You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa,"Ba abinda zai faru Fadeela sai alkairi ai tuni
Ummu Nurain ta watsa ma garin ta ƙasa,banda azababbiyar ƙazantar da take aikatawa yanzu ta ƙaro
futsara,rashin kunya da kuma neman fitina ba tare da dalili ba,kin ga kenan ita da kanta zata buɗe min
hanyar da zan fidda ta daga cikin Gidan da sauƙin","Kuma fa haka ne da gaskiyar ki duk mace mai irin
wannan ɗabi'un ba za ta taɓa zama lafiya da Mijinta ba, Allah ya shirya ta in ta na da niyar hakan",da
haka dai suka gama shirin su suka nufi ɓangaren Fulani kafin Mai martaba ya dawo.



Part 32



Kai tsaye Jadeeda bayan sun yi landing Eko Hotels and Suites da ke located at Plot 1415 Adetokunbo
Ademola Street, PMB 12724, Victoria Island, Lagos, ta nufa hotel ɗin da yake ɗaya daga cikin hotel ɗin da
su kai Shura a cikin Garin Lagos ya na ɗauke da kimanin 825 rooms and suites across four multistory
buildings,tun kafin su isa ta ke trying ɗin wata number amma cikin rashin sa'ah har yanzu ba ai picking
ba,sai faman tsaki ta ke saki time to time ta na ƙara gwada kiran,can kiran na gab da sake katsewa ba
tare da an daga ba akai picking,tare da cewa,,"I'm so sorry friendy ,bcos I'm in a noisy environment,
that's why I'm not picking your call."shiru Jadeeda ta yi ba tare da ta ce da ita komi ba,hakan ya sa ita
kuma ta kasa iya jurewa har sai ta ce da ita,"Ki yi min magana mana kin san tun muna yara bana iya jure
shirun ki",cewar Ruth cikin son shawo kan Jadeeda,daga nan Jadeeda na jiyo sautin kiɗan dake tashi a
wurin da ta ke,sai a lokacin ta ce da ita,"Ban san sai yaushe za ki sauya ba Ruth yau kina wancan Partyn
gobe kina wancan,anya kuwa?"...."No...no..no sis ba haka ba ne ba,na tuba fa na bar duk waɗannan
halayen yanzu haka muna Birthday Party Fredrick ne shiyasa ","Oh really?,yanzu fa haka ina cikin
Lagos,na so in yi surprise ɗin ki shiyasa ban gaya maki ba har sai da na iso",wata ƙara Ruth ta saki tana
mai tsalle kafin ta ce,"Tell me kina ina,gayamin I'm eager to see you,yanzu zan bar duk abinda na ke in
taho", murmushi Jadeeda ta saki kafin ta sanar da ita inda suke,"To ai a cikin Hotel ɗin muke gudanar da
Birthday Partyn ɗin ganinan maza ƙaraso in yi welcoming ɗin ki,wanne Room ɗin ki ke ne ","Room 263
",ta Bata amsa a taƙaice,tamkar waɗanda su ka kwashe tsawon wasu shekaru ba su haɗu ba haka suka
rinƙa murnar ganin juna,"Na yi murnar ganin ki,ba na jin kin taɓa burge ni irin yau,ban san da wacce
murya ko hanya zan iya nuna maki jin daɗi na ba","Kin ga ni kaina I'm so happy,kin san bikin Ester da za
ai shine Church ɗin (SCOAN),, Suka gaiyace ni a Matsayin zaɓaɓɓiyar mawaƙiyar su","wata ƙara Ruth ta
saki mai ƙarfi kafin ta dakata da cewa,"Kai abun alfari na ji daɗin jin haka,tafi-tafi sai ƙara samun ɗauka
ka ki ke yi","Ke dai bari duk hakan ya na faruwa da Encouragin ɗin a da ku ke min tun muna
school","Haka ne yanzu abinda ya kamata Sister ta shi ki fresh up mu tafi Partynnan tare da ke,ba
ƙaramin murna Fedrick zai yi ba idan ya gan ki a wurin,saƙon isowar ki shine zai zama Birthday gift ɗina a
gare sa ","Ah I'm tried I can't go anywhere,na gaji sosai ko kin manta gobe ne z mu fara shagulgulan bikin
Ester,don haka ina buƙatar hutu kafinnan","Kema kin san ba zan bar ki ba,kin ji my dear, please just
thirty minutes ya isa","Amma dai kin san hakan ba zai yiwu ba ko,oyah mu je tashi ki shirya",da haka ta
tursasa ta har sai da ta sa ta shirya suka fita tare.

