You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rasa maize ce mata,jikin shi sai rawa yake saboda bacin rai idon shi ya kada yayi ja, tunda yake ba wanda ya taba kallon cikin idon shi ya gayamai magana son ranshi irin yarinyan nan,da mai take takamane ita har wacece dazata fadamai magana yadda taga dama,umar ne ya rike shi ganin yada yake yunkurin kai mata duka, shikuma yadda ya fuskanta kamar yarinyan ba ita kade bace,duba da yadda hatta kalan idonta ya canxa,dan haka ya tunkare ta yanxu komai zai iya faruwa,
"Kinga yata kiyi hakuri ki sakin mata hannun,insha allah allah baza ta kara maki haka ba itama ta gane kuskuran ta, batace wa Abbey komai ba sai dauke kanta da tayi gefe,
"Kekuwa haba yar albarka yar kyakyawan da babu irin ta kaf fadin habuja, aike yarinyan kirki ce dan allah ki sakar wa yar'uwar ki hannunta, hajja ni da kikace aljana ce,
"Ni ayaushe na fadi hakan yarnan,cewa nayi kaf fadin Nigeria babu kamar ki a yin sallah da azumi sannan gaki da tausayi,zakka da aikin hajji baya wuce ki, ni na isa nace maki aljana, ai nasan hakanan bazaki lauye hannun yar banxa ba,saide in rashin kunya tayi maki saboda kina ganin tanan, to tunda uwarta ta haifeta ta iya fitsara ke tun tana jaririya,balle ga wannan bakin nata kamar na aku saboda da surutu,idon nan nata ko ta murmura shi saiyayi kamar na wata tinkiyata danayi akauyen mu wllh ai....., kinga hajja ya isa haka,tsit hajja tayi tana zarar ido kamar wacce tayi wa sarki karya dan tana tsoron itama yanxu ta sami rabon ta,
saboda wannan nishadin da kika sani na yafe mata, malama ilham sai a aje hannun koh, aiko tana gama gayan hakan hannun ilham ya dawo daide, dariya da hawaye ne ya wanke mata fuska,nagode nagode anty Abrish insha allah babu ruwana dake yanxu, nagode ta fada tamai tatare zanin ta ta fice da gudunta daga part din,

"Ashtar shima upstair ya haura umar yabi bayan shi, itama Abrish hanyan waje ta nufa ba tare da takara ma kowa magana ba, Abbu ne ya tashi yabi bayanta, Abrish tsaya anan, tsaya wa tayi ta juyo tana kallon shi harya karaso, maiyasa zakiyi haka ne Abrish,ba nace ki dunga kokarin sarafa fushin ki ba,
"Bazan iya ba Abbu a haka nake sannan bazan iya canxa Rayuwa ta daga yadda take ba, duk wanda yataba ni bazan kyale shiba sainaga bayan shi, Abrish bata yafiya, Abrish daukan fansa ta sani akan abokin gaba, ba yafiya ba, tana gama fadin haka ta wuce,

"Daga hannu sama Abbu yayi, ya ubangiji allah narokeka daka bayana mana gaskiyar al'amarin dake tattare da wannan baiwa taka, ka bude mana sirrin boyen dake tare da ita,ameen ya allah.



Nima nace ameen ya allah, dan wannan abun da daure kai yake.










Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧22.

