You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RAHIRA* *AMEEN YA RABBIL ALAMIN*πŸ™πŸ™
*MUCH LOVE YAN'UWA*πŸ₯°πŸ₯°




*MASU YIN LABE ARADU ZANYI SHARA SABODA BAZAKU DUNGA LABE WABA KUNA KARANTA WA BAKWA COMMENTS TO ZANYI TANKADE DA RAIRAYA DAN TSAF ZAN SHARE MUTUM DAN HAKA KARKUGA LAIFINA IN NA FIDDA MUTUM* 🀏😎












Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI* πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🀱)


β™§Pegeβ™§19.


*****

"A hankali ya fara bude idon shi, kafin ya bude su tar akan rufin dakin, kokarin tashi yayi zaune, umar dake tare dashi a dakin zaune ya taimaka mai ya zauna, sannu friend maike maka ciwo yanxu, dan yamutsa fuska yayi kafin yace nothing, ina son yin wanka cire min wannan abun ya fada yana mai nuna karin ruwan da ake mashi wanda saura kadan ya kare, cire mai umar yayi,mikewa yayi ya shiga toilet dan yin wanka, yadan jima kafin ya fito, shiryawa yayi cikin kananun kaya kafin ya fesa turaren shi,
Zama yayi acikin kujerun dake dakin umar ya maiko mai cup din daya hada mai coffe aciki yana kallon shi, amsa yayi ya fara sha a hankali, can dai umar yakasa yin shiru saida ya magantu, yace waini friend dama baka da lafiya ne, Ashtar dake kallon shi yai shiru nadan mintoci kafin yace, ni lafiya ta kalau bansan maiyasa ni amai ba nima, ikon allah wannan abun da daure kai yake, saikace wani mai ciki Friend ko dai ciki gareka bamu sani ba, umar ya fada yana mai gumshe dariyan shi, harara Ashtar ya maka mai kafin yace, kamanta ba ciki ba haihuwa nake yi dan rainin hankali tashi kabar min daki na tunda abun naka harda wulakanci aciki, sorry friend ba haka bane wllh ai yanayin abun ne saikace mai ciki wllh, ba dole ba daman mutum yayi amai ansa waccar yarinyan maikama da sadaka yalla zuba min abinci kilama wani abun akasa aciki allah ya ceceni, oh yanxu fisabililahi friend matar takace sadaka yalla, ba matana bade matar su Ammee da Abbey dai, allah ya shirya ka to, ko yanxu a shirye nake kamar carbi, kai kasani dan iska , kanka akeji Ashtar ya fada yana mai mikewa yayi hanyar waje shima umar rufa mai baya yayi,


"Nasra amshi ATM din nan Abbey kune ya bayar kuje tare da Abrish kuyi Shopping,ki siyo mata duk abun da kikasan zata bukata harda atanfofi da less da shadda bawai kije ku kwaso kanyan turawan nan ba saikace wasu gantalalu, kai Ammee kananan kayan da nake sawa fa basa matseni Ammee ai na sani shiyasa nakara ja maki kunne ai,

