''



''A ina za ki huta ɗin?, not when I'm arround.'' ya yi maganar haɗe da kai spoon ɗin abincin bakinsa, da
sauri ya furzar haɗe da faɗin ''haka nace kiyi?, ko kin haukace ne da za ki zabga uban gishiri acikin abinci
haka?."




''I use the measurement da ka ba ni." Ta faɗa haɗe da ƙoƙarin buɗe baki za tayi kuka.



''Ko da wasa naji kin ɓare wannan bakin naki mai kama da na ɓeraye sai kin gane kurenki da daddaren
nan.'' da sauri ta kame bakinta haɗe da gyaɗa kanta ta na ƙara waro idanunta akansa.
''Salimah!, Salimah." Ya na mai ƙwala ma Salimah kira, Salimah dake rakuɓe afalo tun ɗazu ta shigo haɗe
da kallon Aliyun.




''Bayan waɗannan kayan kitchen ɗin da akwai wasu ne ko su kenan?."



Salimah ba tayi tunanin komai ba ta ce ''Eh yaya akwai wasu a storage.''



''kina wanke waɗan nan da waɗancan ne ko kuma ba kya wanke su?."

''way'anda ake amfani da su kullum, kullum ake wanke su, su kuma na cikin cabinet sai every month
ending ake wanke wa, su kuma na store ɗin are still new.''



''Okay nagane shiga ki kwaso min.'' har Salimah ta yi hanyar store ɗin da aka ajiye sauran kitchen utensils
ɗin sannan Hydar ya ƙara faɗin ''Noo Salimah just leave it you can go, ba sai kin kwaso ba.''



''Okay Sir.'' daga haka ta fice daga kitchen ɗin ta na tausayawa Aunty Liyana. (Liyana nima kin bani
tausayi a swear ).😂




Kallonsa kawai take babu ko ƙyaftawa, she can't believe this guy na juya ta fiye da yadda ya juya stearyn
mota a rayuwarta.



Muryarsa ce ta katse ta daga tunanin da ta tafi, ''Kina jira ne na kwaso miki kwanukan?."



''Mai zanyi da su toh?."



''A kaina za ki juye, je ki kwaso kwanukan ki wanke su yanzu ba sai gobe ba, sannan ba na son maimaita
kaina, am I clear?."
''Yess.'' ta faɗa a raunane.



''Good.'' da ga haka ya fice daga kitchen ɗin domin ɗauko wayarsa da car key ɗinsa ya siyo fruits ya
dawo.



''Mugu kawai azzalumi, kuma Allah sai ya saka min, darajar ka ɗaya wallahi ina sonka da gidan sai ya
mana kaɗan wajen yaƙi.'' ta faɗa ta na sharɓe majinarta.



Muryarta har ta fara dashewa, ta kusa mintuna goma ta na kwaso kayan amma still ba su ƙare ba.

A lokacin har kusan ƙarfe goma na dare ta gota, wanke kwanukan ta fara yi amma tsantsi yake mata dan
kusan plate uku sun fashe daga farawarta.



Ganin ya yi kusan minti biyar da fita da motarsa ya sanya ta kwaso wasu daga cikin kwalayen warmers
ɗin ta fara ƙoƙarin haurawa dasu saman ɗakinta.



Ta na yi ta na waigen entrance ɗin falon a haka har ta kai kusan kwalaye shida dukkanninsu da warmers
aciki.



Ana bakwan ne taji shigowar motarsa cikin compound ɗin da gudu ta dawo domin komawa kitchen ɗin
sai dai kashh ta na zuwa dai- dai tsakiyar falo, ya buɗe ƙofar ɗakin haɗe da ƙafeta da idanunsa masu
rikitarwa.....
*Durrah Hydar.*✍️




"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."




Not edited 🤍🙏



*THE REGRET*



(Dana sani).




~PENDING AMARYA CE~
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*✍️




*(J.W.A)*




*THE NOBLE WRITER'S TEAM*💎




Pending Amarya 38




Ana bakwan ne taji shigowar motarsa cikin compound ɗin da gudu ta dawo domin komawa kitchen ɗin
sai dai kashh ta na zuwa dai- dai tsakiyar falo, ya buɗe ƙofar ɗakin haɗe da ƙafeta da idanunsa masu
rikitarwa.....




