You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hangota, ya yi murmushi yana tako sadaf-sadaf ya nufo inda take kamshinsa ne ya sanar da ita zuwansa sai dai ba ta yi yunkurin Sata mashi bazatar da ya yi nufin ya yi mata ba."

"Ya kama kugunta ya yi sama da ita ta tsinko furen, ya sauketa yana sakar mata murmushi ya ce, ""Didi mi za'ayi da fure?"" Ta kalleshi sanye yake da yard mai tsaWa dinkin zamani fitet wanda ya zauna a jikinsa ya yi mashi kyau, yana baza kamshin designer perfumes, ta mi™a mashi furen ta ce, ""Ka yi kyau."""

"Ya amsa ya dora akan hancinsa yana shakar kamshinsa ya lumshe idanu ya bude ya ce, ""Kkoch gomawo."" (Na gode da furen flower). Ta ware idanu ta ce, ""Yau kuma yaren Korea ka koma."" Ya gyaWa kai yana gyara mata gashinta da yake reto yana rufe mata fuska. ""Eodi ga?"" (Ina zaka je)."

"Ya Wan kalleta ta ce, ""Hala baka gane ba."" Ya dai yi shiru yana murmushi. Ta gyaWa kai tana gyara mashi hular dara dake a saman kanshi. ""Ina zaka je?"" Ta tambaya da yaren hausa a wannan karon."

"Ya ce, ""Na ji abun da kika ce tun farko tun da na fiki iya yaren."""

"Ta ce, ""Na sani naga baka bani amsa bane shiyasa na ™ara tambaya."" Ya gyara tsayuwa ya ce, ""Gidan granny?"" Ta taSe baki ta ce, ""Ban zuwa gidan wannan tsohuwar mai mitar tsiya, haka kawai babu gaira babu dalili ta tusa mutum a gaba da mitarta marar dadi this and that."" Ya waro idanu waje ya ce, ""Idan Umma ta ji ki babu ruwana."" Ta ce, ""Gaskiya na furta halinta ne mita kaima ka sani."" Ya kama hannunta ya ce, ""Muje ki faWa mata da bakinki."" Ta waro idanu waje ta ce, ""Wai wa?"" Ya ce, ""Umma mana."" Ta fizge hannunta ta ce, ""Wannan salon mugunta ce, idan na yarda muje in hadiye muciya a zaune."" Ya goya hannuwansa a kirji ya ce, ""Ta ya zaki iya hadiye muciya a zaune,"

"abun ba zai yiyu ba sai dai a tsaye."" Ta ware hannuwa ta ce, ""Abun da nike ™o™arin faWa maka kenan, abun ba zai yiyu ba, ina zaman zamana in janyo ta daina min fara'a a gidan nan."""

"Ya ce, ""To ba za ki je gidan Hajiya Kaka ba, to ina za ki je?"""

"Ta yi jim sai kuma ta ce, ""Mu je tunda wata ranar idan aka yi sa'a tana da kirki, amma a motata za mu je."" Ya ja kujera ya zauna ya ce, ""Okay, ki dauko makulli."" Ta wuce ciki ta kofar baya jim kadan ta fito ya mi™e suka wuce parking space, shi kanshi parking space Win abun kallo ne saboda girmansa da ™ayatuwarsa, ga motoci birjik masu tsada da kyau sai kyalli suke suna Waukar idanu."

"""Kin faWawa Umma?"" Ya tambaya. Ta girgiza kanta, cike da halin ko in kula ta ce, ""A'a amma ko na sanar da ita ba za ta hana ba."""

"Ya jinjina kansa ya ce, ""A wacce motar za mu je a cikin motocinki?"" Ta nuna Jeef dake can gefe kaWan, ""Waccen Jeep din tunda ka siya min ita sau Waya na fita da ita."""

"Ji ta yi ya ce, ""Ba ki dauko mayafi ba."" Ta taSe baki ta ce, ""Rabu da Hajiya Kaka koda na yafa mayafin sai ta yi min"

"korafinta na kin ™arawa, ita fa tafi so mutum ya zunbula dogon hijab har yana sharar kasa."""

"Ta zauna a bangaren direba yayinda ya zagaya bangaren mai zaman hakanan, tana jan motar tana mashi hira yana murmushi, ya ce, ""Motar da na yi maki order gobe za ta iso."" Ta saki murmushi ta ce, ""Wow. Na gode sosai."" Ya ce, ""Babu godiya a tsakaninmu, Rumana idan har ina raye ba zan bari kiyi kukan rashin mahaifinmu ba, ki cigaba da yi min Waukar yaya kuma mahaifi."""

