You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka sani ina faWa maka da babbar murya idan har aka samu damuwa ka kuka da kanka domin ba zan yi maka da sauki ba. Junaid idan wani abu faru da ita ka yi kuka da kanka, Junaid idan aka samu damuwa za ka ga Sacin raina, kuma a lokacin ne za ka tabbatar da baka taSa ganin Sacin raina na gaske da gaske ba."""

"Jikinsa ne ya yi sanyi ya ce, ""A'a Umma tunda baki so a bar maganar."" Umma ta Wan kalleta ta ce, ""Sai ka je ka faWa"

"mata hakan."" Har ya mi™e ya nufi waje sai kuma ya dawo da baya ya ce, ""Zan je da ita."""

"Ta jinjina kai ba tareda tace kanzil ba, a sanyaye ya haye sama maganganunta suna damunsa, Anya kuwa sunyi mata adalci? Babu abun da ta ragesu da shi a rayuwa, sai yake ji abun da su ka yi mata basu kyauta ba, a haka Rumana ta sameshi tana tsallen murna ta ce, ""Umma ta ce ta barni mu je Katsina tare."""

"Ya yi murmushi wanda iyakarsa a kan labbansa ne kawai, ya ce, ""Na tayaki murna, mu je mu ci abinci."""

"Sai da suka sauko sai kuma ya ji kunyar Umma ta kamashi sun ce sun koshi amma bayan ta yi masu abun da suke so sun sauko su ci, maganarta ta fito kenan akan bore su ka yi wa abincinta."

"Umma ta dubesu kamar ba za ta yi maganar ba sai kuma ta ce, ""Kuka ce kun koshi."" Rumana ta yi karaf ta ce, ""Saboda kin ce ban zuwa katsina na yi fushi da abincin shima yaya Junaid na hanashi ya ci."""

"Ji Junaid ya yi kamar ™asa ta tsage ya shige jiki saboda kunya, ya kasa Waga idanu ya kalli Umma, yana zaune shurum kamar wanda ruwa ya ci."

"Umma ta dubeshi ta girgiza kai kawai ta ce, ""Mutane sun yi gaskiya da suka ce na sangartaku da yawa tunda ga shi a yau na zama diyar ku kuma uwayen."" Ta mike tabar wajen ranta a Sace."

"Junaid ya mike yabi bayanta yayinda Rumana take zaune tana kwasar gasar girki abunta, ya biye mata ta barshi da kunya."

"Ya samu dakin Umma a kulle, ya kwankwasa ta yi mashi banza har ya gaji ya juya ya koma parlour."

"Rumana ta yi digging abinci ta kai bakinsa ya amsa yana mata murmushi, ta ce, ""Ina ka je?"" Ya ce, ""Umma na je in ba hakuri."" Kanta tsaye ta ce, ""Ka rabu da ita, anjima za ka ga ta dawo tana shiri da mu, tana kaunarmu bata iya fushi da mu."""

"Har washegari da suka tashi tafiya daga Rumana har Junaid babu wanda yaga fara'ar Umma, har Rumana sai da tasha jinin jikinta kamar za ta yi kuka ta ce, ""Yaa Junaid tun jiya Umma bata yi mamu fara'a ba, tunda ta tashi yau bata yi murmushi ba, mu je mu bata ha™uri."" Ya ce, ""Ki bari idan muka dawo sai mu bata ha™urin."" Ta fashe da kuka ya yi rarrashi har gaji amma taki matsawa ta shiga mota har sai sun je sun ba Umma hakuri, dakyar ya rarrasheta ta hakura suka tafi."

"Suka dauki hanyar garin Katsina, a jirginsa ya yi nufin tafiya amma Rumana ta matsa a kan su tafi a mota tana mararin doguwar tafiya a mota (Ni MATAR ALIYU I was like samun gari, dadi ne ya yi wa Rumana yawa)."

"Ko da Umma taji labari a wajen shugaban masu bashi tsaro bata ce komai ba, ta dai ce su kula mata da yara."