*****

"Alhaji daman inason muyi wata magana ne in ba damuwa, ina jinka malam Abubakar ai yanxu anzama daya, to daman maganan ba akan kowa bane sai kan Abrish, a gaskiya Alhaji ina ganin zaman Abrish anan ba mai yuyuwa bane, saboda hakan zai iya zama matsala ga mutanen gidan nan, Abrish ba kamar sauran mutane take ba, rayuwar ta na cike da abubuwa ma banbanta wanda ba kowa ne zai iya fahimtar hakan ba, shiyasa nake ganin zaman mu a jeji yafi alkairi ba tare da mun shiga hakkin wani ba,
Ajiyar zuciya Abbey ya sauke,kafin yayi dan murmushi yace, malam Abubakar kamar yadda nafada maka tun farko zan rike Abrish awaje na,to babu abun daya canxa, kada ka manta allah yana jarabar bawan shi da kaddara acikin rayuwar shi dan ya gwada imani shi,to itama Abrish hakane tata kaddarar, kuma bawai dan ubangiji baya sonta bane yayita a haka saidan ya gwada imanin ta, mude abun da zamu cigaba dayi mata shine addu'a tare da naima mata magani ko allah zaisa a dace, kuma insha allah Abrish a wajena zata zauna,
Ku anriga da ansama maku gida a kaduna acan zaku zauna fatan hakan yayi, kagama muna kusa sosai ziyara bazata yi mana wuya ba,
"Hakane Alhaji, bamu da abun da zamu saka maka dashi saide muyita maka Addu'an fatan alkairi a rayuwa, babu komai ai yi wa kaine,
"Hakane" saide inason in fada maka wata magana game da naiman maganin Abrish, matsalan itace tun muna enugu ,nakan fita cikin gari inda nasan akwai musulmai malamai,dan suzo suyi mata addu'a ko allah zaisa a dace,
"Saide wani abun mamakin shi ko munxo da malamin wllh za'a nemaita a rasa tun tana karama ,karshe ma da nayi hakan kusan sau uku, wllh kashedi aka bugamin akan idan na kara yunkurin kiran wani malami dan yayi mata magani za'a kashe ni ko kuma a dauke ta gabaki daya bazan kara ganin taba, hakan yasa na hakura da zuwa wajen naima mata lafiya naci gaba da kai wa allah kukana,
"Amma kulum abun nata saici gaba yake maimakon raguwa, saide bama cire tsan mani, nasan allah maji rokon bayin sane koma bai manta da muba, yana sane damu zai amsa addu'ar mu a lokacin da bamuyi tsanmani ba,
Zance ka gaskiya ne malam Abubakar, insha allah zamuci gaba da addu'a, to amma wayayi maka kashedi ne malam Abubakar,
Wllh ni kaina ban sani ba Alhaji,tsakar dare naji ana min magana da wata murya mai ban tsoro wllh tun daganan na hakura,har allah yayi ikon sa, amma wannan abun da daure kai yake, haka sukaci gaba da tattauna wa akan matsalan Abrish,


"Auch momy kiyi a hankali mana yanamin zafi fa, to ke in ba a gasa maki hannun nan naki ba ai yau sai allah,tsakani nan da wannan yarinyan sai allah ya isa tsinana kawai, momy nidai babu ruwana wllh hakanan ta jiki duka yaushe na samo ta sakemin hannun nawa ko awa daya ba ayi ba, nidai kiyi shiru dan allah kada ki sake jamin wani bala'in ina zaman zamana,
"Kinsan allah ba kyale yarinyan nan zanyi ba, saina koya mata hankali ba wai tsoron ta nake jiba, hhhhm bakyafa tsoron ta kikace momy,amma shine da tace maki kika kara tako daya zaki koma gida ba kafafu, maiyasa baki matsa ba momy, inba tsoro kike jiba,
"Ke waya gaya maki tsoron ta naji kawai de ina mamakin rashin kunya ne irin nata, momy ta fada tana wani mitsi mitsi da ido, hhm momy kenan wllh kinsan allah momy dakin kara taku daya saide ki kuma gida ba kafafun wllh,dan wllh yarinyan nan ba tausayi gare taba, momy gwanda ki sama wa kanki salama ki fita harkan yarinyan nan,
"To sannu uwata nace sannu uwata, to wllh kinji na fada maki saina dau mataki akan ta, to shikenan momy allah ya bada sa'a, ilham ta fada tana mai tashi ta wuce bedroom abun ta,


"Come down mana Ashtar, yarinyan karamar yarinya ce,sannan idan kayi la'akari da yanayin ta zaka gane ba ita kade bace,dan haka kayi mata uzuri, kuma ka fita harkan ta kowa yayi rayuwar shi,
"Yarinyan" "yarinyan fa kace, shine harta iya duban tsabar idona ta gayamin magana son ranta, hmmm shiga rayuwar ta yanxu na fara, mu zuba ni da ita aga wazaici riba, yana gama fadin haka ya shige toilet abun shi,
"Friend kenan wllh a yadda naga idon yarinyan nan yau daga gani bazatayi tausayi ba, kaiba sarkin zuciya ba to ga wacce zatayi maganin ka,
Wai tsaya koh de Friend son yarinyan nan yake,to inba haka ba ina ruwan shi da ita, a lalle Friend ka fada da yawa, in tayi tsami maji, hakade yagama surutun shi shikade yafita a dakin dan yasan a yanxu ko yadda ogan ya hau bazai sauka ba,


