You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kalleshi yace.
"Babana tunda angama karatu ai sai aiki koh?"
"Eh Abba dan sun soma rikeni nayi masu aiki naki yarda nace sainayi shawara daku sannan"
"Ai gwandama dabaka yarda ba dan ba inda zaka kara zuwa kadawo kenan, kaima kasar ka ta amfana da kai"
Hajjo ke wannan maganan wanda ke zaune tanacin goronta hankali kwance,
"Hakane gaskiya inna dan nima abun da nagani kenan gwanda kasata ta amfana dani"
"to yayi kyau ya maganan aure fa koh akwai wacce kake so"
Modibbo ya tambaye sa yana kafesa da idanuwa, tofa anzo wajen yafada azuciyar shi nan danan ya hada zufa dan bai san ya zai yi yafa da masu wacce yakeso ba, koh dai yayi shiru? kai gwara yafada kawai kafin suje su hada shi da wata, Uhhkk gyaran murya yayi dan yanajin muryan tama shake yace.
"Eh Abba akwai wacce nakeso"
"Ah to masha Allah yar inace dan muje ayi maganan aure dan kasan yanxu baka zauna haka ba"
Shiru yayi na dan wani lokaci kafin yace.
"Abba yar-yar am"
"kayi magana kana tawani in'ina"
kallon Hajja yayi wacce tayi maganan yanxu kafin ah hankali yace.
"Yar India ce Abba"
"Yar India fa kace!
Hajja ta fada da karfi tana dafe kirji cike da tashin hankali.
"kai yanxu dan nan karasa dawa zakayi soyayya sai da lndi yawa masu bauta wa gunkin shaid'an"
kasa yayi da kanshi zuciyar sa na bugawa da karfi da karfi, kafin yace.
"Inna wannan musulma ce kuma tana sallah"
"Koma mai takeyi baza ka aure taba, baza ka kawomin maijan kune amatsayin suruka ba, ta shigo zuri'ar mu atoh"
Shidai Abba tun dazu yayi shiru yana juya Al'amarin aranshi kafin ya kalli Abubakar wanda tun sanda hajja tace bazai auri Najaf ba hankalin shi yabar wajen yanaji aranshi muddin aka hanashi auren ta zai iya mutuwa wllh.
"Katashi kaje ka kwanta gobe da safe zamuyi magana"
Modibbo yafada yana kallon shi hakanan yamike ya tafi dakinshi dake soron gidan duk jikinshi asanyaye fatanshi daya su amince kada sura ba zuciya da abin da takeso..















Shere fisabilillah.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege 6.




*****

Tofa tashin hankalin da ba'ah sa ma shi rana, Hajja fa ta dage akan Abubakar bazai mata surika da mai jan kunne ba, bawan Allah Abubakar duk ya fita a hayyacin sa, har wata rama yayi ta tashin hankali yanajin muddin aka raba shi da Najaf zai iya mutuwa, domin Allah ne kadai yasan irin so da kaunar da yake mata, an kwashe kusan wata daya ana fama da hajja kusan kullum Modibbo cikin yi mata nasiha yake, akan ta daina zafafawa a rayuwar duniya dan batasan inda rabo yakeba, ba'a san abin da zaije ya dawo ba akan hana shi auren ba da takeso tayi ba, da sauki ma tunda musulma ce ita, haka dai akai ta fama kafin ta sauko ta amince da auren, Abubakar dan murna kamar yazu ba ruwa akasa yasha don murna da farin ciki har sallah raka'ah biyu yayi dan nuna godiyar shi ga Allah subhanallahu wata'ala, yana fatan iyayen Najaf suma su yarda su amince da auren.


Bangaren Najaf itama anyi fama dan iyayen ta sunki yarda, sunce yarsu bazata auri dan Nigeria ba, bayan ga Safir na sonta, Safir dai yaron aminin babanta ne ya dade yana sonta saide ita koh kadan bata kaunar shi, saboda mugun halin shi dan mugune na bugawa ah jarida abun da iyayen ta har yau basu fahimta ba kenan saboda mutumin kirki yake komawa a gaban su, sai da a ka kai ruwa rana kafin su yarda dan cewa tayi zata kashe kanta indai baza su aura mata zabin ranta ba, su kuma suna tsoron rasata dan ita kadai ce yar su da suka haifa, hakanan ba dan sun so ba suka yarda da auren, su Modibbo sun shirya tare da kawun nen Abubakar dashi kanshi Abubakar din aka tafi India naiman auren Najaf Alhamdulilah sun sauka lafiya inda tsofafi akai ta raba ido dan bashi hakin shi, sun sami tarba mai kyau dan musanma Ibrahim khan ya bada kudi a wani Afirca restaurant dake cikin nan Dalhi dan ayi masu girki, sunci sun sha sun koshi inda akasa ranan aure nan da wata uku, kuma amarya tazo sun ganta sun yaba da hankalin ta tare da karamcin iyayanta duk da ba iya yaren juna sukai ba saide afada magana Abubakar ya fassara masu a haka dai suka gama komai.


