You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikin ki da na Babyn gudun faruwar wata matsalar ?".

"A'a kar ka damu na samu lafiya,Doctorn da ya duba ni jiya ma ya isa I'm feeling better now".

"Anya kuwa na yarda,karda fa unborn d`ina ya samu matsala ",ya kai zancen yana mai d`ora hannunsa
a saman cikinta d`an kimanin watannin biyar.

Yalwataccen murmushi ta saki gami da cewa," Au ta Unborn d`inka kawai ka ke bayan kuma jiya shine
ya hana mu samun wadataccen barci ".

"Shikenan tunda na ga abun naka akwai selfish a ciki,tashi mu je in had`a maka ruwan wanka kafin ka
fito na gama had`a mana breakfast tunda Garin ya riga da ya waye"," okay to mu je ".

Acan `bangaren Grandma hankalin ta a tashe ta kai dubanta kan Cecelia da ke zaune ,ta ca`ba adonta
da k`ananan kaya as usual, ta jawo attached d`inta ta d`ora asaman kanta .

"Cecelia akwai matsala there is a problem, something happened","Matsala kuma Grandma,which kind
of problem, shin ko wani abu ya samu Brox Daniel d`in ne ban sani ba ?".

"Ban sani ba Ceceliar, Something wrong ya faru,gabad`aya Daniel ya janca na rasa gane kan shi ko ku
ma a abinda ya ke cikin Zuciyarsa".ta kai zancen muryarta na raunana.

Kusa da ita Cecelia ta matsa gami da jawota jikinta ta fara lallashin ta da cewa,", It's okay mana,ki bar
tashin hankalin ki haka,kin ga ba wata isasshiyar lafiya ce da ke ba kar ciwon ki ya motsa, in Jesus name
komi zai dai-daita kin ji".

" Ameen Cecelia, ta shi mu je Church d`in nan domin so nake in sa ayimin dogon Addu'o'i akan Daniel
lamarin sa ya fara bani tsoro,amma ina mai tabbata maki in har bikin Easter ya zo Daniel bai shigo
Garinnan ba ni da kaina zan shirya in je har can Kanon Inga halin da yake a ciki,domin ba na tare da
natsuwa ko kwanciyar hankali a game da shi".
"Hakan ma yayi dai-dai, da zaran anfara yi mashi addu'a komi zai dawo Normal.

Tunda ga wannan lokacin Grandma ba ta sake zama ba kullum cikin yawaita bauta da yin sadaka take
akan Jesus Christ ya sa hankalin Daniel ya dawo gare su tayi addu'ar da kanta sannan tasa Pastor ko
Reberal yayi,Cecelia ma na iyakar iyawarta.

Yau Sunday Cecelia ce zaune a k`ark`ashin wata bishi sun fito cin abinci,ta rafka tagumi da duka
hannayenta,,k`arasowar Gloria k`awarta ta sa hannunta ta cire mata tagumin kafin ta fara yi mata fad`a
da cewa " Haba Cecelia me yake damun ki,what happen,ko kina son ki cutar da kan ki ne ta ya tun kina
`yar Yarinyar za ki rik`a jefa kan ki cikin irin wannan dogon tunanin,kin San how long nake tsaye anan ina
maki magana amma ko motsin kirki ba ki ba ?".

Sai da Cecelia ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita kafin ta fara ce da ita,"Ki yi hak`uri Besty
ina cikin damuwane lamarin Brox Daniel kullum k`ara worth yake,kullum K`ara yin nisa daga gare mu
yake,yanda kika san Wanda akai masa asiri haka ya koma,ga Maganar Aurena da Samuel sai matsowa
take yanzu haka ya kusa six months bai zo inda muke ba".

A firgice Gloria ta mik`e tsaye kafin ta ce,"what kina nufin Brox Daniel Wanda na sani ko kuma wani
daban ki ke nufi".

