You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 1 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Duhu ne mamaye da illahirin dakin ta ko'ina ta yadda ko tafin hannuwanta ba ta iya gani ballantana gefe da gefenta ko kuma tazarar dake a tsakaninta da bangon ginin dakin ko ta samu ta isa gareshi ta jingina bayanta da shi watakila ta yi dace ta samu sassauci da saukin azabar yunwa da ke nukurkusarta a cikin ciki.

"Ta kasa gaba ta kasa baya, tana a inda take a zaune shurum a cikin duhuwar dakin wanda tunda ta Wora kafafunta a cikinsa take ganin masifa da tashin hankali, ta dafe cikinta tare da Sata fuska, ji ta ke kamar ana luguden wuta a cikin cikinta tsabar yunwa da ke dawainiya da ita, rabonta da abinci tun gayen tuwon da suka wurgo mata jiya da dare wanda ko loma biyar cikakka ba ta yi ba ya ™are."

Tana durkushe a waje Waya hannuwanta dafe da cikinta tana rawar sanyi kamar wacce aka yi wa wanka da kankara a lokacin hunturu.

"Ta mi™e zaune tana rarrafe da lalube har ta ™arasa jikin bangon ginin, ta jingina da shi tana sakin lumfashi cike da wahala da rashin kuzari sai dai ta yi rashin sa'a babu wani abu da hakan ya rage mata na yunwa da wahala da ke addabarta, ta dafe cikinta yunwa tana ragargazarta, tunda suka jefota a dakin sau ukku suka kawo mata abinci; gayen tuwon jiya, sai kosai guda hudu da suka wurgo mata shekaran jiya da safe sai kuma da marece da aka dungure mata shinkafar da ko mai babu ballantana a yi maganar yaji."

Ta sani har da gayya ya saka suke azabtar da ita da yunwa saboda ta hanasu lambar danginta ita kuma ta yi al™awari idan har sai an basu kuWin fansa za su saketa to kuwa ta gwammace mutuwarta da rayuwa domin basu kuWin fansa da ake yi ne ya saka su ke yi.

"Abun takaici da haushi satar mutane ya zama ruwan dare a wannan zamanin da muke ciki, sai ka ji an sace waccen a can, sai ka ji an dauke wannan a can, abun babu daWin ji ko gani, sai ka ji ana cinikin kuWin fansar mutum kamar ana cinikin tumaturi da tattasai, abun kamar almara."

"Babban abun takaici shine kasancewar da na kusa damu ake haWa kai ana yi mamu Wauki Waya-Waya, idan ba haka ba shin ta ina za su samu labarinta ita da ko fita ba damunta ya yi ba koda yake ita nata lamarin ba sharrin informer bane ba, akan hanya masu garkuwa da mutanen suka yi gam da ita shiyasa ko lambar gidansu basu dashi ita kuma ta yi ™iri da muzu ta hanasu lambar wayar duk da azabar yunwa da zaneta da suke yi duk safiya."

"Ta fashe da kuka saboda wahala da ta sha ko sautin kukan ba ya fita, ""Wayyo ni Jidderh... Yaa Imran, Ammi, Abbi, Islam... Kuna ina? Ku zo ku kawo min agaji! Ku zo ku ceceni a wannan halin da nike a ciki a hannun waWannan azzaluman."" Ta kwanta a kan daSen dakin mai sanyi tana mai fitar da lumfashi cike da wahala, fatar cikinta ta la™ume ta yi ™asa tamkar za ta haWe da kashin bayanta."

"Babu zato babu tsammani dakin ya gauraye da haske, wani radadi ya ziyarci idanunta na wannan hasken da ya mamaye mata idanu a lokacin da ganinta ya saba da wanzuwarsa a duhu, ta rufe idanunta da sauri tare da sakin ™aramin ihu tana mai juyar da kanta hannunta a daidai fuskarta domin yi wa idanunta kariya daga hasken da ya yi masu yawa har ya saka tana jin radadi a cikinsu."

