You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ο»Ώ[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Bismilahir rahmanin rahim.
Dasunan Allah mai rahama maijin kai, ya Allah kayi dubun salati ga Shugaban mu Annabi Muhammad (S.A.W.),Allah na rokeka kamar yadda nafara rubuta litafinnan lafiya kabani ikon gamashi lafiya idan munkai da rai da lafiya.
Ya Allah narokeka kabani ikon rubuta daidai kuskuran dake cikinshi kayafe mana ameen ya Allah.



Pege.1.


******


"Wallahi sai naga bayan Ahalin Alhaji Ahmed Modibbo koh da dukiya ta da duk abinda na mallaka zasu kare, Koda zanyi yawo tsurara in dai burina zai cika na ganin bayan sa shida ahalin sa, barin taba bari su cigaba ba muddin Ina nunfashin a doron duniyar nan, na tsane su kamar yadda na tsani mutuwa ta, ba ma kamar yaron nan nasa Ashter"
Hajiya Falmata ta fada tana huci da kumfar Baki, shiru Hajiya Zainab tayi bayan ta gama sauraran kawarta ta tare dayin wani munafukin murmushi tare da kurbar lemon dake hannun ta kafin tace.
Hajiya Falmata Ina ji duk tsanar da kika yi musu Baki kaini ba, domin saboda su ne har yau mijina bai cigaba ba, arzikin su ko Rabin na mijina bai Kai ba bayan Kuma tare suka fara naiman kudin, komi tare suke yin sa tare suka taso tun suna yara, Amma babu komi sannu-sannu bata hana zuwa saide a Dade ba aje ba, karki wani damu ni kadai nasan abinda nake shirya musu dan haka ki kwantar da hankalin ki"
Dariya sosai Hajiya Falmata ta kwashe da ita.
"Shiyasa nakeson ki Ζ™awata na sanki ai akwai mugunta"
Haka suka kara kwashewa da dariya suna tafawa.



Sosai take gudu a cikin jejin kurar dake biye da ita a baya itama gudu take burin ta bai wuce ta kama yar budurwar nan ba Amma ita din taki barin hakan ya faru domin sai kama reshan bishiya takeyi tana sallake su kamar wata biranya, a haka harta karaso wajan wata bishiya ta janyo wata igiya saiga wani Abu ya fito kamar kwando ya rufe wannan kurar ruf a ciki, kurar sai hargari da gurnani takeyi na son fitowa daga cikin wannan tarkon.
Ita kuwa yarinyar da akalla ba zata wuce shaikara goma shatara ba a duniya ta dirgo daga kan bishiyar da take kai tana bin wannan kurar da kallo da kyawawan idanuwan ta da suka kansace blue kamar na mage, Amma ba na iya ganin fuskarta saboda rufe ta da Jan kyallan da tayi hakan ne ya dada haska farar fatar ta, kyaukyawan hannun ta tasa ka ta yaye abinda ta rufe fuskar nata, Subhanallah. Sarki ya tabbata ga Ubangiji da yayi wannan kyaukyawar halittar, domin kallo daya za kayi mata kasan Allah yayi halitta a nan wajan, wanda idan wani ya kalle ta kai tsaye ma zai iya cewa aljana ce saboda tsananin kyauwun ta, gata da kwala-kwalan idanuwa da dan karamin baki daya kasance pink sai Kelle yake yi, ga dogon hancinta kamar karar biro, kyaukyawan murmushi tayi wanda ya Karwa fuskar ga kyau, hakan ne ya bawa dimple's dinta damar fitowa duka guda biyun, a hankalin cikin daddadar muryar ta mai amaon sauti ta fara yiwa kurar magana tana kallonta ido cikin ido.
"Mai yasa a koda yaushe ba kuda buri da ya wuce ku kama mutane ku cinye? Ba kusan hakan daukar Alhaki ne ba? Shiyasa suma mutanen in suka samu dama suke kashe ku saboda sunsan idan basu kashe ku ba, to tabbas ku zaku kashe su, kinga idan kina da 'ya'ya kin maida su marayu, ni bazan kashe ki ba Amma ki min shiru"
Aiko kamar kurar tasan abinda tace kuwa tayi sit da ita.
"Yauwa yar kirki, yanzu zan sake ki kiyi tafiyar ki Amma muddin kika kawo min hari zan kasheki ki tafi barzahu"
Ta karasa maganar tana dalewa kan bishiya saida tayi tafiya mai dan nisa sannan ta ja igiyar saiga tarkon ya bude, kurar na ganin haka ta kwasa a guje tayi cikin jeji abinta, da kallo ta bi kurar harta bacewa ganin ta sannan ta yunkura ta fara saukowa daga kan bishiyar, hannun ta tasa a baki tayi fito saiga wani farin doki ta taho a guje ya tsaya a wajan tsalle tayi ta haye kansa suka nusa cikin jeji haka suka dunga keta dogayan bishiyu da tsaunika har suka karaso wajan wani gida ginin kasa dan madaidaci dashi yasha farar kasa irin Wanda yan kyauye keyi, Amma abin mamaki shine wannan gidan shi kade ne a cikin wannan kungurmin jejin, gefen gidan garken shanu ne da awaki ga su nan gwanin sha'awa ga wajan a share kal-kal, dayan gefen kuma kaji ne da zabbi a cikin keji, sai dayan bangaran kuma Lambo ne daya wadatu da 'ya'yan itatuwa inda wata korama take kwaranya a gefe Daya.


