You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san ingancin su bayan duk da irin su aka raine
ku,koka manta san da kai ma garin ƙiriniyarka ka zuba ma kanka ruwan zafi,ai na ce da irin wannan
maganin mu ka samo kan ka,don haka ba inda zamu yanzu ma zan kira waya imsa a kawo min shi,in
shafa mata",...."Amma Umma Jamila hakan kamar bai dace ba,idan wani abun ya faru da ita kuma fa da
ga baya?","Ka ga je ka ba abinda za faru,Ni inan ma har sai zuwa an jima mun ga halin da take a ciki,idan
naga da wata matsala zan neme ka da gaugawa",ta kai zancen tana mai gyara zama.

"Ka ga je ka abun ka in sha Allah ba abinda zai faru,je ka kayi wanka ka shirya kafito ina son gani
ka",Mama Hadiza ta ce da shi,ba dan ya so ba.

Sai bayan da Mama Hadiza ta tabbata Jaheed ya tafi sannan ta maida kallon kan Umma Jamila ta ce
mata,"Yanzu aikata hakan ki ke ganin ya dace?","To ya zamu yi in har ba so ki ke lamarin ya fi haka ba".

"To Allah ya kyauta In ya dawo ki ce ma shi,Ni na tafi amma ya same ni a Gida",ta kai zancen ta na mai
miƙewa tsaye kafin ta ɗora da cewa ke Bibah,Safina ku ta so mu tafi Gida ,ke kuma A'isha ga kayan
dubiyar da mu ka zo Maki da su in kin ji ƴar dama sai ki ɗan ci wani abun, Allah ya ƙaro sauƙiya kuma mai
da na aike ya kauda fitina a cikin zamantakewar ku",tana kaiwa nan ta tasa su Safina da har cikin ranta ta
ke jin babu daɗi da ba abarta ta juye ma Zeenat ta cikin ta ba.

Tun shigarsa Part ɗin sa bai sake fitowa ba har sai da azahar ta gabato,yai wankan shi fes sanye da
kaftani sai hularsa ƙube da ya kawo ya sanya,sassayen ƙamshi ne kawai ke tashi daga jikinsa,cikin
natsuwa da haiba yake tafiya,ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi Central Mosque inda yake limanci a
ciki,bai wani ɓata lokaci ba ya dawo bayan ya idar da Sallar,kai tsaye apartment ɗin Gimbiya Ayush ya
nufa don ko kallon Part ɗin Zeenat baya son yi domin har wani zafinta yake jin ya na taso masa in ya tuna
da abinda ta aikata,gab da zai shiga Part ɗin ya ga Nurain ya fito a kiɗime sai faman tsalle-tsalle ya ke
gami da sakin ihu iyakar ƙarfinsa,sai faman soshe-soshen jikin sa ya ke tamkar wanda akayi ma wanka da
wuta,da alama dai zane shi ta yi, da hanzarin sa ya nufesa gami da kama shi ya riƙe kam ,sai da ya
tabbatar da ya dawo cikin hayyacinsa kafin ya tambaye shi me ya same shi,cikin sheshshekar kuka ya ce
da shi,"Ba Ummu ba ce ba ta yi min duka don na je na ce mata taba ni abinci in ci yunwa na ke ji,shine ta
ce na cika hayyata ta zane ni ta koroni waje",sai da Jaheed ya runtse idanunsa gami da haɗiye wani abu
mai ɗaci da ya zo ya tsaya ma sa kafin ya ce,"Ya isa haka ka ji Yarona ai dai ka yi break ko ?",sai da yaron
ya fara girgiza masa kai kafin ya ce,"Ni ban ci komi ba ruwan Shayi kawai ta bani,da na ce mata ina jin
yunwa sai ta koro ni,yanzu kuma da na je sai ta koro ni waje ,ta ce in je wajen ubana ya bani abinci in ci.

