You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne."" Jin za'a buWe sabon shafin rattaba mata faWa ta mi™e za ta fita, Aunty Hajjo ta ce, ""Dawo ki zauna, faWan dai da baki so sai anyi maki, kuma wlh ki shiga taitayinki da ni ko kuma in saka a maido min ke a gidan nan ki yi sati ukku."""

"Rumana ta zaro idanu waje jin wannan zancen, ai tuni ta nutsu tana gyaWa kai alamar faWan yana shigarta har aka"

gama suka mi™e Leeserh ta yi masu rakiya har wajen mota.

"Ta ce, ""Didi sai yaushe kenan?"" Rumana ta kwalalo idanu ta ce, ""Tab, ina jin sai biki domin dai dawowata gidan nan babu rana babu wata, haka kawai inzo Aunty Hajjo ta ce a biyoni da kayana in boni in lalace."""

"Ta Salle murfin mota ta shiga tana jiran Junaid ya gama sallama da Leeserh su wuce, akan hanya ta yi shiru kawai tana Wanna waya, ya ce, ""Ya dai ³an mata, wa ya taSa min ke in tambayi dalili?"" Kanta tsaye ta ce, ""Hajjo ce, muje ka tambayeta abun da ya saka ta tutsuyeni tana min faWa."""

"Ya waro idanu ya ce, ""Tab, Aunty Hajjo kotun koli ce saidai muyi hakuri kawai, by the way hijabin ya yi maki kyau."""

"A takaice ta ce, ""Thank you."" Ya ce, ""Ko mu tsaya in siya maki Ice cream."" Ta girgiza kanta ta ce, ""A'a kai dai muje gida kawai tunda Allah ya taimakeni Aunty Hajjo ba tayi min Wurar tuwon dawa ba."""

"Bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba yana hango yadda za'a kwashi ´an kallo, ta kalleshi ta ce, ""Aww dariya"

"ma na baka, to babu damuwa, na gode sosai, Allah ya saka da alheri."""

"Ya ce, ""Ai kece didi kina da abun dariya."" Ya kai hannu zai ja kumatunta ta goce tana turo baki, ya saki murmushi yana faWin, ""Didin yaya Junaid, kamota-kamota nan, kamota-kamota nan."" Duk yadda ta kai ga fushi saida ya saka ta yi dariya."

"Umma tana tsaye a compound motacin suka shigo, aka buWewa Junaid mota ya fito ya zagaya bangaren da Rumana take ya buWe ya mi™a mata hannu ta amsa ya taimaka mata ta fito, suka jera tana tafiya dogon hijabin yana sharar kasa."

"Yadda yake mata hira da yadda take murmushi ya saka Umma ta saki murmushi tana wani tunanin, ta juya ta sauka zuwa parlour, suna shigowa ta ce, ""Wow daughter, hijabin nan ya yi maki kyau."""

"Rumana ta turo baki ta ce, ""A'a fa ban da dungurin uwar miji da muciya, yau kaWan ya rage Aunty Hajjo bata rufeni da duka, a gode Allah tunda na dawo babu tabo a bayana."" Ta haura sama tana turo baki. Ta tattara hijaban ta saka a kasan closet."

"Bayan haurawar Rumana bene, Junaid ya zube akan kujera ya zare hular ya ajiye yana duba waya, Umma ta dubeshi ta ce, ""Miye ya faru?"" Ya ce, ""Ba na ce ba amma faWan ba zai wuce akan mayafin da ta saka ba, ita Aunty Hajjo ta dage a dole sai da ta rin™a saka dogon hijabi."""

"Umma ta ce, ""Wannan lamari sai dai mutum ya zuba idanu, idan na yi magana sai ace na cika son yara."""

Daga haka hirar ta koma akan bikin Junaid da Khaleseert.

