You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba za ku mayar da ni inda kuka daukoni, sannan ina mai gargadinka da babbar murya akan koda wasa ka da ka kuskura ka janye wannan gwangwanin motar daga nan har sai ka mayar da ni inda kuka satoni."""

"Ahmad ya kafeta da na mujiyarsa yana tu'ajjibi da mamakin, yaushe ne har Jidderh ta yi sauyawar da zata rin™a yaSa mashi maganganu kanta tsaye, yarinyar da ko iya Waga kai ta kalli idanun namiji ba ta iyawa saboda tsantsar kunya da tarbiyya amma yau itace take mashi magana da babbar murya tana kiranshi da talaka, motarsa da yake ji da ita itace take iya kira da gwangwani, to wai tukunna da take kiranshi da talaka, idan har shi takala ne itama ´ar talakawa ce kenan tunda ubanta ba fin ubansa arziki ya yi ba."

"Imran ya buWe murfin motar ta fito tana ™arewa harabar gidan kallo tana taSe baki a ranta tana faWin, ""Gida sai ka ce boys quarters kuma a haka wai suna da kuWi."""

"Ita fa ba za ta iya kiran masu wannan gidan da masu kudi ba, cikakkiyar hour daya ba za ta iya yi a wannan kuntaccen gidan nan ba wanda ko wadatacciyar iskar da za ta shaka babu, ai idan ta jima a gidan nan sai lumfashinta ya tsaya ta kamu da ciwon MUTUWA A MAKOSHI."

"Imran ya ce, ""Mu je."" Ta taso mashi tana magana a fusace, rashin kunya fal a idanunta, faWi take tana maimaitawa,"

"""Ai dama dole in shiga ciki ko saboda a yita ta ™are su saka ka mayar da ni inda ka satoni."""

"Bai bari maganarta ya dameshi ba, ya yi gaba ta bi bayanshi, tana tafiya tana kallon gidan cikin kaskanci da wulakanci, ""Har suke iya rayuwa a wannan akurkin kajin,"" ta tambayi kanta."

Kamar wacce aka tsikara ta zabura a yayinda ta tuna labaran da ta ke ji na yadda ake satar mutane ana neman kudin fansa.

"Tsoro ne ya kamata, ta fara nadamar biyoshi da ta yi. Shin ya za ta yi idan ya ki mayar da ita? Shin ya za ta yi idan ya kasance shiri ne aka yi domin su yi garkuwa da ita? Hakan zai iya faruwa idan ta yi duba da gidan da ta fito da makudan kuWaWen da suke da su, Yaa Junaid ta tuna, yana can yana nemanta, ta ja ta yi turus yayinda tsoronta ya ™aru, tsoro ya bayyana ™arara a kan fuskarta, Imran ya Waga murya yana kwalawa mutanen gidan kira, ""Ammi! Abbi! Na samu Jidderh! Na kira baku Wagawa!."""

Wata mata sanye da kayan masu aiki ta fito daga kitchen ta sauke ajiyar zuciya a lokacin da idanunta suka sauka a kan Rumana yayinda hawaye suka zubo a kan fuskarta.

"""Jidderh!!!"" Ta faWa tana mai share hawaye ta nufo inda suke da saurinta tana mai jin farin ciki na samunta da aka yi. ""Mun damu sosai, hankalin kowa ya tashi musamman Hajiya."""

"Rumana ta ware idanu tana mata kallon raini da kaskanci, a fusace ta ce, ""Ke ´ar aiki back off, I said back off, ka da ki kuskura ™azaman hannuwanki su taSa jikina."" Matar ta shareta tana ™ara karasowa inda take ta ce, ""Uwar dakina."""

"Rumana ta daka mata tsawa ta ce, ""Ke ki shiga hankalinki da ni, wa ya ce maki sunana Jidderh? Sunana Rumana. And I'm warning you to not force me make your life miserable."""

"Imarn ya yi wa matar alama, kafin ta ankara suka kamata tana fizgewa tana turjewa amma a banza, ta karfin tsiya suka haye da ita saman bene."

"Tunda take bata taSa shan ba™ar wahalar da tasha a wannan lokacin ba, tunda ta tashi daga gida sai unguwa sai"

"makaranta, ko karatunta a London ta yi tun daga kindergarten har zuwa wannan bugiren da take shirin shiga jami'a."

