You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

juyawa ta koma kan Gimbiya Ayush ta na mai tamke fuskarta tare da k`ank`ance
idanunta saboda tsabar masifa,"Ki sani na yi alk`awarin tarwatsa Shirin ki ta kowacce irin hanya sai
aniyarki ta koma kan ki muguwa Mai bak`ar aniya"...."Wai me ya ke damun ki haka ne ko kin fita daga
cikin hayyacin ki ne Zeenat eyeh ?".ya kai zancen ya na mai shan gabanta ya shiga tsakanin su dan ya ga
ba abinda Zeenat take so ko yunk`urin yi da ya wuce ta ga ta Kai inda Gimbiya Ayush ta ke.

"Kin ga Ummu Nurain ki kwantar da hankali ki domin wallahi ba abinda zuciyar ki ke zargi ne ya faru
ba,ya zo duba ni ne ba ni da lafiya ko ba ki samu labarin na samu miscarrage ba?"."Hmmmmmm kar ki
wani yi yunk`urin son fahimtat da ni sabon karatu ko darasi game da munafunci ko Kuma kusisina irin
taki domin kaf na gama biya alon rayuwar ki tas na shanye,Abu d`aya na ke so da ke ki shiga taitayinki
domin kowa ya san karo da kura ba dad`i".

A fusace Jaheed ya Muna Mata hanyar fita ya ce ,"Ki `bace min da ganin tun kafin Zuciyata ta sa na
aikata ba dai-dai ba a kan ki",..."Idan Kuma na k`i fa sai ka Dake ni na ce maka sai ka dake ni?,haba na
gaji wallahi na ga alamun nema ka ke kai da matar ka ku kai ni kushewata tun kafin lokacina ya yi haba
dan Allah,ka ji tsoran Allah fifiko da ka ke nunawa ya Isa haka ma na,ni fa `yar'uwar ka ce ko ka manta da
hakan ne".

"Ke ce dai ki ke manta ko ke wace ce da Kuma matsayin ki a cikin Gidannan,ki sani matsayin ki ya
zarce wanda ki ke ba kan ki,Ina biye ma ki gami da d`aga ma ki k`afa ne saboda wasu dalilai Amma ki sani
kina gab da Kai ni k`arshe Gimbiya Ayush fa mata ta ce kuma ta sunna me ye aibun Dan na zo inda ta ke".

"Eh ai na sani Kuma na gani,hakan ne ma yasa ka ke d`aukar hak`k`ina kana kawowa wurin ta kana cin
amanata ko",ta Kai zancen fuskarta na k`ara bayyana d`aci da zafin abinda ta ke ji a Zuciyar ta.

Cikin rawar jikin Gimbiya Ayush ta matso kusa da ita tana Mai cewa,"Aa Ummu Nurain na rantse maki
ba abinda ki ke tunani ba ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ya ga ya na tashi saboda rashin lafiyar da na
kwana da ita Amma bayan haka ba wani abu a tsakanin mu".

"Kin ga Gimbiya Ayush bar ta ta yi duk tunani da zata yi,ita ya shafa,in ta so ma ta d`auka akan
shimfid`a ta zo ta iske mu,duk matsalar ta ce wannan Ina da damar aikata fiye da haka,ita d`in mata ta ce
ta sunna,ki sani ko jiya na bar ki da abinda ki ke so ne don son dakatar da fitinar da ki ke son haifar da ita
a wannan lokacin,shin hankali ki bai kai kan za ta iya shiga cikin wani Hali ba a wannan Daren,in ta samu
wata matsalar da wanne baki zan iya kare kaina,ya ya ki ke ganin idan abun ya zo da k`arar kwana da
wacce fuska zan kalli iyaye da ahalinta,shin kina tunanin zan iya yafe ma kaina akan haka,Kuma da wacce
fuska zan cigaba da kallon ki da ita,ke kullum hak`k`in ki ki ka sani ba ki duba da hak`k`in Wanda ki ke
tare da shi,ta ya za ki zauna lafiya da irin wannan halin,a taya za ki haka za ta faru",Ya Kai zancen a
tsawace,tabbas ta fara kai shi bango har ta kai ga fusata shi.

