You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Satanta, hankalina a tashe yake, nima ina sonta ina jinta a raina a matsayinta na ™anwata kwaya daya tilo wacce nike daukarta tamkar wani bangare na jikina."""

"Umma tana mai cigaba da kuka ta ce, ""Idan ciwon zuciya ya kamani kun huta, Junaid sai da na nuna maku bana son zuwanta garin nan amma kuka fitineni har da min boren cin abinci har sai da kuka tursasani na yarje maku zuwan. Babu komai idan na mutu kun huta."""

"Junaid ya yi wurgi da wayar yana nadamar abun da suka aikata na bujurewa maganarta, ya ja motar ya nausata a kan titi ba tare da ya san inda zai dosa ba, yana jan motar fuskarsa dauke da tsantsar damuwa yayinda maganganun Umma suke mashi amsa kuwwa a kwalbatin kunne kamar saukar aradu a lokacin da ake tsaka da ruwa musamman inda take cewa, 'Na baka awanni biyar ka nemo min diyata a dukkanin inda take a cikin garin katsina... A kan wannan maganar zan iya yafe wa duniya kai, sai dai ka nemi wata uwar... Babu komai idan na mutu kun huta...'"

"Ya fara barin gari kira ya shigo wayarsa ya gangara da motar a gefen titi ya haWa kansa da sitirayi yana mai sakin ™aramin ihu, sai da aka ajiye mashi kira har biyar sannan ya Waga, kamar wanda aka yi wa dole ya ce, ""Abdulmajeed."""

"Daga Waya bangaren Abdulmajeed ya ce, ""Kana ina?"""

"""Na fita ne."""

"""Yanzu kana ina?"""

"""Ban san inda nike ba."""

"""Okay ka ba wani ya yi min bayanin inda kake sai in zo in daukeka."""

"""A'a babu bu™atar hakan, zan iya maido kaina da kaina."""

"""Take it easy bro, zamu sameta In sha Allah."""

"Junaid ya haWe kansa da sitirayi yana mai zubar da hawaye ya ce, ""Dukkanin abun da ya faru da ita nine na janyo mata, da na biye mata muka yi wa Umma Sore har saida muka tursasata ta yarda da zuwanmu garin nan. Dolena in nemota, komai ya faru laifina ne. Kada ku nemeni domin ba zan dawo ba har sai na samu Rumana."""

"Ya tsinke kiran tare da kashe wayar baki Waya ya yi jifa da ita a backseat, ya kunna motar ya nausa a kan titi, ya yi tafiya sosai sannan ya gangara gefen titi ya Waura kanshi a kan sitirayi fuskarsa dauke da tarin damuwa, abun ya haWe mashi goma da ashirin, damuwar Satan Rumana, zullumi na halin da take ciki, da kuma damuwar da yake ji a kan maganganun Umma."

"Damuwa da kunci ne suke ragargazarshi a zuciya, ya rasa abun da yake mashi WaWi, ™anwarsa guda tilo wacce ta"

"kasance mafi soyuwa a gareshi ta Sata bai san inda take ba, ga kuma kukan da Umma ta yi a kanshi."

The more ya tuna kukan da Umma ta yi a kansa the more ya ke jin hankalinsa ya kai koluluwar ma™urar tashi. Kukan

uwaye akan yaransu fitina ne musamman shi da ya san yadda suka tursasata har ta yarda aka yi tafiyar nan.

"A hankali ya dago idanunsa ya hango abu kwance kamar mutum, ya yi jim sai kuma ya fito daga motar tare da dosar wajen, mace ce a yashe gashin kanta a barbaje kamar na mahaukaciya, da sauri ya ™arasa ya durkusa ya dagota, ya zaro idanu a sanadin wacce yayi arba da ita, da karfi ya ce, ""Rumana! Rumana!! Didi!!!..."""

"Amma shiru babu amsa, ya shiga girgizata yana faWin, ""Didi! Didi!! Didi wake up! Rumana ki farka! Mi ya sameki? Mi aka yi maki?"""

"Da hanzari ya dauketa ya wuce da ita mota ya kwantar da ita a gidan baya, ya zagaya mazaunin direba ya tada motar, hankalinsa ya dugunzuma matu™a gaya ganin halin da take a ciki, ya rasa inda zai nufa da ita, daga karshe ya yanke shawarar zuwa da ita gidan Aunty Zaynerb, gudu yake sosai kamar wanda yake tseren gudu, ikon Allah ne kaWai ya kai shi gidan Aunty Zaynerb lafiya, ya yi parking a wajen ajiye motoci ya fito ya sureta ya yi cikin gidan da ita."

