You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nabar Abrish anan tare dashi lokacin bai tashi ba sai bayan shigana inajin ya tashi,cewar Nasra,

To gaskiya ayanzu bana tunanin zai yarda da kowa bayan ita,dan shi ita yake ma kallon komai nashi,kamar da ne da uwa,dan haka bazai yarda da kuba in ba itace tayi mai magana ba,dan yanxu maganan ta kade zaiji, saide kuyi hakuri Alhaji, da sauki ma tunda naga kamar matar shice ko, inafa matar shi kanwar shi dai, amma kaiko ashatu bakayi ba,karasa wa zaka makalewa sai aljanar yarinyan nan,wani kallo da Abrish tayi ma hajja yasata canxa maganan ta bata shirya ba, am ina nufim aiya iya zaben uwar riko sosai sosai ma eh,
Anty inajin yunwa,yakara fada yana leken fuskar ta tawajen kafadar ta, rumtse idonta Abrish tayi ji take kamar ta fas faska mai mari wllh,in banda ya mugun raina mata wayo itace anty, shikuma likita da zancen banxa mai nufim shi,itace zatayi ta rainon shi harya sami lafiya, ehman raino tunda wannan dashi da jariri ban bancin su kadan ne babu yawa,saide raino ba jinya ba,

"Abokina zo in duba ka ko,um um yace, anty saifa kinyi mai magana tukun,wani shegen harara ta maka wa dr dayasa yashiga taitayin shi babu shiri,dan shi kwayar idon tama tsoro yake bashi,kai ai daga ganin ta kasan ba yar Nigeria bace ba, ko wannan kyaun nata aisai kasashen waje ko aljanu,
Abrish zaunar dashi aduba bashi kinji yi hakuri, cewar Abbey,batace komai ba sai jawo shi da tayi daga bayanta ya dawo gaban ta,
Zauna tace mai,saiko gashi ya zauna tare da kara rike mata hannu dan kadama ta gudo ta barshi,duba shi dr yayi kafin yadanyi rubuto,sannan ya kalli Abbey yace Alhaji babu wani matsala zuwa gobe ma za'a iya baku sallama idan jikin nashi yakara karfi, yanzu a bashi abinci yaci sai a bashi maganin shi,ok dr mungode,
Kuje ya wanke bakin shi a toilet kafin yazo yaci abincin,to tace ba yadda ta iya haka taja hannun shi har toilet,ana wanke baki yana shanye kunfar kamar karamin yaro, hakade suka gama batare da yaga dariyan Abrish ba ko murmushi,hakan bai dame shiba tunda tana tare dashi ai,
Tea Ammee ta mika wa Abrish,kallon ta Abrish tayi da fuskar ta wanda ke hade, sorry daughter kinji,sa hannun tayi ta amshi cup din ta mika mai, make kafanda shi yayi,ni ke zaki bani , mai kaga amsa kasha tun muna mu biyu dakai, um um ni allah ke zaki bani, oh my god ta fada tare da kumbura fuskar ta,dan wllh yafara kaita karshe fa, daughter please,bayada ta iya haka ta zauna a gefen shi,ta dunga bashi a baki yana sha,tare da wasa da yatsun hannunta wanda yake rike dashi,a haka har ya shanye duka tea din, kafin ta fara bashi tuwon semovita da miyar kubewa danya da tasha man shanu ga nama da kifi aciki tare da ganda, saici yake har wani lumshe ido yake kamar mai shirin bacci, haka ta gama bashi fuska ba fara'a,wanke hannunta tayi ta tashi zata wuce,kawai taji mutum a bayan ta yawani ririketa,
"I hate this man", ta fada aranta tare da dan juyawa ta kalle shi kafin tace sake ni, saketa yayi saikuma ya riko hannunta, ni zan biki anty kinji, banza tayi dashi dan tana tunanin inbasu rubata da mutumin nan ba takusan kaime duka,
Zo ka zauna itama anty ba inda zata, inji Abba yusuf, oh ni dijee ina ganin abu nikam cewar hajja da tun dazun in Ashtar yayi abu saide ta rike haba tace allah gamu gare ka, dan ita dai bata taba ganin abu irin wannan ba sai yau, garjejen kato yasa yarinya a gaba yana kiran anty saboda allah fa, wannan abu damai yayi kama gashi sai wani ririketa yake yi ita ba matar shi ba, gaskiya Ashatu ba lafiya da gasken gaske.












