You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da anga Nasra,kowa sai murna yake musanman amare,

Hajja najin za'a tafi Enugu tace saitaje,juyin duniya anyi taki yadda itafa saita tafi wajen jikar ta.




Nima anan zan tattare kayana dan nabi su Hajja Enugu ko a tayar motace sai munje.🤣😜









Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJ* 🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧ 14.

*****


"Nasra kallon Abrish tayi,wacce tunda suka fara wayan ta tsaresu da ido ko kaftawa batayi, Abrish lafiya kuwa, Nasra ta tambaye ta, lafiya lau kawai ina mamakin yadda kuke magana da mutanen cikin wannan abun, dan dariya Nasra tayi kafin tace, ba mutanen cikin shi bane yan gidanmu ne muke magana dasu,

yan gidan ku kuma?, eh yan gidan mu, yayana yace yana zuwa yanxun nan, nasan zuwa gobe da safe zai karasu, umm kenan yanxu kina nufin yayan ki na hanya, eh yana hanya, to allah kawo shi lafiya, ameen,
"ai zaki bimu mu koma garin mu tare koh"? " a a babu inda zani, to saboda dame bazaki bimu ba? tsayawa tayi da tafiyan da take,juyowa tayi tana kallon Nasra kafin tace,
"Saboda bazan iya rayuwa a inda ba jeji ba,bazan iya rayuwa a inda babu bishiyoyi ba,san bazan iya rayuwa a inda babu namun daji ba, sannan ni kaina bazan iya rayuwa cikin mutane ba saboda ni ba kamar sauran mutane nake ba, ina fatan kin gane abun da nake nufi,
Eh nagane to amma, kinga Nasra mubar wannan maganan,ni zan wuce cikin jeji ki karasa gida,saina dawo, tana gama fadan hakan tayi hanyar jeji abunta,
Nasra dake tsaye tana kallon ta harta wuce, ajiyar zuciya ta sauke,kafin tace a fili, Abrish dole ki koma cikin mutane da zama, bari dai yaya Ashtar yazo zance mai ya dauke mana ke mutafi tare, takarasa maganan da murmushi a fuskar ta,


"Haba dan allah fisabililahi ace tun safe ake abu daya,yaki ci yaki cinyewa fisabililahi ace tun safe muna bin hanya gashi har dare yayi amma baku da alamun tsaya wa saboda rashin imani,mutum tun yana baccin marmari har ya koma na allah ya isa,ni wallahi nagaji,
Hajja ce take ta wannan sababin tun dazu, Ashtar ne ya juyo wanda ya gaji da mitan ta, wai dan allah Hajja bazaki shafa mana lafiya da wannan surutun ba, haba kinbi kin ishi mutane da mita tun dazu,wani ne yace ki biyo mu basai da nace ki zauna ba kikaqi zama, ke gaki mai jika,ai yanxu zaki ba wa yan garin ku labarin yadda hanyar enugu take, kinga suma wani mai shekaru irin naki bazai yi marmarin zuwa enugu ba,
Ashtar zanci mutunci ka uwar tawa kakeyi wa haka, yi hakuri Ammee, ya fada yana mai juyawa,
Aiko kamar kara zugata akayi, taita masifa,Abbey da Ammee ne sukai ta bata hakuri, shi wanda ma take ma masifan ko ajikin shi latsa wayan shima yake,
Saida ta gaji dan kanta sannan tayi shiru, basu suka isa cikin garin Enugu ba sai wajen karfe goma da rabi na dare, a Hotel suka sauka dan hutawa kafin gobe da safe sutafi jejin aburungo,