"Da muryar da take nuni da ta kai koluluwar gajiya da abun da yake faruwa ta ce, ""Ku kira masu gidan domin su saka a mayar dani inda aka daukoni tun ban fara maku hauka a wajen nan ba. Ku ji da kyau, you damn sick head and you damn maid."""

"A daidai lokacin ne, Abbi da Ammi suka bayyana da saurinsu yayinda wata kyakykyawar yarinya ´ar kimanin"

"shekaru shidda ta rugo ta rungumeta tana faWin, ""Adda Jidderh Ina kikaje ne? Ammi tana ta kuka."""

"Rumana ta ture yarinyar tana faWin, ""This stops now! Ke yarinya matsa min daga jiki, ni sunana Rumana, ba Jidderh ba. Hajiya da Alhaji ku saka Wanku ya mayar da ni inda ya dauko ni, tun ba'ayi yakin duniya na ukku a tsakiyar gidan nan ba."""

"Suka dubeta da mamaki, Abbi ya ce, ""Lafiyarki kuwa Jidderh, ina tarbiyyar da muka baki."""

"Takaici yazo ma Rumana wuya a ta ce, ""Tun a can nike faWa mashi ba Jidderh ba ce, sunana Rumana amma ya ki saurarena, Yaa Junaid yana can yana jirana, ku saka ya mayar da ni inda ya sato ni."""

"Ammi ta kamata tana hawaye ta ce, ""Ita ce! Jidderh ce!."""

"Rumana ta fizge daga jikinta tareda ja da baya tana faWin, ""A'a wannan ba Jidderh ba ce, duba da kyau, hutu da jin dadi da yake a jikina baiyi kama da tasowar wannan akurkin gidan naku ba..."""

"Ammi ta katseta da faWin, ""Jidderh mi kike cewa haka? Ni ce mahaifiyarki, Ammi ce. Ina kika je tsayin waWannan kwanakin?"""

"Rumana ta durkushe tareda fasa ihu da dukkanin karfinta, ""Sunana Rumana!!!!"" Ta faWa da muryar dake nuni da ranta ya kai koluluwar Saci akan wannan lamari da ya ™i ci ya ™i cinye kamar cin ™wan makauniya."

"Imran ya yi saurin faWin, ""Abbi ka kira doctor."" Ganin da gaske suke ta fara ihu da dukkanin muryarta tana fasa dukkanin abun da ya tari gabanta, ta koma masu mahaukaciyar karfi da ya ji, tana buga masu ™aramin hauka a falon, faWi take tana maimaitawa, ""Na boni sun yi garkuwa da ni. Yaa Junaid ka zo ka cece ni, duk ni ce na janyo da na saka mukayi ghosting matakan tsaronmu."""

"Suka kamata ta karfin tsiya suka sakata a daki, sai da doctor ya yi mata allurar bacci sannan suka samu ta yi shiru ta yi lamo yayinda bacci ya yi awon gaba da ita."

"Uwale mai aiki ta zage tana girka abincin da Jidderh tafi so wato tuwon shinkafa da miyar kubewa, ta zage ta girkashi ya yi WaWi domin uwar dakinta taci idan ta farka, tana good time da Jidderh sosai shiyasa duk abun da aka yi bata saka a kanta ba, bayan ta gama ta hauro sama."

"Ammi ta ganta da abinci niki-niki ta ce, ""Ina guje maki ki shiga a samu damuwa, kinga dai yadda ta ke yi wa mutane."" Uwale ta ce, ""Kai haba, babu abun da zai faru, ni da uwar dakina ne fa."" Ammi ta ce, ""To shikenan, ina fatan ku wanye lafiya da ita amma lamarin wannan yarinyar yana bani tsoro, yarinya sai kace wacce aljannu suka shiga saman kanta. Yarinya ta zabure da rashin kunya."""

"Imran dake gefe ya ce, ""Ni da ta saukewa kwandon rashin kunya akan titi ne zan baki labari, duk ha™urin Ahmad amma Wazu da ta faWa mashi wata magana sai da ranshi ya Saci, imagine ta dubi motarsa ta kirata da gwangwani sannan ta ce mashi Wan talakawa."""

