You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazata kula ta ba, murmushi tayi kafin tace, Abbey yace zamu fara daukan karatun boko tare idan malamin dake mana karatu yau yazo, kema kinga dakin iya abubwan daza'a koya maki shikenan saiki shiga makaranta mu,kinga saimu dinga tafiya tare,
Sai asan nan Abrish ta juyo da dan murmushi a fuskar ta, tace da gaske nima zan shiga makaranta, ehmana kema zaki shiga makaranta dan yanxu ilimi shine jigon rayuwa, fatana dai ki dage da karatu sosai kinji ko sister, dan na kosa ki shigo makaranta mu in hadaki da kawaye na,
kina da kawaye kenan, eh ina dasu, su nawa ne kawayen naki, su biyar ne,
"Zarah,Bloody,Meenarh,sopy, sai umme,"
"Kuma nima zasu zama kawaye na, sosai ma ai sunsan labarin ki na fada masu a waya, yanxu duk basa nan ne saboda anyi hutun shcool,duk suntafi hutu amma da an dawo duk zaki gansu,
"To shikenan allah ya kaimu,ameen sister na,
"Suna cikin hiran su Ashtar yayi sallama ya shigo, Nasra ce kawai ta amsa, Abrish ko,yita yi kamar bata wajen, gaishe shi Nasra tayi ya amsa,tambayan ta yayi hajja fa,tace tana ciki, mikewa yayi ya wuce dakin hajjan,
Zaune ya ganta gefen gado sai jan carbi take,dan tunda ta laika taga Abrish zaune taki fita, ta gwam mace tayi tajan carbi abunta ko tasami rahaman allah gobe kiyama,
Da dai tafita ta hadu da aljanar can,
Zaunawa yayi gaifen ta kafin ya gaishe ta,amsawa tayi ciki ciki, dan bata manta cinye mata naman ta da sukayi ba jiya,
Shima shareta yayi,kafin yace maiyasa maiki jiya ne, aiko an tabo wa hajja inda ke mata kaikayi, nan ko ta karkace ta ringa ratabo mai zance tun daga a har z, sannan ta kara dacewa in da zaka taimaka kayi wa uban ka magana wata kila yaji naka, zaman yarinyan nan a gidan nan bala'i ne, har gwanda ya hadata da iyayen ta su koma kaduna tare, inba haka ba wllh yan gidan nan mun shiga uku a hannunta dan bata da tausayi ko kadan,
Shi dai baice komai ba, saide yariga yasani daman zata aikata har abun dayafi wannan, to ita wai wacce irin yarinyan ce,da alama duka iskokan jejin nan ne akanta shiyasa tama koma aljana gabaki daya, shi yana ma kokonto anya ba aljanar bace ba wannan da alama anyi musanya da yar aljanu ba tare da iyayen ta sun sani ba, amma wannan bala'i har ina,
"Mikewa yayi ya fita a dakin, sake da baki hajja ta bishi da kallo, shine zai maidani yar iska ko,ga mahaukaciya na sake baki na zubumai zance amma ko mataki baice zai dauka ba,
Yarinyan nan ta gama da kowa na gidan nan, allah ne kawai zai kwato su a hannunta,
Shiko daya fito falon, kallon Abrish yayi ,wace itama ta dago kai ta kalle shi, wani murmushi tayi mai, kafin kuma ta gimtse fuskan ta, shima kwafa yayi yasa kai ya fita a falon da tunanin irin matakin daya kamata ya dauka akanta,


Misalin karfe uku da rabi na yamma, su Abrish ne zaune a gaban malamin dake koya masu karatu, yau tunda yazo baice masu kala ba, sai kallon Abrish yake shikade sai surutu yake acikin ran shi, saurayi ne da bazai wuce sa'an Ashtar ba, saide shi baki ne yana da kyau ba laifi,
Wai zuki ,malam kaga kyau anan wajen ashe su Nasra munana ne, suna da wannan balarabiyan a gida daman, ai kasami wannan malam ka aje a gida to ko ganin ka baza'a dunga yiba wllh, ina da wannan ai zan shana abuna,