"Abun da ya faru a gidan Aunty Hajjo ya saka ta fita sha'anin abun da Al'ameen ya yi mata sai bayan sati biyu abun tunkudo mata zuci, ba ta yi maganar ba, ba ta yarda kowa ya gane mata ba, ta zauna ta kitsa ™aryar da zata yi ta samu taje har garin Katsina ta rama abun da Al'ameen ya yi mata."

Ta gama tsara komai akan yadda za ta yi durar mikiya a birnin Dikko ta rama abun da ya yi mata ba tare da Umma ta

"gane ba, ta samu Umma a dakinta, ""Gobe ne birthday din Beebarh,"" ta yi mata ™arya."

"Umma ta ce, ""To babu damuwa."""

"Rumana ta yi tsaye ba ta motsa ba, Umma ta Wago ta dubeta da alamar tambaya akan zama, ""Ki buWe baki kiyi magana, idan kuma baki da abun faWa ki juya ki fita na gaji da tsayuwa da kike yi min a saman kai,"" ta faWa ganin ta tsaya wanda ya nuna akwai wata maganar bayan wannan."

"Sai da ta yi jim sannan ta ce, ""Umma tunda nan kusa ne da Bello kawai zan fita idan ya zai kaini sai ya tsaya har in gama sannan ya maido da ni."" Umma ta yi jim sai kuma ta ce, ""Okay."" Dadi ya kama Rumana ganin shirinta ya yi aiki, ta juya ta koma dakinta ta faWa a kan gado tana sakin wani shegen murmushi mai tattare da ma'anoni da yawa yayinda take tufka da warwara a kan abun da za ta yi mashi ta rama abun da ya yi mata, tana kitsa abun da za ta yi mashi ta huce haushi na takaicin da ya kunsa mata a zuci, sai ta tabbatar mashi da cewa ta fi karfin ya yi mata magana da gadara har yana cewa ta duka akan kafafunta ta ro™eshi. 'How dare him'"

"Tunda safe take fara'a har Junaid ya tambaya, sanin idan ya ji zai hana sai ta ce, ""Babu komai."" Daga haka ta yi saurin kama kanta tun kafin ta tonawa kanta asiri da kanta, ya Wan kalleta domin bai gamsu da amsar da ta bashi ba sai dai bai tsawaita maganar ba, indai Rumana ce yana zaune za ta sameshi ta fede mashi daga biri har wutsiya."

"Bayan sun gama karin kumallo ta rakashi har wajen motarsa, ta mi™a mashi briefcase dinsa, ya amsa ya ce, ""Akan da"

"birthday da zakije zan yi maki transfer."""

"Sanin ™arya ta yi babu wani birthday sai ta girgiza kanta ta ce, ""A'a."" Da mamaki yake kallonta yana karantar"

"yanayinta ya ce, ""Mi yake faruwa? Mi kike shiryawa?"""

"Da sauri ta ce, ""Babu komai. Amma mi yasa ka ce haka?"""

"Ya kafeta da na mujiyarsa yana nazarinta, duk ta gama tsarguwa, ta ce, ""Ya da wannan kallon?"" Junaid ya ce, ""Saboda ba haka kike ba. This is unlike you."" Ya tsareta da kallo yana takowa zuwa inda take, tana tako baya, alamomin rashin gaskiya sun bayyana ™arara a kan fuskarta, muryarta na rawa ta ce, ""Babu komai fa."""

"Ya girgiza kansa ya ce, ""A'a akwai komai, ban yarda da ke ba, ki faWa min gaskiya."""

"Ta ce, ""Gaskiya kuma?"" Ya saka hannuwa a aljihun wandonsa yana mata kallon tsaf ya ce, ""Eh ki faWa min gaskiyar abun da kike kullawa, na ce zan yi maki transfer na birthday din ™awarki kin ce a'a wanda ba haka kike ba, it is really weird, care to explain."""

"Ganin yana gab da ganota kuma ta san ba zai taSa goyon bayan abun da ta ke shiryawa na zuwa Katsina ba, ta kalli gefe ta ce, ""Awww ina nufin kada ka saka min a wancen, a sabon account dina zaka saka min kuWin."""

