You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum ya ji ya kusa k`oshi,shiyasa na biyo in d`an d`ana kafin in wuce".
"Au tunda k`amshin abincin nawa ya isa mutum ya k`oshi to zo ka tafi ai nasan ka ji k`amshin don haka
ga hanyanan ma za zo ka tafi Gidan ka Matanka na can na jiranka".

"Momy ki bar ni in k`arasa cin abincin sai in zo in tafi,Allah ban k`oshi ba".zuba mi shi Ido ta cigaba da
kallon shi har ya kammala cin abincin.

" Ya jikin Uncle, komi na tafiya lafiya lau dai ko?","Jikinsa da sauk`i kamar dai ko yaushe",sai da ya
gyara zaman sa kafin ya ce,"To Allah ya k`aro sauk`in ya maganar taron k`arama juna sanin da za'ayi a
Canada, shin har yanzu Maganar ta na nan?","Eh tana nan ,ina bibiyar su mai yiwuwa za su iya Kira a
kowanne lokaci"

"Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka koma meye ma k`arasa shi
nan gaba amma banda yanzu,sannan maganar Patient d`in ka da muka fara kabar min sauran aikin,in sha
Allah I'll do my best,ka je ka huta idan ka isa ka gaishe mi da `yata Ummu Nurain da kuma Gimbiya Ayush
banda wannan d`an mai surutun tsiya", murmushi kawai yai ba tare da ya ce komi ba ya nufi hanyar fita.

Tun shigar shi mota ya fara tunani in ya Isa Gidan me zai tadda ,fatan shi d`aya Allah ya sa ya koma me
ye zai zo ya zo da sauk`i,Dan bai ta`ba yin tafiya da ta kai sati ba tare da ya iske tashin hankali a cikin
Gidan na sa ba,tun shigar shi farfajiyar ya fara ganin sauye-sauye a idanunsa,muryarsa ya bud`e da d`an
k`arfi ya kira gate keeper yana mai cewa da shi," Lafiya me yake faruwa na ga Part d`in Gimbiya Ayush a
rufe,haka ma na Ummu Nurain,ko wani abun ya faru ne?".

"Allah ya gafarta Malam bani da masaniya akan faruwar wani abu gaskiya sai dai d`azu bayan fitowa
Sallahr Azahar na ga k`anwar Madam ta Gidan Sarauta ta shigo Gidannan, sun fita tare da Gimbiya a guje
ba tare da sun kula kowa ba, da alama dai Gimbiya ba ta da lafiya kamar hakan na fahimta daga gare
su,bayan ganin wannan lamarin, Na tafi k`ofar Uwar Gida,Na sanar da ita,amma cikin rashin sa'a ta koro
ni ba tare da ma ta saurare ni ba,ta maida ƙofarta ta rufe".

" Subahanallahi me ya same ta to, ta na wanne Asibitin yanzu ?",ya jero mashi tambayoyin ba tare da
ya yi la'akari ba yanda zai si ya san amsoshin su ba,"Wallahi Allah yalla`bai ban sani ba,kawai dai na ga
fitarsu cikin matsananancin tashin hankali bayan haka ban san komi ba"....

K`arar Horn da Me gadin ya ji ce ta dakatar da shi yana mai nufar gate d`in da d`an gudun sa,sai da ya
fara lek`awa ya ga waye sannan ya bud`e fuskar shi d`auke da hamdala.

Motar Na tsayawa Gimbiya Fadeelah ta fito tana mai tallafo Gimbiya Ayush jikinta ,wacce ko tsayiwar
kirki ba ta iya yi,da taimakon Gimbiya Fadeelah su ka Isa Cikin Part d`in har bedroom ta kaita ta kwantar
da ita,duk wannan abun da yake faruwa Jaheed na biye a bayan su sai faman jera mata sannu ya
ke,hannunsa ya kai saman kanta tare da yi mata sannu,hankalin shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare
da tambayar ta,"Me yake faruwa me ya same ta,Allah ya sa koma meye ba mai tsanani ba ne ba ?",ya
tambaya a d`an rikice,inda-inda Gimbiya Fadeelah ta fara ta rasa me ma za ta ce da shi,Gimbiya Ayush ta
fara kici-kicin tashi zaune Zuciyarta sai faman dukan uku-uku ta ke mata,"A kin ga koma ki kwanta jikin ki
ba shi da k`arfin,ki na buk`atar hutu",muryarta cike da rauni irin na marasa lafiya wanda ya ji jiki ta ce da
shi, "Zan iya tashi ai,kuma so na ke in yi maka bayanin abinda ya faru,yanda za ka fahimta", gyara mata
kwanciyar yai gami da janyo blanket ya sake rufa mata," Ba buk`atar ki wahalar da kan ki ga Gimbiya
Fadeelah sai tai min ba yani",ya fad`a a hankali cikin muryarsa mai sanyi.

Kam Gimbiya Ayush ta runtse idanunta a cikin ranta sai faman Addu'a da fatan Allah ya sa kar Gimbiya
Fadeelah ta kwafsa mata ba k`aramin aikinta ba ne ta kwashe komi da ya faru ta sanar ma sa,da sauri ta
bud`e idanun na ta sakamakon jin abinda ke fita daga bakin Gimbiya Fadeelahn take bugun Zuciyarta ya
tsananta hankalinta yai mugun tashi sai faman jujjuya kanta ta ke da bin Gimbiya Fadeelah da kallon da
zai iya dakatar da ita.

"Ina mai baka hak`uri ta sake miscarriage ne ma a wannan karan", Idanuwan shi ya runtse kam ya na mai
k`ara k`arfin ruk`on hannunta da yake a cikin nasa,k`arar da ta saki ce ta dawo da shi cikin
natsuwarta,tuni idanuwansa sun rine sun sauya kala,duban shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da
sake jefo mata wata tambayar da cewa,"Shi kuma wannan mene ne silar faruwar shi, me bincike ya
nuna, kuma ita ya matakin lafiyar ta ya ke?", tuni idanuwansa Gimbiya Ayush sun fara zubda ruwa,irin
haka bata ta`ba faruwa ba,salin alin cikin duk da ta ke zubarwa ya ke fita ba a ta`ba dangana ta da Asibiti
ba iya ita kad`ai da shi ne,wani time d`in ma bayanan hakan ya sa ta ke amfani da wannan damar ta tsara
masa k`arya da gaskiyar da zai yarda da ita,yau kuma an samu kuskuren da jini ya `balle mata wanda har
sai da ta kai ga neman taimakon Gimbiya Fadeelah, Wanda da k`yar ma ta samu ta zo,Addu'ar ta d`aya
Allah ya sa kar ta tona mata asiri in hakan ta kasance bata san zai biyo baya ba, hankali da tunanin ba za
su iya haikato mata ko mi zai faru ba.

"Last two days ta kirani ta ke cemin tana fuskantar Abdominal pain,ta ce min bata son ta sanar da kai kar
ka raba hankalin ka Gida biyu ,hakan tasa nai prescribing d`in medication na aiko mata da su, but amma
still ciwon bai daina ba,yau da sassafe ta kirani ta sanar min,sai dai kafin in zo har ta fara bleeding, haka
na kwashe ta mu ka nufi Hospital, kafin mu kai cikin ma ya fita,a binciken da nayi ne na gano ashe tun
farko cikin a bayan mahaifarta yake hakan ne ya haifar mata da Abdominal pain d`in "Ta ida zancen cikin
rawar murya da kuma inda-inda.

Shiru Jaheed yai na wani lokaci ,ya na mai juya Maganar a cikin rasa,ta ya za ai ace cikinta a bayan
Mahaifa yake bayan shi tun bayyanar cikin bai san da hakan ba,motsin da Gimbiya Ayush ta yi ne ya sa
ya mai do da ganin sa kanta ya na tambayar lafiya me ta ke so ko akwai wani wurin da ya ke mata
ciwo,muryarta a d`arare ta ce ma sa," Yunwa na ke ji ina son in sha ko da tea ne".