"Malam" "malam"
na'am , na'am,ya fada azabure kamar wanda ya tashi a bacci, malam magana nake fa tun dazo ka tsare wani waje da ido, oh to eh, a inama muka tsaya,
Aidaman bamu fara karatun ba, yau ga wacce zaka fara yi mawa,batasan komai ba, daga a b c d, zaka fara mata,
"Wata uwar harara Abrish ta maka wa Nasra kafin tace,mai kika maida ni ne, ko ance maki kowa irin kune,
Abrish bafa wani abun nake nufi ba,dole daganan za'a fara maki kafin ayi gaba,
"Allah koh"
To bani litafin nan, bashi ne wanda za'a koyamin acikin shi ba,
"Eh shine"
"To mugani"
Mika mata litafin english din Nasra tayi batare da tace komai ba, amsa tayi ta fara bude shi, tsawon mintina goma zuwa ishirin,
Kafin ta mika ma Nasra , tace saura wanne kuma, banga ne ba, ina nufin na gama da wannan basai an koya min ba na koya,
Dariya malamin yayi kafin yace amma yarinyan nan kin cika abin dariya wllh, kallon shi tayi kafin tace,
"Am not joking with you so please mind your on business.

Daga Nasra har malamin sake baki da hanci sukai, tare da kallon ta da dunbin mamaki,yarinyan da akace bata iya komai ba itace take zaro turanci haka.






Kut🤭 jama'ah Abrish dayin english, gobe sai makaranta👩‍🏫, amma su Bloody ko sun shiga uku😱 tunda suka kasance kawayen Nasra da Abrish, allah yaso babuni a ciki.🤣🤣




*aradu yau in banga ruwan Comments ba gobe babu posting* *ba da wasa nake ba*🤏😎
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: """"""""""""""""""""""""""""""""""""


🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI*🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)


♧Pege♧25.

*****

"Abrish kece kikayi magana yanxu,"
"are you seprise?"
"Nasra tama rasa mai zatace, anya Abrish mutum ce kowa, ko dai daman can ta iya karatu basu sani ba, wannan abun da daure kai yake,"
Mikewa Abrish tayi zata wuce sai kuma ta dakata tare da juyo wa, malamin nan ta kalla wanda tun dazu ya kasa cewa komai yana tunanin wannan wacce irin yarinya ce, in banda Alhaji da kanshi yayi mashi bayani to daya karyata hakan, amma yasan Alhaji bazaiyi mai karya ba,to ya haka, yana cikin wannan tunanin yaji maganan da takusa sashi sakin fitsari a wando,
"Abrish tace, kai jima na, maima kake cewa, watakon in kana da kamar ni zaka shana abun ka ko, watakon kai gaka tantirin dan iska, duk zuwa gidan nan da kakeyi da sunan karatu ashe kalle min sister kakeyi, to wllh na kara ganin ka acikin gidan nan ubanka zanci,
Yauma kayi sa'an ina cikin farin ciki ne amma da babu wanda ya isa ya hanani cin uwar ka a gidan nan,
Ke nifa ban gane maganan da kike yiba, kada ki fadamin maganan banxa,yanxu nan saina...... marin da tayi maine ya hana shi karasa maganan da yayi niya, bai gama far fadowa daga suman wucin gadin da yayi ba, yakara jin saukan wani marin da sai da hakorin shi daya ya fita, nuna tayi da yatsa kafin tace, ka tsaya iya matsayin ka sannan kabar cikin gidan nan yanxo kafin raina ya baci inyi maka abun da bakayi tsanmani ba,
Da saurin shi ya tashi yayi wajen mashin dinshi, dafe da bakin shi dake fitar da jini, hawa yayi ko takardun shi bai dauka ba, dan yasa ma ranshi shida gidan nan har abada, ashe yar daba suka ajiye acikin gidan nasu, yanxu gashi anyi mai asarar hakuri daya, saide yasa na roba,

"Yanxu mai kikayi kenan Abrish, yaza ai ki mare shi,
Ok baki so in mare shi kenan, shikenan saiki zo ki rama me in zaki iya, tana gama fadin haka ta wuce abunta,
Oh ho Abrish allah ya shirya ki , hauka nake in mare ki yanxu in ki makalar min da hannu na, to bada ni ba, bayan ta tabi da saurin ta,
Shiga cikin falon sukayi, Abrish ta wuce sama ita kuma Nasra ta wuce wajen Ammee,
Ammee kin san mai Abrish tayi yau, a a saikin fada, yau kunga ma da wuri, ba dole ba yau malam yasha duka a wajen Abrish, duka kuma, wllh marin shi tayi har sai da hakurin shi ya fita, to maiya hada su ne, nan Nasra ta kwashe komai ta fada mata,
Rike haba Ammee tayi tace yanxu kina nufin Abrish ta iya karatu, wllh kuwa Ammee,
"Hmm lamarin yarinyan nan akwai daure kai wllh, to yaza muyi sai addu'a,


