You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ginin da na kifa amana ta a akai...!"



Kafin Edwin ya iya cewa uffan, aka buɗe ƙofar da karfi,Uncle Richal ya shigo tamkar walkiya.

Fuskar sa cike da ƙiyayya, idonsa na ƙuna kamar mai cin wuta.



"Me ya kawo wannan shashan nan,shin ka zo ne ka sake rikita lamarin ne?! Edwin!

Edwin ya ce,cikin son fahimtar da shi abinda ya ke tafe da shi,"Uncle Richal, dan Allah, ba haka nake nufi
ba,ka bar Ni for the God sake babu abinda zai faru......."sai dai kafin ya ƙare magana, Richal ya kai masa
wani naushi ya same shi a saitin bakin sa,nan da nan sai ga ruwan jini ya zubo daga bakin Edwin,a fusace
shima Edwin ya fuskance shi yana mai cewa,"Kar ka sake dukana domin ba dan kai na zo nan ba,na zo ne
domin ita ka bar ni,in Yi magana da ita,don ita na zo",....wani dukan Richal ya sake kai masa wanda har
sai da Edwin ya kai ƙasa saboda ƙarfin dukan da ya yi masa.

A hargitse Jadeeda ta sako daga gadon da ta ke kwance ,tana mai daka masu tsawa,"Ku fita ,ku bar Ni
bana son ganin kowa a cikin ku,na tsane ku ku duka ",ta kai tsancen cikin tsananin ɓacin rai gami da
nuna masu hanyar fita.

"Amma ban da Ni ko my Sweathert,ai na san Ni dai ba za ki kore Ni ba ko?.......",ta katse shi da
cewa,"Har da kai domin kai na fi tsana fiye da kowa ,dan haka fita ku bani wuri".



Edwin yana durƙushe ƙasa da jini a leɓensa, ya dube Jadeeda cikin hawaye,"Ni dai na gaza. Amma ina
son ki har yanzu,ba wai na faɗi hakan don in tozarta ki ba,kuma na yi danasanin abinda na aikata,na so in
rayu Kuma in mutu har a binne ni da wannan mikin amma na kasa iya jurewa,ban san munin lamarin da
na zo da shi har ya kai haka ba sai da na g gaba ɗaya gida ya hargitse Momy na kwance ba lafiya kuma
kin yanke jiki kin faɗi,da haka na ke cewa na tuba ki yafe ni ."

Ko kallonsa Jadeeda ba ta yi ba,sai kallonta ta maida kan Doctorn da ya shigo yanzu ta ce da shi,"Dan
Allah ka fidda min su bana buƙatar ganin kowa a cikin su".

Haka ba dan sun so ba Doctor yai waje da su sai faman ɓaɓatu Uncle Richal ya ke
√√√√√√√√√√√√



"Bari mana Nurain,ko so ka ke ka zuba lemun a cikin Miyar ta ka", Ummu Nurain ta faɗa ta na mai amshe
Cup ɗin,ta aje gefe tana mai sanya tissue ta goge masa bakin sa inda ya shafa miya,ɗan dakatawa ta yi
tana mai maida ganin ta kan Abu Nurain da ya dakatar da cin abincin shi yana mai zuba masu idanu.

"Lafiya Abu Nurain,na ga ka tsaya da cin abincin ko dai bai maka daɗi ba ne?". Zeenat ta tambaye shi
cikin kulawa.

Sai da ya lumshe idanunsa gami da gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,"Fiye ma da daɗi
wannan abincin ya zarce duk wata kalma da za ta fito daga baki na in don yabawa ko jinjinawa ne,kawai
dai na ga abin kamar a mafarki,ina jin farin ciki mara misaltawa,ina fatan inama da hakan zai ɗore,ina ma
da rayuwar mu zata cigaba da gudana kamar kowane Gida,ina ma da zaki koma ma min kamar Zeenat
ɗin da na sani na kuma aura tun da farko,ba Ummu Nurain da ke jin duk aikin duniya ya taru akan ta
ba,har tana jin bata iya sauke wasu haƙƙoƙina na cikin Gidannan,mu rayu cikin aminci,farin ciki,kulawa
da kyautatawa,mu sauke haƙƙin kowanne da ga cikin mu wanda Allah da kuma igiyar Aure ta rataya akan
mu,zan so hakan shine mafarki da na jima ina yi gami da fatan wanzuwar shi a zahiri".

Cikin tausasa murya ɗauke da tarin nadama Zeenat tace da shi,"Mijina ka ya feni,na aikata babban
kuskure wanda zai cigaba da cutamin a cikin rai da rayuwata in har ba ka furta kalmar yafiya a gare ni
ba,daga yau na maka alƙawari zan yi maka biyayya,zan bi duk wani umarni na ka,zan aikata duk wani abu
da zai saka farin ciki ko ya faranta ranka,zan kasance mai koyi da Matan Annabi(S.A.W) domin bayyanar
da kishinsu,ba zan ƙara zame ma ka matsala a cikin Gidan ka ba,dan Allah ka yafemin ka zamo,duk dama
nasan kai mai afuwa da tafiya ne a gare ni",ta kai zancen muryarta na fara sauyawa gami da son fara
zubar da hawaye.

"Ya isa haka komi ya wuce ,na yafe miki, duk da dama ban riƙe ki da komi ba, Allah ya shige mana gaba
ya ƙara mana kwanciyar hankali da fahimtar juna a cikin zamantakewarmu"..




Page 43



"Amma dai ba za ka jima ba ko,na ga yamma ta fara yi ga shi gobe Early in the morning jirgin ku zai
tashi,kana buƙatar hutu da natsuwa".
"Mtsss bazan iya ce miki komi ba gaskiya kawai dai sai an ganni domin ina son mu kammala cinikin filin
kafin in tafi,kin san Hamed da shiririta wani lokacin,to su kan su masu filin ba su da tsayayyar magana,ina
so mu kawo ƙarshen komi a yau,dan haka sai kun ganni".

"Okay to sai ka dawo Allah ya tsare,zan shiga Part ɗin na ka sai in haɗa maka duk abinda ya dace
wanda za kai tafiyar da su","A'a No ki zauna kawai ki huta in na dawo na haɗa domin na ga jikinnan na ki
har yanzu da sauran shi"....ta katse shi a ɗan shagwaɓe,"Kamar ya da saura na ni fa na faɗa maka ba
abinda ya ke damuna ina lafiya,lafiya ta ƙalau","A hakan ne ki ke lafiya ƙalau ki na dai ɓoye min abinda
ke damun ki,na daɗe da fara fahimtar hakan duk da har yanzu ban wuce one weak da dawowa ba,kawai
dai na bar ki ne,da tunanin za ki iya magance komi,ko kuma ki neme ni in buƙatar hakan ta zo,na yi juyin
duniya akan ki sanar da ni mene ne damuwar ki kin ƙi, amma duk da haka ban cire rai akan za ki sanar da
ni bato sai dai na ga kwata-kwata ba ki da niyar haka,ki sani ganin ki a cikin irin wannan yanayin ya na
ƙona min zuciya in aganin kamar na gaza wajen sauke haƙƙi ko nauyin da Allah ya ɗora min",Sai da ta
matsa kusa da shi sosai gami da kama hannayensa ta riƙe,cikin sigar natsuwa gami da kwantar da murya
ta ce da shi,"Ka yarda da Ni Mijina da gaske na ke ba abinda yake damuna,inma kuwa akwai to bai wuce
rashin zaman Cikinnan a jikina ba,kasan na sa rai gami da kwallafa rai akan shi,a tunaninna shine kawai
abinda zai iya tsaya min a rai gami da damina kenan","Amma i thought mun riga da mun gama da
wannan maganar ko,me zai sa ki barta tai ta zama a cikin rai da zuciyar ki,zata fa iya yi maki illah,kuma
kin san wannan lamari ne na Allah ba yin kan ki ba ne,fita dan me za ki nemi ki jefa kan ki a cikin wani
hali,dai zai riƙa cutar da ke nuna ya cutar da Ni,gaskiya ban ji daɗin jin wannan zancen daga bakin ki".

"Ka yafe ni Mijina na maka alƙawari da ga yau ba za ka sake ganina a cikin irin wannan halin ba,zan yi
ƙoƙarin ganin na fidda wannan lamarin a cikin Zuciyata gaba ɗaya ko dan in sake acikin natsuwa farin ciki
da walwala,ba zaka sake ganina cikin irin wannan yanayin ba,domin ko kusa ko kaɗan bana don ganin ka
cikin damuwa ko wani yanayi mara daɗi,hakan ya na tashin hankali na gami da rasa natsuwata,ka yafe ni
dan Allah Mujina","Da gaske za ki cire wannan damuwar da tunanin da ki ka sa a cikin ranki za ki koma
Gimbiya Ayush ɗin ki ta asali wacce na sani gami da yin sabo da ita,wacce na ke gudanar da rayuwa da
ita cikin farin ciki,natsuwa da kuma tarin ƙaunar juna?",da sauri ta ɗaga mishi kai gami da cewa,"Eh da
gaske na ke na yi alƙawari,ka san ba abinda zuciya da gangar jikina su ka fi so fiye da na aikata wani da
mafi so ko kuma ka umarce ni da shi".

"Na ji daɗin hakan,na gode sosai Allah yai maki albarka sai na dawo",ya na kaiwa nan ya ɗan jawo ta jikin
shi kafin ya fita.

"Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una",shine kalmar da Gimbiya Ayush ta faɗa ta na mai kaiwa zaune kan
kujerar da ta ke ba tare da wani ƙarfi a jikinta ba,"Ni wannan wacce irin musiba ce,ta wacce hanya zan bi
domin ganin na yi maganin wannan matsalar da kaina,tsoro da firgici ya kama Ni kar asiri na ya toni,ta
wacce hanya zan bi ,in dai-daita komi ba tare da na bari wata matsala ta sake faruwa ba?"...Ringing ɗin
wayarta da ke kusa da ita ya dakatar da ita,sai da ta ɗan yamutsa fuskanta kafin ta ja tsoki ta ɗauki
wayar,ba tare da ta duba waye yiwa kiranta ba,damuwa da kuma tunanin mafita akan lamarin ta ne
kawai abinda ya rufe mata idanu,cikin yanayin murya mai ɗauke da damuwa ta amsa wayar,"Hello besty
kina lafiya ya na ji Muryar ki cikin irin wannan yanayin ko baki da lafiya ne",da ga can ɓangaren aka ce da
ita,"Ohhh Anisa ke ce,ya Gida ya su Umma fatan komi na lafiya"....."Kin ga ki dakata ki faɗa min me ke
faruwa da ke,ko dai ba ki da lafiya ne,Muryar ki ba haka na saba jin ta ba akwai matsala gaskiya","Ina
cikin tashin hankali da musiba Anisa na rasa mafita ko mi ya na gab da lalace min","Subahanallahime ki
ke shirin sanar da ni,kar dai ki ce min asirin da ki ka daɗe ki na binne shi a ƙasa ne aka tono miki?","A'a
Anisa amma ina mai tabbatar mi ki da gab hakan ke shirin faruwa,yanzu dai ke kina ina ?","Ina Gida gani
nai mun kwana biyu,ba mu haɗu ba kuma ba wanda ya kira juna","Ke dai bari Imam Jaheed ya na gari ya
dawo,a dai-dai sanda zan zo inda ki ke ko in kira shi kuma ya dawo hakan ya ƙara dagula min tunani gami
da rashin sanin madafa ko makamar da zan yaƙi lamarin da ya tunkaro ni, amma yanzu dan Allah komi ki
ke ki zo,ya fita zai yi cinikin filayen da ya ke son siye ya sabunta sabon Gidan shi,zai jima bai dawo ba,kin
ga kenan zamu iya tattauna duk wani abu da muke so kafin ya dawo","To Shikenan gani nan zuwa",da
haka suka kashe wayar,zuciyoyinsu kowacce cike da tunanin ka.

Ba a ɗau wani lokaci ba sai ga Anesa ta iso Gidan a rikice,"Lafiya Gimbiya Ayush sanar da ni me ke
faruwa,kin tashi hankalina","Ki zauna ko ruwa in kawo ma ki"...."A'a ki bar shi ki fara sanar da ni abinda
yake faruwa ko na samu natsuwa",Sai da fuskar Gimbiya Ayush fuskarta tai kalar damuwa da ɓacin rai
kana ta ce da ita,"Anesa....Ciki...Cikin jikina yana nan bai fita ba",ta kai zancen tana mai dafa cikin da
hannayenta.

"Innalillahi...taya haka za ta faru,anya kin sha maganin da na kawo maku kamar yanda na ce da
ke?","Wallahi na sha har over doss sai da nayi","Kai gaskiya ban yarda ba ko dai wani Cikin ki ka samu
ne","Ko ɗaya cikin Jikina ba sabo ba ne ba,yanzu haka ya kusa two months,sanadiyar yunƙurin abortion
ɗin da na yi ne ya koma baya"."Taɓ ɗi jam wannan shine ake kira da hukumu lahi,yanzu in ba haka ba
taya za ai ace duk ƙarfin maganinan da ki ka sha ace Cikin bai fita ba,kin sanar da Fadeelah ko?,me ta ce
game da hakan","A Hospital ɗin su aka yi min duk wani gwaji kuma aka tabbatar da cikin yana jikina bai
faɗi ba,hakan yasa na rinƙa bleeding ɗin jini tun bayan faruwar lamarin".

"To tunda haka ne me yasa tun acan ba ki sa an markaɗe shi ba,a fitar da shi kowa ma ya huta ,ta ya za
ki cigaba da zama da shi har kawo wannan lokacin".

"Kin san halin Fadeela,ta riga da ta fitar da hannunta a cikin lamarin,duk yanda na so ta fahimci halin
da na ke a ciki hakan ya gagara,shi kuma idanunsa a koda yaushe a kaina su ke,ya damu matuƙa akan in
sanar da shi asalin abinda ya ke damuna,abu guda ne ya ce-ceni da bai fahimci Cikin yananan bai fita
ba,saboda tunda ya dawo bai samu natsuwa da hutu ba,don tabbas da ya zauna da ya fahimci Cikin
Jikina na nan har yanzu bai fita ba,a ranar da na je Hospital ɗin sai da wani friend nasa ya kira sa ya ce
masa ya ganni,hakan ya sa na kasa iya zuwa wani Hospital ɗin"...."Caɓ akwai babbar matsala bai kamata
ki bar Cikinan ba ya kamata mu bi duk hanyar da zamu bi mu zubar da shi kafin wani ya sake farga da
shi,shin ko wani ɓoyayyen Chemist za mu je inda ba a sanmu ba,a zubar da shi kawai kowa ma ya
huta,na yi matuƙar mamakin rashin aikin wannan maganin ko dan kin saba da shan ire-iren magunguna
na zubar da Ciki shiyasa wannan bai yi ma ki aiki ba".....



“Wallahi Anesa da kin gan ni lokacin zubar da cikinnan, da kin tausaya min, Na sha wahala sosai…...na
kasa yarda duk wahalar da na sha ta tashi a banza,amma ina cikin firgici da tsoro,ina jin kar garin son
kaina da kuma cikar wani buri nawa in gurgunta igiyar Aurena,Ina tsoran kar Imam Jaheed ya fahimci
halin da na ke a ciki,ban san kuma ta wacce hanya zan iya fidda kaina a wurin sa ba".

“Ke dai kin fi kowa tsoro. Amma wallahi karki fa taɓa barin wannan cikin . Maza ba su da hakuri
fa,kuma ba su da kawaici ko kara,in dai a kan mata ne,da zaran ki saki jiki kin fara kwatsa ƴaƴa a Gidansa
sai ya fara sauya maki,gami da tsiro da sabbin halaye,ko yana ƙaunar ki sai kin ga wani ɓangaren sa na
daban.”

Imam Jaheed da shigowar shi kenan ya kasa motsi. Fuskar sa ta sauya launi,bugun zuciyarsa ya
tsananta idanunsa suka ciko da hawaye. Ƙirjinsa ya fara bugu da sauri kamar ana dukan ganga. "Gimbiya
Ayush? Ita? Zubar da ciki, Abortion kenan fa? Kuma da Aurena akan ta,ba sau ɗaya ba sau biyu ba?..."