"Ya Wan kalleta ya ce, ""Okay."""

"Juyawa ya yi da nufin shiga mota ta sauke ajiyar zuciya, da sauri ya juyo har sai da ta tsorata ya dungure mata goshi yana leken fuskarta kamar wanda yake son gano wani abu ya ce, ""Ban yarda da ke ba."" Sai kuma ya sakar mata murmushi ya juya ya shige mota, ya le™o ya ce, ""Ki rakani asibiti."""

"Cikin ranta ta ce, ""Ganganci kenan wanka da borkono, ina binka zaka gane gaskiya tunda har ka fara zargin da wani abun a kasa."" Amma a zahiri sai ta ce, ""Ayi min afuwa na yau, wata ranar sai inyi maka rakiyar."""

"""Okay kuma sai na gano abun da kike Soyewa, da bakinki zaki faWa."""

"Idan har ita za ta faWa mashi ashe kuwa za'a shekara dubu da Woriya bai sani ba. Wace ita ta yarda aji mutuwar sarki a bakinta, haka kawai Umma ta rufe gida ta yi mata Wan banzan duka."

"Junaid ya yi wa motarsa key ya fice daga gidan yayinda ta juya ta koma ciki, ta haura sama zuwa bathroom ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando english wears ta ja kujera ta zauna tana wani shegen murmushi, cikin ranta ta ce, ""Yau zan yi wankan kece raini."""

"Ta cancara kwalliya marar yawa wacce ta dace da fuskarta, ta zura sarkar diamond mai dogon chain tare da ´an kunne, awarwaro da agogo mai Wan karen tsaWa, ta saki wani mugun murmushi tana kallon kanta ta cikin madubi tana tuna yadda za ta koya mashi hankali sai ya gane ya taSo wacce ba'a taSowa a ci bulus."

"Ta janyo dogon gashinta da ya sauko har ya wuce gadon bayanta ta yi mashi kitso guda Waya, ta daura kimoni a kan kayan da ke jikinta, ta janyo siririn mayafi ta daura akan kafaWa ta yi wa wanka kanta wanka da designer perfume, ta suri jikka ta fita tana tafiya a nutse tare da Waura kowace kafa a inda ta janye dayar."

"Ta le™a dakin Umma ta ce, ""Umma na tafi."" Umma ta ce, ""Tun yanzu?"" Rumana ta ™a™aro murmushi yayinda"

"gabanta yake dukan tara-tara ta ce, ""Mune manyan ™awaye shiyasa."" Umma ta ce, ""Okay sai kin dawo."""

"Ta fito compound ta samu Bello yana tsaye a gefen motar da za su fita da ita wacce ta kasance sabuwa dal kalar ash, mai tsaWar gaske, yana hangota ya yi sauri ya buWe mata gidan baya yana kwasar gaisuwa ta shiga ya rufe sannan ya zagaya bangaren direba ya danna horn mai guard ya bude mashi get ya danna motar waje."

"Ta kwantar da bayanta tare da lumshe idanunta ta ce, ""Katsina za ka kaini."" Bello ya ware idanu jin kalamin da ta yi ya ce, ""Na'am?"" Domin tabbatarwa kansa watakila bai ji daidai ba ne."

"Ta buWe idanunta tana faWin, ""Na ce Katsina zaka kaini, kuma zaSi biyu gareka, ka kaini ko kuma in kai kaina da kaina, amma kuma ina faWa maka da babbar murya idan na ji wannan maganar a bakin Umma ko wani a gidan nan, uhmm zamu kwashi ´an kallo da kai."""

"Da sauri ya ce, ""Zan kai ki."" Ta ce, ""Da ya fiye maka."" Ta saki murmushi tana tuna yadda za ta yi maganin wannan saurayin, yana talaka makaskanci amma har yake da zarar faWa mata ta durkusa ta bashi hakuri, idan har sunanta Rumana Abdurrahman to kuwa sai ta tabbatar da ta nuna mashi iyakarsa."