Gimbiya Fadeelah ta mik`e ta na mai cewa,"Bari in had`o maki","Kin ga zauna ki huta bari in had`o mata
ai kin sha aiki,Allah ya bar Zumincin ya kuma biya lada",ya na mai zancen ya nufi hanyar da za ta sada shi
da kitchen d`in, da sauri Gimbiya Ayush ta kamo hannun Gimbiya Fadeelah tana mai fara yi mata
Godiya,dama da biyu ya sa ta ce zata sha tea d`in, "Na gode sosai `yar'uwata,Na ji dad`in kasancewar da
ki ka yi da ni a yau da kuma rifa min asiri da ki ka yi,bazan mata da hakan ba,da badan ke ba da yanzu
ban san wanne irin hali na ke a ciki ba,kuma dan taimakon ki gami da rufa min asiri da ki ka yi, da yanzu
Aurena ya fara walagigi,ban kuma san ta hanyar da zan iya gyara shi ba".

Sa`bule hannunta tayi a cikin nata ta na mai cewa," Kin ga sake ni,hankalin ki ya kwanta kin samu abinda
ki ke so sai ki zuba ruwa ak`asa ki sha dan murna,ga wannan magungunan ki ne, sai ki cigaba da sha
domin jininki ya yi k`asa ,in so samu ne ma ki bari a k`ara miki wani jinin,sannan ki kula da abinda Doctor
Nazer ya sanar da ke".....

"A'a ni bana son a k`ara min wani jini zan sha maganin dai,ba na son wani abun ya biyo bayan hakan","
Okay yanda ki ka so,ni zan tafi ko akwai wani abu da ki ke so in sa a kawo ma ki",Gimbiya Fadeelah ta kai
zancen tana mai gyara zaman mayafinta tare da d`aukar Car key na ta,ba ki sake Gimbiya Ayush ta ke
kallon ta har ta kai ga k`asa hak`uri ta ce mata,"Wai me ki ke nufi ba dai tafiya za ki yi ba,ta ya ina cikin
wannan halin za ki tafi ki bar ni ,kin san ina buk`ata ki a kusa da ni fa","Hmmmmm ta`b wallahi ba zan iya
zama ba mijinki ya dawo biside ma ina jin tsoran kar ya gano gaskiya yai tunanin har da ni aka shirya
komi dan haka tafiya ta zan yi babu ruwana","Haba Sis kar ki yi min haka dan Allah ki zauna da ni yau ba
anan Part d`in ya ke ba yana `bangaren Ummu Nurain kin ga in ki ka tafi,shima tafiya zai yi a bar ni ni
kad`ai ".

Sunkuyar da kai k`asa Gimbiya Fadeelah ta yi ta nai cewa,"Ni dai ki yi hak`uri amma gaskiya tafiya zan
yi,ko ma me kenan na dawo wani lokacin"..... Ta kasa ida cewa komi sakamakon shigowar Jaheed
hannunsa d`auke da Tea sai faman tururi ya ke da alama yanzu ya had`a shi.

"Ya dai ya na gan ki a tsaye,ba dai tafiya za ki yi ba?", ya tambaye ta bayan ya k`arasa kusa da Gimbiya
Ayush ya fara k`ok`arin taimaka ma ta ta shi zaune".

" Eh tafiya zan yi Fulani ce ta kira ni ta sanar min Me marta ba ya na kan hanyar dawowa,so shiyasa na ke
son in tafi","A ai ya kamata ki tafi in kin Isa ki mik`a min gaisuwata wajen Fulanin".

"Yauwa na san kai ai zaka fahimce ni amma tun d`azu na ke ma Aunty Gimbiya bayani amma ta k`i yarda

Murmushi ya sakar mata tare da cewa,"Muna Godiya da kulawar ki ,zan cigaba da kulawa da
Matana,Allah ya biya lada ya bar zuminci,Doctor Fadeelah ko ince Gimbiya Fadeelah",Ya kai zancen ya
na mai sakar mata fuska,murmushin yak`e ta yi tare da cewa,"A'a ka Kira ni da Fadeelah kawai ma ya
Isa","Anya kuwa ayi haka kar fa sarautar ki tasa a d`aure ni har igiya tai rara",Ido ta zaro waje ta na mai
cewa," Wane ni ai sai Anty Gimbiya ta fasa min kai".

