You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abbey yayi,ya fada wa zainab a maimakon yaga ranta ya baci sai yaga sabanin haka,dan murmushi takeyi kamar wacce ya gayan ma wani abun farin ciki, wai mai hakane nagayan maki yadda mukayi da mutumin nan amma ke dariya ma kike yi,kallon shi tayi kafin tace haba kaikuwa maina bata rai,bayan hanyar aiwatar da aikin mu cikin sauki muka samu batare da an zargemu ba,ban gane abun da kike nufi ba,murmushi tayi kafin tace zaka gane zuwa nan gaba ita saratu a tunanin ta ita kadai ta iya wasan to ni wannan ni ta taimaka ma,yanxu ka kirashi kace mun amince ai kishiya yar'uwa ce,ba a bokiyar gaba ba,daukan waya yayi ya kira Abbey ya shaida mai sun amince,inda Abbey yace ran asabar za'a kawo kayan sa rana da kudin gaisuwa,


Su hajiya falmata ne zaune a falon mai gidan tare da yaran su,saifaman aika wa juna harara suke yi ita da hajiya saratu,zuwa can saiga Abba yusuf ya fito adaki,bayan ya zauna yaran suka shiga gaida shi daya bayan daya dan suna mugun shakan shi,bayan yagama amsa gaisuwan,yace Mubarak bude mana taro da addu'a haka akayi addu'a kowa yasha fa, bakomai ne yasan na tara ku anan ba saidan in sanar daku cewan ansa ranar auren Nafeesat tare da Ashtar nan da wata biyu,dan yana dawowa daga kaduna za'a daura auren saide ba Nafeesat kadai zai aura ba ku biyu ne keda ilham yar wajen Badaru,dan haka sai kuje ku fara shirye shiryen biki,ai tunda yafara magana hajiya falmata taji hankalin ta ya tashi,Ashtar da Nafeesat za suyi aure bama wannan ba cin amanan da hajiya zainab zatayi mata kenan,bayan ta riga tasani tana da burin hada Ahfrah da Ashtar, amma yanxu saitaji wani batu daban tabdijan lalle akwai tashin hankali kuwa ita za'a munafunta,wllh ba'a isa ba ai wannan abun san kaine yusuf yayi yaza'a yi ya hada Nafeesat da Ashtar bayan ga Ahfrah itace babba dole tayi maganin a bun,itako hajiya saratu da farko murna suka kama yi amma jin wai za'a hada da wata ilham ranta ya baci,kenan kamar yadda take zama da kishiya itama yarta hakan zata kasance,kai wllh bazai yuyuba dole Nafeesat ta zauna ita kadai baza a hadata da wata ba,komai ta tuna kuma saita kama murmushi dan yanxu nan wani tunani ya fado aranta,kallon Abba yusuf tayi tace ashe tare za'a hadasu da yar'uwar ta,yace eh wllh haka yaya yake fada min nima,to ai bakomai kishiya a bokiyar zama ce ba makiyiya ba,duka yan dakin kallon hajiya saratu suke dan basuyi tsanmanin hakan daga gareta ba yadda suka santa dai,ba lalle ta yadda da hakan ba amma sai gashi taba kowa mamaki,hajiya falmata ko tunda taji abun da tace tasan akwai abun da take shiryawa,to ni nagama magana ta zaku iya tafiya,kamar jira daman hajiya falmata take,mikewa tayi kafin tace to allah yasa alhairi ya bada zaman lafiya,da ameen suka amsa ko kafin sugama amsawa tayi waje abunta Ahfrah ma bayan ta tabi dan tun dazo dauriya kawai takeyi dan zuciyar ta zafi take mata,saboda ta dade tana son yaya Ashtar amma yanxu wai arasa wacce za'a aura mai sai kanwar ta ita bama wannan ba wai za'a hada tare da ilham ya aura,mai yasa ilham zatayi mata haka bayan tasan irin soyayyar da take yi mai amma shine zata ci amma nan ta ,momy.. momy.. haka ta dunga bin mamanta tana kiran sunanta bata tsayaba saida tazo tsakiyar falonta,momy yanxu kina kallo zaki bari narasa yaya Ashtar kallon ta tayi kafin taja hannunta su zauna kan kujera,share mata hawaye tayi kafin tace haba kyakyawa na maina zubar da hawayen ki,ki sani ko da zanyi yawo tsirara ne saikin auri Ashtar,ko da ko hakan zaija rasa rayuka da yawane kedai ki kwantar da hankalin ki kinji,nika dai nasan mai zanyi dan haka ki daina zubar da hawayen ki kina bata min kyakyawan fuskar nan taki,rungumaita tayi shiyasa nake sonki momy na,