Ganin haka da Gimbiya Ayush ta yi yasa tai saurin kama hannunta tare da cewa,"Kinga zo mu je zan
maki bayani yanda yanda za ki fahimta kin ga ranshi ya fara ɓaci akan wannan maganar".
"Dallah Malama rufa min baki duk ba ke ki ka haddasa komi ba Munafukar banza munafukar wofi",ta
kai zancen tana Mai hankad`ata baya cikin tsautsayi ta tafi zata fad`i Bata Kai ga fad`uwar ba Amma
ruwan zafin da ta d`ora hannunta ya bugo shi ruwan ya kifo mata a saman k`afarta,a gigice ta saki k`ara
gami da sallallami d`auke a bakinta tana mai cewa,"Honey shikenan na k`one ,ta k`ona ni,k`afata
zafin,zafin ko ina".

A rikice a rude ya nufeta yana Mai kama k`afar domin ganin abinda ya same ta,sakin k`afarta yai ya
koma kan Zeenat da jikinta ya fara rawar,kafin ta yi wani yunk`uri ya sauke mata mari hagu da dama,rasa
ma me zai ce da ita yai sai daga baya ya koma kan Gimbiya Ayush ya sunkuce ta ya bar kitchen d`in da
ita.

Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanun Ummu Nurain,wannan wacce irin fitinar
da bala'i ne ya sauka a cikin Gidanta,idanuwanta a rufe ta nufi part d`in ta ko gabanta ba ta gani.

A parlour ya sauke ta ya nufi sashen shi cikin hanzari ya d`auko first aid box ya fara bata taimakon
gaggawa.

"Kin ga bari in d`auko maki kaya ki sauya mu tafi Asibiti da buk`atar a duba ki da kyau",Cikin yanayin
wacce ta ke cikin jin zogi ta dakatar da shi da cewa,"Aa ba sai mun je ko ina ba ban wani k`one sosai
ba,zan ma iya taka k`afar bari ma ka gani".

Shigowar su Umma Jamila Mama Hadiza,Safina da kuma Biba domin dubiyar jikin Gimbiya Ayush ɗin ce
ta ɗan ja hankailinsu.

"Aa Jaheed me yake faruwa,na ga Zeenat ta fita daganan a cikin wani yanayin Kuma mun shigo mun
ga Gimbiya Ayush a irin wannan yanayin",Mama Hadiza ta tambaye shi.

Cikin d`acin Zuciya ya ce da ita,", Zeenat ce to k`onata saboda tsabar rashin hankali da bak`in
kishinta","Subahanallahi garinya ya haka ta faru,wannan ai hauka ne,Asibiti ai ya kamata mu tafi ba wai a
tsaya a gida ba ",

"Haka na ce Amma ta ce wai ba sai anje ba","A'a wannan ba Mai yiwuwa ba ne,tashi maza mu tafi tun
kafin abun yai tsamari",cewar Momy Hibba.

Hankali a tashe Gimbiya Ayush ta so hana tafiyan Asibitin don gudun kar abinda take k`ok`arin
`boyewa ya tuni nu,kar k`ilu ya jawo bau,Amma Ina hakan Bata samu ba domin ba tayi nasara ba,ba dan
ta so ba haka suka tafi Asibitin.
*JADEEDAH*



STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)



Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI




And now.....*JADEEDAH*




*YOTA*

BOOK 1




https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a



PAGE 27 ❤
"Anya Gloria ba akwai wani ɓoyayyen sirri da ke wanzu tsakanin Richal da Jadeeda ba ?",Mom
Rebecca ta faɗa bayan sun gama yin dinner.

Shiru Momy ta yi ta kasa iya cewa komi sai can daga ƙarshe ta sarƙe da miyau, saurin ɗaukar Cup ɗin
ruwa ta sha sakamakon ƙwarewar da ta yi,ko ta samu ya lafa.