Commets and shere fisabililahi.🌴🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌴
(WILD GIRL )

*STORY AND WRITTEN*
*BY FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH 🤱)


♧Pege♧33.

*****


"Um um ni zanbita tare zamu tafi, to shikenan zaku tafi taren yanxu dai ka saketa kazo ka zauna saita shirya maku kayan ku kaji, kallon Ammee yayi kafin kuma ya kalli Abrish yace,anty na zauna, ban sani ba, ta fada a fusace dan wllh ya kaita bango, to kinji kaka anty tace bata sani ba dan haka bazan zauna ba sai anty tace,
Kaka kuma cewar Nasra da tasaki baki da hanci, ehman anty karama kaka mana baki ganta babba ba, to yanxu idan ita kaka ce wannan fa,cewar Nasra tana nuna mai hajja, wannan ai tsohowa ce bakiga ta kusan mutuwa ba, duk yadda Nasra taso danne dariyan ta ta kasa saboda ganin yadda hajja ta zaro ido waje tare da daura hannu aka, hatta Abrish dake cikin fushi saida ta dara, suma dai su Abbey aboye sukai nasu,
Nashiga uku na lalace yanxu nice na kusan mutuwa fisabililahi uwar ka bata kusan mutuwa ba saini ,dan tsabar ka tsane ni a rayuwar ka, saikuma ta fashe da kuka,
Shide Ashtar kallon ta yake kamar yasami tv,kafin ya juyo wajen Abrish yace anty maiyasa ta kuka, da dan murmushi ta kalle shi kafin tace tsoron mutuwa take yi, lah anty kina dariya daman, fadan hakan da yayi yasata gimtse fuska tare da ture shi, ya fada kan gado,ko kafin ya dago daga kwance da yake ta fice a dakin,
Ai yana ganin haka ya fashe da kuka saikace karamin yaro, Abbey ne ya matsa kusa dashi yace yi hakuri yanxu zata dawo kaji yi shiru, ina malam Ashtar baisan batun hakuri ba lallashin duniya anyi yaki yin shiru,shi sai yabi anty shi,ga anty kuma tayi tafiyar ta ba asan inda take ba, karshe dai dr yazo yayi mai allurar bacci sannan aka sami lafiya,
Hmm ikon allah yanxu haka rayuwar yaron nan zata ta tafiya, cewar Abba yusuf, to yaza ayi yusuf, ni yanxu ma matsalan shine kagafa baya yadda da kowa sai Abrish,ita kuma yarinyan nan ba kalan sauran mutane take ba,itama kanta naiman yadda za'a kula da ita takeyi, matsalan dake kanta yafi na Ashtar girma, dan haka ni yanxu mafita yakamata mu naima, to yanxu yaya maiya kamata muyi,
Nima kaina yusuf ban sani ba, ni ina da mafita cewar Ammee, duk kallon ta sukayi,


"Kunji yaron can ya haukace ko, cewar Badaru, ga abun farin ciki amma babu daman yi, bala'i dake gaban muma ya ishe mu,yanxu ko ta ina zamu fara naiman yaran mu,dan duk inda ake tunanin za'a gansu anje amma basa nan, cewar Alhaji usman, hmm ku yanxu a tunanin ku waye zai sace yaran nan,fadin Alhaji haruna,dole ya kasance wani abokin takaran mune yayi mana hakan, fadin Alhaji salisu, maganar ka gaskiya ce, to amma wa kuke tunanin zaiyi haka, shiru sukayi dan basu san wanene ba dan mutanen nada yawa,