A hankali ta sauko daga kan dakin ta nufi inda sauran dokunan suke ta dore sa a jiki ta nufi yar madaidaiciyar kofar shiga gidan, sallama dauke a bakinta ta shiga gidan a zaune ta tarar da mahaifin ta akan tabarmar kaba mahaifiyar ta na zuba masa abinci tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa da taji nama da man shanu sai kamshi ke tashi, sai dafaffar Madara da tasha zuma sai turiri takeyi, tashi tayi ba tana amsa sallamar yarinyar tare da kafeta da idanuwa.
"Abrish ba na hana ki kaiwa yamma a cikin jejin nan ba?"
"Kiyi hakuri Ummy bazan Kara ba"
"Yaune na farko da zakice baza ki Kara ba, ai dama kin saba"
"Da gaske Ummy bazan Kara ba ko ba haka ba Abbu"
Ta fada tana kallon mahaifin ta da tunda suka fara draman su baice komi ba sai murmushi da yake yi dan kullum ne sai sunyi ta, da akalla zai kai shaikara arba'in da takwas zuwa arba'in da tara.
"Hakane Uwata ba"
"Ai daman kullum Kaine kake goya mata baya, ke kuma sai ki tashi kije kiyi salla sai kizo kici abinci"
A hankali ta mike tana shigewa makewa yi domin yin tsarki tare da alwalla.









Shere fisabilillah.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege.2.