"Da saurin ta tashiga bathroom, tare da kunna famfon, kafin ta dauki wayan takai kunne, haba hafees sau nawa zan fada maka yanxu ni matar aure ce, ka daina kira na a waya, nace maka yanxu ni bazamu kara haduwa ba halakar mu ta kare,
Daga can bangaren akace, kinsan allah ilham idan baki zo mun hadu yau ba, saina tura wa mijin naki video abun da mukeyi sai inga yadda zaki yi kuma,
Na shiga uku hafees kada kayi min haka, fadamin inda zanzo in same ka, dade yafi maki alhairi dan alakar mu ma yanxu ta fara,
Fada mata inda zata same shi yayi kafin ya kashe wayan,
Na bani, hafees na son jamin bala'i zai bata min shiri na, tama rasa yadda zatayi sai kai kawo take cikin bathroom din batare da tasan mafuta ba,
Dole taje ta same shi ayita ta kare, wanka ta zarce dayi kawai,kafin ta fito ta shirya,
Key din mota ta dauka, tare da fita tanufi hanyar hotel din da sukayi zasu hadun,

(Kut ashe ilham ana taba dan hali kenan)


"Dukan su suna zaune akan dening suna yin diner, Abbey ya kalli Abrish kafin yace, yar Abbey ki shirya on monday zaki fara zuwa makaranta,tun da naji Nasra tace kin iya karatu koh,
Murmushi tayi,bata daice komai ba, Ammee ce da dan dariya tace, su hajiya Abrish sai makaranta, to fatana dai ki dage sosai dan da alama sai kinfi su o o kokari,
Tura baki Nasra tayi kafin tace Abbey kaji Ammee ko,
Rabu da ita auta ai zamuga wanda zaifi kokari a cikin ku, ni kuma sai nayi maku babbar kyauta in dai kuka dage,
Yauwa Abbey mu allah yabar mana kai, hakade suka karasa cin abincin cikin raha da barkwanci, tun Abrish bata sa baki har tasa akayi da ita,

Umma wai yanaji shiru ne haryanxu baki amso min wannan abun da kika ceba, shalelena kada kiji komai cikin satin nan zanje wajen malam ai, dan nasan yanxu ya karasa aikin dayake yi,
Kedai kisha kurumin ki, ai kamar kin sami Ashtar kin gama ne, dan yadda zaiji maganan ki kota uwarsa ba zaiji ba,
Murmushin jin dadi Nafeesat tayi kafin tace shiyasa nake sonki umma na,
Saina koya wa yarinyan nan hankali zata san ba'a gasa da Nafeesat, kedai ki kwantar da hankalin ki shalelena,
A kwance yake umma na,

Rana bata karya saide uwar diya taji kunya,

"Yau ta kama monday, wow zanso kuga yadda uniform din nan yayi wa Abrish kyau,
Farar rigace sai red din siket iya gewa, tasa red shos a kafarta sai farar safa, sai jan hula da red din tak a wuya, gashinta ta nanna de shi, hakama ta rufe fuskar ta da mask in banda ido da gira baka ganin komai na fuskar ta,
Itama Nasra kalan shigan ne a jikin ta,
dening suka nufa dan karya wa,kafin su wuce.




*yawan Comments dinku yawan pege din*🤷‍♀️





Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: """""""""""""""""""""""""""""""""""


🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI*🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧26.

