You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lafiya?"" Ya amsa da, ""Lafiya lau, Jidderh naga adireshin ashe a kasan cover din wayata ta sakashi, zuwa anjima zan kawo maki."" Farin ciki ya lulluSe zuciyarta ta ce, ""Okay sai ka zo."""

"Jidderh tayi matu™ar farin ciki da wannan labarin, tana da yakini akan haduwa da dangin Rumana zai iya kasancewa"

sanadin gane dangin mahaifinta duba da kamanni da ta ke yi da ita.

"Akan hanyarsa ta zuwa gidan ya samu kiran gaggawa, bai shiga ciki ba ya gangara da motarsa a gefen titi ya kira numbarta, babu jimawa ta fito tana sanye da doguwar hijab har ™asa, ya kafeta da na mujiyarsa yana mamakin tsantsar kamannin da ta ke yi da waccen yarinyar."

Jidderh ta ™arasa inda motar take ta gaida shi ya amsa da sakin fuska ya mi™a mata takardar ta amsa tare da

"warwareta tana dubawa, ""Ba ta rubuta Jiha ba."" Ta sanar da shi."

"""Eh ba ta rubuta ba amma lambar motarta ta kaduna ce."""

"Jidderh ta jinjina kai ta ce, ""Na gode. Ba zaka shiga ba."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""Ina sauri ne shiyasa amma ki gaidasu."""

"Ta ce, ""Za su ji."" Ta juya ta koma ciki, kai tsaye ta wuce study room inda take da tabbacin samun Abbi, ta mi™a"

"mashi takardar ta ce, ""Abbi mun samu adireshin gidansu yarinyar, a Kaduna take. Yaushe za mu je?"""

"Abbi ya yi jim sannan ya ce, ""Ranar asabar idan Allah ya kaimu."" Jidderh ta jinjina kanta ta ce, ""Allah ya kaimu."" Ya"

"amsa da, ""Amin."" Ya ™ara da faWin, ""Allah ya yi maki albarka."" Ta amsa da, ""Amin."""

**********

"RANAR ASABAR, JIHAR KADUNA."

"Rumana ta yi turus tana kallon mutanen da ke falon, ta cika da matu™ar mamaki ganin damuwa da tashin hankali a"

kan fuskar Umma a yayinda take sauraron mutanen.

"Abbi ya ce, ""Wannan shine abun da ya faru na shigo Nigeria domin neman asalina."""

"Umma ta dubeshi ta yi shiru na Wan lokaci kafin daga bisani ta ce, ""Tabbas kuna da alaka da Rumana sai dai ba ta yadda kuke tunani ba. Shekarun Jidderh nawa?"" Umma ta tambayi Ammi."

"Ammi ta ce, ""Shekarunta sha bakwai a wannan shekarar take gama makarantar sekondire."""

"Umma ta yi jim kafin daga bisani ta ce, ""Kafin ki haifi Jidderh kin haifi wata diyar a asibiti amma daga baya ta rasu. To Rumana ita ce diyar da kika haifa, Rumana jininku ce."""

"Jikin Rumana ya fara rawa jin kalaman da Umma take faWa, ta yi tsaye shurum ita ba ta yi gaba ba ita ba ta yi baya ba, tana tsaye shurum kamar butum butumi yayinda tashin hankali da ruWani suka cikata suna ragargazarta a zuci tamkar guguwa mai tsananin gaske."

"Falon ya yi shiru, a cikin wannan shirun zuciyarta take bugawa da karfin gaske. Ta kalli Umma ta juya ta kalli su Ammi ta dafe kanta da ya fara juyawa tana mai tambayar kanta da kanta; Shin a mafarki take ko kuma zahiriyya na wannan lamarin wanda zai iya juya rayuwarta daga sama zuwa kasa, na wannan bankaWar da za ta iya juye rayuwarta zuwa upside of down, masu iya magana sun yi gaskiya da su ka ce a wajen tone-tone kaza take tono abun da zai sha mata kai gashi dai ita rashin jinta ya tunkudo tarnakin da yake bazanar saka mata takunkumi a wuya da ka iya juya mata rayuwa zuwa mahangar da ba ta sani ba."