"A wani katon gida ta yi parking suka fito suka dugunzuma zuwa ciki, wata tsohuwa suka samu zaune a kan darduma tana addu'a, suka shiga da sallama, suka zauna suna jiran ta gama, sai da ta shafa addu'a sannan suka gaishe da ita, ta amsa da kulawa."

"Rumana ta ce, ""Baraka zo ki kawo min ruwa, kishirwa ni ke ji."""

"Hajiya Kaka ta kalleta sororo ta ce, ""Ba ta daukowa, na ce ba za ta dauko ba, lalacin da kika saba yi a gidan Aminar shine kika zo nan kiyi min, to ni ba zan dauka ba. Ina ce kina da kafafu da hannuwa don haka ki tashi ki dauko da kanki ko kuma ki fasa shan ruwan, bana son wannan shegen son jikin da Amina ta koya maki, wannan son yara da Amina take da shi ya yi yawa, ace katuwar budurwa kamarki amma ko ruwan zafi ba ki iya daurawa, ato ni dai nawa idanu."""

"Rumana was like, ""Calm down hajjaju idan kika ce ba zata dauko ba ya wadatar."" Hajiya Kaka ta fusata ta yi dakuwa, ""Da uwarki kike, ja'ira marar kunya."""

"Rumana ta turo baki ta ce, ""Yaa Junaid ruwa, ina jin kishirwa."" Gadararta shine tunda har Hajiya ta hana mai aikinta ta dauko mata, toh tana da yaya Junaid a kusa."

"Har ya mi™e Hajiya Kaka ta ce, ""Koma ka zauna, na ce bai zuwa, solobiyo kawai, ke kenan jira kake kaji ta ce uhmm ka tashi ka yi mata, ka koma ™anin ita yayar."""

"Junaid ya koma ya zauna jiki babu kwari. Rumana ta Waga murya ta ce, ""Allah ba ya son mai raba zumunci, raba zumunci haramun ne."" Hajiya Kaka ta taso mata, ""Maganarki gaskiya ce, sai dai ™arya kike yi min domin ban raba zumunci ba, shegen hali da son jiki da ganda ne na hana."""

"Rumana ta Sata fuska kamar za ta yi kuka tana mita Hajiya Kaka ta ce mata makaryaciya, ta ce mata bakin hali."

"Junaid ya bata fuska ya ce, ""Ke wannan tsohuwar matsalata dake kenan sai mutum yazo da ™anwarsa ki saka mashi ita kuka. Daga zuwanmu shine har kina neman ki saka min ita kuka, idan baki maraba da mu ne sai mu tashi mu bar maki gida tunda dai ba ki yi murnar ganinmu ba."""

"Hajiya Kaka ta yi mashi dakuwa tana faWin, ""Ko ubanka Abdurrahman ya yi kadan ballantana kai da aka haifa ina da furfura a kaina, za ta tashi ta dauko ruwan ko kuma sai na yi mata Wan banzan duka."""

"Junaid ya yi shiru domin abun ya fi karfinsa, Rumana ta taSe baki ta ce, ""Allah ya ba ki hakuri, da alama kinyi dambe lokacin da kina yarinya, ni ba zaki tuna yarintarki da ni ba."" Hajiya Kaka ta cika tayi fam ta yi kwafa tace, ""Ya fi maki, idan kina tantama kuma ki yi magana sai in nuna maki samfuri."""

"Rumana ta mike ta nufi hanyar kitchen tana faWin, ""Aniyar kowa ta bi shi, Allah ka shiryi masu neman fitina, fitina tana kwance a kasa, Allah ya la'anci mai tayar da ita."" Hajiya Kaka ta ce, ""Miye?"" Rumana ta ce, ""Ba da ke nike ba, sai shegen son kira kamar tsohuwar zawara."""

"Saura kadan dariya ta kufcewa Junaid ya fuske ya basar, Hajiya Kaka ta ce, ""Da uwarki kike."" Ta juya wa Baraka, ta ce, ""Baraka ki kawo masu dambun kaza."" Rumana ta dauko ruwa ta dawo tana turo baki ita a dole ta yi fushi tunda Hajiya Kaka ta zagar mata uwa."

"Hajiya Kaka ta dubeta daga sama har kasa, Rumana cikin ranta ta ce, ""Ba ta gama wata mitar ba har ta fara tunanin wata, mutum ba ya da gadonka amma ya nemi gadon maganarka ya saka a bakinshi."""