"Mota ce sabuwa dal mai tsadar gaske, Junaid ne yake jan motar yayinda take zaune a bangaren mai zama hakanan tana kallon hanya da garuruwa da suke wucewa tana murmushi wannan shine karon farko da ta yi doguwar tafiya a mota."

"Motoci ukku ne sukayi masu convoy idan aka haWa da motarsu guda hudu kenan, motocin iri Waya ne sak ta yadda babu yadda za'ayi mutum ya iya tantance wacce suke ciki."

"Sun shigo cikin garin katsina a daidai wajen roundabout na liyafa, Junaid ya yi parking daidai wani katon shagon zamani ya ce, ""Didi Ina zuwa?"" Ta gyaWa kai, ya Salle murfin motar ya fita zuwa ciki."

"Ta fito ta jingina da motar tana kallon garin Katsina wanda wannan shine ™aro na farko da ta shigo cikinsa, wani saurayi ta hango ya zuba mata idanu ba ya ko kyaftawa, ta turo baki tana gyara mayafi da ke akan kafadarta, gani ta yi ya nufo inda take har Waya daga cikin security da suke tare zai dakatar da shi ta yi mashi alama akan ya barshi."

"Ta jinjinawa tsaurin idanun saurayin tana so ta ga iyakar tsaurin idonsa duba da yadda ya ke kallonta daga sama har kasa, ta kalli kanta tana sanye ne da tsadadden leshe dinkin umbrella gown, ta rufe kanta da kallabi sai dai jelar gashinta ya fito a waje yana reto a gadon bayanta, ta yafa mayafi a kan kafada yayinda kafafunta suke sanye da"

"takalma masu tsini, powder da kwalli ne kawai a fuskarta kasancewarta ba ma'abociyar chaba adon fuska ba, ta zuba gold wuya da hannu, tana zuba kamshi mai sanyi."

"Ta taSe baki tana kallonshi daga sama har kasa, chocolate ne Wan duma-duma mai saje yana sanye da brown kaftan, da hula dara a saman kanshi, kafafunsa rufe da takalma slippers, ya ™araso inda take yana kallonta da mamaki a kan fuskarsa ya ce, ""Jidderh! Jidderh!! Jidderh!!!"""

"Sai da ya kira sunan sau ukku sannan ta tamka, ""Jidderh kuma?"" Ta ce tana mashi kallon kaskanci."

"Ji ta yi ya ce, ""Jidderh mi kikeyi a nan? Garin ya kika saka wadannan kayan kika fito da su?"" Rumana ta girgiza kai tana wani shegen murmushi ta ce, ""Kai kuma salon da kake amfani da shi kana tsara (toasting) ´an mata kenan. Daga ganin mace mai kyau har ka zo ka yi badda kama kana kirana da suna Jidderh. To ina mai bakin cikin sanar da kai wasanka bai yi kyau ba a nan don haka ka ™ara gaba tun kafin in saka security dina ya yi maka daukar kayan wanki ya watsar a kwatamin kwatar can."""

"Da mamaki yake kallonta ya ce, ""Jidderh hankalinki Waya kuwa?"" Idanunta a tsaitsaye ta ce, ""Zaka ware ko kuma sai na saka anyi maka da yaren da zaka fi fahimta."" Ta ™arasa maganar tana yafito Waya daga cikin securityn ya ™araso, ta ce, ""Idan ya ™ara dakiku talatin bai Sace min daga gani ba, ka Waurashi a kafaWa ka watsar a kwatamin kwatar can."""

"Ya dubeta ya dubi katon da ta kira, juyawa ya yi ya koma wajen motarsa yana tafiya yana waiwayenta fuskarsa dauke da matu™ar mamaki akan abun da ya faru, idanunsa Jidderh suka gani muryarta da komai ita ce amma abun da ta yi mashi ba halinta ba ne ba."

