You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gareshi na kunya ba ta kama hannunsa zuwa dinning table, ya cire hannun ya ce, ""Zan bi ki ai."""

"Ta Wan dubeshi ta ce, ""Miye don na rike hannunka?"" ya yi kasa kasa da murya ya ce, ""Ammi tana kallo fa."""

"Da karfinta ta ce, ""Ko tana kallo sai mi, ina ce hannun yayana na ri™e, kai fa muharramina ne."""

"Maganarta ta farko kunya ta sakashi ita ce ta faWa amma shi ta bari da kunya domin yana da tabbaci a kan Ammi ta jiyota. Sai dai a kan furucin da ta yi daga baya, abun ya dakeshi ba kaWan ba, ita kuwa ko a jikinta wai an tsikari kakkaura."

"Yana gaba tana biye da shi tana murmushi, ya ja kujera ya zauna, ta saka plate a gabansa da fara'arta ta ce, ""Dambu ne da wainar shinkafa da miya. Wanne zaka fara ci?"""

"Ya murmusa yana binta da kallo ya ce, ""Wanda Didin Junaid ta zuba man."""

"Rumana ta yi murmushi, ta zuba mashi dambu wanda ya ji kayan lambu, tunda daga kamshin abincin yasan dole a tashi kansa da wannan girki, ya yi loma Waya yayinda yanayin fuskarsa ya sauya ya kafeta da kallo, ta yi tsuru-tsuru"

da idanu tana tarabbabin ka da abincin ne bai yi WaWi ba kuma tayi wujiga-wujiga idan girkin baiyi WaWi ba sai taja Allah ya isa.

"Junaid ya murmusa hakan ya saka hankalinta ya kwanta, abincin ya yi dadi kenan, ya ce, ""Kin tabbata da kanki kika girka dambun nan?"""

"Ta kama hannunsa tana murmushi ta ce, ""Da kaina na girka."""

"Ya ware idanu ya ce, ""Kai, Kai, Kai, To Allah ya karo zakin hannu, ya yi dadi sosai, ki saka min waigi kafin in fara santi."""

"Ya Waura hannu a kan hular da ke a kansa ya karyata ya ce, ""Didin Junaid abincin nan naki ya yi dadi na karya maki hula."""

"Rumana ta fashe da dariya, yana santi tana mashi dariya, ya kafeta da idanu yayinda kyawunta yake kara bayyana a gareshi, bai taba mata kallon gane kyawu ba sai a wannan ranar kuma ya yarda ita din mai kyawu ce ajin karshe, kyau ma™urar haWuwa."

"Ta ja kujera ta zauna tare da zuba mashi idanu tana kallon yadda yake cin abincin cike da nutsuwa yana lumshe idanu, yana cin rabi ta kwace farantin sanin ba zai iya cin abun da ya haura plate Waya ba, ya dubeta ya ce, ""Miye haka?"" Ta ce, ""Wancen zan zuba maka."" Ya waro idanu ya ce, ""Amma ban koshi ba kuma ya yi dadi."" Ta ce, ""Masar zan zuba maka itama ta yi dadi."""

"Ya lumshe idanu ya buWe ya ce, ""Allah ya yi maki albarka, zuba min inji idan shima ya yi dadin sai inci tunda ba'a"

"san maci tuwo ba sai miya ta ™are."""

"Ta zuba wainar shinkafa da miya har da kaza, yana ci yana haWa wa da naman kazar da ya yi dadi yana mata santi tana dariya, suka lalace a dinning table sai da ya ji babu waje sannan ya kora da zobo."

"Rumana ta saka rigimar sai dai ya bata da kansa, sai da ya leka yaga Ammi bata falon sannan ya yarda ya bata abincin sai dai shagwaSa da ta ke yi yana sakashi a wani yanayi."

"Har da Jidderh za su tafi, Ammi ta rakasu har wurin mota, masu aiki suka saka masu kaya a booth, Ammi ta ce, ""A kula, Allah ya tsare hanya."""

"A tare suka amsa da, ""Amin."""

"Jidderh ta buWe gidan baya ta shiga yayinda Rumana take a bangaren mai zaman hakanan a gefen Junaid, suka kama hanyar airport."