"Aunty Zaynerb, Abdulmajeed da Maryam suna zaune a parlour sunyi jigum-jigum ya shigo dauke da ita, suka mi™e"

da sauri suna salati.

"Maryam ta ce, ""Innalillahi wa inna ilaihi raji'um. Mi ya sameta haka?"""

"Junaid zai ajiyeta a kan doguwar kujera, Aunty Zaynerb ta ce, ""A'a, ka wuce da ita dakina. Abdulmajeed ka dubata ka bata taimakon gaggawa."""

"Suka dugunzuma zuwa saman bene hankalinsu a matu™a tashe, Abdulmajeed ya ba ta taimakon gaggawa tare da saka mata karin ruwa ya ce, ""Tasha wahala ne ga kuma yunwa sai kuma shatin bulala dake a jikinta amma babu wata damuwa bayan wannan."""

"Maryam ta zaro idanu ganin yashinta Wan kaWan, idanunta a waje ta ce, ""Mun boni, Mi ya faru da gashinta? Ko yankeshi sukayi?"""

"Sai a lokacin hankalinsu ya kai a kan gashin, abun ya matu™ar basu mamaki da Waure kai saidai babu wanda ya ce uffan, Rumana ta kasance mai dogon gashi sosai, yadda gashin ya koma a yanzu sai dai idan yankeshi aka yi."

"Sai da ta samu barcin sannan hankalin Junaid ya Wan kwanta, ya ce, ""Aunty ki kira Umma ki sanar da ita."""

"Aunty Zaynerb ta ce, ""Okay."""

"Yana zaune a gefenta ya kama hannunta yana murzawa a hankali yana mai godewa Allah da aka sameta, kanwarsa kwaya Waya tilo, ita ce farin cikinsu. Haka suka kwana a zaune, babu wanda ya rumtsa a cikinsu a wannan daren."

**********

"A bangaren Rumana kuwa sai gab da sallar asuba sannan ta farka ta dafe kanta ta mi™e zumbur, ta ware idanu tana"

"bin Wakin da ta ke a ciki da kallo, sannu a hankali komai da ya faru ya ke dawo mata a kai."

SHIN MI YE ZAI FARU IDAN JIDDERH TA FARKA TA TSINCI KANTA A WAJENSU YAYA JUNAID?

"Rumana tana gidan su Jidderh, Jidderh tana tare da su yaya Junaid,"

kowanne bangare yana murna ya samo tashi.

SHIN YA ZA TA KAYA A TSAKANINSU?

SHIN MI YE SIRRIN DA KE TATTARE DA KAMANNIN DA SU KE YI?

SHIN YA AKA YI AKA KWANA A RAGAYA?

SHIN MI YE SIRRIN DA UMMA TAKE ˜O˜ARIN �OYEWA A DANGANE DA RUMANA?

KU BIYONI DOMIN JIN YADDA ZA TA KA YA.

"Rumana ta Waura hannuwa a saman kai tana mai fasa ihu cikin nadamar biyosu da ta yi gashi sun saceta, ""Na boni na faWa hannu masu sace mutane, shikenan na shiga komar masu garkuwa da mutane."""

"Ita fa ba kudin biyan fansar ta ke ji, wahalar da za su bata kafin a kawo kudin ne yake tada mata da hankali, tana da labarin tsantsar rashin imani da rashin tausayin da suke nunawa akan mutanen da suka sata shiyasa ko dawowa hutu Nigeria bata so."

"Da hanzari ta duro daga saman gadon ta nufi kofa sai dai tana murWa handle ta ji kofar a kulle, tabbacin sun kulleta daga waje, ta zube a ™asa tayi zaman daSaro tana share hawaye tana nadamar biyosu da ta yi ba tare da ta yi gardama a kan su bari yaya Junaid ya fito ba."

"Abun da ya kamata ta yi a lokacin shine ta saka a kirashi ya fito ya warware komai amma sai ta bari zuciya ta Webeta, ta bari gadara da rashin kunya suka sakata ta biyosu zo™ai-zo™ai ga shi nan sun ri™eta lamari ya lalace mata zuwa abun da za ta iya kira da KITSO DA KWARKWATA mai wuyar sha'ani."

