You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi kafin ya gyara zama ya kira sunana. ""Fadimah Zahrah!"" Gabana ne ya fadi, na kalle shi kafin nayi kasa da kaina. ""Na'am!"" ""Idan aure kike so, me yasa baki gaya min ba?"" Girgiza kai nayi, a hankali ya shiga min nasiha, Baffa'm yana da matukar hakuri da sanyin hali, haka yasa ba zaka tab'a jin shi yana faWa da wani ba. Sai da ya gama ya zuba mana idanu yana son jin me zamu ce. ""Kawu shad'ari!"" Kallon Zulaihah yayi zata magana na rike hannunta. ""Meye kike son hana ni magana?"" ""Ya wuce, a barshi ya wuce har gaban Ubangiji ya wuce."" ""Kawu laifi ne don ta kare kanta daga dattin zina? Yar uwarka azzaluma ce, bata da imani."""

"""Kuyi hakuri nasan Allah yana tare da ku, kuma me yasa baku gaya min zaku zo ba? Garin jenuwa babu lafiya, ai da ban barku kunzo ba. Muma zaman dar-dar muke."""

"""Lafiya kawu?"""

"""Lafiyar kenan, sai dai wasu daga cikin yan uwa Makiyaya kuma abin da na fahimta ba™in haure aka samu suka shiga gonar mutanen suka musu barna sannan suka kashe musu mutane kusan goma. HaWe da yiwa matansu fyade, tun ranar juma'a suke son daukar fansa, hukumar tsaro suka shiga cikin lamarin, yanzu haka babu dad'i garin baki daya, shi yasa nake son idan da hali gobe ku bar garin nan."""

"""Baffa'm na dawo kenan fa."" Kura min idanu yayi na wasu dakikai kafin ya ce min. ""Kiyi hakuri ki koma can, idan kin samu miji maza ki kirani ki gaya min."""

"""Baffa'm Sabiru fa?"" Kaina a sunkuye.""Allah bai nufa shi ne abokin rayuwarki ba, yayi aure suna jalingo da Matarshi da yake yana aiki a can."" Wani irin sanyi ya shige ni daga waje har cikin jikina, na hadiye wani irin yawu me daci. ""Baffa."" Kura min idanu yayi sannan ya ce min. "" Allah yana sane dake, ga wannan takardun, ki tabbatar kin nime Mahaifiyarki, domin duk inda take tana cike da kewarki."""

"""Baffa'm me yasa ka bani?"" Na tambaye shi lokacin wani irin sanyi da zazzaSin sun rufe ni. ""Akwai rayuwa akwai mutuwa idan na kasance araye zan tayaki nimanta, idan muka bana raye zaki tsayawa kanki, Zulaihah ku rike amanar juna,kada ku sake wani abu ya raba tsakaninku, ita duniyar ba kome sai rud'i da karya, ba kome zaka bashi damar fushi ba, na horeku da zumunci, kuma duk abinda Addah zata muku, kada ku sake ku yi fushi Allah yana tare da masu hakuri."" Nasihar Baffa'm yake mana, sai da ya gama sannan ya shiga tsokanarmu. ""Kun tuna kuna yara kuke damben wace ce zata sha furar Alhajijo."" Ya dauki wani allon karfe, ya shiga rubutu yana kallona. ""wannan zamanin dole ka nimawa kanka mafita, idan ba haka ba, sharrin zamani sai ya hada da zuri'arka."" ""Haka ne Kawu "" murmushi yayi sannan ya cigaba da rubutun,yana jan mu da hira har ya gama ya wanke a kwanon shan, ya dauko wani saiwa ya jefa yana faWin. ""ku dai rike gaskiya da Amana, ban da cuta da cinAmana, zalunci bai da tsawo domin idan alkadarin ya karye sai an tozarta."""