"Hannunta suka fara rawa kamar suna neman wani abu da za su iya ri™ewa saidai ba abun ri™ewar take nema ba,"

tsabar tashin hankali da ruWani ne na abun da kunnuwanta suka jiyo mata.

"Zuciyarta ta yi nauyi, kafafunta suka yi mata nauyi kamar ana janye su ne a ™asar da take tsaye. Idanunta sun yi ja, tana kallon komai cike da mamaki da rashin tabbas, ta ™ure wa falon kallo tamkar wacce take ™o™arin gane gaskiyar da ke Soye a cikin sa."

"Jinta take kamar tana a cikin wani mugun mafarki, jikinta yana karkarwa, hannunta da kafafunta suna motsa kansu da kansu, idanunta suna kallon waje guda saidai babu abun da take ganewa sai zallar maganar Umma da ta ke mata amsa kuwwa a masarrafar tunani."

"Bugun zuciya yana ™aruwa da kowane dakika, ta fara ja da baya tana girgiza kanta, tana sosa kai kamar wacce aka yi wa KITSO DA KWARKWATA, jikinta da kwakwalwarta sun kasa tantance a tsakanin gaskiya ko mafarki na wannan lamari da yake shirin faruwa a rayuwarta."

"Kafafunta sun gagara Waukarta ta fasa ihu ta zube a ™asa bata motsi, Junaid ya rufa a kanta yana jijjigata yana kiran"

"sunanta, ""Rumana! Rumana wake up! Rumana ki tashi!."" Amma inaa, ba ta motsa ba."

"Ya ™arasa falo da gudunsa ya dauko ruwa masu sanyi yana yayyafa mata saidai bata motsa ba saida ya kwaraya mata ruwan gaba Waya sannan ta damki lumfashi ta buWe idanunta ta saukesu a kansa, da muryarta da bata fita sosai ta ce, ""Yaa Junaid ka ce min mafarki nikeyi, kace min abun da nike jin Umma tana faWa ba gaskiya bane ba."""

"Junaid ya kasa furta mata komai yayinda yake kallonta cike da tausayi, shima kansa yana cikin kwatankwacin ruWanin da take a ciki na wannan abun mai kamar almara. Rumana ™anwarsa ita ce ake faWin ba ´ar gidan ba ce."

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

Taku Har Kullum Aysher Angel (Matar Aliyu)

*ZANE A KAN RUWA*

_(Mai Wahalar Gane Kamanni)_

*NA*

*AYSHER ANGEL*

Page 6 Free Page

"*Littafin Zane Akan Ruwa Na Kudi ne, book 1 shine free, book 2 and 3 akan naira dari takwas 800, Vip 1k, pay via 9169472057, Aisha, Opay Digital Service, sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057.*"

"*Taken Labarin Shine ZANE A KAN RUWA (Mai Wahalar Gane Kamanni) Bari Ganin na bayyana komai, akwai wani laujen a cikin nadi, akwai sauran rina a kaba, wasu igiyoyin a baibai suke.*"

"Tana cin karo dasu Ammi ta yi luu, yana dubawa yaga wani suman ta ™ara yi, ya Wauketa ya wuce da ita dakinsa, koda ta farka babu abun da take sai kuka da sabbatu saida ya yi mata allura ta samu barci sannan abun ya lafa."

"Yayi jigum yayinda tsantsar tashin hankali da ruWani ya bayyana akan fuskarsa. A falo Umma dasu Ammi sun yi jigum-jigum an rasa wanda zai cewa wani uffan, Umma ta mi™e ta ce, ""Masu aiki zasu kawo maku abinci, idan ta farka sai in baku labari tiryan-tiryan akan abun da ya faru."""