"My friend I'm sorry, da `boye miki wannan lamarin da na yi,Na san halin ki ne za ki tashi hankalinmu,
saboda tsananin son da ki ke mashi,Na bari komi ya dai-daita sai in sanar da ke"....

" It can not be possible, ba zai yiwu ba, I will find him,zan nemo shi a duk inda yake,kawai ki bani
address nasa zan je in ga halin da yake a ciki".

"Kin gani ko dama abinda na guda kenan shiyasa tun da faru ban sanar da ke abinda ke faruwa ba,but
please ina so ki kwantar da hankalin ki domin da akwai shirin da muke shiryawa ni da Grandma,by the
grace of God komi zai dawo Normal".

" No no Cecelia bazan iya hak`uri ba kawai ki bani address d`in in je in gani halin da yake a ciki".....

K`arasowar Grandma cikin hanzari da kuma fushi shine ya dakatar da Gloria game da san amsar
address d`in Daniel a gurin Cecelia da ta ke, hannun Cecelia kawai Grandma ta fara ja tana mai bin
hanyar da zata kai su Gida, a firgice Cecelia ke binta sai faman tambayarta me ke faruwa take amma ta
kasa sanar mata har sai da su ka isa Gida.

"Wai Grandma me yake faruwa haka naga duk kin tashi hankalin ki, nima kuma kin tashi nawa?".

Sai da ta fitar da isaka daga bakinta kafin ta sanar da ita abinda ke faruwa da cewa," Yau Pastor ya
sanar da ni wani abu game da Daniel wanda ya tashi hankalina,don haka yau ba zan iya rintsawa ba har
sai na sa Daniel a cikin idanuna,ba zan runtsaba har sai nayi tozali da shi in my own eyes ".

" A'a Grandma ma haka ma ba zai yiwu ba, kin san ko k`arfe nawa kuwa yanzu,zamu yi tafiya dare fa
kenan? ".
" Yo meye matsalan a cikin ba dai zamu ruski Garin da ya ke a ciki ba komi dare,mu tafi kawai".

"A'a ba za ai haka ba gaskiya kin manta k`asarnan yanzu bata da tsaro,taya zamu jajibi tafiya cikin dare
alhakin ko inda zamu ba mu sani ba kuma ba mu ta`ba zuwa ba,ga ra dai mu bari sai zuwa gobe early in
the morning sai mu tafi".

" Ina ni ban aminta da wannan tsarin na ki ba a yau zamu tafi ba sai gobe ba","Haba Grandma taya
idon ki zai rufe ga gaskiya ina fad`a maki amma kin k`i amincewa,taya garin gyaran wata `barnar zamu
jefa kan mu cikin wani halin na had`ari,Na roƙe ki da suansn Yesu mai cetonmu ki bar tafiyatnan sai
gobe,in har ba so ki ke wani abun kuma na daban ya same mu ba",da k`yar Cecelia ta samu tai
convincing d`in Grandma ta bar tafiyar sai da safe amma ba ta barta ta huta ba har sai da ta had`a masu
duk wani abu da ta san zasu buk`ata kafin ya kyaleta,Ai ko Gari na wayewa ko breakfast bata,bar su sunyi
ba su ka d`auki hanya sar Garin Kano don sugano me ya ke faruwa da Daniel d`in su.




*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1




PAGE 8 ❤

FREE PAGE



"To fa wai wake ta faman kiran wannan wayar ne haka ?,in ka kira d`aya biyu ba a d`aga ba sai ka
hak`ura alamun mai wayar ba ya kusa ne ko kuma yana wani abun mai muhimmanci da ya hana shi
d`aga kiran", Cewar Hibba wacce sallame Sallahr Isha'in take nan tun tana Sallah ake faman kiran wayar
Abubakar da ya barta a charge ya tafi masalaci domin gabatar da tashi Sallahr.

Har ta mik`e za ta je taga waye yake ta faman kiran wayar,sai wayar ta katse,sai da Hibba ta ja tsaki
kafin ta koma ta zauna.

"Grandma ya k`i d`aga kiran ko dai yasan muna cikin Garinnan ne shiyasa ya k`i d`aga kiran wayar ? ".

" In ko haka ne da Daniel ya bani kunya,da ya aikata abinda ban ta`ba expecting daga gare shi ba".

"To yanzu ya zamu yi Grandma, ko dai komawa Gida zamu yi ?".

" God for bid, Cecelia ba inda za ni har sai na sanya Daniel a cikin idanuna "....

Cecelia ta katseta da cewa," Kenan haka Na nufin zamu kwana a saman Street ? "," No my dear ba
zamu kwana a saman titi ba,dole wata dabarar zamu sake wata k`ila muyi nasarar samun sa".

"To ko dai wata wayar zamu ara sai mu Kira shi da ita in anyi sa'a ya d`aga shikenan","To shikenan
Cecelia gwada mu gani",wara idanu Cecelia ta fara yi a cikin tashar da suke,can ta hango wani shop,ta
kalli Grandma tace ko can zamu je ga wani shop can sai mu rok`e shi ya ara mana wayar ?"," To mu je
mu gani ko zamu da ce".

A tare suka isa cikin Shagon,bayan sun gaisa Cecelia tace da shi,"Please ka ara mana wayar ka,muna
so zamu yi kira tamu wayar ta mutu ne saboda rashin charge, gashi munyi tafiya mai nisa".

Wani irin kallon mai Shagon ya bisu da shi alamun kamar bai yarda da su ba.

"Haba Yarona ka taimaka ka ara mana,ba cutar da kai zamu yi ba, idan baka taimake mu ba,ba mu san
ina zamu kwana ba,gashi ba mu san kowa a cikin Garinnan ba,please ka tai maka mana".
Haka ba dan ya so ba ya basu aron wayar,Cecelia ta sa number,tana fara shiga ta mik`awa Grandma
wayar.

Sai da Hibba ta ja dogon tsaki kafin ta yunk`ura da k`yar ta nufi inda wayar take,ganin bak`uwar
number ne ya sa ta d`aga kiran tare da yin Sallamar tare da cewa," Mai wayar baya kusa a sake Kira
zuwa anjima ".

Cikin d`aga murya Grandma ta ce, "Who the hell are you, wace ce ke da har zaki d`aga min wayar Yaro
ina Daniel d`in yake ?".

Ba Hibba kad`ai ba hatta Unborn d`in da ke cikinta sai da ya motsa sakamakon tsawar da kuma murya
Grandma da ta ji".

" Na ce maki ina Daniel d`in ya tafi a cikin irin wannan daren,kuma ke kuma wace ce da har aka samu
wayarsa a hannunki?".

Diriricewa Hibba tai Zufa sai faman tsa-tsafo mata take,ta rasa me zata ce da ita,shigowar Abbakar ya
d`an saisaita mata tunanin da hanzarinta ta nufi inda yake ta na mai mik`a mashi wayar amma ta kasa iya
cewa da shi komi.

"Lafiya me yake faruwa ya na ganki a cikin irin wannan yanayin, ko dai jikin ne har yanzu ?"......

" Grandma ce akan line"...shine abinda ta iya cewa kawai

"Grandma kuma ina fatan dai baki d`aga ba ko ?","Yanzu haka tana kan layi tana jinka", sosai tsoro da
fargaba suka bayyana akan fuskar shi,jikin shi a matuk`ar sanyaye ya kai wayar a kunnensa shi tare da
kiran sunanta yanda zai samu tabbacin ita d`ince.

" Eh ni d`in ce dai wace kake gudu, kenan saboda mace ka ne aikata mana duk abinda ka ga
dama"...muryar shi na rawa ya fara k`ok`arin dakatar da ita,hanashi cewa komi tai sai itace ta cigaba da
cewa,"Ka bar komi kake ka zo nan Tasha muna jiranka".

"Tasha kuma wacce irin Tasha,to wai ma wacce tashar ki ke nufi".ya faɗa a firgice

" Tashar Ubanka na ke nufi,ina nan cikin Garin Kano ka zo ka d`auke mu ,kana da za`bi ko dai ka zo ka
d`auke mu ko kuma mu juya mu koma inda muka fito ko kuma mu kwana a Street ya rage ruwanka".

"A'a Grandma ba ayi haka ba,ku jirani ganinan zuwa".



Haka ya kashe wayar ya nufi inda ya ke aje keys d`in motarsa,rasa ma Ina ya aje su yai sai yai gaba sai
kuma ya dawo yai baya,ya ma rasa ne ya kamata yai sai Hibba ce ta d`auko mashi key d`in ya fita,ko da
ya fita yawo kawai ya kama yi akan titi,sai daga baya tunanin shi ya fara dawowa jikinsa,sannan ya fiddo
wayarsa ya Kira layin da su ka kirashi da shi ya Kira shi ya gayama sa Tashar da suke ya nufi can d`in.
"Kin ji tashin hankali Cecelia, wai mace kuma ce ta d`aga wayar Daniel da farko","Mace kuma to wace
ce ita,wanne matsayin ne da ita har haka ?"," Ban sani ba,a iya sani na Mace ba ta cikin d`abi'u ko
halayyar Daniel ".

" Ko dai yana tare da fiance d`in sa ne ?","To in haka ne mai zai sa tun farko ba zai sanar da ni ba,sai ya
rik`a gudunmu",

"Tom ,ni dai bana ce komi ba ,sai dai mu bari ya zo sai mu ji gaskiya daga bakin sa".haka dai suka
cigaba da wannan zancen har zuwa sanda ya iso tashar.

Ko da isar shi tashar da hayaniya Grandma ta taso mashi,cikin ladabi da biyayya ya duk`ar da kanshi ya
na mai cewa da ita," Na rok`e ki da kiyi hak`uri ki dakatar da duk wani `bacin rai ko fushi da ki ke ji a
kaina har sai mun Isa Gida ,in ba haka ba nan mutane zasu taru su san wannan irin hali muke a ciki".

Da k`yar Grandma ta iya had`iye abinda take ji a cikin ranta har suka bar cikin Tashar, ita kuwa Cecelia
sai faman kallon shi kawai take gani ta ke kamar ba Brox Daniel d`in ta da ta sani ba, kamala da natsuwa
duk sun bayyana a tattare da shi.

Yanda Abbakar ya fita cikin tashin hankali da damuwa hakama Hibba take a cikin shi,komi na ta ya tsaya
ta rasa wanne tunanin ko kuma wani abu da zata aikata ya kawo sauk`in wannan lamarin da ya tun karo
su,amma ina kanta a cunkushe yake,tunanin ta ya cure guri guda,babban abinda yafi tsaya mata a rai da
kuma sake tada mata hankali muryarta da Grandma ta ji,ya zasu k`arke shin zata kar`beta a matsayin in-
law ko kuwa za tai rejecting d`inta.

Sanda taji k`arar bud`e gate d`in Gidan da shigowar su sai da numfashinta yai yunk`urin dakatawa da
k`yar ta samu ta janyo shi da k`arfinta.

Sanda suka shigo cikin Parlourn ba k`aramin sake hargitsewa tai ba,sai ji tai inama da ta sani `boyewa
tai bata zauna sun isketa a cikin Parlourn ba.

Cecelia ce ta matsa kusa da ita,tana mai binta da kallo tun daga sama har k`asa kafin ta jeho mata da
tambaya,"Ke ce ki ka Picking Call ɗin d`azu da akayi ?",a tsorace ta d`aga mata kai alamun eh itace ta
d`aga wayar.

"Wace ce ke ko dai fiancee d`in sa ce ke ?".

Ba tare da Hibba ta iya tsayawa ta tantance ma'anar tambayar da Cecelia ta yi mata ba ,ta sake amsa
mata da Eh.