"""Haka ne!"" Suka ci gaba da hirarsu da Zalaihah ina jin su, har ya gama.ya bawa kowacce ta sha. ""Idan kun fita ku bawa Ummi da Munaisah, su sha."" ""In sha Allah!"" Muka fada, ""Baffa'm rubutun me ka bamu?"" Murmushi yayi ya ce min. ""Tsarin jiki ne?"" Gyada kai nayi, har zan fita ya ce min. ""Innawuro!"" Juyawa nayi, ""zo nan!"" Komawa nayi na zauna, bude wani ™unshin takarda yayi ya mika min. ""Ina ta ajiyewa kafin aurenki, ki saka a wannan abin me kama da lalita, wata rana zai miki amfani kada yunwa ko talauci ya sa ki.aikata Zina don Allah ki rufa min asiri kinji. Duk inda zaki kada ki zauna babu sana'a wannan gwal ce na Mahaifiyarki.""gyad'a Kai nayi, a hankali na mike ina mishi godiya, har zan fita ya mika min wasu leda. ""Shi wannan abubuwan masu mahimmanci ne, na yaran Harirah ne nasan..."" Burr muka ga shigowar Nenne, fisge ledar tayi, ""wato ga yar so, ni kuma nawa yaran da baka so su mutu da bakinciki da yunwa bani. Ai keda ganin uwarki sai a lahira."""

"""Harirah kenan. Allah ya bamu sa'a."" Daga haka na fita na barsu, tana saukewa Baffa'm tijara. Ni kan cikin gidan na nufa duk da wani irin zazzaSin da nake ji, bai hanani zuwa sassan Baffa Modibo na gaishe su ba,har dama-dama"

"Yakumbo bata da matsala, sai Amaryarta ce ma Bama shiri. Yakumbo wacce sunanta Sarai tana da yara hudu,"

"Shu'aibu shine babba yana yola a can yake karatu shine yaron da ya fita Zakka a bangaren Baffa Modibo. Sai Jamilu yana nan domin yayi aure yana garin takum, sai Sa'idu kafin Ummi."

"Amaryar Baffa Modibo kuwa, tana da Yara kusan shida duk maza ne, sannan irin haihuwar nan na kunika. Yaran kamar kwarkwata."

"Aminu shine babba, sai Zakaria, Amadu, Adamu, Abdullahi, Abubakar dan karaminsu, wucewa dakin mu nayi na kwanta, ina ganin Zuzu tana dafa mana abinci,domin doya ce take dafawa zata mana miyar kwai. Zulaihah akwai kokari domin duk inda zata, tafi da gidanka take yi, har indomie tazo mana da shi, ga kifin gwangwani irin me Mai din nan. Tana gama dafa doyar take bani labarin yadda tayi da ruwan rubutu,ta ce min. ""ke nabasu suka ki sha, ai kuwa na sha rabi na bar miki rabi."""

"Ni dai bance mata kala ba, na cigaba da kwanciyar da nake, domin idan na bude baki zan yi magana kuka ne zai kwace min. Haka na dauki lalita ta, ina kallo. ""Zahrah ya dai?"" Idanuwa na da suka cika da kwalla na kalleta.""Ashe Sabiru yayi aure bai gaya min ba?"" ""Mtsew sai kace autan maza."" A hankali na fashe da kuka, ina jin wani irin abu yana taso min, kamar kukan nan saka ni ake yi, har sai da nayi na gaji, tana kallona taci abinci ta koshi, ta mike ta daura ruwan zafi, ta fita tayi wanka sannan ta shirya zuwa gidan Babanta, koda ta je can faWa yayi mata me yasa zata zo, gari ba lafiya. Hakuri ta bashi tare da mishi zancen ta hadu da wani tana son ta turo shi,ta kira saurayin ta hada su, sukayi magana ta roki Babanta kada ya bari Addah ta sani. Ya mata al™awarin ba zata sani ba."

***

"Karfe biyar ina wurin dabobbi, ina taya Baffa'm tatsar madara. Wayarshi tayi ™ara dauka yayi yana me sallama. "" Alhaji Abubakar ko?"" ""Eh ni ne?"" ""Okay ko zaka fita kai da wani naka, domin mun samu labarin za a."""