Sun dawo gida dan fara shirye-shiryen biki inda aka hada tare dana Ahmad dan shima ya kamala karatunshi Modibbo ya bashi jari yaci gaba da sana'a inda allah yai ta buda mai hanyar samu, Abubakar shima yasami aiki ah wani asibiti dake Abuja sun bashi gida da mota ga albashin shi mai tsoka, yatattara koma Abuja kafin biki Abubakar yasama wa Ahmad aiki acan, a wani kamfani da ake jakun kuna da takalma sai cafet, haka shima ya tattara ya koma can da zama dan shima an bashi gida, ta bangare daya shima Badaru tunda yaga anje naima wa Ahmad aure kuma har ansa rana shima yaje ya matsa wa iyayen shi saida sukaje naima mai auren zainab ah jos, akasa wata uku kamar yadda akasa na Ahmad dan mugun jin haushin Ahmad din yake saboda ganin yafishi samu, amma dayake munafiki ne bai da kama baitaba nunawa ba ko a fuska yadai bar wa zuciyar shi mugun nufin shi.


Rana bata karya saide uwar diya taji kunya, ayau aka daura auren Abubakar da Najaf, Ahmad da Ameena, Badaru da zainab akan sadaki dubu dari-dari, haka aka kwashi amare sai Abuja, saide zainab ita anan Yola zata zauna tun da mijin ta anan yake, haushi kamar ya kasheta, Amarya Najaf anxo Nigeria taa sauka a gidanta dake abuja tare da yan'uwan ta da sukai mata rakiya dan ganin inda zata zauna, saide suna tausaya mata saboda rayuwa a inda baka saba ba akwai wuya, ita dai tace taji ta gani koh a inane zata zauna tare da Abubakar din ta, Saide muce allah yabasu zaman lafiya ya kawo kazantar daki, haka rayuwa taita tafiya watanni na shudewa haka shaikaru nata tafiya inda yanxu har anci shekara uku da auren su, Najaf koh batan wata bata taba yiba abun na damunsu sunje asibiti ance lafiyan su kalau hakan yasa suka fawala wa allah komai, inda matan Ahmad harta haifi danta na farko mai sunan Modibbo Muhammad gashi yanxu har tana da cikin na biyu, inda allah sai kara budawa su Abubakar hanyan samu yake dan yanxu dukansu kowa na da gidan kanshi sun so iyayansu sudawo wajensu da zama sunki yarda hakan yasa suka hada kudi suka kara gyara gidan ya koma ginin zamani, har da yusuf wanda shima ya kamala karatunshi har yafara aiki, shima yayi aure inda ya auri wata saratu saide banufiya ce ita a makaranta suka hadu soyayya tashiga harta kaisu ga aure, saide saratu akwai shegen son abin duniya bata da godiyan allah koh kadan ga shegen zuwa wajen malaima da bokaye.



Ameena ta sauka lafiya inda ta haifi yaronta na miji kyakyawan gaske gashi jar jawur, yaci sunan baban maman shi, Malik suna cemai Ashtar bayan Ashtar takara haifan twins, inda yusuf yakara auren wata falmata itako a bank suka hadu tazo bude Accaunt ita koma ibo ce, yanxu yana da yara uku, yayan saratu biyu Mubarak da Basheer yar falmata daya Ahfrah, kusan za'a ce halin falmata da saratu daya saide falmata tafita iya taku, Badaru koh sai da yasan yadda yayi ya koma abuja da zama shima saboda kullum matar shi cikin zuga shi take akan Ahmad ne yatare mai hanya samu, sun manta allah ne mai badawa kuma mai hanawa, bayan shekara shida
Najaf ta sami ciki, wayyo allah zo kuga murna abun da suka dadai suna naima shekaru da yawa dan har sun cirai tsanmani sai gashi allah maji rokon bawan shi ya azurtasu, kusan za'a ce kowa yayi murna da samun cikin nan dan har yar walima suka hada,
Bayan wata tara da kwana goma, yau Najaf ta tashi da nakuda inda akayi asibiti da ita, tasha wahala kamin ta haihu inda aka sami diya mace,ya subuhanallah kowa yazu asibiti nan sai ya tafi da maganan yarinyan nan a bakin shi saboda tsabagen kyawunta wasu har mamaki sukeyi saikace aljana, koh dayake ba abun mamaki bane duba da cewa mamanta yar India ce san nan babanta bafullatani, jikinta ko fari tas dashi kamar ka taba jini ya fito, haka akayi taron suna inda yarinya taci suna malika, Naira tayi kuka malam dan kamar kyautan kudin ake masu ba naiman su ake ba, yarinya tayi goshi dan kakan nin ta musanman suka biyu jirgi suka zo tun daga India, kayan ko da suka kawo mata baki bazai iya lussafa su ba,haka akayi taron suna aka gama su hajiya zainab, falmata, saratu, Ameena kowa cikinsu na fama da ciki haihuwa yau ko gobe.