"Ku saura! Kussurara!'',Ruth ta shelanta bayan ta amshi mike a hannun Dj ɗin,"Ko kunsan wannan hall
ɗin yana ɗauke da baƙuntar fasihiya kuma sananniya a cikin sa,Look who we have here,the one and the
only Lucifer,ita da kanta tana jealous ɗin zaƙin muryar ta,Afrika wake up, waiting to listen her song,the
nation rise and shine, her voice is in the anthem of the country,A.k.A Jadeeda Anderson",ta kai zancen ta
na mai nuna saitin inda ta ke a tsaye,nan fa gabaɗaya hall ɗin suka fara ihu gami da taɓi da ambaton
sunanta,wasu sun santa a fuska wasu kuma muryarta kawai su ka sani.

Fedrick ka sa motsin kirki ya yi,bai yi zaton zai sake ji ko ganin ta a sauran rayuwarsa da tai ma shi
ragowa ba,yaso ta so mai tsanani,so mai tsayawa a cikin rai da zuciya,so irin mai yankan
shakkunnan,ganin da gaske itace ɗin ya sa ya zubar da duk kyaututtukan da su ke a hannunsa ya ƙarasa
inda take cike da sassarfa dakuma shauƙin ganinta,yana zuwa bai jira komi ba ya haɗe jikinta da na shi.

Sai da ya gaji dan kan shi sannan ya raba jikinsa da nata,"Na yi kewa ki Angelenah,Son ki na ƙoƙarin
durƙusar da ni ya hana ni zuwa ko ina ,ya dakatar da ni da ga samun ko wanne cigaba na rayuwa,ina son
ki da dukkan raina Jadeeda Anderson",wani ihu gabaɗaya Hall ɗin ya sake ɗauka,"Ki ce da ni wani abu
mana ba zan iya samun natsuwa ba in har ban ji wani abu daga gare ki a yanzu ba",ya kai zancen yana
mai sake haɗe jikin su a karo na biyu,duka ta kai masa da hannu tana mai sakin murmushin yaƙe a kan
fuskarta,sai da ta kai bakinta saitin kunnensa kafin ta fara cewa da shi,"Za ka fara ko,ko kamanta a inda
ka ke ne,nan ba University College of London (U.C.L) ba ne ba,don haka ka ɗan riƙe kan ka kaɗan zuwa a
tashi",ta kai zance tana mai fuskantar shi gami da jujjuya masa idanunta bai san sanda komi na shi ya
daskare ba,wanda ita kuma tai amfani da wannan damar ta sa Dj sakar ma su sautin waƙar Dr Sid and DJ
Sose Mai taken Over the Moon,da wannan damar ta samu hankalin mutane ya kauce akan su,sai dai me
duk inda za ta sa ƙafarta Fedrick na biye da ita,haka har su ka tashi daga Partyn,a hankali ta ke tafiya ta
na yi tana waigen baya duk tana haka ne don ƙoƙarin gujema sake haɗuwa da shi take amma ina haƙan
ta bai cima ruwa ba,domin sai ganin shi kawai ta yi ba tare da ta yi zato da tsanmani ba,da alama ya sha
ya bugu sosai,bayanda ta iya dole sai kama shi tai ta nufi Room ɗin tada shi,da kyar ta samu ta iya kai shi
cikin Parlonta shima sai da taimakon Waiter na hotel ɗin.

Kamar wacce tai tsere haka ta ke sakin numfashi da huttai,wayarta ta laluba tana mai fara kiran
number Ruth,a ɗan zafafe ta fara yi mata magana da cewa,"Ruth wai ina ki ka shiga ne,tun ɗazu sai
neman ki na ke ban gan ki ba,kina ina",cikin rashin gaskiya Ruth ta fara yi mata magana cikin inda-
inda,ba tare da ta faɗa mata inda take ba"Koma ina ki ke,ke ki sa ni,amma ki gaggawar zuwa ki fidda min
Fedrick daga cikin Room ɗina","....Fedrick Kuma garin ya akai ya san Room number ɗin ki da har zai zo
wurin","Ya sha wine ne ya fita daga cikin hankalinsa,Ni kuma ba wani sanin friends ɗin sa na yi ba,balle
in samu wani ya tafi da shi,don haka ki ma za ki zo ki san yanda za ki yi ,ki fitar min da shi","Okay okay
I'm on my way ganinan tafe".
Cikin yanayin wanda ya sha ya bugu Fedrick ya matso kusa da ita tare da cewa,",Ba wai ....sai
kin....kin.kin... kira wani ba kawai ki bar ni,mu kwana a tare ko kin manta mu ɗin masoya ne,kuma wata
rana Aure za mu yi,don haka kar ki wani damu...",ya kai zance ya na mai yunƙurin faɗowa kan ta da sauri
ta janye daga wurin ya faɗa kan three seater da ke kusa da su.

"Kar ki bari a tafi da ni don ko an tafi dani sai na dawo,domin zuciyata tana liƙe da ta ki ne,ba zan samu
natsuwa a cikin barci na ba har sai na jiki a kusa da ni,sai na ji numfashi da kuma bugun zuciyar ki a
saman ƙirjina"......irin wannan maganganun ya rinƙa faɗa har barcin Giyar ya kwashe shi,sanda Ruth ta
zo bai ma sani ba,ita da taimakon saurayin da Ruth ɗin ta zo da shi da kuma security guda ɗaya suka
sanya shi a motar su ka nufi kai shi gidan sa.

Wata kyakkyawar ajiyar Zuciya Jadeeda ta saki ta na mai dafe gefen kanta da yai mata nauyi,wuri ta
samu ta zauna gami da rafka tagumi da hannu bibbiyu, abubuwan da suka faru tsakaninta da Fedrick ne
suka fara dawo mata a cikin kwakwalwar a lokacin baya ta da sauri ta runtse idanunta gami da miƙewa
ta nufi bedroom ɗin ta bakin ta ɗauke da addu'ar Allah ya sa ta gama abinda ta zo yi lafiya ta koma Gida
lafiya ba tare da wani abu makamancin na baya ya sake faruwa da ita tsakanin da Fedrick ba,sosai ta
dage da addu'ar Allah ya sa su rabu lafiya ba tare da hayaniya ko hargitse ba,ko isasshen barci kasa samu
ta yi ,saboda ta sa shi a cikin ranta,har dana sanin kawo shi cikin ɗalinta ta rinƙa yi da ma ta sani a can
waje ta yasar da shi ba tare da ta kula dashi ba,balle har ta kawo shi Room ɗin ta.

Yau Ester Sunday ta ɗau wankanta cikin expensive dress nata cikin jerin wanda Uncle Miey ɗin ta ya
saya mata,ta nufi Synagogue, Church of All Nations (SCOAN),taro yayi taro a wurin haka suka cigaba da
gaggaisawa da mutane,sai da manyan Reversed, Pastors da masu faɗa a ji a cikin Church ɗin su ka zo
kafin a bata damar zuwa ta buɗe taron da daɗaɗan waƙoƙin ta kamar yadda aka tsara,Revered Anderson
na can zaune a high table cikin manyan Reversed fuskar shi ɗauke da farinciki da zallar alfahari game da
samun ƴa irin Jadeeda da ya yi.

Cikin zazzaƙa kuma maɗaukakiyar muryarta ta fara cewa,"When every knee shall bow and every
tongue weather you like it or not it's mandatory that you confese and acknowledge that Jesus Christ is
lord,A day is coming when the arrogance people will come to a halt where the pride of people the
plignative of men ,the brilliant of people and the intellectual capabilities of people/men will mean
nothing and on that day ever knee will bow,and the lamb shall make war revenquish the power of the
enemy among us,we mute the voice of the adversery.we discredit the voice of the accuser of your
people in the name of Jesus,we command salvation for All",ta ɗan tsagaita kafin ta fara kai kawo a
harabar gurin da ta ke.

"Now let God arise in the name of he,seated on the right of the father to ever make intercess,our soon
coming king, Jesus Christ the son of God ,the lord of the all time and age,you are on the throne, you are
the Lord".

"We are a chosen generation,we have been called forth to show his excellent, hey all I required for
life".
Sai da ta kawo nan a zancen ta sannan duk taron mutanen da ke cikin Church ɗin suka zauna kafin
daganan ta yi ma gan ɗin ta da suka iso yau alamar da su sakar mata sauti ,cikin tautaysan lafuzanta ta
da tsara waƙararta mai taken New soul,"Pass me not

O gentle saviour

Hear my humble cry.

Oh! and while on others.

Thou art calling

Do not pass me by

He he he

Pass me not

O gentle saviour....

Haka ta cigaba da raira waƙarta hatta kai ƙarshe kafin su cigaba da gudanar da event ɗin su ,kamar
yanda su ka saba,sosai ta samu yabo gun manyan mutane da Pastors da ma Revered.

A gajiye ta dawo hotel ɗin,bayan ta rabu da su Papa sun tafi na su masauki su.jin knocking ɗin door
ɗin ta yasa ta miƙa a ɗan kiɗime tana mai tambayar waye,"Who is on the door",ta tambaya cikin
rarrababbiyar murya,"Am ki buɗe ƙofar,Ni ne ba wani abu zai faru ba,i just come to see you","Oh Blood
of Jesus Christ Fedrick kai ne wai ,to ka sani I'll not open ba zan buɗe ba,ka koma inda ka fito"...."Ni.no
don't say that,Bai kamata ki aikata haka ba,na yi ta bin ki tun a Church Amma ki ka ƙi ssurarana kin ga
bai kamata in zo nan ba ki sake watsamin ƙasa a ido ba".

"Okay ka cigaba da tsayuwar a wurin in ka gaji ka tafi",ta na kaiwa nan ta kwashi abubuwan da za ta
buƙata ta nufi bedroom ɗin ta haka ya cigaba da bugawa ya na magiya har daga ƙarshe ya haƙura ya
tafi ,bayan ya tabbatar ba za ta buɗe ba duk da haka a cikin ransa bani wani abu da ya sauya game da ita
ba,don haka ma ya ƙudurce a cikin ransa gobe ma zai dawo.

Washegari Ester Monday haka suka cigaba da gudanar da event ɗin su kala-kala,kafin daga bisa ni su
tashi,taron ya koma gidajensu,irin taron family, friends da sauran su.

Ita kanta Jadeeda hankalinta ya yi Gida ta ƙosa ta tafi cikin family ɗin ta su yi Shagali kamar yanda su
ka saba,haka ta nufi Room ɗin ta ta fara haɗa luggage ɗin ta domin jirgin safe ta ke son ta bi.

"Blood of Jesus!", shine abinda ta faɗa cikin firgici da tashin hankali bayan ta ci karo da Fedrick zaune
akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a Parlonta.....
Part 33

"Wai tsaya kar dai ki ce min tafiyar da na ji Mahaifin ku yana magana akanta ita ce wannan munafukar
kishiyar ta ki ta shiga ta fita aka tafi da ita?",Mama ta tambayi Zeenat.

"Tafiya kuma Mama dama kin san da maganar tafiyar ne ke","Shakka babu na san da wannan tafiyar
amma ban taɓa tunanin zai ce zai tafi da wata a cikin ku ba,domin na ga bai cika tafiya da ku ba in har ba
ko aikin Hajji bane ya kama shi","To ai gashinan yanzu ya tafi da matar so ya bar ta ki ƴar da tarin baƙin
ciki,da kin sanar da hakan ai da tani ta kasance cikin shirin ko ta kwana".

"Taɓ Allah Aunty Zeenat kar ki yarda kar ki kuskura ki bar su ,su ji daɗin zaman garin,ki kira shi ki tada
mashi hankali",cewar Asiya.

"Ai kuwa haka zan yi barinsa in kira shi","Yauwa Aunty Zeenat kar ki wani yi duba dare ya yi maza kira
shi ".

Haka ta fara kiran shi amma ana ce mata user busy,shi yana can ya na waya da Baba ƙarami yana ba shi
labarin yanda taron ya ke shirin kasancewa.

"Abbu komi lafiya,yanzu ma haka dawowata kenan,mun fara tattaunawa akan yarda taron zai kasance
zuwa gobe da safe ma in sha Allah za'a fara taron,za'a gudanar da taron live ne ma","Masha Allah a
labari ya yi daɗi,ina maku fatan nasara,zuwa da safe zan sake kira,daganan ma sai in haɗa ka da Baba
Malam domin ya damu yana son jin muryarka","Allah sarki nima ina kewan rikincin sa,na yi kewan ganin
sa",....."Gidan ku Muh'd Jaheed yanzu mahaifin nawa ka ke kira da mai rikici,sai dai ko Hibba ce
rikitacciya ba shi ba,shin ko kun haɗu da Alƙasim?","A'a ba mu haɗu da shi ba mun dai yi waya ya ce zai
ɓullo mu haɗu da shi","Hakan ya yi in yaso in ka sami dama sai ka leƙa Companyn ka ga yanda ake
gudarnar da shi","To in sha Allah zan yi ƙoriri in ga naje",da haka su ka gama hirar ta su,ya nufi Room ɗin
sa mai Number 264,kafin ya ƙara sa wayar shi ta sake wani ringing ɗin, dakatawa ya yi,yana mai picking
ɗin call ɗin ,"Ka sa a dawo min da Yarona kamar yanda ka ɗauke shi da kan ka",shine lafazin da ya fara
ratsa dodon kunnensa,dan ne abinda ya ji yai ta hanyar cewa,"Ummu Nurain ki na lafiya kuwa?,da irin
wannan kalamin ya kamata ki tarbe ni,ko kin manta tafiya nai,tafiyar ma mai cike da da hatsari,eh mana
hatsari mana tunda na hau flight ne,amma kuma sai ki rasa da me za ki tarbe ni sai da irin waɗannan
zafafan kalaman ?".

"Zafafan kalamai ai su suka fi dacewa da kai,shin kai ka manta abinda kai min kafin barowar ka Gidan
ne ?","Hmmmmmm Zeenatu kenan ,ban san sai yaushe za ki sauya wannan halin na ki ba",...ta katse shi
da cewa,"Ka ga ni ba wannan ce ta sa na kira ka ba,kawai ka sa a dawo min da ɗana ko kuma wallahi in je
har Gidan inyi tijara iya ta kuɗi Sannan in ɗauko ɗana","Zeenatu dan Allah kar ki fasa ki je Gidan,ki je ki
aikata duk abinda ki ka so,ba dai Nurain bane je ki ɗauko shi,Ni kuma ina mai tabbatar maki da sai na
raba ki da shi ,ke ko da makarantar almajirai ce sai na kai shi".....

"Ɗan nawa za ka kai makarantar almajirai?",ta tambaye shi cike da mamaki,"Oh kina ganin hakan ba zai
yiwu ba ne ba,to ki gwada ki gani,daga nan sai ki ga zan iya aikatawa ko ba zan iya ba".
Kuka ta fashe da shi da iya ƙarfinta tare da cewa,"Wallahi Yaya Jaheed baka isa ka raba ni da ɗana
ba,ina nan ina jiran ka ba zan bar duk abinda ka ke min ya tafi a banza ba,na rantse sai ka riski tashin
hankali,musiba da kuma fitinar da baka taɓa zato ba a cikin Gidan ka ,ina jiran ka ka dawo ka iske ni,abu
ɗaya zai hana faruwar duk abinda na lissafi maka ka sa a dawo min da ɗana gabana",tana kaiwa nan ta
tsinke wayar gami da ƙara ƙarfin kukanta,tare da cewa,"Mama wai kinji in har na je na ɗauko Nurain sai
ya kai shi makarantar allo don ya nuna min ya fini isa da iko akan shi","Makarantar allo kuma akan me ba
gatanan ana yi a Gidan su ba mai zai sa ya tafi uwa duniya?".