Dariya yai ya na mai sake kai mata tea spoon d`in saitin bakinta,"Am ni gani ma nake kamar jininta ya fita
da yawa na ga idanunta kamar duk sunyi fari ?".

"Eh haka Doctor ya faɗa kuma nima na ga hakan....."

Da sauri Gimbiya Ayush ta amshi zancen da cewa,"Ni fa ina da Jini kuma sun ba ni magunguna da zan
rik`a sha,in sha Allah zan koma Normal ".

" Ni dai kun ga tafiyata ,Allah ya k`aro sauk`i",ta kai k`arshen ta na mai juyawa ta tafi.

Kallon shi Gimbiya Ayush ta yi tana mai sakin hawayen da ta ke ta faman rik`o tare da cewa,"I'm sorry na
kasa rik`e maka ajiyar da ka bani,Na so ace ma haifo Babynnan ya zo duniya ,ya kira ka da suna Daddynsa
ya amsa sunanka a matsayin mahaifinsa".....,"Shhhshhh ya isa haka ai ba yin ki bane ba hakan daga Allah
ne k`addarar mu ce ba yanda za ai mu tsallaketa kuma mumini na kwarai ne kawai ke iya d`aukar
hakan".

"Haka ne na gode da tunasarwarka mutum mai ilimi da hankali ne kawai yasan da haka,ina mai sake
Godiya game da saurin fahimtar da ka ke min akan irin wannan abun da ya ke yawan faruwa da ni da
wani ne da tuni ya fara zargina akan da sanina hakan ke faruwa".....ya sake katseta a karo na biyu," Ta ya
zan iya yin wannan munmunan tunanin a gare ki bayan irin son da nake ganin kina nuna ma
Babyn,kuma fa a jikin ki ya ke,kin juri dukkanin wasu wahalhalu da kuma ciwace-ciwace akan kawai ki ga
kin haife shi ya zo duniya,ke d`in Mace ta Gari ce kamar yanda na ke fatan wata rana ki zama Uwa ta
Gari",Murmushi ta saki har ta `boye fuska a k`irjin sa tare da amsawa da Amen,shima murmushin ya saki
tare da cewa,"Kin ga tashi ki shanye tea d`in ki kar yai sanyi ",ta na jikin shi ta ba shi amsa da cewa," Ni
na k`oshi,ina son in ji d`umin Mijina ne yanzu".....dakatawa tayi ba tare da ta idasa faɗar abinda ke
bakinta ba,gami barin jikin sa bayan,"Bi a hankali mana jikinki akwai ciwo ,me ya furu haka?",ya tambaye
ta,sai da tayi kalar ban tausayi da fuskarta kafin ta ce da shi,"Ka tashi ka tafi Part d`in Ummu Nurain
nasan zuwa yanzu tasan ka dawo","A'a ba inda zani ina nan,Kina buk`ata ta a kusa da ke",...."A'a kar ka
ce haka,wani abu mara dad`i ka iya biyo bayan hakan".

"Ba abinda zai faru da izinin Allah, ku duka fa Matana ne kuma a k`ark`ashin ikona ku kenan haka ki jira
ni ina dawowa", sake baki ta yi ta na mai bin sa da kallo,shi kuma ya nufi hanyar da za ta sada shi da Part
d`in Ummu Nurain, wanda tun dawowar shi bai shige sa ba.




*JADEEDAH*



STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)



Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1




*YOTA*

PAGE 24❤




Da sallama d`auke a bakin shi ya shiga cikin Parlourn, duk wadatar kayan sanyaya muhalli da ke a cikin
Parlourn hakan bai hana gur`bacewar iskar shak`a a cikin sa ba,kujerun da suka yi ma Parlourn k`awanya
har wani jurwaye suke saboda tsabar daud`a,kan danning table d`in kayan da aka ci abinci ne tsibi
guda,idan ka kai dubanka tsakar tyles d`in wandunan,riguna har ma da takalman Nurain a bar batse a
wurin,runtse idanunsa yai yana mai had`iye abinda ya tsaya masa a mak`ogwaronsa,murmushin dole
Jaheed ya k`irk`iro a saman fuskarsa ya na mai k`arasawa inda Nurain ya ke kwance sai faman bige-bige
ya ke alamun sauro ya na d`ibar roma a jikinsa,shafa kan shi yai tare da cewa,"Yarona gajiya da k`iriniya
sun sa ka yi barci da wuri kenan,ban ji dad`in haka ba na so ace mun gaisa saboda na yi kewar ka
sosai",ya kai zancen yana mai maida kallonta kan Zeenat da ke zaune sai jijjiga jikinta take tana faman
cika tana batsewa,kayan jikinta kan su abun tada hankali ne,kanta d`aure da d`an kwalin atanfa,ta d`aura
shi kamar kullin magani ya d`auru sosai,jikinta sanye ta ke da rigar material, rigarma a bai-bai ta
sanyata,sket ne a jikinta irin Na English weres d`in nan,komi nata a hargitse ya ke.

Kusa da ita ya matsa ya na mai zauna wa kusa da ita tare da cewa,"Ummu Nurain sannu da Gida,ya
kuke,fatan na same ku lafiya",ko motsi ba tai ba balle ya sa ran za ta ce da shi wani abu,ba tare da ya
d`au zafi da abinda ta aikata ba ya kai hannunsa saman fuskarta ya na mai jiyo da ita yanda za ta
fuskance shi,ya ce da ita,"Ba ki ce da ni komi ba ,ko ba ki jin abinda na ke cewa ba?",bige hannunsa tayi
tare da cewa da shi a zafafe,"Kar ka sake sa hannun ka ka ta`ba ni ".

" Ya Salam mai ya faru da yai zafi da har ya kai ki ke furta irin wannan zancen",a sakarce ta d`ago tana
mai zuba ma shi idanunta tare da cewa,"Tambaya ta ka ke me ya faru ?,shin kana son ka ce min ba kasan
abinda ya faru ba,wallahi ina jin zafi tare da mamaki idan na ji ka yi min irin wannan tambayar, sai in yi
tunani kamar ka d`auke ni a matsayin wata banza wacce ba ta ta`ba shiga aji da nufin koyan wani ilimi
ba"....

"Ammm....dan Allah ki dakata ki bar furta wad`annan maganganun marasa dad`in sauraro,in har akan
fara sauka ta Part d`in Gimbiya Ayush ne ina mai baki hak`uri, ba wai nayi hakan intentionally ba,Na
dawo ne na iske Gidan ba a yanda na saba riskarsa ba,ina cikin bin ba'asin hakan Motar su ta dawo wai
ashe bata da lafiya daga Hospital su ka dawo,hakan ne yasa na fara isa nata Part d`in amma ki yi hak`uri
in ranki bai so hakan ba".

Ta`be baki ta yi tana mai kauda kanta gefe tare da cewa,"Oh hakan ne yasa aka take namu hak`k`in
dan a farantawa Mowar Gida ko,hmmm ai ka kyauta"...ya katseta da cewa" Ta yi miscarriage ne ya
kamata ki je ki diba ta",Maganar ta bigeta don ita ba ta ma san ta na da wani ciki ba,don ba wani wanda
ya ke shiga harka wani in har ba `yan fitinar ne su ka ta so ba,a dak`ile ta ce,"Allah ya bata lafiya ,amma
ni dai kam ba zan je Part d`in ta ba","Saboda me `yar'uwar ki ce fa tana da hak`k`i akan ki kamar yanda
ke ma ki ke da shi akanta...",da Katar da shi ta yi ta hanyar d`aga ma shi hannu gami da cewa,"Ka ga dan
Allah, ka daina damuna da batun Matar ka,da gaske raina `baci ya ke kana sa in rik`a jin zafi da haushinta
akan me dan Allah,ina jin tsanar ta fiye da komi a raina,ka barta tayi rayuwarta nima in yi tawa rayuwar".

Subahanallahi, shine abinda ya fara fita daga cikin bakin sa bayan ta kai k`arshen zancenta,ya so ya
nusasshe da ita kuskuren abinda ta fad`a amma ina hakan ba zai yiwu ba, domin ya tabbatar k`ara
hargitsa lamarin zai yi hakan yasa ya ja bakin sa yai shiru sai da suka d`auki wani lokaci kafin ya d`ago ya
ce da ita,"Dama na shigo ne in ga halin da ku ke a ciki daganan sai in yi mu ku sallama domin zan koma
can Part d`in wajen ta domin ta na buk`atar wani a kusa da ita,saboda gudun abinda dare zai haifar"......

