You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taga anyanke kiran,daga kafadunta tayi kafin ta juya dan kumawa saide daga kafan da zatayi taga samari biyu a gaban ta bude baki tayi zatayi magana taji anshaka mata wani abu ta bayanta tun daganan bata kara sanin inda kanta yake ba,zarah da taji shiru shiru bata dawo saita bita dubawan duniya tayi bata ganta ba hankalin tafa ya fara tashi dako wayanta tayi ta fara kiran ta amma sai taji ringen din wayan akusa da ita ko da ta juya,ganin wayan tayi akasa dukawa tayi ta dauki wayan dan harma ta fashe saboda faduwan da tayi,innadillahi'wa'ina ilahi raji'un tai tananata wa saboda yadda gaban ta ke faduwa,bata fatan abun da zuciyar ta ke saka mata yazama gaskiya,bata kuma cikin wajen ba mota tashiga tanufi gidan su Nasra koh da taje gidan ta duduba ba Nasra dan ko mai kama da ita bata gani ba,dakin Ammee ta nufa zata bude kofan ta shiga itama Ammee ta bude kufan ta fito, a a zarah lafiya kuwa ko har kun tasu daga wajen bikin ne,a a Ammee Nasra ta dawo gida,Nasra kuma aini tun sadda kukabar gidan ban kara ganin taba nama dauka tare kuke,innadillahi'wa'ina ilahi raji'un lafiya kuwa zarah,Ammee akwai matsala kamar ya akwai matsala,Ammee banga Nasra ba,kamarya baki ganta ba kiyimin bayani yadda zan fahimta,nan zarah takwashe duk yadda sukai da Nasra ta fada mata,walahi Ammee da nasan intafita bazata dawo ba da ban barta taje ko ina ba ta fada cikin kuka,itama Ammee hankalin ta ya tashi sosai inban innadillahi'wa'ina ilahi raji'un ba abun da take nanata wa,zuwa lokacin kuma mutane sun fara dawo wa duk wanda aka tambaya yaga Nasra saide yace a a,nan danan gidan yadauka gabaki daya da bacewar Nasra,hatta amaren kowacce tayi zoru zoru da ido,aransu ko sakawa suke arasa ranar da za'a sace kanwar ango sai ranar auren su,suko sunshiga uku,Ashtar ko daman da haushin diner aranshi saikuma gashi yanxu an sace mai kanwa duk akan wannan bazar diner idonshi yayi ja sosai saboda bacin rai haka jijiyuyin kanshi duk suntashi,haka aka shiga neman Nasra amma duk inda ake tunanin zataje anje babu ita ,kowa fa yashiga tashin hankali,hajja ko kuka take kamar wata karamar yarinya tana cewa ita wannan auren bakin aure ne tunda arasa sadda za'a sace mata jika sai ranar auren,kowade yayi jigum jigum dan wannan tashin hankalin har ina allah dai ya bayanata cikin kushin lafiya,


Oga ina muka nufa da wannan yarinyan ne, kai jagwal mubar arewa gabaki daya ka dauki hanyar ENUGO,dan indai mukace zamu aiwatar da aikin mu a arewan nan zasu iya kamamu,musanman ma daya kasance yayanta soja ne yanxu gabaki daya garin zai dauka dan haka mike hanya kawai, angama Oga.













Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR* *DAJI*πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

*NA* *SABUWAR*
*MARUBUCIYA*
*FATEEMAH* *ALMUSTAPHA* *ADAM*
(UMMON ABDALLAH🀱)

Pege12.


