You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

faWawa ta yi a hannun wasu makwamusan? Saidai kuma wannan mutumin bai yi mata kama da masu garkuwa da mutane ba."

"Yana matsota ta ta™ar™are ta fasa ihu, ya yi baya da sauri tare da toshe kunnuwansa saying, ""Rumana please mana ka"

"da ki fasa min kunnuwa."""

"Ta ™ara fasa ihun da ya fi wancen amo, kamar zai yi kuka ya ce, ""Don Allah ki kwantar da hankalinki, ba zan cutar"

"da ke ba, na rantse."""

"Kalamansa ba su saka tsoronta ya ragu ba, a gareta kowace fuska tana iya zama ma™aryaciya duba da ko lokacin da aka saceta da mace ´ar uwarta aka yi amfani."

"Ta sauka daga saman gadon da sauri, ta koma kusurwar dakin tana takure a waje guda tana kallonsa cike da tsoro da shakku."

"Da muryar kuka tace, ""Idan ba kai bane ka saceni, to ya aka yi baka san sunana ba?"" Ya dafe kansa da ya fara sarawa"

"ya ce, ""Sunanki Rumana Abdurrahman Imran, Šiyar Abdurrahman, Jikar Imran, ™anwar Junaid."""

"Ta girgiza kanta, ta saka bayan hannunta ta share hawayen da suka zubo mata tana sauke lumfashi da sauri-sauri idanunta cike da tsoro."

"""A'a ban manta sunana ba,"" ta faWa da murya mai rauni."

"Junaid ya tsaya cak yana tu'ajjibin wannan abun mai kama da almara, lamarin ya fara bashi tsoro, kodai ta buge kanta ne ta rasa tunaninta."

"Ya lumshe idanu ya buWe idanunsa a kanta yace, ""Rumana mi suka aikata maki da ya sakaki manta sunanki?"""

"""Na san sunana,"" ta faWa da Waga murya. ""Miye sunanki?"" Ya tambaya. Tana sauke ajiyar zuciya da sauri-sauri ta ce, ""Sunana Jidderh. Ban taSa zama Rumana ba."""

"""Amma Rumana, ke ce, ke ce ™anwata Rumana,"" ya ™arasa maganar kamar zaiyi kuka."

"Ta girgiza kai zuciyarta na bugawa da karfi ta ce, ""A'a saidai idan kaine ka rasa tunaninka amma wannan ba Rumana ba ce, Sunana Jidderh."""

"Zuwa wannan lokaci ya gama yarda da watakila ta yi loosing memory dinta ne, ya nufi inda take da zummarsa yana faWin, ""Rumana."""

Ihun da tayi ne ya tilasta mashi komawa da baya yaja tunga yana mamakin rashin zuwan mutanen gidan duk da wannan uban ihun da take tsalawa.

"Ta fashe da kuka tana mai haWe hannayenta a waje guda alamar roko ta ce, ""Kana tsoratani, Please ka mayar da ni wajen ahalina. Mi ya sa nike a nan? Mi ya sa nike a inda ban sani ba tare da mutumin da ban sani ba amma kuma ya ke yi kamar ya sanni da dadewa?"""

"Ya ce, ""Rumana nine yayanki Junaid."" Ta fasa ihu ta ce, ""Please ka daina kirana da sunan da ba sunana ba."""

"Ya sassauta murya da alamar rarrashi ya ce, ""To da wani suna kike son in kiraki?"" Ta ce, ""Sunana."" Yace, ""Rumana!."" Ta fasa ihu ta ce, ""Jidderh! Sunana Jidderh! Sunana ba Rumana ba ne! Sunana Jidderh!"" Ya ce, ""Alright... Jidderh..."""

"Har kansa ya fara ciwo saboda ihun da ta ke yi. ""A ina ka ganni?"" Ta tambaya."

"Ya ce, ""Mun fito daga shopping mall nayi mantuwa na barki a mota na dawo ban tarar dake ba, ina nemanki na sameki a yashe a gefen titi."""

"Ji ta yi tsoronsa ya ™ara durar mata, a yaushe ta je shopping mall? Akwai alamun tambayoyi da yawa akan wannan mutumin, shin miye manufarsa na nunawa ya santa bayan kuma bai santa ba, shin mi yasa yake kiranta da sunan da ba sunanta ba?"