"""Anan aka haife mu, anan muka girma bamu da inda yafi nan, sai dai mu mutu, Yallabai mun gaya musu, bamu ne muka musu barna ba, taya zamu cigaba da amsar laifin da bana mu ba, a matsayinku na jami'an tsaro hakkinku ne kula da rayuka da dukiyoyin mu."""

"""Shi kenan, kada kace ban sanar maka ba, na gaya maka gaskiya kuma ba a bamu umarnin kare kowa ba, don Allah ka fita daga cikin Jenuwa."""

"""Shi kenan!"" Baffa'm ya faWa yana kallona, taya zai fara. Haka ya wuce ni ya saka aka kira mishi sauran mutanen rugar ya gaya musu abin da ya™e faruwa. Shiru suka yi kafin aka samu wasu tsagera suka kama dariya.""Baffayo kana nufin Mu bar rugarmu saboda kada mu mutu? Kusan kai ma kana da shanun nan,don haka babu inda zamu ai wannan maganar karya ce wallahi babu wani! Harin da za a kawo mana, da alamu tsufa ya fara kama baffayo."" Kiri- kiri matasan nan suka ™aryata shi, haka yasa shi komawa gida da tarin takaici da bakinciki."

"Koda ya dawo ana kiraye-kirayaen sallar Magariba, a masallaci ma yayi magana dayawa suka karya tashi sai yayi shiru, koda ya dawo bayan isha muna cin abincin, ya shalenta abin yake faruwa a cikin gidan, Babangida ya ce mishi. ""Baffa taya zasu kiraka su gaya maka, kawai dai wannan zance ne. ""Bai fito ya ™aryata baffa ba, amma maganarshi sak ce da ta sauran mutanen, ban san me yasa ba ko don a gabana aka yi wayar sai naji zuciyata tayi sanyi, kuma wani irin tsoro da fargaba, ya shige ni Zulaihah ma ta shiga haWa duk wani abu me muhimmanci akan mu bar garin cikin daren nan, amma wani abin mamaki kana naka, Allah yana nashi, wurin karfe tara na dare, muka dinga jin ™arar harbe-harbe, hankalin Baffanmu ya tashi, yana shigowa dakinmu ya ce min..""taso Fadimah."" Tashi nayi a rikice ya cewa Zulaihah. ""Kema tawo!"" Dakinshi ya wuce damu,"" kada ku sake ku fito matukar bani na bude muku kofar ba, da izinin Allah babu abinda zai faru."" Ashe ya tafi har dakin Nenne ya kwaso yaranshi, Yar matan nan tace ta adana Yaranta, domin mugun nufinsa ya janyo wannan tashin hankalin,da bai fada ba ai da babu abinda zai faru. Bai mata magana ba ya dawo duk inda ya nime su bude kofar ya kwaso yaran sunki,.haka yasa shi dawowa ya dauki addarshi ya tsaya a kofar gidanmu."

"Ban tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba,domin kuwa kana d'aga kai zaka ga yadda garin yayi jajjur da wuta da hayaki. Baka jin kome sai karar bindigu da kukan dabbobi."

"Ban san me yasa idan wani abu ya faru mutane ke huce takaicinsu akan shanu ba, shanu suna da daraja a rayuwar"

"Bafulatani, domin zai iya hakura da rayuwarshi akan dabbarshi, amma mutane basu ganewa. A cikin yan dakikai nayi wannan nazarin, ""Tau!"" Muka ji kar'ar harbi kamar a cikin gidan anan aka yi,kuma babu karya a cikin gidan aka yi. ""Malam Buba yau addarka ba zata amfane ka, da kome ba, domin kafin ka kai sara mun tashe ka aiki."" Jijjiga kofar nayi ina hango Baffa'm a kwance, domin sun haska mishi katon torchlight dinsu mai shegen haske, Baffa'm a kwance jini na zuba ta gefen cikinshi."