Misalin karfe shida na yamma Ashtar ya tashi daga baccin dolen da aka sashi,tunda ya duba dakin baiga Abrish ba ya kuma ya takure waje daya,yaki yiwa kowa magana, yane Friend katashi kenan,hararan shi Ashtar yayi yace ,waye kai ni ban sanka ba, nine baka sani ba Friend,um ni kakira min antyna,anty tace bazata zo ba saikaci abinci kasha magani tukun, indai naci abinci zata zo,ehman da gaske nakeyi, to ban abinci,zubamai abinci yayi yako ci,yasha maganin,
To na gama ka kira min anty, um anty zata zo amma saikayi sallah tukun, to in nayi zata zo ko, zuwa kai, alwala yayi tare dayin sallah kuma yayi ta cikin natsuwa,zaka dauka mai hankali ne, to yanxu ka kwanta bari inje in kira maka anty ko, to yafada tare da kwanta wa,


Anya koh kina tunanin abun da kika gayan nan zaiyi aiki,baza'a shiga hakkin yaran nan ba, to Abba su in ba hakaba to babu wani mafita da ya wuce hakan, shikade ne za'ayi hankali mu ya kwanta sannan asami abun da ake so, shikenan allah yasa haka shi yafi alkairi, ameen ya allah.







Commets and shere fisabililahi.[8/17, 5:06 AM] AMINA KABIR CAPS: 🌴🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌴
(WILD GIRL)


*STORY AND WRITTEN*
*BY FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)



♧Pege♧34.

*****

"Washagari da safe dr yazo ya basu sallama, ya kalli Ashtar yace abokina allah yakara lafiya yasa kafara ne,ko kallon shi Ashtar baiyi ba,dan tunda garin allah ya waye yaki yiwa kowa magana,saboda baiga anty shiba tun jiya shiyasa yake fushi da kowa,musanman ma umar da jiya yace mai zatazo kuma bata zo ba,
Friend tashi muje gida, banza yayi da umar bai kula shiba, aifa hali zanen dutse duk da yana cikin halin mantuwa bazai daina miskilanci ba,fadin umar aran shi, dakyer umar ya shawo kanshi kafin ya yadda ya bishi,dan cemai yayi indai bai bishi ba to bazai kara ganin anty ba,wannan dalilin yasa ya bishi sai wani kumbura fuskar yake yi,tare da tura baki, umar dai bai kula shiba har suka isa gida,
Da sallama umar yashiga falon,yana rike da hannun Ashtar,amsa masu su Ammee sukayi dayake kowa duk yana part din Ammee saboda kiran su da umar yayi yace kada suzo dan za'a basu sallama ne, shiyasa suke jiran su anan, zama sukayi umar ya gaida su Abbey tare dasu Ammee,da fara'a a fuskar su duk suka amsa mai,Ashtar kuwa ko kallon su baiyi ba hankalin shi nakan Teddy din Ayman yaron yayan shi Muhammed,zuwa yayi ya amshe a hannun yaron tare da zama akasa ya fara wasa da ita, ai Ayman na ganin haka yasa wa uwar shi kuka, kallon shi Ashtar yayi kafin ya fashe da dariya yace yaro bazan baka ba nima wasa zanyi dashi,kaje maman ka tasai ma sabo wannan nawane zamu Dunga wasa dashi ni da anty na, banda kai yaro yafadi haka yana mai gwalo,
Kowa kallon shi yake cikin tausayi su twins ko kuka suka kama yi,yanxu yayan sune cikin wannan halin,innadillahi'wa'ina ilahi raji'un, ya allah mun tuba kayafe mana kura kuran mu,
Aboki makaryaci,to ina anty ta kaifa kace wajen ta zamu zo kuma yanxu ni ban ganta ba ,kaga kayi karya sau biyu kenan,ni wllh na daina yarda ma dakai,kacika karya da yawa,fadin Ashtar dake banka wa umar harara, aboki yi hakuri anty ka ta tafi makaranta amma ta kusan dawo wa yanxu na kaji, nafa daina yarda dakai makaryaci,ni wllh saika kaini wajen anty na, yafada tare da mikewa tsaye rumgume da teddy akirjin shi hanya waje ya nufa yana fadin, antyna ni ka kaini wajen antyna bazan zauna anan ba saika kaini wajen anty na, da sauri umar da Mubarak suka kamo shi sai fisge wa yake yi yana masu ihun akaishi wajen anty shi,