"A lokaci guda ta ji jiri yana kwasarta ganin dakin a bayyane da kuma yadda ko'ina ya gauraye da haske mai karfin gaske. Bayan Wan lokaci idanunta sun samu nasarar sabawa da hasken ta Waga kai tana kallon gabanta, wata rikitacciyar zabura ta yi ganin mutum zaune a kan kujera, ba ta san lokacin da ya shigo ba, ba ta ji alamun shigowarsa ba shiyasa ganin nasa ya zo mata a bazata, bugu da ™ari yadda ya rufe fuskarsa da takunkumi ta yadda idanunsa kawai take iya gani."

"Ta haWe hannayenta a waje guda alamar roko tana zubar da hawaye ta ce, ""Please ku mayar da ni wajen ahalina, ku ji tsoron Allah, wannan abun da ku ke yi zalunci ne."""

"Mutumin ya gyaWa kai ya ce, ""To shikenan babu damuwa ki bamu lambarsu sai mu faWa masu inda zamu ajiye ki."""

"A rikice take amma rikicewar bai kai yadda zai yi mata dubara har haka ba, yana gama maganar ta gane inda ya dosa, ta ji a ranta cewa yana sone ta bashi lambar ne da manufar su kira su nemi kuWin fansa."

"""Nawa zaku tambaya kuWin fansata?"" Ta tambaya a lokaci guda tana karantar yanayin mutumin ne wanda yake dogo kakkarfa."

"Kanshi tsaye ya ce, ""Million Wari biyu domin koda ganinki ba ki yi kalar yayan talakawa ba."""

"Ba ta san lokacin da dariyar takaici ta kwace mata ba, million Wari biyu, ko danginsu baki Waya ba za su yi wannan kuWin ba don haka ba za ta bayar da lambar ba, ba za ta ™arawa Abbi zafi akan wanda yake a ciki ba, ita shaida ce tunda ya shigo Nigeria hankalinsa bai kwanta ba don haka ba za ta ™ara mashi da tashin hankalin tattara kuWin da ba zai iya haWawa ba."

"Ta fashe da dariya tana faWin, ""Ka da ka wahalar da kanka, wannan Jiddar dake a gabanka ´ar koko da kosai ce kalar yayan masu kuWi ne kawai gareni amma ubana mahaifi talaka ne fukut, abun da zamu sakawa kofar salati wahala yake mamu."""

"Ya kafeta da idanu ya ce, ""Ahh haba, to su kuma kayan masu tsaWa da kike sanye da su fa."" Ta ce, ""Gidan da mamarmu take wanke-wanke aka bani su kwance."""

"Ya fashe da dariya ya ce, ""˜arya kike ko mahaifinki bai kai kudin da muke zato ba amma ba daga gidan tuwo kike"

"ba."" Ya daka mata tsawa ya ce, ""Ki bamu lambar iyayen ki mu faWa masu kuWin fansarki."""

"Ta shiga girgiza kanta kamar kadangaruwa tana faWin, ""A'a ba zan ba ku lambar kowa ba, saidai ku kasheni."""

"Ya jinjina kai ya ce, ""Da alama baki ladabtu ba ne amma ina da tabbaci abun da zai zo maki a nan gaba zai tilasta maki bamu lambar ta yadda ke da kanki za ki rin™a kuka kina mamu magiya domin mu amshi lambar mu kirasu ko sun biya kuWin fansar ki huta da wahalar da za ki gani."""

"Ya mi™e yana takowa inda take, yadda idanunsa suke yawo a kirjinta ya saka gabanta faWuwa, ta dunkule a waje Waya tana rawar sanyi, ya kama hannuwanta ya mayar baya yana mai tura kanshi a gefen wuyanta yana sakin wani shegen gurnani."

"Ta yi iyakar ™o™arinta amma ta kasa kwacewa daga rikon da ya yi mata, tana kuka tana karanta dukkanin wata addu'a da ta zo mata a kai a daidai wannan lokacin da ake ™o™arin keta mata haddi a mafi koluluwar zalunci."

"A daidai lokacin ne kuma wani abun mamaki ya faru domin ya yi iyakar ™o™arinsa amma abarsa taki tashi har fiddota ya yi yana kaWawa amma taki tashi, a fusace ya mi™e daga kusa da ita ya wurgar da ita gefe ya fice ransa a Sace."

"Ta sauke ajiyar zuciya tana mai faWin, ""Alhamdulillahi, Allah Kaine abun godiya, Allah na gode maka akan wannan agaji da Ka kawo min."""