"""Wani irin ganganci ne haka ya saka na biyewa rashin kunya da gadara na biyosu gashi sun yi garkuwa da ni, sai da Umma ta hanani zuwa garin nan, sai da Umma ta ja min layi da zuwa garin Katsina amma muka matsa mata. Ga irinta nan tun ba'a je ko'ina ba na fara nadamar zuwana, shiyasa jayayya ko ja in ja da maganar iyaye babu riba ko kaWan, babu wani haske a cikin aikata hakan."""

******

GARIN KADUNA

SATI BIYU DA SUKA WUCE

"Umma tana zaune a parlour tana kallon news Junaid ya sauko ya zauna a kan kujera dake a Waya gefen suka cigaba kallon a tare, lokaci zuwa lokaci suna zantawa akan labaran duniyar da suke kallo, Junaid ya mi™e ya fita babu jimawa ya dawo."

"Umma ta dubeshi ta ce, ""Yaushe ne tafiyarka katsina?"""

"Ya ce, ""Jibi, In sha Allah."" Ya ™arasa maganar yana mai zama akan kujerar da ya tashi."

"A daidai lokacin da Rumana take saukowa daga bene ta tsinkayi hirarsu, ta zauna a gefensa ta ce, ""Waye zai je Katsina?"""

"Ya nuna kansa ya ce, ""Ni."""

"Ta kwanta a kan kujerar da ya ke zaune tare da yin pillow da cinyarsa, da yanayinta wanda yake tattare da shagwaSa da hutu da ya zauna a jikinta da sangarta irin na yara da suka tashi babu kwaSa babu kyara ta ce, ""Nima zan je tun da ban taSa zuwa ba."""

"Ya lakuci hancinta ya ce, ""To shikenan sai ki shirya mu je tare."""

"Ta fara murna jin zai tafi da ita garin Katsina, Aunty Zainab ™anwar mahaifinsu ce take aure a garin amma tunda ta"

tashi ba ta taSa zuwa ba.

"Ta mi™e zaune tare da rungumeshi ta ce, ""Na gode, yeey, za mu je Katsina."""

"Babu zato babu tsammani Umma ta daka mata tsawa, abu ne wanda bai taSa faruwa ba, tunda suke Umma bata taSa Waga masu murya ba ballantana kuma ya kai ga tsawa musamman autarta kuma tilon diyarta mace Rumana, daga Rumana har Junaid da mamaki suke kallonta."

"Ta haWe rai ta ce, ""Ki yi wa mutane shiru, babu inda za ki je,"" ta ™arasa maganar da tsawar da tafi wacce ta yi da"

farko.

"Rumana ta yi baya da sauri a sanadin tsawa da Umma ta yi mata a karo na biyu, hawaye suka cicciko idanuwanta tana bubbuga kafafu ta ce, ""Amma yaya Junaid ya ce zai je da ni."""

Ita a dole sai ta je tunda Junaid ya ce zai je da ita.

"Umma ta yi mata mugun kallo ta ce, ""Ni kuma na ce babu inda za ki je."""

"Rumana ta fashe da kukan shagwaSa tana buga kafafu faWi take tana maimaitawa, ""Sai na je... Sai na je... Sai na je..."""

"Ta faWo a kasa tana murgina tana kukan banza tana faWin, ""Sai naje... Sai naje... Sai naje..."""

"""Amma Umma..."" Junaid ya fara magana sai dai bai ™arasa maganar ba Umma ta yi mashi kallon da ya saka sauran maganar ta makale a makoshinsa, ta murtu™e fuska ta ce, ""Ka yi min shiru a nan tun kafin in ci maka mutunci a gidan nan, babu inda za ta je, ka ji ni da kyau, babu inda Rumana za ta je, wannan shine abun da na ce kuma ya zama doka a wannan gida."" Ta mi™e ta haye bene a fusace tana faWa sosai, ta inda take shiga bata nan take fita ba."

"Junaid ya bita da kallo fuskarsa dauke da tsantsar mamaki, tana matu™ar kaunarsu, tana da kulafuci a kansu, ba ta kaunar dukkanin abun da zai Sata masu rai, har ya kai koda ba ta son abu idan suka nuna suna so tana masu, amma ya rasa dalilin da ya saka dukkanin lokacin da aka yi maganar zuwan Rumana garin Katsina take rufe idanu ta koma kamar ba ita ba, wannan ya sa Rumana ba ta taSa zuwa garin ba, ya rasa dalilin da ya saka Umma ta hana Rumana zuwa garin Katsina duk da ™anwar mahaifinsu ce take aure a garin."