"Bayan sun shiga garin Katsina a wajen Wandagoro ta buWe idanunta ta ce, ""Ka samu wuri ka yi parking."" Bello ya yi kamar yadda ta umarce shi, ta zaro katin zarar kudi daga handbag dinta ta mi™a mashi, ""Zan ja motar daga nan, idan na gama abun da nike zan nemeka, ga katina ka yi siyayya ka kaiwa iyayenka ranar na ji Umma tana cewa kai Wan garin nan ne amma ka da ka yi nisa, ba zan jima ba za mu wuce."""

"Furucinta na cewa da ta yi za ta ™arasa ita Waya ya sakashi a ruWani ya ce, ""Na'am."""

"Ta fusata ganin ya barta da kati a hannu, a fusace ta ce, ""Ba zan maimaita ba tunda na tabbatar da ka ji abun da na ce, kuma da hausa na yi maka, ko ba zaka amsa bane ka bar min hannu a sage, kana Sata min lokaci."""

"Bayan ya amshi katin ya fito tare da buWe mata kofa ta fito ta koma gaba ta ja motar ta nausa a kan titi, kai tsaye gidan su Jidderh ta nufa. Hanya bata Sace mata ba tana tuki tiryan-tiryan har ta isa gidan, ta danna horn mai guard ya bude kofar dake gefen get ya leko domin ganin waye, da mamaki yake kallonta ganin shigar da ta yi domin a tunaninsa Jidderh ce, yana ta mamakin yaushe kuma ta fita, ya bude get ta cilla motarta cikin gidan."

"Bayan ta yi parking sai da ta duba fuskarta a mirror da ke wayarta sannan ta fito tare da janyo jikkarta wacce take limited edition, tana tako cike da nutsuwa yayinda iska yake sama da kimoni da ke jikinta, yana kaWawa da ita, ta yi kyau makurar haWuwa, dukkanin wanda ya kalleta sai ya ™ara."

"Ammi da Abbi suna zaune a parlour, ta kutsa kai ciki, da mamaki suke kallonta, ta zauna tare da Waura kafa Waya a kan Waya ta ce, ""Barka da warhaka."""

"Suka zuba mata idanu suna tu'ajjibin lamarin, ta shigo kanta tsaye babu sallama babu gaisuwa sai dai ce masu da ta yi, 'Barka da warhaka.'"

"A daidai lokacin Jidderh ta sauko daga bene, suka zubawa juna idanu suna mamakin tsantsar kamannin da su ke yi,"

"Rumana ce ta fara janye idanunta, Jidderh ta ™araso falon tana murmushi ta ce, ""Rumana. Barka da zuwa."""

"Rumana ta yatsine fuska tana takaicin kamanni da su ke yi ta ce, ""Barkanmu."""

"Jidderh ta zauna ta fuskanceta sannan ta ce, ""Na ji dadin zuwanki, na jima ina neman hanyar da zan sameki."""

"Da mamaki Rumana ta ce, ""Ni kuma? To, Allah ya sa lafiya."""

"Jidderh ta gyara zama ta ce, ""Tun bayan faruwar wannan al'amarin nike fatan haduwa dake."""

Da mamaki take kallon yarinyar wacce take rattaba mata zancen kamar wacce ta tambaya.

"Kamar wacce aka yi dole ta ce, ""Ohh ikon Allah."" Jidderh ta lumfasa sannan ta ce, ""Mahaifinmu ya shigo Nigeria neman danginsa, ganin kamanni da nikeyi da ke nike ganin idan kika hadamu da danginki zai iya yiyuwa mu samu gano."""

"Rumana ta katseta da faWin, ""Mafarinku."" Jidderh ta girgiza kanta ta ce, ""A'a asali ake cewa."""