"Nafeesat" na'am umma kina jina koh, eh umma, yauwa kinga yanxu tunda anga wannan kanwar tashi, a yanxune yakamata ace munyi wannan shirin namu domin jawo hankalin Ashtar akanki, ina fatan kin fahimta, eh umma, dauko wata laida hajiya saratu tayi,kwance wa tayi tare da ciro wani dan kwalba, kinga wannan kwalban, "eh" to turare ne aciki anason sai zaki wajen shi ki saka shi da zarar ya shaki kamshin turaren to ina mai tabbatar maki sai yadda kikace dashi, cike da murna Nafeesat tasa hannu ta amsa, da murmushi a fuskar tace umma kina nufin daya ji kamshin turaren nan sai yadda nayi dashi, kware kuwa shalelena, murna ce ta kama Nafeesat, tana sakawa aranta da zarar ya dawo to zata saka turaren nan,kuma tasa ya kuri waccer banzan, dan ita kade ce ta dace dashi,


Tabangaren su Ashtar kuwa, ko da gari ya waye,daya daga cikin sojojin da suka zo dasune wanda yasan dajin saboda shi dan Enugun ne, shine yayi masu jagora har zuwa jejin, ko da aka tsaya bakin jejin ai hajja na ganin jejin nan,sai cewa tayi da alama shirya kashesu akayi,in ba haka ba taya za'a ce akwai masu rayuwa acikin jejin nan wanda daga gani in banda namun daji ba abun dake rayuwa aciki, suma su Abbey sun fara tunanin hakane saboda yanayin dajin beyi kama da inda yan adam zasuyi rayuwa ba, shide Ashtar bai kula suba,sai waya daya ciro number da Nasra ta kirashi dashi ya kira,ko dayayi kira na farko be shiga ba hakama na biyu,sai ana uku sannan yashiga yana ko fara Ringin aka dauka, muryan Nasra yaji tana gesheshi be amsa ba sai cewa yayi gasu a bakin dajin da akayi masu kwatance,
Mika wa Abbu wayan tayi dan itama ba sanin hanyar fitan tayi ba, cewa yayi gasunan zuwa, to yace tare da kashe wayan ,ya kalli su Abbey yace mutumin da take gidan shi yace gashinan zuwa ya tafi damu, ina zaitafi damu hajja ta fada tanazare ido waje, baice mata komai ba, saima latsa wayan shi yaci gaba dayi,
Nasra ce ta kalli Abrish cikin murna tace zo muje wajen jeji mutawo da yan gidan mu, a a kuje ke da Abbey ku dawu idan sunzo nan saimu gesa, yanxu dan allah bazaki jeba , a a kude saikun dawo, to shikenan,

"Sunanan tsaye sukaji kukan doki na tunkaro inda suke, kowa kallon wajen da kukan ki fitowa suke, wani mutum suka hango akan doki yadan manyanta dan zaikai Abbey a shekaru koma ya girme shi,sai wata yarinya dake bayan shi wacce basa ganin fuskar ta da kyau saboda mutumin daya dan kareta, saida suka matso sosai kusa dasu sannan suka gane Nasra ce, murna ce ta kama su dukan su,dokin na tsaya wa Nasra ta dirko akai har faduwa tayi,saboda sauri zuwa tayi da gudu rumgume Ammee da Abbey tayi ta fashe da kuka,itama Ammee kuka ta saki sakesu tayi taje ta rumgume hajja,kakube ta hajja tayi tana kuka tace oh Nasisi na wani mara imanin ne ya kawo ki cikin dajin nan fisabililahi saboda tsabagen mugunta, hajja kinga mutumin da yarshi ta taimake ni hannun wa inda suka sace ni, kina nufin macece ta amsheki hannun wa innan azaluman, eh hajja, tana ina to yar albarka, ai hajja taki biyo mu wai in kunje can gidan su sai ku gaisa acan, to yanxu gidan nasu zamu kenan, ehmana hajja har abinci umme tayi maku,wacece umme kuma, maman Abrish ce, wace... kinga hajja tun dazu sai tambaye tambaye kike, sai zuba surutu kuke dan allah,