"Duk wani cike cike daya kamata ayi wa Abrish tare da inta biyu duk anyi mata, kuma ta wuce, hakan yasa aka kaita ss2,ajin su Nasra,"
Tunda aka shigo da ita gabaki daya yan ajin sukayi mata kuri da ido, kowa burin shi yaga fuskar ta saboda ganin ta jar jawor saikace baturiya,
Ita ko kallon kowa take kafin idonta ya kai kan Nasra,tafiya tayi wajen ta tare da zama akan kujeran dake gaban ta,bata kara kallon kowa ba,
Shiko malamin dayan ajin kowa kallon ta yake da mamaki saboda sun san duk sabon dalibin daya shigo makaranta sai yayi bayanin kanshi wajen yan aji, amma ita saita nemi waje ta zauna abun ta kuma akan set din Bloody sarkin matsifa, yanxuma bata class din ne ta fita tare da tawagar ta,
Nasra ce ta mike tana dariyan yake tace, am so sorry guys, am har name is Abrish Abubakar she is my sister, shine dan takasance yar'uwar ki sai akace bazatayi bayanin kanta ba saike ce zakiyi mata, uncle din ke wannan maganan yana wani babbata fuska irin kada a kawo mai rainin nan, kallon kasan ido Abrish tayi mai kafin ta cije laiben ta na kasa,
"am uncle ita haka take bata cika magana bane, ko kurma ce ita, a a uncle tana magana fa haka dai yanayin ta yake, dariya uncle din yayi kafin yace aiko ba makaranta nan ya kamata tazo ba, makaranta kurmaye ya dace da ita,ba makaranta masu magana ba, nan yan ajin aka dauki dariya,musan man ma mazan ajin sunfi kowa dariyan,
"Daura hannu Nasra tayi akai kafin tace mun shiga uku,uncle kaja mana bala'i, ita dai Abrish tunda ta rumtse idonta bata bude ba, sai yanxu, "
Idon nata ya kada yayi jajir dashi, hatta kwayan idon nata yatashi daga blue color zuwa black color, juya hannun ta tayi nan take wani bakin hayaki ya fara fitowa,can kuma saita damke hannun, tana damke wa duk yan class din suka fara rike wuyan su suna kakari, alamun an shake sune,
Da sauri Nasra tazo gaban Abrish ta duqa tare da hade hannun ta waje daya alamun roko tana hawaye, tace na rokeki dan girman allah da manzon sa kiyi hakuri ki kyale su, wllh rashin sani ne yasa sukayi maki haka, na roke ki kiyi hakuri ki rabu dasu,
Ko kallon ta Abrish batayi ba,duk Nasra ta rude ganin yadda gabaki daya yan ajin suka fita hayacin su duk idon su ya firfito waje, su Bloody da suka shigo ajin yanxu duk kame wa sukayi waje daya,da sauri Nasra taje wajen su tana jawo hannun su tare da cewa kuzo mu roketa ko zatayi hakuri ta kyale su dan allah, ja baya safiya da zarah suka kafara yi kafin umme da Bloody subi bayan su da gudu, suna zuwa daide kofan ta rufe kanta tare da Windows din ajin, ihu suka fara surfawa babu tsaya wa,
Kafin kace mai kufar ajin ta cika makil da malame tare da daliben makaranta,sai kukarin bude kofan akeyi amma taki buduwa, ihun da su Bloody keyi yacika wa Abrish kunne hakan yasa ta rufe masu baki da wani bakin kyale duk sun hada uwar zufa ga hawaye da majina duk ya bata masu fuska,
Komawa wajen Abrish Nasra tayi tarike kafanta tace, Abrish na rokeki da sunan allah kiyi hakuri ko ubangiji mu munayi mai laifi ya yafe mana balle mu yan'adam da rokeki kiyi hakuri dan girman allah Abrish,kada kiyi kisan kai, kiyi kokarin sarafa fushin ki dan allah, kallon Nasra tayi wacce duk hawaye ya bata mata fuska,
"Amma kinsan banason raini ko"
"Nasani wllh"
"To amma maiyasa suke da raina mutane"
"Wllh baza su karaba ko da akan wani ne bake ba"
"Ajiyan zuciya Abrish tayi kafin tace zan hakura ne kawai saboda kin hadani da allah, amma da badan hakaba wllh bazan hakura ba,"
Dariya da hawaye ne suka cika fuskar Nasra, nagode yar'uwa ta nagode sosai, harara ta galla wa Nasra, kafin ta sake hannun ta da tun dazun ta damke, nan kofan ajin da Windows din duk suka bude, suma daliban ajin da malamin tari suka fara yi wasu ko sun suma ma, su Bloody ma duk suna gefe ido ya raina fata duk sunyi zuro zuro dasu,
Shugaban makaranta ne ya shigo yace maiya faru ne haka, duk an rasa mai magana acikin su dan suna tsoron yin wani abun yanxu ayi masu abun dayafi na farko, wai ba tambayan ku nake ba, babu de wanda ya tanka mashi saican yaji ance, malam dan kalli nan, juyowa yayi ya kalleta saida gaban shi ya fadi, nan ya tuna abun da Alhaji Ahmed yace mai akan yarinyan,
Malam a gaskiya abun da zance maka akan yarinyan nan sai kunyi hakuri da ita, saboda ita dai ba kamar sauran mutane take ba, sannan tana tare da wa'in nan mutanen na boyen da zarar an bata mata rai zata iya yin komai, dan haka na rokeka dan allah kuyi hakuri da ita sannan dan allah ajawa mutane nan makaranta nan kunne akan ta dan allah, zan dunga biya mata kudin makaranta mutum uku ita kade, nidai kawai so nake kubarta tayi karatu anan,
Dayake yaji kudi sannan gashi mayen kudi ne,ai da gudu ya amince batare da yayi la'akari da abun da zai sami jama'ar makaranta ba,
Ajiyar zuciya ya sauke,bayan ya gama wannan tunanin, kafin yace maiya farune,?
"Laifi sukayi min shiyasa na hukunta su, laifi wani iri kenan, dage kafadunta tayi kafin tace raini, sun rainani ne shiyasa,
Yama rasa mai zaice akan hakan, yarinyan tafi karfin shi,