Ya ɗaga idanunsa masu cike da tambayoyi,kafin ya iya cire ƙafarsa ya tura zuwa cikin Parlon,ba wai iya
Gimbiya Ayush ba,hatta da Anesa sai da ta firgita da ganin sa,ita kuwa Gimbiya Ayush sai da numfashin
ta ya tsaya na wucin gadi,komi na ta a tsaya,zuciyarta ta fara kai kawo shin ya tsinkayi tattaunawar da su
ke,ko kuma bai ji komi ba.

Da ɗan saurinta ta yi kan shi don son ta fahimci gaskiyar abinda ta ke zargi,duk da ta kasa karantar komi
daga gare shi,"Habibi lafiya na ga ka dawo ko ka yi wata mantuwa ne?".

“Kamar dai akwai abubuwa da dama da nake tunanin ban sani ba… Wanda suke faruwa a cikin Gidan
ko ?”ya faɗa cike da ɗacin zuciyar da ya ke ta so ma shi.

A rikice ta ɗago idanunta ta zuba su akan shi zuciyarta ta buga,kafin ta gama saita natsuwar jikinta ya
cigaba da magana, “Idan mace ta ɓoye gaskiya mai girma ga mijinta… me hakan ke nufi? Ƙarya? Kiyaya?
Ko kuma tsoro?”, Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta kasa cewa komai. Zuciyarta ta shiga
rawar tsoro. Ashe ya ji? Ashe sirrin ya ƙare?,ya bayyana yau ƙaryata ta ƙare,ya riga da yasan ɓoyayyar
fuskata da na jima ina ɓoye masa,

Cike da mamaki da ciwon zuciya, ya ce da ita, “Kin sani ina kallon ki a matsayin mace mai kamala da
amana, Gimbiya Ayush,na ɗau so,ƙauna gami da amana na damƙa ma ki ina kallon ki a matsayin wata
babbar kyauta da Allah ya bani,ashe shirmen na ke,ashe ni ki bari ina ta hauka akan son ki,da tunanin na
yi dacen Mata ta kwarai,ashe kallon sakarai ki ke min",Yayi shiru.kafin ya ce da karfi, kamar wanda ya
kamu da kunya da tsana,"Zubar da ciki bayan kina da yaure? Kuma ba so ɗaya ba? Gimbiya Ayush??!”.

Gimbiya Ayush ta fashe da kuka. Ta durƙusa gaban mijinta, tana fadin,“Na ji tsoro ne Habibi… Na ji
kamar idan na haihu za ka guje ni,za ka bar ni,na koma ba wani amfani da zan maka illah in zama mai
renon Yara a gare ka".

Da wani mugun kallo ya bita gami da ja da baya, ya ɗan kalli ƙasa,kafin ya ce “To me kike tunani yanzu da
na sani?,Gudan jini na su ki ka zubar,Jini na ɗana shi ki ka zubar a cikin bola da kwatoci Kin san me kika
zubar da shi kuwa?",wahalata,Jiɓi na da kuma ƙarfina,kin san kuwa irin wahalar da Uba mahaifi ke sha
kafin ya fitar da ɗa daga jikinsa,amma a haka ki ka riƙa zubar mun da su a rariya,tamkar wanda ki ka
maida wani ɗan iska,yau ko a waje mu kai wannan cikin ai ya kamata ki shawarce ni kafin ki zubar da
shi,kai!..... Abortion a gidana abun da mamaki,gaskiya kin shammace ni,ban san haka ki ka ɗauke ni
ba,ashe ni wulaƙantacce kuma abun ƙyama ki ka ɗauke ni ba",ya ɗan tsagaita yana mai cije leɓen shi na
ƙasa,zuciyar shi na ƙuna .

Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kai, hawaye na gudu a fuska,Yayi shiru,kafin ya juya wurin Anesa wacce
tuni hantar cikinta ta kaɗa.

"Wa ma ki ke da suna,Anesa ki ke ko wa?,ke ce wacce ki ke ba Mata ta shawara akan zubar da Ciki
bayan ke ko Auren kin kasa,amma a haka ki ke bata gurguwar shawara,da ya ke ita kuma bata da hankali
ta biye miki ba tare da ta san rijiya gaba dubu ki ƙoƙarin jefa ta a ciki ba".