"Ammi ta hau taSa hannuwa tana salati tana faWin, ""A'a lamari ya girmama, Uwale ki dawo da wannan abincin, maganin ka da a yi ka da a fara."" Imran ya ce, ""A'a ki barta ta kai mata, zama da yunwa babu WaWi."""

"Ba don Ammi taso ba tabar Uwale ta shiga, tana tsoron abun da za'a zo ayi ta yamudidi da yarinyar domin mutane ba zasu duba halin da ta shiga ba, rashin kunyar za su duba."

"A bangaren Uwale kuwa shigarta dakin yayi daidai da farkawar Rumana, ta mi™e tana bin dakin da kallo, Uwani ta ajiye abincin akan table ta ™arasa domin taimaka mata ta nike zaune, Rumana ta tureta tana sababi, ""Ke ´ar aiki kada ki kuskura hannunki ya ™ara taSa jikina."""

"Uwale ta washe baki ta ce, ""Yi ha™uri uwar dakina abinci na kawo maki."" Rumana ta harareta ta ce, ""Tunda ance maki daga gidan tsiya da fatara na fito, ai ni abun da zai saka inci abincin wannan gidan saidai idan ance min yana maganin mutuwa ne don haka ki juya ki koma da tsiyarki."""

"Uwale ba ta yi ™asa a gwuwa ba ta juya ta Wauko abincin ta kawo mata, ""Gashi uwar dakina na dafa maki tuwon shinkafa da miyar kubewa."""

"Rumana ta toshe hanci tareda kawar da kanta tana jin amai yana taso mata na kallon tuwo da miyar kubewar, ""Back off you damn maid, ki matsa min da wannan dosar tumakan tun kafin ya sakani amai."""

"Ta ture faranti ya zube a jikin Uwali, Imran da Ammi da suka shigo jin tana magana sama-sama, su ka yi turus suna tu'ajjibin abun da ta yi."

"Imran ya daka mata tsawa, ""Ke baki da hankali da za ki zubar mata da abinci a jiki, matar da ta yi jika da ke."""

"Rumana ta daka mashi tsawa ta ce, ""Karka sake ka ™ara yi min tsawa, you are on a very thin ice, so I advise you to"

"choose your next move more carefully."""

Ha™urinsa ya zo karshe ya nufi inda take gadan-gadan da nufin ya wanketa da mari watakila ta dawo hayyacinta daga wannan haukan da ta ke yi masu.

"Fahimtar abun da yake shirin aikatawa, Ammi ta kama hannunsa ta ce, ""A'a ka da ka yi haka, Allah kaWai ne ya san abun da ya faru da ita da ya sakata komawa haka."""

"Imran ya ce, ""Ammi ki barni idan na yi mata dukan tsiya sai ta dawo hayyacinta."" Jin ya ambaci duka Rumana ta fashe da dariya tana taSa hannuwa ta nuna kanta ta ce, ""Ai ban yi lalacewar da zaka Waura hannunka a kaina ba, ni Rumana banyi lalacewar da kowani shara da bola zai Waura hannuwa a kaina ba."""

"Ya nufo kanta gadan-gadan, sanin bata da karfin ramawa ta yi wufff ta wawuro faranti ta wurga mashi, da sauri ya koma da baya, ta fasa ihu tana wurgo masu dukkanin abun da ya tari gabanta, babu shiri suka yi waje da gudu suka maido kofa."

"Ta ri™e kugu tana faWin, ""Sai na yi maku ™aramin hauka a gidan nan, idan satar mutane halinku ne daga kaina kun"

"gama."""

Ta zauna a gefen gado tana maida lumfashi.

"Abbi ya dawo daga masallaci suka faWa mashi abun da ya faru, dama gudun abun zai je ya dawo ne ya saka ya bar Imran a gidan."

"Ya Waga waya ya kira doctor, tana zaune ta dafe kanta, Abbi ya turo kofa ya shigo, ta Wago idanu ta ga mai gidan ne, ta kafeshi da na mujiyarta tana jiran ta ji da wacce ya zo."