Ranar dai haka har aka tashi batare da yan class dinsu sunyi komai ba, dan dukan su basa cikin yanayin da zasu iya karatun, itako oga koh ajikin ta kamar bata aikata komai ba,
Lokaci daya tsoron ta ya darsu a zuciyar yan makaranta ba yan ajin kade ba,


Da sallaman su suka shiga falon, Ammee dake zaune ta dagu kai da murmushi tace yan makaranta an dawo kenan, ke yana ganki haka wani zuro zuro dake kamar wacce ta kwana ta wuni bataci abinci ba,
Murmushin yake Nasra tayi kafin tace,Ammee yau munsha karatu shiyasa kika ganni a haka ai, tana gama fadin haka tayi upstair da sauri dan batason Ammee ta kara mata wani maganan a halin yanxu,

To allah ya kyauta maki kekam da wannan son jikin,
Itama Abrish saman ta haura bayan tayi ma Ammee sannu da gida, har zata shiga dakin su, taji an jawo ta, a fusace ta juya,amma ganin wanda yayi mata haka yasa ta kara tamke fuska kafin tace dalla malam sake ni,
"Idan naki fa" Ashtar ya fada cikin sanyin muryan shi,
"Murmushi tayi kafin tace kafi kowa sanin abun da zan aikata maka,dan haka sakeni, bai saketan ba,
saima cewa yayi maiyasa ke kokadan zuciyar ki bata tausayi ne, yanxu abun da kikayi a makaranta ku ya dace kenan,
"Kace bibiyata kakeyi kenan, kasami aikin yi kowa, dan yanxu na fara bazan taba kyale wanda ya shigo gona taba saina dau mataki akan shi, kuma na fadan maka kafita hanyata amma kaki ji ko,
To duk abun danayi maka kai kasiya da kudin ka,
Tana gama fadin haka ta tureshi har ya bigi bangon dake wajen, kafin ta shige daki abunta,
Afili yace, shiga rayuwar ki yanxu na fara Abrish bazan barki ba ko da zakiga bayana ne, saina koya maki tausayi mutane tare da soyayyar su aranki,bazan taba kyale kiba,


(Kana ko da aiki malam Ashtar🤔)


Oyoyo my salma, Nafeesat ta fada tare da rumgume budurwan da bazata wuce sa'an taba, tana da dan jiki kadan sannan tana da tsayi bawai sosai ba chocolate color ce sannan kyakyawa ce ba laifi, murmushi tayi wa Nafeesat wacce taja hannunta sukayi daki, key tasawa kofar kafin ta kara rumgume salman tace, i miss you my love, ture ta salma tayi kafin tace hmm ni zakice wa kina missing sweet bayan tunda kikayi aure kika manta dani, rike hannunta Nafeesat tayi kafin ta wani shagwabe fuska, tace haba my love ya zakice haka, sanin kanki ne bazan manta dake ba, kwanaki nayi ta kiran wanyan ki baya shiga, shine dana kira zuly tace kinje Landon ne shiyasa, amma kema kinsan kina raina,
Ta bude baki dan yin wani korafin Nafeesat tai saurin hade bakin su waje daya hakan yasa tayi shiru tana amsan sakon dan itama tayi missing din sweet din nata.





An bani jama'ah🙆‍♀️ gabaki daya matan Ashtar bana kirki acikin su.



Yawan Comments yawan pege din🤷‍♀️.





Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌴🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌴
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)


♧Pege♧27.