''What are you trying to do?." Ya tambaye ta da muryarsa mai amo.

Cikin inda-inda ta fara magana ''Ai...... Ai....... Daman ba su kaɗai bane kayan kitchen ɗin nawa ba akwai
wasu a ɗakina.''



''Su kenan?." Ya ƙara jefo mata wani tambayar, ''Yee....yeeaah, i think gaba ɗaya na kwaso.'' ta ƙarasa
maganar ta na sosa goshinta, da gumi ya ɗan ɓata, alamun dai rashin gaskiya.
''Kin gama wanke wanken?." Ya yi tambaye ta haɗe da matsowa sosai wajen da take, komawa baya ya yi
kaɗan haɗe da kallon cikin idonsa ta ce ''A'a.''



Ƙarar saƙo ne ya shigo cikin wayarta dake yashe a ƙasar Turkish carpet ɗin falo, hakan yasa idanunsa
sauka kan saƙon dake ɗauke da Instagram icon, da ya fito cikin jerin notifications.



A hankali ya tako zuwa wurin da wayar take haɗe da ɗaukar wayar, wani kalar runtse idanunta ta yi haɗe
da juyar da kanta gefe ta kalli ɗayan gefen, Allah Allah kawai take Allah ya sa ba Nifraz bane ba ya tura
ma ta saƙon.



''Mufti menk has shared a reel.'' shi ne abin da ya gani rubuce akan fuskar wayar, cikin muryarsa mai
daɗi ya ce ''Unlock the phone.'' ya yi maganar ya na mai ƙafeta da idanunsa.



''Buh that's my private life, mai za ka yi da wayata?." Ta faɗi maganar kamar za ta fashe da kuka.

''Don't let me repeat myself, I said unlock this phone!." Ya yi maganar a ɗan tsawace.

Amsar wayar ta yi haɗe da buɗe masa wayar, daman kuma ba ta fita daga chat ɗinta da lily ba a IG ɗin,
soo kawai scrolling ya yi tayi ya na komawa can bayan chats ɗin, yadda ka san ta fizge wayar daga
hannunsa haka take ji, dan ko Ammi idan ta amshi wayarta ta na dubawa zuwa take ta haɗa ta da Abbhi
ya ƙwato mata ballantana wannan hallittan.

Cikin wata kaliyar shaƙaƙƙiyyar murya ya ce ''Get lost.'' ''To where?, ina zanje babu wayata, ko kai ka siya
min, wadda aka samin ma alefe ba gane kanta nake ba, idan ma ka ɗauka ita ce just gimme my pho....''
ba ta ƙarashe maganar ba ya bata mari lafiyayye a fuska haɗe da nuna mata hanyar kitchen.

Jiki a sanyaye ta bar wajen hawaye na zuba a fuskarta, bayan ta ƙarasa kitchen ɗin ma kuka kawai take
haɗe da faɗin ''Ni anya wannan hanyar da Lily ta ce in bi ba barinsa zan yi ba, haka kawai a maida
martani ayi ta saka jikina tsami, da yarinta na, za'a maida ni tsohuwa, ni dai Neneh sai da Allah ya ishe
min.'' ta ƙarashe maganar ta na goge hawayenta.



Sai wajen ƙarfe 12 na dare Liya ta kwanta bacci ba tare da ta hau online ba.
******



Ɓangaren Yaya Alih kuwa, tun bayan da ya saka ta wuce kitchen yake ta faman karanta chat ɗinta da lily,
abin na basa nishaɗi, the Lady we call Lily is soo simple buh her fake life pass her power, sometimes su
kan faɗi kalan guy ɗin da suke so with some naughty talks, he can even say those girls are ƴan iska girls.



Wani voice ɗin Lily ya kunna wan da take bawa Liyana shawarar, ta ɗan ɗinga saka sexy wears, da kuma
yawan yawo arround in da yake, duk abin da zai mata ta maida shi wasa, he will fall for her, idan kuma
wannan hanyar bai ɓille ba sai abi ta wata hanyar.




