You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunanin wannan aljanar yarinyan, koh dan ta taimaki Nasra ne nake tunanin ta haka, No bashi bane, tashi yayi ya zauna dan bubuga kanshi yayi yana mai fadin,ki fita akai na ki fita nace, kwanciya yayi tare da jawo filo ya rumgume, tuno sanda suka hada ido yayi yadda ta maka mai harara tare da murguda mai baki,murmushi yayi, she is so cute and i like her, kama bakin shi yayi ya rike yana zaro ido waje,kai wai da gaske ni nayi wannan maganan ,Ashtar you have to see a dector, daukan wayan shi yayi waiko hakan zai dauke mashi hankali amma a banza, haka yaita fama sai wajen asuba bacci ya dauke shi,


Kwance take adakin ta wajen karfe daya na dare, tunanin maganan da Abbu ya fada mata takeyi, wai itace zatabar jeji ta koma cikin gari, ina bazai yuyu ba gaskiya,
Saboda damai bazai yuyu ba, taji muryan nan da ake mata magana dashi, ehmana saboda zan bar jeji,saboda lokacin barin shi yayi, idan baki manta ba kwanakin baya munce maki kin kusan barin jeji to ayanxu lokacin ne yayi, to amma maiyasa zan bar jejin, saboda barin shi kadai ne zai cika maki burin ki, tashi tayi zaune, kuna nufim barina jejin nan kadai ne zai cikamin buri na, kware kuwa, dariya tayi, idan ko hakane a yanxu a shirye nake dumin zuwa koma ina ne,mudin burina zaicika, sannan kuma duk wanda yayi kokarin shiga gonata koh yake kokarin kawo min cikas akan cikan burina,hmmm bazan taba raga ma koma wanene ba, dariya aka bushe dashi, muna alfahari dake, munason kisani ayanxu karfin ki ya karo fiye dana da,saboda ayanxu zaki iya karantar tunanin koma waye sannan duk wani abu daya danganci asiri zaki iya ganin shi,saboda gidan da zaki je akwai masu mugun nufi dayawa acikin shi,dan haka ki shirya danmarar cin uban duk wanda yayi ba daide ba, muzamu tafi duk inda zaki muna tare dake sarauniyan mu, murmushin gefen baki tayi,ina son kalan wannan wasan yana sani nishadi,


"Kinga wannan maganin bakaramin kudi nakashe akan shiba,har Niger naje dan wannan maganin,ki tabbata kinsa mai a abinci yaci,sannan wannan kwallin kisa a idon ki kada ki sake ki hada ido da kowa idan bashi ba,ko da dabbace kuwa inba hakaba duk wanda kika hada ido dashi ya dunga binki kenan kamar kaska, kinga na abincin nan shiyafi muhimmanci kifa same, momy to taya zansa me na abinci yaci bayan kinsan ko kallon arziki ban isheshi ba balle har nayi mai girki yaci, ilham banason shashanci fa, banaji kince sun tafi enugu dauko kanwar shi ba, "eh" to idan zasu dawo ai za'a yi masu girki, saiki sami wanda kikasan dole yaci shi ki zuba maganin aciki kin gane, na gane to amma momy idan wani yaci maganin babu matsala,babu matsalan komai, ina mai tabbatar maki dayaci abincin nan mai maganin hmm yariga yaxo hannu kenan sai yadda mukai dashi, dan koh maganar uwar shi bazaiji ba kamar yadda zaiji namu, dariyan jin dadi ilham tayi shiyasa nake sonki momy na,


(Hhhm su ilham adaiyi a hankali dan aljanar gidan tana kan hanya)