Bayan shaikara biyu:
Assalamu'alaikum su Abubakar ne sukayi sallama tare da shigowa falon gidan Ahmad, da sauri Ashtar yaje ya amshi malika a hannun Najaf dan shi acewar shi matar shi ce ita, iyayen sukanyi mai dariya ne kawai Abubakar yakan cewa koh da bayan rainane insha allah malika bata da miji sai kai, haka zakaga Ashtar yasata agaba yana mata wasa itako taita mai murmushi dan yariyan mugun miskilace dan da farko an dauka bata magana saida ga baya aka gane miskilanci ne kawai indai kanason kaji maganan ta sai tana tare da iyayen ta koh Ashtar shine zakaji surutun ta da dariya, amma koh Nasra da take sa'an ta dasu Nafeesat bata wasa dasu wai batason raini bayan dukansu bai wuce watanine a tsakanin suba, idan tana yin wani abun mamaki ma takeba iyayen da yan'uwan dan zaka dauka wata babbar macace, haka su Abubakar suka zauna ana hira can Ashtar yace uncle ai zaka bani auren baby malika koh idan nagama girma na zama soja, dariya uncle yayi yace insha allah malika bata da miji sai kai da yarda allah koh bayan rainane zaka aureta, nikam yaya a kwanakin nan kullum baka da aiki sai kiran mutuwa koh akwai wani abu dake damun kane wanda bazaka iya fada min ba, murmushi yayi yace Ahmad ai ita mutuwa bashi da lokaci da zarar lokacin ka yayi ko second daya bazaka karaba, kawai dai fatan allah ya sa mucika da imani duka falon aka amsa da amin, dayake yanxu Najaf najin hausa sosai, basu suka tashi tafiya gida ba sai wajen bayan sallahn isha'i, yau hakanan gabansu sai faduwa yake kamar wani abu na shirin faruwa dasu, koma mainene suna fatan yazo masu da sauki haka suka rabu kamar kar sutafi dan har cewa sukai abar masu malika ta kwana sukace gobe an kawota tayi sati da yake takan zo tayi kwanaki ah gidan, Abubakar ne yaja Ashtar gaife tare da bashi wata jaka bansan mai suke magana akaiba naga dai Ashtar sai girgiza kai yake hawaye ya cika mai ido, shima Abubakar girgiza mai kan yayi tare da dafa kafadan shi bansan mai yace maiba naga dai yanufi cikin gidan ya aje jakar a inda bawan da zai gani, sannan ya fito waje iyayen basuce mai komai ba saboda dama shi dan gidan Abubakar ne ba'a shiga sha anin su,