Fitowa sukayi da Abrish wacce fuskar nan nata a hade take ko alamun murmushi babu, mota deriva ya bude masu suka shiga wa inda Ashtar yasa dan tsaron lafinyan su suka bisu suma,Abrish da taga an fito waje saita fara fara'a tana kalle kallen hanya tare da tambayan Nasra na bata amsa, a haka har suka iso shopping Mall din, tunda suka shiga Abrish ta fara zuba kyauyancin ta Nasra na kwasan dariya,
Ba karamin siyayya Nasra tayi mata ba,dan duk wani abu daya kamata ace mace yar gata kuma maiji da kanta nadashi to sai da Nasra ta siyawa Abrish,kafin itama ta daukan wa kanta abun da ba'a rasa ba,
Bangaren kayan sanyi dasu icce cream suka je, ai Abrish na ido hudu da fanta ta nufi wajen, Nasra da bata lura da itaba dan hankalin ta yatafi ga daukan wani chocolate, jitayi ana ke hajiya bafa ashan abu anan sai anbiya,juyawa tayi zaro ido tayi ganin Abrish na shirin dukan saurayin dake mata magana saboda daukan fanta da tayi ta fara sha a wajen,shine dan yayi mata magana zata make shi, da sauri tazo taja hannun Abrish tana maiba saurayin hakuri,wajen biyan kudin sukaje Nasra ta biya komai kafin a biyo su da kanyan zuwa mota,
" Alhaji salisu ne ya fito shima dan tafiya gida,idon shi ya kai kan Nasra dake kokarin shiga mota kara matsawa yayi dan yakara tabbatar da abun daya gani, itace kuwa to ya haka ina su Bahba suke da har yarinyan nan ta dawo gida, da sauri ya shiga cikin motan shi yana mai daukan wayan shi, Alhaji haruna ya kira,yana dauka ko sallama babu ya hau fadin to wllh Alhaji haruna yaran nan basuyi aikin nan ba ,
wasu yaran kenan, su Bahba mana,
"Yanxunan naga kanwar wannan tsinannen yaron da mukasa akashe ta fito daga Shopping Mall, da alama ma siyayya tayi, Alhaji haruna dake zaune da sauri ya mike yace akwai matsala maza yanxunan mu hadu a gidan huta wata zankira Alhaji kabiru ma yanxu nan, Amma ya su Bahba zasuyi mana haka,

"Daga Shopping Mall din wajen telan su dake masu dinki sukaje ta bashi dinkin Abrish kafin suyo gida, koh da suka isa gida kayayyakin da suka siyo suka baje suna nuna wa Ammee da umme , kayan kam sunyi kyau sosai,

Ko da dare yayi kowa ya kwanta yana bacci banda Abrish wacce sai juyi take takasa bacci can dai ta mike zaune ta sauka akan gadon tana sanye da kanyan bacci pink color ajikin ta riga da wando haka kanta tasamai hula fara,
"Window dakin ta nufa , bude shi tayi laikawa tayi garin shiru dan wajen karfe daya ne na dare, zura kafafunta tayi kafin kuma ta mike a saman iska tana ta fiya,bata tsaya ko ina ba sai cikin lambun gidan, kan katuwan bishiyan mangoro taje ta kwanta tana mai sauke ajiyar zuciya, kafin tace a fili, haba da mutum yabi ya kwanta cikin daki saikace daddawa ba gwanda ka fito waje ba abunka su da sukaji zasu iya aisai suyi tayi, ta fada tana mai juyawa ta bangaren daman ta, mutum taga yana tafiya kamar barawo ta bayan ginin part din Ammee , tashi tayi sosai kafin ta matsa kusa saida ta matsa sannan ta gane, hajiya falmata ce sai wani waige waige take, daka ganta kaga mara gaskiya Abrish dai na kallon ta batace komai ba saima harde hannu wanta da tayi a girji,
"Duka wa tayi tafara haka rami sosai kafin ta ciro wata bakar mage da jaba sai wasu layun zata sa a ramin, alokacin ne Abrish ita kuma tayi wani girgiza sai gashi ta koma wata shirgegeyan macijiya wanda tsawonta yakusan wuce ginin gidan, hajiya falmata dake duke tana aiki taga inuwan abu akanta, juyawa tayi a hankali dan taga mainene a bayanta, koh da idonta yayi tozali da wannan macijiyan gata ita ba fara ba ita ba kuriya ba sannan ita ba ja ba idonta ko jarjawur yake, sankarewan tsaye tayi kafin zuwa can tasaki wani ihu, tanayin ihun Abrish nakai mata sara a kafa, wannan ihun da tayi saida gidan ya amsa duka saboda dare ne, bata daina ihun ba saboda azabar da takeji a kafanta ba kadan bane, mutanen gidan duk suka fito da masu tsaron gidan suka dunga bin inda ihun ke fitowa har sukazo bayan gidan , ko da sukazo basuga komai ba banda hajiya falmata ita kade tana ihu tana rike kafanta,
Amma abun dazai baku mamaki shine duk wannan halin datake ciki bai hanata boye kayan tsubun ta ba dan kada mutanen gidan su gani, kowa mamakin maiya kawota wajen yake a tsakiyar dare haka, daukanta akayi dan zuwa asibiti saboda cewan da take maciji ya sareta a kafa duk tayi kashi da fitsari a zaninta sai doyi take,