"Ya ce, ""Rumana,"" da sauri yayi saurin gyarawa tun kafin ta ™ara fasa mashi ihun ya ce, ""Awww Jidderh, calm down"

"Didi."""

"Ta ce, ""Waye Didi? Sunana ba Didi ba ne, sunana Jidderh."" Ya ce, ""Alright Jidderh."""

"Ta kafeshi da na mujiyarta tana karantar yanayinsa, bai yi kama da masu cutarwa ba, bugu da ™ari da iyakar"

"gaskiyarsa yake magana, yayinda lokaci zuwa lokaci take hango tsantsar ruWani a tare da shi."

"Hawaye suka wanke mata fuska tana hango zallar ruWani a kwance akan fuskarsa, itama cike take da ruWani a wannan dakin da tsinci kanta a cikinsa, tare da mutumin da ba ta sani ba, da sunan da ba sunanta ba."

Tambaya guda biyu suna mata kai kawo a masarrafar tunani; Shin mi yasa ta hango ruWani a tare da shi? Shin mi ya sa yake magana da iyakar gaskiyarsa?

Ta yi nisa a duniyar tunani har ba ta san lokacin da ya tako inda take ba saidai Waga idanu ta yi ta ganshi dab da ita.

"Ta ta™ar™are ta fasa ihu muryarta tana rawa na tsoro da ruWanin da take a ciki. Junaid ya rungumeta yana faWin, ""Rumana ki nutsu! Rumana ki nutsu!!."""

"Amma inaa bata nutsu ba sai kokowa ta ke yi da iyakar iyawarta. Ba ™aramin dambe suka sha ba, suka yi wujiga- wujiga, ya yi matu™ar mamakin karfinta har zuciyarsa tana raya masa anya kuwa Rumana ne? Rumana ba ta da wannan karfin domin da hannu Waya zai iya handling dinta amma wannan ta zame mashi kadangaren bakin tulu wanda hausawa suka cewa bai fito ba saidai ya shirya, a barshi ya Sata ruwa, a bugeshi a fasa tulun."

"Ta haukace mashi tana jifarshi da dukkanin abun da ya tari gabanta, a tamanin ya fita ya maido kofar ya rufe ya danna key."

Ya le™a dakin Abdulmajeed ya sameshi yana ta sharara barci da earplug a kunnansa sai a lokacin ya gane dalilin da

ya kasa duk ihu da haukan da ta yi mashi mutanen gidan basu tashi ba.

"A ruWe ya sauko parlour, kansa ya Waure ya rasa abun yi. Saidai yana sauka falon ya ci karo da Umma wacce shigowarta kenan."

"Da mamaki ya ce, ""Umma yaushe kika zo?"""

"Ta ce, ""Yanzu, a private jet na tafo. Tana ina?"" Ta tambaya."

"Ya yi tsuru-tsuru da idanu ya rasa ta inda zai fara mata bayani akan abun da ya faru, ta daka mashi tsawa, ""Tambayarka nike! Tana ina!!! Za ka bani amsa ko kuma sai na falla maka mari tukunna!!!!."""

"Muryarsa tana rawa ya ce, ""Tana sama amma tana wasu abubuwa da ban gane masu ba, tana cewa sunanta Jidderh that Rumana ba sunanta ba ne, idan na matsa kusa da ita sai ta yi min ihu tana rokona a kan in mayar da ita gidan su, tana yi kamar ta manta komai."""

"Umma ta zaro idanu ta ce, ""Ni Amina na boni! Mi suka aikata mata da ya sakata mantawa da sunanta?"""

"Ya ware hannuwa alamar shima bai sani ba, ta nuna mashi hanya ta ce, ""Mu je."""

"Yana gaba suka wuce sama zuwa bedroom din da ta ke, suna shiga Jidderh ta rakube a karshen gado jikinta yana rawa, ta ce, ""Please ku maidani a wajen dangina, na rokeku da girman Allah ku mayar da ni gidan mu."""

"Junaid ya nufi inda take yana faWin, ""Rumana ki nutsu, Junaid ne yayanki."" Jidderh ta fasa ihu tana mai takurewa a jikin bango ta ce, ""Na faWa maka ba sunana Rumana ba, sunana Jidderh, ka bar taSani haramun ne."""