"Hajiya Kaka ta juya tana kallon Junaid ta ce, ""Junaid da hankalinka da tunaninka ka tusota gaba ku ka zo biyo santa babu mayafi babu hijabi."" Rumana ta yi karaf ta ce, ""Ba santa muka biyo ba, a motata muka zo."""

"Hajiya Kaka ta kalleta shekeke ta ce, ""Har ni zaki faWawa mota torh tun kafin a haifi wanda ya siya maki motar nike hawanta."""

"""A haka kuma nike hawan wadda ta fi ta ki tsaWa,"" Rumana ta yi magana ciki-ciki. Junaid ya fashe da dariya na diramar Hajiya Kaka da Rumana."

"Hajiya Kaka ta ce, ""Ku rin™a yi wa kanku faWa, kun tusa yarinya a gaba babu cas babu as sai dai ta yi abun da ranta yake so, idan mutum ya yi magana ace ya cika mita, to dai Wiya mace take kuma wata rana gidan wani za ta je hakazalika muna rayuwa ne amma bamu san abun da gobe za ta haifar ba."""

"Rumana ta kalli kanta, riga da wando ne a jikinta, rigar ta sauko har ta wuce kugunta, ta rufe kanta da hula, ta turo baki kawai yayinda Junaid ya ce, ""A mota muka zo fa."""

"Hajiya Kaka ta dubeshi shekeke ta ce, ""Ohh, ya yi kyau. Na faWa kuma a yau zan ™ara faWa idan ba za ku iya ni ku kawo min ita inyi mata tarbiyya."" Junaid ya saka dariya yana hango Rumana a gidan Hajiya Kaka zaman dindindin. Tabbb ko na wuni Waya ba zata iya ba, za ta gudu koda kuwa a kafafu ne sai ta nemi hanyar gidan Umma"

"Baraka ta kawo masu dambun kaza cike da plate, haka suka wuni a gidan, Junaid yana dariyar diramar Hajiya Kaka da Rumana, su yi faWa su yi WaWi."

"Saida marece sannan suka fara haramar komawa gida, Rumana ta murtu™e fuska ita a dole ta yi fushi tunda Hajiya"

Kaka ta zagar mata uba wanda yake kwance a kabari.

"Hajiya Kaka ta ce, ""To uwata yi ha™uri tunda nayi maki laifi, a yafi juna domin nidai ban kullaci kowa a raina ba."""

"Da murya ciki-ciki Rumana ta ce, ""Ai dama dole zaki ce mu yafe tunda kin san baki kyauta ba, tunda muka zo kike tada zaune tsaye, ke a dole sai kin binciko abun magana kin tsoma bakinki a ciki."""

"Hajiya Kaka ta ce, ""Na'am."" Rumana ta ce, ""Cewa na yi Allah ya yafe mamu baki Waya."" Hajiya Kaka ta ce, ""Amin."""

"A wannan karon Junaid ne ya amshi ragamar tukin yayinda escorts dinsu sukayi masu convoy, babu kowa a parlour"

"suka le™a kitchen suka samu Umma tana girkin dare, Rumana ta rungumeta ta ce, ""Nayi kewarki Ummana."""

"Umma ta ce, ""Nima nayi kewarki Didi."" Junaid ya ce, ""Barka da aiki Umma."" Umma ta ce, ""Barkanmu."" Ya ce, ""Sakonki na wajen Hajiya Kaka yana a parlour."" Ta ce, ""Okay, ka wuce min da shi bedroom."""

"Rumana ba ta yi tunanin kamawa Umma ba ita kuma Umma bata ce mata ta kama mata, ta haura sama ta yi wanka ta kwanta a parlour tana kallo yayinda Junaid ya fita wajen abokansa."

"Tunda ta tashi washegari maganganun da Al'ameen ya yi mata suke ci mata tuwo a ™worya, har ita wannan Wan tahalikin zai yi wa gadara, ji take kamar ta sameshi ta cigaba da kwallo dashi har sai ta ji fushinta ya ragu, da ace za ta haWu da shi da babu tantama sai ta saka escort dinta sun yi mashi dukan tsiya."

"Ta fito balcony ta ja kujera ta zauna tana turo baki tana kwafa idan ta tuna abun da Al'ameen ya yi mata a garin Katsina sai ta ji kamar ta fasa ihu, tana ta kwafa ita kadai har Umma ta lura ta tambaya, ""Miye?"""