"Fahimtar hakan sai ya yi sauri ya ce, ""Saida na faWa masu ba Jidderh ba ce amma suka yi burus da ni, tafo ku je ya mayar dake inda ya daukoki."" Ta sauke ajiyar zuciya ta ce, ""Thanksgoodness an samu wanda ya fahimceni."""

"Ta mi™e ta nufi kofa, Abbi ya shammaceta ya yi mata rikon da ta kasa kwacewa, tana ihu tana fizgewa amma inaa karfin ba Waya ba, ya danneta doctor ya yi mata allurar barci, tun tana fizgewa har bacci ya ci karfinta ta sulale a jikin Abbi tana barci."

Shin wacece Jidderh? Shin wacece Rumana? Mi yasa suke Kamanni? Muje zuwa kada dai ku manta sunan Littafin ZANE A KAN RUWA mai wahalar gane kamanni.

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 2 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Abbi ya dauketa a hannuwansa ya kaita dakin Jidderh da fatan idan ta farka ta tuna komai tunda a tunaninsa ta samu damuwar mantuwa ne.

"Ya dawo falo suka yi jigum-jigum, Ammi ta rafka tagumi tana tarababbin wannan lamarin ta ce, ""Al'amarin wannan"

"yarinyar yana da matu™ar mamaki da Waure kai, kalamanta sunyi tsauri."""

"Abbi ya ce, ""Allah kaWai ya san abun da su ka yi mata da ya saka ta koma haka, amma lamarin yana da matu™ar Waure kai, Jidderh yarinya mai kunya ma'abociyar karatun Al™ur'ani, ita ce ta koma haka, tana magana da tsauraran kalaman da ko ni mahaifinta ba zan iya furtasu ba."""

"Imran da ya ga abun da ya fi wanda suka shaida ya ce, ""Yarinyar nan ta sauya baki Waya."" Abbi ya ce, ""Fatan shine Allah ya sa idan ta farka ta dawo daidai."" Suka amsa da, ""Amin."""

*********

"A bangaren Jidderh kuwa, mutumin yana fita babu jimawa katon dake kawo mata abinci ya shigo ya Wauki kujerar ya fita da ita, mintina biyu a tsakani wutar ta dauke duhu ya mamaye ko'ina na dakin."

"Ta wahala matu™a gaya, a tsorace take, duhun dakin ya haWu da tsoron al'amarin da ya kusa faruwa da ita na keta mata haddi da wannan mutumin ya so ya yi, ya haifar mata da tsoro har ya saka lumfashinta Waukewa jikinta yana rawa, tana kwance akan daSe mai sanyi tayi lamo, babu abun da ke tashi a dakin sai sautin fitar lumfashinta, motsin motsawarta kansa tsoro yake mata ballantana kuma motsin wani abun daban."

"Amma duk da haka ba ta yarda ta yi ihu ko kururuwa ba, ta Wage ta cigaba da karanta addu'o'in tsari tana rokon Allah akan ya kuSutar da ita daga hannun waWannan azzaluman mutane."

"Ta Waga kai a yayinda ta jiyo sautin buWe kofa, ta ware idanunta akan katon gardin da ya shigo yana muzurai ya daka mata tsawar da sai da ta razana ta fashe da kuka, ta saka hannu ta rufe idanunta a sanadin yawa da hasken ya yi mata, wani abun mamaki shine Kamannin da ta ke yi da Rumana, kamarsu Waya sak kamar kobo da kobo, babu abun da ya banbantasu."

Katon Basamuden gardin ya dungure mata faranti da ke Wauke da doya da kuli-kuli tare da kofin ruwa.

"Yunwa ta ke ji ba kaWan ba, ta wawuro farantin tana cin doyar da sauri-sauri kamar wacce za'a kwacewa, tana ci tana korawa da ruwa."

"Ya daka mata tsawar da sai da ta firgigita ta yi baya da sauri jikinta yana rawa, da muryar tsawa ya ce, ""An ce ki bada lambar danginki kin nuna taurin kai, to mu zuba da ni da ke, shege ka fasa Wan halak sai yanka, ina tabbatar maki da idan ki ka ji wuya da tsananin yunwa da kanki za ki bada lambar kuma dolen dole su bayar da kudin fansarki."" Ya fita tare da dannawa dakin makulli."