"Abrish dake kallon kowa daya bayan daya,can ta kwashe da wata dariya kafin tace yanxu wasan ya fara.






Nima anan zance saimun hadu gobe dan ganin yadda zata kaya.


*Happy jumma'ah to all muslim*







Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI* πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🀱)



β™§Pegeβ™§20.


*****


"Su Abba yusuf ne a kofar dakin da aka shigar da hajiya falmata,sai kai komu suke awajen duk hankali su atashe yake, tunda likitan ya tambaye su koh ansa wani kalan macijine ya sare ta, amma basu sani ba dan koh wani abu mai kama da maciji su basu gani ba, shiyasa hankalin su duk yaki kwanciya, dan yanxu kusan karfe ukun dare amma ba wani labari,
"Likitan ne yafito daga dakin, duk sukayi wajen shi sukayi,doctor ya jikin nata, ku biyo ni Office, bayan shi suka bi zama sukai akan kujerun dake Office din,
"Doctor ya jikin matana yake, Alhaji ka kwantar da hankalin ka jiki alhamdulilah, dan munyi nasaran cire goban macijin, yanxu hakama tana dakin huto, a gaskiya da ace baku kawota da wuri ba ina mai tabbatar maku da kun rasa ta,dan macijin daya sare ta,guban shi nada karfi yadda bazaka iya tantance wacce kalan guba ne ba ajikin mutum,saboda kallan macizan nan ne masu hadakan jiki, idan nace hadaka ina nufin zaka ga maciji daya ne amma jikin shi mabanbanta, ma'ana color din jikin shi zasu iya kasancewa uku zuwa hudu,mutane kance kalan wannan macijin na aljanu ne wasu kuma suce haka halitar macijin yake,to gaskiya munci wuya kafin musami makarin wannan guban dan sai da wata doctor tashigo dakin ta bamu alluran,kuma da mukayi mata alhamdulilah mun sami nasara, saimu gode wa allah, sannan mugode ma waccan likitan,
"Duk Alhamdulilah su Abbey ke cewa, doctor ina zamuga likitan dan mugode mata, eh nabarau ta a dakin saide bansan ma Office dinta ba da alama sabuwar ma'ikaciya ce ita dan bansanta ba,dan fuskar tama a rufe take da facemak, ga wannan maganin zakuje kusiya,ya fada yana mai mika masu takardan daya rubuta maganin ajiki,
Godiya sukaime kafin su fito harda likitan, dakin suka nufa tana kwance sai baccin wahala take, nan Abba yusuf ya kwana sukuma Abbey da Abbu,Ashtar yazo ya dauke su suka koma gida,

"Ita koh Abrish bayan antafi kai hajiya falmata asibiti, zuwa tayi ta dauko kanyan tsubon da hajiya falmata ta boye bayan wasu ganyeyaki, wuta tasa masu nan duk suka babbake saide tukan su, tukanma kadeshi tayi yabi iska, komawa tayi kan bishiyan ta tayi kwanciyar ta, nan danan sai bacci harda minshari,
"Nasra ce da tashigo dakin bayan sundawo daga tsakar gida,gani tayi ba Abrish a dakin nan saita dauka tashiga toilet ne, Abrish kina bayi ne taji shiru,zuwa tayi ta kwankwasa kufar bayin nan ma shiru,bude wa tayi ta leka wayam ba kowa aciki, to ina Abrish tayi ne dan banma ganta ba da muka fita waje, kila kuma tashige wani wajen ne,koma dai ina taje nasan zata dawo, ta fada tana mai kwanciya a gadonta,