*******

"A hankali suke fitowa daga katafaren shopping mall din yana ri™e da hannunta yana ba ta labari yana murmushi sai dai hankalinta sam ba ya a kansa yana akan majigin waya kirar samsung fold da ke a Waya hannunta, lura da ya yi da hakan sai ya amshi wayar yana mai faWin, ""Rumana miye kike kallo ina maki magana hankalinki ba ya a kaina?"""

"Ta mi™a hannu da nufin ta amshi wayar, ya mayar da ita bayansa ya kafeta da idanu yana faWin, ""A faWa min abun da ake kallo a ciki."""

"Sai da ta murmusa sannan ta ce, ""Littafin mutuniyata nike karantawa marubuciya Aysher Angel."""

"Dafe kansa ya yi ya ce, ""Gosh! Na yi mantuwa ki jirani a mota babu jimawa zan dawo."" Ta gyaWa kanta ta ce, ""Alright."""

"Ta mi™a hannu da nufin ya ba ta wayarta, ya lakuci hancinta yayi mata gwalo ya juya ya nufi hanyar komawa cikin"

katafaren shopping mall din ba tareda ya bata wayar ba.

"Ta Waga kafafu a nutse ta nufi wajen ajiye motoci, fara ce sosai har yellow fatarta ta ke yi saboda haske, tana sanye da leshe dinkin umbrella gown ta yane kanta da kallabi ta yi mashi daurin da ya matu™ar yi mata kyau, mayafinta a kan kafaWa, ta zuba sarkokin gold wuya da hannu."

"Ta juya tana kallon bayanshi da murmushi kwance kan fuskarta, tunda mahaifinsu ya rasu yaya Junaid bai bari ta yi kukan rashi ba, ya maye mata gurbin mahaifinsu, wasu hidindimun da yake mata ko a zamanin Abba bata samu hakan ba, da ace haka yayye maza su ke yi wa ™annansu bayan rashin mahaifi da kuwa zai rage masu wani kaso na raWaWin rashin."

******

"""Imran ka rage sakawa kanka damuwa In sha Allah za'a samu Jidderh a cikin koshin lafiya,"" Ahmad ya faWa yayinda ya ke jan motar akan titin mai cikowar ababen hawa."

"Wanda aka kira da Imran ya juyo ya dubi abokin nasa, fuskarsa dauke da tsantsar damuwa ya ce, ""Ahmad dole ka ganni a cikin damuwa, kwanaki ukku kenan babu Jidderh babu labarinta, Satan Wiya mace budurwa a wannan zamanin ba ™aramin tashin hankali ba ne ba musamman ga iyayenta da ´an uwanta, mu dai fatanmu shine Allah ya tsare mata mutuncinta, ya kareta, ya dawo mamu da ita a cikin koshin lafiya."""

"Ahmad ya amsa da, ""Amin."""

"Imran ya ce, ""Dole kake ganina a cikin damuwa, tunda abun nan ya faru kullum Ammi a cikin kuka take, Abbi kansa daurewa kawai ya ke yi amma kallo Waya za ka yi mashi ka fahimci yana a cikin matsanancin tashin hankali da ruWani. In takaice maka zance babu wanda hankalinsa yake kwance a cikin gidanmu,"" yana maganar ne yayinda a lokaci guda idanunsa suke kallon waje yana ™urewa mutanen da suke wucewa kallo yana fatan ganin Jidderh."

"A daidai lokacin da suka shawo corner idanuwansa suka sauka a kanta, sai da bugun zuciyarsa ya tsaya na wani lokaci. Ya kalleta ya ™ara kallonta, har muntsular jikinsa ya yi domin tabbatar da abun da idanunsa suke gane masa, tabbas ita ce, Jidderh ce, ya tsaya cak daga maganar da ya ke a sanadin hango Rumana da ya yi."

"""Jidderh!!!!"" ya ambata da saurinsa."

"Ahmad ya kalli inda yake kallo, ya ce, ""Wallahi ita ce."" Ya gangara da motar ya yi parking a gefen titi, ko parking din kirki baiyi ba Imran ya Salle murfin motar ya nufi inda take da saurinsa yana tafiya gudu-gudu, ya rungumeta yana mai sauke ajiyar zuciya, ya ce, ""Jidderh! Alhamdulillah mun sameki, Allah shine abun godiya."""