Abbey gaisawa sukayi da Abbu, kafin Abbu ya gaida hajja aiko ta amsa cikin fara'a tana washe baki, Abbey ne yace to mukarasa gidan naka ko, da to ya amsa, Ashtar ne ya tambayeshi yace dan allah babu hanyar da mota zata wuce ne, akwai hanya ku biyo ni, cikin mota suka shishiga su da sojojin har Nasra mota ta shige, Ashtar ganin doki shikade babu kowa akai,aiko yai haye warshi dan dama yana kaunar doki bakadan ba, tafiya Abbu ye tayi dasu cikin jejin nan sunzo kusan tsakiyar jejin kenan,suka iske zakuna kusan uku tsaye a hanya , taka burki sukai da sauri suma su Abbu tsayawa sukai,zakunan ne suka fara nufo inda suke,hajja dake cikin mota qagube Ammee tayi kamar ba surukar taba, itama Ammee duk a tsorace take,dan basu taba ganin zaki ido da ido ba sai yau, sojojin nan duk fitowa sukai suka saita zakunan da bindiga shima Ashtar bindigan shi ya ciro, Abbu ne ya kalle su yace kada wanda yayi harbi, saboda me baza muyi harbi ba muka tsaya cutar damu zasuyi, Ashtar ya fada yana mai kara gyara saitin bindigan shi, idan kukai harbin nan zakuja wa kanku matsala ne wanda gwanda karo da zaki, akan karo da matsalan da zaku jawo, shiru Ashtar yayi yana tunani,tunda har mutumin dake zaune a dajin yace kada suyi harbi aiko bekamata suyi ba tunda shi ya fisu sanin kan dajin, sauke bindigan shi yayi kafin yace ma yaran shi kada suyi harbi, to amma Abba taya zamu wuce mutafi kaga sun tare hanya, Ashtar yake tambayan Abbu, kada ka damu maisu zata zo ta kure su, maisu kuma?, eh, yabashi amsa,shide Ashtar shiru yayi batare daya kara magana ba,saide tambayoyi ne tab a bakin shi,
Sunan sude, sun tsaya ganin ikon allah kuma gashi zakunan sai kara tunkaro su suke,duk tsoro yafara kama su, tuko kadan ya rage sukarasa wajen su dan har sun fara ja baya suna shigewa mota,

Sai sukaga wata iska mai kama da guguwa ta tashi,mutum suka gani ya diro gaban su batare da sunga daga inda ya fito ba, nanfa tsoron su ya karu dan sun dauka aljanu ne, dan anjuya baya basusan mace bace ko namiji ne,

Ku tsaya inda kuke,Abrish ta fada tana mai kallon zakunan nan take ko suka tsaya,daman kamar jiran umarnin ta suke, su hajja dake cikin mota suka fito suma waje,dan ganin ikon allah, Nasra ce tai dariya tace ai daman nasan Abrish saitazo nan wajen, kowa ita ya juyo yana kallo, Ashtar ne ya tambaya wacece Abrish, yatace Abbu ya bashi amsa, Ammee ce tace, itace ta taimakeki kenan auta, eh Ammee itace, kowa Abrish din ya tsora wa ido wacce haryanxu bata juyo ba zakunan take kallo,
Zuwacan tace masu, ku juya ku koma inda kuka fito, bana son nakara ganin ku a hanyar nan, idan kuma nakara ganin ku komai bayi maku,ku kukaja wa kanku, kuwuce kutafi, nan ko dukansu suka juya suka tafi,
"Sai bayan sun tafi sannan Abrish ta juyo, kowa sake baki yayi yana kallon ta baga mazan kadai ba harsu hajja, wasuma daga cikin sojojin sake baki sukai miyu na dalala, dan murmushi tayi wanda har yasa dimples dinta lotsawa duka biyun, aiko sojojin nan sai gasu suna sake bindigan su, saboda basu taba ganin mutum mai kyaun taba sannan ga gashi wanda kadan ya rage bai taba kasa ba, saboda yau shigan riga da wando buje tayi wanda kasan shi yake a matse saman shi kuma abude kamar de yadda wandon yan pakistan yake,sai riga mai dogon hannu wanda tsayinta ya tsaya mata iya wajen kugu kawai,duka kayan bakake ne sai rigan samane daya kasance ja wanda akayishi kamar alkebba,kan tama jan hulane saide bata daure gashin taba saita zubu dashi duka bayanta, hakan ne ya kara haska ta gata fara tas saitayi kamar aljana,sannan ga yanayin kwayan idonta yadda ya kasance blue color ne,