"Bangaren su Alhaji haruna kuwa, bayan sun hadu a gidan hutun shi,tare da Alhaji salisu da Alhaji kabiru, suna magana akan dawowar Nasra bayan sunsan an riga an dauke ta, to ya hakan ta kasance maiyasa ta dawo a raye batare da an maidu gawar ta ba kamar yadda suka shirya,
"Alhaji haruna yace hakan na nufin kena ankama su Bahba, daman ni ina mamakin yadda tsawon sati uku amma Bahba bai kirani yace aiki ya kammala ba, to kuwa in hakane yakamata musan inda aka kaisu dan baza mu bari su tuna mana asiri ba, kashe su kawai ya kamata muyi, Alhaji salisu ne mai wannan maganan, maganan ka gaskiya ce zanyi magana da yarona dake cikin mutanen Ashtar dan ya samo mana bayane akan su, to hakan ma yayi dan yaran nan kusan duk sirin mu sun sani yakamata muyi abun daya dace,maganan ka gaskiya ce Alhaji kabiru,
nan dai sukaci gaba da kula muguntar su batare da sun san wa'inda yanxu suke nema allah kade yasan inda suke,


"Waini wani gafalin tsiyar ne ya kaita bayan gida a tsakiyar dare, idan ba mugun abu take shirin yiba, to allah na tuba banufen mutum kuma da mugunta kila anje shirya yadda za'a ga bayan mune sai allah yayi ikon shi, ni ki daina kallo na da wa'in nan idon naki kamar na cinnaka,ai ba karya nayi ba in kina da gaskiya ki fadi uban mai ya kaiki bayan gida a tsakiyar dare,
"Itade hajiya falmata tunda hajja tazo asibitin tafara sababin ta batace kala ba,saboda ita kade tasan yadda takeji aranta, abun bakin cikin ma bokan ta yace indai aikin ya wuce jiya to bazaiyi ba kuma dan bashi da sauran amfani,sannan ga saran macijin da tana da tabbacin aljanu ne suka sareta dan haryanxu inta tuna yadda kamanin macijin yake sai jikinta ya dauki rawa,
Wannan rashin sa'ar har ina, daman tafa anso wannan asirin ne akan idan ta birne shi to Nafeesat zata kwanta rashin lafiya wanda bazata tashi ba karshe saide ma ta mutu, daganan shikenan sai Ahfrah ta auri Ashtar, sannan inta shiga gidan tasan yadda zasuyi da ilham, amma komai ya baci sanadiyar macijin nan, ai wllh da mutum ne yayi mata haka saitaga bayan shi,amma ba komai bari tasami lafiya zata koma tasami wani taimakon dan wllh sai Ahfrah ta auri Ashtar,


Nikoh nace wanda baiji bari ba zaiji hoho,hajiya falmata.