"Rumana ta ™ara sautin kukanta, ya durkusa ya kamata ya janyota jikinsa yana rarrashi, ta yi lamo tana sauke ajiyar"

"zuciya, ""Kinga har kin Sata fuskarki, mu je in siya maki ice cream."""

"Ta ma™e kafaWa tare da turo baki cike da sangarta ta ce, ""Sai dai idan za ka boyani kuma za ka je da ni katsina."""

"Ya dungure mata hanci ya ce, ""Angama Ruma. Didi. Kamota-kamota,"" ya juya ta Wane bayanshi ya haye sama yana goye da ita suna dariya."

"Kai tsaye ya wuce da ita dakinta, da kanshi ya gyara mata fuska, ya bude closet dinta ya zaro mata doguwar riga kirar kimoni ya Waura mata akan riga da wando da ke a jikinta, ta Waura hula a saman kanta, ya kama hannunta suka fita, ""Za ki yi driving dinmu?"" Ya tambayeta. Ta girgiza kai ta ce, ""A'a."""

"Yana tu™i tana buga game a wayarsa idan ta yi nasara ta yi murmushi idan aka kamata ta Sata fuska gami da turo baki, kira ne ya shigo wayar yayinda SOULMATE da manyan ba™a™e ya bayyana Saro-Saro akan magijin wayar tare da hoton wata kyakykyawar budurwa."

"""Waye?"" Ya tambaya. Ta ce, ""Aunty Leeserh ce."" Bai yi yunkurin amsar wayar ba tunda ya san ba bashi za ta yi ba."

"Ta Waga kiran ta sakashi a amsa kuwwa, daga Waya bangaren aka ce, ""Salaam alaikum. Helloo."" Rumana ta ce, ""Didi ce."""

"Ta Waya bangaren Leseerh ta ce, ""Didin yaya Junaid, Kin wuni lafiya?"""

"Rumana ta amsa da, ""Lafiya lau."""

"Ta ce, ""Ki bani aron yayanki mana."""

"Rumana kanta tsaye ta ce, ""Ina game da wayar idan na gama zai kira."""

"""Alright then ´ar gatan yayanta,"" Leeserh ta ce ta tsinke kiran."

"Hajara ™awar Leeserh da suke tare ta ce, ""Kutuma, wacce mai karfin halin ce kika kira wanda zaki aura ta yi maki"

"haka."""

"Leeserh ta murmusa ta ce, ""Laa kee ™anwarsa ce fa."""

"""Shine har take da karfin halin da za ta yi maki haka, ni fa har shi sai naji ya ba ni haushi, matar da zaka aura ta kira"

"™anwarka ta hana."""

"""Hajara kenan, Junaid shine wanda zan aura, yana sona ina sonshi, yana yin haka ne saboda ya damu da ™anwarsa, amma mutum ne mai tausayi, mai hakuri, mai fahimta, ma'abocin ilimin addini, ba zan iya ce maki ga wani halinsa na banza ba, mutum tara yake bai cika goma ba, shi a nan weakness dinsa yake, Rumana ce weakness dinsa ni kuma na saka a raina don kawai ya damu da ™anwarsa ba zan ce zan rabu da shi ba, idan na rabu da shi akan wannan abun guda Waya ban san waye zan faWamawa ba, kinga kenan nayi kamun kafiyar Baidu, sakin na hannu kamun na dawa."""

"Hajara ta jinjina kai tace, ""Hakane kuma, abinci wani gubar wani, koda yake idan Allah ya yi Zaki zaici gatari sai a siyar da gatarin a sayi akuya."""

******

"A bangarensu Rumana, sai da ya kaita ta yi shopping ya siya mata ice cream sannan ya dawo da ita gida, da daddare bayan sun gama dinner kowa ya wuce bedroom dinsa."

"Umma tana lissafi, Rumana ta sameta, duk da Junaid ya ce zai tafi da ita amma ta san abun ba mai yiyu ba ne idan Umma ta hana. Kamar mai tsoron magana ta ce, ""Umma."""

"Umma ta dubeta ta ce, ""Ya aka yi autata?"" Jin haka ta turo baki ta ce, ""Bake ba ce ba kika yi min tsawa."" Umma ta yi dariya ta ce, ""Ayyerh torh yi hakuri autata na daina."""

