You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakiWaya, wani irin narkewa zuciyarshi take, musamman da yayi ido biyu da yan uwanshi, akwai wani abun da ya bashi mamaki ya aka yi"

"hakan ya faru? Ace Aryan da Amaan da Jamilah sun yi hatsari a lokaci guda, ya aka yi haka ya kasance? Yana gama"

"aikin tare da taimakon wasu likitocin da Nurse, ya fito daga dakin yana zare safar hannunshi, Hajiya ya hango a can gefe zaune. Da sauri ya cire facemask, ya nufe ta da sauri, yana tab'a kafadarta tana tafiya bakiWaya ta kwanta, ""Hajiya!"" Ya kira sunanta da karfi, abinda ya ja hankalin mutanen cikin wurin kansu kenan, wasu daga cikin nurse na asibitin da suka san Hajiya, sune suka turo abin daukar mara lafiya ya d'aura ta akai. Kome na kan Majid ya tsaya cak, bai gama fita daga mamakin hatsarinsu Amaan ba, ya kuma katari da sumar Hajiya."

"A wannan karon ya gaza taimaka mata, Dr Najib ne ya tsaya akan Hajiya. Bayan ya gama aka turata daya daga cikin dakunan VIP domin yadda jininta ya hau bata son hayaniya bata son ganin duk abinda zai sake d'aga mata hankali. Zama Majid yayi yana kallon yadda ta koma duk saboda su, shi kan bai san inda zai cusa ranshi ba, amma har ga Allah ya gaji da tashin hankalin da yake faruwa a cikin gidansu."

"Yana tsaye aka sakawa hajiya bututun zukar numfashi, don alamar hawan da jininta yayi ya tab'a mata"

"zuciya, shi yasa suka saka mata oxygen din, ko zai taimaka mata wurin zukar numfashinta, fitowa yayi daga dakin ya tsaya yana sauke numfashi. Sakatariyar Hajiya wato Salamatu, tana tsaye jingine da bangon dakin, kamar zata yi kuka. ""Ya Hajiya da jikinta?"" ""Da sauki"" ya furta a sanyayye, ""Alhaji me ya faru ne?"" D'ago farareen idanunshi yayi, ya zuba mata. Kafin ya sauke gwauron numfashi, lashe bakinshi yayi yana faWin. ""Ban san kome ba."" Ya faWa yana kallon ™asa, ""Amma taya haka ya faru?"" Inji Salamatu, bakiWaya hankalinshi baya tare da shi, sama sama ya tsinkaye muryan Anisah. Tana ihu kamar mahaukaciya, d'ago kai yayi ya zuba mata idanu, a hankali ta rage sautin kukanta. Daga nan ya maida hankalin shi kan nazarin shi."

"Bayan awa guda, hankalin mutane ya koma kansu Familyn Ba'are, musamman labarin Amaan da abin da ya faru, kafin kace kwabo an shiga rubuce rubuce akansu da nuna su, kamar wutar daji labarin ya karad'e ko ina, sai da ta kai babu wanda yake shiga asibitin da sunan Familyn Ba'are, sannan wani abin mamaki yadda yan jarida suke ta zarya asibitin."

"Karfe sha biyu na dare, Aryan ya farka cikin tsannanin ciwo da wahala. ""Hammayo!"" Ya kira sunan Majid."

"Kallon Aryan yayi yana duba na'urar da yake kanshi. ""Anisah tana cikin tarkon Shaidaniyar Tani."""

"Bai kula shi ba, domin gani yake kamar magagin ciwo ne. ""Hammayo ka bincika Anisah."" Jan allura yayi ya mishi a cikin drip Winshi. Rike hannun Majid, ""Na rantse da Allah, tana cikin damuwa kayi wani abu."" Daga haka barci yayi gaba da shi. *Anisha kuma?* Ya faWa a ranshi, a hankali ya fito yana jin wani tashin sense. Bai tab'a ganin tashin hankali irin wannan ba."

"A hankali ya fita tare da nufar office din da bai tab'a shiga ba, ya zauna yana me jin kamar ya fasa ihu. Wayarshi ya ciro yana saka a kunne. ""Kayi tracking number Anisah ina jiranka."" Kashe wayarshi yayi yana nazarin irin matakin da zai dauka."