Wajejen karfe biyu na dare Ahmad yaji wayar shi na ringin, dauka yayi batare daya duba mai kiran shiba saboda da baccin dake idon shi, abun da aka gayamai a wayan yasa yaji ya naimi baccin ya rasa bakin shi na kerma hakama jikin shi sai rawa yake yace ban gane maikake fada ba, daga can bangaren aka kara maimaita wa gobara ce ta kama gidan Abubakar gashi har yanxu motar kwanokwano bata isu ba, tashi yayi yana ta maimaita kalmar, innadillahi'wa'ina ilaihin raji'un, hajiya Ameena da tun kiran wayan ta tashi take tambayar shi maike faruwa amma bai tsaya bata amsa ba, kawai mokulin mota ya dauka ya fita koh takalmi bai tsaya sa waba haka yatafi, ita dai ta bishi da Addu'an allah ya tsare dan ganin yadda yaja mota da gudu yabar gidan bata kuma bacci ba alwala tayi tayi sallah tana mai Addu'an kariya, koh daya isa mutan kashe wuta har tazo ta kashe, saide wani abun karin tashin hankalin shine kaf gidan an duba ba Malika da mamanta koh gawar su ba ah ganiba saide ta Abubakar wanda koh kamanin fuskar shi bazaka gane ba, saboda ya kune sosai koh da aka tafi dashi asibiti rai yayi halinsa,kafin safiya mutuwar Abubakar da bacewar matar da yar shi ya zaga koh ina, kada ma hajja taji labari wanda nan take ta yanke jiki ta fadi jinin ta ya hau, haka akaita zaman makoki tare da naiman su malika amma shiru kakeji,Ashtar kuwa tun da ga lokacin shirun shi ya karu akan na da ya daina dariya kwata kwata, bayan rasuwar Abubakar da shaikara daya shima Modibbo ya rasu, wayyo hajja duk ta koma abin tausayi mutuwan da da miji abun ba dadi,wa innan Ahalin dole ka tausaya masu saboda suna jin jiki sosai na mutuwan mahaifin su da yayan su,
Ahmad da yusuf sun hada kudi sun gina babban gida anan maitama, kowa da bangaren shi ba karamin kudi suka kashe wa gidan nan ba haka suka fidda wa hajja bangaren ta samarin gidan ma kowa da nashi wajen, daker hajja ta yadda ta koma Abuja saboda yusuf ma ya koma can da aiki sannan auta tayi aure itama tana zaune a kaduna tare da mijin ta da yaranta biyu,
Haka hajja ta koma batare dason rantaba saide duk sanda ta bushi iskanta takan tafiyanta yola tayi kwana biyu acan.



*Bayan shaikara goma sha takwas*
Anyi naiman su malika har an bari saboda a na tunanin suma sun mutune,saide shi Ashtar akwai mutanen dayake zargi,musanma ma abokin uncle Abubakar, mai suna Alhaji tanimu kawai yayi shirune yasa ido akan kowa yana bincike a sirrance.
Iyayen suna fama dashi yai aure yaki yi gashi har Muhammad yayi aure yana da danshi Ahmad suna kiran shi Ayman, su Nafeesat dasu Nasra an girma falmata takara haihuwan da namiji.

Wannan kenan

*BACK TO STORY*

Yawan Comments, yawan kara pege .




Shere fisabililahi.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege 7



Kwance take akan dan madaidacin gadon ta wajen karfe daya na dare, idonta a rufe suke kamar mai bacci Amma a zahiri ba bacci take yi ba, zuwa can saita mike zaune sai kace wacce aka tsikara da allura ta mike ta nufi hanyar waje kallon ko ina tayi duhu ya mamaye ko'ina dan dare yayi sosai, hakan yasa ta rufe idon ta zuwa can saita bude a maimakon agan shi kamar yadda idonta yake sabanin haka fari ya koma tas dan ko kwayan idon ta daya kasance blue color ba'a gani hakan ne yabata daman ganin ko ina kamar rana, kallon dakin iyayen ta tayi ganin shi tayi a rufe kuma bataji alamar motsin su ba hakan ya tabbatar mata da barcin su yayi nisa sosai, hakan ya bata daman tunkarar hanyan waje a maimakon tabi ta kofa saita kama katanga gidan su duk tsawon ta kuwa haka ta haye ta fita waje, hanyan cikin dajin dodar ta mika ko alamun tsoro babu a tattare da ita duk da irin halitun da take gani kuwa wanda su a tunanin su bata ganin su tunda bil'adama ce ita ba aljana ba, haka ta dunga tafiya cikin dajin nan har sai da tazo tsakiyar dajin ta tsaya a gaban wata rijiya, kallon rijiyan tayi wanda kafin a iya bude murfinta sai an tara kartin maza majiya karfi kusan mutum goma sannan za a iya bude ta saboda girman ta da nauyi zaka dauka wani baban tsauni ne aka ajiye akai, amma ita koh haka tasa hannunta ta daga murfin ta ture gyefe kamar wacce ta dauki dan karamin dutse, kallon cikin rijiyan tayi wanda ko alamun haske babu aciki in banda duhu baka ganin komai tsalle tayi ta fada cikin shi akala tayi tafiyan kusan minti biyu kafin tazo kasan rijiyan, a maimakon kaji karan ruwa kamar yadda sauran rijiyuyi suke wannan saide karan duro wanta akasa kawai kaji, duhu ne ta koh ina acikin rijiyan wanda ko tafin hannun ka baka iya gani in banda ita dake ganin komai kamar rana, mikar da hannunta tayi kafin ta nuna wani waje saiga wani haske kamar wuta ya fito ta hannun ta ya sauka akan wani dan abu kamar kofi, nan danan wuta ta kama ci sai ga haske ya gwaraye koh ina, rufe idonta tayi kafin ta bude nan danan sai gashi ya dawo dai-dai, nufan wani dan ma daidacin gado tayi wanda aka yishi da banbu andaura wata katuwar katifa akai sai wata kujera dake gefe daya wacce itama da banbun aka yita,(wani icce ne banbu zaku ganshi dogo kamar rake saide icce shi)