"Rumana ta yi mata kallon raini tana takaicin yadda take mata gyaran kalami kamar ta ce mata tana neman agaji, magana ce ta baka idan wanda aka faWawa ya gane to ai shikenan, duk kurewarta da iya hausa aje a dawo za ta haWu da wanda ya fita ji da sanin salo da lagon azancin magana."

"Ta taSe baki ta ce, ""Babu shakka kinji hausa. Sai dai ba'a katseni idan ina magana da fatan kin gane abun da nike nufi."""

"Jidderh ta ce, ""Ayyerh, Afuwan."""

Rumana ta jinjina kanta ta baza idanu domin ganin ta inda zai Sullo saidai babu shi babu alamarsa.

"Jidderh ta mi™e zuwa kitchen ta kawo mata ruwa da snack, Rumana ta kalleta ta kalli abincin ta yatsine fuska ta ce, ""A'a ki mayar da abun ki bani da bu™ata. Abun da ya kawo ni daban, lokacin da aka kawoni wannan gidan akwai wani saurayin talaka da ya zo wanda bayan fitarsa ne na gudu, shi nike son gani, idan har ya yi min abun da nike so ni kuma zan hadaku da dangina."""

"Jidderh ta ce, ""Uncle Al'ameen ne, bari in kirashi."" Rumana ta ce, ""Mu yi haka kuma ki faWa mashi sauri nikeyi in koma inda na fito beside jina nike takure a wannan akurkin gidan."""

"Maganar ta doki Jidderh amma sai ta taushi kanta ta yi mata uzurin watakila bata faWa da nufi ba, ta koma sama ta Wauko wayarta ta kira Uncle Al'ameen ta sanar da shi abun da ya faru, dama yana tsumayin yarinyar, mintina biyar a tsakani motarsa ta yi parking a gidan kasancewar yana kusa."

"Lokacin da ya shigo falon Rumana ta yi mashi kallo Waya ta watsar tana cika da batsewa tunawa da abun da ya yi mata, cikin ranta ta ce, ""Talaka da shi."""

"Suka gaisa da su Abbi, Jidderh ta gaida shi, Imran ya shigo ya samu kujera ya zauna tare da gaida shi."

"Jidderh ta ce, ""Rumana ga shi ya zo."""

"Rumana ta kalleshi ido cikin ido ta saki murmurshin gefen baki sannan ta ce, ""Ta ce sunanka Al'ameen, Ko? To Mr Al'ameen na zo daukar fansa ne na ramuwar gayya wacce tafi ta gayya zafi. Jidderh idan har Al'ameen ina nufin Aminu, ehh sunansa Aminu, idan har Aminu ya durkusa a kan gwuwowinsa ya rokeni ya bani ha™uri akan gadarar da ya yi min ni kuma na yi maki al™awari akan zan hadaku da dangina."""

"Baki Waya mutanen falon kallonta suke da mamaki jin furucin da ta yi, ita mai gayya mai aiki kuwa ko a jikinta, bata damu da kallon da su ke yi mata ba, ta Wora da faWin, ""Ya da wannan kallon kamar wacce ta yi wani babban sabo, naga ba ni ba ce na fara, shine ya fara kuma sai na rama, har ya isa ya yi min magana da gadara yana talaka,"" ta faWa a fusace, ta Wora da faWin, ""A waccen ranar na ce mashi ya faWa maku gaskiya akan ni ba Jidderh ba ce amma cike da izza da gadara ya ce har sai na durkusa a kan gwuwowina na rokeshi. Nima a yau zan rama ya ji yadda ake ji. Aminu ka durkusa a kan gwuwowinka ka ba ni hakuri a kan abun da ka yi min, sai in hadasu da dangina."""

"Imran ya ta so mata, da tsawa ya ce, ""Mi! Kina hauka ne!!."""

"Hankalinta a kwance ta ce, ""A'a psychiatric baki Wayanta ce a sama kaina."""

"Ya ware idanu ya ce, ""Keee!!!"""

"Bata bari ya rufe baki ba, ta daka mashi tsawar da tafi tashi amo, ""Kai har ka isa ina magana kana katseni, ™aramin alhaki. Ka yi min shiru a nan, da na gaba da kai nike magana, don't you dare provoke me domin idan na dawo kanka sai na tabbata ka yi nadamar haduwarka da ni a waccen ranar."""

"Ta juya ta fuskanci Al'ameen ta ce, ""Mi kake jira? Ka durkusa a kan gwuwowinka ka rokeki ni kuma zan hadasu da dangina."""

Jidderh ta girgiza kanta idan har sai anyi haka to kuwa bata bu™atar taimakon.

"Ammi da Abbi suka rasa bakin magana, Al'ameen kallon yarinyar yake cike da tsantsar mamaki, bai taSa tunanin tsaurin idanunta ya kai har haka ba."

"Ta ce, ""Kai nike jira Aminu idan ba za ka yi ba sai in koma in sake sabon lale."""

"Jidderh ta ce, ""Uncle ka da ka yi, zamu samu wata hanyar, idan har sai ta wulakantaka sannan za ta taimakemu torh"

"ta barshi ba mu da bu™ata."""

"Al'ameen ya ce, ""A'a Jidderh babu wata hanyar sai wannan, dama ce wacce bai kamata mu yi wasa da ita ba."""

"Rumana ta saki murmushi tana kada kafafu, ta kalleshi ta watsar tana faWin, ""Ni Rumana Wiyar Abdurrahman ™anwar Junaid guguce daidai da kugun dukkanin wanda ya nemi takani, sai in Waga mutum in naa-naa da kasa kuma bai isa ya tambayi dalili ba."""

"Ta gyara zama tare da sakin shu'umin murmushi ta yi mashi alama da hannu a kan ya durkusa ya roketa, Al'ameen ya"

zuba mata idanu sai kuma ya fara ™o™arin sauka daga saman kujerar da nufin ya durkusa a kan gwuwowinsa.

Jidderh ta kawar da kanta gefe yayinda hawaye suka cicciko idanuwanta ganin cin mutuncin da aka yi wa kawunta.

"Rumana ta murmusa, ganin yana ™o™arin sauka akan gwuwowinsa, ko a haka ta yi nasara, ranta fes, ta Waga mashi hannu ta ce, ""Ka dakata, ba sai ka durkusa ba domin ko a nan na nuna maka cewa ruwa ba sa'an kwando ba ne sannan kuma shi ZANE A KAN RUWA wahalar gane kamanni yake da shi, dalili kuwa shine dukkanin yadda kake tunanin ka fuskanceshi idan aka yi wani juyin sai ka fahimci cewa ashe ba ka gane komai ba, koda yake shi ZANE A KAN RUWA dole ya kasance mai wahalar gane kamanni, to ta ina za'a tantance kamanni ballantana a ganeshi. Kake kallona na zama ZANE A KAN RUWA ne kake ™o™arin fahimtar KAMANNINA ko kuma kaga mace mai kyau ne kake ™o™arin kwada sa'arka, to tun wuri ka yi wa kanka faWa domin ruwa ba sa'an kwando bane yana shiga yake fita domin babu katanga da za ta tareshi."""

"Sai kuma ta yafito Islam ta zaro damen dollars ta mi™a mata ta ce, ""Ga shi baby girl ki sayi chocolate na manta ban"

"siya maki akan hanya ba."""

"Ta Waga waya ta lalubo lambar Bello ta ce, ""Mu hadu daidai inda muka rabu, ka tabbata kayi wa iyayenka siyayya sannan ka yi min takeaway na fried rice."""