*****

Bangaren Ashtar kuwa,amsan wayan Nasra yayi a hannun zarah number da aka kira ta dashi ya cire, yazeed ga number nan na torama yanxu nan a binciku min mai ita,to yallabe,kashe wayan yayi kallon umar yayi yace muje,basu zarce ko ina ba sai hotel din da akayi diner din,wurin manager sukaje,ID card dinsu suka nuna mai munzu binciken dakin camera ne saboda sace wata yarinya da akayi,muna fatan zaku bamu hadin kai muyi binciken mu lami lafiya batare da wani hayani ya ba,kaisu dakin camera din yayi,dubawa sukayi har akazu inda ta fito dan amsa waya,da inda samarin nan suka zagaye ta saide abun ban haushin shine duka fuskar su arufe take da wani bakin hula,kalan wanda yanfashi ke sanyawa,daganan kuma cameran ta dauke saboda fasata da daya daga cikin samarin yayi,shattt ina masu kula da bangaren cameran suke dahar hakan ta faru amma baku iya gayawa yan sanda ba,Ashtar ya fada cikin fushi,duk sukai shiru suna kallon shi,tsawa ya daka masu wanda hakan yasa suka rude,cikin rawar baki daya daga cikin ma'aikatan yafara magana,yallabe wllh yau ton kan lokacin bama dakin dukan mu lokacin saboda wutan daya kama adakin masu kula da abincin hotel dinnan,kuma koh da muka dawo bamu lura da shiba saiyanxu,hakadai duk wani binciken da sukayi basu sami wata shaidaba da zasu gane mutanen,badan sun suba suka dawo gida,saide alokacin ko ina ya dauka da bacewar Nasra,abunka da manya nan dan nan duk wata hanyan wucewa sai anbincika mota kafin ta wuce,lokacin da ake wannan binciken su jagwal sunyi nasaran fita daga garin Abuja,
Sir wannan number wayan wani mutum ne sunan shi Dauda yau kimanin shekara biyar kenan da rasuwar shi sanadiyar hadarin mota dayayi,kuma SIM din ba a kara amfani da shiba tun lokacin sai yau da aka kira Nasra da shi kuma yanxu mun bi didigin layin saide bamu samu komai ba saboda ta iya yuyuwa,ko anjefar da SIM din koh ankashe wayan da akayi amfani dashi,shiru Ashtar yayi dan yarasama mai zaice kanshi yadau zafi komai ma ya shigemai baima san yazai yi ba, haka de aka kwana gidan biki bacikin kwanciyar hankalin ba,


Ta bangaren su Bahba kuwa,basu suka isa Enugu ba sai wajen karfe biyar na asuba saboda irin gudun da jagwal ke zubawa dan yasan hanya sosai saboda suna zuwa akai akai,musanman ma idan sunyi wata tsiyar nan suke guduwa,
Oga ina muka nufa ne,jagwal ai bazamu shiga cikin gari da itaba muje jejin aburungo saboda kaga koh kasheta mukayi namun daji zasu sami abinci kaga kenan bawata shedar da za'a ganta balle akama mu,sai Oga inayin ka Oga saboda ka iya salon mugunta iri iri dariya suka sa gabaki daya,gawska ne yace Oga nifa kafin a sheke yarinyan nan,zan dan dana saboda nafa kyasa,shege mutumi na aiba kai kadai zaka ci gurasarta ba muma sai munhau balle gata yar shila ba karamin dadi zatayi ba,dariya suka kara kwashe wa da ita,Nasra wanda tun sanda suka fara maganan ta farka saboda maganin da suka shaka mata ya saketa,in banda innadillahi'wa'ina ilahi raji'un ba abun da take ambata aranta saboda jin irin abun da suke shirya yi mata,to ita mai ta tsare masu da zasuyi mata haka ita wata taba yima laifi,innadillahi'wa'ina ilahi raji'un na shiga uku ya allah ka kawo min dauki,su Bahba basu lura da tashin da tayi ba, itama batayi wani motsin da zaisa sugane idonta biyu ba,ita yanxu burinta tasamu abun da zata kwance hannunta dashi saboda sun daure mata hannun da igiya,tana cikin wannan tunanin taji motar ta tsaya fitowa sukayi kafin gwaska ya sabota akafada,yar shila haryanxu bacci take bata farka ba aya ana ta baccin bankwana,duk suka kwashe da dariya,kafin su nufi cikin jejin dukan su saida suka danyi tafiya mai nisa kafin su tsaya,nifa Oga yunwa nakeji,to ajeta anan maza kaje cikin gari kasiyo mana abincin dan nima yunwa nakeji kaikuma jagwal dako mana barasar mu a mota, bari in jira ku anan,haka kuwa suka tafi shikuma yasami waje ya zauna tare da samun itace ya kunna wuta saboda da sanyin dayakeji,Nasra ko ita a yanzu burin ta tasami abun kwance hannunta,zuwacan taji ai takalmin ta na kafarta har yanxu dakyer tasamu takai hannunta wajen kafan,wani dan karfe da akayi kwaliyan takalmin dashi ta samu ta ballo shi da kyer,kafin kuma ta fara kokarin kwance kanta aiko tana fara gwagura karfen saiga igiyan ta fara dan yagewa saboda daman bawani kwari gare taba,duk wannan abun da takeyi ko kadan Bahba bai lura ba dan gengadi ma yake yi,zuwa can saiga jagwal ya dawu da barasar,shima waje yasamu ya zauna agaban wutan haka sukayi ta zama suna dan hiransu har zuwa lokacin da gawska ya dawo da abinci,ci suke suna dariya da shewa dan giya ta fara kai masu karo,itako Nasra allah ya bata ikon kwance igiyan saide bata motsaba daga inda take balle suyi tunanin ta tashi,

Bahba ne ya mike yana kara daga kwalban giya yana sha,wurgan da kwalban yayi tare dayin wata mika yace,to naci na koshi yanxu sauran sukuwa akan yar shila aiko su gwaska sai dariya, sai Oga kana wuta Oga,muna bayanka muma danyau saimun kwashi rumo,tunkaran inda Nasra ke kwance yayi tare da juyota,Nasra wanda ta damki kasa a hannunta yana juyota ta watsa mai kasan a fuska,ihu ya kwala saboda kasan daya shigan me ido,su jagwal da sukaga abun daya faru sukayo kanta,koh kafin sukaraso ta kwasa da gudu tayi cikin jeji batare da tasan inda zata nufa ba,suma rufa mata baya sukayi,Bahba wanda yasamu ya wanke idon shi da kasa ya shiga ya zaro bindigan shi dake kugun shi,shima ya rufa masu baya gudu takeyi sosai,kai daga ganin gudun kasan na ceton raine,


Mai magana yau maike faruwa a jejin nan, Abrish ce tayima akun ta wannan tambayan,uwar dakina nikam yau ba inda naje bansan komaiba,bata sake yimai magana ba dan Abrish bade miskilanci ba,tana zaune akan bishiyan mangoro Apple take ci wanda tunda zata fito tashiga lambun su ta tsinko yayan itatuwa,
Kamar daga sama tadunga jin kukan mace tare da harguwan maza,daga kanta tayi ta leko kasan bishiyan saide bataga kowa ba,kwanciyan ta ta kara yi saide mai kukan nan ta kara ji,mikewa tayi asaman iska taga saman bishiyuyin dajin,kale kale ta farayi bataga kowa ba saida ta juya bangaren kudu nan ta hango yarinya wacce ashekaru bazata wuce sa'ar ta ba sai gudu take,daga bayanta kuma wasu manyan samari na binta, tunda taga haka tasan ba alkairi kesa mazan nan nabin macen nan ba,dan haka tunkaran wajensu tayi,tana zuwa tayi sama da macen nan samarin nan suka tsaya kallon kallo a tsakanin su dan sude basuga abun daya dauke yarinyan ba, Abrish wacce ta dauke Nasra ta kalleta,ganin yadda take fitar da numfashi saita bata tausayi hada yatsonta biyu tayi na hannun dama saiga wani haske yafito ya sauka a goshin Nasra tundaga nan kuma sai jikinta yasaki kamar matatta rike hannunta tayi tare da rufe idon ta nan taga duk abun daya faru tun daga saceta har zuwa yanxu,ranta ne ya baci aiko yau bamai hanani cin uban ku a dajin nan,itako Nasra asman tane ya tashi saboda gudun da tayi ga kura wanda hakan yasa shi tashi kawai gudun takeyi amma batare da ganin ko gaban taba,kawai itade taji wani abu kamar yai sama da ita daganan kuma bazatace ga yadda takeba,

Kwantar da Nasra tayi akan bishiya,kafin ta nufi wajen su Bahba da har yanxu sun kasa cigaba da tafiya kamar an dasasu a wajen,kallon su tayi suma kallon ta suke duk da fuskar ta dake rufe amma kallo daya sukayi mata tsoro ya shigesu dan kallon aljana suke mata,daga kafa sukayi dan guduwa saide dagawan da zasuyi,akayi sama dasu ihu suka fara,fara ihun su kenan aka dunga juyi dasu kamar wasu fanka haka aka dunga masu kafin kuma amaka su da kasa,haka za'a dagasu sama sannan a maidusu kasa da karfi,kafin kace kwabo sun hada jini da majina dan shiko Bahba harda zawo yayi suma su jagwal banda futsari ba abun dake bin kafan su,dan allah anty aljana kiyi hakuri wllh da munsan nan din gidan kine da bamu zo ba dan allah gwago aljana kiyi mana rai wallh munzama mutanen kirki daga yau,ko kala batace masu ba saima juyawa da tayi tatafi,ta barsu a haka ana ta buga kwallo dasu su basa sama su basa kasa dan kashin su duk ya karkarye,

Zuwa tayi tadauki Nasra,daurata tayi akan doki kafin itama ta hau sukama hanyan gida,mahaifin ta dake cikin lambu ya hangota akan doki kuma idan de ba idonshi gizo yake yimaiba mutum ya hango a gaban dokin ta,daman tunda yaganta ta dawo ba lokacin dawu wanta ba yasan ba lafiya ba, fitowa yayi daga cikin lambun yar baba wacece wannan,Abbu mushiga ciki tukon daukan Nasra tayi suka shiga ciki,kafin tayi masu bayanin yadda ta ganta,to yanxu su samarin suna ina sunacan jeji,mai kikayi masu Abrish Abbu,ya tambaya, hukunci daide da laifin da suka aikata,tana gama fadan haka ta shige daki abunta,girgiza kai kawai yayi tare da cewa allah ya shirya ki da ameen umme ta amsa,dan itama kullum saide tayi mata Addu'an shiriyan dan abun nata yayi yawa,

Su Bahba kuwa tun safe ake masu abu daya har yamma wajen karfe biyar sannan aka daina,sun suma yafi so ishirin,kamar yadda wahala ta sumar dasu haka wahala ne ya farfado dasu,nan suka zube kamar matattu kadan ne maraban su da matattu shine numfashin da sukeyi,wasu mafarauta ne sukazo wuce wa suka gansu,farko ma sun dauka sun mutu saidaga baya suka gane da sauran numfashi a tare dasu,kwashe su sukayi tare da tafiya dasu kwayen su.







Su Bahba anji jiki wllh πŸ˜‚ amma yan Group din *YAR* *DAJI* kuna kallo ko dauki ba wanda ya kawu masu,amana batace haka bafa,kuna yawa wllh,🀣 nikam na sanfe badani ba,πŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈπŸƒβ€β™€οΈ








Shere fisabililahi.


S
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ *YAR* *DAJI* πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
(WILD GIRL)

*NA SABUWAR MARUBUCIYA* *FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🀱)

Pege 13.

*****

Bayan sati daya.


Mommy ni bangane wannan wani irin aure ne ba haba fisabililahi yanxu tsawon sati daya kenan ko kallo ban isheshi ba,saikace ni nasa a sace kanwar shi amma ai nasan ba haka yake yi wa yar'uwar shiba watakon dan yaga ni ba jinin sa bace yakemin wulakanci,ni nagaji wllh mommy,
ilham,na'am, bari ingaya maki wani abu da baki sani ba,a dai yanxu daga ke har waccan kishiyar taki bazaku sami hankalin Ashtar ba,musanman ma dayake ganin ranar auren ku dashi,aka sace mai kanwa,kinga ko kenan bazakuyi wata daraja ba, amma ki kwantar da hankalin ki shalelena,bari har komai ya lafa ,zanje wajen malam na amso maki temako,shidin banza bai isa ya wulakanta min ya ba kibarni dashi,sai munyi maganin shi, kedai yanxu abun da nakeso dake kada kisake ki nuna gajiya warki da wuri inso samune kima nuna kin fishi damu da batar kanwan tashi,kin fahimta ko,eh mommy nagane,kuma insha allah zanyi iya kokari na wajen janyu hankalin shi kaina,yauwa yar kirki haka nakeso, kashe wayan tayi, allah yasa yaya Ashtar ya so ni kamar yadda nake sonshi,