"Me na aikata maki da har na can-canci ki bada shawarar da a cutar da ni haka!?",ya kai zancen a
tsawace,kafin ta dawo daga razanin da tashiga ta ji saukar mari a duka kuncinta,wanda ba ƙaramin jin
marin tai ba,har sai da ta kai ga fasa wata irin razananniyar ƙara gami da yin hanyar fita a guje shi kuma
ya rufa mata baya yana cewa sai ta faɗa mi shi gaskiyar dalilin da ya kawo ta har cikin Gidan shi kuma
aka haɗa baki ita ana cutar da shi.

"A'a.... a'a...kai ya akai me ke faruwa ya na ga kun fito a cikin irin wannan yanayin kamar waɗanda wani
abun ya biyo daga ciki ?",Yayah Hanne Mamar Biba,wacce ta ke ƙanwa a wurin Mahaifin shi ta ce wacce
shigowarta kenan.

Kasa iya magana yai sai faman nuni da hannu ya ke,ya nuna saitin inda Gimbiya Ayush ta ke da kuma
Anesa da ke ƙoƙarin wajen ganin ta samu hanyar barin Gidan.

"Lafiya me ya ke faruwa ya na gan ka a cikin irin wannan yanayin shin ko akwai wata matsala ne a Gidan
na ku?",cikin rawar murya bayan ya samu ya kwato numfashinsa ya ce da ita,"Mama ki ce ta fita...ta tafi
ta bani wuri bana son ganinta",ya kai zancen ya na mai nuna inda Gimbiya Ayush take,tun kafin ya kai
ƙarshe Gimbiya Ayush ta zube ƙasa tana mai ɗora hannayenta a saman kanta gami da fashewa da kuka
tana furta kalamai daban-daban.

"Subahanallah me yai zafi haka ta ya zaka yanke irin wannan ɗanyen hukuncin,ai bai kamata ba,idan rai
ya ɓaci hankali ake sawa a dawo da shi".

"Mama Hanne dan Allah ki fitar min da ita,ta tafi Gidan su,ina jin zuciyata na sake tafarfasa gami da shiga
cikin wani ƙunci a duk lokacin da na kalli inda ta ke,dan Allah ki fitar min da ita daka Gidana,ko kuma ni
in bar mata Gidan",ya kai zancen hawaye na fara zubowa daga cikin idanunsa.

"Kai...kai lamarin nan yai tsamari,ku zo mu shiga daga ciki",fafur Jaheed ya ƙi shiga in har tare da
Gimbiya Ayush ne ba inda zai motsa,ganin hakan yasa Yayah Hanne tasa Bibah ta ɗauko Mayafin
Gimbiya Ayush su ka bar Gidan shima da ƙyar ta yarda za ta bi su, kafinnan Yayah Hanne ta tafi da shi
Part ɗin shi gami da fara lallahinsa.

Page 44
"Yau ni Hannatu na gode ma Allah na ga abinda ya fi ƙarfina, wannan wanne irin rikitacen al'amari ne ya
kunno kai a cikin Gidannan,ta ya za ai ace nayi-nayi ka sanar da ni me ya ke faruwa amma hakan ya
gagara,sai hawaye ne ke faman fita daga idanunka,ka kasa ce min komi".

Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa tai saurin waigawa,Bibah ce tare Zeenat da ke ta faman raba idanu
alamun ba ta san abinda ke faruwa a cikin Gidan ba,sai daga can baya Gimbiya Ayush ce,sai faman rusa
kuka ta ke ba ƙaƙautawa,"Umma Hanne me ya ke faruwa na ji Gidan ya cika da hayaniya ?", Ummu
Nurain ta tambaya.

"Ni ma abinda na ke son in sani kenan,na shigo Gida na ga ƙawar Gimbiya Ayush ta fito a kiɗime in
taƙaice maki labari, Muhammad ya wan-wanke Yarinyarnan da mari ta fita Gidannan a gigice,Da bakin
shi ya kori Gimbiya Ayush ya ce ta bar mashi Gida,tun daga nan ya shige cikin ɗaki,har yanzu na ya ƙi
fitowa kuma nayi-nayi ya sanar da ni abinda ke faruwa wallahi Yaronnan fafur ya ƙi sanar da ni abinda ya
faru".

Subahanallah yanzu Abu Nurain ɗin yana ciki?", Zeenat tai tambayar a kiɗime ta na mai ƙarasawa
wajen Door ɗin ta fara bugu gami da yi masa magiyar ya buɗe.