"Bata jira amsarsu ba ta haura sama, ta faWa bedroom dinta ta zauna a gefen gado ta dafe kanta da ya ke sara mata yayinda damuwa da tashin hankali ya bayyana akan fuskarta na rabuwa da za ta yi da Rumana, a gefe guda tana tuna Wiyarta Meemah da aka rabata da ita cike da zalunci."

"Saida marece sannan Rumana ta farka Junaid ya ba ta abinci ta ki ci, sai da ya matsa mata ya yi mata dubara akan mafarki ne ya faru sannan ta yarda ta amsa ta ci."

"Ya mi™e zuwa dakin Umma ya sameta tsaye a balcony tana kallon waje yayinda tsantsar damuwa ta bayyana akan fuskarta, ya ce, ""Umma mu je mu kori mutanen nan tun kafin su yi sanadin mutuwar yarinyar nan, kina gani sau ukku tana suma, koda na kaita daki sai da ta ™ara wani suman."""

"Umma ta share hawayen dake akan fuskarta ta ce, ""Ba za su koru ba domin Rumana diyarsu ce halak malak."" Ya ce, ""Amma muna da kuWin da za mu amsheta kuma babu abun da suka isa su yi."" Umma ta ce, ""Kaico, shi kuma hakkin su sai muyi ya da shi, Junaid na gaji da dakon hakkin mutanen nan a saman kaina, a yau zan bayyana komai in ba su ha™uri in nemi yafiyarsu sannan in basu diyarsu su tafi da ita."""

"Ji Junaid ya yi kafafunsa ba za su iya daukarsa ba, ya yi zaman daSaro a ™asa yana faWin, ""Amma Umma ya aka yi kika ce Rumana ba diyarki ba ce bayan ni nasan kece kika haife ta?"" Ta ce, ""Saboda hakan shine gaskiya."" Ya shiga girgiza kansa yana faWin, ""No, hakan ba zai taSa faruwa ba, bazan yarda da wadannan zantukan ba domin babu abun da ya bada ma'ana a wannan lamarin."""

"Umma ta girgiza kai ta ce, ""Dama shi ZANE AKAN RUWA wahalar gane kamanni gareshi kamar HAWAYE AKAN RUWA ne idanun da suke fitar da shi ne kawai suka san raWaWi da kunci da ya ke fita da fitarsa."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""Shima wannan ban gane ba, nifa bana jin zan iya gane dukkanin wani zancen da ya shafi batun cewa Rumana ba diyarki ba ce ba."""

"Umma ta ce, ""Gaskiyar kenan sai ka amsa da ha™uri, dama a rayuwa ba komai ba ne ya ke Worewa haka zalika ba komai ba ne mutum yake nema yana samu."" Daga haka ta nufi kofa tana faWin, ""Ka sameni a parlour in faWi komai a gabanka domin ba na son ko bayan raina a zo a na wallahi tallahi da kai akan wannan maganar. Daga yau zan saka narkakken dutse in yi wa wannan lamarin togaciyar da babu wanda zai nemi ba'asi ko tada zaune tsaye, a yau yarinya za ta koma hannun iyayenta na asali."""

Daga haka ta fice ta barshi zaune shurum yana luguden laSSa.

"Kai tsaye dakinsa ta nufa inda take kyautata zaton za ta samu Rumana, ta sameta zaune a gefen gado ta yi tagumi tana karanta wasikar jaki, Rumana tana ganin Umma ta yi tsuru-tsuru da idanu yayinda bugun zuciyarta ya ™aru, hannunta suka fara karkarwa."

"Umma ta ce, ""Ka da ki kuskura ki ™ara sumar min a nan domin ban shirya Waukar wani alhakin na daban ba, masu iya magana sun ce a wajen tone-tone kaza take tono ajalinta to ke kuma tashin hankali kika tono na abun da na yi shekera da shekaru ina Soyewa don haka sai ki amsa da ha™uri."""