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 12 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

"Rumana ta koma sukuku. Ba wai tana jin wani takamaiman ciwo bane amma zuciyarta cike take da wani yanayi da ta kasa fahimta, tana jin kamar akwai abun da ke damunta amma kuma ya Suya, ya ™i bayyana ballantana ta nemi maganin maganceshi. Ta rasa abun da yake mata daWi, ta kuma rasa abun da ke saka mata damuwa. Komai ya rikice mata."

"Junaid da ke zaune a gefenta ya dade yana kallonta, yana lura da yadda ta yi shiru. Ya matsa kusa da ita, ya kirata a hankali, ""Didi."""

"Amma shiru ba ta motsa ba, idanunta a rufe kamar wacce take barci, amma a zahiri ba barcinta ta ke yi ba, hankalinta yana yawo a wani wurin daban."

"Ya sake cewa cikin damuwa, ""Didi, mi yake damunki ne? Ko hira ma kinki ™i yi min?"""

"Ta Wan motsa lebenta kaWan, amma ba ta buWe idanunta ba. Murya a raunane ta ce, ""Haka nan nike jina wani iri."""

"Amsarta ta saka Junaid ya ™ara shiga damuwa. Rumana ™anwarsa yarinya ce mai fara'a da annashuwa, wacce kullum"

"take cike da dariya da raha. Yanzu kuwa kamar an sauya ta, an Wauke mata walwalarta an bar mata damuwa."

"Jirgin yana ci ga ba da tafiya, amma a gareta kamar lokaci ya tsaya, tunani kala-kala yana yawo a zuciyarta, amma babu Waya da take iya kamawa ta fahimta."

Da ™arfe biyu na rana jirginsu ya sauka a garin Kaduna. Convoy suka tarar motoci masu tsaWa sai she™i su ke yi suka

tarbe su.

"Rumana ba ta damu da komai ba, ba ta damu da tsaron da ke zagaye da su ba, ba ta damu da gaisuwar da ake musu ba. Ta kutsa kai cikin mota, convoy din motocin su ka yi escorting dinsu zuwa gida."

"Motocin suna parking a harabar gidan, direba bai gama parking ba, ta buWe murfin motar da sauri ta fito kamar wacce ake bi, kai tsaye ta nufi cikin gidan da gudu tana faman kiran, ""Umma! Umma!! Umma!!!"""

"Muryarta tana rawa, cike da tashin hankali da ita kanta ba ta san dalilinsa ba. Ta shiga falon, idonta na yawo kamar wacce take neman mafaka."

"Zuciyarta na ayyana mata watakila idan taga Umma ta samu sassaucin abun dake damunta, watakila ganin Umma"

"Win zai iya kawo mata nutsuwa, ya warware mata wannan Waurin da ke damunta a zuciya."

"Ta rungume Umma tare da fashewa da kuka tana faWin, ""Na yi kewarki Umma."""

"Umma ta share hawayen da suka zubo mata ta ce, ""Nima na yi kewarki Rumana."""

"Junaid ya shigo tare da Jidderh, Jidderh ta gaishe da Umma, ""Umma Ina wuni?"""

"Umma ta amsa da, ""Lafiya lau."" Ta dora da faWin, ""Ya hanya?"""

"Jidderh ta amsa da, ""Alhamdulilahi."""

"""Ya kuka baro mutan gidan?"""

"""Lafiya lau."""

"Umma ta maida dubanta akan Rumana ta ce, ""Rumana ki wuce da ita dakinki ku yi wanka, zan saka masu aiki su kawo maku abinci."" Rumana ta gyaWa kai."

"Umma ta ce, ""³ata Jidderh, Allah ya huta gajiya."" Jidderh ta amsa da, ""Amin."""

"Suka haura sama, Rumana ta fada akan makeken gadonta tare da sakin murmushi ta ce, ""Gida, Gida ne, duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi."""

"Sai da Jidderh ta yi wa gidan kallon nutsuwa sannan ta gane mahaukacin girman da ya ke dashi da zunzurutun dukiyar da aka kashe a wajen ginashi, a yadda gidan yake da girman gaske za'a iya dauko gidansu a saka a gidan ba tare da gidan ya rage filin azo a gani ba."

"Washegari aka fara gudanar da hidimar biki, gida ya cika makil da ´an uwa da abokan arziki, kowa na ta hidimarsa, ana kai-komo, ana dariya, mata suna ta rangada guda ana farin ciki amma duk wannan annashuwa ba ta shafi Rumana ba."