"A daidai lokacin ne kuma Junaid ya iso ya kama hannunta ya ce, ""Mu je."" Ya buWe mata Waya bangaren mai zaman hakanan ta shiga sannan ya zagaya bangaren direba ya ja motar suka wuce, suka bar saurayin sake da baki, ya bi motar da kallo cike da matu™ar mamaki."

"Bai yi ™asa a gwuwa ba ya zaro wayarshi ya kira wata number ya yi jim sannan ya ce, ""Imran. Shin Jidderh tana gida?"" Daga Waya bangaren Imran ya ce, ""Eh tana gida."" Mamakinsa ya ™aru, ""Tana kusa da kai?"" Ya tambaya domin ya tabbatar da gaske tana nan."

"Imran ya ce, ""A'a ina balcony tana dakinta."" Ya ce, ""Ka je ka dubata."" Imran ya wuce dakin Jidderh ya sameta zaune"

a kan darduma tana karatun Al™ur'ani.

"Muryarta da ya jiyo a cikin kira'arta mai dadin saurare tana rera karatu a cikin Suratur Rahman ya tabbatar masa da ba ita bace wacce ya gani, kansa ya Waure shin idan ba ita bace to wacece ya gani domin kamannin sun yi yawa, tsayinsu, muryarsu, kamannin fuskarsu da komai iri Waya ne sak babu banbanci ko kaWan."

"""Uncle In bata wayar?"" Muryar Imran ta katse mashi tunani. Ya ce, ""A'a ka kyaleta."" Ya tsinke kiran yayinda mamaki ya bayyana ™arara a kan fuskarsa, ta tabbata wacce ya gani ba Jidderh bace. Amma tambayar ita ce tunda ba Jidderh bace, Shin wacece? Mi ya saka take matu™ar kamanni da Jidderh kamar kobo da kobo that har ya kasa banbancesu?"

"(Wannan kenan, mu koma ainihin labari)"

**********

KATSINA

"Rumana ta mi™e tsaye tana bin dakin da kallo, hoto dake a kan bedside table ne ya dauki hankalinta ta daukeshi tana kallo, da mamaki kwance akan fuskarta take kallon yarinyar dake cikin hoton ganin kamarsu Waya sak kamar kobo da kobo."

"Ta ajiyeshi ta dauki hoton da mutanen gidan baki Waya suke a ciki, matar da mijin ne, sai mai kama da ita sai kuma wannan ™aramar yarinyar da kuma wanda ya zo da ita, ta tsura masu idanu tana nazari, dukkanin yaran fuskar mahaifin suka biyo, suna kama da shi sak kamar kobo da kobo, ta ajiye hoton tana mai taSe baki tana mamakin yadda mutum zai iya kwana a wannan ™aramin dakin, katon bedroom ne amma ya fi mata kama da akurkin kaji idan aka haWa da dakinta da kuma gidan da ta fito, ta bude closet tana bin kayan da ke ciki da kallo, rabin kayan hijabs ne"

"sai dogayen riguna, atamfa, shadda, leshe, babu mayafi ko daya, ta taSe baki duk da tana kama da wacce take da dakin amma rayuwarsu ta bambamta."

"""She have weird taste,"" ta furta tana ™arewa kayan kallo."

*****

"Da misalin karfe bakwai na safe, Abbi, Ammi, Imran da Islam sun yi jigum-jigum a parlour, da™yar suka samu suka"

rufeta bayan da suka kai mata abincin safe ta yi masu haukan da ya fi wanda ta yi masu jiya.

Wannan saurayin da ya hadu da Rumana ne ya shigo falon da sallama a kan bakinsa.

"Islam ta ruga da gudu ta yi hugging kafafunsa tana faWin, ""Uncle Al'ameen, Jidderh bata gane mu ba, tana ta cewa ba sunanta Jidderh ba, wai sunanta Rumana."""

"Al'ameen ya dubesu ya ce, ""Mi take nufi da Jidderh bata ganeku ba, bata cikin hayyacinta ne ko kuma bugar mata kai sukayi ta rasa tunaninta na baya!?"""