"Wa'innahu sulaimanu wa'innahu minan shedanin rajim,ah uzubil lahi mina shaidanin rajim bismilahir rahmanin Rahim,
"Lafiya hajja daga ganin nashigo wajen ki zaki fara jan dogayen ayoyi, Abrish ta fada, tana mai naiman waje ta zauna akan kujeran dake falon hajja, gwagona mai kike nema dan allah, da bazaki samo a wajen su Ameena ba saikin zo waje fisabililahi, ni wllh komai kike bukata basai kinxo ba ki aiko a amsan maki, hajja ta fada tana mai zare ido duk ta hada uban zufa kamar wacce tayi aikin wahala,
"Aini hajja yau a wajen ki zan kwana dan haka inane dakin ki dan ina gefen ki,
Ai hajja batasan lokacin da ta sauko daga saman kujera ba zuwa kasa, innadillahi'wa'ina ilahi raji'un, dan girman allah kiyimin rai,kwana a wajena kuma, aifa saiki yi, Abrish ta fada,tare da kwanciyar ta a saman dugon kujera, to bari ni intafi wajen Ameena ko saratu kokuma wajen halmata, sai in kwana acan saike ki kwana anan,
Ai hajja babu inda zaki yau munanan tare, ni so nakema kiban labari mai dadi, kinsan ku tsofafi kun iya labari sosai,
Wllh banda ni, ban iya komai ba keni in banda karatun Qur'ani ba abun dana iya,
"Kinga shikenan saiki koyamin nima daman banyi nisaba,
Au waike daman kinsan yadda ake karatun Qur'ani ne, mai kike dauka na daman,
"Niba musulma bace kamar ki"
"Ni na isa nace ke ba musulma ba, saide sadda aka raba tausayi da imani to ke bakya wajen, nice banda tausayi da imani,
"Nifa ba haka nace ba, laibe nane ya ciji harshe na.






🤣🤣🤣 to hajja asha bacci lafiya tare da Abrish,yauke baccin ki harda minshari wllh.








Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)
*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)


♧Pege♧23.

*****

"Ashtar ne bayan ya kamala cin abinci ya tashi zai wuce dakin shi,Abbey dake zaune a daya daga cikin kujerun falon yana karanta jarida, ya dago kai ya kalle shi,
Kai zunan, Abbey ya kira shi, gani Abbey,maikake nufi ne Ashtar, shiru Ashtar yayi dan shi baisan mai yayi ba, yanxu kai abun da kake ka kyauta wa kanka kenan, kayi hakuri Abbey saide bansan laifin dana yiba, ai bazaka sani ba , ina ankare dakai tunda aka daura maka aure har zuwa yanxu amma koh hanyar part dinka baka naima ba, ko kana nufin su matan da aka aje maka ba mutane bane,
"Shidai shiru yayi dan harga allah mantawa yake ma dayana da aure,in ba an tuna mashi ba,
"Yanxunan basai anjima ba katattara kayan ka kazo ka wuce part dinka wajen matan ka, umarni ne ba shawara ba kaji nafadan ma, "to Abbey" ya fada murya ciki ciki,ya tashi ya haura sama , Ammee da tashigo falon yanxu hannun ta rike da cup din coffe , binshi tayi da kallo, tariga tasani baya son auren nan biyayya kawai yayi, to yazaiyi dole yayi hakuri tunda ya riga daya amsa tun farko, fatan ta dai kawai allah ya bashi ikon yin adalci,
"Ammee kinga Abrish kuwa, Nasra ke tambayan Ammee,Abrish ai tana wajen hajja tace yau acan zata kwana, zaro ido Nasra tayi kafin kuma ta kwashe da dariya, tace yau lallekam hajja na da yar kwana,shine ta tafi babu gayata, to nima natafi acan zan kwana,
"Kadafa kuje kusamin uwa a gaba na fada maku, Abbey taya ta kwana fa zamuyi, to saida safe ki gaida hajja,zataji Ammee bye bye,