He just smiled dan ganin wawtan ƴan matan biyu da ya gani, wai shi za'a yi seducing, yarinyar da ko
shape ɗin arziki ba ta da shi, jikinta kamar na ƙwailayen shekara 14 , ita take cewa zata yi seducing ɗinsa,
that girl most be in a mental health sannan ta gudo.



Tsaki yaja haɗe da faɗin ''Filthy thing.''

Kallon agogon ya yi ya na mai ganin ƙarfe 1na dare har ya wuce, hakan ya sanya sa wucewa toilet ya yi
wanka haɗe da yin alwala tare da saka kayan baccinsa, sai da ya yi sallah sannan ya saka sleep mask
ɗinsa ba tare da ya bi ta kan wayar ba kuma.



Arround ƙarfe 4 na asuba ya ji wayarsa ya na ringing ta shi ya yi daga barcin haɗe da ɗaga wayar dake
kan bedsides ya na mai karawa a kunnensa.

Muryar Abbhi ya ji mahaifin Liyana ''Assalamu alaikum Son.''

''Wassalamu alaykum Abbhi.''



''Son sorry na tashe ku a bacci, ina daughter na take?."

''Tana nan lafiya Abbhi.''

''Okay shikenan, dama tun jiya nake ta ma ta magana a online she didn't reply, kuma i called her, almost
20 missed call she didn't respond, ko bacci na kasa yi shi ne na sanya Ilham ta bani number ka.''
Sai da ya ɗan ja tsaki ƙasa - ƙasa, sannan ya ce ''Wallahi Abbhi ta na lafiya kawai dai da yamman nan ne
ba ta ji daɗin jikinta ba, shi yasa, dan har hospital muka je sai arround 10 muka dawo na dare, ta ce na
gaya maka ma na ce kar a gaya dan kar a ɗaga muku hankali.''



''Ma shaa Allah, amma jikin da sauƙi ko?." ''Eh Abbhi yanzu ma bacci take da na tashe ta.''

''Just leave her ka ji, Allah ya yi albarka.''

''Amin a kwana lafiya.''




Ilham, Ammi har da Rufaidhat duk suna falon dan babu wadda ya sanya ta rintsa a cikinsu, dan different
types of taught ke zuwa cikin kansa, ko ta yi hatsari ta na hospital, ko ta mutu a ɗaki ba'a sani ba.



''mtsww akan wannan ka sa muka kasa runtsa idanu, toh wallahi, Allah ya ishe min baccin da aka ƙi sani
yi kuma, ƙilan ta ma club taje tayi tatil sannan ta yi dare, shi ma mijinta dake ɗan nanaye ne, ya rufa
mata asiri.''



''Rufaidhat watch your tongues when it comes to my daughter, kowa yaje ya kwanta.''

Daga haka ya haura saman side ɗinsa.



Ita ma Rufy ta tashi haɗe da hararar Ammi tare da faɗin ''Babu arabi ba boko, kin ga kinje kin haifi fitina
a maimakon Fatimah.''



''Ai abin sa'a ne taɓa nonon sirika, ke kici sa'a ma ki haifi ya' har ta zama fitinar.'' Ily ta faɗi hakan ta wuce
nasu ɗakin dan ita ma ta san maganar akwai nauyi.




***_______****
Ɓangaren Liya kam ji take kamar za ta mutu saboda ciwon jiki ga wani sara ma ta da kanta ke yi kamar
zai cire, sallar asubar ma a daddafe ta yi shi da misalin shida na safe, sosai ta ke jin rashin samun kuzari a
jikinta, barimma Kwankwason ta da take ji kamar an cire ma ta spinal cord ɗinta, da ƙyar ta samu ta yi
wanka da ruwan zafi sannan ta shirya cikin wani plane abaya mara kwalliya, ko gashinta ba ta busar ba ta
koma kan gadon haɗe da jan bargo domin wani kalan bacci ke fuzgarta.