"Duk irin burin da ta dade tana yi a zuciyarta game da bikin yaya Junaid, duk yadda ta yi mafarkin wannan rana da yadda za ta shiga ta fita ta yi rawa ta nuna farin cikinta amma sai gashi yau komai ya sauya. Wani irin yanayi ne ya lullubeta wanda ita kanta ta kasa fassara shi. Ba ciwo ta ke ji kai tsaye ba, amma zuciyarta cike take da wani nauyi da damuwa marar suna."

"Tun da suka iso, ta killace kanta a cikin daki. Hayaniyar waje na shigowa kunnenta, amma kamar tana wani duniyar daban."

"Duk kiran da ake yi mata ana ce mata amara kirjin biki tazo ta tarbi baki amma sai ta ki amsawa. Idan aka matsa mata sai ta ce, ""Ba ni jin dadi,"" ta rufe kanta da bargo kamar mai tsananin ciwo."

Sai an tashi tafiya program sai ta yi likimo akan gado ta ce bata da lafiya.

"Junaid ya shiga damuwa matu™a gaya domin bai taba ganin Rumana a cikin irin wannan hali ba, musamman a rana"

"mai muhimmanci irin wannan. Ya shigo dakin da kansa, ya zauna kusa da ita yana dubanta da damuwa a fuskarsa."

"""Didi, me yake damunki haka? Ko wani abun ne aka yi maki?"" ya tambaya cikin sanyin murya."

"Rumana ta juya gefe ba tare da ta kalle shi ba, ta ce da kyar, ""Haka kawai nike jin ba na jin dadi."""

"Bai gamsu ba. Ya daura hannunsa a goshinta ya auna zafin jikinta, amma bai ji wani zafi ba. ""Mu je asibiti a duba ki,"" ya fada da kulawa."

"Nan take ta tashi zaune, idanuwanta suka cicciko da hawaye. ""A a, don Allah yaya, ba sai mun je ba, zai wuce,"" ta fada tana kokarin danne kukanta, amma sai ta kasa, kuka ya kubce mata."

"Kukan nata ya kara rikita Junaid. Bai taba ganin ta cikin irin wannan tashin hankali ba. Ya yi kokarin lallashinta, amma duk da haka ta nace akan cewa ba za ta je asibiti ba. Har ta kai ga kuka mai tsanani, wanda ya sa dole ya hakura da maganar, duk da cewa zuciyarsa cike take da damuwa."

"Ya fita daga dakin jikinsa a sanyaye, zuciyarsa babu dadi. A waje ana ta shagulgula, ana kiran sunansa, ana bukatarsa a wurare daban-daban, amma hankalinsa gaba daya yana akan Rumana. rashin sukuninta ya dauke masa walwala, ya kasa maida hankali akan komai."

"Dukkanin inda ya je, zuciyarsa tana cikin dakin da ta ke. Duk dariyar da yake yi ta tilas ce, ba daga zuciya ba. A ransa tambayoyi ne suka cika masa kai, me yake damun Rumana? Me ya sauya masa ita haka a lokacin farin ciki irin wannan? Farin cikin wannan biki bai cikar masa ba, matukar Rumana tana cikin wannan hali."

"Yayinda Junaid yake cikin wannan rudani, hidimar bikin na ci gaba da gudana. Ana ta kiransa daga nan zuwa can, ana tambayarsa shawara, idan ya yi baya sai abokai su ™ara janyoshi suna nuna mashi shi ne ginshikin bikin, amma duk da haka walwalarsa kalilan ce. Idan ya amsa, amsawar ba ta da kuzari, idan ya yi murmushi to na dole ne."

"A gefe guda kuma, Rumana na cikin daki tana kokarin danne abun da ke cin zuciyarta. Ta rufe ido tana jin hayaniyar waje tana damunta kamar ana yi ne a karkashin kunnuwanta, tana jin komai ya fice mata daga kai. Ba ta iya fahimtar kanta; ko bakin ciki ne, ko kishi, ko wani abu da bai gama bayyana ba."

"Ta mike ta zauna a gefen gado, ta daura hannayenta a kanta. ""Me ke damuna haka?"" ta tambayi kanta amma ta tuna ta ™ara tunawa amma babu amsa, kanta ya cunkushe ta matsa ta ™ara matsawa amma babu abun da ta tuna tamkar wacce take lalube a inuwa. Babu abun da tunanin ya tsinana mata sai wani nauyi da ya kara mata a kirji."