"""Kai ku shiga ku fito mana da yaran da suke cikin gidan, matan ku ware mana manya da kanana, mazan a musu yankan raggo a gaban Malam Buba da yace basu ne suka mana barna ba."" Inji mutumin, ""tow;"" dakyar"

"Baffa'm ya mike yana rike kafar mutumin. ""Don Allah dan ladi kada ka cutar dasu, wallahi bamu bane. Akan me"

"zamu cutar da zaman da muka yi na amana da ku?"" Shure Baffa'm suka yi tare da take mishi wurin ciwon, suna murtsukawa. Haka suka fito da kowa na gidan, har da Baffa Modibo. Babangida da Habibu. Sa'idu da su Aminu. Dukar kofar da nayi yaja hankalinsu ba zan iya ganin wannan cin mutuncin ba, gara na mutu da Mahaifina. ""Aiho boye wasu kuka yi?"" Ya dokawa Baffa'm gindin bindigarshi akan ciwon, ""ku balla kofar ku fito da su."" Haka suka nufi kofar da gudu Baffa'm ya tashi yana me tare kofar. ""Ku min kome na yarda, don Allah ku kyale mata da yaran basu yi kome ba."" Rufe shi da duka suka yi, tare da janshi daga kofar dakin suka Salle kofar, tare da finciko mu. Suka yi waje damu. Ganin suna dukar Baffa'm babu me cetonshi na nufe shi, tare da fara ture su, haka aka fisgo ni suka bugani da kasa, tashi nayi da rarrafe kafin na isa sun mishi wani irin duka tare da cin zarafinshi suka tube mishi suturarshi. Rike gashin kaina mutumin yayi yana dariya. ""Ke me baba ko? Maza jeki, Malam Buba idan kana son mu kyaleka dole sai ka amince kayi tarayya da Yaranka mata. Su kuma Yara mazan su kwanta da iyayensu Mata ko kuma mu,mu kwanta da su."""

"Suka fada suna dariya irin abin ya musu dad'i. ""Ku kashe ni ba zan iya ba, ba zan iya kallon wannan kazantar ba."" ""Ashe? Tow kai daure min hannun mazan a musu yankan raggo su kuma matan ku ware min yan matan manya kuma su raba su."" Har zuwa wannan lokacin yana rike da gashin kaina. ""Dan Ladi kada kayi abin da zai dame ka, don Allah kada kaci zarafin Musulunci mana, addinin Kirista bai baka damar cin zarafin mata da yara ba."" Amma mutanen nan suna dariya suka d'ago Babangida. ""Kaje ka kwanta da uwarka kacita kamar yadda namiji yake cin Matarshi a gadon auren, kada ka biyewa Ubanku ba zai tab'a barin ku tsira ba, kana gamawa ga kofa ka fita ba zamu tab'a ka ba."" Kusan yadda dan Adam yake da buri, kuma a ran Babangida gani yake idan ya aikata haka zasu barshi ya rayu, Baffa'm yasan yaudara ce kawai. Rike hannun Babangida yayi ya ce mishi. ""Idan ka sake ka aikata haka, zasu kashe ka Allah ya saka hijabi a tsakaninku har abada ba zasu kasance a shimfidarka ba, Mahaifiyarka da yan uwanka, haramtattu ne a gare ka. Don haka kada ..."" Dauke kan Babangida suka yi da harbi, sai gashi a jikin Baffa'm. Wani irin ajiyar zuciya Baffa'm ya sauke ya ce musu.""Gara ku kashe mu da ku kasance kuna saka mu,aikata barna."""

"Wurgar da ni Mutumin yayi na na rarrafa wurin Baffa'm, na mika mishi kayanshi. Ina durkushe a gabanshi. ""In sha Allah duk tsanani yana tare da sauki, kada wani abu ya ba™i tsoro gwagwarmayar "" Sake mishi harbi suka yi a"

"gadon bayanshi. Ya fadi a jikina. ""Kada tsoron mutuwa yasa ki ki tserewa da zaki rayu. Kiyi iya yinki Allah yana tare da mai gaskiya da takawa."" Wani Harbin suka yi mishi sai da jin ya wanke min fuska. Har lokacin bai cika ba, babban burin shi yaga mun tsira ba tare da sun ci zarafin mu ba."

"Janyo shi suka yi, akan idanuna kamar wata gaula ina kallonsu, suka shiga bude mishi wuta har sai da ya daina"

"shure shure yana kalmar shahada, ban san ya aka yi ba amma ihu da karar harbe-harbe nake ji amma ban san me yake faruwa ba..haka suka yi ta bin Yaran nan suna harbinsu har da Baffa Modibo, akan idanun Nenne suka kashe mata Yaranta maza biyu, Yakumbo Sa'idu, Amaryar Baffa Modibo kuwa a wurin ta samu tab'in hankali domin kuwa ganin jinin yaranta yasa ta kama dariya. Bayan sun kashe mazan baki Waya, haka suka yi ta bin iyayenmu mata suna kwanciya dasu, ko nace Fyade. Hawwa'u da Hadiza kan, ko taron da mazan suka musu ne, amma ban san kome ba, sai da naji an rufe mu da duka ni da zalaihah. Ni dai naji kamar an suka min wani abu ban kuma sanin kome ba."

"Bayan sun gama ta'aadacinsu, suka sakawa gidan wuta, kafin wani lokaci rugar mu ta zama makabarta domin babu inda babu gawarwaki. Sannan yadda suka tozarta mu haka suka bar mu a wulakance. Bayan tafiyarsu Addah da duk rashin imaninta yau sai da tayi kuka, Ita ta tashi da gudu tana shiga dakinta ta Ciro kaya tana daukar zanuwa da zanin gado, ita da Yakumbo. Dukkan iyayen nan kana ganin yadda suke abu kasan karfin zuciiya ne domin Nenne da suka mata wulakancin bata iya tashi ba, haka aka yi ta lullube gawarwakin da sauran mu, ita kan Amaryar Baffa Modibo, bayan sun gama mata fyaden, kasheta suka yi sannan suka barta a wurin. Zama Addah tayi a gaban gawar kannenta ta fashe da kuka. Sai lokacin kuka ya zo mata, har gari ya waye sai lokacin yan agajin gaggawa suka kawo mana taimakon gaggawa. Aka wuce damu asibiti sai dai kuma babu gado domin kuwa asibitin cike yake."

"Wani abin da nake son ku sani, Taraba tana kudu da kasar Kamaru, sannan koda aka bamu taimakon babu wani"

"abu, tura mu camp na yan gudun hijira aka yi, muna zuwa can,aka ce babu wuri dole aka hada mu da hukumar gudun hijira aka mana takardu aka wuce da mu Kamaru...."

This is the beginning.....300¦ .. #thedambuje

"[2/16, 9:24 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

"*Wato jiya an yi kuka, hmm ayi hakuri na kara bada hakuri. Abin labarin a sannu wannan naku ne masu bibiyata."

Allah ya saka da alkhairi  na ji dadin comments dinku na jiya ya tashi kaina su Auntys and mommies har da niman kari Na gode sosai*

*008*

"Saboda azabar ciwo da muke fama da shi, bama fahimtar juna ko me yake faruwa, iyayen mu mata kawai zaka kalla ka fahimci suna cikin wani yanayi amma gudun kada su sare a gaban idanuwan Yaransu yasa suke fakar idanunmu suna kuka. A haka muka isa har Kamaru tafiyar kwana biyu,"

"Adamawan Kamaru aka kai mu, anan babban camp na yan gudun hijira ya™e. Sai da muka je asalin headquarter aka mana takardu, sannan aka wuce da mu asibitin da ya™e asalin garin, anan aka shiga bamu taimakon gaggawa."