"Rumana ta fashe da kuka tana faWin, ""Please Umma ka da ki yi min haka, na tuba ba zan ™ara ba."" Umma ta ce, ""Rumana ki daina Sata yawun bakinki domin bakin alkalami ya riga ya bushe,"" ta nuna kanta ta ce, ""Ni da kike gani ba ni ba ce na haifeki, waccen matar dake zaune a parlour ita ce ta haifeki, ki biyoni a parlour domin ki ji yadda aka yi aka kwana a ragaya."""

"Rumana ta fasa ihu tana girgiza kanta ta ce, ""A'a na yafe kwanan ragayar."" Umma ta girgiza kanta ta ce, ""Kaico sai dai kin yi rashin sa'a domin ta inda aka hau ta nan ake sauka."" Rumana ta ce, ""Amma ba za'a rasa Soyayyar hanya ba."" Umma ta ce, ""Shi kuma hakkinsu fa."" Rumana ta ce, ""Ni ban san su ba, ba ni da ala™a da su, ke ce na sani, ke ce kika haifeni."""

"Umma ta saka hannu ta share hawayen da suka zubo mata ta ce, ""Kayya, sai dai ba komai ba ne ya ke Worewa ba."" Ta juya ta fita zuwa falon ™asa ta samu su Ammi zaune ta ce, ""Ku yi ha™uri na barku ku kaWai, ta farka, yanzu za ta sauko sai in fede maku daga biri har wutsiya akan abun da ya faru."""

"Babu wanda ya ce mata uffan a cikinsu, suma suna cikin tsantsar mamaki da ruWani domin a iya saninsu yarinyar da suka haifa ta mutu bayan haihuwa, hakazalika Abbi da ³an uwan Ammi ne suka sadata da makwancinta, kenan idan har Rumana Wiyarsu ce, to wacece waccen yarinyar? Jin zantukan Umma suke kamar almara, sun zo da saka ran samun labari akan dangin Abbi sai dai abun da suka tarar ya kiWima masu tunani."

"Har mintina goma sha biyar suka shuWe babu Rumana babu Junaid, Umma tana kiran lambar Junaid ba ya Wagawa ta"

mi™e ta haura sama ta samu wayam babu Junaid babu Rumana.

"Ta fita ta samu mai guard inda ya tabbatar mata da sun fita, hankalinta ya tashi tana kiran lambarsa ba ya Wagawa, ta dafe kanta ta rasa wani tunanin za ta yi, shin mi ya sa suka yi haka bayan ita dasu sun san da cewa shure-shure ba ya hana mutuwa haka zalika ranar wanka ba'a Soyon cibi."

"Ta koma falon inda Ammi da Abbi suke, ta rasa abun da za ta ce masu daga baya ta karfafi kanta ta ce, ""Ku yi ha™uri amma yaran nan sun tafi kuma ina kyautata zaton London za su wuce, watakila ku ga kamar na yi amai na lashe sai dai lamarin ba haka yake ba, kamar yadda na faWa a Wazu Rumana diyarku ce, tabbas haka zancen yake, Rumana diyarku ce, kuma zan maido maku da ita sannan zan sanar da ku yadda aka yi, amma ina son ku bani lokaci in daidaita komai sannan in je har London in tafo da su sai mu zo har nan gidanku a Katsina in kawo maku ita kuma in baku labari akan YADDA ABUN YAKE."""

"Abbi ya jinjina kai ya ce, ""To shikenan babu damuwa."" Ta ce, ""Amma ku bari ku kwana a nan washegari sai ku wuce."" Ammi ta ce, ""A'a duk dare nafi son in gani a Katsina."" Saida Umma tayi insisting sannan suka yarda suka kwana, washegari suka dauki hanyar Katsina, Umma taso ta saka direba ya kaisu amma suka ™iya."

"Ammi da Abbi suka sauka Katsina basu zame ko'ina ba sai gidansu Ammi wajen Alhaji Baffah, suka taru a falon Alhaji Baffah, ita, Abbi, da kuma Hajiyarsu Ammi wato Hajiya Attuwa."