"Yanayin yarinyar da kuma yadda take magana ya saka Umma a yanayi na tsoro da ruWani, ta zaro idanu waje yayinda gabanta ya yanke ya faWi, tana tsoron abun da zai je ya dawo domin kallo Waya ta yi wa yarinyar ta gane ba Rumana bace ba."

"Ta yi kasa da muryarta ta ce, ""Ki kwantar da hankalinki, ba za mu cutar da ke ba, miko min hannunki in gani."""

"Ji Jidderh tayi ta aminta da matar, ta mi™a mata hannunta, Umma ta ware hannun tana kallo, gabanta ne ya yanke ya fadi ta fara ja da baya tana girgiza kai tana faWin, ""Na boni!! Junaid ka cuceni!! Kun cuceni!!!"" Saura kadan ta fadi, ya yi saurin tarota, ta fizge ta juya ta fita, yabi bayanta da sauri."

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 4 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

"Umma ta zube a kan kujera hankalinta a matu™ar tashe ta ce, ""Ba Rumana ba ce, waccen yarinyar ba Rumana ba ce."

"Junaid kun cuceni. Ina mutanen gidan!?"" Ta tambayeshi da tsawa."

"Ya ce, ""Suna bacci da ya ke jiya kwana muka yi bamu rumtsa ba."""

"Umma ta dafe kanta da ya ke juya mata ta ce, ""Junaid ka cuce ni, Junaid ka gama da ni, Junaid kawai ka wuce ka bani wuri, koda yake wucewa zakayi kaje ka nemo Rumana domin wancen yarinyar ba Rumana bace."""

"Junaid ya waro idanu da tsantsar ruWani ya ce, ""Umma, Rumana ce."""

"Umma ta daka mashi tsawa, ""Na ce maka ba ita bace, Junaid ka tashi ka bani waje, ba na son ganinka, Junaid ka Sace min daga gani tun kafin zuciya ta debeni in yi furucin da ba zai yi mamu WaWi ba."""

"Jiki a sanyaye ya wuce staircase ya haye sama sai dai yana shiga dakin ya tarar da shi wayam, babu ita babu alamarta, tashin hankali wanda ba'a saka masa rana."

"Aunty Zaynerb, Abdulmajeed, Maryam, Umma da shi kansa suka bazama a cikin gidan suna nemanta amma babu ita babu alamarta."

"Suna cikin wannan halin ne aka kwankwasa kofar dake a gefen get, Mai guard ya buWe Rumana ta shigo tana tafiya da sauri-sauri gudu-gudu, tana haki ta ™arasa inda suke, tana maida lumfashi ta ce, ""Yaa Junaid ka ba mai kekenapep kudinsa, Umma yunwa ni ke ji ku bani abinci."""

"Da mamaki suke kallonta, shin har yaushe ne ta fita daga gidan har ta hau kekenapep, shin ina ta je? Junaid da Umma ne kaWai suke da wannan amsar sanin waccen ba ita ba ce. Umma ta yi karaf ta ce, ""Mu je ta ci abinci. Junaid ka je ka bashi kudin."""

"Junaid ya juya zuwa bakin titi ya tarar da Wan sahu har ya gaji da jira, ya zaro dubu goma ya mi™a mashi, ya amsa yana kallonsa da mamaki ya ce, ""Kudin sun yi yawa."" Junaid ya girgiza kai ya ce, ""Ba su yi yawa ba."" Ya ce, ""Na gode."" Junaid ya ce, ""Ka gode Allah."" Ya juya ya koma ciki yana mai farin cikin bayyanar Rumana saidai tambayoyin da su ka yi mashi katutu a cikin masarrafar kai sune: Shin wacece waccen yarinyar? Me ya sa take matu™ar kamanni da ™anwarsa Rumana?"

BAYAN HOUR DAYA

"Rumana, Junaid da Umma ne kaWai a dakin, Rumana tana zaune akan praying mat tana takurar abincin dake a gabanta, Umma ta dubeshi ta ce, ""Junaid ka tashi ka bamu waje."" Ya ce, ""Na'am."""

"Ta daka mashi tsawa ta ce, ""Na ce ka je parlour kuma koda wasa kada ka sake wani ya ji abun da ya faru Wazu, idan na ji wannan maganar a wani waje sai na yi mugun saSa maka."""