Kwanciya tayi akan gadon,kwanciyar ta keda wuya saiga wasu macizai nata fitowa akalla zasu kai kusan goma haka sukai ta shawagin su a filin wajen tana kallon su ko ajikinta saima baccin ta
data kama yi harda minshari ba ita ta farka ba sai kusan asuba tukun,kallon kasa tayi taga har yanxu macizan na nan inda ta barsu rufe idonta tayi kafin ta bude sai ga wani haske na fitowa daga cikin idonta yayi kan macizan,nan danan suka dunga hadaiwa harsuka zama wata narkekiyan macijiya tashi tayi ta dafa macijiyan saiko macijiyan nan tayo kasa da kanta wannan ya bata daman hawa kan macijiyan,sama ta dunga yi da ita harsuka kawo kofar fita rijiyan tsalle tayi ta dure kafin ta dafa kan macijiyan saigashi ta bace,murfin rijiyan ta jawo ta rufe kallon hanya tayi haryanxu akwai sauran duhu dan wajen karfe hudu da rabi ne,tafiya taci gaba dayi cikin duhun nan ko ajikinta dan tariga tasan duk hanya da zatabi taje gida,kama katanga tayi ta haye dakinta ta shige bata dade da kwanciya ba taji muryan babanta na tada ta tayi sallah,amsa mashi tayi kafin ta fita waje danyi tsarki da alwala,


Niko nace baban Mubarak mazai hana a hada Ashtar da Nafeesat aure kaga idan ya aureta ankara dan kon zumunci,sannan kuma kaga ita yar'uwar shi ce zatafi fahimtar shi akan koma wazai aura koya kagani, hajiya saratu ke wa Abba yusuf wannan maganan,kallon ta yayi nadan lokaci kafin yace ko nima zanso hakan ko dan zumunci mu yakara karko saide bazan sa yaya yayi wa Ashtar dole ba tunda ba sonta yake ba kawai tayi hakuri har zuwa lokacin da allah zai kawo mata wanda ke sonta ta aura,haba Abbansu ya zakace haka ai ba dole zakuyi maiba Ashtar mai biyayya ne akan duk abun da kukace balle kuma auren yar'uwar shi aiba zaiki ba, numfashi ya sauke danji yayi bazai iya mata musu ba,saide ma yasami bakin shi na fadan kar kiji komai insha allah zanma yaya magana tasa aranta kamar ta aure shi ta gama,murmushin mugunta tayi dan tasan aikin boka ne ya fara ci,kafin tace shiyasa nake sonka mijina akwai ka da saurin fahimta,mikewa yayi tare da cewa bari kiga inje insamai shi dan yau ba aiki yana gida baije ko ina ba,toh allah yasa adace idan kaje da ameen ya amsa kafin yasa kai ya fita,bai zarce ko ina ba sai sashin Abbey bayan sun gaisa aka danyi hiran zumunci zuwa can yasa ko maganan dake tafe dashi,murmushi Abbey yayi kafin yace gaskiya naji dadin maganan nan yusuf kuma insha allah acikin satin nan za'a sa rana,daya dawo daga kaduna aikin dayaje sai a daura aure to mai za'ah jira tunda yana da gida da komai auren ne kawai yaki yi,yanxu kuma tunda ga yar'uwar shi ai shikenan magana ta kare,hiran yadda shirye shiryen zai kasance sukai tayi,sun da jima kafin Abba yusuf ya tafi,bai dade da fita ba Badaru ya shigo bayan sun gaisa yake cewa magana nazo muyi akan yaran nan daman,wasu yara kenan Abbey ya tambayan shi Ashtar da ilham nace maizai hana a hadasu aure tunda kaga har yanxu beyi auren ba kamar tsoron matan yake, tunda ya fara magana Abbey yake kallon shi kafin ya numfasa yace,gaskiya naji dadin maganan nan amma saide inda matsalan take shine yanxun nan yusuf bai dade da fita akan maganan hada auren Ashtar da Nafeesat,to amma ai namiji mijin mace hudu ne kaga sai ya hadasu duka ya aura,idan har ilham zata iya zama da kishiya to mu ashirye muke,ton da Abbey ya fara magana Badaru yai fiki fiki da ido a ranshi yana cewa watakon bama yace yar dan uwan shi ta hakura ba saide yar shi tayi zaman kishi da ita wanda hakan zai iya kawo masu cikas akan cikan burin su to amma bari yafara zuwa suyi shawara da zainab tukun,numfashi ya sauke kafin yace babu komai wllh bari na fara zuwa gida muyi magana da madam tukun na komai ake ciki zan maka waya,sallama sukai kafin yatafi gida cike da bacin rai,