Tun da sassafe yayi wanka ya shirya, danji yake in baiga fukar taba yau akwai matsala, dakin su Abbey ya kwankasa,bashi izinin shiga akai, samun waje yayi ya zauna tare da gaishe su,amsawa sukayi tare da tambayan shi ya yakwana,lafiya lau nake Ammee, sai ina haka da sassafe kaci kwalliya, dariya yayi kamin yace Abbey zanje jeji ne wajen kwashe dabobin nan, oh to yayi kyau daman yakamata ace wani yaje wajen koh dan asan iya adadin dabobin kasan wasu direbo bin sai a hankali zasu iya daukan wasu daga cikin dabobin su saida,sai sukawo maka sauran suce iya wanda aka basu kenan, ai cin haram bai mawasu wahala, hakane shiyasa ma nace bari inje akashe a gabana, (niko nace gayi gaskiya malam zade kaje ganin Abrish) to yayi kyau ka gaishe min da malam Abubakar inkaje,zaiji insha allah,

Koh daya isa gidan bayan sun gaisa da Abbu,nan aka dunga kwashe dabobin ana sawa a mota,saida aka gama kwashe wa sannan suka shiga gida, gaisar da umme yayi ta amsa da fara'a tana tambayan shi yasu Amme, yace duk lafiya lau suke, sai wurga ido yake yanason yaga ta inda zai ganta, amma ko alamun mai kama da ita bai gani ba, mikewa yayi akan zai tafi umme ta hana,

Zauna akawo ma abun kari, a a wllh umme naci abinci,gaskiya sai kaci abinci bazakazo ka tafi haka ba batare da kaci komai ba,dan dariya yayi tare da zaman,yanason ya tambayi ina Abrish take ya kasa,to maima zaice,kawai sai yace yana neman ta babu dalili, hakade harya gama karin shi da kunun gyada da kusai, batare daya ganta ba, sallama yayi masu ya tafi batare daya ganta ba,duk jinshi yake wani iri,to wai maike damu nane mai ruwana da ita, maiyasa nakejin wani abu akanta mtsssw gaskiya na fara samun matsala a kwakwalwa na,


*To akace rana bata karya saide uwar diya taji kunya*,
"Gashi haryau ranar tafiya tayi inda Ammee da hajja sai umme,motar su daya, hakama Abbu da Abbey suma motar su daya,sai oga shida aljanar shi da Nasra motar su daya, Abrish tayi bakin cikin barinta jeji amma tace watarana sai ta dawo sannan ta wani wajen tana farin cikin zata cika burinta.




Muma gamunan mota guda da yan Group din *YAR DAJI* munje Enugu,yanxu kuma zamu koma Abuja garin shugaban kasa, tare da Abrish din mu mai zamani.πŸ€Έβ€β™€οΈπŸ’ƒπŸ˜œ






Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI*πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🀱)


β™§pegeβ™§18.