"Daga Waya bangaren Bello ya ce, ""To Hajiya amma kamar nawa zan kashe masu."" Ta murmusa ta ce, ""Wacce zasuyi farin ciki da kai."" Ya fara zuba godiya, ta ce, ""Ka da ka damu yiwa kaine."" Suna ajiye wayar ya yi wa iyayensa sallama ya kira ™aninsa suka fita tare domin ya tafo da siyayyar kayan abinci da zai yi masu duk ba wai babu bane tunda Junaid yana masu biya babba amma tunda har ta nuna tana son ta yi mashi alheri ya kamata ya ba ta wannan damar."

****

"Rumana ta maida dubanta akan Jidderh kafin ta ce, ""Jidderh ki ce mashi ya biyoni waje zan ba shi adireshin, amma koda ya ce ban bashi ba kada ki yarda, ™arya yake na ba shi ko kuma kanshi ba ya aiki shiyasa bai gane karatun ba kin san wasu ™wa™walwar kifi ne da su."""

"Ta mi™e ta nufi ta fita tana tako Waya bayan Waya cike da nutsuwa, ta jingina da motarta, Jidderh ta fito balcony tana hangota yayinda takaicin abun da ta aikatawa Uncle Al'ameen yake ragargazarta a ciki, ji take kamar ta ce basu so amma ya ta iya, idan ta yi hakan abun da aka yi mashi ya tafi a banza kenan."

"Al'ameen ya fito ya ™arasa inda take ya tsaya gefenta, ya ce, ""Ki bani adireshin."""

"Ta ce, ""Sai ka rokeni tukunna, ka wani tsareni kana magana kamar mai bani umarni."""

"Al'ameen ya Wage mata gira ya ce, ""Ko in durkusa ne,"" ya yi mata haka ne domin ya nuna mata bai damu ba amma a cikin ransa yana takaicin abun da ta yi mashi, yarinyar da ba za ta wuce sa'ar diyarsa Fatima ba."

"Rumana ta kalli agogo da ke a hannunta taga lokaci ya ja ta dafe kanta ta ce, ""Gosh,"" ta mi™a hannu ta ce, ""Ba ni"

"wayarka."""

"Ya zaro wayarsa ya mi™a mata ta yi jim sannan ta mi™a mashi ta ce, ""Ka matsa zan wuce."" Ya matsa mata, ta buWe motar ta shiga ta danna horn mai guard ya buWe mata get ta danna motar waje, saida ta rasa ta inda za ta koma inda suka rabu, sai da ta yi tafiya mai Wan tazara sannan ta samu waje ta yi parking ta kira numbar Bello babu jimawa ya ™araso suka dauki hanyar kaduna."

"Ta dauki takeaway da Bello ya ajiye a backseat tana tsakurar abincin tana jin nishadi na ramuwar gayyar da ta yi, Bello ya Wan juyo da kansa ya ce, ""Hajiyarmu ta ce a yi maki godiya, Allah ya ™ara budi."" Ta ce, ""Amin, ka ce mata na biya mata Umrah ita da mahaifinku."""

"Farin ciki ya cika Bello yana ta zuba mata godiya, ta ce, ""Babu komai yiwa kaine."""

Tana komawa Kaduna ta manta da komai ta cigaba da harkokin gabanta. Tuni iyayen Bello suka Waga zuwa Umrah da ta biya masu.

******

"Al'ameen ya yi tunanin a wayarsa ta rubuta adireshin sai bayan tafiyarta ya tabbatar da bata rubuta ba domin ya bincike wayar babu inda ta ajiye mashi address, ya cika da takaici ganin duk da muzantashi da ta yi amma still ta raina masu hankali ta tafi ba tareda ta bada adireshin ba."

"Sai dai abun da bai sani ba shine kamar yadda ta ce za ta bashi adireshin ta bashi sai dai ba ta hanyar da zai gane cikin sauki ba, ranar yana cire cover din wayarsa, ™aramar takarda ta faWo, da mamaki yake kallon adireshin dake rubuce a kan takardar, ya yi saurin kiran Jidderh."

"Daga Waya bangaren ta ce, ""Uncle Al'ameen an wuni

Please Login or Register in order to submit comment