"A daidai wannan lokacin fushi, haushi da takaici suka cika zuciyar Rumana, shin da miye wannan makaskantancin"

yake ta™ama da da har zai rungumeta?

"A fusace ta tureshi tana mashi kallon kaskanci ta ce, ""Kai Malam wannan wani irin iskanci ne da rashin mutunci, baka da kunya ne kai ko kuma iskanci ne ya yi maka yawan da baka tantance mutane."""

"Imran bai damu da furucinta a kansa ba murnar ganinta ya cika mashi zuciya, ya kama hannunta yana faWin, ""Jidderh!"""

"Rumana ta zagba mashi harara da takaici akan fuskarta, ta fizge hannunta ta ce, ""Ba Jidderh ba ce, wannan Rumana ce."""

"Kansa ya shiga girgizawa yana faWin, ""Jidderh ba na wasa da ke, wuce mu je gida."" Ya ™arasa maganar da kakkausar"

murya.

"Ya Wora da faWin, ""Iyayenmu sun damu, Ammi da Abbi suna cikin matu™ar tashin hankalin Sacewarki."""

"Cikin ranta ta ce, ""Ikon Allah."" Amma a zahiri murtuke fuska ta yi ta ce, ""Na faWa maka ni ba sunana Jidderh ba sannan kuma ban sanka ba don haka ka wuce ka bani waje tun kafin in tara maka jama'a inyi maka terere."""

"Har ta fara nadamar sakawa da ta yi sukayi ghosting masu basu tsaro suka fito su kaWai, da ace sun fito da matakan tsaronsu da wannan Wan talakawan bai isa ko kusa da motarta ya matso ba ballantana kuma har ya samu damar taSa mata jiki."

"Tsawa ya yi mata a karo farko, ""Jidderh!!!"" Ya furta sunan da karfi cikin tsawa."

"Ta yi baya da sauri, a rayuwarta bata son tsawa ko kaWan, bata tashi gidan ake yi mata tsawa ba, zuwa wannan lokacin abun ya fara ba ta tsoro, ta juya tana fatan hango Junaid saidai inaa babu shi babu alamarsa."

"Muryarta tana rawa ta ce, ""Malam ban sanka ba, ban taSa ganinka ba, sunan da kake kirana da shi ba sunana ba ne ba. My name is Rumana, I'm not Jidderh."""

"Bai saurareta ba domin ya gama yarda da cewa watakila wani abun sukayi mata wanda ya rikita mata lissafin kai: shin idan ba haka ba ta ya Jidderh za ta kasa ganeshi? Ya kama hannunta saying, ""Jidderh shin wani abun ne ya samu kanki da har kika gagara tunawa da yayanki Imran? Ki zo mu je gida, iyayenmu suna cikin tashin hankali da damuwa. Jidderh tun bayan Satanki ahalinmu suke a cikin tashin hankali. Ammi tana ta kuka, Abbi ya kasa samun sukuni."""

"Ta fusata da ri™e mata hannun da ya yi, ta fizge hannunta tare da wanka mashi mari tana mashi kallon kaskanci da raini ta ce, ""Kana hauka ne!? Is this some sort of prank!? Na faWa maka na maimaita cewa sunana ba Jidderh ba, sunana Rumana, kuma ban sanka ba."""

"Imran ya dafe kuncinsa yana kallonta da mamaki, Ahmad kuwa zaro idanu ya yi waje, lallai abun babba ne Jidderh wacce ko kallon cikin idanun mutum batayi idan tana magana amma yau itace ta shararawa yayanta Imran mari."

"Rumana ta juya inda Ahmad yake ta ce, ""Kai Malam ka kama abokinka ka wuce dashi tun kafin in saka mutane su yi mashi Wan banzan duka akan iskancin da yake nunawa a kaina."""

"Saidai shima abun da ya faWa babu abun da ya ™ara mata sai takaici domin buWar bakinsa sai cewa ya yi, ""Jidderh ka da ki yi haka."""

"Ta rasa bakin magana, ta taSa hannuwa tana dariyar rainin wayo sai abun yake mata kamar wasan kwaikwayo ko kuma ta kirashi da almara, tana ganin rayuwa a wajen nan, ta ce, ""Ikon Allah sai kallo, ni Rumana ina ganin rayuwa a wajen nan, da alama dukkaninku ne kuka samu damuwa a kawunanku."""