Jaheed rasa me kuma zai ce yayi duka-duka Nurain nawa ya ke Yaro ne da bai wuce 8yrs ba amma shi
Zeenat ke ma irin wannan izayar,ko kayan jikinsa tun wanda ya sa mishi jiya da daddare ne ɗaukar shi yai
ya je saitin door ɗin yana bugawa da ƙarfin tsiya,daga can ake tambayar waye,ko kusa kasa buɗe baki yai
balle harta samu damar da za ta san amsar waye ke knocking ɗin jin yadda ya cigaba da buga ƙofar ne ya
sa ta fahimci waye a tsaye,zuciyarta kasuwa gida biyu tai wani ɓangaren na cewa ta buɗe masa ko kuwa
ta kyale shi,wanda hakan ba ƙaramin ƙara tunzura shi tai ba,ganin da gaske ba zai daina knocking ɗin ba
ya sa tai shahadar ƙuda ta buɗe ma sa da shirin tarbar duk abinda ya zo da shi,walau na arziƙi ko na
tsiya.

Wani abun mamaki ko ta kan ta bai bi ba sai kewaye ta da ya yi ya shigo,kai tsaye kitchen ya nufa saɓe
da Nurain akan kafaɗar shi ,sai da yai danasanin shigar shi kitchen ɗin domin komi na cikin kitchen ɗin a
ƙazance ya ke kuma a wulaƙance ,da ƙyar ya samu ganin wata ƙaramar tukunya ya ɗora takan elactric
cikin sauri da azama ya ke komi ko ya samu ya dafa masa ko da Noodels ko kuma ya dama masa Custard
ya bar cikin wannan azabbar ƙazantar,domin wasu plates ɗin har sun gaji sun bushe wasu kuma an
tsuma ruwa a cikin su.

Kamar wacce a ka wurgo haka ta faɗo cikin kitchen ɗin idanuwanta cike da masifa,ko ɗagowa bai yi ba
balle ta samu arziƙin ya tanka mata.

"Na daɗe ban ji ko ganin wani mutum mai tauye haƙƙin matarsa gami da nuna fifiko akan ɗaya kamar
kai ba,wai me nai maka ne,da na can-canci irin abinda ka ke aikata min haka",ko motsin kirki bai yi
ba,sai ma cigaba da harhaɗa abinda zai amfani da shi ya ke,"Magana fa na ke maka",ta ce da shi, tana kai
zancen ta na mai kwace Cup ɗin da ya ɗauko,

ganin da gaske ba zai kulata bayansa ta sauke Pot ɗin dake kan Elactric ɗin tare da cigaba da cewa,"Ga
shinan kaima ka watsa min ruwan zafin in hakan zai sa hankalin ka ya kwanta,idan ma hakan bai maka
ba,ga wuƙa ka caccaka min in mutu kowa ma ya huta da ga kai har ni ɗin ,na rasa gane wannan tsananin
ƙiyayyar da ka ke nuna min ba",yanayin yanda ta ke behaving tamkar sabuwar mahaukaciya shine
abinda ya sa ya tsaya yana mai binta da kallo,cike da tunani ko ta zauce ne.

"Zeenat ki fita a idona,ki sani ina dan ne zuciyata ne akan duk abinda ki ke aikatawa,bana son ki sani in
yanke maki hukuncin da za ki yi dana sani da shi,ki shiga cikin taitayin ki da kan ki,a koda yaushe ina maki
fatan shirya a gurin Allah","Na sani ai dama komi ya faru ni ke da laifi,ba za ka taɓa duba da rashin
adalcin da ka nuna min ba,kai fa ka ɗauki kwana na ka kai ɗakinta sannan ka dawo da safe, mamadin ka
fara isowa sashe na amma sai ka sake nufar na ta ɗakin a karo na biyu, wannan shi ne kake kira da naka
salon adalcin ehye ?",