"Mom wannan wacce irin magana ce,me ya kawo ta,kamar ba ta da muhalli a irin wannan wurin
","Hmmmmm Gloria kenanan dama na san irin haka ce zata faru,ba lalle ki yarda da duk abinda zan faɗa
ma ki ba a yanzu ba,amma ki sani tuni zuciya ta daɗe da fara kawo zargi kala daban-daban a cikin
tarayyar Richal da kuma Jadeeda"...."Mom zargi fa haramun ne,kuma ke fa tamkar Uwaki ke a gare su
wannan bai kamata ya fito daga bakin ki ba",Girgiza kai Mom Rebecca tayi kafin ta ce,"To Shikenan
tunda haka ki ka ce na bar maganar ba zan sake danganta su da irin wannan magana ba tunda baki yarda
ba",tana kaiwa nan a zancenta ta tashi ta bar mata dinning ɗin gaba ɗaya.

Tun bayan fitar Granny da ga dinning room ,Momy ta shiga cikin ƙololuwar tashin hankali, Zuciyar ta sai
faman saƙa mata munanan tunanin ta ke, kwakwalwar ta cushe,ta kasa samun natsuwa balle har ta
samu damar da zata samu makama a cikin zancen,tun tasowar Jadeeda ta san akwai kyakkyawar alaƙa a
tsakanin su,ya kan ɗauki dukkanin wani lamarin ta da muhimmanci baya taɓa manta wani abu da ya
shafeta,duk da kasancewar ba a ƙasa ɗaya suke zaune ba hakan bai hana shi halartar duk wani abun da
zai sa ta farin ciki,shaƙuwar su takai matuƙa har ta kai ya fi kowa sanin sirrikanta da kuma abinda take
so,sai dai ko ɗaya bata taɓa kawowa a ranta cewa da akwai manufar hakan ba,sai yanzu zuciyar ta ta
fara kawo mata hakan a matsayin zargi.

"Kai a'a hakan ma ba zai yiwu ba,Richal ba zai taɓa aikata min irin haka ba,ya na da hankali ya san
girman sirrin da ke lulluɓe acikin wannan lamarin ba zai aikata haka ba",Gloria ta faɗi hakan ta na mai
cigaba da kaiwa da komowar da ta ke.

"Idan kuma hakan ta kasance fa yake nan ?",wani sashe daga cikin zuciyar ta ya sanar da ita haka,sai
da bugun zuciyar ta ya ƙaru kafin ta dafe saitin wurin tare da cewa,"Shakka babu kuwa da ya aikata
babban kuskuren da bai taɓa aikata shi a rayuwarsa ba,zai yi dana sani mai girma,har sai takai shi ga jin
dama bai bari sakarar kuma mayaudariyar zuciyar sa ta rinjaye shi ga aikata abinda ya aikata ba".

Tunani ne ya cinkushe mata kai har ta kai ga ta fara iya daina gane komi ji da ganin ta sun fara gushewa
,kanta kuma na tsananta mata wajen sarawa.

Amma duk da hakan ta kasa iya dakatar da kanta game da tunanin da take, abubuwa masu yawa sai
yanzu suke zuwan mata,misali irin yanda suke ba junan su kulawa da kuma yanda shaƙuwar su take,kafin
ka ce me tuni ta fara ganin duhu a cikin idanunta da ƙyar ta samu ta daga bango ta isa bedroom ɗin ta ta
zube a kan shi wasu zafafan hawaye na son zubo mata amma zuciyarta ta ƙeƙashe kwata-kwata ba ta
son ta yarda da zarge-zargen da suke kai kawo mata a cikin ranta,balle har ta yarda da su.

"Anty Jee wai ina za ki ne dare fa ya fara yi na ga sai faman kwalliya ki ke,is there anything special da
ki ke expecting ɗin sa ne?","Yeah off course ko kin manta Uncle Miey ya na can yana jirana,zai yi Surprise
ɗina da wani abu mai matuƙar muhimmanci,so ya ki ga fitar tawa ta fita ko in sake wata",ta kai zancen
tana mai jujjuya jikinta yanda zata ganta sosai,sanye ta ke da mini skect sai wata half ɗin riga mai hannu
guda,wacce ko cibiyarta ba ta rufe ba,ƙafarta sanye da high heel shoe,gashin kanta ya sauka har saman
shoulder ɗin ta,komi nata shigar red and black, skect da bag ɗin ta black sai rigar jikinta da shoe ɗin ta
red.

