You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganinta da yayi yake tunanin itace komai nashi, baya yarda da kowa sai ita,bayajin maganan kowa sai nata,sannan ga riketa dayake yi duk lokacin daya ganta,kuma ita ba matar shiba sannan ba muharamar shiba,
Shiyasa da mukaga haka muka yanke shawaran daura masu aure,wanda fitan da mukayi sallah azahar aka daura masu auren, wannan goron da sweet din da kukesha na auren sune, ku su ilham ke da Nafeesat ina fatan zaku zauna lafiya da yar'uwar ku lafiya ku riketa da amana, dan allah banda fitina ku kwantar da hankalin ku kuyi jinyar mijin ku tare harya sami lafiya,
Gabaki dayan su Abba yusuf suka kurawa ido wanda tun dazun yake maganan, wutar kansu ya dauke gabaki daya,musanman ma su ilham, kowa yama rasa tunanin da zaiyi, Abrish fa yarinyan da take kamar aljana, Nasra ko cewa take aranta wllh su Nafeesat kun shiga uku,allah yaji kanku kawai,
Bro um bro, waini kam yaya Ashtar bazaiyi matar kanshi bane, bangane ba yanxu matan nashi na wani suka koma, kai ni tsiya ta dakai baka fahimta wllh,nufina dukafa matan shi babu wacce take zabin ranshi duk dole akayi mai ya aure sufa, hakane kuma maganan kafa, amma sai nake ganin tun kafin yasami wannan matsalan kamar yana son Abrish fa, nima naga hakan, to amma ya zaiyi allah yabashi mata har uku a bagas, dama ni, kai yanxu bro ina zaka kai mata har uku, inda ake kaisu mana, kaji min mutum toni mata hudu ma zanyi, to allah ya baka sa'a kaji watarana saide a dauko gawanka matan sun babbake ka, ba ameen ba dan rainin wayo,
Talle masu keya da umar yayi yasa su yin shiru dan tun sadda suka fara gulman yan
a jinsu, allah ya shirya ku twins sudai sai zarar ido suke dan basuyi tsanmani wani najin suba,
nan dai kowa ya watse tare da dunbin tunani a zukatan su, dan dole su naimi mafita akan yarinyan nan dan bakaramin matsala zata kawo masu ba,

Wai lafiya Badaru daka kiramu kace mu hadu dukan mu, lafiya fa kace,aimu yanxu bamu ba sauran kwanciyar hankali, kamar ya kayi mana bayani dan ni nadauka an gano inda yaran mu suke ne, kai dan allah ta yara da sauki insha allah za'a gansu, amma wannan gobaran da take tinkaro mu bana tunanin muna da ruwan kasheta, dan allah kayi mana bayani yadda zamu gane,
Ashtar dai ya auri Abrish, Ashtar kuma wani Ashtar din, har Ashtar nawa kasani kai, banda wannan yaron, yana cikin haukan wani ya dauki yarshi ya bashi, kaifa tsiyata dakai kenan haruna baka ganewa kwata kwata,
To bari inyi maku gwari gwari, bawata ya aura ba face wannan,aljanar da ta addabi rayuwar mu,
Wani zaman yan bori Alhaji salisu yayi kafin ya daura hannu akai anyanka ta tashi, salisu bata yanku ba shiyasa ta tashi wllh da ta yanko bazata mike ba, fadin Alhaji usman dake fifita da hulan shi, Alhaji haruna yama kasa magana kwata kwata dan har wani jiri yake gani, baya yayi zai zube akasa Alhaji basheer da hayatu sukayi saurin tare shi, Alhaji haruna Alhaji haruna, Badaru ku miko ruwa ya suma ne, nima dazan sami mai ban ruwan so nake, mun shiga uku mukam,
Wai mai muka aikata wa yarinyan nan ne, dahar boka na saman tsauni zaice zataga bayan mu daya bayan daya, ka tambayan hayatu nima bansan laifin mai mukayi mata ba, dole mu naimu mafita yanxu dai mukai haruna asibiti tukun,daukan shi sukai tare dasawa a mota sai hospital,