"Duhu ya ™ara mamaye Wakin da lalube ta wawuro farantin ta rarumi abincin tana turawa da sauri, ba ™aramar yunwa"

"ta ke ji ba, saboda sauri har kwarewa ta ke yi. Ta dafe cikinta tana kwarara amai."

"Sai da ta amaye dukkanin abun da ta ci sannan ta kwanta a ™asa ta yi lamo tana maida lumfashi, dutse ta ji a kusa da ita ta janyoshi ta rikeshi gam a hannunta ta fara ™a™arin amai tana ihun neman agaji hannunta dafe da cikinta tana yi kamar wacce take fama da ciwon MUTUWA A MAKOSHI."

"Da gudu ya dawo ya buWe dakin ya rufa a kanta domin duba abun da yake damunta, ta shammaceshi ta buga mashi dutsen a saman kai, ta ™ara buga mashi ya zube a ™asa yayi warwas, ta mi™e ta tsallakeshi ta fita da gudu, babu kowa a gidan ta buWe kuba da ke a kofa ta fita, gida ne da aka ginashi a dokar daji babu makwafta, babu alamar gida a kusa."

"Ta hanga gabas ta hanga yamma, ta duba kudu ta duba arewa amma babu alamun mutane a kusa, wannan shi ake kira dokar daji ko kuma ta yi mashi inkiya da ihunka banza."

"A lokacin gari ya fara duhu kasancewar gab da almuru ne, tsoro ya kamata ta tattara doguwar rigar da ke jikinta ta fara gudu da dukkanin karfinta, gudu ta ke yi babu ji babu gani, sai da ta shafe lokaci mai tsayi sannan ta samu kanta a bakin titi, jiri ne ya deSeta ta zube a ™asa ta suma."

******

"Aunty Zaynerb ce tsaye a parlour da waya a hannunta, ta dubi Junaid da ke tsaye kanshi a ™asa ta ce, ""A shekarunka da gogewar rayuwa da kake dashi amma har kayi irin wannan gangancin, kabar yarinya ita Waya a inda kasan babu wanda ta sani. Shin tun asalin farko mi ya saka kuka tafi babu matakan tsaro? Ai ga irinta nan an nemeta an rasa, kuma dole in kira Hajiya Amina in sanar da ita halin da ake ciki, tun Wazu take kira tana tambaya."""

Junaid ya dago da sauri yana rokonta domin ya san tur™a-tur™a tare da baya da kurar da sanar da Umma zai haifar.

"""Aunty please ka da ki sanar da ita, sai da ta hana in tafo da Rumana amma muka matsa, a hakan ma sai da ta gindaya min sharudda kafin ta bari na tafo da ita amma duk da ranta bai so ba, idan ta samu labarin abun da ya faru ba za ta yi min da WaWi ba."""

"Aunty Zaynerb ta yi mashi wani kallo ta ce, ""Ka yi min shiru a nan kuma dole in kirata domin ta cancanci da ta san halin da ake ciki, diyarta mace budurwa wacce ba rayuwar ™asar nan ta iya ba ta Sace sannan ka dubi tsabar idona ka ce min in rufe mata."""

"Kamar zai yi kuka ya ce, ""Idan kika faWa mata akwai damuwa, sai da ta yi min gargadi sosai akan idan aka samu damuwa za ta ci min mutunci."""

"Aunty Zaynerb ta ce, ""Then ka shirya cin mutunci da faWa da zaka kwasa a wajenta domin dole ne ta ji halin da ake ciki, ina ganinka mai hankali ashe baka da shi, yarinyar da hutu ne kawai yake kawota Nigeria amma shine za ka barta a tsakiyar titi a wannan zamanin da satar mutane ya zama ruwan dare, a wannan zamanin da zakaga ana cinikin kuWin fansar mutum kamar ana cinikin tattasai da attarugu."""

Yana mata magiya ta yi banza da shi ta haye saman bene.

"Durkushewa ya yi yana mai dafe kansa ya rasa abun da ya ke mashi WaWi. Lamarin ya hade mashi goma da ashirin, ga tashin hankali na batan kanwarsa ma fi soyuwa a gareshi, ga kuma zullumi na Sacin rai da zai samu a wajen Umma idan ta ji abun da ya faru, ga kuma still damuwa na halin da Umma za ta shiga a lokacin da ta samu labarin Satan autarta."