"Tunanin ki shine matsalar ki,baƙin kishin ki shine ke jagorantar ki ga aikata duk wani shirmen da ki ke
aikatawa,ban taɓa ji ko labarin Mata ko Uwa irin ki ba,idan har ki ka cigaba da tafiya a haka,ina mai
tabbatar ma ki da ba wanda zai alfahari da ke cikin makusantan ki,kalli fa wannan yaron ki ne har kawo
iyanzu baki bashi kalacin safe ba,bai ci komi ba,a haka kike kiran kan ki a matsayin Uwa,kalli tarkacen
ƙazantar da ki ka tara,kwanuka sai ƙudaje ke bi,a cikin ɗakin ki babu wani abu daga warin kayan dauɗa
sai tarin datti da ƙazanta,kalli shigar dake ke jikin ki komi na jikin daban ya ke,a haka ki ke kiran kan ki da
Matar Aure,abun akwai rikitarwa a ciki,a yanzu da zan tambaye ki a cikin kalma ɗaya ki faɗa min ko ke
wacce ya za ki iya ?,ki sani wannan halayyar ta ki kan kashe ni da mamaki,wani lokacin na kan shiga
firgici da tunanin wai wa na kawo gidana da sunan Matar Aure,ki sani duk da ina jin ba daɗi amma ki sani
kan ki ki ke cuta ba ni ba,domin inada wata mafakar bayan ke, wannan bala'i har ina, Wallahi Allah ya
sani na gaji ko dai ki gyara ko kuma in runtse idanuna in kauda duk wata alaƙa in ɗau tsatstaauran
mataki akan ki na gaji wannan musiba har ina",ya kai zancen yana mai sa hannu ya ture ta ya sunkuci
Nurain ya nufi Room ɗin ta don nemo masa kayan da zai sauya masu da na jikinsa so,sai dai me duk
kayan da ya ɗauko sai yai dana sanin duniyan akan siyan su ma da yayi gabaɗaya,yawancin kayan,duk
masu dauɗa ne, sai waɗanda akai ma jiƙa-jiƙa ba tare da sun fita ba aka shanya su,ba ruwan ta da
la'akari da tsadar kaya ko wanne iri ne in aka sa su sai sun fita daga cikin hayyacinsu,duk abinda yake
faruwa ta na biye da shi ,ta na mai faɗin duk abinda ya zo mata a baki,amma ko kusa bai kula ta
ba,kalmar da ya faɗa ce ta sa yai tsam gami da zuba mata idanu,"Wallahi kai ba adali ba ne ba,ba ka can-
canci jagorantar al'umma ba saboda ka fiye son kan ka da yawa,kuma idan ka ga ka bar wajennan ka
faɗa min mene ma'anar duk kalaman da ka faɗa a kitchen a kaina,sai ka faɗa min wanne irin mataki ne
ka ke son yankewar a kaina","Ki gode Allah ni ban kasance cikin jerin Mazaje masu bugun Matan su
ba,ko ɗazu ma kin aikata abinda ya kamata in nusar da ke kuskurensa ne tunda wuri",shine iya abinda ya
iya cewa da ita,"Ai na sani dama Zaka iya aikata fiye da haka in har za a taɓa matar so ,ka sani daga yau
babu sauran ragowa tsakani na da ita ,kai ba ma ita ba har da kai ɗin ma muzuba mu gani ɗan halakka ka
fasaa".Wani murmushin yaƙe kawai ya sakar mata ya nufi hanya fita ,waje ba tare da ya sake bi ta kanta
ba.

"Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una,na shiga uku tayi nasara akai na,yau Yah Jaheed ne ke irin wannan
ikirarin akaina Shikenan ta yi nasara a kaina ta raba Ni da mijina hankalinta ya kwanta,ta lalata soyayyar
da aka gina ta tun ƙuruciya,wallahi bazan bar ki ba Gimbiya Ayush,sai dai mu bar Gidannan a tare da
ke,domin ba ki isa ki fitar da ni daga cikin Gidan da aka gina shi da suna na ba",takai zancen ta na mai
durƙushewa ƙasa gami da sakin kuka da iya ƙarfinta.

Kai tsaye Part ɗin shi ya tafi da shi yai mashi wanka ya sake masa kaya kafin ya nufi Part ɗin Gimbiya
Ayush ya ga halin da ta ke a ciki , Allah ya taimake shi ƙunar ba ta tashi ba,Umma Jamila tuni ta yi tafiyar
ta Gida abinta,sannan ya tafi da Nurain can main house ɗinsu




Part 29



Zazzau ne su ke a cikin Parlon ,kowa cikin su fuskarsa a sake ɗauke da haiba da kuma natsuwa,Alaranma
Sama'ila,Kawu Salihi,Kawu Musa, Kawu Kabiru dama,Baba ƙarami da sauransu dai, duk nan suke zama
idan ya kasance babu karatun da za a gudanar tsakanin sallahr Magriba da kuma Isha'i,"Ya maganar
tafiyar ta ka ina fatan ka shirya ma ta ,domin na ga tafiyar kamar ta ƙara so", cewar Baba ƙarami.

"Eh Abba na shirya da so nai ma in yi zamana a can Abujan har zuwa lokacin da za ai taron sai kuma na
samu saƙon sun maida taron Lagos shiyasa na dawo in ɗanyi ƴan shirye-shiryen da zan yi kafin in
wuce","Ya Salam kace tafiyar ta ƙara yin nisa kenan?", Alaranma Sama'ila ya tambaya,"Eh wallahi Kawu
haka tafiyar ta koma duk sun canja wasu abubuwan".
Kawu Salihi ne ya tambaye su da cewa "A'aha tafiya ce ta kama shi ne zuwa wani wajen"."Eh tafiya ce
ta kama shi na manta lokacin da mu ka yanke hukuncin wakilta shi a tafiyar baka nan,amma kamar ai
nasa a kira ka ayi maka bayani ko,kan taron Manyan Malamai domin samun haɗin kan mazhabobi da
za a gudanar a Abuja to ka ji ashe an maida shi Lagos","Af Af na tuna munyi maganar da kai kuma bayan
haka na samu labarin gurin wani Abokin kasuwanci na a can Jigawa","Yauwa to tafiyar ce ta taso,ina
tunanin saura kwana biyu ma tafiyar".Nan dai suka cigaba da tsara yanda za su yi tafiyar da kuma ƙarin
shawarwarin da zai amfana da su, shigowar Baba Malam tare da Alƙasim nan su ka sake dawowa da
zancen farko,daga ƙarshe kuma suka koma tattaunawa akan lamurran cikin Gida da na kasuwancin su.

Sai bayan da suka gabatar da da Sallahr Isha'i sannan ya fara shirin tafiya Gidan shi,ya shiga cikin
Gidan domin yi ma su Sallama,Momy Hibba ta ce da shi,"Ina Mai Gidan nawa ya ke na ga ka fito ba tare
da shi ba,ko nan zai mana kwana",sai ya ɗan haɗe ransa kafin ya ce,"Momy yana wajen Ummiey,kuma
ina ga ya dawo nan da zama sai ko zuwa wani lokaci ko da zai koma",itama ba ta kuma ce masa komi ba
sai sauke ajiyar Zuciya da ta yi ,kafin kuma ta fara cewa da shi,"Ka yi haƙuri yana daga cikin jarabtar ka,
bawa kuma baya tsallakewa ƙaddarar sa,zamu yi maganar ni da Ummiey Maryam kome kenan zan sanar
da kai mai yiwuwa za a iya samun maslahar wannan lamarin","To Momy ina godiya,bari in zo in tafi dare
na ƙara yi dama zuwa na yi in maki Sallama,Kuma ina son in iske Ummiey kafin tai barci","Okay to
Shikenan Allah ya tsare a gaida mutanen Gidan mu ma zuwa goben za mu shigo mu ga mai jikin",da haka
yai mata sallama ya nufi wajen Mahaifiyarsa .




~~~~~~~~~~~




"Momy Allah ba na son tafiyar nan jikin ki har yanzu bai koma normal ba,ina tsoran kar wani abu ya
same ki bayan ba na nan",sai da Gloria ta tashi zaune da ga kwance da ta ke kafin ta ce,"My Daughter
bai kamata ki yi loosing this opportunity ɗin ba,ba kowa ke samun ta ba taron nan yana da matuƙar
muhimmanci a gare kin ga ba kowa ke samun wannan babbar damar ba,don haka za ki je wannan taron i
promise to you babu abinda zai faru da ni har ki je ko dawo for the sake of father lord".

Rau-rau Jadeeda ta yi da idanunta hawaye na son zubowa daga ciki "Kin ga matso kusa da ni,Papa ɗin
ku kan shi ba zai ji daɗi ba in ya ji cewar kin fasa attaiding ɗin wannan taron,manyan mutane ne fa suka
gaiyace ki,kuma ta hanyarsa ,to me zai sa ki watsa masa ƙasa a ido",haka dai ta cigaba da lallashinta har
ta samu ta amince da za ta yi tafiyar,"Wai ina Edwin tun safe da ya shigo ya gaishe ni ban sake jin motsin
shi ba ?",Min ta tambaya,"Ba ya wuce Room ɗin shi domin na ga motar shi babu inda ya je","Yana ɗaki
kwance?,me yake damun shi wannan ba ɗabi'ar shi ba ce,to ko dai ba shi da lafiya ne ?","Momy ni dai
ban sani ba amma Ni kaina na yi noticing sauye-sauye daga Brox Edwin,ya keɓe kan shi,bai cika shiga
cikin mu kamar yanda ya saba,ba tsokana ko barkwancin da ya saba jan mu da shi,shi kaɗai kawai ya ke
rayuwarsa,ko abinci ba ya ci tare da mu,a Room ɗin sa ya ke komi shi kaɗai".

Shiru Madam Gloria ta yi,kafin daga bisani ta ce da ita,"Je ki ki gani in ya na cikin ɗakinsa and call him
for me",ba tare da Jadeeda ta ce komi ba ta nufi Room ɗin Edwin,tun kafin ta ƙarasa shiga ta fara jiyo
hayaniya daga cikin dakin ana cewa,"Guy kar ka bari wannan maganar ta zama dalilin da zaka sanya
rayuwar ka a cikin haɗari say it out,ka fito fili ka sanar da abinda ke damun ka,ka na aikata kuskure ne
fa,zurfin cikinnan ba abinda zai haifar maka da shi inda ka sake jefa rayuwar ka cikin wani sabon
haɗari"....."Joseph baka da hankali irin wannan maganar ka ke ikirarin in fitar da ita,You Are Mad Ina
tunanin ka samu matsala".

"Kai ne dai ka ke da matsala amma ba ni ba,kuma za kaga ne hakan nan gaba,ni ba zan iya cigaba da
kallon kana cutuwa ba,in har ba za ka fito fili ka sanar da ahalin ka abinda ke damun ka ba ,ni zan sanar
da su",a firgice ya ɗago yana kallon sa fuskar shi cike da mamakin abinda kunnuwan shi su ka jiye
masa,sai da Edwin ya kwantar da zuciyarsa kafin ya ce da shi,"Ka ga Jesoph ka fahimci ni ,komi na
rayuwa family first bai kamata saboda wani buri nawa in sa family na cikin damuwa da tashin hankali
ba,zan bi komi a hankali,okay dan haka bar min komi a hannuna".

Kasa haƙuri Jadeeda ta yi sai ganin ta su kai a tsakiyar su,a ɗimauce Edwin ya miƙe tsaye,ya na mai
nufo inda ta ke gami da kama kafaɗunta tare da cewa,"Jadeeda yaushe ki ka zo,a dai ki daɗe da zuwa ba
ko,ina fatan baki ji komi gane da abinda muke tattaunawa ba ?",sai da ta zuba mashi idanunta kafin
tace,"Ni ban ji komi ba,kuma yanzu na zo,Momy ce ta aiko ni ta ce ka zo tana san ganni ka","Na ji
ganinan zuwa amma kafinnan ki tabbatar min da cewar ba ki ji komi dangane da hirar da muke
tattaunawa ni da Abokina ba",saɓule hannun shi daga kafaɗar ta tayi kafin taba shi amsa a taiƙaice da
cewa,"Ni banji komi ba",tana kaiwa nan ta bar mi shi Room ɗin gabaɗaya,kasa iya zama yai sai bin
bayanta da yai cikin sauri da azama.

A tare su ka isa inda Madam Gloria ta ke zaune,suna shiga suka iske Papa da Uncle Richal sun dawo
daga sabon shopping Mal da aka buɗe ma Uncle Richal domin san hana shi komawa ƙasar da ya baro.

"Lafiya ku ka shigo kamar an biyo ku",Papa ya tambaya yana mai bin su da kallo.

Cikin rawar baki Edwin ya tari numfashi sa da cewa,"Papa ba komi Momy ce ta aike ta ta kirani"ya
bada amsa a ɗarare.

,"Zo nan Edwin matso ka zauna kusa da ni",jikinsa a sanyaye ya isa kusa da ita ya zauna,da ganinsa kasan
ba a dai-dai ya ke ba.

"Edwin my son me yake damun ka ,da ganin ka akwai wani abu da ka ke ɓoyewa a cikin zuciyar
ka",Madam Gloria ta tambaye shi,inda-inda ya fara kafin ya samu ya natsar da kan shi ya bata amsa,da
cewa,"Momy ni ba abinda yake damina,ina tunanin gajiyar tafiya ce","Gajiyar tafiya kuma tun yaushe ka
dawo almost a week,har yanzu ba ka huce gajiyar tafiyar ba?,a komi fa ka ware kan ka,ko saukowa ka
kaci abinci da Familyn ɗin ka ba ka yi hakan duk gajiya ne",Momy ta sake jefa masa wata tambayar.
"Momy i swear gaskiya na faɗa ma ki,yanzu haka ina tare da friend ɗina ne Joseph"....."Momy Allah
da abinda ke damun shi,kawai dai ba zai faɗa ba ne ba,ni na riga da na san da haka tun kafin ya dawo ".

Papa ne ya maida hankalin shi akan sa tare da cewa,"Fill free my dear son nan duka Familyn kane ka
faɗi duk abinda ke damun ka we will sort it together,ba wai kai kaɗai abun ya shafa ba ,duka damuwar
mu ne",duk wannan bayanin da Papa yake Edwin baya tare da shi,gabaɗaya hankalin shi,idanun shi da
kuma tunaninsa nakan Jadeeda,zuciyarsa na gaya masa tabbacin ta saurari tattaunawarsa da friend ɗin
sa.

"Edwin kana ji na kuwa",Papa ya faɗa da ɗan ɗaga murya,hakan ne ya yai gigita shi tare da cewa,"Eh
Papa zuwa anjima ma zan amso sauƙon",cikin mamaki Papa yace,"Saƙo kuma wa yai maganar saƙo
anan?".

Har Momy ta buɗe baki za ta ce wani abu Uncle Richal ya dakatar da ita tare da maida hankalin shi kan
Edwin yace dashi,''Ka ga tashi ka tafi je ka wajen Friend ɗin naka ba damuwa",....Momyh tari numfashin
shi da cewa,"Amma Richal taya za sallame shi alhalin ana irin wannan maganar mai girma da kuma
muhimmanci","Sister bai kamata ku turken shi anan kusa lalle dole sai ya faɗa maku damuwarsa ba,mai
yiwuwa lamarin bai kai yanda ku ke tunani ba,may be yana jin zai iya dai-daita komi, Edwin fa ba yaro ba
ne ya mallaki hankalin sa bai kamata irin haka nashiga tsakanin ku ba,idan lamarin ya kai lamari bani
tantama zai sanar da ku",da wannan bayanin Edwin ya samu ya sulale daga cikin su.

"Richal ba ka fahince ni ba, dole sabon halin Edwin ya taɓa kowa a cikin Gidannan,kalli fa raha da
wasannin da yake duk ba ya yin su kullum jikin sa a sanyaye,haba abun da rikitarwa gami da tsayawa a
cikin zuciya da rai","Na sani Sister amma ba ta irin wannan hanyar ya kamata mu bi domin gano
damuwarsa ba,hakan ka iya creating wata sabuwar matsalar",shiru su duka su ka yi kafin Papa ya
ce,",Kuma fa maganar ka gaskiya ce,to amma yanzu ta wacce hanya zamu yi amfani da ita domin mu
gano asalin abinda ya ke faruwa da shi","A bibiyi lamarin shi,ku sake ƙara janyo shi a jikin ku,inda halima
a daina barin sa shi kaɗai".

Nan dai su ka amince da shawarar da Uncle Richal ya kawo, sannan su ka cigaba da kawo wa su
hanyoyin daza su yi amfani da su duk dan su ga sun kai ga gaci akan abinda su ka sa gaba,hatta da
maganar tafiyar Jadeeda zuwa Lagos sai da suka yi daga ƙarshe Uncle Richal da kan shi ya ɗauki Jadeeda
su ka nufi sabon shopping Mal ɗin sa ya zaɓa mata duk abinda ya tare masa gaba,hatta da kayan da za ta
sa in ta isa Lagos shi ya zaɓar mata,komi ya gani in har ya ga zai mata kyau to sai ya ɗaukar mata wasu
kayan ma set guda yake samata, choculate ba'a magana,haka su ka dawo da kaya niƙi-niƙi.



*Jadeeda*



*YOTA*
Part 30



"Asiya wai ke ce tunda wannan uwar safiyar",Ummu Nurain ta ce tana mai buɗe mata door ɗin
shigowar,"Kai Aunty yanzu ne safiyar yanzu da wajen goma da wani abu","Ke haba har goma ta yi,Ni ban
ma san garin har rana ta fito haka ba",",Ai ko dai rana ta yi yanzu haka ma Mamanmu ce ta ce inzo in jiye
mata kanun zancen da ake ta yawo da shi a cikin Gida",tsaki Ummu Nurain ta saki kafin ta juyo su ka
shigo a tare, Ummu Nurain hamma ta saki gami da yin miƙa tare da cewa "Waɗanne maganganu ne ke
ta faman yawo a cikin Gidan?",Ya mutsa fuska Asiya ta yi tare da cewa,"Wai cewa su kai saboda tsabar
baƙin kishin ki kin ƙona ƴar Sarki da ruwan zafi".

"Munafukan banza a haka za su ƙare ba wani a cikin su da yasan gaskiyar abinda ya faru sai yaɗa
gutsiri tsoma","Kenan da gaske kin ƙona ta kamar yanda ake faɗa ?","Mtssssss na ƙona ta mana amma
wallahi ba intentionally na ƙona ta ba,kawai tsautsayi ne,kin san ni bana shiga harkarta na je kare
martabar Aurena gami da kwatar haƙƙina takawomin wargi nqi kuma na hankaɗar da ita cikin tsautsayi
ta ɗora ruwan zafi ya sheƙo mata a ƙafarta".

Wata irin dariya Asiya ta kwashe da ita,har ta na tafa hannayenta tare da cewa,"Maganinta kenan
uwar kinibibi da iyayi,ai yanzu sai muga da ƙafar da za a nunama mutane isa da gadara,ai ni na so ace
ruwan zafin da ya tashi ya saɓule har fatarta muga ta tsiya".

"Ba zaki gane ba Asiya amma ina zaman baƙin ciki da takaici a cikin Gidannan kuma duk a saboda
wannan munafukar,kan wannan lamarin har marina Yah Jaheed yai wanda irin haka bata taɓa shiga
tsakanin mu ba",maganar ba ƙaramin kaɗuwa ta jefa ma Asiya ba,"Mari fa Aunty Zeenat akan wancan
shashashar matar tasa ?, wallahi in ni ce da ba iya nan abun zai tsaya ba".

"Hmmmmm ai ba ayi komi ba Asiya ,barshi ba dai yau zai dawo nan Part ɗin ba na rantse sai na tada
ma shi hankali fiye da yanda ya ke zato da tsammani,kuma ko ɗaya a yanzu bana danasanin ƙonewar da
ta yi ko ba komi na zaunar da ita guri ɗaya kuma daga yanzu za ta san ruwa ba tsarar gwando ba ne ba ".

"Hehehe ana yi muna jin daɗi,ai babu nadama don kin illata ko raunana kishiyar ki,a ai ba a jira,ba a
sanya ki sani in itace ta samu wannan damar ba jira ba sanya za ta aikata miki fiye da haka,gobe ma in ta
ƙara kawo maki wargi kome ke kusa dake ki ɗauka ki buga mata a ka in ya so kome ye ya biyo
baya",dariya Ummu Nurain ta saki gami dakai mata duka tare da cewa,"Shegiya Asiya ƴar ƙarama dake
amma kin iya tuggu,ke wannan in aka yi maki kishiya ai tabani ta lalace"......"a'a a'a bar yi min mugun
baki,Ni ko zuwa nai na iske na ci alwashi sai na fidda ta balle kuma a zo a iske ni,Aunty ni fa kwata-kwata
na tsani kishi ,Ni fa zan iya aikata abinda za a ƙulle kaf ahalin mu indai akan kishiya ne","A'a Ni kin fi
ƙarfina bar ni dai zan aikata

Please Login or Register in order to submit comment