Grandma ma ce ta maida kallonta kan Daniel tana mai cewa da shi," Yanzu Daniel for the God sake
mene ne haka saboda ka na tare da Mace sai ka manta da mu,ka fidda mu daga cikin rayuwar ka,ka tada
hankalin ka ka tada hankalin mu,me ya same ka da har ka aikata hakan?".

Abbakar rasa me ce yai ganin yanda suka sauyawa lamarin ma'ana da kuma yanda suka d`auki ke shi da
sauk`i,ganin ya kasa iya cewa komi yasa Grandma ta maida hankalin ta kan Hibba, ganin yanda take a
firgice yasa ta kamo hannunta suka zauna akan two seater dake kusa da su,cikin kwantar da murya ta ce
da ita,"Kin ga My dear ki kwantar da hankalin ki ba abinda za mu yi miki,Na ga duk kin tashi hankalin
ki,ko ba ki san cewa ba a san Pregnancy Woman tana shiga cikin tashin hankalin ko damuwa ba, cikin na
ki watan shi nawa yanzu?".

Cikin rarraba kalami ta bata amsa da,"watan shi bakwai","Oh sannu kin ji ina rok`on Yesu Almasihu da
ya kare ki ya sa ki sauka lafiya ke da abinda ke cikin ki".

Cecelia ce tamasa cikin murna tare da cewa,"Ina fatan in an tashi a haifi mace sai a sanya mata
sunana kin ga ta My first Daughter kuma gata name sake d`ina".

Sosai wad`annan maganganun ma su suka tada ma Hibba hankali ba ma ita kad`ai ba hatta da shi
Abbakar d`in sai da k`irjin shi ya buga da ya ji abinda su ke cewa.

"Ka bani mamaki Daniel,ban ga dalilin da zai sa don ka fara Dating ka k`aurace mana ba, meye nawa
don kana tare da wacce ka ke so,iyakacin fa in samu ku albarka tare da fatan alkairi, ba zan hana ka kayi
rayuwa da wacce ka ke so ba".

Sake baki su duka biyun su kai sosai Abbakar ya Lula duniyar tunanin da San gani dalilin da yasa suke
d`auki lamarin ta wannan fuskar, sai a lokacin ya kai dubanta shi kan kayan da ke jikin Hibba k`ananun
kaya ne a jikin ta saboda cikin Na sanyata yawan jin zafi,wa da hakan yasa su ke ganin lamarin ta wannan
fuskar,su duk a zato da tsanmanin su itama Hibba Crista ce.

" Ka tashi hankalina Daniel akan lamarinnan bana samun isasshen barci Na takura ,Na Sanya Pastor
yana yi maka addu'a ni duk a tunanin ko wani mugun abun ne ya same ke".

Dakatawa tai tana maaida kallonta kan Hibba ta ce da ita,"Kar ki damu da zaran kin haihu zamu had`a
da bikin suna da kuma bikin ku musha shagali biyu a lokaci d`aya,fad`a min ya sunan ki".....

"Grandma ba fa abinda ku ke tunanin ba ne ba, ni da ita munyi Aure mu d`in mata da Miji ne".

Kamar wad`anda aka d`aukewa wuta haka Grandma da Cecelia suka tsaya cak komi nasu ya dakata na
wucin gadi.

Cecelia ce tai k`arfinta halin sake tambayar shi abinda kunnuwansu ya jiye masu," Da gaske kake Brox
Daniel, wannan ɗin Matar ka ce,kayi Aure,kuma ba tare da mun sani ba, me hakan ke nufi?".

Wani yak`e Wanda yafi kuka ciwo Grandma ta saki gami da cewa,"Kinga Cecelia bi komi a hankali ya
riga da yayi Auren fa,ba wai zai yi ba ne ba,abu guda da za ki tambaye shi,me muka aikata mashi wanne
laifi ne mai girman gaske da mu kai ma shi har da muka can-canci ya fiddamu a cikin lamarin rayuwar
sa?",Grandma ta kai k`arshe batun muryarta ta fara rawa alamun batun ya ta`ba mata Zuciyarta.