*****

"Koh da suka karasa cikin gidan,Abrish ba abun da take sai aikin kallo,inta kalli can saita kalli can, tana mamakin wannan wai gida ne itafa duk abun dake wajen bata taba ganin irin shi ba a rayuwar ta,shiyasa yanxu gabaki daya hankalin ta yatafi a kallon komai, Nasra da tun dazu take mata magana amma bata masan anayi ba, hannunta takama Abrish zo muje kiyi wanka, binta tayi abaya gani tayi sun fara hawa tsaunin nan,(upstairs) itade bin bayan ta kawai take har suka isa dakin Nasran, toilet taja ta suka shiga ,Toothpaste tadauko da abun wanke baki sabo tasa mata Toothpaste akai,gwada mata yadda zata wanke bakin tayi saita fita a toilet din saboda kiranta da Ammee tayi,
"Aiko da Abrish tasa abun wanke bakin nan waizata wanke baki, zakin da taji na Toothpaste din nan kawai saita lashe abunta,yanxu wannan abun mai zaki Nasra zatace nawanke baki dashi lallema Nasra nan batacika hankali ba wllh, bari kaga wllh saina kara sha da dadi fa, dauko Toothpaste din tayi budewa tayi kamar yadda taga Nasra ta bude matso shi tayi a hannunta mai uban yawa ta shiga shan abunta, tana cikin yin ta'asar nan Nasra ta dawo ta isketa zaro ido waje tayi,Abrish mai haka kike yine yanxu man wanke bakin kike sha, harara ta maka mata kinji min Nasra da wani abu,yanxu ke fisabililahi saiki bani wannan abun mai zakin tsiya kice nawanke baki dashi,nifa nan malama abun danasan ana wanke baki dashi,gawayi ne da gishiri saiko asuwaki,amma ke kin dauko wancar ruban da abun zakin nan waina wanke baki dashi ba dole na shanye kayana ba,ta fada tana maikara dago hannunta zata lashe sauran daya rage,da sauri Nasra ta rike hannunta, tarawa tayi a famfo ta wanke mata kafin takara zuba man wanke bakin,duk yadda nayi kiyi itade Abrish ido ne nata, daker aka gama wanke bakin nan dan har kumfar lashe kin zubarwa tayi saita shanye kayan ta,ba yadda Nasra ta iya haka ta rabu da ita,wanke mata kai tayi kafin ta barta a toilet din dan tayi wanka,
Bayan tayi wanka ta fito Nasra dauko Hair dryer tayi cewa tayi ta zauna akan mirror chair, zama tayi tare da kallon mirror din,zaro ido tayi kafin tace kai yanake ganin mai kama dani anan, dariya Nasra tayi kece fa ba mai kama dake ba,
"Nikuma" ehman wannan mirror sunan shi da hausa ana cemai madubi,shi aikin shi kawai mutum yaga kanshi a ciki kinga ne, eh na fahimta yanxu, busar mata dakai Nasra tafara,shima dai kusan da rigima aka gama shi dan cewa tayi Nasra zata babbaka mata kaine,


"Kwalliya Nasra tayi mata wanda yakara fito da kyaun ta sosai, ga bakinta yasha maroon din jambaki, saita kuma kamar yammatan baturen nan, wata desigenr din Abaya ta dauko mata cikin kayan ta maroon color tasaka, gelen kuma tayi mata rolling dashi saita kuma kamar wata yar larabawa,ita kanta Nasra tsayawa kallon ta tayi saboda tsabagen kyaun da tayi, to koh ita Abrish tana mamakin itace haka, to wai daman haka nake ban sani ba tafa da,tare da shafa gefen fuskar ta,
Ammee ce ta shigo dakin Nasra kufito muje aci abinci ,"to Ammee"
"Nasra bakuwa mukayi ban sani ba" bakuwa kuma Ammee , ehmana bakuwa baga balarabiyan kawar ki zaune ba, saida Nasra tayi dariyan ta mai isarta kafin tace Ammee,Abrish dince baki gane ba, da sauri Ammee ta kara kallon ta, tab yanxu Abrish daman haka kike,masha allah yarinya ta kinyi kyau sosai, sai murmushi Abrish ke saki,

Kama hannunta Ammee tayi suka fito,Downstairs suka nufa runda suka fara saukowa hankalin kowa ya dawo kansu, su twins dake shan coffe duk sai suka sake kufunan su yafadi kasa ya fashe,Ashtar daya dago danya zuba masu tujara idon shi yayi arba da ita,baisan sadda ya fesu coffen dake bakin shiba nan danan ya fara tari Umar wanda shima be dade dazuwa gidan ba,hankalin shi gabaki daya yatafi kanta yana tunanin ina kuma suka samo balarabiyan yarinya a gidan,
Ammee ina kika samo mana balarabiyan yarinya kuma,hassan ke tambaya wanda bakin shi ya gaza yin shiru, Abrish cefa duk hada baki sukai wajen fadan sunan Abrish dai itafa,