"A'aha Bibah ya na gan ki tsaye a nan wai ko har kin dawo Kaita ki kai ki ka jiyo?","Wallahi Mama ba
inda mu ka je,tun fitar mu muna tsaye a waje sai faman kuka ta ke,nayi duk yanda zan yi amma ta ce ita
ba inda zata".

Sai a lokacin Yayah Hanne ta ga Gimbiya Ayush da ke rakuɓe a can gefe sai faman kuka ta ke da iya
ƙarfin ta.

Ta backyard Ummu Nurain ta samu ta shiga cikin Part ɗin na shi,da hanzarin ta ta samu ta isa gare shi
muryarta na rawa ta ce da shi,"Abu Nurain lafiya me ya ke damun ka,waye yai silar jefa min kai cikin irin
wannan damuwar da har yai nasara zubar da hawaye daga cikin idanunka,faɗa min ko shi waye,na
rantse ba zan bar hawayen ka su zuba a banza ba",kamar yanda ta zo ta iske shin ,ko motsin kirki bai yi
ba balle kuma ta sa ran zai ce da ita wani abu,haka ta cigaba da jero masa tarin tambayoyi ba tare da ta
samu amsar ko ɗaya daga cikin su ba,daga ƙarshe cikin fushi ya ɗago yana mai sauke idanunsa da su ka
sauya launi ya ce da ita,Cikin kakkausar murya,"Ki bar wurin nan kar ki nemi ki ƙara hassala ni,in kuwa
ma ba haka ba kema za ki bita zuwa na ku Gidan".

Wannan furuci na shi ba ƙaramin hargitsa ma Ummu Nurain hankali yai ba dan a rikice ta ɗago ta na
mai sauke idanuwanta akan shi cike da mamaki.

"Eh haka na ke nufi kuma ba da wasa na ke ba fita ki bani wuri domin a yanzu na fi buƙatar kaɗai ci".

Hawaye ne suka fara sauka a saman tata fuskar itama,kafin ta ce da shi,"Saboda laifin wani,saboda na
yi yunƙurin shawo kan matsala,saboda na yi niyar cire ka a cikin wannan lamarin,saboda na nuna
damuwar ka damuwa ta ce,shine za ka furta irin wannan munanan zancen a gare ni?"...ya katse ta da
gaggawa,"An gaya maki a irin haka ake raba Miji da damuwar da ya ke a ciki,kin zo kin tasa ni a gaba
akan lalle sai na sanar da ke abinda ya faru,kin ga dan Allah ki tashi ki fita I need a privacy",ya Kai zancen
ya na mai nuna mata hanyar fita.
Jiki a sanyaye ta fito idanuwanta na zubar da kwala,"Ke lafiya ya na ga kin fito a cikin irin wannan
yanayin,"Mama nima ya ce in tafi Gidan mu in har zan takura ma shi da tambaya

"Kai A'a da sake ni wannan lamarin ya fi ƙarfina,ke Bibah sa waya ki ramin Mahaifiyarsa in sanar da ita
abinda ya ke faruwa",da to ta amsa mata kafin ta fara kiran layin cikin Sa'a bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga
bakinta ɗauke da sallama gami da gaisuwa.

"Kin ga ki riƙe gaisuwar ki ganinan Gidan Jaheed na zo na iske su ba a dai-dai ba yanzu haka ma yace
duk matan su tafi Gidan su dan haka ki zo kar ai ɓatatta".

"Subahanallahi shi Jaheed ɗin ne ya aikata hakan to yayi hauka ne ?","Ba na ce ba na dai san nayi
iyakar iyawa ta ganin na shawo kan lamarin amma hakan ya gagareni,ƙarshe ma cewa yai in tafi komi ya
wuce amma sai ya koma ya rufe kan shi a cikin ɗaki, nayi-nayi ya fito ya ƙi,don haka ki zo ki gane ma idon
ki".

"Yayah Hanne ki yi haƙuri amma ba zan iya zuwa wannan Gidan ba,ki kira Momynsa inda hali sai ta zo
taga me yake faruwa"...."Amma ke dai kam Allah ya kyauta miki ɗan

Please Login or Register in order to submit comment