Ta bangaren Nafeesat ita ma hakan take dan tasa maman ta a gaba tana kuka,akan mai za'a hadata kishi da wata,saida maman tayi lalashi kafin ta gaya mata magana a kunne,hakan yasa kukan nata ya tsaya cak,umma kin tabbata hakan zaiyi aiki,kware kuwa aiki sosai ma,to in haka ne na daina kuka bari na tashi naje na fara shirin abubwan da za'ayi,yauwa yarinya ta haka nakeso amma da kya zauna kina bata hawayenki akan wata banza can jeki maza abunki, fita tayi cikin murna abunta burinta ya kusa cika,takusan zama matar yaya Ashtar,


Fitowa tayi daga daki,rataye take da kwari da baka a bayan ta gefen kugunta kuma wuka ne suke cikin gidan shi,kallon Abbu tayi wanda ke cin yayan ita tuwa,kafin tace Abbu na shirya mutafi,mutafi ina ya fada yana zaran ido,kuyan fada mana naga yau bamu fita da wuri ba gashi har rana ta fito,murmushin yake yayi kafin yace yar baba aike yanxu kin iya fada basai ankara kuya maki ba,kafeshi tayi da idonta kafin tace ni ban iyaba yanxu nake koya,to nima ai ba iyawan nayiba karan bani ne kawai irin nawa dan haka kiyi ta fiyan ki ke kadai dan nikam ba lafiya gareni ba,maike damun ka Abbu,ciwon baya da hagargari ne sai kafa da hannu,amma ayanxu ya fara ko ta fada tana kallon shi,eh yanxune ah...ah. dazun ....shekaran jiya ne ina jin, dan allah yi tafiyan ki kinji yar albarka,girgiza kai tayi kawai kafin tayi hanyar waje,aranta ta riga ta sani Abbu ya gaji da halin tane shiyasa ya sama wa kanshi salama,itama ako yaushe tana tunanin maiyasa ta kasance haka ne duk da bata zauna cikin mutane ba amma ta kyautata zaton ita kadaice mai irin wannan rayuwan,to maiyasa ta zamu haka allah kadaine masani kuma shi zai bayana gaskiya idan lokaci yayi , mai magana... mai magana,na'am uwar daki na wani aku ya amsa cikin karamin muryan shi,maike faruwa acikin daji,ta tambayi akun uwar daki na eh to wasu mutane ne sukazo ciki suna son daukan giwa ne,kallon shi tayi dayake yana saman icce ne ita kuma tana tsaye ne awajen iccen,akan wani dalilin zasu dauke shi,nima ban sani ba uwar daki na,to basu isa ba wllh tahu muje,hawan kan dokin ta tayi sukayi cikin dajin,suna ko zuwa ta iske har sunsa biyu a mota sauran sai kuka suke irin na giwaye,ranta ne ya baci akan wani dalilin zasu kwashe su a inda suke rayuwa aiko yau saitayi maganin su gobe ko ance su dawo baza su dawo ba, hayewa tayi saman bishiya dan bataso suganta,kafin ta ciro wani dan abu kamar sarewa acikin jakar fatan ta,busawa tayi nan danan saiga busar ta cika dajin,masu kwasan giwa sai aka tsaya kallon kallo a tsakanin su,zuwa can sukaji kasar na girgiza kamar anason daga ta,ashe wannan busan da tayi namun daji ta kira masu,zakuna suka fara bilowa kafin damisa zuwa can saiga macizai dila,baraiwa,biri,kai duk wani nau'in namun dajin da akwai acikin dajin nan saida suka fito,haka suka fara caskala su son ransu,hajiyar taku na saman bishiya tana kallo ko ajikinta,saima mangoron da taciro ta kama sha tana kallon su ita abun ma nishadi yasata dan har kwarewa take saboda dariya,saida taga sunji jiki sun hada jini da majina kafin ta kara busa sarewan sai gashi ko wani daba ya kama gaban shi harda giwayan,bayin allah suko ko iya daga hannu su basa yi dan ba karamin jin jiki sukai ba,saukin suma daya da su zaki da damisa basu cinye suba wanda hakan ya basu mamaki,nan koh umarni hajiya ne batayi niyan su cisuba shiyasa.