Ammee Abrish fa tunda ta fita bata dawo ba, haryanxu kusan karfe goman dare kuma bata cikin gidan nan kaf na duba, cewar Nasra, subuhanallah to ina taje, wllh ban sani ba, kinga bamuga ta zama ba,muje wajen Abbey ki yanxu adubata, mun shige su kada dai yarinyan nan zuciya tayi tabar gidan, Ammee kefada tana nufan hanya fita daga cikin bedroom dinta,
Gidafa ya dauka ta ko ina ba'aga Abrish har lambu an duba batanan, to yanxu jama'ah ina zataje, fadin hajja, mama ku kwantar da hankalin ku,indai Abrish ce zata dawo,duk inda taje, ko kafin mu dawo nan indai ranta yana a bace bata zama inda muke dan zata iya yimana komai shiyasa indai batason ta aikata wa mutum mugun abu in ranta na bace,takeyin nisa da mutane dan haka ku kwantar da hankalin ku indai Abrish ce gobe ma zata dawo, to shikenan amma duk da haka na sanar wa yan sanda, dan musan inda matsaya take zamanin yanxu ya baci da yawa,fadin Ammee, hajiya ki kwanta da hankalin ki zata dawo kada kusa damuwa aran ku, cewar umme, to shikenan allah ya maidota lafiya,ameen duk aka amsa dashi,

"Gari yawaye har wajen karfe takwas amma ba Abrish ba alamun ta,ga Ashtar dayasa su gaba da rikicin anty shi,dan har ya fara masu fashe fashe a gidan,saida suka daure shi tukun aka sami lafiya, suna zaune ana jimamin batan Abrish ga police basu ganta ba, kawai suka fara jin hargagin masu gadi awaje duk ya cika gidan,ga wani kuka saikace na namun daji, duk hanyar waje suka nufa, wani dan iskan birki duk suka ja sakamakon ganin namun daji nata shigowa falon,harda su damisa ga burai ga zakuna, can ta kasa kuma macizai ne ke shawagi, Abrish ce ta shigo falon fuskar ta dauke da murmushi, akunta yana hannun ta ga wani dan karamin biri a kafadan ta,
Barkanku da safiya iyayena da yayyena tare kishiyoyina, af na manta ina mijina yake ne,
Anty taji an fada daga gyaifen ta, oh my love waye ya daure min kai haka, tafada tare da karasawa inda yake ta kwance shi, rumgume ta yayi, yana fadin anty ina kika tafi kika barni, kwantar da hankalin ka my sweet honey babu inda zan kara tafiya in barka, laah anty kinga zaki da biri acikin gida,eh kana son sune,um um suna cizo ai,kar kaji komai aikai mijin yar daji ce babu abun da zasuyi maka, da gaske anty, sosai ma baby love, hannun shi yasa tare da taba zakin dake kusa da ita , nanko zaki ya dunga shige mai yana sosa kanshi, dadi ne ya kama Ashtar ganin basuyi mai komai ba,aiko yaci gaba da wasa dasu, mikewa tayi,ta barshi anan da zakin kafin ta karasa wajen su Abbey da suka makure waje daya dan hajja kam harda zawo ta saki a wando,amma ko damuwa batayi ba, Abbu da umme ne kawai basuyi tsoron da yan gidan suka nuna ba, cikin karfin hali Abbu yace, Abrish mainene kikeyi haka zaki kwaso namun daji ki kawo gida, kallon shi tayi tare da cewa, Abbu kiwon su zanyi ai, kuma anan gidan, eh anan gidan naga gidan iyayen miji nane kuma mijina na zaune a gidan, dan haka anan zanyi kiwon su tunda *YAR DAJI* dansu ke aure,dole suyi rayuwa tare da namun daji a gidan nan.








Commets and shere fisabililahi.🌴🧘‍♀️ *YAR DAJI* 🧘‍♀️🌴
(WILD GIRL)


*STORY AND WRITTEN*
*BY FATEEMAH ALMUSTAPHA ADAM* (UMMON ABDALLAH🤱)

♧Pege♧36.

*****

"Haba Abrish taya mutane zasuyi rayuwa tare da namun daji a gida daya, cewar Abbu, to Abbu inma ba'a taba ba toyau a gidan nan za'a fara,"
Ammee inane daki na tunda yanxu nima na zama suroka agidan nan, da kyer Ammee tace, saide kiyi amfani da dakin Ashtar na part din shi, hakan ma yayi Ammee na , "baby love" um antyna, taso muje part dinmu, dan kasan yanxu ni dakai miji da mata ne, anty mai miji da mata kuma, au nafa manta kai yanxu yaro ne bakasan komai ba, tana gama fadan hakan ta kama hannun shi,har sunkai bakin kofa ta tsaya,