Assalamu'alaikum, Aminwa'aleki salam, ah ah Nafeesat kece shigo mana, shigowa tayi tare da zama akasa, tashi ki zauna akan kujera a a nanma yayi Ammee,to shikenan tonda dai yanxu kin maidani surukar ki,karfi da yaji,murmushi tayi kawai,toya kuke ina fatan komai lafiya, lafiya lau muke Ammee babu matsalan komai, aranta ko cewa take matsala ko muke cikin matsala dan kwandon sharama yafimu daraja,a wurin yaya Ashtar, haka akeso ai allah yabaku zaman lafiya mai daure wa,da ameen ta amsa,
Sallama akayi tare da shigowa,amsawa sukai, ko da Nafeesat ta juya taga ilham ce,saita dauke kai bayan ta maka mata harara,karasuwa tayi,tare da zama akasa itama, gaisar da Ammee tayi,ta amsa cikin kulawa tare da tambayan ta kamar yadda tayi wa Nafeesat,itama cewa tayi babu matsala,bayan aranta ba haka bane,Ammee ma tariga tasani akwai matsala kawai bazasu fada bane,amma ita tasan ko da hakan bata faruba kafin Ashtar yabasu hankalin shi da kulawa a garesu sai andau lokaci,saboda aura maisu dole akayi batare da sonshi ba,to kuma saiga wannan abun ya faru na bacewar Nasra,fatan tadai duk inda yarta take ya kasance tana cikin koshin lafiya,ilham ko tsakaninta da Nafeesat saide insu hada ido sumaka wa juna harara,
Suna zaune ahaka, Ammee nadan jansu da hira, Ahfrah tayi sallama ta shigo, gaisar da Ammee tayi tare da zama akan kujera, kallon su ilham tayi taga yadda suka wani natsu harda su zama akasa,waisu irin ana gaban surukan nan,ita wallahi dariya ma suka bata, hmmm kuyi ku gama nadan lokaci ne,dan wallahi yadda na rasa Ashtar to kuma sai kun rasa shi, saide muyi biyu babu, dan kuma saide ku hakura dashi, murmushi tayi bayan ta gama wannan tunanin aranta, amare kenan ykk,ta fada tana masu murmushin mugunta, lafiya lau anty Ahfrah ashe kinan bana ganinki kwana biyu, ina ko zaki ganni bayan kin shige cikin gidanki,kin manta da yayar ki, kai anty Ahfrah ba haka bane,gidana ai naki ne,amma shine koki lekoni bayan muna gida daya, kwarai kuwa gidanki nawane amma bayan na kawar dake na auri yaya Ashtar, ta fada aranta,a fili kuwa,sai cewa tayi bahaka bane kinsan ku amare ne banaje na takura makuba,amma yanxu tunda kinason na dunga zuwa zanje, yauwa antyna, mikewa Ammee tayi tace bari nashiga ciki ni tunda kunsami abokiyar hira ko,ta fada tana dan dariya,aiko dai Ammee gwanda kije ki huta zan tayasu hira,to yayi kyau hakan,
Haka suka zauna suna dan hiransu na yaya da kanwa,ilham wacce tunda Ahfrah tashigu ta gimtse fuska,mikewa tayi tare dajan tsaki ta wuce,duk binta sukai da kallo, itama Nafeesat tsakin tayi, aikin banza kawai, Ahfrah ce tace allah ya kyauta,da ameen Nafeesat ta amsa,