"Da sallaman ta tashiga wajen hajja, yanayin da taga hajjan ne yasata kwashe wa da dariya batare da ta shirya ba, dan gabaki daya ta jike da zufa duk da akwai Ac a dakin sannan kuma ga fanka kunne, amma hakan bai hanata yin uban zufa ba, itako oga boss tana zaune dirshen ta tasa kwanun nama a gaba tana ci abun ta,
"Hajja jin ana dariya ta juya dan ganin mai dariyan, hmm yarinyan dole kiyi dariya tunda kinsa ana kokarin kashe ni lokaci na baiyi ba,daman nasan duk kun tsaneni yan gidan nan amma babu komai allah na gani kuma yana jinku duk sai yabi mani hakki na akanku, tunda daini ba abun danayi maku, saikuma ta fashe da kuka saikace wata karamar yarinya haban zaninta tasa ta fahce majina, ita dai Nasra wayama ta ciro ta kama yiwa hajja video, yanxu fisabililahi naman dana tara na babban salah na boye shi ko jikokina na hana, ina tsakuran abu na , amma wannan yarinyan kiri kiri tace min wai hajja ina naman ki na sallah da kika boye dakomin zanci, koma yanxu kace mata aljana ta nuna ma iya kanka, to inba aljana ba yaza'i tasan da naman nan a dakin,
"Hajja bade zaki daina cemin aljana ba ko to zanko nuna maki aikin aljanu yau,
Ni na isa nace maki aljana gwago na, ai ko uban uban ubana bai isa ya kira ki aljana ba balle ni karan kada miya, hmm nadai gaya maki yau komai zakiyi saina kwana a wajen ki kima zauna da shirin ki,
Ashtar ne yayi sallama a falon ciki ciki duk yabi ya wani hada fuska,Nasra dake ma hajja dariya tayi saurin rufe bakin ta, idon shi akan Abrish ya sauka da ta tasa uban nama a gaba tana ci gefenta ya kalla inda ta kwaso uban laimoka kusan gora goma ga gora uku da babu komai alamun an shanye sannan ga wani a bude, wajen ta ya nufa kai tsaye,
'Hajja da taga haka harda hamdalan ta ta dauka zaiyi ma Abrish wani abun ne, amma ga mamakin ta waje ya samo ya zauna kusa da Abrish din sannan yasa hannu acikin kwanon naman shima ya dauka tare da daukan goran coke ya bude,yana cin nama yana korawa da laimun, daga hajja har Nasra sake baki da hanci sukayi tare da kallon shi da mamakin abun da yayi, ita ko Abrish ko a jikinta ko kallon bai isheta ba, saima kallon Nasra tayi tace ke bazaki zo ki kwashi rabun ki ba, tunda yau kakarmu tayanke saka, aisai mu kwashi gara, idan kuma zaki tsaya kallo sai kiyi tayi aiki ke yasama, kallon Ashtar Nasra tayi taga ko inda take bai kalla ba saima fukar shi dake hade tun sanda ya shigo, aiko tashi tayi tare da dawowa inda suke ta zauna , itama ta fara cin naman,
"Hannu hajja ta daura akai kafin tace yau nashiga uku ni dijee wannan matsifa har ina yarinya kinzame mun bala'i, "nice bala'i hajja " to in bake ba wacece fisabililahi kunzo kunsa min nama a gaba kuna ci, harda wannan basamuden da nake tunanin zai tsawatar maku sai shine ma yakara bada goyon bayan cigaba da abun da kukeyi ,
"Kiyi sha'anin ki hajja lokacin ki ne yanxu, nawa yana zuwa anjima,
"Mikewa Ashtar yayi tare da fita acikin falon batare dayace wa kowa kala ba, binshi da kallon gefen ido Abrish tayi , kafin ta tabe baki, tace um dole dai yau wani yaje ya kwana wajen amare ,
"Wllh nama na dakaci allah ya isa ban yafe ba kuma sai ka biyani kayana,
Hajja kitashi ki wuce ki kwanta dare yayi kina damun mu da hayaniyar ki, murguda baki hajja tayi tace daman aini zama na a wajen nan banda hawan jini ba abun da yake jamin,kuma nama na da akaci ban....... nayafe wllh aike yarinyan kirki ce wazaice bayafe maki ba, hajja ta fada ganin irin kallon da Abrish tayi mata,tashi tayi ta lallaba ta shige daki harda murza key a kofan, toilet ta nufa dan rage maranta dan tun dazo ta kule mata,
"Wai allah amma bazan yafe wa wannan yarinyan ba muguwa kawai, hajja ta fada bayan yafito daga cikin toilet din, hajja dan karo mana sanyi wannan abun naku fc kuke cemai ko Ac , mutuwar tsaye hajja tayi, kafin ta juya da sauri ta kalli saman gadon ta, Abrish tagani zaune tsakiyar gadonta ga wasu kananun macizai sai yawo suke akain gadon, ihu ta saki kafin kuma ta fadi kasa a sume,
"Ruwan da aka yayyafa matane yasa ta farfado daga suman da tayi, amma saide bata cikin hayyacin ta dan sai sanbatu takeyi,
"To ubangiji na shine allah,sannan shugaban mu annabi Muhammad saw, eh to kullum bana fashin sallah wllh, zaka kuma ina naga kudin yi, yayyana kuma ai sune masu kudin sune masu zakkan Amadu da yusufa ba, dan shiku Abubakar yanan kabari yama rigani zuwa, to nidai bana wasa da addu'a wllh,
"Doctor yi mata allurar bacci dan bata hayacin ta, bakuga sanbatun da takeyi bane, Ashtar ya fada yana mai kumshe dariyan shi, ganin hajja sai amsa tambayoyin kabari take a duniya, duk ta fita hayyacin ta,