"Imran ya daka mata tsawa a karo na biyu, ""Jidderh!!!!"" Ba tare da ya ™ara furta komai ba ya ja hannunta yana nufar"

motar da suka ajiye a gefen titi.

"Ta yi iyakar ™o™arinta amma ta kasa kwace hannunta daga lafiyayyen rikon da ya yi mata, ta zaro idanu yayinda gabanta ya yanke ya faWi: Miye yake shirin faruwa da ita? Tana jin labarin satar mutane da ake yi, ka da abun ne ya zo kanta, kada dai cinne aka yi mata tun daga Kaduna aka biyota Katsina aka yi ram da ita."

"Ta fasa ihu da dukkanin karfinta tana faWin, ""Ka sake ni."" Tana ™o™arin cire hannunsa daga rikon da ya yi mata sai"

dai ba rikon wasa ya yi mata ba bugu da kari karfin ba Waya ba.

"Imran ya dubeta da damuwa ya ce, ""Jidderh ba cutar da ke zan yi ba, gida zan kaiki wajen iyayenmu."""

"Ji ta yi ranta ya Saci ta daka mashi tsawa ta ce, ""Ka sakeni ko kuma in tara maka mutane, in yi maka ihun Sarawo, masu satar mutane kawai."" Gani ta yi ya ci ga ba da tafiya kamar bai ji abun da ta faWa ba."

"Ganin da gaske yake ta ta ta™ar™are ta fasa ihu da dukkanin muryarta hakan ne ya janyo hankalin mutane zuwa garesu, mutane suka taru a kansu, ganin haka ta fashe da kuka tana faWa masu abun da ya faru, ""Ban sanshi ba ya zo yana kirana da Jidderh yana wasu maganganu this and that..."" Imran ya katseta, ""Karya take, ™anwata ce, yau kwana ukku kenan rabonta da gida an nemeta an rasa."""

"Ta rasa bakin magana ganin yadda a gabanta ake mata ™arya da haWin tuggu da kitumurmura, yaushe ta haWa jini da shi da har hakan ya faru, ita kuwa miye zai saka ta haWa jini da wannan talakan, babban abun bakin cikin da takaicin shine da iyakar gaskiyarsa yake furta abun da ta san cewa ™arya ce zallarta."

"Bata ™are wannan tunanin ba muryar wani dattijo ta doki dodon kunnenta yana faWin, ""Ba sai ka rantse ba, dukkanin wanda ya kalleka ya kalleta zai tabbatar da cewa jininka ce."" Wani saurayi da ke kusa da shi ya ce, ""Haka ne, tabbas."""

"Ta fasa ihu tana faWin, ""Na faWa maku ba ni ba ce, ban sanshi ba. Wani haukan ne ya sameku da har zaku dangantani da wannan talakan marar galihu: Mi yasa ku ke yi min haka? Ko kuma kun haWa baki ne kuka shirya tuggu da makirci domin cutar da ni, torh ko miye wasanku ina mai bakin sanar daku cewa babu nasara a nan domin ha™arku ba za ta cimma ruwa,"" ta yi nuni wa Imran ta ce, ""Da ni da wannan ba mu da ala™a ta kusa ko ta nesa, ta ina ma zan yi dangantaka da wannan talakan makaskanci, ku dubeshi ku dubeni, suturar jikinmu kanta ta nuna banbancin."""

"Wani mutum ya ce, ""Ke yarinya ki bi duniya a sannu, ki bi yayanki ku wuce, kai yaro ka kamata ku je gida."""

"Ji ta ke yi kamar ta fasa ™ara, ""Na ce maku ba yayana ba ne ba, ban sanshi ba."" Mutumin ya ce, ""Rayuwa kenan,"

"Allah ya shirya mamu zuri'a."""

"Ganin abun da gaske ne, ta goya hannuwa a kirji, da gadara ta ce, ""Babu inda zan je."" Ahmad ya ce, ""Don Allah ku"

"taimaka mamu, wallahi ™anwarshi ce."""

"Kanta ta dafe cike da haushi da takaici ganin babu wanda ya fahimceta a cikin mutanen, bugu da kari hotuna da Imran yake nuna masu, ta rasa abun cewa."