allah sarki masu daukan giwa yau kun taro aradu da ka wllh, nikam nayi ta kaina πŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈba dani ba garin daukan rahoto a hada dani πŸ˜‚ naga alaman su Oum abrar basu da niyan guduwa dan har wani kara daga kai sukeyi saboda gulma, hajiya safiya kuma yau autancin an ajishi gefe antafi gulma a daji,to bari Abrish ta ganu ku ba ruwa na ni dai.🀣🀣🀣






Shere fisabililahi
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM (UMMON ABDALLAH)


Pege 9.


*****


Saida tayi dariya mai isar ta sannan ta sauko ta haye dokin ta, ta miki hanyar jeji abunta saida tayi tafiya mai dan nisa sannan ta karaso wajan wani rafi gefen sa kuma bishiyar kuka ce, haka ta kama reshen bishiyar ta haye ta kwanta hankali kwance barci ya fara daukar ta, kamar a mafarki taji ana magana a kunnen ta.
"Abrish lokaci ya kusa! Lokaci ya kusa!! Lokaci ya kusa na barin ki wannan jejin"
Ana gama fadin haka aka kyalkyale da wata irin mahaukaciyar dariya, babu alamar tsoro ko firgici a tattare da ita saboda ba yau ne karo na farko da ta fara da ta fara Jin wannan muryar tana mata magana ba, zata iya cewa tun tana yarinya karama tasan muryar saboda ko yaushe cikin gaya mata maganganu, Wanda kuma idan sun gaya yakan zama gaskiya, ko wani karfi dake ilahirin jikinta bata san dashi ba saida wannan muryar ta sanar da ita sannan tasan dashi, kuma da suke cewa ta bar jejin, to ta bar jejin taje Ina?
"Ni da jejin nan mutu karaba takalmin kaza, babu inda zanje, gara ma ku shafa min lafiya ku kyale ni hakanan, zai fiye muku alkairi babu inda zanje"
"Dole kije! Dole kije!! Ya zame miki dole ki bar jejin nan ko kina so ko bakiso, ya zame miki dole Abrish"
"Mtsww, ai sai ku tayi Kuma na rigada na gama magana"
Ta karasa fadar haka tana kara gyara kwanciyar ta, itama muryar shiru kake ji daganan bata sake magana ba.


Kwance wadan nan bayin Allah suke saboda matukar wahalar da suka Sha a hannun dabbobin su ko daga hannun su basu iyayi, yan uwan su da suke a gida suka ji shirun yayi yawa yasa suka biyo Hanya suna dubawa ko zasu gansu, suna cikin tafiya suka iske su a cikin mawuyacin Hala, cikin tashin hankali marar masaltuwa suka kwashe su suka nufo cikin gari dasu domin a kaisu Asibiti a basu taimakon gaggawa, zukatan su cike da mamakin ko wa yayi musu wannan aika-aikar kode aljanu ne dan kuwa wannan dukan baiyi kama dana mutane ba.
"Niko nace aikin Dabbobi kenan kuka gani"
Haka suka dunga jimami har suka karaso asibitin.



Haka aka dunga shirye-shiryen biki batare da Uban gayya yasan za'ayi masa aure ba, auran ma Bada mata Daya ba mata har guda biyu a lokaci daya, Amare kuwa sai shan gyara suke sha ko wacce burin ta tafi yar uwa ta shiga a wajan oga dan haka iyayan su ma basu zauna haka ba sai shige-shigen wajan boka da malamai suke yi, kowa so yake burin sa ya cika.
{Allah ya kyauta, Ubangiji ya karaba mu da aikata shirka a rayuwar mu, ka tsarkake mana zukatan mu}
Zaune su Abee suke sunje gaida Hajja da yake safiya ce.
"Hajja Ina kwana"
"Ban kwana ba Amadu, nace ban kwana ba"
Ta fada tana turbune fuska.
"Hajja ayi hakuri idan wani laifin muka yi"
Shiru tayi kamar bata san da zaman su ba a wajan, ganin haka yasa Abba Yusuf fadin.
"Barka da safiya Hajja"
"Yusufa ka kiyaye ni, ku fita idona in rufe, da mutunci na da furfura ta baza ku zubar min da mutunci ba, yanzu haka kukeso kuyi wa yaron nan aure da mata ridi-ridi har guda biyu ba tare da sanin sa ba, dan kunga Yana muku biyayya shine zaku tauye sa, ku gaya min a cikin ku akwai Wanda nayi wa Auran dole, ko kuwa kai Yusufa daka dauko min kabila na hanaka auranta ne? Amma shine ku zakuyi wa yaro aure ba tare da sanin sa ba, kun kyauta kenan abinda kuka yi? Ko sadda yaron nan ya kawo min Yar India ai ban hanasa auranta ba"
Saita rushe da kuka data tuno da rasuwar Abubakar Saddi'k dinta, gefen zani ta kama ta face majina.
"Nasan da ace yana raye bazai taba bari ku aikata wa yaron nan haka ba, Allah sarki ko yanzu Ina Malika da uwarta suke? Ko suna raye ko suna mace Allah kadai masani"
Suma idanuwan su duk sun kada saboda da tunawa da Abubakar Saddi'k da suka yi, gashi har yanzu ba'a san inda iyalinsa suke ba.


"Kiyi Hakuri Inna in sha Allah zamu fada masa, abinda yasa yanzun bama fada masa ba shine, yaje wani aiki ne Kuma aikin Yana da mahimmanci a wajan sa shiyasa bamu gaya masa ba saboda karya shiga damuwa harya kasa yin aiki, Amma insha Allah da zarar ya kammala ya dawo zamu sanar dashi kafin a daura aure"
"To da dai yafi muku alkairi, dan bazan dauki cin mutunci ba ehee!!! Hakanan zakuyi wa kamilin Jikana auran dole kuma kuyi shiru da bakin ku sai kace wanda baida gata"
Haka dai ta dunga mita ita kadai, su kuwa shiru suka yi suka gyale ta dan Hajja akwai mita inta fara batasan tayi shiru ba, in kuwa ka bata hakuri kamar ka Kara zugata ne sai da ta gaji dan kanta kafin kuma ta fara musu nasiha, haka suka yi mata godiya suka fito suka nufi wajan aiki dan har sun ma makara.














Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

NA SABUWAR MARUBUCIYA
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM (UMMON ABDALLAH🀱)


Pege 10.

*****

Lokaci nata tafiya gashi haryau biki ya rage sauran kwana shida,kuma ayaune ango zai dawo daga tafiyan da yayi, amma bai sanar wa kowa ba akan yau zai dawo saide sugan shi kawai,hon yayi a bakin get din nan mai gadi ya budemai shiga yayi,sannan ye paking kafin ya bude murfin motan ya fito ya maida ya rufe,sashin mahaifiyar shi ya nufa yana mamakin wa'in nan mutanen daya gani a gidan su,to koh wani abu akeyi a gidan be sani ba,koh ma dai mainene bari yashiga wajen Ammee zaiji komai, da sallama ya shiga falon mutanen dake zaune a falon ne suka amsa mai,yawan mutanen falon duk yan'uwan Ammee ne sai yan tsiraron dangin Abbey, dan sauran duk a sashin Hajja suka sauka, yana shiga abokanen wasa suka yumai ca suna ango kasha kamshi kaikuma jinkirin auren naka ashe in katashi yi mata biyu zakayi shiyasa kaki aure da wuri, murmushi yayi kafin yace naga alama mutanen nan bayan surutu harda makanta ya samai ku wllh,habawa nan suka haushi da surutu shidai baice masu komai ba,saima yanufi dakin Ammee ya barsu dan bazai iyawa shirin tan su ba wllh,shi dariya ma suka bashi wai ango kuma mata biyu ko ayaushe yayi dasu zaiyi aure,ai shi bazaiyi aure ba yanxu harsai ya gama binciken daya keyi kuma shi haryanxu baiga macen da tayi mai ba,kuma inyayi aure akazo a kaga malika fa shikenan yayi mata kishiya kai bazai yuyu ba,dan shi rayuwar auren shi da malikan shi ya tsara kuma ita kadai insha allah,haka dai ya karasa dakin Ammee yana tunanin masoyiyar shi da haryau baisan inda take ba,da sallama yayi kafin aka amsa mashi bude kufar yayi yashiga,Ammee na zaune tare da kanwar ta anty khadija,zama yayi a kasa kan cafet gaishe su yayi suka amsa,Ammee dake kallon shi da dan mamaki tace babana shine zaka dawo bakayi ko waya ba dan asama maka abinci kafin kazo,murmushi yayi yace Ammee ai nasan in nazo bazan rasa abun ciba shiyasa nace bari nayi maku bazata ne kawai,aiko kayi inji anty khadija,kallon ta yayi kafin yace anty khadija ina zaradeen kwana biyu bamu haduba ,yana nan yaje jigawa wani aiki ne ai dakai dashi zumuncin bai damai kuba shiyasa,dan murmushi yayi batare da yace komai ba dan surutu ba damun shi yayi ba,kallon Ammee yayi kafin yace Ammee wai maike faruwa a gidan nan ne naga mutane da yawa haka,saida gaban ta ya fadi kafin ta daure tace kaje bangaren ka kayi wanka ka huta zan sa akawo maka abinci ka zuwa anjima zamuyi magana idan Abban ku ya dawo,amsa mata yayi da to kafin ya tashi ya fita dan dama a gajiye yake so yake yayi bacci kawai,
Yana fita ta sauke ajiyan zuciya,anty khadija ce tace yaya kina ganin zai yadda da auren nan kuwa,to khadija in bai yadda ba ya zaiyi saide yayi hakuri kawai allah yasa hakan shi yafi alkairi,Ameen,

Tunda Nafeesat taji yazo take ta murna burinta kawai ta ganshi,amma ba dama haka dai ta daure tunda sauran yan kwanaki ya rage sun duga kwana gida daya,kullum zata ganshi sanda ta so,

Itama ilham taji labarin zuwan shi,sai addu'a take allah yasa yaxu ya ganta kafin a daura aure dan tana son ganin kyakyawan fuskar shi.