"Wai garin yaya hakan ta farune, Abba yusuf ke tambaya, wllh Abba muna zaune nida Abrish a falo mukaji ihunta to shine fa da mukazo muka isketa a sume, shiyasa muka kira ku, to allah ya kyauta ameen, Ashtar ne yaja hannun Abrish sukayi waje,
"Mai kikayi mata, maiko zanyi mata, ko kaji ance ina dakin ne, abun ya faro, hmm nafasan halin ki, amma saide bansan rashin tausayin naki yakai haka ba tunda bakya ragawa tsofafi,
saikuma kayi ai, nikaga ban guri in wuce, bani da lokacin wannan abun, dan naga baka da abunyi nikoh ina dashi,
Tafadi haka zata wuce,
"Ki sani komai kike idona na kanki, murmushin gefen baki tayi, kafin tace to muzuba muga wazaici riba, shikenan zamu gani, yanxu takun sakan ya fara, yana gama fadin haka ya wuce, oh Ashtar kana wasa da wuta, bakasan wacece Abrish ba, kaci darajan abu uku wllh daba haka ba hmm, ta fada tana cije gefen bakin ta, ta koma cikin part din hajja,



"Alhaji wannan shine photon yarinyan saide babu wani bayani akanta, illah bayanin da akayi maka akanta,
"Bude picture din Alhaji haruna yayi ya kalla, saide maimakon picture din Abrish saiyaga photon gwagun biri ajiki yana dariya, wannan wani iskancine photon gwagon birin ne yarinyan, kamar ya Alhaji, wurga mai photon Alhaji haruna yayi, dauka yayi ya kalla kai dafa kaina na dauke ta wllh toya haka, fitar min a anan tunkan inci mutumcin ka shasha zan nemota da kaina, dan bazan barta ba wllh .









Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI*🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧24.

*****

"Da sauri sauri yake sakuwa daga upstair din,yanason ya biya ta wajen hajja kafin ya wuce aiki, harya kusan fita daga cikin falon yaji ana mai magana, dakatawa yayi daga tafiyan da yake yi tare da juyowa ya kafeta da idon nan nashi, maisa yanxu mutum ya rude,
"Cikin in'ina tace, am daman.... daman naga zaka fita ne batare daka karya ba, sai wani sosa kai take dan tasan ba lalle ne yama kula taba kasada ce kawai tayi,

"Yaushe muka fara wannan wasan dake,ko kinga nayi maki kama da maijin yunwa ne, ko nidin yaron kine, kiyi rayuwar ki kamar yadda kuka saba kada kuce zaku shiga harkata cikin gidan dan ni ba sa'an ku bane, kubar ganin wai an daura mana aure daku kuce zaku rainani, haryanxu baku da wani matsayi a wajena da har zakuyi min girki inci,ki fadawa dayar itama ku fita sabgata,ina fatan kin fahimta kinji ni ko baki jini ba,
"Naji" ko kala baikara cewa ba ya fita abun shi,
"ilham dake labe tun dazu ta fito tana kwasar dariya, wanda ya kara sa ran Nafeesat baci,
To uwar shishigi,wani iyayin ne ya kaiki yimashi girki, waike a tunanin ki zaki iya jawo hankalin shi kanki, kina mafarki yarinya, kwanaki kadan suka rage na fitar dake cikin gidan nan saboda ni kade nafi cancanta da zama matar yaya Ashtar,ba tare da wata ba, kuma ki ributa ki aje wllh saina sa kin fita acikin gidan nan ba tare dakin shirya ba,amma kafin nan zanso kiga yadda zamu sha soyayyar mu nida mijina, yakamata kisani ilham tafi karfin ki,
"Hmmm, ilham kenan kina bani dariya wllh, ke a tunanin ki zaki iya jawu hankalin yaya Ashtar kanki kenan, bari na fada maki wani abu da baki sani ba, muddin ina raye to babu wacce ta isa tayi rayuwa tare da yaya Ashtar,in dai bazan samai shi ba to babu wacce ta isa ta same shi, kibar ganin kema matar shi ce kamar ni, a lokacin da zan juya kambuna wllh ko ganin shi sai yayi maki wuya,ina mai kara gargadin ki daki tsaya iya matsayin ki acikin gidan nan kada kice zaki wuce iyakan ki dan karanmu dake bazatayi maki dadi ba,
"Oh haka kikace",
"kware ko kina da jana"
"Bani dashi saide ince maki"
"Muzuba mugani" ,za aga wa zaici riba tsakanin mu,
"Shikenan zamu gani"