"Hatta Ashtar da kallon mata ba damun shi yayi ba,saide abun mamaki ko dauke idon shi ya kasayi akanta, gaban shi sai faduwa yake,yarasa dalilin haka sa hannun shi yayi ya dafe saitin zuciyar shi dan yaji yana mai zafi,

Itama Abrish din dake kallon su daya bayan daya tana zuwa kan Ashtar sai da gabanta ya fadi, da sauri ta dauke kanta juyawa tayi dan tafiya, Abbu ya tsaida ta,tsayawa tayi tana sauraran shi batare da ta juyo ba, Abrish saide fa ki shige mana gaba mutafi dan kada mukara cin karo da wasu namun dajin, batace komai ba sai gyada kanta da tayi, shi shiga mota sukai kowa na mamakin wannan kyaun haka,ita de hajja a ranta cewa take kai wannan yarinyan ba mutum bace aljana ce,

Itako Abrish igiyan bishiya ta kama ta dale abunta haka taitayi in ta kama waccan ta dale saita sake ta kama wacan,yadda kasan wata biri, sude tafiya sukaci gaba dayi kowa na sake saken shi akanta, hakade har suka isa gidan.








Aradun allah nagaji da typin sai gobe in allah ya kaimu da re da lafiya, ayi hakuri da wannan yau,.









Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌳
( WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM*(UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧15.

*****


"Koh da suka karasu gidan,Kowa mamakin ganin gidan yake,kuma daga gani shikade ne gida acikin jejin, sukuwa mutanen na maizaija masu zaman cikin jeji, Abbey yake gaya aranshi, isu Abbu yayi masu zuwa cikin gidan,
Shiko Ashtar ba abun dayafi daukan hankalin shi irin lambun nan,sannan abun daya kara birgeshi wannan koramar dake kusa da lambun, har suka karasa shiga gidan yana santin lambun aran shi,

Da fara'a umme ta taresu bayan sungama gaisawa,su Ammee suka shiga yimasu godiya akan irin taimakon da sukayi wa yarsu, ai hajiya babu komai yiwa kaine balanta kaga mutum yana cikin halin dayake neman taimako inde akwai yadda zaka taimaka mai to maizai hana bazamu taimaka ba,ai da' na kowane abun daya faru da dan' wani kaima zai iya faruwa da naka dan' shiyasa akeson taimako saboda bakasan waye zai taimaka wa naka ba, umme ce ke wannan maganan, hakane gaskiya kam, duk suka fada,
Mikewa umme tayi abinci ta dauko wanda sukayi wa bakin ya dunga jairawa agaban su,Nasra ce ta tashi tana taya ta,
"Tuwon shinkafa ne da miyar kubewa danye wacce taji ganda da nama ga man shanu,sai danbum dayaji zogale ga naman zabbi da akayi mashi gashin tukunya,sai fura wacce taji kindirmo ga kayan marmari gai ruwan randa mai sanyi sosai,

Duk da sunci abinci kafin su fito,amma ganin wannan abincin yanxu sai sukaji kamar basu ci komai ba,musan man ma hajja da dama tanacin abincin hotel din tana mita akan an hadata da dankalin turawa da shayi, yanxu ko da taga mutuminta tuwo aisai ta bude ciki ta kawsa, suma su Ammee ci sukai sosai dan abincin yayi dadi,