"Imran ya ware hannuwa ya ce, ""Bamu sani ba, but she's acting weird, sai tana abu kamar ba ita ba, tana cewa ita ba Jidderh bace, that sunanta Rumana kuma kalamanta sunyi tsauri kamar wacce ba'a yi wankin bakin jarinta ba."""

"Islam ta ware idanu ta ce, ""Yaa Imran miye wankin bakin jarinta?"""

"Ya ware hannuwa ya ce, ""Nima ban sani ba."""

"""Tana ina!?"" Al'ameen ya tambaya."

"Imran ya nuna mashi matakalar bene ya ce, ""Tana dakinta."""

"Al'ameen ya ce, ""Okay bari in yi mata magana."" Ammi ta ce, ""Amma ka kula ka da garin yi mata magana ta ji maka ciwo."" Ya jinjina kai ya ce, ""Babu damuwa."""

"Ya nufi matakalar bene, ya zare makulli da ke akan kofar ya shiga, Rumana ta mi™e ba tare da ta kalli wanda ya shigo ba ta ce, ""Tun muna shaida juna ku mayar da ni inda kuka daukoni, na faWa maku ni ba Jidderh bace, sunana Rumana."" Maganar ta tsaya cak a sanadin tozali da ta yi da wanda ya shigo dakin ta nunashi da hannu ta ce, ""Kai!."""

"Al'ameen ya tsara tsayuwa ya ce, ""Ni ne da kaina ´ar gadara, abu ya yi kyau, na ce yanzu ina katon da kika ce ya"

"daukeni a kafaWa ya jefar a kwatamin kwata."""

"Ta ware idanu ta ce, ""Ohhh dama kaine ka saka suka satoni?"" Ya girgiza kai ya ce, ""A'a ko Waya bani bane na saka suka daukoki ba, saidai wacce kike kama da ita mamarta cousin dita ce, a ranar da na ganki kin yi min kama da ita ne shiyasa na yi maki magana amma sai kika zaSi kiyi min rashin kunya. Yanzu wa gari ya waya?"""

"She was like, ""Kana hauka ne?"" Ya maida kofa ya rufe ya ce, ""Kuma fa da gaskiyarki ina ganin kamar na ci kai,"" ya yi wani shegen murmushi ya ce, ""Ya ake ciki ´an mata? Idan kin bani izini ina so in tsaraki kamar yadda saurayi yake idan ya ga budurwa yana so."""

"Rumana ta ware idanu, ta rasa bakin magana, ji take kamar ta rufeshi da duka, ji take kamar ta cigaba da kwallo da shi a wajen. Ta taSe baki ta ce, ""Koma miye mun hadu da kai tun kafin Wiyarsu ta Sace, Jidderh take ko wa, koma miye sunanta ban damu ba, ka je ka faWa masu komai su kyaleni in tafi."""

"Duk da ya fahimci inda maganarta ta dosa amma saboda ya kular da ita sai ya ce, ""Ban gane ba."""

"Ganin yana nema ya Sata mata lokaci ta fasa ihu ta ce, ""Suna zaton ni ce diyarsu Jidderh kuma ni da kai mun san ni ba Jidderh ba ce don haka ka je ka faWa masu gaskiya tun kafin laifin saceni ya rataya a kanku."""

"Dariya ta bashi sai da ya dara sannan ya ce, ""Na san ke ba Jidderh ba ce sai dai su basu sani ba, tambayar ita ce shin waye zai faWa masu su yarda, ke ko kuma ni."""

"Ta buga tsaki ta ce, ""Malam kana taSa min lokaci ka je ka faWa masu tun kafin na fusata raina ya Saci."""