"Gashi uniform din islamiya ne, anjima karfe uku zamu tafi," "ok" kawai Abrish tace batare data kara cewa komai ba, kallon ta Nasra tayi kafin tadawo inda Abrish ke zaune, zama tayi kusa da ita tare da marairaice fuskar tace, dan allah na rokeki wani abu zaki yimin, dan kallon ta tayi kafin ta daga mata kai,
"Na rokeki dan allah idan munje islamiya ko da anyi maki abun daya bata maki rai ki daure kiyaki zuciyar ki, kiyi hakuri dan girman allah kada kice zaki rama, ta bude baki zatayi magana, Nasra tariga ta da fadin ,yanxu bazakiyi min wannan alfarman ba a mazayin yar'uwar ki, ajiyan zuciya ta sauke kafin tace naji, da gaske,
"A a da wasa, Abrish ta fada tana mai galla mata harara, dariya Nasra tayi tace nikam yi hakuri kafin yanxu ki fasa, batace mata kalla ba saima shiga bathroom da tayi danyin wanka, fita Nasra tayi dan ita tayi wankan ta,
"Ko da tafito wankan shiryawa tayi cikin riga da wando na Pakistán red color da dan ratsin fari fari ajikin shi, sake gashinta tayi ya zubo mata har wajen kafafunta abun makale gashi ta dauka ta tattare shi daga sama ta daure shi, hakan yasa yadage yadawo wajen kugunta,rabashi tayi wani ta baya wani ta gaba, daukan gyalen tayi tasagala shi a wuyanta,saita fito yar India sak da ita, kallon mirror tayi daukan lips gloss tayi takara wa Pink lips dinta, bakaramin kyau tayi ba,daukan chocolate tayi kafin tanufi hanyar falo abunta, tunda ta fara saukowa daga upstair din mutanen falon ke kallon ta, zama tayi akan kujera tare da kallon Ammee tace Ammee nayi kyau kuwa, dan dariya Ammee tayi kafin tace,aike kullum da kyaunki daman ko bakiyi kwalliya ba, murmushi tayi wanda har dimples dinta suka lotsa, Ashtar wanda yake mata kallon kasan ido, saida zuciyar shi tawani harba sanda tayi murmushi nan, da sauri ya dauke kanshi daga kallon ta saboda tsinkewan da zuciyar shi keyi inya kalleta, tashi tayi zata fita a falon,
"A a daughter ina zakije baki ci abinci ba, Ammee na koshi sai anjima zanci, a a banyarda ba dan naga alamun ke kinfi bawa zaki mahimmanci akan abinci dan haka maza zoki wuce kici abinci, dan tora baki tayi kafin tace Ammee, kingafa bazanji wani maganan kiba yanxu maza zokici abinci tunkafin ajimu,
Bayadda ta iya haka ta zauna ta zuba sinasir taci, duka kwara biyu kawai taci tace ta koshi,
Twins ne suka shigo, da dan dariya fuskar su hassan yace, sister kice yau mun laika India Pakistán ne dariya tayi kafin tace yaukam India muka tafi bro,usaini yace ai karkiji komai sis insha allah zamuje India kwanan nan ko a tayar jirgi ne saikin je, babu maisamin ya a tayar jirgi itama zuwan kanta zatayi, yauwa gaya masu Ammee, suna cikin rahar su saiga ilham tashigo, gaida Ammee tayi, amsawa tayi cikin fara'a kafin tace jiya ina kikaje ne naga baki shigo ba,
"Am jiya ba um daman naje gida ne, momy bata da lafiya, subuhanallah maike damun ta ne, na'am zazzabi ke damun ta ne, ta fada sai zarar ido take, dan tasan bacan taje ba kuma kada Ammee tace zata kirata, aiko bata gama tunanin nan ba, taji Ammee nacewa aiko ban saniba bari na kira ta naji ya jikin nata, da sauri tace a a basai kin kira ba,
Kamar ya basai na kira ba, am ina nufin ai jikin nata yayi sauki ne sosai ai ina ganin dakin barta ma, tafada tana dariyan yake,
Anya yarinyan nan tana da gaskiya kuwa, Ashtar ke tambayan kanshi dan duk wani alamun rashin gaskiya sun bayana akan ta, saide baice komai ba saima wayan shi dayaci gaba da latsa wa,

Da gaske kenan momy ba lafiya,taji anfada daga bayan ta, da sauri tace eh wllh batajin dadi, "i see" Abrish tafada tana dan murmushi kafin tace shiyasa kika kwana a Hospital tare da

Please Login or Register in order to submit comment