Mai magana, na'am uwar daki na, zauna anan duk maganan da akayi ka kwaso ka fada min, an gama uwar daki na, damisa kaikuma ka tsaya anan kayi masu gadi ko wani abu zaizo dan cutar dasu, in kina wa allah da annabi kiyi hakuri ki tafi da abun ki,wani kalan tsaro zai bamu wannan ai saide shi ya cutar damu,bade ya bamu tsaro ba, yanxu hajja tsaron ne bakwaso, eh wllh jaiki da abun ki bama so, ok ku biyo ni muje, kaikuma mai magana ka tsaya anan, tana gama fadan haka ta fice a part din rike da hannun Ashtar,
Ajiyar zuciya duk aka sauke, wannan bala'i har ina fisabililahi ace yarinya ta adabi kowa agida, fadin hajiya falmata, tabo ta Afrah ta dunga yi tare da kifta mata ido tana nuna mata akun da aka bari wajen, sai yanxu ta tuna dama wani aku awajen da sauri tasa kanta tsakanin cinyoyin ta ta buye waidan kada yama gane fuskar ta balle ya nuna ta,


"Oya wuce bathroom kayi wanka, nifa ke zakiyi min anty dan ban iya ba, mai kace ni zanma wanka ashe kuwa yau zaka shekara bakayi wanka ba, zaka wuce kosai na mare ka, ni allah ke zaki yimin, sai mugani ai, tana gama fadin haka ta wuce bathroom dan tayi wanka ta,tun da shi bashi da niyan yi, cire kayan ta tayi tafara wanka, daga bayanta taji mutum, wani joyawa tayi tare da zaro idano waje, ganin Ashtar daga shi sai gajeren wando,
Kai maikazo yi acikin nan bance ma tun farko ka fara wanka ba sai yanxo zaka wani biyo ni a baya, fita nace, shi Ashtar ma baisan tana yiba dan hankalin shi nakan brest din ta, saide taji yace laa anty ji balan balan a kirjin ki, kallon kanta tayi saikuma ta dago tare da kallon shi, dagewa tayi iya karfinta ta sake ihu tare dayin waje da gudu ta fita a bathroom din, dan kwata kwata ta manta babu komai a jikinta shiyasa ta tsaya yimai tijara ashe shi yananan yana kalleta bata sani ba,
Shima ganin ta fita da gudu yasa yabi bayan ta da gudun, dan yayi tunanin abune ya biyo ta shiyasa shima ya fita yana ihu, ko daya fita bai isketa a dakin ba dan haka sai yayi waje da gudu daga shi sai gajaren wando, itako Abrish karshe dakin Nafeesat tashige takarasa wankata, sai jamai allah ya isa take akan ganin ta da yayi ba kaya, ita wllh ta tsani wannan mutumin bata sonshi ko kadan,

"Hajja ce tanufi hanyar waje dan tafiya part dinta ko ta wanke zawon dake jikin ta, in banda allah ya isa ba abun da take fada aranta, dan babu halin yin magana a fili tunda an aje masu mai daukan rahoto,tun dazon suke zaune shiru saikace anyi masu mutuwa,
Hartazo ta kofar da zata fita a part din Ammee taja burki sakamakon ganin zakin da tayi yana wangale mata baki, ta dayan bangaren kuma macizai ne sai daga kawuna suke, ashe da Abrish zata wuce nan waje ta barsu akofar fita part din Ammee,
A hankali hajja ta fara ja baya, suma namun dajin suna binta a hankali, duk yadda hajja taso daurewa kasawa tayi,da gudun gaske ta joya hanyar komawa cikin gidan zawo na zuba ajikinta harda fitsari,ga hawaye shabe shabe a fuskar ta, suma namun dajin ganin haka da sukayi sai suka rofa mata baya da gudu,
Kusan tare suka shiga falon da namun dajin, ai mutanen falon na ganin haka suma suka fara naiman hanyar tsira, kowa da inda yake shige wa, falon duk ya hargitse da ihun mutane, hajja dai na gaife akwance ta some, hajiya saratu saboda rudewa da cikin ta yayi ame ta farayi babu tsayawa,
Masu gadi na waje babu halin shigowa saboda suma tsoron suke ji, ana cikin haka saiga Ashtar ya shigo tinbar dashi in banda gajeren wando nan babu komai a jikin shi, ganin yadda namun dajin kebin yan gidan suna gudo da ihu ga hawaye a idon su, sai hakan ya bashi dariya ya dunga yi babu tsayawa harda faduwa akasa.








Commets and
Shere fisabililahi.

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment