You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya na fad`in baya san ganin ta,wanne irin
Zunubi ne ita kuwa ta aikata da har ta can-canci irin wannan hakuncin.

Ganin da gaske ba zata fita ba kamar yanda ya ya ke so yasa da kan shi ya fizge Jaheed dake rungume
a jikinta ya ja hannunta a tsiyace bai sake ta ba har sai da ya kai ta tsakar Gida sannan ya jefar da ita har
yunk`urin fad`uwa k`asa tai.

Tun kafin ya ce komi Baba Asabe dashigiwar ta Gidan kenan ta fara sallallami gami da cewa,"A aha wa
idona je gani kamar Hibba, sai yau mu ke ganin ki `yar dad`i Miji ?",Salatin da ta saki ne ya janyo hankalin
sauran mutanen Gidan
"Ban damu da ki cigabada da zuwa cikin Gidannan ba ko ki daina ba amma da ga rana irin ta yau na
haramta maki shigowa cikin nawa sashen,Na yafe ki bani ba ke,ki fita harka ta kiyi taki harka ki aikata
duk abinda ki ka so,Na cire hannuna a cikin dukkanin lamuran ki"......

" To sai me idan ka cire hannunka a cikin lamarin ta shin zata mutu ne ko wani abun na daban da babu
shi a cikin littafin k`addarar zai same ta?".Cewar Mama Hadiza da fitowar ta kenan

"Ki gafarce ni Mama amma wallahi Hibba ta kunyata ni,gabad`aya ta fita a raina taje can ta yi rayuwar
da taza`ba ma kanta amma ba shakka wata rana za ta fahimci ta aikata kuskure,a lokacin da ba lailai ne
ta iya gyara shi ba"...

"Kar ka kuskura ka yima `ya ta baki ,domin ba kai ne ka haifar min ita ba,idan kuma ka sake sai na
wanka maka Mari a fuskar ka", Ba shi K`aramin da aka ce za a mara ba ilahirin mutanen Gidan da suke
tsaye a wurin sai da suka sha jinin jikin su

Cikin sauri,in'ina had`i da sheshshekar kuka Hibba ta shiga tsakanin su ta na mai cewa,"A'a Mama haka
ba za ta faru ba,in dai akai na ne bazan yarda ki d`ora hannunki a jikinsa da sunan hukunci ba,zan tafi zan
daina zuwa har sai sanda shi da kan shi ya gaiyato ni cikin Gidannan,zan jure zafi,rad`ad`i da kuma
kewarku da zan yi har zuwa sanda zai yafe min laifin da yake zargin na aikata,ko kuma ranar da gaskiya
za tai halin ta".

" A'a Hibba ba inda za ki ,Kema `yace haifaffiya a cikin Gidannan don haka ba inda za ki".

"A'a Mama ko da ni ke `ya a cikin Gidannan ban kasance mai yi maku biyayya ba, ko mai sanya ku cikin
farin ciki ba,danvhaka tafiya zan yi",ta na kaiwa nan ta juya ta nufi hanyar fita daga cikin Gidan ba tare
da ta bi ta kan haka ko wayarta da ke d`akin Mama Hadiza ba.

Tana fita kuwa tai sa'a ta ci karo da mai a dai-daita ta shiga,sai da su kai nisa sannan ta tuna da ta baro
waya da Jakarta a can,mai a dai-daita d`in ta rok`o ya bata aron wata ta Kira Abbakar.

Yana jin muryarta hankalin shi ya tashi , fitowar shi kenan daga meeting d`in nan take yai handling d`in
komi a wurin assistant managern sa yayi Gida hankali a tashe.




*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a




BOOK 1




PAGE 6 ❤

FREE PAGE



"Na rok`e ki ki dakatar da wannan kukan,yana tada min hankali,ba zan iya jure ganin ki a cikin irin
wannan yanayin ba,kisanar da ni me ya faru?".

Cikin sheshshekar kukan da ya ci k`arfinta tace da shi," BBB...bbbb...babu komi babu abinda ya faru
kawai na dawo Gida ne".

Tsuru yai ma ta da idanu ya na kallonta,fuskarnan ta ta har wani yellow-yellow ta ke saboda kukan da
taci.

"Ban damu da dole sai kin fad`a min me yake faruwa ba,amma dan Allah ki dakatar da
kukannan,Zuciyata ba za ta iya d`auka ba,ina jin zafin da zuciyata ta ke min har a saman gangar jikina",
ya kai zance yana mai share mata hawayen da ke zubowa daga cikin idanunta.
Kafin ya d`ora da cewa "Ban da damu da duk wani abu da ka iya biyo bayan tarayya ta da ke ba,abu
guda,kawai na ke so daga gare ki", tsam ta mai da hankalin ta gare shi gami son jin me zai buk`ata a
wurin ta.

" Ki yarda da ni, ki bani amanar rayuwar ki,zan zame mi ki bango majingina kuma kafad`ar da zaki d`ora
kan ki akan ta,zan baki farin ciki, in maye mi ki gurbin abinda ki ka rasa,burina da kuma fatana ki amince
da ni,zan kasance da ke a kowanne irin yanayi ".

" Na dad`e da amincewa da kai kuma na yarda da Soyayyar ka a gare ni gaskiya ce,ko da wasa bana da
niyar barinka,Na shirya fuskantar fiye da abinda ma fuskanta a yau indai akan ka ne".

''Tu da har haka ne ki daina min asarar hawayennan na ki,domin ni a gare ni suna da matuk`ar
tsada,sun fi lu'u-lu'u,Zinari ko tagulla".

Yanayin yanda ya kai k`arshen maganar tashi ne yasa ta fara sakin fuskarta har da d`an murmushinta.

"Yauwa kin ga yanzu tunda kin saki fuskar ki sai a zo ai girki bari muga yau me za a cika yaji ko gishiri ko
kuma dai ruwa za a cika ?".

"No...no...wallahi ka bar shi indai haka ne,gara in girka da kaina tunda dama aiki na ne"," A'a ni zan yi
ki zauna ki huta abin ki".

Haka dai suka dinga jayayya har k`arshe dai su kai girkin a tare ba tare da ya barta ta samu damar da
zata tuna abinda ya faru da ita a Gidan su ba.



₹₹₹₹₹₹₹



Cikin natsuwa da kamala Baba Malam ya fito daga motar da ta kawo shi har Gida bayan sun gama taron
su na mayan malamai,a koda yaushe cikin shiga ta kamala yake ,hannusa rik`e da casbaha,duk da
kasancewar ya manyanta tsufa ya bayyana a gare shi amma ko kusa ba dagazawa ko `yankwanewar
tsufa a tare da shi,tun da ya tun karo Gidan na shi ya ji hankalin shi bai kwanta ba har ya sa k`afarsa a
cikin farfajiyar Gidan, ganin mutanen Gidan tsaye cirko-cirko ya sa ya k`arasa wajen cikin hanzari tare da
tambayar su,"Lafiya me yake faruwa anan?".

Cikin sarewa da kuma yanayin da ke bayyanar da d`acin Zuciyar da mai magana yake a ciki Mama
Hadiza ta ce,"Gashi nan tambayar shi sai ya fad`a ma ka me ya ke faruwa,ya gaya maka ya kasa d`aukar
k`addara da jarabawar da Allah ya saukar akan Hibba, har sai da ya kai ga ya fito gaba da gaba yana
fad`ar munanen kalamai da son aibata ta a gaban mutane".

"Subbahanallahi K`arami me ya ke damun ka,ina hankali,ilimin da tunanin ka ya tafi,mai yasa kake
aikata aiki irin na jahilai ?".
"Baba Malam ka gafar ce ni,ba wai ina nuna damuwata akan Auren da Hibba ta yi bane ba,a'a can
jawar d`abi'un ta sune abinda ya kasa goguwa a cikin rai da zuciyata".

Baba Asabe ce ta d`an matso gaba gami da cewa" Hehehe nanaye yau `yar gwal kuma `yar so ta aikata
kuskure,kuskuren da ke neman kawo hatsaniyar da ba a ta`ba yi a cikin Gidannan ba",ta d`an dakata ta
na mai fuskanta inda Malam K`arami ya ke da Cewar,"Ni fa ban ga laifin ka ba Yarinyar da idanun ta suka
bud`e ai kamata yai a sallamawa duniya ita ta je can taci gashin kanta ",.....



"Ki dàkata min na ce Asabe,ki bar ni dan Allah in yanke hukunci a cikin Gidana".Malam Babba ya faɗa a
zafafe,duk da ta ji maganar tamkar saukar aradu hakan bai hanata ta turo kallabinta kan goshi ba,sannan
ta juya ta na mai `yan maganganu k`asa-k`asa,ba wanda ya sake bi ta kanta.

" Ka bani mamaki K`arami da har ka kasa iya jure abinda ka ke ji har sai da ka bayayyanar da shi a ciki
kowa ya fahimta,tun bayan yayenta mahaifiyarta ta bar maka ita sakamakon ganin kai ne kad`ai a cikin
`ya`yanta Allah bai ba haihuwa da wuri ba, Hibba fa kaine ka raine ta kuma ka tarbiyantar da ita,duk
wani abu da take yi koyarwarka ce,ba ta shak`u da uwa Mahaifiyarta ba kamar yanda ta shak`u da kai,ka
bani kunya da mamaki tunda yau har sai da ka kai ga k`ureta har ta na k`ok`arin kai hannunta jikin ka,To
bari kaji bayan yarda na d`aura Auren Hibba ba sai da nayi cikakakken bincike akanta da ma duk wani
abu da ake zarginta,har cikin makarantar ta su sai da na je,kai ba ma iya makarantar su ba har ma'aikatar
da ta ke koyan aikin sai da na je,Babu abinda na ji sai yabo da shi albarka game da ita,to ka sani Hibba
bata can ja daga Hibban da ka raina ba,har yau har gobe bata aikata wani abu na tir ko ashsha
ba,hasalima ni alfari na k`arayi da kasancewar Hibba cikin tsatsona,ya rage ruwanka ka nemi gafarta ko
kuma ka cigaba da zarginta,ka sani kaima kana da wasu `ya`ya a haka zaka tarbiyantar da su Zuciyar ka
cike da zargi da kuma rashin yarda ?".Baba Malam na kaiwa nan a zancen shi ya bar wurin ba tare da ya
bi takan kowa ba,itama Mama Hadiza juyawa tai ta bar gun fuskarta d`auke da farin ciki wanke `yarta da
Baba Malama yai a gaban mutane.

Haka mutanen wurin da suka taru suka fara barin wurin da d`aya da d`aya,Baba K`arami kuwa jikin sa
a sanyaye ya nufi na shi sashen.

Hannu bibbiyu ya tallafe kan shi ya rasa wanne irin tunanin ma ya kamata yayi kuma wacce mafita ya
kamata ya samu yai amfanin da ita.

"Ka gani ko Abban Jaheed so nawa ina baka hak`uri akan ka tsaya kai bincike akan wannan lamarin
amma ka k`i yanzu ka ga me Gari ya waya ko?".

"Ke dai bari Ummien Jaheed ban san me ya shiga kaina ba,a yanzu na yi danasani har ban san ta ina ya
kamata in fara gyaran kuskuren da na tafka ba".

"Ka je ka same ta ka lallashe ta ka bata hak`uri,domin ni a gani na kamar hakan zai fi".

" Shikenan zan je domin ba lalle ne yau in iya rufe idanuna ba tare da na sata a ciki ba".
"Sai dai ko ka kirata ta zo ko kuma ka je Gidan na ta",Sai da yai shiru Na wani d`an lokaci kafin ya ce,"
Gara dai in je Gidan na ta kamar za ta fi jin dad`in haka kuma tai saurin yafe min mummunan zargin da
na yi mata".

"Uhmmmmm haka ne kuma sai ka tambaya a raka ka".

" A'a ba sai an raka ni ba,Na San Gidan",sai da Ummie Maryam ta fiddo idanunta waje kafin ta
tambaye shi da cewa,"Ka san Gidan a taya ?".kau da kan shi gefe yai ba tare da ya bata amsa ba
murmushi ta saki a cikin ranta ta na mai cewa,"Ashe dai duk fushin da aka yi da ita Soyayyar ta na nan a
cikin ran ka".

Ana fitowa Sallahr magariba Malam K`arami ya nufi Gidan Hibba a bakin gate d`in shiga cikin Gidan
Abbakar ya iske shi da matuk`ar hanzari ya matsa kusa da shi,har da duk`awar shi kafin ya bashi hannu
su gaisa.

"Na zo ne ina son ganin Hibba", Baba K`arami ya ce

" Haba Malam ai da kasani Kira na kai sai in kawo maka ita har Gida komin dare ba sai ka wahalar da
kan ka ka zo ba".Abbakar ya fad`a cikin girmamawa

"Kar ka damu babu wani abu kuma na San in na zo da kaina za ta fi jin dad`i shiyasa ma na zo",sosai
Maganar ta shigi Abbakar tunda a iya sanin shi Baba K`arami na d`aya daga cikin wad`anda ba sa son
Auren sa da Hibba,bai san wanne irin sauyi ne aka samu da sauri daga gare shi ba.

" To ka shigo ciki mana kamar zai fi","A'a bar nivanan kawai kai mata magana ta fito sai mu gaisa in
koma","A ba ayi haka ba dan Allah ka shigo",da kyar Abbakar ya samu ya yarda zai shiga amma da fir ya
rufe idanunsa akan ba zai shiga ba,haka ya jagoranci shi har cikin Parlourn su ,lokacin kuma ita Hibban ta
na k`ok`arin tashi daga kan prayer mat d`in da ta idar da Sallah.

Duk da razanin da ta shiga na gani sa hakan bai hana ta nufi inda ya ke ba,bakin ta sai k`ok`arin son
cewa wani abu take amma ta kasa.

" Allah Sarki k`anwata mamaki ki ke na gani na a cikin Gidan ki ko,gami da fargabar abinda ya kawo ni
ko ?,to ki kwantar da hankalin ki na zo ne in baki hak`uri akan dukkanin abinda ya faru ,Na gane gaskiyar
lamarin ki yafe ni,ban kasance" ......

Sai da ta duk`a har k`asa kafin ta e "A'a dan Allah ka bari ban can-canci haka daga gare ka ba,ni fa
k`anwar ce kuma `ya a gare ka bai kamata ka rik`a bani hak`uri ba".

" Wa ya gaya maki haka Hibba, ai a addinin mu duk girmanka in har kai ma wani laifi kuma ka gane
kuskuren ka,to ka bashi hak`uri ka nemi ya fiyar shi komi k`ank`antar shi ko da kuwa kai ka haife shi ko
wani abu makamancin haka,babu girman kai a addinin mu,haramun ne aikata shi dan haka ina rok`ob ki
da ki yafe min ki manta komi da ya faru kar ki rik`a shi a cikin ran ki".

"Wallahi Allah na yafe maka duniya da lahira kuma ni dama ban rik`e da komi ba kullum addu'a ta
Allah yasa ka fahimce ni kar mu cigabada da rayuwa a haka don ba zan iya jurewa ba".
" Allah kam ya amsa addu'ar ki ashe ni ne a duhu Baba Malam ya riga da ya dad`e da fahimtar duk
sharri akai miku,yanzu haka kowa na Gidan ya san baki da laifin komi ba ki aikata abinda ake zargin ki da
shi ba".

Sosai fuskokin su suka yalwata da jin wannan labarin,"To ya Mama itama tana farin ciki ?",ta jefo mishi
da tambayar.

"Eh itama tana farin ciki,ji taje kamar gobe ma ki dawo"," Ai ko in dai haka ne Goben ma zan zo"....

"A'a a'a kar ki zo ki bari sai wani lokacin amma zan turo maki da Yaron ki yai miki yini tunda gobe
weekend".

" To shikenan yanda ka ce,ko a hakan ma zan yi farin ciki,Allah ya kai mu goben ".

Duk abinda suke Abbakar na kallon su gwanin burgewa har fata yake ina ma da shi ne da nashi dangi
ne a cikin irin wannan yanayin na farin ciki.

" Yayah bari in kawo maka wani abu kaci kafin ka tafi".

"A'a kar ki wahalar da kan ki domin ba abinda zan ci,tafiya zan yi".

" A'a Malam bai kamata ka zo ka tafi ba tare da kaci wani abu a cikin Gidannan ba ko Yaya ya ke".

"Kwayi kwa gama ba abinda zan ci,tun da na gama abinda na zo yi kunga ma tafiyata", ya fita abinshi
ba tare da sun yi nasarar dakatar da shi ba,ita Hibba san da zata fito daga kitchen har ya riga da ya
fita,sai tsaye tai hannunta rik`e da himilin kayan abincin da ta jero ma shi akan tire.

" Ya akai ka bar shi ya tafi dan Allah? ",ta tambaye shi cikin shagwa`ba.

" To ya zanyi Babe,ya ce a'a kuma kin ga babban mutum ne bazan iya jayayya da shi ba".

"To shikenan amma ban ji dad`i ba na so ace yaci wani abu a zuwan shi na farko Gidana".

Matsowa kusa da ita yai ya na mai amsar kayaan hannunta ya aje gefasu sannan ya d`ora da cewa," To
mene ne na damuwa,ya riga da ya dawo gare ki gabad`aya fa,a koda yaushe fa yanzu za ki iya zuwa ki
gan shi,kuma kina da damar da za ki girka duk abinda ki ke so anan cikin Gidan na ki ki kai ma sa har Gida
kuma ya ci to me zai dame ki ?".

Ba k`aramin jin dad`in lafuzzan da suka fito daga bakin shi tai ba,har sai da fuskar ta ta yalwata da
murmushi har kasa rufe bakinta tai sai cewa tai da shi,"Kuma fa haka ne ka yi gaskiya,yanzu zuwa nan da
yaushe ka ke ganin ya kamata in sake kai masu ziyara ?".

"Yanzu za ki shirya muta fi,k`arshen murna da zumud`i".

Turo masa baki tai gami da shagwa`be mi shi fuska,shima yanayin yanda tai da fuska haka yai gami da
tsare ta da idanu.
Ganin haka ya sa tai rau-rau da idanunta za tai mashi kuka da sauri ya matso kusa da ita yana mai kai
hannunsa saman kunne shi ya rik`e ta re da fara bata hak`uri da cewa,"Na rok`e ki kar ki `bata wannan
farin cikin dake kwance asaman fuskar ki ,kin ga a yanzu muna da goyan bayan ahali gabad`aya akan
maganar Auren mu".

" Ni ma tuna hakan nasa ni injini a cikin wani mad`aukakin farincikin in kuma kara sakankancewa da
iko,girma d`aukaka da buwaya na Ubangiji na Allah,da ya aikata abinda ya so a sanda ya so akan lamarin
mu ".

"Haka ne My wife yana da iko fiye da haka ma dan haka yanzu mu gode mi shi akan baiwa da ni'imar
da yai mana".

" To Habibina yanda ka ce ai haka za ai fad`a taka cikawa tawa",ta kai k`arshe zancen murmushi
kwance a saman fuskarta.




*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a




BOOK 1
PAGE 7 ❤

FREE PAGE



"Why are you disturbing me Cecelia, in this early morning, kin kira kin kira na ki d`agawa ba sai ki kyale ni
ba haba dan Allah, yau fa Sunday ce,yauce ranar guda kawai da make samun hutu".....

"Deborah ce ba Ceceliar da ka raina ba", Grandma ta katse shi cikin d`aga murya.

Cikin in'ina da kuma rud`ewar da yai sakamakon jin muryarta da yayi,"Grandma", ya ambaci sunanta
tare da d`orawa da cewa,"Kiyi hak`uri ban san ke bace ba shiyasa ban d`aga da wuri ba".

" Oh kayi tunanin marainiyar wayon taka ce ko, to ba ita ba ce nice,Anya Daniel, ba akwai wani abu da
kake `boyemin ba wannan sauyin naka ya fara bani tsoro,let me ask you kana ma zuwa Church kuwa?".

Wani zazzafan gumi ne ya fara keto mi shi tare da sanyi a lokaci guda,har sai da Grandma ta sake
tambayarsa tare da cewa,"Wai ko ba ka jin abinda nake cewa ne?".

Shiru Abubakar yai hankalin shi yai matuk`ar tashi hakan ya sa ya kasa iya sarrafa harshen shi.

"Na shiga uku ni Deborah, me nake shirin ji haka daga gare ka,Yesu Almasihu ka kawo min
d`auki,yanzu Daniel so kake kace min ka daina zuwa Church wanne rud`un duniya ne ya same ka,ko so
kake ka ta`bewa ta samu wurin zama a cikin rayuwar ka,me kake so ka zama ?", ta tambaye shi cikin
tsananin tashin hankali.

"Amm mmm...uhmmm.....Grandma ki yi hak`uri ki saurare ni,you know ranar Sunday ita kad`aice ranar
da nake samun hutu,shiyasa nake yawan tashi a makare", muryar shi ta raunana sakamakon k`aryar da
zai mata ya ciga da cewa," Amm...ammm...amma fa ina zuwa time to time ".

" k`aryar ka ke Daniel, you are a liar ba ka zuwa Church muryarka ta tona maka asiri,Na shiga uku na ni
Deborah, Anya ba sauya min kai a kai ba,haka fa nai ta fama da kai ka zo muyi Merry Christmas tare da
kai k`iri-k`iri ka k`i zuwa,har happy new year mu kad`ai muka gudanar da shagulgulan bikinta,,wai meke
damunka mene ne ya sa kasauya,me kake son kazama da har ya sauya d`abi'un ka har haka,Daniel ka
gayamin asalin gaskiyar da ke faruwa anan ?",ta kai k`arshen Maganar da sigar tambaya cikin nuna
tashin hankali da kuma fushin da ta ke a ciki.

Sai da Abubakar yai da gaske kafin gwarin gwuiwa gami da dakiyar Zuciya ya ce da ita,"I swear ni ba
abinda ya canza ni,inayin bauta iyakar iyawata ina zuwa wurin bauta gami da tsarkake ko neman kariyar
kaina daga dukkanin wani abun k`i ba lalle sai ranar Sunday ba duk ranar da na samu sassaucin aiki ina
kai ziyara zuwa Church ".

" Hah Daniel ban yarda da kai ba I'm not believing you,you are a big liar,ka kawo min wata hujja guda
ɗaya da za ta iya sawa in amince da kai ".

"Grandma i swear ina zuwa Church, mai zai sa in bar asalina,in bar koyarwa da tarbiyar da ki ka bani
ba".

" To in har haka ne ka tashi a yanzu ka nufi Church d`in da kake attainding ka had`a ni da wani Pastor
ko Reberal to fa sannana ne zan gasgata abinda kake cewa".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un",shine abinda Abubakar ke ta yawan mai-maitawa,yau ya tabbata
sharri ko illah da k`aryar ke dashi,a yau ya k`ara tsanar k`aryar da yake mata tun bayyan musulumtar
shi,bai san dalilin da yasa yake tsoro da shakar gaya masu ya musulumta ba,ko dan tsoran kar yarasa su
amatsayin su na dangi kuma ahalin da yake da da su akaf fad`in rayuwar sa.

Idanuwansa da suka rine sukai jajajur ya sauke akan Hibba da tun farkawar ta a barci taga bashi a cikin
bedroom d`in ta biyo sa Parlourn, yanayin da ya gani akan fuskarta yasa shi yai saurin d`auke idanunsa
akanta.

Ammon muryar Grandma da ya sake karad`e masa kunnensa ya fargar da shi gami da dawowa
hankalin shi akanta," I repeat it ka tashi ka je ka had`a ni da Pastor d`in Church d`in da ka ke zuwa ko
wani wanda zai gamsar da ni in yarda".

"Shikenan Grandma......shikenan zan je yanzu amma ki sani duk abinda ya faru da ni it's your fault,
because i'm felling sick, na dad`e kwance bana da lafiya,I spend almost two weeks bana da lafiya,sai jiya
aka sallame ni, na dawo Gida".

"Jesus Christ amma kuma Daniel shine baka gaya min ba,me yasa kake haka,mai yasa zurfin cikinka
yayi yawa,ka ga fad`a min mene ne matakin lafiyar taka a yanzu,ina fatan dai kana samun sauk`i,ka Na
dai taking medicine naka akan lokaci ko ?".ta fad`a cikin rud`u

" Ina samun lafiya in sha Allah tomorrow zan yi resuming a bakin aikina"....

"In sha Allah kuma Daniel, Na ji kamar haka ka ce ko dai kunne na ne ke jiye min ba dai-dai ba ?".

A diririce ya ce da ita"I'm sorry ba haka na ke nufi ba,I mean by the grace of God".

."A'a Daniel there are something wrong don haka,....hello.... hello".....ta kasa k`arasawa sakamakon
mutuwa da wayarta ta yi a dalilin rashin charge.

Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar ya fad`a gami da kai hannunsa saman kan shi ya rik`e alamun
alamun jin zafi ko ciwon da yake ji,cikin sauri ya sake bin layin nata amma kuma yaji wayar a kashe.

" Ya Salam Allah ka sa ba wani abun sabo Grandma ta ke shirin aikatawa ba da har ya sa ta kashe wayar
gabad`aya",shine abinda ya fara fad`a bayan gama kirannata.
"Me ye zai sa ba zaka fad`a ma su ba,ka sanar ma su da Cewar ka Musulumta a bar wannan `boye-
`boyen da kuma shiga cikin irin wannan tashin hankalin".Cewar Hibba bayan ta k`araso kusa da shi game
da mik`a mi shi Glass Cup na ruwa mai sanyi.

Bayan ya sha ruwan ne ya bata amsa da cewa," Ina jin tsoro Hibba, ina jin tsoran abinda zai biyo baya,
idan har suka san gaskiya zan iya rasa su su duka ban san dalilin da yasa na ke jin bugun Zuciya a duk
lokacin da nai tunanin ko yunk`urin aikata hakan ba,Cecelia k`aramar Yarinya ce,ita kuma Grandma ta
tsufa ga shi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,ina jin tsoran halin da za su shiga idan suka samu
wannan labarin".

"Abu mafi a'ala ka sanar da su sai ka fi samun kwanciyar hankali fiye da ka cigabada da `boye wannan
lamarin mai girma a cikin Zuciyarka,ka sani kana tare da Allah, ka Sani dogaro da shi kad`ai ya Isar ma
akan komi".

" Kar ki damu in sha Allah zan yi k`ok`arin aikata hakan,amma yanzu ya jikin naki,ko dai zamu je
hospital ne a sake duba

Please Login or Register in order to submit comment