Ko mintuna biyu ba ta yi ba da daddaɗen baccin da ya ɗauketa ba ta ji ana ƙwanƙwasa ma ta ƙofar
ɗakinta, wani ɗan guntun tsaki ta ja haɗe da faɗin ''Waye!." Ta ɗan faɗa a tsawace, wanda ke bugun ya
cigaba da ƙwanƙwasawa countinuesly ba tare da ya gaji ba, "wai Salimah wannan wani kalar karuwanci
ne haka da safiyar Allah kina tashin mutum daga bacci , da wani ɗan iskan bugu."



Wani knocking aka ƙara mai shegen ƙarfin da ya fi na baya, hakan ya sata tasowa afusace haɗe da murɗa
handle ɗin ƙofar da ƙarfin tsiya, saboda masifar da take cinta har rufe idanuwa take, " wai ke Salimah,
wannan wani kalar iskanci ne mara license da za kina min a cikin gida dan kut....."



Ba ta ƙarasa ba idanunta suka sauka kan Hydar dake tsaye da kayan gym, hannunsa riƙe da wayarta ya
na ta scrolling, " countinue what you doing, ki ƙarashe zagin." Ya yi maganar ya na ɗago manyan
idanunsa haɗe da sauke ma ta su akai, sosa wuyanta haɗe da sauke idanunta aƙasa dan har ƙwalla ta
fara zubar ma ta a idanunta tun kafin ya fara mazgarta.




" Welcome." Ta yi maganar a sanyaye haɗe da fara wasa da fingers ɗinta, " Your Dad wants to talk to
you." Ya yi maganar tare da miƙa mata wayar.

" Allah sarki Abbhina." Ta yi maganar wani ɗan guntun ƙwalla ya ƙarasa sauko ma ta, tare da fara ƙoƙarin
juyawa ta shige cikin ɗakin nata.



" Ina zaki je ?."

" Ɗakina zan shiga na yi wayar."
" Tsaya anan ki yi ki miƙo min."

Kamar ta zunduma ihu haka take ji, a nan ta tsaya sannan ta yi dailing number Abbhinata, line busy
Abbhin ya danna ma ta sannan cikin second biyar aka biyo kiran.



" Hello dear."

Abbin ya faɗa a sanyaye, fashewa ta yi da kuka haɗe da faɗin " Abbhina I missed you, da kowa ma gaba
ɗaya, please ka ce masa ya kawo ni yau naga fuskokin ku abeg."



Ta yi maganar ta na jan majina a kiɗime Abbhin ya ce ''Is anything wrong over there?."

Satar kallon Hydar ɗin ta yi sannan ta kalli wayar dake handsfree duk conversation ɗinsu ya na jinsu, a
hankali ta ce ''Nooe just wanna say hi to you guys, ina ɗan zazzaɓin dare ƴan kwanan nan.''



''Okay well, amma kwana za ki yi, muje shan ice cream, idan ƙasar za mu bari ma duk you're okay, ni dai
farin cikin ki shi ne nawa daughter, you're the only one for me, soo kar ki yi zazzaɓin da zai sa Abbhi ya ji
kamar ya rasa ki okay?."



Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce ''Toh Abbhina, sai na zo.''

''Okay bye dear, kar ido na ya bushe fa in ta sa rai.''

''Kar ka ji komai my rock.''

Daga haka suka yi dariya gaba ɗaya, sannan ta katse wayar, dan har ga Allah ta ɗan ji sanyi a ranta.




Wani kalar harara ya watsa ma ta sannan ya amshi wayar da ta miƙo ma sa ''Ke ko kunya ba ki ji ba
mahaifinki ya kira ki ba ki gaida shi ba kin fara koro bayani, ke ba ki yarda ba ubanki ne ƙawarki ko?."

''Amma wannan ai zagi ne.''

'' Shut up while I'm talking joor, kafin na buge miki bakin nan na ki mai kama da na jaɓa.'' daga haka ya
zura wayarta a aljihunsa tare da ƙara faɗin ''I need custard, with fried plantain for my breakfast, now!."
Daga haka ya barta a wajen baki sake.
Juyawa ta yi ta kalli wall clock ɗin ɗakin ta ga 6:06 na safe, by this time ai bacci take mai daɗin gaske a
lokacin da take gidan Neneh, dan ko gidan Ammi ma ba kullum take barinta ta yi bacci ba.