Da yatsun hannunta ta yi mata alamar ta kai maƙura,"Am bari in ƙara fiddo da Anty Jeee ɗina",ta kai
zancen tana mai saukowa daga kan bed ɗin da take ta ɗauko eye glass black ta sanya mata,gami da tsara
mata simple make up a saman fuskarta,sai da ta ƙara yi mata ɓarin mabanbanta tauraruwa a jikinta kafin
ta juyar da ita saitin mirrorn dake ɗakin gami da cewa da ita,"Ya ki ka ganki yanzu nasan in ku ka haɗu
da Uncle R ba zai iya noticing ɗin ki da sauri ba".

Dariya Jadeeda ta saki gami da kai ma Nora bugu ta goce tare da cewa,"Ba kyau zan yi ba ko da suffa za
a sauya min in har Uncle Miey zai iso gare ni da bugun zuciya kaɗai ya isa ya gane ni,balle kuma wata
kwalliya da ko matakin Princess ban kai a kira ni da ita ba","Wa ya gaya maki haka ai Auntyna ta wuce da
wannan matsayin ,sai dai a kira ki da Queen ba Princess ba","Ma za ki cigaba har wani ya jiki,da anzo zan
tsere jikinsa in ce ba ruwana","A haba ai nasan ba za ki aikata hakan ba,ke ɗin ta dabance,za ma ki iya
ɗaukar laifin akan ki,saboda tsabar ji da ni da ki ke kin san wani time ɗin ina mamakin yanda wasu
abubuwa na mu suka sha ban-ban da na ki,misali yanayin hasken fatar ki,ɗan ƙaramin jiki da ki ke da shi
babu wani abu guda ɗaya wanda ku ke kamanceceniya da shi da wani a Gidannan komi na ki so special
ke ka ɗai ke da irin sa".

Ta buɗe baki za tabata amsa Martin ya shigo a hargitse kamar wanda aka watso shi , Muryar sa na
rawa yace da su,"Momy....Momy ....jikinta ya motsa tana can bata iya gane komi da alama ta na cikin
mawuyacin hali na yi ta ƙoƙarin in ga ".....ko tsayawa su ji ƙarashen abinda ya ke faɗa ba su yi ba,su ka yi
waje gami da budar Room ɗin ta don ganin halin da ta ke a ciki,ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba
lokacin da su ka ga halin da Momy ta ke a ciki,nan su ka fito suna neman agajin gaggawa gurin Driver,
Gate Man da kuma sauran masu aikin Gidan.

Allah ya tai make su sun isa Hospital ɗin da wuri da ita cikin ƙanƙanin lokaci Doctors su kai ca
kanta,sun yi iyakar bakin ƙoƙarin su kanta,duk da kasancewar Doctor Muh'd Jaheed baya nan,sun samu
ta dawo cikin hayyacinta amma kuma cikin rashin sa'ah ta kasa iya tan-tance kowa a cikin su,ta kasa iya
kama sunan kowa a cikin su, Jadeeda sai ta kira da Momy Rebecca ,Nora Kuma ta kira ta da Martin haka
dai ta cigaba da soki burutsu,zance ba kai ba ƙafafu.

"Doctor hankali na a tashe ya ke ,ba fa ta iya gane kowa kamar ba ta cikin hayyacinta ?",Rev. Anderson
ya faɗa ,da dawowar shi kenan ya iske lamarin.

"Am Sir she is out of danger bata cikin wani hatsari,za mu ɗorata akan medicine by the grace of God za
ta koma normal", wannan shine abinda Doctor ɗin da ya duba ta ya ce,kasa haƙuri su kai har sai da su ka
sake tuntuɓar wasu Doctors ɗin amma maganar ɗaya ce, cewa a hankali za ta koma normal,sai faman
kai kawo su ke ,sun kasa kwantar da hankalin su,ga dare har ya fara tsalawa.
"Wai ina asalin likitan da ya duba ta ya ke,a kira shi ko ma samu ta fita daga cikin wannan
yanayin ?",cewar Granny da hankalin ta yake a matuƙar tashe.

"Granny wannan Special Doctor ne ba kowanne lokaci ya ke zuwa ba","Jesus Christ oh father lord ka
kawo mana ɗauki.

Sai tin bed ɗin Jadeeda ta je ta duƙa gami da dafa ƙafafun Gloria idanuwanta na zubar da hawaye ta
fara yi mata addu'a,"Oh Lord Jesus hear me when I call,o God of my righteousness! You have relieved
me in my distress have mercy on my Mom and hear my prayer,na sani kai ka faɗa a cikin littafin ka mai
tsarki Jeremiah chapter 33 verse 3 kace call to me and I'll answer you show you great and mighty thing
wich know not,bari Ubangijin sama da ƙasa ka yaye ma Mahaifiyarta wannan lalurar da ta ke fama da
ita,oh Lord father kasa wannan cuta ta zama waraka kuma kaffara gare ta,bari Ubangijin halitta kasa ta
miƙeta taka da ƙafafuwan ta,ka warkar da ita ,ka fidda mu daga cikin tashin hankali da ruɗun da muke a
ciki ",ta kai zancen tana mai zubar da zafafan hawaye akan fuskarta.

"Anty Jeeyy mai zai sa ba zamu nemi alfarmar su kira mana shi ba ya zo ya duba mana ita ko da zuwa
gobe da safe ne?",Martin ya ce da ita,"Sai dai mu kwatanta hakan idan zai yiwu,wani lokacin ba a cika
yin dacen zuwan su ba","Kin ga Jadeeda ko nawane zan biya in har zai zo ya duba ta,ya ambaci iya
amount ɗin da ya ke so zan biya shi matuƙar zai shigo cikin garin Abuja zuwa da safe","Shikenan Papa
bari in Yi magana da wani daga cikin Doctors ɗin ko za mu da ce".

Haka ta fita sai dai me cikin rashin sa'ah Doctor ɗin da ke unduty a ranar ya shiga treater,sai da su kai
jiran sanda ya fito kasa tsayawa ya sauraren su yai ƙarshe ma sai ya sake shiga wata treater ba tare da
yaba su wani lokaci mai tsawo ba,wanda hakan ba ƙaramin sake jefa su cikin wani sabon tashin hankali.

"Yanzu Papa haka za mu zuba ma Momy idanu ba tare da mun iya taimaka mata da wani abu ba,zuciya
ta sai ƙara karyewa ta ke".cewar Nora

Sai da ya janyo ta jikinsa kafin ya fara lallashinta gami da son kwantar mata da hankali,ringing ɗin
wayar Jadeeda da ta ishe su tun ɗazun ne ta sake ratso kunnuwan su ,sai da ta saki tsaki kana ta jawo
wayar da son duba waye ke kira,sunan Uncle Miey ta gani yana yawo akan screen ɗin da sauri ta ɗaga
gami da fara ba shi haƙuri gami da sanar da shi abinda ya ke faruwa,bai jira komi ba ya katse kiran gami
da nufo Hospital ɗin .



"Am ɗan dakata kamar fa ya taɓa bani wani card da zan iya contacting ɗin sa da shi", Jadeeda ta faɗa ta
na mai yunƙurin fara laluban jakarta ba ta iya ta samu komi a ciki ba hakan ya sa ta juyawa gami da nufar
hanyar fita,nan ta ci karo da Uncle Richal ya na shirin shigowa,a taƙaice ta yi ma shi bayanin abinda ke
faruwa ya juya ya bita su ka nufi Gidan tare.

Ba su wani ɓata lokaci ba suka isa gidan duk inda ta san ta na aje wani abu mai muhimmanci sai da ta yi
watsa-watsa da su ,har sai da ma ta fara cire rai wajen ganinta sanna Allah ya nuna mata ita,tsuru ta
zubama card ɗin idanu,Wanda ba wani abu da ke jikinsa daga sunan mallakinsa sai phone number,a
Zuciyar ta sai faman mai-maita sunan ta ke Doctor Hibba Ibrahim Neurological Doctor,"Ki kirata mana
wata ƙila a dace", Uncle R ya ce da ita sautin maganar da ya yi mata ta sa ta dawo daga dogon tunanin
da ta tafi,jikinta har yana rawa ta sanya number gami da fara dialing ɗin ta, har kiran ya gama shiga ba ai
picking ba,hankali tashe ta sake dialing ɗin number a karo na biyu,sai dai abinda ya faru da farko shi ya
sake faru,amma duk da hakan Jadeeda ba ta sare ba haka ta cigaba da trying ɗin number kira bayan kira.

A firgice Hibba ta farka bakin ta ɗauke da salati gami da rarumo wayarta ta duba domin ganin ƙarfe
nawa,ganin time ɗin da tayi ne ya sa ta saki wayar cike da tashin hankali ta nufi bed ɗin da Abubakar ke
kwance cikin mawuyacin hali,wanda hakan ya hana lura da tararin miscall ɗin da aka tara
mata,nannauyan barci ne ya kwashe ta tun bayan sallame sallahar Isha'i wanda hakan ne yasa bata samu
damar sanya mashi Drif ɗin da ta ke sama da ba,lokaci bayan lokaci,baƙaramin tashi hankali gani da
firgice ta shiga ba , wannan dalilin ne ya sa duk iya kiran da Jadeeda ta yi mata ba ta kula da shi ba.da
ƙyar ta samu ta iya control ɗin halin da ta ke a ciki bayan wani dogon lokaci.

"My Angel wannan matar ƴar wulaƙanci ce ji bi duk tarin kiran da ki ke mata ta ƙi ɗagawa",....."Uncle
Miey mana ka yi mata kyakkyawan zato mana ka sa ni ko ta na da wani uzurin da ya ke gabanta da har ya
hana tai picking ɗin kiran","Oh sorry haka ne wannan tunanin bai zomin a rai ba",da haka su ka sake
komawa can Hospital ɗin ba tare da sun yi nasara ba,dole sai haƙuri su kai ba tare da sun sami wani
taimakon daga wani ɓangare ba,da ga ƙarshe da suka ga halin da ta ke aciki ya tsananta dole su kasa aka
yi mata allurar barci.

Sai da gari ya waye Doctor Nass ya shigo Hospital sannan ya samu da taimakon Doctor Jaheed daya
sanar da shi abinda yake faruwa ta waya ya sanarda shi duk abinda ya kamata ya yi,sannan fa aka samu
ta fita daga cikin halin da ta ke a ciki.




*Jadeeda*



https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a



*YOTA*



Page 28
"Mama bari in je Part ɗin Zeenat ɗin in ji haukan da ya sa ta aikata wannan ɗayan aikin sai kace wacce
bata da hankali ko kuma wacce wani ke sarrafa tunani da hankalinta"cewar Safina..."A'a ban aike ki
ba,barta da halinta, Allah kaɗai ya san iya ina maganar za ta kai da zaran kin furta wata kalma,yanzu
uwarta da kakarta sai su maida laifi akai na don haka ta je ta aikata duk abinda ta so","Kai Mama dan
Allah ki bar ni in je",.....ta katse ta tare da cewa,"Na ce a'a abinda ya fi ki taimaka ma shi Mamudan ya
duba ƙafar ƴar mutane inda yiwuwar sai an dangana da Asibiti a tafi kafin abun yai tsamari".

"Yayah Allah da kin bar ta ita Safinan domin ita ce dai-dai da ita,in banda hauka irin na ta taya zata
zuba ƴar mutane ruwan zafi saboda tsabar rashin sanin ya kamata irin nata","Ni dai ban sa ku ba,ba na
son ace daga zuwa dubiya mun haifar da wani sabon tashin hankalin,duk da Safina ta ke ƙwarta kuma
ƴar'uwarta ai bai kamata ta tunkareta da irin wannan maganar ba,ku barta da Mijinta hukuncin da zai
yanke mata ma kaɗai ya ishe ta