"Ammi ta kwashe dukkanin abun da ya faru ta sanar da iyayen nata, Hajiya Atuwa ta cika da tsantsar mamaki ta rasa bakin magana saidai jinjina kai kawai da ta ke yi."

"Alhaji Baffah ya ce, ""Allah mai iko, kenan ita yarinyar diyarku ce."" Ammi ta jinjina kanta ta ce, ""Eh haka ta ce."" Sai a lokacin Hajiya Attuwa ta saka baki ta ce, ""Idan haka ne, ya aka yi ban ganku kun tafo da ita ba."""

"Abbi ya gyara zama ya ce, ""Ko labarin yadda aka yi yarinyar ta zama Wiyarmu bata faWa mamu ba saboda yayan yarinyar ya dauketa sun gudu ta tabbatar mamu da babu shakka London zai wuce da ita amma za ta je ta tafo da su tazo har nan Katsina ta sanar damu komai sannan kuma ta damka mamu diyarmu."""

"Alhaji Baffah ya jinjina kai ya ce, ""Na gane amma kai baka ganin kamar akwai rashin gaskiya a lamarinta, sai nikega kamar tana so ne ta yi amai ta lashe, ma'ana ta hadiye maganarta ta hanaku yarinyar."""

"Hajiya Attuwa ta Wora da faWin, ""Idan kuwa haka ne ya kamata hukuma ta shiga lamarin, ai babu wanda ya fi karfin hukuma."""

"Ammi ta yi saurin faWin, ""A'a ba na jin hakan take nufi, ina ganin tunda har ta nemi mu bata dama to mu bata damar mu gani idan ya so idan daga baya ta nuna alamun rashin gaskiya sai mu saka hukuma a ciki."""

"Abbi ya jinjina kai ya ce, ""Nima abun da nike ganin ya kamata muyi kenan, a yadda na fahimta ita kanta bata jin"

"WaWin abun da yaran suka yi ba, ta nuna damuwa ™arara akan lamarin."""

"Alhaji Baffah ya ce, ""To shikenan sai mu bata damar mu gani abun da za ta yi."" Suka cigaba da tattaunawa akan lamarin sai wajen karfe biyu sannan Ammi da Abbi suka koma gida."

****************

"Tunda suka Wauki hanyar Abuja Rumana take kuka, ba irin kukan shagwaSa da sangarta da ta saba ba, kuka ne mai Wauke da tsoro da damuwa da kuma wani irin ™unci da ya cika zuciyarta har ya kasa samun mafita. Lumfashinta yana fita a hankali, idanunta sun kumbura sun yi ja saboda tsabar kukan da tasha, hannayenta suna rawa kamar wacce aka tsorata da wani abu mai firgitarwa."

"""Bazan iya rayuwa a wani gidan da ba gidanmu ba,"" ta faWa cikin rawar murya, tana ri™e hannun Junaid kamar wacce"

take jin tsoron kada ya kuSuce.

"Ta ™ara sautin kukanta tana faWin, ""Bazan iya rayuwa da wasu ahalin da ba kai da Umma ba... bazan iya ba... wallahi bazan iya ba..."""

"Ta girgiza kai tana sake fashewa da kuka, hawaye na zuba daga idanunta kamar ruwan sama, tana jin kamar an cire ta daga duniyar da ta sani aka jefa ta cikin wata sabuwa mai cike da duhu da rashin tabbas."

"""Mu gudu daga Nigeria tun kafin Umma ta tilasta min rayuwa dasu,"" ta ™ara cewa, muryarta na rawa."

"Junaid ya juyo ya kalleta yanayinsa cike da tausayi da damuwa, kalamanta bana wasa ba ne, tsoro ne yake ragargazarta a zuci har ta kasa shiru."

"A hankali ya matsa kusa da ita, ya Wora hannunsa a kafaWarta yana ™o™arin kwantar mata da hankali."