"Tunda aka aje mata kofin a gabanta take kallon abun dake ciki,tea ni mai kauri dayaji madara da milo, amma ita bata sanshi ba shiyasa take kallon shi, Abrish kisha tea ki mana yana hucewa kallon Nasra tayi kafin tace wannan abun zan sha,ehman da dadi sosai kisha, daukan kofin tayi kafin takai bakin ta dan kurba tayi kadan ta tsaya,gardi gardi taji da zaki,karawa tayi akaro na biyu saitaji da dadi fa, kafin ketawan ido ta shanye tea ta aje kofin,farfesun kayan ciki tare da kwai da dankalin da aka aje masu ta jawo gaban ta cikin minti daya ta gama da nata, Nasra dai kallon ta take tana mamakin irin abincin da Abrish ke ci saikace maici da aljanu, daman daga ita sai Abrish suka rage a gidan tare dasu ilham, dan su Ammee sun tafi asibiti, suma yanxu zasu tafi,
"Abrish ce ta tashi dan komawa cikin falon tajira Nasra ta zo stair din karshe kafarta ta gurde ta tafi zata fadi, Ashtar daya sauko yanxu dan wucewa wajen aikin shi, yai saurin taro ta jikin shi,kallon juna suka shiga yi, mai aikin gidan dake saman upstair garin gulma ta sake basket din folawan dake hannunta na kwalliyan daki,nan koh ya dunga zubu masu kamar a India, wakar da akasa a tv ne ma yakara basu kala,
"Su Nafeesat wa'inda tunda abun ya faru suka shigo dakin dan sutafi asibitin tare,bakin ciki kamar ya kashe su, ganin Ashtar rumgume da wata mace ba suba,
"Abrish ta fara janye idonta kafin ta ture shi yayi baya tana hararan shi, shima Ashtar din harara ya maka mata yaja tsaki ya wuce,ko kallon inda su ilham suke beyi ba, hakan yakara kular dasu,

Abrish ta nufi hanyan upstair, ilham ta daka mata tsawa,ke yar kauye dakata, tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon ta karasuwa inda take tayi tana fadin ke har kin isa, kija hankalin mijina kanki, ta daga hannun ta akan zata mari Abrish,
"Saide mai hannun ya tsaya cak a dage tayi tayi ta sauke yaki yi saima wani azaba da takeji, murmushi Abrish taki kafin ta matso kusa da ilham tace, mijinki koh mijinku dan naga bake kade ke da shi ba,
"Da kike cewa inajan hankalin shi kaina, kenan kinga nike da abun dayake so bake ba tunda har hankalin shi ya dawo kaine, kinga koh bazance ya fita hanya taba saboda dake, idan nayi niya saina aure shi ke baki isa ki hana ba, to amma saide ban shirya wa aure yanxu ba kin gane, dan haka ki sama wa zuciyar ki salama bayanxu zamu fara takun sakan ba sainan gaba,
"Kallon hannunta tayi kafin tace ke a tunanin ki zaki iya mari na, hmmm haryanxu baki san wacece Abrish ba,kuma kada kiyi fatan sanin ta dan bazaki ji dadin hakan ba,
Sannan banga wanda ya isa yasani sakar maki hannu ayau ba sainaga dama,dan haka aje ayi jinya, malama ilham,

"Tana gama fadin hakan ta wuce ko kallon yan cikin falon bata kara yiba, su Nafeesat duk suna tsaye sunkasa motsi, kuka ilham ta fashe dashi tana dan allah kiyi hakuri ki sakar min hannu wllh ba marin ki zanyi ba, wajen Nasra ta nufa ta rike hannunta da dayan hannun nata wanda yake lafiya,tana kuka tace Nasra kiyi mata magana dan allah tayi hakuri ta sake min hannu, Nasra da duk tausayin ilham ya kamata tace gaskiya ilham banajin ko nayi mata magana zata sake hannun ki saboda ita indai batayi niyan abu ba ba wanda ya isa yasa ta, kiyi hakuri harsu Abbey su dawo kila idan sunyi mata magana ta sake maki,nima takaina nake bazanje ba ayimin ila, kuka ta fashe dashi tana nashiga uku, Nafeesat ki taimaka min kada na kuma musaka, a a babu ruwa na aikece matar yaya Ashtar mai baki da kishi, yanxu sai kishin naki ya taimakeki ta fada tana mai kwashe wa da dariya, saboda ganin yadda hannun nata ya ankwashe sannan ga uwar zufan da ta hada ga hawaye harda majina, Haka ta zauna ta dunga kuka tana rokun Abrish ta sake mata hannun ta amma a banza, dan batama san tana yiba.















Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI* πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🀱)


β™§Pegeβ™§21


*****

"A gaskiya Alhaji duk wani bincike nayi,amma babu inda alamu ya nuna Oga yakama su Bahba dan daya kamasu da nasani, saide a bayanen dana samu,wai wata yarinya ce ta taimake ta acan garin enugu,kuma inajin ita kade tasan inda su Bahba suke,dan yanxu hakama yarinyan da iyayen ta suna gidan zaune tare dasu oga,
"Kana nufin macace ma ta bata mana aiki, yakamata na santa, sannan itama yakamata ta sanni, yakamata tasan cewa ba'a shiga gonar Alhaji haruna akwana lafiya, wllh bazan kyale taba tunda ta bata min shiri kuma sai ta fadamin inda takai su Bahba koh na kashe ta,
"Alhaji kana ganin zaka iya da wannan yarinyan kuwa,wacce ke rayuwa acikin jeji tare da namun daji,yarinyan da mutane ke tunanin aljana ce saboda kyaunta,to nidai Alhaji duk abun da zai danganci yarinyan nan babu ni a ciki dan bazan kai,kaina halaka ba ana zaune kalau, kama san wanda zaimaka aiki akanta amma bani ba, yana gama fadin haka ya kashe wayan, hakanan ina zaman zamana kaja min bala'i babu gaira babu dalili,

"Huci kawai Alhaji haruna ke fitar wa kafin yace,Allah yasa itace shugaban aljanu wllh wllh wllh saina ga bayanta tunda ta shiga rayuwa ta,ta bata min aiki ,daga ita har tsinannan yaron nan bazan barsu ba,


"Friend kasami bayane kuwa akan wa'inda suka sace Nasra, a a ban samo ba,daman inason inyi wa Nasra da wannan aljanar yarinyan tambayoyi ne akan mutanen yau,to sai ga abun da ya faru kuma, ayya ni banma tambaye kaba ya jikin nata,to da sauki suna de hospital din haryanxu,amma dazu dana kira Abbey yace an basu sallama zasu wuce gida,ina jinma yanxu haka sunkai gida,to allah ya kiyaye gaba,Ameen bro muje gidan koh dan nima nakammala aikin da nakeyi, ok muje,


"Tunda suka tunkaro hanyar falon sukejin kuka da ihu ,da sauri duk suka karasa ciki falon, ilham suka gani zaune akasa hannu a lankwashe ga fuskar ta duk yayi dama dama,da majina ga hawaye hudan da jambakin da aka shafa duk ya dame saita koma kamar mahaukaciya,
"Subuhanallah ni dijee keko yarnan maiyasa mi hannun naki daya lankwashe ko karye wa yayi, hajja ta fada tana mai rike haba, hajiya zainab wacce tare suka dawo da mutan gidan daga asibiti,da sauri ta nufi yarta,shalele maiya samai ki wayayi maki haka yau ni na shiga uku an maida min ya musaka, momy dan allah ku bata hakuri wllh ba marin ta zanyi ba,ta taimaka ta sakemin hannuna dan allah momy kuyi mata magana,Abbey dan allah kayi mata magana nasan zataji maganan ka dan allah Abbey,
"Ashtar wanda suka shigo suma yanxu, ya kalleta ya juya ya kalli umar suka hada ido, aisai suka kwashe da dariya saikace wasu tababbu, kallon su kowa ya tsaya yi sake da baki,ganin irin kallon da ake masu yasa suka gimtse fuska kamar basu ke dariyan ba, kara kallon ilham Ashtar yayi saikuma ya kara kwashe wa da dariya harda rike ciki, ita ilham dake kuka tun dariyan su na farko ta tseda kukanta,yanxu kuma da Ashtar ya kara mata wani dariyan,ai sai takara fashe wa da kuka,
"Ashtar banson iskanci ya kana kallon halin da yarinya ke ciki zaka zo ka tasamu gaba kana dariya, harda kai umar danake maka kallon mai hankalin ka biye mai, kayi hakuri Abbey wllh dariyan ce taki rikowa Ashtar ya fada yana mai gimtse fuska shi da kyer,dan wllh rabun dayayi dariya kalan wannan harya manta,amma yau daya kalli fuskar ilham yaga yadda ta koma saikace wacce ta gudu daga gidan mahaukata ai sai tabashi dariya, barsu mana su nuna mana rashin imani su kalan na sojoji, hajiya zainab ta fada tana hararan Ashtar wanda ya juya kanshi gefe yana dan murmushi,shide Badaru baice komai ba saboda takaicin ga yadda hannun yarshi ya koma sannan wannan taka darin na masu dariya,