"Al'ameen ya jinjinawa tsaurin idanunta, ya goya hannuwa a kirji ya ce, ""Huh... Umarni kike bani?"" Ta ce, ""Eh umarni nike maka kuma dole kayi, ni Didi walki ce daidai kugun uban kowa."" Ya ce, ""To shikenan,"" ya zauna a kan kujera ya daura kafa Waya a kan Waya yana mai murtuke fuska ya ce, ""Ki yi min dole."""

"Ta dafe kai ji take kamar ta fasa ihu, kamar za ta yi kuka ta ce, ""Yaa Junaid da Umma suna cikin tashin hankalin"

"Satana, ka je ka sanar dasu ni ba Jidderh bace, ko sun barni in koma wajen dangina."""

"Ya gyara zama ya ce, ""Saboda mi zan yi haka bayan rashin kunya da ki ka yi min a waccen ranar da kuma tsaurin idanu da kika nuna min a yau. Tambaya nike, saboda mi zan yi haka."""

"Kanta tsaye ta ce, ""Saboda shine gaskiya shiyasa za ka je ka faWa masu."" Ji ta yi ya ce, ""Idan na ki fa?"" Da mamaki ta ce, ""Ban gane ba?"""

"Al'ameen ya ce, ""Ranar da muka hadu kika min rashin kunya sannan yau kuma kina ba ni umarni, kina da abun mamaki ´an mata. Idan kina son in faWa masu gaskiya to ki rokeni, ki durkusa a kan gwuwowinki ki bani hakuri a kan rashin kunya da kika yi min, a lokacin ne zan yi tunani in gani idan zan iya faWa masu gaskiyar."""

"Rumana ta saka dariya tana taSa hannuwa ta ce, ""Ni Rumana Wiyar Alhaji Abdurrahman Jikar Imran ™anwar Junaid"

"ni ce zan durkusa in roketa, ashe kuwa za'a shekara a shekare ana abu Waya."""

"Ya ware idanu ya ce, ""Kenan kin gwammace in barsu su yi ta daukarki a matsayin Jidderh."""

"Ta taSe baki, ji take kamar ta rufeshi da duka, sai dai ba za ta yi wannan kuskuren ba domin babu mai tare mata a kusa, ta murtuke fuska ta ce, ""Idan ka gadama ka faWa masu gaskiya, idan ka gadama kada ka faWa masu, a je a dawo dolensu su barni in tafi tunda ni ba Jidderh bace. Now, ka bani aron wayarka inyi kira."""

"Mamaki da dariya take bashi, ta gama gadara ta dawo tana cewa ya ara mata wayarsa, ya murmusa ya ce, ""Yanzu kuma wayata kike son in ara maki, ina ce wayata ce torh ban badawa Jidderh."" Ya ™arasa maganar da kiranta da Jidderh domin ya kular da ita. Ta fasa ihu ta ce, ""Ni ba Jidderh ba ce, sunana Rumana."" Ya ce, ""Eh na sani Rumana aww Jidderh."" Ya fice yana mata dariya, ji take kamar ta bi shi ta yi ball da shi a wajen (Wannan"

shiga hanci da kudundune haka kuce wa Al'ameen ya fita hancin Rumana tun kafin ta saka a watsashi a kwatami ).

"Ta ta™ar™are ta fasa ihu tana mai jin takaicin yadda yake mata magana cike da gadara da gatsali, sai dai meyy, tana Waga idanu ta ga kofa a buWe, ba ta yi wata-wata ba ta mi™e ta fice da sauri ta bi ta kofar baya ta bayyana a bayan gidan, a gefe ta hango kofa ta yi sa'a kuba ce kawai aka saka, ta buWe ta fice ta yanki hanya tana ™o™arin tuna sunan unguwar da gidan Aunty Zaynerb ya ke."

"Al'ameen yana sauka ™asa ya ce, ""Wannan yarinyar ba Jidderh ba ce ba, sunanta Rumana."""

"Baki Wayansu suka zuba mashi idanu cike da tu'ajjibin abun da ya faWa, sudai idanunsu Jidderh suka gani amma yake"

"ce masu ba ita bace, to idan ba ita bace, to wacece, kuma mi yasa suke matu™ar kamanni, sannan ina Jidderh take."