****

*Niamey: Niger republic*

Ranar zaben.

"Wato wannan ranar abu biyu za a gabatar na farko yadda suka shirya idan har suka fi su Aryan Mamman Ba'are yawan vote. To zasu amshe BA'ARE GOLDEN EMPIRES daga hannunsu Hajiya da Yaranta, na farko kenan, na biyu zasu sayarwa mutanen kasashen waje, sannan su zare hannun jarin Hajiya da Yaranta."

"Sai dai wannan lokacin al'amarin daga ita har Yaranta sun sadakar musamman da suka ga Aryan Mamman Ba'are ya dawo babu Majeed, sai jikinta yayi sanyi a matsayinta na Uwa ya zata yi? Hawaye ne ya zubo mata tana kallon Aryan Mamman Ba'are."

"Tasowa yayi ya mika mata hanky yana faWin. ""Kukan me kike yi?"" ""Na hango faduwarmu ne, burinsu idan muka fadi hatta gidan BA'ARE housing estate zamu bari, duk wani abu da ya shafi BA'ARE zamu bari."" Dariya yayi yana faWin.""haka muke so sannan a wannan karon za a sake gwanjon kome har da estate kenan?"" Ya fada yana mikewa daga inda ya zauna ya koma wurin shi, masu hannun jari da matsayi a board din kamfanonin BA'ARE mineral oil and gas, amma babban al'amarin da wannan rikicin yana kan GOLDEN EMPIRES ne."

"Hajiya Nana ita ce a sawun gaba, sai Hajiya Tani da d'anta Sajjid Mamman Ba'are, sai Hajiya Rabi Mamman Ba'are, sai Hajiya Fauziya Mamman Ba'are, can sai ga Hajiya Harirah Mamman Ba'are, dukkansu da yaransu mata da maza."

"Dukkansu nan babu wacce za a nuna mata takarda ta karanta, kawai kishin jahilci ake yi, Hajiya Sa'adatu Mamman"

"Ba'are, ita ce Hajiya mahaifiyarsu Captain. Kuma ita ce Amaryar Alhaji Mamman Ba'are,sannan ita ce take da Yara maza uku cif. Su Majeed suna da yayu mata manya, amma kusan da yake akwai kishi da hauka yasa kowa yake rayuwarsa a inda ya™e."

"Idan ka cire Hajiya Harirah da take da abin bata yarda ta kashe kanta da kishi ba, domin sai da ta nime ilimi, saboda ta fahimci wani abu da sauran suka gaza fahimta."

Can Alhaji Haladu Abdul Majid Ba'are sai

"Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kafin Hajiya Hadiza Abdul Majid ba'are."

"A bangaren Hajiya Sa'adatu Mamman Ba'are, Akwai Amaan Mamman Ba'are, sai Aryan Mamman Ba'are, sai Jamilah Mamman Ba'are, sai Aneesah ita ce auta."

"A hankali wurin yayi ta cika, kuma a wannan zaman babu bare amma kuma wani abin mamaki shine zuwan wasu"

"daga cikin turawa da yan siyasar da Sajjid Mamman Ba'are ya gayyato, ya tashi ya taro su. Har wurin Nana suka gaishe ta. Kafin suka gaida kowa sannan suka koma wurin zamansu, Abdul Majid dan Hadiza Abdul Majid ba'are, ya mike tare da nufar wurin Hajiya suka gaisa. ""Hajiya Abdul Jeed ba zai zo bane?"" Idanunta da suka cika da kwalla ta ce mishi. ""Ban sani ba, na dai tura Aryan bai ce min kome ba."""

"""Lallai Jeed dole ya bayyana anan. Domin an shirya makirci na bala'in fitar hankali."""

"Duk wahala da ta sha, da iya azabar da ta sha, wai karshe abin da ta samu shine ya tsonewa kowa ido. Suna da nasu amma ita nata da na Yaranta ya tsone musu ido. Hajiya Hadiza Ba'are watsawa danta Abdul Majid harara tayi, ita kan bata san wani irin d'a ta haifa ba, ko a gidan Ubansu haka yake makalewa ya'yan kishiyoyinta yana basu kulawa kamar wani son shi suke."