Fada suke sosai acikin dukar dajin nan kamar a filin daga dan zakayi tunanin fadan gaske sukeyi amma nan ko duk gwaji ne can kuwa allah yaba wa Abbu sa'a ya bige wukan hannun Abrish ta fadi kasa itama Abrish din faduwan tayi,nan da nan ranta ya baci dan ta tsani acita yaki da koma waye,nan take idonta yayi ja sosai saboda bacin rai,buga hannunta tayi akasa saiga raishinan icce na karyowa sunayin wajen Abbuu ganin haka yasa yadunga amfani da wukan shi dumin kare kanshi,mikewa tayi tsaye batare da kyafafunta sun taba kasa ba ita ba a sama ba ita ba akasa ba,wata guguwace ta tahu tayi gaba da kallabin ta haka yasa gashinta daya kasance baki wuluk zubuwa har wajen kwarin ta dan kadan yarage yataba kasa,haka iska yaita kada gashin yana tashi sama,gani tayi hakan baiyi mata ba kawai saita dauko duk wani dutse dake wajen ta dunga tora mashi,gani yayi muddin baiyi wani abu ba zata iya halakashi hakan yasa ya kwala kiran sunanta Abrish...kidakata nace ki dawo hayyacin ki so kike ki kasheni ne Abrish bakyajina ne wai ABRISH KI DAKATA NACE....ya fada da karfi maganan da yayine ya shiga kunne ta hakan yasa ta dakata da kokarin halakashi da takeyi,zubewa tayi a wajen ta zauna tana kallon shi ,bawan allah sai maida numfashi yake yi dan saura kadan ya mutu wllh goran ruwa ya raruma ya kafa bakin shi bai saukeba harsai daya shanye tukun kafin ya daga kai ya kalleta,ita shi take kallo har yanxu da idonta da sukai jawur dasu,
A hankali yatako yazo wajen ta,kafadanta ya dafa kafin yace Abrish saunawa zance ki dunga kokarin sarafa fushin ki ba ko yaushe akeyin nasara ba, a kullum ina gaya maki ki kasance mai tawakali dan ba komai kake naima ka samu ba kuma ba komai ake cin nasara ba,kin sani sarai muddin kikayi fushi hatta namun dajin nan najin jiki balle ni,dan allah kiyi kokari ki dunga sarafa fushin ki kinji,bata cemai kalaba harya gama maganan shi sai ma mikewa da tayi ta nufi cikin dajin da gudu bata tsaya ko ina ba sai wajen rijiyan nan budewa tayi ta shiga ciki abunta,

Shiko Addu'an shiriya yayi mata tare da fatan allah ya bude masu abun da ke boye tattare da ita,yarinyan saikace aljana in banda a gaban shi aka haifeta aisai yace an canzata ne,ko dayake waya sani ko idan suka ajiyeta tana wasa sunje wani wurin an dauketa an kawo wata mai kama da ita,kawai shi dai fatan shi allah yakara tsaresu daga kaidin ta,shi wllh ma yagama koya mata fada dukda tana yarshi bazai iya ba wata rana zata iya kasheshi, allah dai ya saukaka masu kawai,haka yanufi gida da damuwa aran shi dan bazaibi bayanta ba duk inda take zuwa anjima zata dawo gida yasani.






Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

NA SABUWAR MARUBUCIYA
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH🀱)


Pege 8.

******

Ko da Badaru ya isa gida kwashe yada sukayi da

Please Login or Register in order to submit comment