"Zuciya ta kawo mata wuya tabbacin yadda abun yake kona mata rai, ta yi subul da baka tace, ""Da mi yake takama da"

"har zai yi min magana da gadara,"" ta ™arashe maganar da karaji."

"""Waye?"" Umma ta tambaya."

"Rumana ta yi kwafa a karo na adadin da ita kanta ba ta sani ba sannan ta ce, ""Wannan saurayin wanda na hadu da shi a garin katsina, dukkanin lokacin da na tuna abun da ya yi min sai in ji ban iya kyalewa, har yana da karfin halin da zai iya duban tsabar idona ya yi min magana da gadara yana cewa in durkusa a kan kafafuna in rokeshi."""

"Umma ta daka mata tsawa, ""Ke! Ba na hanaki magana a kan dukkanin abun da ya shafi wannan abun ba."" Rumana ta yi baya da sauri ta ce, ""Amma ya raina min hankali ne, ya yi min magana da gadara."" Umma ta fusata ta daka mata tsawa a karo na biyu ta ce, ""Ke wacece da ba za'a raina maki hankali ba, ke wacece da ba za'ayi maki magana da gadara ba, kika wuce sakarai, banza, wofi. Idan kika ™ara maganar da ta danganci abun da ya faru a katsina sai na zaneki."""

"Rumana ta yi rau-rau da idanu kamar za ta yi kuka, Junaid ya fito yasha gayu ya kure kyau yana baza kamshi, yana daura wristwatch ya ce, ""Umma, na tafi."" Umma ta ce, ""Allah ya kiyaye hanya."" Ya maida dubansa akan Rumana dake faman taSe baki ji take kiris ta fashe da kuka, ya ce, ""Waye ya taSa min ke?"""

"Za ta yi magana, Umma ta daka mata tsawa a karo na ukku ta ce, ""Ki yi min shiru a nan tun ban mareki ba, sai in yi kwallo da ke a wajen nan."" Junaid ya ce, ""Subhanallahi, mari kuma?"" Umma ta fusata ta ce, ""Ehh ko kana da magana ne, yanzu in fara buga misali a kumatunka ta gani ganin idanunta."""

"Junaid ya ware idanu, lallai abun babba ne, Umma ta murtuke fuska ta ce, ""Ta ™ara yi min maganar ta gani idan ban rufe kofa ba nayi mata Wan banzan duka na barta a kwance ba, mu gani idan kai da ta ke takama da kai idan ka isa ka yi magana ka gani idan ban haWa da kai nayi maku shegen duka ba."""

"Junaid ya yi shiru domin abun ya fi karfinsa, Rumana tayi rau-rau da idanu ta ce, ""Yaa Junaid zan bi ka mu tafi tare tun kafin ka barni da Umma ta rufeni da duka tunda ta daina sona, magana kaWan sai ta ce za ta yi min duka."" Junaid ya mi™a mata hannu ya ce, ""Ta so mu je dama wajen Leeserh zan je."""

"Rumana ta warware mayafi dake a saman kanta ta yi lullubi da shi, ya kama hannunta suka fita zuwa parking space, yana tuki yayinda ta kwantar da bayanta a kujera ta lumshe idanu ta yi shiru tana kitsa yadda za ta rama abun da Al'ameen ya yi mata, har suka ™arasa gidan ba ta sani ba tana can ta lula a duniyar tunani tana tukfa da warwara, sai da ya taSota sannan tasan sun zo gidan, ta Salle murfin motar ta fita ta zauna a kan bayan motar tana buga game, ya tsaya kusa da ita, yana leken wayar yana mata hira suna dariya."

"Katon gida ne sosai, wata kyakykyawar budurwa ´ar kimanin shekaru ashirin da hudu ta fito daga cikin gidan, kalar chocolate ce, doguwa mai kyawun jiki samfurin slender, tana sanye da umbrella gown, ta kashe Waurin kallabi, mayafinta a kan kafaWa, tana tafiya tana baza kamshi da kyakykyawan murmushi akan fuskarta, khaleesat kenan wacce Junaid zai aura."

"Junaid ya juya tare da kafeta da na mujiyarsa yana kallonta ba ya koda kyaftawa da murmushi kwance akan fuskarsa,"

"yana kallonta tana ™ara yi mashi kyau a idanu har ta ™araso tana faWin, ""Rumana ´ar gatan yayanta game kike yi?"""