*********

JIHAR KADUNA

"Umma tana zaune a kan kujera ta rafka tagumi ta rasa dalilin da ya saka gabanta yake yawan faWuwa, a haka kira ya shigo wayarta ta dauka ta yi jim tana sauraron abun da ake faWa mata daga Waya bangaren."

"Mi™ewa ta yi zumbur tare da dafe kirji, a ruWe ta ce, ""Yaushe? Garin ya? Innalillahi wa inna ilaihi raji'um. Ki saka su ™ara bincike, su duba ccvt footage na lokacin da abun ya faru. Ina wayarta? Kuyi tracking wayarta? Ina Junaid yake?"""

"Lokaci guda ta rikice hankalinta ya tashi ta rasa abun da ya ke mata WaWi, ta zube akan kujera rijib yayinda zufa ta karyo mata tana faWin, ""Wayyo ni Aminene na boni na lalace, shin ina zan saka kaina idan ya kasance sirrin da nike Soyewa tsayin shekara da shekaru ne yake shirin fallasa? Rumana akwai sirrin da ba na so ya bayyana shiyasa ba na son zuwanki garin Katsina shine ma dalilin da ya saka ko rayuwa a kasar nan ban barki kinyi ba amma kuka matsa kuka addabi rayuwata har sai da na yarje maku tafiyar da jikina yake bani za ta kawo baya da kura,"" hawaye suka zubo mata ta ™ara da cewa, ""Rumana bana fatan rasaki. Kina ina ne? Where are you Didi?"""

******

"Junaid yana zaune a mota, hankalinsa a matu™ar tashe domin ya tabbata zuwa wannan lokacin mai afkuwa ta afku, Umma ta riga da ta ji abun da ya faru, ya kalli wayar Rumana wacce take a motarsa yana nadamar amsarta da ya yi daga hannunta, da ace akwai wayar a wajenta sai su kira su ji inda take ko kuma subi diddigin layinta su samu location dinta."

"Abun da yake ™ara tada mashi hankali shine yarinyar bata saba rayuwa a kasar nan ba, ga kuma abun da ya faru,"

yana tsoron ka da a cutar masu da ita.

"Kira ya shigo wayarsa yana dubawa ya ga Umma ce ya yi zuru ya kasa Waga kiran har ya tsinke, miss call biyu ta ajiye mashi amma ya kasa Wagawa, ta tura mashi text message, yana gama karantawa hannunsa har rawa yake wajen kiran numbarta, muryarsa tana rawa ya ce, ""Umma barka da dare."""

"Bata amsa mashi ba, ta murtu™e fuska kamar yana a gabanta, da kakkausar murya ta ce, ""Junaid! Junaid!! Junaid!!! Sau ukku ka ji na kira sunanka. Junaid na baka awanni biyar ka nemo min Wiyata Rumana a dukkanin inda take a cikin garin Katsina, ban damu ba koda za ka bi lungu da sako na garin ne kana kwala mata kira, nidai abun da nike so shine ka maido min Wiyata a nan Kaduna kamar yadda ka daukota ko kuma ka hadu da fushina, Junaid a kan wannan maganar zan iya yafe wa duniya kai, sai dai ka nemi wata uwar,"" sai kuma ta fashe da kuka."

"Nadama ta kamashi na bujurewa maganarta da suka yi suka tafo, shiyasa a rayuwa idan iyaye suka ce ka da ka yi to ka hakura domin abun da babba ya hango yaro ko ya taka tsani ba zai hangoshi ba, bujurewa maganar iyaye babu abun da ya ke janyowa sai nadama da dana sani, biyayya a garesu kuma WaWi gareshi, mai biyayya ga iyaye rayuwarsa tana kyau da albarka, akwai ganin daidai a tare da biyayyar, iyaye suna da matu™ar muhimmanci da daraja."

"Da muryar kuka ya ce, ""Ki yi hakuri Umma, ki bar zubar min da hawaye, zan nemeto zan bazama a cikin garin Katsina in nemo ta, nima na damu da

Please Login or Register in order to submit comment