"""Ki kwantar da hankalinki,"" ya faWa cikin sanyin murya, yana kallon idanunta kai tsaye domin ta fahimci gaskiyarsa."

"Ya ce, ""Didi ki kwantar da hankalinki bazan taSa bari hakan ya faru ba. Ina tare da ke kuma ba zan taSa jefa ki cikin wani hali da ba ki so ba."""

"For once kalamansa sun saka taji sanyi amma tuna cakwakiya da turka-turkar dake cikin lamarin ya saka ta koma gidan jiya, damuwarta ta koma sabuwa yayinda kalamansa suka zame mata tamkar iskar da ta ratsa kunnuwanta ba tare da ta zauna a zuciya ba, tsoron da take ji a wannan lokacin ya fi karfin kalamansa su kwantar mata da hankali."

Motar na ci gaba da tafiya yayinda hanya take ja kamar ba ta da ™arshe. Gari yana sauyawa a gefensu daga ™ananan

kauyuka zuwa manyan gine-gine.

Ta yi shiru ba don ta daina kukan ba sai don kawai lumfashinta ya gaji. Sai kuma ta sake fashewa da wani sabon

"kuka, mai ™arfi fiye da na baya."

"Tana share hawaye da bayan hannunta tana faWin, ""Ba zaka fahimta ba. Ni ban saba da su ba... ban san su ba... ni ina son zama daku ne kawai... ni ina son mu zauna mu uku ne kawai... Ni, da kai da kuma Umma."""

"Junaid ya ja lumfashi a hankali yana jin kalamanta suna dukan zuciyarsa. Wannan ba ™aramin abu ba ne a gareta, wannan canjin rayuwa da ake son tilasta mata kamar ana so ne ta manta da duk wani abun da ta sani ta fara wani sabon shafin rayuwa ba tare da shiri ba."

"Ya ce, ""Zaki iya amma ba ta tilas ba. Zamu yi komai a hankali. Ba zan bar ki kisha wahala a rayuwa ba hakazakila ba zan barki ki rayu a inda baki so ba."""

"Ba ta amsa shi ba, ta juyar da kanta gefe tana kallon waje amma saidai ba ta ganin komai, hawayen da suka cika idanunta sun rufe mata magannan."

"Lokaci na wucewa daga seconds zuwa minutes zuwa hour amma halin da take ciki bai sauya ba. Kukan zuci da na zahiri ya zame mata tamkar abokin tafiya, yana bin ta a duk inda motar ta dosa."

"Har suka fara shiga birnin tarayya Abuja kogin hawayenta bai kafe ba, shigowarsu Abuja bai Wauke mata hankali ba."

"A gare ta, komai sabo ne, kuma duk abun da yake sabo a wannan lokacin yana ™ara mata tsoro ne."

"Har ya kama hanyar gidansa yayinda take faman share hawaye da sauri-sauri, can kuma kamar wacce ta tuna da wani abun tsoro, sai ta Wago kai da gaggawa tace, ""A a, a a, zata iya binmu har can gidan naka ta amsheni ta mayar masu... don Allah muje hotel... don Allah..."""

"Muryarta a wannan karon ba kuka kawai ba ne, akwai ro™o a ciki, akwai firgici na wanda yake neman mafita. Ta ™ara matsawa jikinsa, tana ri™e shi da ™arfi."

"Junaid ya ja lumfashi yana kallonta da mamaki. ""Hotel kuma?"" ya maimaita cikin ´ar ™aramin murya a lokaci guda kuma yana ™o™arin rabata da jikinsa domin yadda take shige masa da yadda take manne masa yana jefa shi cikin wani yanayi da bai taSa tsintar kansa a ciki ba, wani yanayi mai rikitarwa tsakanin tausayi, kulawa, da kuma wani abu da yake ™o™arin dannewa a zuciyarsa."

"Amma duk ™o™arinsa na son ja baya, sai ta ™ara matsowa kamar ™aramin yaro da ke neman mafaka daga abin da"

yake tsoro.