Saboda ya nuna min ni ba a bakin komi na ke a wurin sa ba shiyasa","A'a wannan lamarin ya yi nisa bari
Baban ku ya dawo sai na sanar da shi don ayi ma abun tufkar hanci tunda wuri.

Sai faman kai kawo Jaheed ya ke,a harabar ƙofar Room ɗin nasa shi bai shiga ba,sai saƙawa da kwance
Wa ya ke,shi a nashi tunanin a iya abinda ya aikatawa Zeenat kafin tahowarsa ya isa tai hankali gami da
shiga cikin taitayin ta,ya yi tunanin ,za ta zauna ta gano dalilin da yasa ya ke nuna mata irin waɗannan
sabbin halayen da kuma ko in kular da ya ke yi mata,amma da alama ya ga hakan ba lalle ne ya yiwu
ba,tunanin shi kuma kacokan ya koma wajen samun hanyar da zai nusar da Ummu Nurain kuskuren da
ta ke aikatawa,a baya dai yasan ya yi lallashin ya yi mata alkunya,ya fito fili ɓaro-ɓaro ya nuna mata
kuskurnta,har ta kai shi ga ƙaro mata abokiyar zama,yanzu kuma ya fara nuna mata halin ko in kula
amma duk da hakan ba a samu wani canji daga gare ta ba sai ma ƙoƙarin ƙara fanɗarewa da take,a
kullum sake tsiro da sabbin halaye take,a da iya ƙazanta ce kawai ta ke fama da ita,yanzu kuma ta kai har
ta iya fuskantar fuskar shi ta gaya masa duk kan kalan maganganun da su ka zo mata a baki,rashin kunya
kamar me,ba tare da ta yi la'akari da matsayin shi a wurinta ba,to yanzu ta ina ya kamata ya ɓullo
mata ?, shine abinda ya tsaya masa a Zuciya hana shi samun matsaya ko madara akan haka.

"Ka ga Fedrick ka fitar min a ɗaki,I said get out of my room,ni na rasa ta wacce hanya ka bi ka shigo min
ɗaki","Kin ga Jadeeda babu inda za ni inanan har sai ki faɗa min wanne matsayi na ke a cikin Zuciyar
ki,na gaji I'm tried,son ki ya daɗe da yi min illah,yanzu nema ya ke ya haukata ni,ba zan iya ba,akan ki na
rabu da iyaye na,na zaɓi in kasance da ke don kawai ina tsananin son ki, na gaji babu inda za ni",ya kai
zancen ya na mai gyara zaman shi.

Iya ƙololuwar tashin hankali Jadeeda ta shiga ji take ina ma da ta sani ta bi Papa masaukinsa da irin
haka bata faru da ita ba.

Cikin ƙasa da murya gami ,tausasa ta ya ce,"Haba Jadeeda ki ji tausayi na mana,kin sani iyayena sun
daɗe da musulunta na rabu da su na zaɓi da inyi rayuwa da ke,duka Gidan mu Musulmai ne,Ni kaɗai ne
mabiyan addinin Cristian,saboda ina jin tsora gami da tabbacin in na rabu da shi kamar na rabu da ki,
amma ke a kullum ƙara yin nisa da ni ki ke,babu wata halitta da ki ka tsana ta raɓe ki sama da ni,mai na
aikata maki har haka".

Can nesa da shi kaɗan ta samu ta zauna tare da cewa da shi,"Ba wai na tsane ka ne ko bana son ka ba
ne ba a'a,just ba na son maganar Aure ta na shiga tsakanina da kai,zai fi kyau mu cigaba da yin friendship
ɗin mu like yanda mu ka faro tunda farko ",.......ya katse ta da cewa,"Saboda me uhm?, saboda ban kai
matsayin fitacciyar mawaƙiya kamar ki ta so ni ba,ko saboda ba na da kyawun da za ki iya nuna ni a
matsayin Mijinki ? ".
"Oh God Fedrick ka maida hankalin ka jikin ka mana , soyayya fa bata yiwuwa ta ɓangare guda,dole
sai kana ra'ayi nima ina ra'ayi,na ce ba na yi ko dole ne,kabar ni dan Allah ka je ka nemi wata".

A hargitse ya juyo ya na mai bin ta da shanyanyun idanunsa ,ita kanta sai da ta tsorata ,kasa ce mata
komi yai sai da ya janyo bottle ɗin Wane ɗin da ke gefen shi ya ɗaga kai ya sha iya shan shi kafin ya ce da
ita,"Ba ki so na fa ki ka ce ?,in tafi in ba ki wuri,anya kuwa ba akwai wani wanda ki ke so ba da ya sa ki ke
treating ɗina like that ba?",ya kai ƙarshen tambayar yana mai sake ɗaya bottle ɗin wine ɗin sa sai da ya
shanye ta tas sannan ya cire bakin sa a jikinta tare wular da ita a tsakiyar ɗakin gami da miƙewa ya nufe
ta yana mai cewa,"ki ba ni amsa ta shin kina da wani wanda ki ke so ne,ko yaya",ya sake tambayar ta
cike da tsawa,gami da cigaba da kusantowa inda take".

"A'a..... a'a...... Fedrick ka dakata,ka dawo cikin hayyacinta,kar ka aikata abinda za kai da na sani akan
sa","Ba wani danasanin da zan yi ,anya kuwa kin don zafi gami da raɗaɗin da nake ji a cikin Zuciyata a
saboda san da na ke maki, a'a bana tunanin kin sani,amma ina son in tabbatar ma ki da ina maki
mahaukacin so da zan iya aikata komi akan sa,hakan ya sa ba zan taɓa iya jurar ganin ki da wani ba,ba
shakka in haka ta kasance mutuwa zan yi baƙin cikin da takaici sune za su zama silar yankewar
rayuwata,kin san wacce irin rayuwa na ke gudanarwa tun bayan rabuwa da ke da nayi a U.s na sha
wuya ,har jinya na yi kamar zan rasa raina,da ƙyar na samu na farfaɗo da saran zan sake haɗuwa da ke
amma ina hakan bai yiwu ba domin kin toshe duk wata kafa da ki ka san zan iya bibiyarta in iso gare
ki,wai wacce irin tsana ki kai min for the God sake?".

Cikin rawar murya wacce ke bayyanar da asalin tashin hankalin da take a ciki ta ce da shi,"Ba tsanar ka
na yi ba,kawai dai ina son".......ya katse ta da cewa,"Ki na son me kar dai ki ce min sunan wani za ki furta
min a matsayin wanda ki ke so",ya faɗa cikin sigar wine ɗin da ya sha ta fara aiki a jikin sa.

Kafin ta ce wani abu ya ɗora da cewa,"Da in bar hakan ta faru gara in kashe ki , sannan in dawo in
kashe kai na na san wata ƙila in muka je can lahira za ki iya so na,in kin ga ba wani wanda y fi ni a kusa da
ne ,kin ga kenan zamu rayu a matsayin Mata da Miji a rayuwar barzahu da za mu gudanar",ya kai zancen
yana mai rarumo tsagin bottle ɗin da ya sha ya nufe ta da shi sai faman tangaɗi ya ke,alamar ya fara
buguwa.



Jikin Jadeeda tuni ya daskare ta kasa ko motsin in kacire zuciyarta da kanta da ta ke faman girgizawa
dakuma zuciyarta da ta ke faman bugawa da sauri da sauri,in Banda su ba abinda ya

Please Login or Register in order to submit comment