Ashtar sai baza ido yake acikin gidan yanason yaga ta inda Abrish zata biyo, dan tunda suka shigo gidan har suka gama cin abinci amma baigan ta ba, to ina aljanar yarinyan nan tayi ne, ya fada aranshi, to ni ina ruwana da inda tajema,tsaki yaja kasa kasa,
Niko nace yar nan ina yarinyan ku take ne,tunda muka shigo gidan nan bamu ganta ba,hajja ce mai wannan maganan, dariya umme tayi kafin tace,ai Abrish ba lalle ma ku ganta ba harku tafi dan tana cikin jeji sai yamma zata dawo, yamma fa tana mace ita ko tsoro bataji, inji Ammee wacce ta zaro ido waje, Abrish dai taji tsoro,ni harso nake naga ranar da yarinyan nan zataji tsoron wani abu, kina nufim batajin tsoron wani abu, gaskiya nidai ban taba ganin taji tsoron wani abun ba a dai cikin duk abun dazai tsorata mutum,,jinjina kai kawai suke yi, Abbu ne yace bari a aika,a kira ta tazo ku gaisa, mai magana, na'am baban uwar dakina,kaje kacewa Abrish tazo ina kiran yanxunan, to yanxu kuwa, tashi yayi yatafi,
To jama'ah tsuntsu da magana,hajja aku ne fa,inji Nasra dake wa hajja dariya ganin yadda tun dazu sai zarar ido take da taji ance Abrish bata tsoron komai,

Koda akunta ya fada mata sakon Abbu,dan yamotsa fuska tayi,aranta ko mita take an takura mata, tasan kiran bazai wuce akan taje su gaisa da iyayen Nasra ba, ita wllh an matsa mata, haka dai ta tashi ta tafi batare da ranta ya so ba,
Shiga gidan tayi da sallama kafin tanemi wajen zama ta zauna,tunda ta shigo suke kallon ta, gaishesu tayi,amsa wa sukai, tare da yi mata godiya akan abun da tayi wa yarsu, ita dai batace komai ba saidan murmushin da tayi,
"Dago kanta tayi,idonta bai sauka akan kowa ba sai Ashtar wanda shima ya tsareta da ido, kallon ido cikin ido sukayi wa juna, Abrish gani tayi bashi da niyan janye idon shi akanta,hakan yasa ta maka mai harara tare da murguda dan karamin bakin ta, zaro ido waje yayi, kambu ni aljanar nan take harara tare da murgude, aiko zanyi maganin ta bata sanni bane, kara tamke fuska yayi tare da dauke kanshi akan ta,
itama baki ta tabe, kawai yabi ya tsare mutum da ido, da wasu idanowan shi kamar na mujiya, ni mutum ya shiga gonata surfa shi zanyi kamar masara, gwanda ma kashafa wa kanka lafiya, ita kade sai masifa take aranta,
Lokacin yin sallah ne yayi, mikewa sukayi mazan suka fita waje danyin jam'i tunda suna da dan yawa, matan kuma cikin gida sukayi alwala tare da sallah su,