Nifa ban gane ba wacece anty shi,fadin Nafeesat dake kallon uwarta, nima kya tambaye ni, bayan tun jiya muna tare dake acikin gidan, shikenan yanxu wai ya manta ni, ya manta iyayen shi ma balle ke daba wani matsayi gareki a wajen shiba,fadin Afrah dake hararan Nafeesat, kijimin Afrahn na kibar ganin ke yaya tace ki fada min maganan banza wllh yanxu zan rama dan ba tsoron ki nake ba, wani dariyan rainin hankali Afrah tayi kafin tace, au da gaske to bismila,dan naga alamun wani jinya kike son karawa, to maima zaki iya ke da kike gurguwa mara hannu da kafa, Nafeesat zatayi magana hajiya saratu ta hanata, tare da cewa wai kin manta yanxu matsayin ki da nata ba daya ba, kefa matar aure ce yanxu,itako ko saurayi bata dashi balle tayi auren amma shine zaki dunga bata bakin ki wajen magana da ita,matar mejor Malik Ashtar kikefa,
Kokuma matar mahaukaci ba,fadin Hajiy falmata dake dariya,dan ita wannan ciwon na Ashtar farin ciki yasata ba kadan ba,
idan shi mahaucine kece shugaban shi a haukan, dan kema bakifi karfin jarabawar ubangiji ba ayanxu saiya maida ke abun da baki tunani ba, mahaukatan banza da wofi yaro bashi da lafiya maimakon kuyi jimami saima babin fadan da kuka bude agaban iyayen shi saboda baku da mutumci, ni wllh bansan uwar mai yusuf ya gani atare dakuba daya aure ku,mata baku da aikin yi sai fada da hassada a tsakanin ku,to wllh kufita idona tun kafin raina ya baci nayi maku abun da baku taba tunani ba,dan azamanin yanxu zawarci a wajen ku ba abu bane mai wahala yanzo sai insa ya kada ku gidajen iyayen ku,
Shiru duk akayi anrasa maiba wa hajja hakuri da sababin da takeyi,dan ba karamin haushi sukaba wayan falon ba,musanma Abba yusuf daya kasance matan shine,suko sunyi tsit sai zarar ido suke,jin hajja na kukarin sawa a sake su,
Sallaman su Abbu ne ya katseta daga masifan da takeyi,a a Abubakari harkun iso kenan, fadin hajja wacce keta zabga uban murmushi,saikace ba ita bace ta gama bala'i yanxu ba, eh wllh mama mun same ku lafiya ya mai jiki kuma, wllh lfy lau mai jiki kuma,kun ganshi nan ba abun daya iya sai kiran anty dayiwa mutane fatan mutuwa, mutuwa kuma mama, ehman mutuwa aikasan dayake baya kaunata jiyan nan yace wai na kusan mutuwa fisabililahi hakan ya dace, ni banyi mai fatan mutuwa ba amma shi yana yimin,sai kuma ta fashe da kuka saikace karaman yarinyan, su twins da muhammad sai dariya suke mata a boye, Ashtar dai na gyefe su umar sunbi sun ririke shi,saboda kokarin guduwa dayake yi shiwai zashi wajen anty shi saikace yasan inda take ne,
Ana cikin wannan rigiman su Abrish suka shigo falon da sallama dan antaso daga makarantar, ai tunda yaji muryan ta kuma ya kyalla ido ya ganta, baisan sadda ya wazar dasu umar ba yayi wajenta da gudun shi,jitayi kawai mutum ya fada jikinta tare da rumgume ta yana fadin anty ina kika tafi kika barni,tun jiya aboki mai karya sai cewa yake zaki zo baki zoba, nidai duk inda zakije daga yanxu tare zamuje ko, ya fada tare da dan dago kanshi daga kafa dan ta,yana kallon fuskar ta wacce take a hade saikace bata taba dariya ba arayuwar ta,
Sake ni ta fada batare da ta kalle shi ba, um um allah bani sakin ki kikara guduwa,saima kara rumgume ta yayi saikace wani yace zai kwace mai ita, lumshe idonta tayi kafin ta budesu tare da daga kanta sama, tana sauke numfashi a hankali,dan ayanxu ji take kamar tasami bulala tayi mai dan banza duka wllh, tana mamakin kanta wanin zubin akan mutumin nan,batasan maiyasa bata yimai abun da takeyi wa sauran mutane ba, na farko dai ba tsoron shi take jiba sannan bata shakkan shi, to maiyasa bazanyi maganin shiba ko zai sama min salama a rayuwa,wannan takuran har ina saiya wani manne mata,kamar yasami maman shi kokuma matar shi, dolema inyi maganin ka dan bazaka shiga rayuwa taba ka batamin shiri ba gaira babu dalili, ajiyar zuciya ta sauke,kafin takara cemai ka sakeni nace ko, um um, zan mare ka wllh in baka sake ni ba,
Wllh ko kasheni zakiyi bazan sake kiba,kuma allah duk inda zaki saina biki saide kita dukana amma saina biki,
Wayyo allah na, natsani wannan mutumin wllh, ta fada aranta, sudai su Abbey nasu ido,dan so suke suka yadda za'a kare wannan draman,Nafeesat ko tacika tayi fam kadan take jira ta fashe saboda kishi, su hajiya saratu suma dai kallon ikon allah suke,