A hankali ta dunga bude idonta, harta budesu duka,kallon dakin ta dunga yi alamun dai kamar tanason tantace wani abu,kukarin tashi takeyi dafe kanta dake dan sara mata tayi, jingina tayi da bangon dakin bayan ta tashi zaune,daga labulen dakin akayi,shigowa akayi da sallama,amsawa tayi daga kai tayi ta kalli matar,a shekaru zatakai Ammee ta ko Ammee zata fita da kadan ne, karasowa umme tayi da murmushi a fuskar ta, masha allah jiki yayi kyau harkin tashi,sannu yar nan,yauwa a ina nake, kina gidan da akwai aminci ne,zata kara magana umme ta katse ta,tare da cewa bari nakai maki ruwa kiyi wanka,sannan kici abinci,sai muyi magana daga baya,da to ta amsa, nace dan allah kwana na nawa a kwance,satinki daya akwance, zaro ido tayi, har sati ina kwance,dariya umme tayi kina mamaki ne,a a saide nasan hankalin iyayena zaitashi sosai ne, hakane insha allah tunda kin tashi sai tafiya gida ai,murmushi tayi kafin ta tashi tabi bayan umme,
Bayan tayi wanka taci abinci,umme tayi mata bayanin yadda Abrish ta temake ta, tayi farin ciki sosai da allah baiba wasu Bahba nasara akanta ba, ina Abrish din taje anty,ai Abrish bazaki ganta yanxu ba tana cikin jeji sai yamma, jeji kuma,batajin tsoro, rike haba umme tayi,tsoro Abrish din ne zataji tsoro, anty kina nufin batajin tsoro ita, batajin tsoron komai da kika ganta ni har son naga abun dazai bata tsoro nake, harna kosa naganta wllh, zako ki ganta saide ba lalle ki iya zama da itaba,dan tana da baudan den hali, dariya Nasra tayi,nidai koya take zan iya zama da ita,in banda ita dayanxu kila ina kabari ko namun daji sun cinyeni, to shikenan zaki ganta dan takusan dawuwa tunda yamma tayi,

Abbu ne ya shigu gidan da sallama a bakin shi, amsawa sukayi, a a mara lafiya harta tashi kenan,ya fada yana zama akan tabarman da umme ta shinfida me, wllh kuwa ina shiga dakin dan in duba ta na iske ta tashi, haka akeso ai da fatan yanxu babu inda ke maki ciwo ko,babu Abba,ta fada tare da gaishe shi amsawa yayi cikin kulawa, jiki yayi kyau masha allah,allah ya kara lafiya mai durewa,ameen,
Yarinya a ina kike,sannan maiya hadaki da samarin nan har suke son kasheki, nima kaina ban sansu ba kawai na fito amsa wayane suka kamani, batare danasan mainayi masu ba, to allah ya kyauta ameen, ke yar wani gari ce, ni yar Abuja ce, yanxu tun daga Abuja suka daukoki suka kawo enugu, enugu kuma Nasra ta fada tana zarar ido, eh kina enugu acikin jejin aburungo, jeji kuma kenan a jeji kuke rayuwa ku,eh a jeji muke rayuwa mu Abbu ya fada yana murmushi,ganin yadda duk ta tsorata, to ni yanxu taya zan koma gida,shine muma bamu sani ba, shiru tayi tana tunani, kafin zuwa can tace zan iya samun waya, waya gaskiya mu bama amfani da waya,saide idan naje cikin gari jibi nasiyo maki,wani dariyan farin ciki ne ya kufce mata,godiya tashiga yimai dan ita ayanxu burinta taje gida,
Suna zaune Abbu nadan mata tambayoyi tana bashi amsa, Abrish tayi sallama tashigo gidan,kura mata ido Nasra tayi dan ita dai inda ita kadaice ba abun da bazai hanata guduwa ba dan yanxuma gabanta in banda faduwa ba abun dayake yi,wannan kyau yayi yawa wllh ko wacce tayi kanta,iya inda zata tsaya kenan,balle idon ta daya kasance kamar na mage, itama Abrish din kallon ta take kafin tadanyi murmushi, tace mai suma kin tashi kenan,itama Nasra murmushin tayi tace eh, to yayi kyau, Abbu, umme, barkanku da hutawa,yauwa Abrish kin dawo kenan, eh umme, to kije kiyi wanka sai kizo kici abinci to umme, kallon Nasra tayi wanda tun dazo takasa dauke idonta akan Abrish saboda kyaun da tayi mata hakanan kawai taji tashiga ranta, murmushi suka sakar wa juna, kafin Abrish ta shige daki,

Ashtar yau kimanin sati daya kenan amma ko wata alama bamu samu ba akan wa inda suka sace Nasra, gabaki daya kaina ya kulle wllh, ajiyan zuciya Ashtar ya sauke,kafin yace Umar ni kaina bansan yadda zanyi ba,asanin danayi wa Nasra ko abokin fada bata dashi,saide in daya daga cikin mutanen danake bincike akansu wani yasa a saceta,dan inbar abun da nakeyi, hmmm to bazan bariba yanxuma na fara kuma insha allah saina ganu kanwata, hakane allah ya bamu sa'a,ameen,