"Bayan lokaci Junaid ya sake dawowa, ya tsaya a bakin kofar dakin na ´an dakiku kafin ya tura kofa ya shiga."

"Idanunsa sun cika da gajiya da damuwa, amma ya kokarta ya boye su."

"""Rumana,"" ya kira sunanta yana zama a gefe."

"Ta dube shi da idanunta da har lokacin suke dauke da alamun kuka. Bai yi magana ba, ya dauki minti yana kallonta yana neman amsar tambayarsa a fuskarta."

"""Rumana ki yi hakuri da duk abun da yake faruwa, na tambayeki kin ce babu komai amma zuciyata bata nutsu da wannan amsar ba, a jikina ina jin kamar kina boye min wani abu. Rumana Idan wani abu ne yake damunki ki fada min, ba zan iya jurar ganin ki a haka ba."""

"Ta juyar da kanta gefe, muryarta na rawa ta ce, ""Babu komai, kawai ba na jin dadi ne."""

"Junaid ya ja lumfashi mai nauyi. Ya san wannan amsar ba cikakkiya ba ce. Amma kuma ya ga idan ya matsa, za ta sake shiga wani sabon tashin hankalin sai ya mike daga inda yake ya koma kusa da ita sosai, ya rage tazarar da ke tsakaninsu. ""Ki dube ni,"" ya ce cikin sanyi."

Ta yi jinkiri kafin ta daga kai ta kalle shi.

"""Na dakatar da komai a waje saboda ke,"" ya faWa da gaskiya a muryarsa sannan ya dora da faWin, ""Idan kina cikin damuwa, farin cikina gushewa yake yi. Don Allah ki barni in taimaka maki ko akan me ne ne."""

"Wadannan kalaman nasa sun motsa zuciyarta. Ta ji wani abu ya tsinke a kirjinta, amma har lokacin ba ta iya bayyana abun da ta ke ji ba domin itama kanta ba ta san miye ba. Hawaye suka sake gangarowa daga idanunta ba tare da izini ba."

"""Ni kaina ban san mi yake damuna ba,"" ta furta a hankali, tana jin kunyar kalaman nata musamman ganin yadda ya damu."

"Junaid ya yi shiru na wasu sakanni. Wannan amsar ce ya fi tsoro, domin ba ya da mafita ga abun da ba a iya fassarashi a gareshi ba. Ya kai hannunsa ya shafi kafadarta a hankali ya ce, ""Babu komai, tunda baki san abun da yake damunki ba sai mu nemoshi a tare."""

"A hankali ya fara jera mata tambayoyi, yana ™o™arin fahimtar abun yake damunta, ko wani abu ne ya faru da ita, ko kuma wani ne ya Sata mata rai. Amma duk tambayar da ya yi sai ta yi shiru, kamar wacce aka datse harshenta. Ta ™i Waga kai ta kalle shi, balle ta ba shi amsa."

"Da matsa sai ta fara hawaye, ya Waga murya cikin Sacin rai yana faWin, ""Rumana, me yake damunki ne haka? Ki faWa min yanzu ko kuma ranki yayi mummunan Saci,"" sai kawai ta fashe da kuka mai ™arfi, tana girgiza kai tana faWin, ""Ka barni kawai& don Allah ka barni,"" kuka ne da yake fito da Sacin ranta da nauyin da ke cunkushe a cikin zuciyarta."

"Junaid ya ™ara fusata ya ce, ""To shikenan, idan ba za ki faWa ba sai ki ci gaba da kukan naki tunda dai ba zaki daina taurin kai ba."""

"�acin rai ya bayyana karara akan fuskarsa. Ya mi™e tsaye cikin Sacin rai, ya juya ba tare da ya sake cewa komai ba, ya fice daga Wakin. Tun daga wannan ranar bai sake bi ta kanta ba ya tattara lamarinta ya watsar."

RANAR JUMU'AH

"Tana kwance a kan gado ta yi lamo, wayarta ce ta yi tsuwwa ta daga kiran ba tareda ta damu da duba wanda ya kira ba."

"Daga Waya bangaren Abdulmajeed ya yi mata sallama, ""As-salmu ¿alaykum wa ra%matullhi wa baraktuh."""

"Ta amsa, ""Wa ¿alaykumus salamu wa ra%matullhi wa baraktuh."""