******

A hankali yayi juyi akan makeken Royal bed dinsa da ya gaji da haduwa kamar ba a kasar Nigeria ba, a hankali ya bude lumsassun idanuwan sa da suka gaji da bacci ya kalli a gogon da ke manne a bangon dakin, karfe hudu da rabi dai-dai a gogon ya nuna masa a gigice ya duro daga kan gadon tunawar da yayi baiyi sallar la'asar ba bacci ya kwashe sa, shi har mamakin irin barcin da yayi yakeyi ace har anyi salla ba tare daya sani ba, a gurguje ya fada toilet dinsa daya hadu matuka da gaske yayi wanka tare da dauro alwalla ya fito kugunsa daure da tawel da wani karami a hannun sa yana goge bakar sumar kansa da ruwa ke tsiyaya yana sauka akan kafadar sa, a sauri-sauri ya saka gajeran wando da singled sannan ya dora jallabiya a kai tare da shinfida sallaya ya tada salla, yana idarwa ya mike ya nufi inda kayansa suke ya bude gasu nan a Jere sunsha goga kamar kayan mutum goma Amma duk na mutum daya ne, a hankali ya dunga bin kayan nasa da kallo har idonsa ya sauka akan farar T-shirt dinsa da bakin jeans, dauko su yayi ya saka tare da feshe ilahirin jikinsa da turaruka masu matukar kamshin gaske, zanso kuga yadda ya hadu a cikin wannan shiga mukullin motar sa ya dauka tare da fitowa daga dakin, wajan da aka tanada dan ajiyar motoci ya nufa yana zuwa ya shiga daya daga cikin motocin da tafi ko wacce kyau da daukar hankali ya fice daga gidan, darect gidan iyayen sa ya nufa dake nan Maitama domin gaishe da iyayan sa.
*Malik Ashtar Ahmed Modibbo* kenan kyaukyawan matashi ajin farko mai jini a jiki wanda Yan mata ke rububin mallakae sa, balaraban Soja maiji da kudi, izza da Kuma miskilanci, Yana da matsayin mejor kuma har yanzu yaki yin aure a inda yake da shaikara talatin da biyar a duniya, d'a mafi soyuwa ga Alhaji Ahmed Modibbo tare da Hajiya Ameena.


Horn yayi a kofar tangamemen gidan nasu daya gaji da haduwa da naira tayi kuka, wangale masa gate din akayi ya danna hancin motar sa a cikin gidan, fitowa yayi ya nufi kofar da zata kaishi falon gidan tana tafiya cike da tsantsar izza takama da kuma milkin Soja dake yawo a jinin jikin sa, da Sallama ya shiga falon zaune ya tarar da mahaifiyar sa Hajiya Ameena akan daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, tunda ya shigo fara'ar fuskarta ta karu akan ta da, shima murmushi ya mayar mata yana zama a kasa kusa da kafafuwan ta tare da Dora kansa akan cinyar ta, cike da shagwaba ya fara magana.
"Barka da hutawa Ammee na!
"Barka dai Baba na, sai yanzu aka samu shigowa?"
Kara shagwabe fuska yayi kamar wani karamin yaro, ba tare daya bata amsar abinda ta tambaye sa ba yace.
"Ammee yinwa nake ji"
"Taso maza muje Kaci abinci nace maka ka daina zama da yinwa kaga da kayi aure da ka huta, wata kila so kake saika gama tsofewa a gida baka yi aure ba ko, to gwanda ma kayiwa kanka karatun ta natsu?"
"To wata kila tunda ke kika haife sa idan kika gaya masa yaji maganar ki, ni kuwa tunda ya Raina ni dan yaga bani na haife sa ba shiyasa, Amma ai ko babu komi nice nan na haifi ubanka, balle ka yaga min rigar mutunci da furfurata da komi"
Dattijuwar tsohuwar ta fada tana kif-kifta idanuwa cike da masifa.
"Shikenan fa wannan tsohuwar tazo kenan zata addabi mutane suna zaman-zaman su"
Ya fada chan kasan makoshin sa batare daya kalli ko in da tsohuwar take ba ya shi nufi inda dinning yake ya zauna ya zuba abinci sa Sinasir ne da miyar ganye da taji nama sai kamshi take, ya fara ci.
Ganin abinda Ashtar yayi ya kara tunzura Hajjo tace dawa Allah ya hadata in ba dashi ba.
"Yanzu Ashatu da yake bata iya fad'in sunan nasa ba, yanzu ni nake maka magana Amma ka tafi ka kyale ni kamar wani rakumi, tsolo-tsolo saboda diban albarka"
Ta karasa maganar tana fashewa da kuka tare da face majina da gefen zani.
"To bari uban naka ya dawo naji ko shine ya baka lasisin debe min albarka, kuma aure ne dole sai kayi shi ko kana so ko baka so, ni na rigada nayi maka mata ma a kyauyen mu wata yarinya makobtan mu mai suna furaira malam gata gata fara kyaukyawa ajin farko ga hanci kamar doya bakinta kuwa yana kama dana mawakin nan Gwanja yake ko gea-gwa"
Ammee dake ta dariya kasa-kasa tace.
"Gwanja sunan sa Hajjo"
"Yauwa shifa Allah yayi miki albarka, yarinya a tsaye kamar gorar fanta Amma shine zaka min diban albarka nida nazo maka da abin arziki to bari uban naka ya dawo"
Ta karasa maganar tana Kuma fashe wa da kuka a karo na biyu, haka ta fita tana sababi tare da tare da face hanci dan dama shigowar shi data gani yasa ta shigo falon tazo tayi masa tijara.