Wai tukunnan ma maiya samaita ne da naga hannunta haka a lauye wani ya karya ki ne,Ashtar ya tambaye ta, yaya Ashtar dan allah kayi mata magana wllh baxan kara ba yauma tsautsayi ne ya kaini, nidai ta sake min hannu na,
Wacece wai,Abrish dan allah kuyi mata magana itace ta rike min hannu,Abrish kuma inji Ammee,
Wllh itace gasu Nasra ma ku tambaye su a gaban su akayi, wai anyi haka Nasra, Abbey ya fada yana mai tsare Nasra da ido, eh Abbey ilham ce ta daga hannu zata mare ta shine hannun ya tsaya a haka,kuma tace bazata sakar mata shi ayau ba,
Subuhanallah kai yar taka ashe aljana ce bamu sani ba, hajja ta fada tana mai kallon Abbu wanda yayi kasa da kanshi, aranshi daman yasani sai hakan ta faru zaman Abrish a gidan nan,yana da tabbacin wannan kadan akayi ba'a komai ba shiyasa zaman su a jeji yafi mai alkairi tare da kwanciyar hankalin,saboda yasan wacece Abrish bata yafiya sannan ko kashiga gonar ta ko kar kashiga,duk randa mugun tan ta ya motsa wllh kowa ya shiga uku,
Hajiya zainab ce ta tashi cikin fushi ta nufi umme tana mai nunata da yatsa,wllh kiyi wa shegiyar yarki magana ta sakemin hannun yata inba haka ba nadau mataki a kanki, tafiya take idonta rufe saboda masifa sauran taku kadan ta karasa gaban umme taji ance,
"Na rantse da allah kika kara taku daya zuwa wajen mahaifiya ta wllh saide ki koma gida ba kafafu, dan haka zabi ya rage naki, tsayawa tayi cak ta daga kanta dan ganin mai magana kowama na dakin upstair yake kallo, Abrish ce tsaye ta hade fuskar babu alamun tama taba wani abu waishi dariya,kwayan idonta a maimakon blue color ya koma red color, sakowa ta karasa yi cikin falon,kafin ta kalli kowa sai kuma tayi wani murmushi kafin tace,nice nan na tseda hannunta daga aiki saboda tayi abun da babu mahalukin daya taba yunkurin aikatawa a kaina,shiyasa nayi mata haka dan ta banbance tsakanin, *YAR DAJI* da kuma yar kauye da ta kirani dashi, da ace nazo maki sa fuskar *yar daji* ,ina mai tabbatar maki hannun naki duka zan cire, to amma ki gode wa allah nazo maki a fuskar yar kauye, kamar yadda kika kirani,
"Ke ki daina wannan abun yanxunan ki sakar mata hannun ta, Malika Ashtar kana tunanin zaka sani abun da banyi niya ba ,to baka isa ba dan ma kasani, abu biyu zuwa uku kesa na ragama acikin gidan nan, wanda zuwa nan gaba zaka sansu, amma duk randa ka kaini bango,haduwar bazata yi mana kyau ba, dan haka ja baki kayi shiru,
"Ashtar yama

Please Login or Register in order to submit comment