Bayan an idar da sallah Abbey yace yana son magana da Abbu, to bismila muje can, wata yar rumfa ce dake kusa da lambun wacce akayita da kaba,shiga sukai suka zauna akan tabarman kaban dake kai,
Malam Abubakar abun dayasa kaji nace inason magana dakai ba komai bane ila inason in roki wata alfarma a wajen ka, ina fatan zakayi min ita, to Alhaji indai baifi karfi na ba zanma ita insha allah, insha allah ma baifi karfin kaba, daman ba komai bane fahce inason dan allah,kai da iyalenka ku bimu mu koma Abuja tare, saboda bai kamata ace kuna rayuwa acikin jejin nan ba ku kadai ba makwabci ba yan'uwa sai namun daji kawai, duk da bansan dalilin ku na zama anan ba, amma nasan akwai dalili hakanan bazaku barau gari ba kuzo jeji ku zauna, dan allah kada kace a a, kodan rayuwar yarka ta inganta, dan allah,
numfashi Abbu ya sauke, kafin ya kalli Abbey yace,Alhaji koh da bakayi min wannan maganan ba daman a kwanan nan ina da niyar barin cikin wannan jejin tare da iyalina, ko dan Abrish tasan ya rayuwa take acikin mutane,
Alhamdulilah kace nayi magana akan gaba kenan, kware kuwa to amma Alhaji ko zamu biku bazamu zauna a Abuja ba,saboda wani dalilin,amma ita Abrish zata iya zama ni daine da matata zaman Abuja bazai yuyu ba a halin yanxu, zan iya sanin ko mai dalilin,gaskiya a a saide koh nan zuwa gaba zaka iya sani Alhaji amma ba yanxu ba, to shikenan in bazaka damu ba inason Abrish ta zauna a wajena nan Abuja, dan shiru Abbu yayi,yana tunani acikin ranshi zaman Abrish acikin gidan shi ta wani wajen matsala ne ta wani wajen kuma taimako ne, sannan sauki ne na samun hanyar cikan burin su, kallon Abbey yayi kafin yace Alhaji ba komai ai kaima yar kace zata iya zama a wajen ka, murna ce ta kama Abbey dan shi hakanan kawai yaji yana son yarinyan kuma yanayin ta na mai kama da wani ko wata wacce yasani,
Malam Abubakar saiku shirya ko zuwa jibi saimu wuce, dabobin nan naka gobe sai azau a kwashe su su fara yin gaba ko, da wurwuri haka Alhaji, ehmana malam Abubakar maiza jira, ai kawai sai tafiya kodan afara shirye shiryen makaranta Abrish da wuri, gaskiya kam,to Alhaji tunda Abrish wajen ka zata zauna,dawakan nen saide ku ajiyesu a wajen ku dan nata ne, dan dadbobin ma kusan nata ne dan nawa basu da yawa aciki da akwai inda zaku ajiye su dasai a aje mata abunta acan, eh akwai gidan gona na sai a aje mata acan kawai, dawakan kuma sai a ajesu a gida na,tun da akwai wajen ajiye su, to hakan ma yayi mungode sosai Alhaji allah yakara bude mafi albarka ya biya maka bukatunka duniya da rahira, Ameen karka damu aiyi wa kaine yanxude muje dan ku fara shiri da wuri,dan nasan saikun kin kitsa kayan ku,hakane,

Shiga cikin gidan sukayi,zama sukayi ana dan taba hira, tashi Ashtar yayi yace bari yadan shiga lambun can da to suka amsa mai, fita yayi a gidan lambun ya shiga,
Yanayin sanyi wajen yayi mai dadi sosai wani dan kujera da aka sasaka na icce dake karkashin bishiyan Apple, zama yayi akai bayan ya tsinka Apple daya ya wanke, kallon yadda ruwa ke zubuwa daga saman dutsen wajen zuwa cikin koramar nan, abun burge shi yayi, dan haka yaciro wayan shi yana daukan hoton wajen,ya daga wayan dan yayi salfe ya hango mutum kwance saman bishiyan Apple din harsai da gaban shi ya fadi dan yadauka wani abun cutar wane ko aljani, ashe wannan aljanar yarinyan ce ya fada yana mai maida wayan shi aljihu, juyawa yayi yana kallon ta,cin Apple din ta take hankalin kwance koh kallon inda yake bata yi ba,dan tun lokacin daya shigo wajen ta ganshi,surutun da akeyi acikin gidan yasata fitowa wajen nan dan tasha iska amma shine wannan shima ya kwaso jiki ya tawu dan ya matsa mata, tura bakinta ta tare dayin karamin tsaki,
Ke aljana,Ashtar ya fada yana mai zagayowa bayan kujeran yadda zai dunga ganin ta dakyau, aljana ba dake nake magana ba sauko ina son magana dake, idan iccen dake wajen sun tanka mashi to itama ta tanka, lalle yau naga wacce tafini miskilanci, ya fada aranshi, ke wai badake nake magana ba,ban son raini fa, ci kanka bata cemai ba, dugawa yayi dan dauko dutse, daguwan da zaiyi yaga wayam bata ba alamun ta a wajen, waige waige ya fara yi ko ta sauko kasa amma ko mai kama da ita bai gani ba, kai nifa daman nasan yarinyan nan ta hada iri da aljanu,inba aljana ba yanxu yanxu ta bace ya fada yana mai komawa ya zauna, itako Abrish tana kallon shi ganin da tayi, saboda yana ganin tane zai matsa mata da surutu shiyasa tayi abun da bazai iya ganin taba, ko uwar mai zanmai in na sauka kasan zai wani matsa min, mtsss taja tsaki,