"Ya ce, ""Umma ki yi hakuri."" Ta ™ara daka mashi tsawa ta ce, ""Ka Sace min daga gani kuma ka ji abun da na faWa maka."" Rumana ta yi rau-rau da idanu ta ce, ""Ayyerh Umma ki daina yi mashi tsawa, ba laifinsa ba ne, laifi na ne, ni ce na ce muyi ghosting matakan tsaron mu."""

"Umma ta yi mata mugun kallo kamar za ta kai mata duka har sai da hantar cikinta ta kaWa, ta yi baya da sauri tana raba idanu, Umma ta nuna mashi kofa ta ce, ""Nace ka Sace min daga gani, aikin banza aikin wofi, yara kana faWa masu gaskiya ba su ji, ay ga irinta nan."""

Jikinsa a sanyaye ya fita.

Umma ta tsare Rumana da idanu har sai da tasha jinin jikinta tana ™o™arin mikewa ta saka hannu ta maido da ita ta

"zaunar, ta murtuke fuska ta ce, ""Ke nike saurare, ki faWa min abun da ya faru."""

Rumana ta ture plate dake gabanta tare da sanar da Umma abun da ya faru tun daga nunawa da Imran yayi ya santa har zuwa kofar da Al'ameen ya bari a buWe ta gudo.

"Umma ta ce, ""Jidderh ita ce wadda Junaid ya kawo gidan nan, da safiyar nan muka nemeta muka rasa shine muka fito nemanta kika shigo. Ki saurara ki ji ni da kyau, ka da ki kuskura ki sanar da kowa abun da ya faru, dukkanin wanda ya tambayeki ki ce kin manta komai. Kinga dai abun da rashin jin maganata ya janyo maki, idan kika ™ara aikata makamancin haka zare hannuwana zan yi daga dukkanin abun da ya biyo baya in ce babu ruwana, sai dai ki je can ke da wanda yake daure maki kugu ku ™arata da shi. Tunda dai ba ku gudun Sacin raina, tunda dai ba ku sona, idan kuka saka min ciwon zuciya, idan bakin cikin da kuke saka min ya kasheni, kun huta,"" ta ™arasa maganar da rauni."

"Jin Umma tana kiran mutuwa Rumana ta fashe da kuka tana faWin, ""Umma ki yi hakuri ba zan sake ba, kuma ba zan sanar da kowa abun da ya faru ba."""

"Umma ta ce, ""Da ya fiye maki don idan kika kuskura wani abun ya biyo baya ki kuka da kanki daga ke har wanda yake daure maki kugu kuna min abun da kuka gadama. A yau zamu wuce kaduna ta jet da na zo, daga rana irinta ta yau babu ke babu dawowa garin nan, Rumana ko a mafarki na ji labarin kina maganar abun da ya faru ko kuma kina maganar kina son zuwa garin nan ki kuka da kanki."""

"Rumana ta yi rau-rau da idanu ta ce, ""Ayyerh Umma na faWa maki ba zan sanar da kowa ba, na gama maganar garin nan daga yau har abada."""

"Umma ta ce, ""Da ya fiye maki."""

*******

A GIDANSU JIDDERH

"Sun yi jigum a parlour cikin tashin hankali, Jidderh ta faWo kamar wacce ake jefo, za ta fadi ™asa Uncle Al'ameen"

"ya yi saurin tareta yana mai ambatar sunanta, ""Jidderh."""

"Ta buWe idanunta ta sauke a kansa, da muryar da ba ta fita sosai ta ce, ""Uncle Al'ameen!!!"""

"Daga nan ba ta ™ara cewa komai ba, suna mata magana su ka ji shiru, suna dubawa sukaga ashe suma ta yi."

********

BAYAN WATA DAYA

"Tun bayan faruwar wannan al'amari tunanin Rumana da ya kamanni da su ke yi ya tsayawa Jidderh a rai tana ganin cewa watakila suna da alaka, watakila tana da alaka da ahalin Abbi da ya shafe shekara da shekaru yana nema tun bayan da ya baro Morocco ya yi ™aura ya shigo Nigeria neman su."

"Ta samu Ammi da maganar tare da sanar da ita shawarar da ta yanke akan maganar, Ammi ta yi jim tana nazarin maganganun Jidderh sannan ta ce, ""To shikenan amma ki je ki samu mahaifinku ki ji ra'ayinsa tukunna."""