''Which kind wahala be this one nah, ni yaushe na iya ma wani dama custard da za'a ce na dama.''

Ta yi maganar ta na goge gumin da ya keto ma ta, ganin ba ta da mai amsa mata ne ya sanyata nufar
kitchen ɗin da har Salimah ta gyara shi dan jiya babu wani gyara shi da ta yi.

Store ɗin ta shige haɗe da ɗauko plantain ɗin ta fara ɓarewa a cikin bowl haɗe da yanka shi kalar yankan
da ake masa, ruwan zafi ta ɗaura akan gas sai da ya ta fasa ta ɗauko garin custard ba tare da kwaɓa shi
ya zama kamar gasara ba ta dama shi cikin ceramic bowl ɗin da suke haɗa fruits salad, wani kalar gudaji
ya yi duk babu kyaun gani, kafin ta juyo daga dama custard ɗimma har plantain ɗin ya fara ƙonewa, da
sauri ta kwashe haɗe da zuba su acikin plate, ganin custard ɗin ya yi wani iri ya sanyata zubar da shi
haɗe da wanke bowl ɗin, gashi wayarta na hannunsa balle ta kira Ily, jin muryarsa kamar ya na waya ya
sanyata saurin zuba custard ɗin haɗe da zuba masa ruwan sanyi sannan ta yi sauri ta dama duk da ya yi
ruwa bai yi wani kaurin na muzo mu gani ba.



Wani jar ta gani jere guda biyu a waje ɗaya hannunta kawai ta kai ga na farko ba tare da ta wani duba
menene a ciki ba ta juye haɗe da stiring ɗinsa ba tare da kuma ta damu da taji taste ɗinsa ba.



***_____***



Zaune yake akan kujerar dinning ya na kallon laptop ɗinsa yadda ya saba duba factory ɗinsa na China,
hannunsa na dama kuwa na manne da kunnansa ya na magana a waya, yadda yake amsa wayar ne ya
bata tabbacin cewa Amir ne ke ma sa magana kuma kusan ma akanta ne idan za ta iya zama judgmental,
wani kalar murmushi ya saki tare da faɗin ''Amir ba na son ƙorafi, I've made it clearly to you babu inda
zanje da wannan yarinyar, yadda ba ta jin magana, ta zo ta yi abin da zai sa a koro ni daga can, Amir ka
riƙe advice naka please.''

Daga haka ya kashe wayar, haɗe da kulle laptop ɗin, A hankali ta tako har inda yake tare da ajiye tray ɗin
akan dinning ɗin, wani banzan kallo ya wurga ma ta dan yanzu wani kalar tsanarta ya ji ya na masa yawo
a kogon zuciya.



Bayan ta ajiye breakfast ɗin a hankali ya ɗauki tea spoon haɗe da shan custard ɗin, a million ya furzar
haɗe ƙafeta da wani shegen kallo ''Dan ubanki uban mai ya kawo gishiri cikin wannan custard ɗin!." Ya
faɗa a tsawace shiru ta yi ƙwalla na zuba a idanunta a zafafe ya ƙara faɗin ''Ba magana nake miki ba."
Muryarta na shaking ta ce ''Dan Allah ka yi haƙuri wallahi ban iya ba Salimah ce ke yin komai ba ni ba.'' ta
ƙarashe maganar idanunta na zubdar da hawaye.



''Salimah!.'' Salimah ce ta fito jikinta na ɓari dan tun tuni ta na jikin ƙofa saboda wani kalar tausayin Liya
da take ji, so take ta faki idonsa ta shiga kitchen ɗin amma ta kasa saboda ya na zaune a falon.( TOH
Salimah mun ji uzurinki koma gefe 😵‍💫 ).