Dafa kirjin shi Abrish tayi da hannunta nan wani farin haske yadin fita a hannunta zuwa kirjin shi, sauke hannun ta tayi kafin tace sakeni to, saketa yayi , kamar yadda tace, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kama hannun shi suka karasa inda su Abbey ke zaune, ita sai yanxu ma ta lura da iyayen ta,sake hannun nashi tayi tanufi wajen umme ta da murmushi a fuskar ta shima bayanta yabi, umme yaushe kukazo, yanxu nan bamu dadai da zuwa ba, murmushi takara saki kafin ta kalli Abbu tagaida shi,amsa yayi shima da fara'a a fuskar shi dan ganin yadda yar tashi ta kara kyau abun ta, bayan ta gaida su Abbey ta mike zata wuce sama dan canza kaya tare dayin wanka, hanyan upstair ta nufa, saijin mutum tayi yana binta a baya, tsayawa tayi tare da dafe kanta, kallon shi tayi kafin tace,wuce ka zauna ina zuwa yanxu, tora bakin shi yayi tare da makale mata kafada, ni zan biki ne,kama hannun shi tayi har wajen Ammee ta zaunar dashi akusa da ita,
Kaganta nan sunan ta Ammee itadin mahaifiyar kace, komai kakeso kayi mata magana da inanan da bana nan, zata baka, dan tafi kowa jin zafin ciwon ka anan wajen sai kuma mahaifin ka, kuma zata kula dakai fiye dani,dan haka zauna anan ka tayata hira, zanje inyi wanka yanzu in dawo,ai zaka sha chocolate ko,daga mata kai yayi da murmushi a fuskar shi,to ka zauna anan yanzo zan dawo in ba hakaba bakai ba chocolate, um um zan zauna ai zaki bani chocolate din ko in na zauna,sosaima kuwa, yaron kirki, to zan zauna wajen Ammee harki dawo, yafi maka alkairi kam, ta fada aranta tare da barin wajen, dan bakaramin kokari tayi ba wajen danne baccin ranta ba,