Wani mutum ne tsaye acikin wani falo daya gaji da haduwa,saboda Nairan da aka zuba aciki yana tsaye gurin window lemu ne a hannun shi bayan dan mintoci yana dan kurba,sai mutum biyu zaune akan kujerun falon,dukan zasu iyayin shekara hamsin da wani abu,wasu samari ne su uku suka shigo falon baku sallama kai daga ganin su kaga yan daba,saboda irin shigan dake jikin su gasu saboda da shaye shaye duk sun koma wasu kalan mutane ga wani dan iskan aski da suka yi,dayan ne wanda ke gaban sauran ne da alama shine oga,cikin muryan yan daba yace sai Alhaji yane Alhaji ka dukamin kira ko wanine yayi maka tsiya yanxu mukaishi rahira,mutumin nan dake tsaye ne yatako ya dawo cikin falon yana murmushi kafin ya ciro wani poto ya mika masu,yace bahba wannan yarinyan nakeson ku saceta bayan kun saceta kuyi naisa da ita daga cikin garin nan sannan ku kashe ta,Adress din gidan su yarinyan da komai yana wajen sambo zai baku,A ranar daurin auren yayanta da daddre zasuyi diner,to alokacin nake son ku dauketa ku tabbata kun fita da ita daga cikin garin Abuja gabaki daya,angama Alhaji kawai kaide kajira saka mako,sambo ka basu sallaman su to ranka ya dade,godiya muke ya Alhaji,
Haka suka fita suna murna dan sunsan ba karamin kudi zasu amsa ba a wajen shi,bayan sun fita daya daga cikin mutanen yace Alhaji Haruna kana ganin hakan da mukayi zaisa yaron nan yadaina binceken daya keyi akan mu kowa,hhhm Alhaji salisu kenan tabbas bazai daina ba saide ma ya kara tunzura shi,nikuma muddin bai daina ba saina karan da yan gidan su gabaki daya mu zuba mu gani,nan suka sa dariya gabaki dayan su,



Abbey bai dawo gida ba sai dare,saida yaci abinci ya huta kafin ya kira Ashtar a waya yace yaxu ya samaishi a falon shi, da sallaman shi ya shigo falon tare ya iskesu da Ammee zaune akan kujera daya, waje yasamu kan cafet ya zauna bayan ya gaishe su suka amsa, Abbey yace ya aikin,Alhamdulilah Abbey ai har na gama,to masha allah,allah ubangiji ya taimaka ya baku sa'a ya karai ku daga sharin abokan gaba,da Ameen ya amsa,shiru sukayi nadan lokaci kafin zuwa can Abbey yace Malik,tunda yaji Abbey ya kira shi da sunan shi yasan magana ce mai mahinmanci,dan haka ya tataro dukan natsuwan shi yace,Na'am Abbey, Malik nasan zakaga kamar abun da mukayi maka son kaine,ko kuma kayi tsanmani bama sonka,to koh daya munyi hakane saboda mutuncin ka,saboda ayanxu kakai shekara talatin da biyar amma bakayi aure ba bayan bawai baka da halin yiba,hakan ne yasa na hadaka aure da yan'uwan ka Nafeesat da ilham,dukan su kannan ka ne kuma kasan halin su dan a gabanka suka tasu, to ina ganin hakan bazai zama matsala ba,kayi hakuri nasan ba'a kyauta maka ba auren mata biyu a rana daya kuma ba wa'inda kake so ba,abun da ciwo amma hakanan zaka daure ka amshi auren dan ranar asabar din nan mai zuwa ne daurin auren,ina fatan kamar yadda nasan ka mai biyayya da amsan duk abun da nabaka ko da baka son shi,ina fatan hakama zaka amshi wannan auren,kwana nawane saikaga ka fara son su, to kaji da lilin kiran komai kace,muddin kaji bazaka iya zama da suba sai a fasa auren, shiru yayi dan tunda Abbey ya fara maganan ya fita hayyacin sa in banda zufa ba abun dayake yi duk da AC dake falon amma kamar babu,saida Abbey ya kara mai magana sannan ya tuna inda yake,da kyer ya saita kanshi kafin yace duk yadda kukayi Abbey daide ne allah yasa haka shi yafi alkairi,da Ameen suka amsa kafin su shiga shimai albarka duk da daman sun san da wuya ya bijere masu,tausayin shine ma ya kamasu ganin yadda lokaci daya ya koma to amma ya za'a yi sai hakuri anriga an gama komai,

Zuwa can Abbey yace to a wani gidan zaka sa matan naka dan asan inda za'a masu jaire,Abbey duka gidan saina gyara su fara zama a bangare na dake gidan nan kafin a kammala, to hakan ma yayi tashi kaje allah yayi ma albarka yasa yadda kake faran tamin yayan ka suyi maka fiye da yadda kamin,da ameen ya amsa kafin,yatashi ya fita shi yarasa ma tunanin da zaiyi aure aure dai wai kuma shi,kai a a kila dai mafarki yake yanxu zai farka,mari ya labta wa kanshi zafin dayaji ya tabbatan mai da ba mafarki yake ba,lallekam akwai tashin hankali.










Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI* πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)


*NA* *SABUWAR* *MARUBUCIYA*
*FATEEMAH* *ALMUSTAPHA* *ADAM* (UMMON ABDALLAH🀱)


Pege 11.

*****

Ashtar fa yaga da gaske auren za'a yimai,kuma da mata har biyu,to shi ina zai kaisu yaran da basu da kamun kai,kuma waishi zai aure su,tab ai Abbey wannan auren kanku zaku daura mawa dan nikam ba ruwana dasu saide ma ankawo min masu gadi ne,yafadi haka a fili tare da kara gyara kwanciyar shi,

Yau aka kai laifen ,inda ko wacce akayi mata akwatina shabiyu,wan bako sisin ango aciki Abbey shi yayi komai dan ango ko kwandala bai bayar ba danshi har mantawa ma yake da aure zayi, yau takama ranar jumma'ah kuma ayaune za'a daura auren Ashtar tare da amaren shi,

Wai Ashtar bazaka tashi ba haba mana dan allah kariga kasani da an sauko sallah jumma'ah za'a daura auren,amma shine dan wulakanci kana kwance baka da niyan tashi balle ka shirya,wai dan allah Umar maiyasa zaka takura wa rayuwa ta ne haba ka kyaleni ko dole ne sai naje kawani bi kacika min kunne da ihu,ancika din malam dalla ka tashi ko nakira Abbey wllh,ka dadai baka kirashi ba kaji, umar fa yaga fada bazaisa Ashtar ya shirya ba sai ya kuma lallashi,daker ya samu yatashi ya shirya cikin faran shada tasha aiki malam sai sheki takeyi kallo daya zakayi mai kasan ango ne,saide fuskar nan tashi ba rahama ko kadan ya hadeta kamar bai taba dariya ba,
Bayan ansako sallah jumma'ah aka daura auren,Malik Ashtar Ahmad Modibbo,tare da Nafeesat yusuf Modibbo,sai ilham Badaru Hamza, akan sadaki dubu dari dari, yan'uwa da abokan arziki saiyi wa ango allah yasa alhairi suke wanda a fuskar shi bazaka taba gane farin ciki yake ba ko akasin haka, ko jira agama gaisawa da mutane baiyi ba ya gudu gida,ta kofar baya yabima dan baisan asan da dawo wanshi,duk anbi ancika mutum da hayaniya,can ko wajen daurin aure koh da umar ya duba yaga began shi ba yasan ya gudu ne,aranshi yace halin Ashtar sai shi bazai taba canzawa ba,

Umar abokin Ashtar ne tun na yarinta tare sukai makaranta da komai hatta aikin soja tare suka shiga inda umar yanxu yana matakin capten ne,kusan za'a ce sun kuma yan'uwa saboda yadda amintan su take haryasa iyayen su suka zama abokain juna,

Dare yayi kowa na shirin zuwa diner dan yawanci duk antatafi amarema duk sun shirya ango kawai suke jira saide har yanxu shiru bai zuba,shiko Ashtar suna can da umar anashan artabu dan cewa yayi shi babu inda zashi ai bai akesu su hada diner ba yayi lallashin duniya yaki shirya wa harsai da ya hadashi da Ammee kafin ya shirya amma fuskar nan babu anuri ko kadan dan ranshi amugun bace yake,in banda Ammee da tasashi dole wllh bazai zuba,hakadai akayi aka gama batare da anga ko murmushin ango ba,
Nasra dake zaune taga ankirata a waya dauka tayi amma saide batajin abun da ake fada saboda kidan dake tashi a wajen,kallon kawanta tayi tace zarah ina zuwa bari nadan amsa kira a waje,to saikin dawo fita tayi waje tasa wayan a kunne tana hello wake magana hello shiru taji ko da taduba wayan

Please Login or Register in order to submit comment