Umme ma mamakin yar tata take wai daman kyaun nata harya kai haka, kai masha allah,
Duk zama sukai akan cafet da aka shinfida dan cin abinci kowa zuba abun dayake so yake,
Nafeesat wacce ta shigo ansha kwalliya ana ta baza kamshin turaren da boka ya bada sai yanga take, Abrish wacce takai loman shinkafa bakinta ta dago da sauri,kallon Nafeesat tayi, aranta tace kam uba daman maganan da aka fadamin da gaske ne aiko zaki ci ubanki ta kanki zanfara, upstair ta kalla bokitin da mai aiki keyin mopping dashi ta aje bata gama mopping dinba saboda Ammee data aiketa dauko mata wayanta a daki kuma akwai ruwa aciki, nuna bokitin Abrish tayi da hannunta ta yadda ba wanda zai gane,nanko bokitin ya matso daide saitin Nafeesat dake tsaye ta wajen upstair din tana amsa waya, kifa hannun nata tayi alamon kifewa,nanko bokitin ya kife duk ruwan dake ciki ya zubu mata a jiki,kowa dago kanshi yayi yana kallon ikon allah, karfen mopping din ne ya fado mata akai daide goshinta,dafe wajen tayi tare da sakin ihu dariya ce ta kama ilham dake gefe kowa ma dariyan yake yi kasa kasa ganin yadda goshin nata yayi wani zon toto dashi, saiyaba wa kwalliyan fuskar ta wani samfarin daban, juyawa tayi da gudu tana kuka ta fita a part din saboda bakin cikin ga aikin ta beyi ba ga ruwan dayayi mata wanka harda fashe goshi,amma bakomai akwai gobe,
Tabe baki Abrish tayi ta juya kanta dan cigaba dacin abincin ta,idon tane ya sauka a kulan da ilham ta bude na farfesun kayan ciki zata zuba wa Ashtar, kallon ta tayi tana karanta abun da take cewa, dazarar kaci wannan farfesun yaya Ashtar shikenan kaxo hannu wllh,
Oho basai yaci mugani ba Abrish ta fada, Ashtar daya debu zai kai bakin shi yaji zuciyar shi na tashi bai damuba yakara kusanta chokalin da bakin shi kafin kace kwabo amai ya taho mai da gudu ya tashi yayi inda suke wanke hannu amai yafara yi ba tsaya wa,kowa tashi yayi aka nufe shi hankalin su duk ya tashi,duk abun dayaci saida ya amayar dashi, duk ya fita hayacin shi, doctor aka kira duba shi yayi tare da samai karin ruwa,
Wannan wani irin ciwo ne lokaci daya, hajiya zainab ke fada wacce bakin ciki kamar ya kashe ta dan ilham ta gaya mata a farfesun tasa maganin,gashi koh ci beyi ba abun haushin, Abrish dake gefe duk budirin nan da ake ko ajikinta dan sai da tacika cikinta tayi nak, haka fanta saida tasha kusan gora biyar gana shida a hannunta,sai kallon kowa take daya bayan daya, aranta ko cewa take, mu zuba ni daku shege ka fasa,
Saikuma tai dariya tonuwa da Ashtar da tayi, shi baya cika takura ba da wani iyayi dani kake magana kadan ma ka gani.







*Juma'aht Mubarak yan'uwa musulmai ina ma kow fatan alkairi* *ya allah alkairi dake cikin wannan rana ka hada mu da shi*, *ya ubangiji allah duk wani sharrin dake cikin wannan rana karaba mu dashi* *Ameen ya rabbil alamin*πŸ™πŸ™πŸ™


*JUMA'AHT MUBARAK TO ALL MUSLIM* πŸ•‹πŸ•‹







Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR DAJI*πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM*(UMMON ABDALLAH 🀱)




β™§Pegeβ™§17.