Abbey ne ya kalli su Abbu yace ku tashi mu tafi masallaci muyi sallah, duk mazan mikewa sukayi tare da fita, akabar su Ammee kadai,
Ammee yunwa nakeji,zanci abinci, shafa kanshi tayi kafin tace to dan Ammee yanxu kuwa zan kawo ma abinci,tana fadin haka ta mike dan zuwa kawo mashi abinci farin ciki ya cika mata zuciya ganin Abrish tasa ya yarda da ita,

Yaya Ashtar Nafeesat ke kiran shi amma ko juyowa baiyi ba balle ya kalleta dan shi ya dauka badashi take ba,yaya Ashtar shiru dai ba amsa,ganin haka yasata mikewa tare da zuwa inda yake, hannu tasa tare da riko nashi, juyowa yayi tare da kallon ta, ganin bai santa ba yasa ya fisge hannun shi yace sake ni, kuma saina fada wa anty kin rikemin hannu da zafi muguwa ni ban sanki ba, zaro ido Nafeesat tayi jin abun dayace,mai su Afrah zasuyi ba dariya ba,saboda mugunta,barin part din Nafeesat tayi gabaki daya dan bazata iya zama hauahi ya kashe taba,


"An daura auren Malik Ahmed moddibo tare da amaryan shi Abrish abubakar, akan sadaki naira dubu dari, muna masu fatan zama lafiya tare da zuri'an dayyiba, fadin ladan.






Yaufa ake yinta anan wajen.😳






Commets and shere fisabililahi.
[8/18, 6:08 AM] AMINA KABIR CAPS: 🌴🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌴
(WILD GIRL)


*STORY AND WRITTEN*
*BY FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)


♧pege♧35.

*****

"Anya kuwa kunne ta daide yake jiyo mata wannan batun, to kodai ta fara samun matsala a kunne ne bata sani ba, mai Abbu yake kokarin cemata ne yana nufim ita akayi wa aure ko mai, kai ina gaskiya ba daide taji wannan batun ba, gwanda ta kara tambayan shi abun dayake fada,"
"Abbu nifa ba fahimtar abun da kake fada nake ba,gwanda akara yimin gwari gwari yadda zan gane, dan ban yarda da abun da kunne na yaji minba, fadin Abrish da tayi kicin kicin da fuska tana kallon Abbu dake zaune kan kujera, eh maganan da kikaji nakeyi gaskiya ne,dan yanxu dawowan da mukayi daga masallaci aka daura auren ku da Ashtar shiyasa ma na kira ki dan nayi maki bayani da kaina, dan allah Abrish kiyi hakuri ki zauna da wannan bawan allah kodan halin dayake ciki gashi yanxu ba yarda yake da kowaba in bake ba,wannan dalilin ne yasa muka yanke shawaran yi maku aure,saboda rike kin dayake yi,gashi ke ba muharamar shiba,amma yanxu tunda akwai aure tsakanin ku koh ya rikeki babu matsala tunda yanzu miji da mata kuke, ta bude baki zatayi magana Abbu yayi saurin taran numfashi ta, dan yasan yanxu tana furta magana wllh saita aikata abun gwanda ya tare ta da wuri, dan allah na rokeki kada kice komai kiyi mana wannan alfarman, ki zauna dashi tsakani da allah duk da munsan an shiga hakkin ki,anyi maki aure ba tare da shawaran ki ba, amma ina ganin babu komai tunda ni mahaifin ki na yarda dan haka kema bazaki ki yarda ba, dan nasanki kinamin biyayya indai nace inason abu kikanyi ko baki so,to wannan ma haka nake rokanki alfarman dan allah kiyi hakuri,kiyi hakuri ansan duk wanda akaba wa hakuri an cuce shi, amma hakurin zakiyi ki amshi auren nan da hannu biyu,
Shiru Abrish tayi idon ta ya kada yayi jajir ranta na wani irin kuna, aure dai sukayi mata ba shakka, itafa a tsarin rayuwar ta babu soyayya balle wani aure,amma shine wa'in nan mutanen zasuyi mata haka, maiyasa suke son shiga cikin rayuwar tane, duk wani abu da tasan zai hadata da Ashtar batason shi, dan zama tare dashi zaisa ta kasa cika kudurin ta na shekara da shekaro, maiyasa saini, ga matan shi har biyu shine sai sun kara da ita a matsayin ta uku,kan uba, wllh basu naimi zaman lafiya ba, su da kansu sun bude shafin bala'i dan yanxu zasusan Abrish na cikin gidan, da wasan yara kawai akayi,yanxu za'ayi asalin wasan, ba aure ba zata zauna amma suma zasusan sunyi mata aure,