"""Eh... hotel..."" ta sake faWa, tana girgiza kai. ""Don Allah... kada ka kai ni can... bana jin zan iya rayuwa da wadancen mutanen... don Allah mu gudu..."""

Ya yi shiru yana kallon fuskarta da ta cika da hawaye da tsoro da kuma wani irin rashin tabbas da ya saka zuciyarsa take jin tausayinta.

"A hankali ya juya idonsa ya kalli hanya yana tunani cikin sauri. Bai shiryawa wannan lamarin ba, koda ya biye mata suka gudu bai shirya abun yayi tsawo har haka ba, bai yi tsammanin abubuwa zasu juya haka ba. Amma a wannan lokacin, abun da ya fi muhimmanci a gareshi shi ne yadda zata samu nutsuwa, ko da kuwa na Wan lokaci ne."

"Ya sauke numfashi a hankali, ya Wan jinjina kai."

"""Okay,"" ya faWa a ta™aice."

"Ya sauya akalar motar zuwa hotel mafi kusa da su, Rumana ta sassauta ri™on da ta yi masa, amma har lokacin tana manne da shi, kamar yaron da ake ™o™arin rabawa da Innarsa."

"A hankali kukan nata ya ragu, amma ba duka ba, saidai ya koma irin kukan nan ne na shiru mai Wauke da ajiyar zuciya da lumfarfashi."

"Yayinda suke ci gaba da tafiya, kan Junaid ya cunkushe da tunani: shin me ke jiransu a nan gaba? Shin wannan shawarar ta hotel Win zata zama mafita... ko kuma wata sabuwar matsala ce zata buWe ™ofa?"

But for now ya ajiye komai a gefe. Abun da kawai yake ji shi ne rawar lumfashinta a jikinsa da kuma yadda ta ri™e

shi kamar shi ne kaWai mafakarta a wannan duniya.

"Da muryarta wacce take tsinkewa saboda kukan da tasha tace, ""Ina... Ina son... Ina son muje hotel... ne. saboda"

"Umma zata iya samunmu a can gidan naka ta daukeni ta kaiwa waWancan mutanen."""

"Ta faWi hakan ne tana kuka, kukan da yake fita hade da sheshshe™a, lumfashinta yana tangal-tangal kamar wacce ta dauko ruwa a robar da ta fi karfin kanta. Kowace kalma tana fitowa ne a wahale, cikin tsananun kuka da rawar murya, ta zama abun tausayi ™warai da gaske."

"Ya kutsa motar cikin harabar hotel Win ya yi parking, motar ta tsaya, Rumana bata motsa ba, sai da ya buWe ™ofar"

"sannan itama ta buWe kofar bangaren, amma tana fitowa waje sai tsoro ya rufeta, ta manne masa, ta ri™e shi da ™arfi."

"Ba ta saba da irin waWannan wurare ba, komai a gareta ya zama sabo, hayaniyar wajen, shige da ficen mutane, har"

"ma da yadda ake kallonsu, wannan ya ™ara mata tsoro, ta ™ara shige masa sosai."

A tare suka taka zuwa cikin hotel din tana manne da shi yayinda yake jin wani irin yanayi mai rikitarwa. Ba wai don komai ba sai don yadda take jingina da shi.

"Yadda take ri™e shi yana motsa masa abubuwa da yake ™o™arin dannewa. Duk da haka ya daure, ya mayar da hankali"

kan taimaka mata.

"A wajen reception, tunda suka shiga wani mutum yake kallonsu, kallon tuhuma da zargi na irin wanda ya gama yanke hukunci akan baWala ce ta kawosu."

"Wannan kallon ya saka Junaid jin babu daWi. Ya gyara tsayuwarsa, yana baza tazara akan yadda take manne da shi,"

"amma tace sam bata san wannan zancen ba, ta ™ara ri™e shi, ba tare da ta damu da komai

Please Login or Register in order to submit comment