"Šaga Waya bangaren ya ce, ""Rumana mi yake faruwa ne ko kuma ince waye ya yi maki laifin da har girmansa ya kai ki yi wasarairai da hidimar bikin Junaid, ina lura tunda aka fara hidimar bikin nan babu abun da kika halarta, hakan kuma yana Sata mashi rai, duk kwanakin nan mun kasa gane kansa, yanzu dai gamu nan zaune shurum mun yi magana har bakinmu yana nema ya yi ciwo amma ya ce ba zai je dinner ba sai a tare da ke."""

"Ta ja lumfashi idanuwanta cike da gajiya da ruWani da ba ta gama fahimtarsa ba. Muryarta ta fito a sanyaye, amma akwai nauyin damuwa a cikinta, ta ce, ""Shi yaya Junaid Win ne ya ce idan babu ni ba zai je dinner ba?"""

"A dayan bangaren, Abdulmajeed ya yi dariya yana kokarin rage damuwar da ke cikin maganar ya ce, ""Eh, ga shi nan a kusa da ni. Ko wanka bai yi ba, yana nan zaune kamar wanda aka tilasta masa zuwa duniya."""

"Ta lumshe idanu na lokaci. A hankali ta ce, ""Ba shi wayar."""

"For seconds tayi ™ananun maganganun da bata fahimta kafin daga bisani aka ce, ""Gashi nan yaki amsa wayar."""

"Ta saki wani ™aramin lumfashi mai kama da yanke kauna. Ta gyara zama ta ce, ""Okay bara in kira shi da kaina."""

"Ta tsinke kiran ta lalubo lambarsa ta kira, hannunta yana rawa ba saboda tsoro ba, sai saboda wani yanayi da take ji a zuciyarta wanda har yanzu ba ta iya fassara shi ba. Ta danna lambar idanuwanta na kallon nesa kaWan daga saman gadon da take inda hotonsa yake manne ta kura masa idanu kamar wacce take neman karfin gwiwa daga can."

"Kira ya shigo wayarsa, a karo na farko ya kalli allon wayar sunan DIDI da manyan bakake ya bayyana, ya yi shiru ba tareda ya damu da picking kiran ba."

"Abdulmajeed ya kalle shi, ya ce, ""Ka Waga ita ce fa."""

"Junaid ya ja lumfashi mai nauyi, ya mike ya taka zuwa gefen taga sannan ya amsa kiran, muryarsa kasa-kasa ya ce, ""Hello."""

"Daga daya bangaren, muryar Rumana ta fito a hankali, ba da karfi sosai ba, amma cike da wani abu da ya saka zuciyarsa tsayawa na dan lokaci. ""Yaya Junaid me ya sa baka dauki kirana ba?"""

"Junaid ya yi shiru na Wan lokaci, yana kallon gefe yana ™o™arin haWiye haushin da ya taso masa. A takaice ya ce, ""Oho."""

"Ta lumshe ido tana faWin, ""Fisabilillah, aurenka sunkutum da guda amma ka ce ba za ka je dinner ba saboda ni."""

"Kamar wanda aka yiwa dole ya ce, ""Eh, nima I can be disturbing."

"Rumana ta nuna kanta da yatsa, idanuwanta cike da hawaye ta ce, ""Ba ni ba ce amaryar, ba ni ba ce kirjin biki, Me zai saka ka ce ba za ka je dinner ba sai da ni?"""

"A wannan lokacin, haushin da ke nukurkusar Junaid ya taru ya kai makura. Ya Waga murya yana faWin, ""Saboda na gaji da abun da kike yi wa mutane! Kin koma sukuku da ke, idan aka yi magana sai ki ce baki da lafiya alhali ™arya ne lafiyarki lau. Idan wani abun ne yake damunki ki fito ki fadawa mutane, ba wai ki ware kanki gefe kina kunci ba."""

"Ya Wan yi shiru, sannan ya ci ga ba, ""Ke ce ya kamata ki shige gaba a hidimar nan, kece ™anwata kwaya daya tilo"

"amma sai kika koma gefe kika nade hannuwa. Idan aka yi magana sai ki fake da 'ba ki da lafiya'."""

Rumana ta yi shiru kalamansa sun shiga zuciyarta fiye da yadda ta zata. Idanuwanta suka cika da hawaye.

"Hawaye na zubowa daga idanunta ta ce, ""Why are you doing this to me? Na ce ban da lafiya ka ™aryatani."""