"Hajja ba ita ta tashi ba sai wajen karfe biyar na asuba, saide wannan karan batayi sanbatun da tayiba tashin ta na farko,
"Sannu hajja kin tashi ya jikin"
"Da sauki Nasratu" , karfe nawa yanxu ne wai, hajja asuba ce yanxu, tun jiya wai nake kwance, ehmana hajja, to wai maiya sameki ne jiya ihun ki kawai mukaji fa, kuma koda mukazo a sume muka ganki, shinefa muka kira su Abbey aka kira likita ya duba ki,
"Um ni kina tacewa ku ku to kedawa dan dai waccan aljanar yarinyan a dakin nan na isketa, kuma ai ku biyu na baro a falon na shigo dakin,harda makulli nasa na rufe dakin, amma ko dana fito daga ban daki nan nazo na isketa zaune akan gado nafa tare da macizai,
"Kallon ta kawai Nasra keyi da mamaki dan ita tana tunanin har yanxu hajja bata dawo hayacin ta bane, to wai watake nufi ne,
"Hajja wa kike nufi wai ni ban gane ba"
"ai bazaki gane ba"
"Wa ko nake nufi banda waccan yarinyan da uban ki ya dauko mana" ,aini Amadu in banda bala'i ba abun daya kwaso mana,
"Kai hajja kiji tsoron allah, Abrish din da muke tare da ita a falo, shine zakice kin ganta a dakin ki, saikace ita aljana ce da zata shigo maki daki batare da key ba, bayan kin rufe kofar allah ma yaso akwai wani key din,da jiya saide kiyi bunga yau akaiki kabari, saide muce allah yaji kanki,
"Kuka hajja ta fashe dashi, yanxu yar nan, ni kikewa fatan mutuwa saboda bakisan annabi ya fako ba, to wllh bani zan mutu ba saide uban ki Amadu ko uwaki Ameena,
Kujimin hajja nan, bayan nan jiya jiya kika gama amsa tambayoyin kabari a dakin nan,shine yanxu zakice bakya son mutuwa aiko dole ki laika kabari, daman ai kinsha miya da yawa,ya kamata kibi bayan Modibbo wllh,

"Innadillahi'wa'ina ilahi raji'un,wllh saide iyayen ki su mutu ba ni ba, kuma bari uban naki yazo yayimin tsakani dani dake, tare da waccan aljanar yarinyan, dan bazaku kashe ni lokaci na baiyi ba,
Kidai tashi kiyi sallah dan an kira tun dazu,in kuma zaki zauna ne kina surutu,kika mutu warakili yasami na bugu, babu ruwana,
Ta allah ba taki ba wllh muguwa kawai, dan zama da waccan mara imanin yasa kema kin zama muguwan karfi dayaji,

"Wacece mara imanin,taji anfada daga bakin kofa, da sauri takai kallon ta wajen, dariyan yake ta saki, kafin tace ni na isa na kiraki mara imani,wllh ba dake nake ba, da wata kawatace na yarinta to shine ta kirani a wayan salula yanxu, am daman sallah zanyi bari kiga natafi nayo alwala, ai kaf fadin gidan nan babu wanda ya kaiki tausayi da imani , am to to ni nawuce bandakin, da sauri hajja tayi cikin bathroom, murmushin gefen baki Abrish tayi kafin ta juya ta koma falo,
"Nasra da ta idar da sallah, da sauri tabi bayan Abrish zaune ta ganta a kasa tasa robar ice cream a gaba tana sha, ga chocolate da ta bude tana ci, zama tayi a gefen ta kafin tace,
Abrish yanxu da sanyi safiyan nan kike shan zaki, kefa macace bai kamata kina shan zaki sosai ba, ci kanki batace mata ba,
"Daman tasan

Please Login or Register in order to submit comment