Karfi da ya ji Imran yake neman daurata a kafaWa tana gardama tana dukansa da dukkanin karfinta saidai inaa ko gizau bai yi ba.

"Ganin suna neman su yi mata daukar kayan wanki zuwa cikin motar ya saka ta tsaya da gadamar da ta ke yi ta ce, ""A'a ku tsaya, ku dakata, ™arya dai fure take bata ´a´a ni kuma nasan ™arya ka ke yi amma mu je gidan naku, idan su mutanen gidan suka duba suka ga ba ita bace dolensu su saka ka maido dani domin idan kai kanka ba ya da seti, to ina fatan su ya kasance kansu garas yake ba ya motsi, ta yadda za su banbance a tsakanin aya da zakuwa, su kuma saka ka maidoni tunda na tabbata sunana ba Jidderh bane, Sunana Rumana sannan kuma ban sanka ba."""

"Ya kama hannunta ta fizge tana mashi kallon kaskanci ta ce, ""Ko a mafarkinka ka da ka ™ara Waura wannan kazamin hannun a jikina, ban da hauka da rashin hankali har ka dubeni ´ar huta wacce ta tashi cikin daula da arziki ka ce min ™anwarka, miye ya haWa keke da jirgin sama, hanya ko ta kobon sisi bamu haWa ba amma muje mu samu su mutanen gidan naku su saka ka maido da ni."""

"Ya yi gaba ta bi bayanshi, Ahmad yana biye da su, Imran ya buWe mata gidan baya ta shiga yayinda shi da Ahmad suka zauna a gaba, tana ji Imran yana kiran waya yana sanar da cewa ya ga Jidderh yana ta farin ciki da murmushi, ta buga tsaki ta ce, ""Aikin banza aikin wofi, sai wannan murna ta koma ciki domin wannan ba Jidderh bace, Rumana ce."""

"Daga Imran har Ahmad babu wanda ya tankata duk da sun ji abun da ta furta sarai, suna mata uzuri akan watakila wani abun ne ya faru da ita wanda ya sakata mantawa da komai."

"A bakin wani madaidaicin gida suka tsaya ya shigar da motar ciki bayan da ya yi horn mai guard ya wangame mashi get, duk da gidan yana da girma amma ita kallon akurkin tsuntsaye ta ke yi mashi duba da inda ta fito, tazarar da ke tsakanin gidan su da wannan gidan tazara ce mai girman gaske, basu ma haWuwa."

"Imran ya juyo da murmushi akan fuskarsa ya ce, ""Welcome home."" Ta murtuke fuskarta tana mashi kallon kaskanci ta ce, ""Na faWa maka sunana ba Jidderh ba ne,"" takaici ya zo mata wuya ta daka mashi da tsawa ta ce, ""Don't you dare call me with that name again. Damn it, wannan abu da mi ya yi kama, ina faWa maka gaskiya amma ka rumtse idanu kana bin ™arya da son zuciyarka domin ka wahalar da ni, wai mi yasa wasu mutanen suke da matsala ne, ga gaskiya kiri-kiri ana gani amma saboda son zuciya da neman suna sai a goyawa ™arya baya domin a nemi suna,"" Ta ™arasa maganar da ™araji amma sai ya yi kamar bai ji ba."

"Ahmad da ya gama waya ya ce, ""Hajiyarmu ta kira."" Imran ya Salle murfin motar ya fito yana faWin, ""Ka gaida min da ita."" Ahmad ya ce, ""Za ta ji. Jidderh sai na shigo ko?"""

"Rumana bata san lokacin da ta daka mashi tsawa ba ta ce, ""Kada ka ™ara kirana da sunan da ba sunana ba, damn it."""

"Ya murmusa ya ce, ""Jidderh yau ni ake yi wa tsiwa koda yake babu komai idan na dawo zan tambayi ba'asi kuma sai kin amshi kaye."""

"Wannan furucin da ya yi ya matu™ar Sata mata rai musamman cewa da ya yi zata amshi kaye, ta murtu™e fuska ta ce, ""Careful Wan talakawa, you are praying a dangerous game. Kai da kanka ka san cewa kirana da ka yi da suna Jidderh ™arya ka ke yi. Wacece Jidderh? Sunana Rumana, kuma a yanzu ba anjima

Please Login or Register in order to submit comment