Basu sukabar jejin nan ba sai yamma akan jibin zasu zo dan su wuce,sabone sosai ya shiga tsakanin umme da Ammee haka ma hajja, Nasra tunda akace mata tare zasu koma da Abrish Abuja take murna duk da tasan sai ansha fama da ita kam,

Da daddare suna zaune a tsakar gida bayan sun gama cin abincin dare, Abrish na kwance a tabarma tana busa sarewan ta,Abbu ne ya kira sunan ta, amsawa tayi tare da tashi zaune, Abrish inason in gaya maki ne cewan jibi zamu bar jejin nan zamu tafi tare dasu Alhaji garin su, ke zaki zauna a wajen Alhaji ne gidan su Nasra mukuma zamu nemi wani garin mu zauna ne,dan haka saiki shirya kayan ki kinji ko, tunda ya fara magana ta tsare shi da ido, ranta ya baci mai ake nufi kenan, so ake tayi rayuwa a inda ba jeji ba sannan ba dabobi taya akeson ta zauna acikin mutane bayan ita ta fita daban dasu, ina bazai yuyu ba,ba inda zataje,
Kinyi shiru bakice komai ba, Abbu ya tambaye ta,kallon shi tayi kafin tace,babu inda zani Abbu bazan je ba ta fada tana mai mikewa tayi daki rifo kufan tayi da karfi tana cigaba da fadin ita bazata ko ina ba,
Daman Abbu yasan sai hakan ta faru da wuya ta yarda amma zaisan yadda zai lalabata ta yarda dan hakan shine kadai hanyar da zata gane rayuwa sosai tare da cikan burin ta,


Alhaji haruna tunda wa'in nan yaran naka suka sace yarinyan nan bamu kara ji daga garesu ba shiru har yanxu, Alhaji salisu nima kaina naiman su nake dan in na basu aiki dasun gama suke sanar dani amma wannan shiru, ko dayake tunda kaga haryanxu ana binciken wa,inda suka sace yarinyan kila shiyasa basu naime muba, wata kila suna mafaka ne a wani garin, kasan su Bahba ko ta ina zuwa suke,hakane kuma da wannan dan wannan,to bari mujira har zuwa nan da kwana biyu indai basu kiraba to yakamata mu dau mataki cikin gagawa, gaskiya kam, hakadai sukaci gaba da kula muguntar su tare da mugun nufinsu.




Niko nace allah ya shiryasu yasa su gane gaskiya, dan duk wanda ya zalinci wani to tabbas sai yaga sakaya tun a duniya,







Shere fisabililahi.
[8/10, 11:17 PM] +234 903 550 2413: 🌳🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌳
(WILD GIRL)


*NA SABUWAR MARUBUCIYA*
*FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧16.


*****

"Tunda suka koma Hotel din, Ashtar yake ta tunanin Abrish, yanxu ma kwance yake akan makeken gadon dake dakin hotel din yana aikin tunanin ta, Oh No wai maiyasa tun dazun nake

Please Login or Register in order to submit comment