Wata irin mik`ewa Ummu Nurain ta yi a zabure,jin saukar kalamansa ta yi kamar an watsa mata ruwan
zafi,ji tai ina ma da ruwan zafin aka watsa mata zai fi mata sauk`i akan sauraran zafafan lafuzzan da su ka
fito daga bakin sa,muryarta na rawa ta kai kunnenta saitin bakin sa tare da cewa,"Me na ji ka ce, fatana
Allah ya sa kunne na ne bai jiye min abinda ka ce dai-dai ba ?",kallon mamaki ya bita da shi,shi a nashi
ganin bai ga wani aibu ko `batanci a cikin lafuzzan da ya yi ba,shima mik`ewa tsaye ya yi ya na mai
fuskantar ta kafin ya mai-maita mata abinda ya ce,"Ce mi ki nai zan koma Part d`in Gimbiya Ayush
saboda gudun faruwar wani munmunan abun cikin dare".

Wata tak`aitacciyar dariya Ummu Nurain ta saki har tana bugun cinyoyinta kafin ta d`ora da cewa,"Ko
da na ji da walakin goro a miya,shin wai kai baka jin kunya babban mutum Malami mai hankali ka rik`a
nuna fifiko a Gidan ka Anya kuwa?,to wallahi in dai da amincewata za ka koma wancan Part d`in to ban
amince ba ba da yawuna ba ".

A tsawace ya ce da ita,"Zeenat wannan wanne irin shashanci ne haka,ta ya za ki saki baki ki rik`a gaya
min duk abinda ya zo mi ki a baki,ki sani ba wai na zo nan in tsaya ina musayar yayeu da ke ba ne ba,Na
zo ne in sanar da ke hukuncin da na yanke,Dan haka kin ga tafiyata", ya kai zance ya na mai kewayeta ya
nufi hanyar fita.

Wani tsalle ta daka sai ga ta a gabanshi,hannayenta da k`afafunta ta bud`e ta na mai kare duk wata
hanya da zai bi ya fita,tuni hawaye sun fara sintiri a saman fuskarta, amma duk da hakan Zuciyar ta batiyi
sanyi ba haka ma bakinta bai mutu ba,"Wallahi rashin adalcin ya Isa haka da ga yau ba zan k`ara bari ka
cigaba da cutar da ni ba,ko ka manta kafin ka yi tafiya irin haka ce ta shiga tsakanin na da kai, don haka a
wannan Karon na lashi takobi ba zan bar haka ta faru ba,ba zan k`ara bari ka zubar min da k`ima da
mutunci a wurin ta ba,ba wani abu da ka ke so kuma ka ke jin dad`in sa wanda ya wuce ka nuna ma
mutane gazawata ba,don haka yau ba inda zaka anan za ka kwana,in kuma kana ganin ba haka ba ka
ture ni sai ka wuce".
"Kin ga bana son tashin hankali da ke don haka salin alin ki bani hanya in wuce"," Na ce an k`i a baka
hanyar ka ture ni ka wuce,sannan ne zan gama yarda da ka zama Mijin ta ce,mai danne hak`k`in wata
akan wata,in kuma ba ka iyawa kwana ya kama kanan dan dole",a ɗan fusace ya juyo yana mai
cewa,"Wai taya ki ke tunani da zaton zan ita kwana a wannan d`akin na ki,kalli tarin bola,k`azanta da
tarkacen da ke a cikin sa ke kan ki kalli jikin ki komi na ki a hargitse",.....ta katse shi da cewa"Tooooo
tanan ka biyo to ai wannan ba laifina ba ne d`an ka da wannan cikin da ke jikina su ne su ka mai da ni
hakan ka ga kenan ba ni za kai ma gori ba,kuma asali ai ba haka ka rabo ni daga gaban iyaye Na ba","Ba
wani ba su su ka mai da ke haka ba haukan ki ne kawai ya mai da ke haka ,ko ke ce Mace ta farko a
duniya da ta fara zama Uwa,kan ki ne farau haihuwa,don haka tun kina fahimtar me na ke cewa ki bani
hanya in wuce",ya kai zance ya na mai son kewayeta ya wuce,sai dai duk inda zai aje k`afarsa sai tai tsalle
ta dire gurin ko nauyin jikin ta bata ji gabad`aya masifa da zafin kishi sun rufe mata ido,haka su ka dunga
zagaye d`akin,har Allah ya sa ya samu sa'a rik`eta sai da ya,kai ta tsakiyar Parlourn sannan ya sake ta ya
juya da sauri ya na mai shirin barin Parlourn har ya kama handle d`in Door d`in zai buɗe,ya ji amon
muryarta a cikin kunnensa da cewa,"Wallahi ban yafe maka ba in har ka sake komawa waccan Part d`in,
tunda dai hak`ina ne a barmin kaya na,ko da Ko bazan amfana da shi ba,da wani irin sauri ya waigo ya na
mai zuba mata idanunsa da suka fara sauya kala,rasa me zai ce da ita yai,ganin hakan da ta yi ta saki
kuka mai k`arfi wanda zafinsa ya kan fita har a cikin muryarta daga k`arshe ta bar Parlourn da gudunta ta
nufi bedroom kai tsaye.