"Da karfi ya ce, ""˜arya kike lafiyarki ™alau. Yarinyar nan Jidderh ™anwarki, saboda ke ta zo bikin nan amma sai kika watsar da ita, kika watsar da bikin. Saidai da Farida na haWata, jiya a gidan Hajjo ta kwana wajen Farida wanda ko na rantse ba zanyi kaffara ba akan cewa ba ki san a can ta kwana ba."""

"Ta sauke kai kamar yana a gabanta ta ce, ""To ka yi ha™uri."""

"Junaid ya girgiza kai zuciyarsa har lokacin cike take da takaici, ""Ha™urin shi ne ki shirya mu wuce dinner, kafarki"

"kafata."""

"Ta yi shiru na Wan lokaci kafin daga bisani ta ce, ""Gashi kuma ban shirya tafiya cikin gungun maza ba."""

"Junaid ya ware idanu cikin mamaki da Wan haushi ya ce, ""Kato kike son ki ce min?"""

"Ta girgiza kai da sauri, cikin sauri ta gyara maganarta da faWin, ""Ba haka na ce ba, anyway tunda ba za ka je ba ka hutar da mutane, sai ka kira ka ce na ce ba zan je ba don haka kaima baka je ba."""

"Ba tare da jira amsa ba, ta tsinke kiran."

Junaid ya tsaya yana kallon wayar zuciyarsa gaurayen da jin haushi da mamaki da kuma wani irin nauyi da ba ya iya fassara shi.

******

"Rumana ta dungure wayar na mintina biyar kafin daga bisani ta kira lambar Abdulmajeed ana picking ta ce, ""Yaya Abdulmajeed... ya aka yi? Ya shirya ko har yanzu taurin kan yake nunawa?"""

"Muryar Junaid ta ji yana faWin, ""Ina nan, ban shirya ba na fiki taurin kai."""

"Ta sassauta murya ta ce, ""To Allah ya huci zuciyar ranka ya daWe... yanzu zan shirya."""

"Junaid ya ce, ""Da ya fiye maki, haka kawai kina neman mayar min da aure sansanin damuwa ba tareda kwakwakwaran dalili ba."""

"Da sauri ta ce, ""To Allah ya bada ha™uri."" Ta tsinke kiran."

"Ta mi™e ta rage kayan dake jikinta ta Waura towel ta wuce bathroom, ta jima a cikin bathroom Win fiye da yadda ta saba, ruwan dake zuba yana saukar mata da nauyin dake zuciyarta, tana ™o™arin wanke damuwar da ta kasa fassarawa. Bayan ta gama, ta fito a sanyaye, ta tsaya gaban madubi na lokaci tana kallon kanta, tana son gano wani abu a cikin idanuwanta amma ta kasa."

"Ta zaSi Waya daga cikin dinkunan bikin da ta yi, leshi ne mai kyau da aka yi mata Winkin doguwar riga wacce ta zauna a jikinta tamkar an halicceta ne domin ita. Launin leshin ya fito da kyawunta, amma duk da haka, babu walwala a fuskarta. Ta yane kanta da kallabi sannan ta Wora mayafi a saman kafadunta, saida ta tabbata komai ya yi dai-dai kafin ta juya ta fita."

"Ba ta bi ta babbar ™ofa ba, ta bi ta backdoor kamar yadda ta saba yi a ´an kwanakin nan musamman idan tana son gujewa hayaniya ko tambayoyi. Gidan cike yake da mutane da shirye-shiryen biki, yayinda ita kuma a lokacin babu abun da zuciyarta take bu™ata da ya wuce nutsuwa."

"Ta isa parking space, ta buWe Waya daga cikin motocinta wacce bata taSa amfani da ita ba, ta shiga ta ja ™ofar, ta kunna motar, amma kafin ta jata sai da ta jingina bayanta da kujera ta lumshe idanu na ´an da™i™u, tana jan lumfashi a hankali."

"Sai kuma ta buWe idanunta, taja motar ta fice daga harabar gidan ta nufi hanyar gidan Aunty Hajjo, zuciyarta cike da tunane-tunane iri-iri, wasu da take ™o™arin mantawa, da wasu kuma da suka ™i barinta."

Akan hanyarta ta buWe gilashin motar iska mai sanyi yana bugawa a fuskarta amma hakan bai rage mata nauyin da take ji a zuciya ba. Duk da haka akwai wani ™aramin fata

Please Login or Register in order to submit comment