*****


"Tunda Abrish ta shiga cikin motan nan ba abunda take sai tabe tabe, saboda wani irin laushin da taji akan kujerun kamar katifa,sannan ga wani abu sai juya shi ake direvan ta tsura wa ido duk inda yabi da hannun shi saita kalle shi, tana mamakin wannan abun dayake yi,zuwa can ta dauke idonta a kanshi ta maida kan hanya saboda taga sunfito cikin jejin, kallon jejin tayi nan take kewar namun dajin nan ya kamata, sun saba sosai lokaci daya kuma an rabasu, kallon akunta tayi wanda ke gaban mota zaune, kallon hanya taci gaba dayi tana mamakin dama haka garin yake sai ganin mutane take da shiga daban daban masu yanayi maban banta, wani nishadi take ji aranta wanda bata tabajin irin shiba,sai murmushi take saki abunta, duk abun da tagani saita juyo ta tambayi Nasra wanda wani shirmen idan tayi saide tayi dariyan ta mai isarta, Ashtar daya gaji da hayaniyar su, juyowa yayi yace kuyi mana shiru sai zuba kuke saikace lalatacen redio,murguda baki Abrish tayi anki ayi shirun kai ina ruwanka damu wani yasaka jinmu dole,aisai ka tushe kunnen ka koh,duk zaro ido waje sukayi yan cikin motan, Nasra da tunda Abrish ta fara maganan take zungurin ta akan tayi shiru dan tasan halin yaya Ashtar sarai bayason ana mai rashin kunya sannan in yayi magana dole abi abun dayace, inko kaki bi kaci ubaanka awajen shi, amma ita Abrish mai kankat agaban shi take zubamai rashin kunya, shima dai direvan jiran hukuncin da oga zai dauka yake, amma ga mamakin su sai sukaga yayi murmushi kawai tare da girgiza kai, aranshi ko cewa yake yarinyan saina koya mata hankali zatasan koni wanene, amma saiyaji tana cewa saide mu koya wa juna hankalin, da sauri ya kalleta taya tasan maganan dayake aranshi, kadaina mamaki dan nasan maganan da kake a ranka, Abrish ba kamar sauran mutane take ba, dan haka ka guji abun dazai hadani dakai, tam, tana mai juyawa taci gaba da kallon ta, Nasra da direva kuwa aransu suma sai cewa suke anya ba aljana bace ba, idan sunan da kuka bani kenan na amsa to, duk shiru sukayi ba wanda ya kara gigin yin magana aranshi, Ashtar kuwa daman shi yadade yana zargin aljana ce take rayuwa cikin mutane yau ko ya kara yarda da hakan,