*Bayan kwana biyu*

Abrish ce ta fito cikin shirinta na zuwa jeji,kallon Nasra tayi dake zaune tana yanka lemo wanda suka shiga cikin lambu suka dibu,yau bazaki bini bane, zanje mana tashi tayi suka tafi,

bayan sun dawo Abbu yabata yar tecno karama daya siyo mata hade da SIM card, farin ciki ne ya kamata tashiga jera wa Abbu godiya, haba godiyar ta isa haka,gobe sai muje na kaiki inda zaki sami yanar gizon kiyi waya,abbu Network a ke cewa,to wannan aisaiku yan boko, sister kinga wayan da Abbu ya siyomin, nagani toke yanxu yazakiyi amfani da ita,ci ake ko wanka dashi,naganshi wani dan karami dashi gashi baki, sister waya ce fa ba abun ciba ko wanka, to inba wanka ko ci maizakiyi da ita, zan kira yan gidan mune muyi magana,yan gidan ku,eh, amsar wayan tayi dubawa tayi kafin ta dagu ta kalli Nasra,nifa banga kofan dazasu fito ba, hmm komai zance maki yanxu bazaki fahimta ba, to ai gaskiya ne taya zakiyi magana dasu ta wannan abun mai kamar dutse, dariya ne ke cin Nasra amma ta gimtse ta,dan ya yan kwana biyun nan da tayi da Abrish,ta fahimci batason raini ko kadan,shiyasa ta maida dariyan zuwa murmushi,tace gobe idan munje yin wayan zaki gani, to allah ya kaimu,ameen,

Safiya tayi inda Abbu, da Abrish sai Nasra,sukaje kan wani dutse dake gaba da gidan su, hauwa sama sukai, latsa wayan Nasra ta fara,number Ashtar tasa,dan tasan ayanxu shi zata kira a halin da ake ciki, wayar har ta gama karanta bai dauka ba kara kira tayi akaro na biyu shima de harta katse bai dauka ba,

Ashtar ko alokacin yana zaune tare dasu Abbey suna magana akan Nasra,yana ganin kiran wayan yaki dauka saboda yaga bakuwar number ce,sake kira akayi akaro na uku, Abbey ne ya kalle shi yace ka dauka mana kasani ko wani ne yaji labarin inda Nasra take, shima sai yanxu tunanin hakan tazo mai,dauka yayi tare dasawa a kunne shi,
Assalamu'alaikum, wake magana, brother Ashtar Nasra ce, Nasra ya fada yana mikewa tsaye,Nasra kina ina,kina ina yanxu haka, ina Enugu bro, whattt? Enugu dai,eh bro,waya kaiki can ,bro yanxu bazan iya yima bayani a waya ba kawai kazo ka daukeni,zaki iya gane inda kike yanxu haka, a a saide inba mutumin danake zaune gidan shi yayima bayani,wani mutum kenan, mutumin da yarshi ta tsinceni, to bashi wayan,
Ba wa Abbu wayan tayi,bayan sun gaisa Abbu yemai bayanin inda suke, godiya yayi ma Abbu, sosai,mika wa Nasra wayan yayi, Nasra kina jina, eh bro, yanxu nan zan taho kinji kada kisa damuwa aranki insha allah ina hanya,to bro,ina Ammee take, gatanan ya fada yana mika wa Ammee wayan, wacce tunda taji ya ambaci sunan Nasra,suka mike tsaye dukan su,
Ammee na,um auta ta,sai suka fashe da kuka dukan su, aka rasa mai lallashin wani, Ashtar ne ya amshe wayan ya kashe,daker Ammee ta tsaida kukan ta,kafin ta kalli Ashtar, yanxu Enugun zaka tafi,eh Ammee can zantafi,to jirani na dauko himar dina,mutafi, Ammee ina zaki,Enugu mana, Ammee please kibari naje na tahu da ita, kaga kafata kafarka ,kasan allah sainaje, yariga yasani tunda tace allah ai sai taje din,bayadda ya iya haka ya amsa mata da to,shima Abbey cewa yayi dashi za'a je, kafin kace kwabo gida yadauka

Please Login or Register in order to submit comment