Kinyi shiru bakice komai ba, cewar Abbu dan shi yadda idon nan nata yayi ja tsoro yake bashi, can kasan makoshi tace naji ai, ba aure kukayi min ba, hmmm to zan zauna shikenan,
Ina wllh bai yarda da Abrish ba,akwai abun da take shiryawa, cikin sauki bazata yarda da auren nan ba, amma yanxu yadda ta yada dashi da wuri yasa yana zargin wani abu,dole akwai abun da zata aikata,
Hmm Abbu kenan kamar yadda kake tunani hakane ,zaman aure zamuyi shi cikin gidan nan amma zan koma masu *yar daji* na, tana gama fadin haka tafice daga dakin, Abbu na kiran ta amma ko juyowa batayi ba balle ta amsa,

Tazo wucewa ta falo Ashtar ya ganta,harya mike yana kiran anty umar ya rike mai hannu tare da maidashi zaune, kowa ya tsorata da ganin yadda lokaci daya ta koma wata abun tsoro dan idonta saboda jan da yayi zaka dauka rushine aka zuba aciki,jijiyoyin kanta duk sun tashi,abunka da farar fata gabaki daya fuskar ta tayi ja sosai,kamar wacce akayi wa dukan tsiya, ko kallon inda mutanen falon suke batayi ba tafita gabaki daya daga part din,

Maiya farune malam Abubakar, ajiyar zuciya Abbu ya sauke kafin yace,ta yarda da auren amma gaskiya sai kunyi hakuri da ita ayanxu dan gabaki daya haushin kowa takeji, umm ya zamuyi to dole ai mudau hakuri tunda mune mukayi mata laifi, hakane allah ubangiji ya sanyaya mata zuciyar ta dai, ameen ya allah,

Ni ka sakeni na tafi wajen anty na, au anty ba anty ba anto,kai yanxu kaje wajen anty inaga bamai gane kalan fuskar ka saboda marin da zaka sha awajen ta,kai allah na tuba a wannan yanayin da take ciki ko da kudi aka hadaka kaje wajenta ai bazaka ba, tura baki gaba Ashtar yayi nidai inason zuwa wajen ta katashi ka kaini,babufa inda zaka gwanda kayi zaman ka wajen Ammee yafi ma alhairi, ni bazan zauna ba wajen anty zani,to zo muje na kaika, binshi yayi harda murna wani daki dake nan kasa umar ya shiga dashi tare dayin sauri ya rufe kofar, ihu ya kamayi da bugun kofar akan abude mai, duk shiru sukayi tare da kyale shi,dan gwanda ya zauna adakin nan da yaje wajen Abrish a halin da ake ciki,duk jigum sukayi saikace wa'inda akayi wa mutuwa bakajin komai sai ihun Ashtar yana zashi wajen anty abude mai kofa, babu wanda ya kula shi, harya gaji yayi bacci abakin kofan dakin,

Su Badaru ne sukayi sallama tare da shigowa bayan sun gaisa,aka bode taro da addu'a,
To dalilin daya taramu anan gabadaya shine, munason mu shaida maku sakamokon wannan rashin lafiyan da Ashtar ke ciki na loosing memory,gashi ya manta komai nashi hatta mu iyayen shi, saikuma gashi tashin da yayi a hospital yaga wannan yarinyan Abrish a tare dashi, wanda

Please Login or Register in order to submit comment