Hannu bibbiyu ya kai yana mai dafe kansa bakinsa ba abinda ya je furtawa sai Innalillahi wa'inna ilaihir
raju'un,daga k`arshe wuri ya samu ya zauna sai da ya kwashi lokaci mai tsawo kafin hankalin shi ya koma
kan Nurain da ya ke ta sharar barcinsa sai bige-bigen cizon sauro ya ke,wurin shi ya nufa ya d`auke shi
kacokan ya na kara shi a jikin sa ya ji wani irin warin daud`a da zarnin fitsari da ke tashi a Jikinsa kai tsaye
Parts d`in shi ya nufa da shi ba tare da ya sake bi takan kowa a cikin matan na shi ba,Zeenat kuwa
saboda tsabar bala'i sai da ta lalla`bo taga ina ya yi kana hankalin ta ya kwanta ta tafi ta kwanta badan
Zuciyarta ta samu salama ba.

Kayan jikin Nurain ya fara cire ma shi, ya samu ya fitar da su daga waje,ya na tafe ya tuna ranar da ya
siyo ma Yaron kayan da kuma farashin da ya siyo su duka-duka kayan ba su fi kwanan wata uku ba amma
har sun kai ga fita hayyacinsu,tayanda ba zai sake marmarin ya gan su a Jikinsa ba,ruwa mai zafi a
bathtub ya haɗa ya dawo ya tashi Nurain d`in a hankali ,"Lah Abbu kaine yaushe ka dawo?",shine abinda
ya fara fita daga bakin Nurain, murmushi ya sakar ma shi tare da janyo shi jikin sa ya ce da shi,"Na dawo
tun d`azu amma sanda zan shigo sai na iske ka yi barci"cikin muryashi yara `yan shekaru shidda zuwa
bakwai ya ce da shi,"Kai amma na ji dad`in dawowarka kasan da baka nan Ummunah tayi ta dukana tana
zagina kuma bata bani abinci akan lokaci,ko wanka ba ta yimin sai taga dama,har kuma"......ya dakatar
shi da cewa,"Ya isa haka Nurain yanzu ba gashi na dawo ba,ba zata k`ara dukan ka ba kuma ni da kaina
zan rik`a yi maka wanka yanzu haka ma ga ruwa can na had`a ta shi mu je in yi maka wanka ka ji Yaron
kirki".tun kafin ya rufe baki tuni har ya nufi hanyar bathroom d`in, sai faman kawa yake ba abinda ya
dame shi.

Sai da ya d`auki lokaci mai tsawo yana musanya ma shi ruwa kafin ya fito da shi,ya shafe masa jiki da
lotion mai tsada,ya sanya masa kayan sa masu sauk`in nauyi,da yake dama yana da da kaya a wurin
saboda faruwar irin

Please Login or Register in order to submit comment