"Komawa wurin zamanshi yayi yaki yarda ya kalli Hajiyarsu, da Nanah kakarsu kenan. Kanshi yana can bakin kofar"

aka fara taron tare da zab'en ra'ayi akan matsayin BA'ARE GOLDEN EMPIRES. Abin dai ba a cewa kome.

"Haka aka fara voting, jikin Yaran Hajiya yayi sanyi ban da Amaan Mamman Ba'are, dan shi dama yasan haka zata"

"faru, kuma shi yana tare da su, babu me kaso mafi girma da yawa a kamfanonin kamar Majid, don haka gara ayi uwar watsi kowa ya rasa, Aryan Mamman Ba'are kuwa ko a jikinshi domin bai tashi ya kada kuri'ar shi ba, kallon shi Alkalin yayi ya ce mishi. ""Malam Aryan Mamman Ba'are, shin baka ga kowa ya kada kuri'a ba ne?"" D'ago kai yayi yana yak'e ya ce mishi. ""Alkali kayi shiru yanzu zan kundume wasar domin uban gayya ya bayyana."" Ya cigaba da danna wayarshi alamar game yake yi, ""Malam Aryan kuri'arka ake jira fa."" ""Ba iya nawa ba, har da na wancan da yake tsaye a bakin kofar."" Ya nuna musu Majid Mamman Ba'are sanye da kayan turang. Shadda ce skyblue, yasha babban riga da takalmi halfcover, kanshi sanye da rawani ya rufe fuskarshi da ita, yadda yake tafiya kasan cikakken jarumi ne. Mikewa Aryan Mamman Ba'are yayi ya tafi can bayan kujerar da aka ware babba kuma an lullube shi da mayafi, Hajiya ya dace ta zauna a wurin amma saboda fitina ta hakura, sai gashi Aryan ya janye lulluben da aka mata, sannan ya jata baya, Majid Mamman Ba'are ya isa wurin y zauna, dukkansu sai da suka mike tsaye. Yadda ya zauna sai da ya jingina da kujerar sannan ya aza kafa d'aya kan Waya, ya janye mayafin da yake fuskarshi. Yana bin ilahirin mutanen wurin da rikitaccen Idanuwan shi me dauke da wutar takaici da b'acin rai. ""Amma taya dan iskan Yaron nan ya dawo?"" Cikin kwafa Hajiya Tani tayi magana tana kallon Majid da ya daura daya kan Waya, yana sakin wani murmushi yana kallon Aryan da ya koma wurinshi da zama. ""Alkali Bismillah!"" Inji Aryan ya faWa yana murmushi. ""Tow Malam Aryan kuri'arka da ta Abdul Majid Mamman Ba'are ya rage, akan sikeli"" hannu ya kai aljuhun rigar shi ya Ciro wasu zinarai manya guda uku, sai na shi daya yana zuwa ya saka nashi, yana kallon kowa a wurin sannan ya saka daya na Majid Mamman Ba'are, tuni hannun ya rinjayi daya hannun cikin tsokana da niman magana ya ce. ""Alkali idan na saka sauran biyu ina cewa Ba zaku ce nayi son kai ba?"""

"""Baka da matsala Malam Aryan"" cikin wani irin juyi ya ajiye dayan, sai ga shi bakidaya ya rinjaye gefen. Kafin d'aga dayan sama ya ce musu. ""Kun ganshi nan kuri'ar Majid Mamman Ba'are na karshe kenan!"" Ya ajiye . Shiru wurin ya Wauka. Babu wanda ya kawo Majid zai bayyana, balle a kawo zancen kuri'arshi, sannan babu wanda ya kawo wannan al'amarin haka shi daya kuri'arshi daya ta mutane goma ce

Please Login or Register in order to submit comment