"Ka kunyatar da ni,ako da yaushe in na zauna cikin friends d`ina bani da abun fad`a da ya wuce My son
Daniel ya girma,in Aurensa ya zo zan yi kaza,zan sai kaza,zan sa kaza a jikina amma shine za ka yyudare ni
ka je can kai Auren ka ba tare da na sani ba?".....
"Ki gafarce ni Grandma ba na aikata hakan don son nuna ba ki isa a cikin rayuwata ba ,ko don kunyatar ki
ba, a'a na kasa samun natsuwa , Zuciyata na faɗa min ba lalle ku amshi abinda na zo maku da shi
ba,kullum cikin fargaba da tashin hankali na ke"...

"A'a Daniel ƙarya ka ke dama can ka ayi biyar kunyata ni,Kai Ni ban ma yarda da abinda ka ke cewa ba".

"Ki gafarce ni Grandma da gaske ne nayi Aure,sunanan ta ma Hibba kuma musulma ce,ni ma kuma na
dad`e da musulumta".

Wani irin tafiya taga-taga Grandma tayi zata fad`i k`asa inba dan yana kusa da ita yai saurin tare ta ba
da Allah kad`ai yasan irin fad`uwar da za tai.

" A'a Daniel na rok`e ka da ka k`aryata abinda kunnuwana suka jiye min ka ce ba gaskiya ba ne
ba,mafarki na ke,mafarkin abinda ba zai ta`ba yiwuwa ba",Grandma ta fad`a hawaye Na rige-rigen sauka
akan fuskarta

Shima hawayen yake sakamakon ganin ta na hawayen da k`yar ya iya cewa da ita,"Da gaske ne
Grandma na yi Aure,kuma sannan Na musulumta ni yanzu ba mabiyin addinin Crista ba ne,ni
musulmine ,suna Na Abbakar ba Daniel ba".

"A'a Brox Daniel kar kai haka ,kar ka ce ka bar addinin gaskiya, Addinin iyayen da kakannin ka,shin ina
wata gaskiya ta ke a cikin Addinin da ba addinin Crista ba,ka tuba ka dawo ya zuwa addinin ka ka ji
d`an'uwana Daniel"...

Da hannu ya dakatar da ita," Kar ki sake kirana da wannan sunan suna Abbakar ba Daniel ba".

"Oh Jesus ka kawo min d`aukin ka, sun asirce min d`a shikenan sun raba ni da shi,ka ga ka biyo ni mu
je can Jos in had`a ka da Pastor Yohanna ya ba ka makarin asirin da su ka yi maka".

Cecelia ce ta matsa kusa da Hibba idanuwanta na zubda hawaye ta ce da ita,"Me ki ka yi ma
d`an'uwana da har ki ka rabashi da tunanin sa ki ka raba shi da addinin shi", ta kai zance ta na mai daka
mata tsawa.

" A'a wallahi ba abinda nayi masa,hasalima shi da kan shi yai sha'awar shiga muslunci ba tare da an
tursasa shi ba ". Hibba ta bata amsa bakinta na rawa

"K`aryar ki ke dole da akwai abinda ku ka aikata ma shi ,to ki sani ina mai rantse maki da Allah d`aya
sai kin rabu da shi,sai kin bar cikin Gidannan domin nan ba gurin zaman ki ba ne ba"..... Cikin d`aga
murya Abbakar ya daka ma Cecelia tsawa tare da fara yi mata warning," Ki shiga hankalin Cecelia Mata
ta ce fa,ki fita a harkata domin babu ruwanta a cikin wannan Maganar,don rad`in kaina na ce ina son in
musulumta haka kuma ina cikin hankalina na ganta Na ce ina sonta".