"Jidderh ta gyaWa kai, ""Yana Ina?"" Ta tambaya. Ammi ta ce, ""Yana dakin karatu."" Jidderh ta mike zuwa study room inda ta sameshi yana karanta jarida, ya faWaWa fuskarsa da murmurshi ya ce, ""Daughter."""

"Ta zauna tana mai gaishe da shi ta dora da faWin, ""Abbi barka da warhaka."" Abbi ya ce, ""Barkan mu."" Sai da ta yi jim sannan ta ce, ""Abbi dama akan wannan yarinyar ne wacce aka kawo a madadina a watan da ya wuce."""

"Abbi ya ajiye jaridar da ke a hannunsa ya maida hankalinsa kacokam a kanta ya ce, ""Miye a kanta?"" Ta gyara zama ta ce, ""Kamanni da mu ke yi da ita abun dubawa ne, ina ji a jikina kamar za ta iya kasancewa tsanin da za mu bi mu hadu da ahalinka wanda saboda nemansu ne ka baro Morocco ka shigo Nigeria."""

"Abbi ya lumfasa, shima abun yana ci mashi tuwo a kworya sai dai ba ya da hanyar nemanta shiyasa bai tada maganar ba. ""Kin tuna gidan da aka kaiki ne?"" Ya tambaya da saka ran watakila ta tuna gidan da aka kaita ne shiyasa ta tado maganar."

"Jidderh ta girgiza kanta tabbacin ba ta tuna ba, ya ce, ""Idan haka ne babu abun da ya rage mamu da zamu dauka a matsayin madafa da za mu yi amfani da shi domin cimmata."""

"Jidderh ta ce, ""Ba zan iya gane gidan ba saboda lokacin da aka kaini bana a cikin hayyacina sannan lokacin da na fito ina a ruWe, amma Ammi ta ce min Uncle Al'ameen ya ce ya taSa haduwa da yarinyar tun kafin faruwar wannan lamarin, ina so in je in sameshi in gani idan zan iya samun karin haske daga gareshi."""

"Abbi ya yi shiru na tsayin lokaci kafin daga bisani ya ce, ""Babu damuwa ki je, Allah ya yi maki albarka, yadda kike ™o™arin ganin kin faranta min kema Allah ya baki wadanda za su faranta maki."" Jidderh ta amsa da, ""Amin."" Tana mai jin WaWin wannan addu'a da mahaifinta ya yi mata."

"Mi™ewa ta yi ta koma dakinta ta yi wanka ta shirya cikin atamfa dinkin riga da zane, ta tattare gashinta ta yi mashi gammo, ta Waura kallabi, ta zura doguwar hijab har tana sharar kasa, ta sauko parlour ta samu Ammi tana kallon wa'azi."

"Ta ce, ""Ammi zan wuce."" Ammi ta ce, ""Amma direba ba ya nan."" Jidderh ta ce, ""Babu damuwa sai in hau kekenapep."" Ammi ta yi jim sai kuma ta ce, ""Alright, Allah ya kiyaye hanya. Ki gaida min da su Hajiya."" Jidderh ta ce, ""Za su ji."""

"Tana fita bakin titi ta samu kekenapep ya sauketa a wani katon gida, ta wuce cikin gidan tana tafiya a nutse yayinda dogon hijab da ke a jikinta yake sharar kasa."

"Bangare biyar ne a katon gidan, ta shiga bangaren da ke a farko, wata tsohuwa ta samu a zaune a cikin katon falon tana kallon wa'azi, Jidderh ta shiga da sallama, ta zauna tana mai gaishe da ita, ""Hajiya, Ina kwana?"" Hajiya Attuwa ta amsa da, ""Lafiya lau. Ya mutan gidan?"" Jidderh ta ce, ""Suna lafiya lau. Suna gaidaku."""

"""Kin shiga sauran sassan kuwa?"" Hajiya ta tambaya."

"Jidderh ta girgiza kanta ta ce, ""A'a, ina so in fara ganin uncle Al'ameen tukunna sai shi shiga gaishe-gaishen ya biyo baya, wai ina yake ne tunda na shigo ban ji duriyarsa ba."""

"""Yana a haraba ta Waya bangaren,"" Hajiya ta sanar da ita."

"Jidderh ta ajiye jikkarta ta fita compound ta sameshi zaune a bayan motarsa hankalinsa kacokam akan wayarsa yana latsawa, ta ™arasa tare da dafa motar, ya dago da murmushi akan fuskarsa ya ce, ""Hauwa kuluwa inji Alhaji, yau Waya na ari bakinsa na ci masa albasa na Wana sunan matar mamman."""