Haka sukaci gaba da tafiya ba abun dake zaidasu sai sallah da cin abinci,masu bacci natayi suna tashi,Abrish koh tunda aka fara tafiyan koh rimtsawa batayi ba,bata da aiki sai kallon hanya tsakanin ta da Ashtar kuwa dasun hada ido sai harara da suke aika wa junan su,
Basu suka isa garin Abuja ba sai wajen karfe takwas na safe, haka Abrish ta sake baki tana kallon dogayen ginin dake garin Abuja, wajen karfe tara suka iso gida,shiga cikin gidan da sukayi saida kan Abrish ya sara mata, daga ido tayi tana kallon cikin gidan,mamakin ganin irin girman gidan da tsaruwan shi take,wannan shi ake kira aljannar duniya,suma su umme dai kallon gidan suke,duk kale kalenta bataga bishiya ba, jawo hannun Nasra tayi wacce ke rike da hannunta, lafiya kuwa Abrish dan ita yanxu tsoron ta take tunda har zata iya sanin tunanin mutum, kince min gidan ku akwai bishiya ni banga komai inba wannan tsaunin ba, ta fada tana mai nuna upstairs,dan dariya Nasra tayi tace suna bayan gida ai,to muje can,a a kinga bari idan munje kinyi wanka munci abinci sai ki kwanta ki huta idan kin tashi saimuje ko nanfa bayan gida ne,ba yadda ta iya haka ta bita suka tunkari cikin gidan,
"Mutanen gidan duk fitowa sukayi ana ta murna dawo wansu,harda su Badaru wa'inda suma sukazo taran nasu, babu wanda ya lura dasu Abrish dan hankalin su baikai wajen ba,part din Ammee duk aka nufa sai bayan an zaunane ana kara gaisawa sannan Aka lura da dasu umme,tambayan suwaye akayi,nan Abbey ke basu labarin sune suka taimaki Nasra, nan yara da manyan aka shiga gaisawa ana masu godiya, Ammee ce ta duduba bataga Abrish ba, a a ina Abrish tayi ne, suma sauran duk sai yanxu suka lura babu ita a wajen, Nasra ce ta mike tace bari na dubata a waje kila bata shigo bane,
To maza dubata dan nasan yanxu a wajen ta maqale,Ammee ta fada, waje Nasra tayi amma ba Abrish ba alamun ta, a a ina Abrish ta shiga ne, duk fa dubawan da tayi bata ganta ba, wajen masu tsoron gidan taje, tambayan su tayi basuga wata yarinya ta fita ba, gaskiya hajiya ba wanda ya fita in banda ku da kuka shigo gidan babu wanda yakara fita,
Komawa cikin gidan tayi hankali tashe dan koh sallama bata yi ba, "Ammee" "Ammee" banga Abrish ba,kamar ya baki ganta ba,wallahi bata tsakar gida nan kwata kwata, subuhanallah to ina tashiga Abbey ya mike yana mai tunkara hanyar waje suma mutanen gidan duk waje suka fito naiman duniya sunyi shi a filin gidan basu ganta ba,kuma ance bata fita ba,
To ina yarinyan nan tashiga ne, jama'ah hajja take fada,duk shiru akayi can Abbu ya dago da sauri yace kuna da bishiya ne a gidan nan, yo danan bishiyoyi kai duk suna bayan gida,inji hajja,
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace tana can, can ina, Abbey yake tambayan shi,bayan gidan ai yadda ta kwana ta wuni bata hau bishiya ba, nasan idonta idon bishiya to sai ta hau shi dan haka ku kwantar ma da hankalin ku tana can nasani, to ya akai tasan da bishiya a bayan gidan,inji Ahfrah da ta kosa taga wannan yarinyan,nice na fada mata wllh dan da muka shigo gidan ta fara mitan ita bataga bishiyan da nace mata muna dasuba shine nake fada mata a bayan gida suke,
Su wllh sai yanxu ma tunanin duba bayan gidan yazo masu kai, Ashtar wanda tunda suka fara naiman ta bai sani ba yana ma dakin shine dan har yayi wankan shi ya shirya cikin kananun kaya dasuka amshi jikin shi, yafito dancin abinci ya iske falon wayam ba kowa hayaniyar su yaji a tsakar gida, fito wa yayi yana tambayan ba'asi aka gaya mai,dan tsaki yayi yace kuma tunda kukaga baku ganta anan ba aisai ku duba wajen aminanta mana, kaiko Ashatu yaushe tazo garin balle hartayi aminai, hajja aminan ta bishiyoyi mana, yafada yana mai nufar hanyar dazai kaishi bayan gidan,suma rufamai baya sukayi,