"A'a Daniel kar ka ce haka,ka zo mu bar wannan Garin zaman ka a ciki ba alkairi ba ne ba,ka rabu da
wannan Matar ba son gaskiya ta ke maka ba tunda har ta iya raba ka da Addinin ka,kar ka manta tun
kana d`an k`arami ka na raine ka,Na baka kulawa da Soyayya,me ye zai sa yanzu da rana tsaka ka za`bi
wata bare kuma ka fifita akaina,don haka ina mai umartaka da ka tashi a yanzu ba sai gobe ba mu bar
wannan k`addararen Garin da banga amfanin zaman ka a cikin sa ba,ita kuma kai divorce d`inta ta tafi
Gidan Ubanta".

Wasu hawayen ne suka sake zubowa daga Idon shi kafin ya duƙar da kan shi ƙasa ya ce da ita "Ki
gafarce ni Grandma, nasan kinyi matuk`ar k`ok`ari a wajen rsino da tarbiyar mu,a kan haka nake baki
hak`uri domin ba zan iya yi maki biyayya a dai-dai wannan ga`bar ba,Addinin da nake a kai yanzu ya ce
babu biyayy ga abokin halitta indai a wajen sa`bawa Ubangiji ne,kuma ni Maganar gaskiya ina son Mata
ta da abinda ke cikinta,kuma ban shiga cikin Addinin muslunci don in barshi ba,kuma ina yi maku
Addu'ar Allah ya sa ku gane gaskiya ku dawo cikin sa".....

"Dakata min mara kuyar banza mara kuyar wofi, ai ashe bayan nasarar fidda ka daga cikin Addinin ka
da su kai har rashin kunya su ka koya ma ka,to bari ka ji madamar ba ka sake ta ka zo mun bar wannan
Garin a yanzu,ka bar masu Addinin su anan,tunda dama nan ka same shi,ita kuma ka sake ta da zaran ta
haihu sai mu zo mu amshe abinda ta haifa shikenan, in kuma ba haka ba sai dai ka za`ba ko ni ko
ita,domin ba zan iya cigabada da ganin ka tare da ita ba".

Sai da Abbakar ya duk`ar da kanshi k`asa, hawayen saman fuskarsa na tsananta zuba kafin ya iya cire
baki ya ce da ita," Grandma ki gafarce ni amma ba zan iya aikata da`ya daga cikin abubuwan da ki ka
lissafo ba,ina son Addini na da kuma Mata ta,haka ke ma ba zan iya rayuwa babu ke ba"....

"A'a Broth don't do that, wannan babban kuskure ne ta ya za ka yarda ka rabu da whole family d`in ka
akan wata Mace ,Haba Broth think wisely mana,tabbas ka sa na ji Na tsananin wannan Matar har ma da
abinda ke cikin ta ban san su ban ko San ganin su,By the grace of God d`an cikin ma ba zai rayu ba,ba za
a haife shi da rai ba".....kafin ta rufe bakin ta ya sharara mata mari har biyu da iya kacin k`arfin shi,K`ara
mai k`arfi ta saki gami da k`ank`ame Grandma ta na mai ambaton sunan Jesus.

"Ba ka da hankali ne a gabana zaka sa hannu ka dake ta kuma akan mace ? "," Grandma ki Na jinta
fa,kin ji mugun bakin da kuma aibatawar da ta ke yima iyali na fa".

Duka Grandma ta fara kai mashi ta ko ina a jikin sa tana yi tana cewa ya cuce ta tunda har ya yarda ya
bar Addinin Crista ya koma musulmine,sai da tai iya yinta ta sanan ta dakata dan kanta kafin ta
dakata,"Ka sani daga yau bani ba ka,Na fita daga cikin duk wani sha'ani na ka ko na rayuwar ka,sannan
kai ma ina son ka fiddamu a cikin taka rayuwar ba mu ba ka tunda Addini ya raba mu,a yau ba sai gobe
ba zamu bar maka Gidan ka ka cigaba da rayuwa da wacce ka za`ba".

Tana kaiwa nan ta sa`bi jakar da suka zo da ita gami da kama hannu Cecelia suka nufi hanyar barin
Gidan kowa a

Please Login or Register in order to submit comment