"A tare su ka yi dariya, ya ce, ""Kin ce kina son ganina. Ta samu ne?"" Ya karashe maganar da barkwanci."

"Ta rausayar da kanta ta ce, ""A'a na zo gaisuwa ne da kuma neman iri."" Ya Wan kalleta ya ce, ""Na amshi gaisuwar saidai irin ne ban sani ba, na gyaWa kike so ko masara ko na maiwa."""

"Ta yi dariya ta ce, ""Akan Rumana ne."" Ya maimaita sunan da mamaki yana ™o™arin tuna wacce take nufi."

"Ganin bai gane ba ta ce, ""Wacce Yaa Imran ya kawo gida yana zaton ni ce."" Tunawa da ita ya saka shi sakin murmushi da bai san dalilinsa ba ya ce, ""Mi ye a kanta?"" Jidderh ta ce, ""Ina tunanin watakila tana da alaka da ahalin Abbi shiyasa nike kamanni da ita kamar kobo da kobo. Kuma na samu labari a wajen Ammi cewa ka hadu da ita tun kafin wannan lamarin ya faru."""

"Al'ameen ya gyaWa kansa ya ce, ""Tabbas hakane babu shakka sai dai babu wani abu da na sani a kanta da ya wuce wannan. Idan akwai bai wuce kasancewarta diyar masu kudi na sosai da sosai ba domin har matakan tsaro take tare da su a lokacin da na ganta sannan tana da girman kai da gadara."""

"Jidderh ta ce, ""Alright amma please idan ka tuna wani abu ka kirani."" Ya ce, ""Babu damuwa matar mamman."""

"Dariya ya ba ta ta ce, ""To shikenan kawun matar mamman. Ka gaida min da Fatima."" Ya ce, ""Za ta ji."" Ta juya ta ce, ""Na wuce sauran sassan in gaidasu tun kafin in koma ciki Hajiya ta koroni da mita."""

"A tare su ka yi dariya, tana faWin, ""Wannan tsohuwar rigima ne da ita, daga shigata ko ruwa ba ta ba ni ba ta fara tambayata idan na shiga na gaishe da su."" Ta nufi sashen da ke kusa da wannan. Ya bi ta da kallo yana murmushi yana son tuna wani banbanci na kamanni dake tsakaninta da waccen yarinyar saidai babu wani banbanci."

"Banbancin da yake tsakaninta da waccen na shigar suruta a bayyane yake, Jidderh ta kasance ma'abociyar saka dogon hijab har yana sharar ™asa yayinda waccen mayafi kansa akan kafaWa take daurashi a yadda da shi da babu duk Waya."

"Sai da marece sannan ta fara haramar komawa gida ta yi sa'a Uncle Al'ameen yana nan ya sauketa har gida, ya shiga suka gaisa da Ammi, ta ce, ""Ka tsaya ka ci abinci."" Yace, ""A'a na koshi."" Jidderh ta ce, ""Ko a zuba maka a cooler?"" Ya ce, ""To shikenan, shukran Matar Mamman."" Ya yi wa Ammi sallama ya fita zuwa motarsa."

"Har ta mota ta kai mashi cooler ta ce, ""A gaida min da Fatima."" Ya ce, ""Za ta ji."" Ta juya ta koma ciki yayinda ya"

Wanna horn mai guard ya wangame mashi ya Wanna motar waje.

*******

A BANGAREN RUMANA

"Tun daga ta koma kaduna ta ™asa mantawa da abun da Al'ameen ya yi mata ba, musamman inda yake cewa ta durkusa akan kafafunta ta rokeshi idan ta tuna ji take kamar ta fasa ihu, 'How dare him' har ita zai ce ta durkusa ta rokeshi."

"Bayan tarin dukiya da gata da take da shi amma har ya dubeta ya yi mata wannan maganar cike da gadara, ji take ba za ta iya hakura ba har sai ta rama sai dai tana tsoron tada maganar tana gudun fushin Umma ya sauka a kanta."

"Tsaye take a gaban iccen flower tana tsalle tana son ta tsinko furen amma ta ™asa kasancewar tsayinta bai kai ba, Junaid ya duba parlour bai ganta ba ya fito compound nemanta

Please Login or Register in order to submit comment