"Rumana ta Wago ta ce, ""Ehh Aunty Leeserh, da girman kujerarki amaryar next month."" Daga haka ta maida dubanta akan majigin wayarta. Leeserh ta ce, ""Yau kin yi mashi rakiya kenan?"""

"Hankalinta a kan game da take bugawa ta gyaWa kanta tana faWin, ""Kinga na manta ban gaishe da ke ba. Ina wuni?"" Leeserh ta amsa da, ""Lafiya lau."" Junaid da neman magana ya ce, ""Amma da muka tashi da safe ni baki gaidani ba, kuma da sha biyu ya yi baki gaidani ba."""

"Rumana ta Wago ta ware manyan idanunta a kansa na tsayin lokaci sannan ta ce, ""To ina kwana? Ina wuni?"" Daga"

"haka bata ™ara magana ba, ya lakuci hancinta yana faWin, ""Yauwa ta wajena, Didin yaya Junaid, kamota-kamota."""

"Leeserh ta ce, ""Ki shiga wurin Hajjo kusha hirar yaushe gamo."" Rumana ta girgiza kanta ta ce, ""Kai, a'a gaskiya, don ba ni da gaskiya, ranar ta yi min faWa a kan saka hijab kuma ban saka ba, ku tafi abunku ina nan ina buga game abuna."""

"Khaleesat ta girgiza kanta ta ce, ""A'a muje."" Ta wuce lambun gidan, Junaid ya kama hannun Rumana suka bi bayanta."

"A nesa da su ta ja kujera ta zauna, Allah ya kamata Aunty Hajjo ta fito ta ganta aikuwa tasha faWan da sai ta yi dana sanin biyoshi da ta yi."

"Aunty Hajjo ta murtu™e fuskarta ta ce, ""Na ce ina hijabinki, a mota kika mantoshi ko kuma tun daga gida kika fito"

"haka kidigai-kidigai."""

"Rumana babu bakin magana saida idanu ta yi tsuru-tsuru kamar ka ce kyit ta gudu, Aunty Hajjo ta daka mata tsawa ta ce, ""Ba da ke nike magana ba, ko nima gadarar taki zaki nuna min."""

"Rumana ta ce, ""Uhmm."""

Aunty Hajjo ta tusata a gaba har falo tana tambayar ba'asi fitowar da tayi babu hijab babu mayafi.

"Rumana ta yi rau-rau da idanu tana faWin, ""Ayyerh Aunty Hajjo ki yi ha™uri."" Aunty Hajjo ta kwalawa Farida kira ta"

"ce, ""Farida zo ki Wauko min dorina in nuna mata na fi ta taurin kai."""

"Rumana tana jin zancen bulala ta mi™e zata gudu, Hajjo ta ce, ""Dawo ki zauna ko kuma kina fita in hada har da shi"

"Junaid din da yake daure maki kugu in zanneku."""

"Jin za'a zane Junaid Rumana ta dawo ta zauna tayi tsuru-tsuru da idanu ta ce, ""Ayyerh ban dinka ba, waccen da kika bayar ya yi min yawa na baiwa mai aikinmu."""

"Aunty Hajjo ta cika da al'ajabi, ""Saboda ban isa in sakaki kiyi ba shiyasa kika dauki hijaban kika bayar saboda ki nuna min ban isa dake ba."""

"Rumana ido ya raina fata ganin Farida ta kawo dorina, gashi dai za ta ci duka ga shi babu mai cetonta. Tana yarfe"

"hannuwa tana hawaye ta ce, ""Ayyerh na tuba bazan ™ara yawo da ™aramin mayafi ba."""

"Aunty Hajjo ta ce, ""Ni dake shege ka fasa Wan halak sai yanka tunda har ita Aminar ba zata iya maki tarbiyyar ba sai ni inyi maki da kaina."""

A LAMBU

"Tunda Aunty Hajjo ta shiga da Rumana ciki hankalin Junaid kacokam ya koma a can, har Leeserh ta lura ta ce, ""Ba fa dukanta za ta yi ba."" Ya ce, ""Ba dukan ba, idan ta sakata kuka akwai daru."" Leeserh ta gumtse dariyar dake neman kufce mata na yadda yayi tsuru-tsuru da idanu kamar shine aka tutsuye, ta ce, ""Ko muje in rakaki kayi rescuing dinta."" Ya ce, ""A'a fa, ranar da na shiga tasowa tayi da bulalarta a hannu zata haWa da ni ta zanemu."""