"Jin haka ta ce, ""Katsina..."" Tun kafin ta ™arasa maganar Umma ta sakar mata tsawar da ya sakata fashewa da kuka irin na yara sangartattu, Umma ta murtuke fuska ta ce, ""Na ce ba ki zuwa katsina, idan hutu kike son zuwa ki shirya gobe ki bi flight ko train Abuja wajen Hajiya Maamaah, ko kuma ki tattara ki koma London dama a can kika saba rayuwa."""

"Rumana ta turo baki cike shagwaSa ta ce, ""Ni katsina nike son zuwa."""

"Umma ta nunata da hannu, da kakkausar murya ta ce, ""Ki Sace min daga gani!"" Rumana ta fara kukan shagwaSa tana bubbuga kafafu, da tsawa Umma ta ce, ""Za ki fita ne ko kuma sai na mareki."" Kalmar mari kawai da ta ambata ya saka Rumana fasa ihu tana dafe kuncinta kamar wacce aka mara da gaske."

Umma ta fusata ta wanka mata mari. Ta dafe kuncinta tare da fashewa da kuka ta fice da gudu tana kukan da idan mutum ya ji sai yayi tunanin yankata ake yi.

"Junaid yana zaune a kan gado yana waya da Leeserh, Rumana ta shiga dakin da gudu ta haye a kanshi tana dukan kirjinsa tana kuka. Hankalinsa a tashe yake tambayarta abun da ya faru, ""Didi mi ya faru?"""

"Ta yi shiru tana kuka ta tada mashi hankali sai da ya tambayeta a karo na ukku sannan ta ce, ""Umma ce daga na yi mata maganar zuwa katsina shine ta mareni, da gaske ta mareni, duba ka gani."""

"Ta nuna mashi kuncinta inda yatsun Umma ya kwanta, ya yi matu™ar mamaki duba da bata taSa dukanta ba har surutu ake yi mata a kan tana sangartasu da yawa."

"Ya ce, ""Mari kuma! Jirani ina zuwa."" Ya zura jallabiya a kan guntun boxer da ke a jikinsa sannan ya fita, kai tsaye ya wuce dakin Umma, ya ce, ""Umma!."""

"Da kakkausar murya ta ce, ""Idan garin ne ba ta son zama ta shirya gobe ta wuce Abuja wurin Hajiya Maamaah ko kuma ta sayi ticket ta koma London."""

"""Mi yasa sai Abuja ko London? Mi yasa ban da Katsina?"" Ya jefa mata tambayoyin fuskarsa dauke da tsantsar mamaki."

"Umma ta daka mashi tsawa ta ce, ""To ubana tutsuyeni in faWa maka ba'asi, Junaid ka juya ka fice min daga daki, Junaid ka Sace min daga gani."""

"Da sauri ya juya ya nufi kofa a sanadin tsawa da ta ™ara mashi a karo na biyu. Ya samu Rumana har ta yi bacci, hawaye ya bushe a saman fuskarta, shatin yatsu ya fito a kan kuncinta a daidai inda Umma ta mareta, abunka da rashin sabo da hutu da ya zauna a jikinta sai shatin yatsun ya fito Saro-Saro."

Ya lallaSa ya dauketa ya wuce da ita bedroom dinta ya kwantar da ita tare da ja mata blanket ya yi mata addu'a tare da kashe haske ya koma bedroom dinsa.

"Washegari da asuba suna gama salla suka koma barcin safe, Umma ta shiga kitchen ta zage ta haWa masu breakfast wanda ya kaita har wajen karfe bakwai, masu aiki suka jera a kan dinning table."

"Junaid yana tashi da safe dakin Rumana ya fara le™awa jin ™arar ruwa a bathroom ya zauna a gefen gado yana jiranta, yana chatting da Leeserh, har minti biyar ya yi bata fito ba ya mi™e ya fita zuwa dakinsa."

"Ta fito ta samu ba ya nan, ta yi mamaki tunda ta ji shigowarsa ta shirya ta fita zuwa dakinsa, yana jin motsinta ya"

"Wago ya ce, ""Zo ki gaisa da Leeserh."""

"Ya mi™a mata wayar da yake video call da Leeserh ta amsa suna hirar biki yayinda shi kuma ya mi™e ya wuce bathroom ya yi wanka ya shirya, har lokacin hirar tasu bata ™are ba ya amshi wayar ya ce, ""Bye love."" Leeserh ta ce, ""Take care, love you."""

Ya kama hannun Rumana suna tafiya tana mashi hira yana dariya suka nufi staircase.