Shi wallahi ma dariya take basa, wai hanci kamar doya Kuma a haka takeson ya aure ta lallai ma Hajjon nan.
"Mai yasa ka wuce ta tana maka magana?"
Ya tsinkayo muryar Ammee tana tambayar sa.
"Kiyi hakuri Ammee"
"Tom shikenan, Amma ka dunga lalla ba ta kaga wani abun nata harda tsufa"
"Toh" yace Yana mikewa ya dawo ciki falon saboda ya kammala cin abincin nasa.
"Ammee gobe zanje Kaduna akwai aikin da zanyi a tsawon 2months a chan"
Fatan Alkairi tayi masa tare da fada akan auren da yaki yi Dan itama shine burinta.

















Shere fisabilillah.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege 3


*****

"Boka so nake a saka mishi soyayyar ta a zuciyar sa, yaji ba kamar bazai iya rayuwa ba in baya tare da ita, ya aure ta ko yana so ko baya so, koh nawa aikin zaici zan bayar matukar buri na zai cika"
Wata irin mahaukaciyar dariya bokan ya kwashe da ita har saida dajin ya amsa kafin ya gimtse fuska kamar bai taba dariya ba sannan ya fara yan tsurkullen sa da wani irin yare da baza ka taba fahimtar abinda yake fada ba, bayan wasu mintuna daya gama yan tsurkullen sa ya dago da jajayan idanuwan sa yana kallon ta kafin daga bisani ya fara magana da muryar sa mai firgitarwa hadi da kada yan hanji.
"Zata iya auran sa Amma baza ta taba samun soyayyar sa ba, shima auran bayan anyi sa da akwai wata yarinyar da muddin ta shigo gidan to ko mai zaku yi kuyi sa cikin shiri domin tamkar masifa da bala'i ne zai tunkaro ku, Wanda hakan zai zama garkuwa da kariya a gare su domin har yau na kasa gano yarinyar wace jinsi ce aljana ko bil 'adama don haka saiku shirya daga zarar ta shigo cikin ku kashin ku ya bushe, bake kadai ba harda ire-iren ku masu son cutar da ahalin Ahmed Modibbo domin fansa zata dauka akan duk Wanda ya zalince su"


Hajiya Saratu dake gurfane a gaban Boka hantar cikinta ta kada hankalinta ya dugunzuma ainun, cike da firgici tace.
"Babu yadda za'ayi nasan kamannin yarinyar yakai Shugabana?"
"Babu ta yarda za'ayi ki Santa, dan haka kije zanyi aiki akan auren nasu Amma babu batun soyayya"
Cike da tashin hankali ta aje masa damin kudi tare da mikewa ta fito da baya da baya harta bar wajan zuciyar ta cike da tunanin yadda za'ayi tasan wannan yarinyar da zata kawo mata cikas akan cikar muradin ta don ko zatayi yawo tsarara sai burinta ya cika.