"Leeserh ta fashe da dariya tana faWin, ""Kai Hajiya Hajjo tana shigar maku hanci ta kudundune kuma babu yadda kuka iya da ita, duk garin nan ita da Hajiya Kaka ne kawai suke taSa Didi a zauna lafiya ba'a yi wallahi tallahi ba."""

"Ya yi yake ya ce, ""To ya muka iya? FaWan da ya fi karfinmu ai dole muke mayar da shi wasa."" Ta gyara zama ta ce, ""Amma sun fi ku gaskiya ya kamata ana kwaSarta ba wai komai ta yi a mayar da shi daidai ba."""

"Junaid ya Sata fuska ya ce, ""Yarinya ce fa, duka-duka nawa take."" Sanin ba amsar shawarar zaiyi ba sai ta ce, ""Haka ne kuma, da wannan don wannan."""

Daga haka ta sauya hirar tun basuyi bara-baran akan lamarin Rumana ba.

A PARLOUR

"Aunty Hajjo ta juya ta mayar da dubanta inda Farida take ta ce, ""Farida Wauko min sabbin hijaban da aka dinko maki."" Rumana tana jin haka ta yi karaf ta ce, ""Zan yi wa yaya Junaid magana sai a dinka min akan hanyarmu ta komawa gida."""

"Ita a dole ta yi mata dubara don kada ta amshi hijabin a yi mata faWan ba ta sanya ba, Aunty Hajjo ta yi mata banza."

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 5 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

"Babu jimawa Farida ta kawo leather cike da hijabai wadanda yawansu zai kai goma, Rumana ta amsa tana zuba godiyar dole."

"Aunty Hajjo ta ce, ""Ba godiya ba, ki Wauko Waya ki saka."" Ta yi jim, Aunty Hajjo ta daka mata tsawa, ""Zaki saka ko kuma sai tsumagiya ta fasa maki baya tukunna."""

"Rumana tana jin maganar duka ta fara hawaye, hannunta har rawa yake wajen fiddo hijabi ta warware tana faWin, ""Bai gogu ba sosai."""

"Da maganar ta kashe Aunty Hajjo ba tace da ita uffan ba, saidai kallon da ta yi mata kansa magana ce mai zaman kanta domin ya isar da sakon da ta ke son isarwa."

"Rumana tana hawaye ta zura hijabin, Aunty Hajjo ta ce, ""Good kuma daga yau idan kika ™ara zuwar min gida da mayafi akan kafaWa sai na rufe kofa na zaneki, idan kin gadama kije ki bayar ki Wagewa gidana kafa inje har gidan naku in zaneki a gaban ita Aminar da Junaidun inga idan a cikinsu akwai wanda ya isa ya tambayi dalili."""

"Rumana ta mi™e kanta a likafa ta fice tana Wauke da katuwar leather din, ta wuce ta compound taba Waya daga cikin masu basu tsaro ya saka mata a mota har ta shiga mota Farida ta fito ta kirata wai Aunty Hajjo ta ce ta je ta ci abinci, har za ta ce ta koshi ko mi ta tuna sai kuma tabi bayanta, a ranta tana addu'ar Allah ya sa ba tuwo bane ba, don ko tana amai sai Aunty Hajjo ta sakata ta cinyeshi, wannan fitar da ta yi shi ake kira da ba'a rabu da bukar ba an haifi abu, ta yi gudun gara ta faWa gidan zago, ta yi gudun faWan Umma ta zo ta tarar da na Aunty Hajjo."

"Tana ido hudu da faten doya ta sauke ajiyar zuciya ta zauna tana tsakurar abinci tana danna waya, Aunty Hajjo ta fizge wayar ta ajiye saying, ""Idan kin gama cin abinci sai ki yi dannar waya tukunna."""

"Dole ta ha™ura da chat da takeyi har saida ta gama cin abincin, Aunty Hajjo ta zubo mata dambun nama, ""Ga shi ke"

"da yayanki."" Ta amsa ta yi godiya."

"Junaid ya shigo ya gaishe da Aunty Hajjo, tunda Junaid ya shigo yake satar kallonta ya ce, ""Aunty Hajjo kuma hijabin ya yi mata kyau, Wow, Masha Allah, Didi you look lovely."""

"Aunty Hajjo ta ce, ""Sai ku rin™a mata faWa tana sakawa ba wai mu saka yarinya a gaba ba babu cas babu as saidai komai tayi ku lankwasa ku ce daidai

Please Login or Register in order to submit comment