"A tare suka sauko ™asa zuwa dinning table, kowane ya ja kujera ya zauna bayan da suka gaida Umma, ta amsa babu yabo babu fallasa, mai aiki ta yi serving kowa, Rumana ta tsurawa abincin idanu tana turo baki yayinda Junaid ya yi cokali Waya ya lumshe idanu yana jinjina basirar Umma a fagen sarrafa girki."

"Rumana ta tsakuri abincin ta kai baki, ta Sata fuska tare da furzar da shi, ta ture plate din tana yatsine fuska kamar wacce ta ga kashi ta ce, ""Ban cin wannan abun, babu WaWi."""

"Junaid ya kalleta ya ce, ""Na'am."" Da idanu ta yi mashi inkiya, shima sai ya ture plate din gabansa ya ce, ""Nima"

"Waurewa kawai ni ke yi amma abincin bai yi WaWi ba."""

"Umma ta dubesu cike da mamaki ganin sun mi™e, ""Ina za ku je?"" Ta tambaya. Rumana ta ce, ""Restaurant mu yi breakfast, wannan abincin babu dadi, yaji ya yi yawa, mai kadan, babu dadi kamar magani. Ko, Yaa Junaid?"" Junaid bai yarda sun haWa idanu da Umma ba ya ce, ""Ehhh haka ne."" Umma ta zuba masu idanu kawai, a kan idanunta suka fita."

"Junaid ya tsaya a compound ya ce, ""Didi ba ki kyauta ba, Umma ba za ta ji WaWi ba."" Ta Sata fuska kamar za ta yi kuka ta ce, ""Na Sata da kai tunda kaima ba ka son farin cikina, ka wuce ka bani waje na tsaneka."""

"Ya ware idanu ya nuna kansa ya ce, ""Kin tsaneni kuma?"""

"Ta girgiza kai ta ce, ""Ni ba haka na ce ba."""

"Ya tsareta da na mujiyarsa, ""Ba ki ce haka ba ko kuma ba haka kike nufi ba, uhmm, you don't say that, or you don't mean that?"""

"Ta ce, ""Ba haka nike nufi ba, bakina ne kawai ya faWa."""

"Ya tsareta da idanu ya ce, ""Ya faWi mi?"""

"Ta ce, ""Ya ce ya tsaneka."" (Ta yarda ta ce ta tsaneshi amma ta Waurawa bakinta laifi shi da ya furta) murmurshi ya yi ya kama kumatunta ya ce, ""Amma ni ina sonki didi, want a piggyback ride."" Ya juya ta haye bayansa ya yi sama da"

"ita yana gudu da ita a bayansa suna dariya har suka isa wajen motarsa, ta zauna a bangaren mai zaman hakanan yayinda yake jan motar."

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 3 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Umma tana tsaye daga balcony tana hangosu har motar ta fice daga gidan yayinda convoy na motoci biyu suka mara masu baya.

"Da misalin karfe biyu na rana bayan ya dawo daga sallar Zuhr suna zaune a garden tana bashi labari suna dariya, mai aiki ta zo da sakon Umma cewa, 'Abinci ya sauka.'"

"Junaid ya ce, ""Alright, muna zuwa."""

"Rumana ta yi karaf ta ce, ""Mun koshi."" Mai aiki ta yi tsaye tana tantama a kan maganar wa za ta faWa a cikin su."

"Junaid ya ce, ""But?"" Rumana ta kama fuskarsa ta fuskantar dashi zuwa gareta ta ce, ""Look at me. Look at me. Trust me, wannan ita kaWai ce hanyar da za mu bi Umma ta barka ka tafi da ni Katsina."""

"Ya yi jim yana nazari, ta marairace fuska, ya juya inda mai aiki take tsaye ya ce, ""Ki ce mata mun koshi."""

"Ta juya ta koma ciki, Umma da ke zaune a parlour ganin basu dawo a tare ba ta ce, ""Baki gansu ba ne?"" Jamila ta rusuna ta ce, ""Sun ce sun koshi."""

"Umma ta rasa bakin magana, ta ce, ""Okay, ki je."" Ta janyo ta wayarta ta kira numbar Junaid bugu Waya ya dauka, da kakkausar murya ta ce, ""Junaid ka sameni a parlour yanzu."""

"Jim kadan ya shigo kansa a kasa yana sosa ™eya, ta ce, ""Ka Wago ka kalleni da kyau, saboda na ce Rumana ba za ta je katsina ba shine kuka tsiri yin bore a kan abincina, to shikenan babu komai ka je da ita, amma ina san

Please Login or Register in order to submit comment