"Ni dai Momy ba sai mun je wani Hospital ba,ban wani ƙone da yawa ba,kin gani ma zan iya taka
ƙafar", Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai yunƙurin taka ƙafar,duk dan kar su je Hospital ɗin,babban
abinda ta ke tsoro bai wuce gudun kar garin neman magani a gano asalin fitar cikin ta ba ,kar a samu
matsalar bayyanar ƙaryar da take lulluɓe ta da fatar gaskiya,"A'a ɗiyata ki yi haƙuri mu tafi Asibitinnan ba
zai yiwu a bar ki cikin irin wannan halin ba",Umma Jamila ta ce tana mai son lallashinta da son ta bari su
tafi ta daɗin rai.

"Umma Jamila ba na son a ɗaga maganar ne,ba na son iyayena su san da faruwar lamarin,idan har su
ka ji abun har ya kai mu ga zuwa Hospital za su iya yunƙurin ɗaukar wani mataki ni kuma ba zan so haka
ta faru ".

"Eh to kuma fa haka ne ƴarnan amma kin sa ba ta yanda za ai ace iyayen ki ba za su samu labarin
abinda ya faru ba ko","Na san da haka amma ba za su yi tunanin abin ya na da girma ba har haka,
matuƙar ba mu kai ga zuwa Asibitin ba",ta kai zancen tana addu'a Allah ya sa haƙanta ya cimma ruwa.

"Uhmmmm tabbas yarinyar nan ki na da gaskiya Allah kaɗai ya san ina maganar nan za ta tsaya in har
akace ta yi nisa,don haka yanzu bari in aika can Gida da akwai wani magani da na samo shi da na je can
ƙauye,shima maganin ƙuna ne,sai a gwada shi mu gani ko za a dace","Anya wannan shawara mai
ɓullewa ce kawai ki bari a kai yarinyar mutane Asibiti kamar zai fi",Mama Hadiza ta e,"A'a Yayah ,ki bar
lamarinan a iya nan in ba haka ba fitinar da baki son ta afku ita ce za ta faru,domin ina mai tabbatar ma
ki iyayen Gimbiya Ayush ba za su taɓa iya barin wannan lamarin ya tafi a bazan ba"

Shigowar Jaheed bayan ya sauyo kayan da ke jikinsa ta dakatar da su daga zancen da su ke daga
ganin shigar da yayi ba acikin natsuwa yayi ta ba,shine ma ya ce da su,"Ya ƙafar da zafi har yanzu ko ?",
ya tambaye ta yana mai sauke idanunsa kan ƙafar,da sauri kamar wacce wani ke shirin riga ta ce da
shi"Da sauƙi ta bar ma zogin",Bai ce da ita komi ba har sai da ya sanya hannunsa ya juyoda ƙafar yanda
zai iya ganinta sosai kafin ya ce,"Gaskiya ban yarda da abinda ki ka ce ba,ga ƙafarnan duk ta fara ja",rau-
rau ta yi da idanunta kafin ta ce,"Allah da gaske na ke maka,babu wani ciwo da na ke ji,na ma
warke"...."Oh har ma kin warke kenan,kodayake laifina ne ma da na tsaya jin ra'ayin ki akan haka bayan
nasan baki son duk wani dalili da zai kai ki zuwa hospital,dan haka ki shirya tafiya ba fashi",ya na kai
zancen ya maida hankalin shi wajen su Mama Hadiza tare da cewa,"Yauwa na ce Mama ko za ku zauna
muje mu dawo,domin in a ka ga mun tafi gabaɗayanmu za su iya tunanin ko wani abun mai girma ne ya
faru"......"Dakata Mamuda a bar zuwa Asibitin nan tunda na ga ka ɗan yi mata irin wannan ƴan shafe-
shafen na ku ,kuma a gida inada wani magani kasidin ne,in dai magana ake ta ƙunar wuta da zaran an
shafa shi Shikenan".

"Kai haba Umma Jamila, wannan wanne irin batu ne,ƙonewa fa tai taya kuma za ki kawo batun wani
magani da ba asan asali ko ingancin sa ba","Eh fa ina za a

Please Login or Register in order to submit comment