"Da mamaki wanda yake haWe da rudani Ammi ta ce, ""Ban gane ba, Mi kake son sanar da mu?"" Al'ameen ya zauna sannan ya ce, ""Gaskiya take faWa maku sunanta Rumana, tana kamanni da Jidderh ne amma ba Jidderh ba ce ba,"" ya juya ga Imran, ya ce, ""Imran ka tuna kwanakin baya lokacin da na kiraka ina tambayarka Jidderh har na ce maka ka je ka tabbata idan tana gida."""

"Imran ya gyaWa kai ya ce, ""Eh na tuna lokacin."" Al'ameen ya lumfasa sannan ya ce, ""To lokacin da wannan yarinyar na hadu na yi mata magana ina tunanin Jidderh ce ina mamakin shigar da ta yi."""

"Imran ya ce, ""Then wacece ita? Ina Jidderh take? Mi yasa take kamanni da Jidderh? Mi yasa suke kama kamar kobo da kobo da har mu da muke rayuwa da Jidderh muka ™asa tantance ba ita ba ce?"" Tambaya ce wacce basu da amsarta sai dai su tambayi ita Rumana."

"Baki dayansu suka dugunzuma zuwa sama, sai dai wayam suka tarar da dakin, babu Rumana babu alamarta, ta yi"

"Satan dabo, sun duba baki Waya gidan amma basu ganta ba, ganin kofar baya a buWe ya tabbatar masu da a nan ta fita."

"Al'ameen, Abbi da Imran suka bi sawu amma ko mai kamanni da ita basu gani ba."

"A bangaren Rumana kuwa tana fita bakin titi ta debi hanya ta cigaba da tafiya a lokaci guda tana son tuna sunan unguwarsu Aunty Zaynerb amma ta gagara tunawa, sai da ta yi tafiya mai tazara har kafafunta suka fara ciwo sannan ta yi nasarar tunawa."

"Ta tsayar da kekenapep ta ce, ""Kofar ˜aura."" Ta shiga har ya fara tafiya sai kuma ya juyo ya ce, ""Kudinki naira Wari biyar."" Ta ce, ""Babu damuwa idan ka kaini zan shiga gida in amso maka."" Yana jin haka ya ja burki, ""A'a ba na haka, daga haka wasu suke guduwa."" Ta cika da mamaki ta ce, ""Na ce maka idan mun je zan shiga gida in amso maka."" Ya girgiza kai yace, ""A'a."""

"Duniya juyi-juyi yau ita ce ake yi gardama akan naira Wari biyar, bata ce komai ba ta zura kafafunta waje ta fita ya sa kai ya wuce."

"Ta ™ara tsayar da wani Wan sahun, a wannan karon sunan unguwar kawai ta faWa mashi ta kama bakinta ta yi shiru ba tare da ta faWa mashi sai sun je za ta shiga ta amso kudin ba, coz bata son ta ™ara mintina biyar ba tare da ta ganta a gidan Aunty Zaynerb ba."

********

GIDAN AUNTY ZAYNERB

Sai bayan sallar asuba sannan mutanen gidan suka samu barci yayinda Junaid yake zaune a gabanta hannunsa a cikin hannunta a haka barci ya yi awon gaba da shi.

"Cikin barci Jidderh ta fara juye-juye da kanta na mafarkin da ta ke yi tana tsala gudu a dokar daji yayinda wannan gardin katon ya ke biye da ita har ya kusa cimmata, gudu take da dukkanin karfinta amma ta kasa Sacewa ganinsa shima kuma ya kasa cimmata."

Ta durkushe tare da rufe idanunta tana buWesu ta tsinci kanta a wani daji mai yawan duhu yayinda wasu muryoyi da

ba ta sansu ba suke magana ™asa-™asa.