"Sanda sukaje wajen basuga kowa ba,kallon saman bishiyoyi suke ko zasu ganta dan har kiran sunanta suke amma bata amsa ba, itako tunda sukazo wajen tana kallon su tayi banza dasu dan tana cikin lambun wajen abunta ta dale bishiyan mangoro wanda ta gama tsinka tana shan abunta,
Ashtar ne yanufi cikin lambun dan yasa kila tana can, bin bishiyoyin yayi da kallo haryazo kan bishiyan mangoron da take kai, tana kwance abunta hankali kwance shanma mangoron ta take, kallon ta yayi rai bace,yace dan wulakanci kina jin ana naimanki amma kikayi wa mutane shiru,banza tayi dashi, sauko kasa nan ma shirun dai nace ki sako kasa koh,kallon shi tayi kafin ta diro daga saman bishiyan saboda hango su Abbu suna zuwa wajen, dayake ta juya bayan ta bamai ganin fuskar ta sai bayanta wanda gashinta yazubu har wajen kafafunta, kallon ido cikin ido sukeyi wa juna ita da Ashtar, kafin Ashtar ya dauke idon shi akanta saboda wani kalan abu yake gani a idon nata,bazai iya juran kallon idon ba,
Su Ammee ta suka karasu wajen Ammee tace,Abrish daman nan kikazo hankalin mu duk ya tashi juyowa tayi dan tayiwa Ammee magana ,ai mutanen gidan nayin arba da fukarta suka fara kankamai juna,masu addu'a nayi masu naiman hanya tserewa nayi, Badaru daya kankamai hajja yana fadin, wa'innahu min sulaimanu wa'innahu min dauda wa'a aljana bazan kara yin fashin yin zakka ba,Badaru cikani kagamin ja'irin yaro in aljanar cema wannan Addu'an taka saide tasa takara kame ka, zaka cikani kosai naci mutumcin ka Abbey ya janye mata shi dan Badaru duk ya gigice danshi a tunanin shi aljana ce ganin irin kyawunta sannan farinta har daukan ido yake ga idonta blue color ga gashin har kafa ai dole ya rude,duk Addu'an da tazo bakin shi yi yake, bashi kade ba hatta hajiya saratu garin gudu bata lura da minjagara ba dake aje a kasa takashi tayi hakan yasa ya dago ya bige mata baki,kafin kace kwabo bakin ya fashe ya kumbura ye suntum dashi,hajiya falmata da hajiya zainab ruwan agwagi suka fada ,Ahfrah ko juyawan da tayi kanta ya bugu da icce nan goshinta ya fashe,ilham da Nafeesat mantawa sukai dasu kishiyoyi ne alokacin rumgume juna sukayi suna ihun aljana,twins ko bayan Ammee suka boye saikace ba maza ba, har gwanda ma Abba yusuf da Muhammad da matar shi safiya suna gaife sai Addu'an suke suma,tsawan da Ashtar ya buga masu ne yasa duk kowa natsuwa, Abrish koh dake gaife in banda dariya ba abun da takeyi,wannan dariyan nata kara hautsina masu ciki yake yi, kallon ta Ashtar yayi kafin yace yimin shiru kema oho ko kallo bai ishe taba, saida tayi dariyan ta mai isarta kafin tayi shiru Abbey ne yace zo yata,matsowa inda yake tayi kallon mutanen wajen yayi daga masu fashe shen baki sai masu fashe shen goshi kallon su hajiya falmata yayi wa'inda sukayi tsamo tsamo acikin ruwan agwagi,Abba yusuf yace aisai ku fito, ko fitowa sukayi, kowa ya taru banda Mubarak, ina Mubarak ne Abba dan allah asauko dani,duk kallon inda mai maganan yake sukayi,yana can saman bishiyan kwakwa wacce ko da kudi aka hadashi bazai iya hawa ba amma yanxu gashi garin gudun aljana ya haye abun shi,dariya ce ta kwace wa Ashtar bai shirya ba kafin ya dago yace da waya hau dakai,ai malam yadda ka hau haka zaka sauko, wllh bro bansan yadda na hauba ku taimaka ku sauko dani,sai dariya suke mai kafin Abbey yace adauko tsani asamai,tsanin aka dauko aka samai dakyer ya sauko duk ya hada uban zufa,
"Ku yanxu in aljanar ce haka zaku dinga gudu fisabililahi, to ba Aljana bace sunanta Abrish itace ta cece Nasra hannun wa'inda suka saceta, Abrish ga yarana da kani na sai matan shi ga yaran shi sai wannan Badaru amini na kallon Badaru tayi nayan sakanni kafin ta dauke kai, ta maida kallon ta kan hajiya zainab da akace matar shice murmushi tasakar masu wanda ita kadai tasan ma'anar shi, Abrish ga Ahalina,kuma ga Abrish, fatan zaku hada kai kuzama yan'uwa, insha allah Abbey,ita dai Abrish batace komai ba sai murmushin da tayi,tanabin kowa da kallo daya bayan daya,a haka dukan su sukayi cikin gida ,saide haushin Abrish ya kama su hajiya saratu da yayyan su lokaci daya sukaji tsanan ta.








*MUSU YIN COMMENTS INA GODIYA SOSAI SOSAI ALLAH YA BIYA MAKU BUKATUNKU DUNIYA DA

Please Login or Register in order to submit comment