Kallon Salimah ya yi sannan ya cillo ma ta dubu goman da yake aljihunsa tare da faɗin ''Ki koma gidan
Neneh za ta cigaba da aikace-aikacen gidan nan, ko kuma shirya kayan ki kawai zan sauke ki.''

''Toh yaya.'' Salimah ta faɗa haɗe da wucewa cikin ɗakin domin kwashe kayanta.



Wayarsa ya ɗauko tare da kiran mutane kusan huɗu, cikin ƙanƙanin lokaci wani dattijo da samari uku
suka ƙaraso cikin falon, ''Alhaji barka da safiya.'' suka haɗa baki wurin faɗa.



Kallon ko wannensu ya yi sannan ya ce ''Barka dai Baba, daman ina son na sallame ku ne na ƴan watanni
amma akowani wata za'a saka muku kuɗin aikin ku, za ku iya tafiya.''

''Toh mun gode Alhaji Allah ya ƙara buɗi, ɗan shuwa jikan shuwa.''

Bayan sun fita juyowa ya yi ya ga har a lokacin kuka take ''From today babu baccin banza a cikin gidan
nan, girki, buɗe gate, bawa flowers ruwa, wanki, guga, komai ke za ki yi, tun da aure kika zo yi ba hutu
ba, am I clear?."



Bai jira amsar ta ba ya yi ma ta pointing kan kujerar dinning ɗin a sanyaye ta zaune sannan ya turo ma ta
tray ɗin abincin tare da faɗin ''Cinye abincin nan, tun da ba akuya aka kawo miki ba da za ki kawo min
kalar wannan abincin.''



A hankali take cin abincin ba tare da ta ɗago ta kalli fuskar shi ba, cokalin custard ɗin da take sha ne ya
faɗi aƙasan tiles wanda hakan ya sa ya ba ta wani kalar dirty slap, wanda sai da jinta ya ɗauke na wucen
gadi.
A daddafe ta gama cin abincin da ya tilasta ma ta, sannan ta shige banɗaki ta yi wanka haɗe da shiryawa
cikin wani abaya, shiru shiru ta ji har kusan ƙarfe shida na yamma ba taji ya ce ta fito ta tafi gidan Ammin
ba , sannan kuma bai ba ta wayarta ba.




***________****




Tsaye ta ke a jikin ƙarfen balcony ɗin dake compound jikinta sanye yake da abaya ɗin jikinta tun na ɗazu,
tun ƙarfe sha biyu ya fita daga gidan domin kai Salimah gidan Neneh, har yanzu bai dawo ba, horn ɗin da
taji ne ya sanya ta firgita, dan wani kalar tsoronsa da tsoron gidan ne suka ɗirar ma ta arai, ita kaɗai
ƙwal kamar mayya.



Da ɗan sauri taje ta buɗe ƙofar ta kusa mintuna uku ta na buɗe shi saboda nauyinsa da yawa yake, da
mugun gudu ya shigo cikin gidan, goge gumin da ya zubo ma ta tayi haɗe da kulle gate ɗin da ƙyar
sannan ta fuskanci ƙofar shiga falon dan shi ya jima da shiga cikin gidan.



Tsaye ta tadda shi ya na haska falon da wayar hannunsa ''Ni kike jira na kunna miki inverter ko ba ki san
aikin ki ba?."

Ya yi maganar ya na ɗan takowa wajen da take, ''Dan girman salatin Annabi kar ka dake ni.'' ta yi
maganar ta na ɗan ja da baya zuwa wajen stairs, wani kalar tsantsi ne ya kwasheta kanta ya buge da
benen farko wanda hakan ya sanyata sakin wani kalar razananniyyar ƙara........




*Durrah Hydar.*✍️
"Tomorrow is not promised but I will keep the things that I need."



*THE REGRET.*



Pending Amarya ce ✍️



JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION.

THE NOBLE WRITER'S TEAM 💎




*** Pending Amarya 39***




Tsaye ta tadda shi ya na haska falon da wayar hannunsa ''Ni kike jira na kunna miki inverter ko ba ki san
aikin ki ba?."
Ya yi maganar ya na ɗan takowa wajen da take,

Please Login or Register in order to submit comment