"A daidai lokacin ta farka a firgice lumfashinta yana fita da sauri-sauri, ta tara gumi sai haki take tamkar wacce tayi tseren gudun wuce sa'a."

"Abun da ta gani ya ™ara rikitar da ita, daki ne mai kyau da ™ayatuwa, gadon yana da laushi, labulen taga yana motsi na iska da ya ke ™adawa da shi, amma ba gidansu bane ba, ba gidan Alhaji Baffah bane ba, bai yi mata kama da inda ta sani ba."

"Ta mi™e zumbur tana bin dakin da kallo yayinda tsoro ya cika mata zuci. ""Ina nike?"" Ta tambayi kanta da kanta, ™wa™walwarta na son tuna yadda ta zo wurin sai dai ta kasa tunawa. Abun da ta iya tunawa kawai shine kuSuta da ta yi daga hannun waWanda suka yi garkuwa da ita da kuma tsintar kanta da ta yi a bakin titi daga nan bata ™ara tuna komai ba."

"Wani motsi ta ji a kusa da ita da saukar lumfashin mutum a dab da ita. Ta kalli inda take jiyo lumfashin, hannu ne"

"ri™e da nata hannun cike da kulawa, ta kalle shi da sauri, idanunta a ware cike da tsoro da fargaba."

"Yana zaune akan kujera da ya janyo kusa da gadon, kansa akan gadon yana barci yanayinsa kamar wanda ya shafe dare yana jiran farkawarta."

Ta yi iyakar ™o™arinta domin raba hannunta daga rikon da ya yi mata amma ta kasa. Ta kalleshi ta ™ara kallonshi

"saidai ba ta tuna inda ta sanshi ba, kuma bai yi mata kama da waWanda suka yi garkuwa da ita ba."

"A hankali ya buWe idanunsa ya saukesu a kanta, ya sakar mata murmushi, ""Morning sunshine,"" ya faWa a cikin murya mai taushi."

"Bata ce dashi ci kanka ba, tana dai zaune shurum tana luguden laSSa amma ta gagara furta koda kalma Waya yayinda mamaki ya kamata ganin yadda yake mata magana tamkar ya santa bayan ita kuma bata sanshi ba."

"Ya ™ara murmusawa yace, ""Rumana kin farka kenan, Uhmm Didin yaya Junaid."""

"Da jin sunan ta shiga ruWani. Zuciyarta na buga da ™arfi kamar za ta faso kirjinta. Wannan ba sunanta ba ne. Ta ja hannunta daga nasa, ta matsa baya da sauri tana girgiza kai yayinda tsoro ya mamayeta tunawa da mutanen da sukayi garkuwa da ita da kuma ba™ar wahalar da ta sha a hannunsu."

"""Waye kai?"" ta tambaya cikin rawar murya. Ta zabura tana faWin, ""Ina nike? Kuma ni ba Rumana ba ce."""

"Fuskarsa ta bayyana mamakin da kalamanta suka saka shi. ""Rumana,"" ya sake faWa a hankali, ""Ni ne yaya Junaid, kina a gidan Aunty Zaynerb, ki kwantar da hankalinki kin kuSuta. You are safe with me."""

"Ta kalleshi ta ™ara kallonsa, babu abun da ya yi mata kama da lafiya a nan musamman a wannan yanayin da ta tsinci"

"kanta a inda bata sani ba, da mutumin da ya ke nuna kamar ya santa yana kiranta da sunan da ba sunanta ba."

"Tsoron garkuwar da aka yi da ita ya dawo mata sabo. Tunaninta ya fara ayyana mata watakila wannan sabon mafarki ne, ko kuma sabon tarkon da suka dasa mata domin su samu lambar gidansu su kira su amshi kuWin fansa."

"Ta takure a waje guda, idanunta suka cika da hawaye, zuciyarta na tambayarta tambaya guda Waya kacal; Shin da ta gudu daga wajensu ta kubuta kuwa, ko kuma ™ara

Please Login or Register in order to submit comment