Niko nace wai mai yasa kowa burin sa bai wuce ganin bayan ahalin Alhaji Ahmed Modibbo ba, shin mai wannan bawon Allah ya tsare musu a duniyar nan da har sukeson ganin bayan sa dashi da ahalin sa, ku biyo ni danjin asalin tarihin Alhaji Ahmed Modibbo da har yasa ake farautar rayuwar sa.

Shin wace yarinya ce wannan da boka ya kasa gano ko wacece.

Sannan Kuma mene ne dalilin zaman su Abrish ah daji, wannan su kadai suka barwa kansu sani, ku biyo ni dan jin yadda zata kaya.












Shere fisabilillah.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege 4.


*****


Shin wane ne Alhaji Ahmed Modibbo?.

Ahmed Muhammad Modibbo shine cikakken sunan sa, d'a ga Hajiya Khadija da Muhammad Modibbo, su hudu ne a wajan iyayen su, Abubakar Saddi'k shine babba sai 'kanin sa Ahmed da kuma Yusuf sai autar su Maryam, su yan asalin garin Yola a karamar hukumar Ganaye, inda suka tasu da matukar kaunar junan su, ga tsabtatacciyar tarbiyar da suka samu daga wajan iyayan su musamman ma ta bangaran mahaifiyar su ta basu tarbiya dai-dai gwargwado, sun Sanya su a makarantar addini data zamani abinda zai birge ka dasu shine yadda suke da hankali ga natsuwa gasu kyauwawan gaske ajin farko da yake kyau mahaifiyar su suka dauko data kasance shuwa-arab ga dadin dadawa mahaifin su bafullatanin asul ne shiyasa suka dauko kyawun ta ko wanne bangare guda biyun, Abubakar Saddi'k na kammala secondary dinsa ya samu scholarship a India saboda yaron akwai basira inda zai karanci Pharmaceutical, inda shima Ahmed ya kammala nasa karatun zai shiga University da yake lokaci daya aka saka su a makarantar inda shi kuma zai karanci Business Administration.


A haka a haka shi kuma Yusuf yana S.S.3 ita kuma Auta na J.s.s.3 dan gaskiya Malam Muhammad Modibbo yana da rufin asiri dai-dai gwargwado haka rayuwar ta cigaba da tafiya wata na tafiya shaikara na shudewa gashi yanzu har Abubakar Saddi'k zai dawo gida iyayan sa da yan uwan sa sai murna suke yi dan tsawon shaikara uku kenan Rabon da su Sanya sa a idanuwan su haka shima, haka yake shirye-shiryen dawowa kasar sa ta haihuwa wato Nigeria da tarin nasarori domin asibitoci dake kasar sunyi masa tayi daya zauna yayi aiki tare dasu Amma yace musu aa sai yayi shawara da iyayan sa tukunna, inda ya kamu da soyayyar wata yarinya yar India Mai suna Najaf Ibrahim Khan a wani babban Shipping Mall yaje siyayya yana tafiya a hankali domin zuwa wajan da zai biya kudi, itama ta taho tana duba cikin jakar ta da dukkan alamu akwai abinda take naima a cikin jakar dan gaba daya kacokam hankalinta yana cikin jakar da take dubawa, shi kuma hankalin sa ya tafi akan kiran wayar da akayi masa yana kokarin amsar kiran basu lura da junan su ba suka yi karo da junan su nan take wayar hannun sa ta fadi kasa tayi kwatsa-kwatsa, jakar hannun tace ta fadi kasa komi na ciki ya tarwatse a kasa.


"Oh my god"
Ya fada yana sunkuyawa hakan yayi dai-dai da itama ta duka domin ta dauko masa wayar tasa, yakai hannu itama takai nan hannun su ya hadu dana junan su a tare suka janye hannuwan su saboda wani irin Shok da suka ji, lumshe ido yayi saboda daddadan kamshin ta daya doki hancin sa babu zato, sake kai hannu tayi a karo na biyu ta dauko wayar nan take taga yarda wayar ta fashe, a hankali ta dago dara-daran idanuwan ta tana kallon sa.
"Mujhe kshama Karen" ma'ana am sorry kenan, Abubakar Saddi'k daya zama kamar status bai ita cewa komi ba sai binta da yake da kallo Tasha Jan sari riga da wando ta yafa karamin mayafi a kanta hakan sai ya bawa gashin goshin ta damar fitowa duk maganar da take yi ba jinta yake ba harma ta fara tunanin ko baya ji ne, saida ta tafa hanayen ta a saitin fuskar sa sannan yayi firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya lula.


"Sorry mai kika ce, dan ya manta ma a inda ya ke, ya manta da cewar basa jin Hausa"
Maimaita masa ta sake yi cikin yaran turanci shi sai yanzu ma ya gane abinda take nufi wato tana basa hakuri ne bisa facewar da wayar sa tayi.
"It's ok, don worry"
"No I have to buy new phone for u"
"No you don't have to do that"
"Oh thank you so much, am Najaf by name"
"Wow nice name, am also Abubakar Saddi'k"
"So you are a Muslim"
"Me to am a Muslim, nice to meet you Abubakar Saddi'k"
"Thank you"
Daga haka ya taimaka mata suka kwashe ta da suka zube ya Saka mata a cikin jakar sannan ya mika mata, karba tayi tana masa godiya tayi gaba abinta, shima wajan biyan kudi yaje ya biya ya nufi gida, a haka suka rabu kowa da tunanin dan uwansa a cikin ransa.














Shere fisabilillah.
[8/10, 11:16 PM] +234 903 550 2413: πŸŒ³πŸ§˜β€β™€οΈ YAR DAJI πŸ§˜β€β™€οΈπŸŒ³
( WILD GIRL)


NA SABUWAR MARUBUCIYA πŸ“”βœβœ
FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM
(UMMON ABDALLAH 🀱)



Pege 5.



******

A haka Abubakar Saddi'k ya koma Hostel cike da tunanin Najaf, tare da mararin sake ganin ta ko da sau daya ne, saboda a kallon farko zuciyar sa ta kamu da tsananin soyayyar ta, haka ya dunga tsake-tsaken sa a cikin arai.
"Yanzu idan har mun sake haduwa ta yarda dani ta amshi soyayya ta, iyaye na fa? Ba lallai su yarda na aure ta ba duk da kasancewar ta musulma Amma al'adun mu sun banbanta da nasu, dama ace a yar Nigeria ce da komi zai zo da sauki, a bangaran ta itama ga nata iyayen suma ba lallai ne su amince ba 'yar su tayi nisa dasu ba, ya Allah yanzu ya zanyi"
Ya fadi maganganun a fali muryar sa a raunane, haka ya kwanta ya dasa tunanin Najaf a ransa har bacci barawo yayi awon gaba dashi, gari na wayewa ya shirya ya nufi makaranta Amma ko ana lectures kwata-kwata hankalin sa baya kan abinda ake koya musu, a haka har tsawon sati daya gaba daya baya maida hankali akan karatun sa saide tunanin Najaf, tafiya yake yi Amma gaba daya hankalin sa ya tafi wajan tunanin Najif, kamar a mafarki yaji ana magana a bayan wata bishiya tare da dariya, ji yai kamar yasan muryar mai maganar, jiye zuciyar sa ma gwadayin son ganin wannan mai zazzakar muryar.



"Assalamu-alaikum"
yayi sallama juyowa tayi takafeshi da idanonta nan masu rikita tunanin shi. "Ameen wa'alaikumus-salam"
ta amsa mai tare da kara kafeshi da ido a karo na biyu tanason tuna inda tasan fuskar canko ta tuna.
"Abubakar its you"
Tafada tana murmushin nan nata mai kyau, shima murmushin shine ya karo ganin taganeshi bata manta dashi ba yace.
"Yah its me, are you in this school, yap so how are you"
"Am good and you"
"Same to you am fell so good today, that is good"
Shiru sukayi nadan wani lokaci kowa da abun dayake sakyawa aranshi gani yayi shirun nan bazai fisheshiba gwanda ya magantu.
"Mai ya kawo ki makarantar nan, ko a nan kike karatu"
Ya fada cikin harshen turanci.
"No, nazo wajan wata kawa tace"
taba yar hira suka yi inda harya amshi number wayanta dan wannan itace damarshi ta karshe dan bayason yasake rasata akaro na biyu nan suka rabu akan zaikirata inta koma gida zuciyar shi fari kal saboda farin cikin yaga abokiyar rayuwar shi ya koma gida.


Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda Abubakar yaima Najaf tayin soyayyar shi kuma ta amsa dan itama tun ganin farko takamu da sonshi sadai bata nuna ba saboda kunya irin ta mace ayanxu abunda suke ganin zai kawo masu matsala a soyayyar su shine iyayensu dan basu da tabbacin zasu yarda haka dai sukaci gaba da rayuwa har zuwa sanda Abubakar ya gama karatun shi yace zai tafi gida inda hankalin Najaf yata dhi sosai dan tana ganin idan yatafi bazai dawo ba saida yai aikin lallashi tare dayi mata Alkawarin zai dawo kuma zasu dinga waya haka nan dai ta hakura ba dan taso ba sai dan ganin shima yada hankalin shi yatashi.... wannan kenan.


Toh yan'uwa da abokan arziki kowa na ta murnar dawowar Abubakar inda shima Ahmad yadawo gida domin ganin yayan nashi abin sonshi inda abokin shi Badaru kuma amininshi yabi yoshi shima wai zai gaida yayan nashi shima Badaru dan Ganaye ne kuma tare suka tasu tun suna yara kusan komai iri daya sukeyi sai dai hali daya babbanta dan shi badaru irin mutanan nan ne masu shegen hasada arayuwar su sannan bashi da tausayi ko kadan ga shegen son abin duniya dason nuna shi wanine
Inda shi kuma Ahmad yakasance ba ruwan shi da abin duniya ga tausayi gashi abin hannun shi bai tsole mai ido ba akwai son kyauta sau tari sukanyi fada akan bakin halin badaru amma yaki bari, ah yanxu haka kowa nada budurwan shi inda budurwan Ahmad sunanta Ameena shikoma Badaru Zainab inda duk anan makaranta suka hadu, Ameena yar gombe ce inda zainab ita kuma yar jos ce wani abunda zai baku mamaki shine kamar an auna kowa da halin kowa sai yasamu daidai da halishi dan zainab da Badaru halinsu dayane ba babbanci inda halin Ameena da Ahmad yaxu daya suma
saide Badaru najin haushin Ahmad saboda yasami budurwan da tafi tashi kyau naisa ba kusa ba kuma gata fara dukda tashi itama tana da kyaunta daidai gwargwado saide bakace gaskiya ga idonta saikace na yan chaina shiyasa yakejin haushi saidai bai nunawa afili yabar abin acikin zuciyar shi tare da bakin gudirin shi a rai.


Bayan sun isa gida anci ansha ankuma gaigaisa makwabta sai shigowa suke danyi mai barka da zuwa, baisa mu ya kwanta ya huta ba sai dare, yau tsawon kwana biyu kenan da dawowar shi a yanzu haka suna zaune ne ah tsakar gida shida Modibbo tare da Hajjo dan Ahmad kwanan su daya suka koma saboda jarabawar fita suke zanawa yusuf kuwa na majalisa dan shi yanzu yake 300 level inda yake karanta Accounting auta kuma tayi bacci dan ita yanxu tagama secondry school, Modibbo ne

Please Login or Register in order to submit comment