Marad'i

"Bikin sallah, anyi shi cikin farinciki duk da bani da kowa a marad'i, amma kuma Maman Barakatu da Yaranta, sun saka ni farinciki. Haka muka kwashe wunin ranar muna yawo,koda muka dawo sallah muka yi. Akwai wani abu da na fahimta a rayuwa, shine duk inda zaka shiga matukar naka yana tare da kai zaka ji kamar ka samu duk wani farincikin da kake nima, haka nake ji a duk lokacin da na kalli Amirah sugrah, uwa uba Yazid da ya maida ni mutum, bawan Allahn nan ban san da me zan saka mishi ba. Bawan Allahn nan yayi hidima dani ko nace yana hidima da ni, domin taimakon da yayi min hár abada nake jin babu wanda zai min irin shi. Bugun kofar falon da nake kwance ya katse min tunanina, tashi nayi naga Barakatu ne da Amirah. ""Wai zata zo wurinki ne har da kukanta."""

"""Mirah me yasa kike da halin rashin kirki, tow ai sai ki shigo."" Da sauri ta miko min hannu na amshe ta. ""Tante kiyi hakuri, kawai bata son nisa dake ne."" ""Kyaleta kiuya ce kawai, amma ina wani nisa sai tazo ai."""

"Haka na amshe ta, Barakatu itama ta shigo muka zauna. ""Mama"" ta kira sunana, tana rike hannuna, ""Ko kina jin yunwa ne?"" Kallonmu Barakatu tayi, kuma na bata abinci taki ci fa."""

"""Yau tana jin rikici ne."" Haka na wuce kitchen na hada mata shayi na kawo mata, ta fara sha tana gamawa kamar wasa yarinyar nan ta koma gefe sai barci. ""Halin Amirah sai ke Tante kada ki ce ban bata abinci ba, amma taki ci."" Ta fada tana mita, ita nan Amirah ta bata takaici, tashi nayi na kawo mana abincin na ajiye mana, ""Ga abinci."" ""Ni kan ba zan ci ba, tunda aka yi na jiya naci nayi ta yawon ban daki, na ha™ura kunu nake ta sha kawai."""

"""Da dai kin ci abincin."" Na fada mata, tura baki tayi tana mikewa, ""ina gaya miki, cikina baya son abinci yanzu sai dai ki hada min shayin Amirah shi kan zan sha."""

"""Lallai cikin nan naki, kwadayayye ne tow ki shiga kitchen ki haWa."""

"Dariya ta saka tana tafiya, ""Tante na gode, Allah a koshe nake kawai zolaye ce."" Tana faWar haka ta bar falon, ajiyar zuciya na sauke, sau dayawa rowa yana rage kima, kyauta kuwa yana kara daraja da girma. Da nace mata ba"

"zan bata ba, da ba zata ji dadi ba amma da nace taje ta haWa gashi don kanta tace a'a, kuma abin da na lura kamar"

tarbiyyar mahaifiyarsu ce.

"Yaran basu da kwadayi, sannan duk abin da zan basu basa rawar jiki a kai, asalima tsoron karba suke kada iyayensu, su musu faWa kaga inda ake tarbiyya da adalci, a wannan zamanin da son kai da son zuciya, wani yaron baka isa ka shiga gidansu ba, idan ka shiga ma yayi ta maka rashin kunya iyayenshi na dariya wai ai yaro ne, wani kuma kana zuwa da shi wani wurin yayi ta kunyata ka kenan, duk ™o™arinka akanshi kuwa, irin wadan nan Yaran iyayensu ba karamin kokari suke wurin tarbiyyar su ba, sai dai muce Allah ya shirya mana zuri'a amma Iyaye na kokari akan Yaransu, domin wata zaki sha mamaki idan da zaka ga yadda take fama da Yaran."

"Ban haifa ba, amma bana jin zan yiwa Amirah irin rikon uwar wani, saboda Amirah tawa ce ni Waya na. Shi yasa nake sonta da dukkan zuciyata, kuma bana jin har abada wani zai fini son Amirah, koda kuwa uwarta ne, sai dai ta gaya min ita ta haifi Yarta amma ba zata gaya min soyayyar yarinyar ba. Daukarta nayi zuwa banWaki na mata wanka, sannan na sauya mata kaya, kafin na fito ni ma na nime ruwan zafi na zubawa cikina da yake cike, ina tsaye rike da kofin a jikin window."

"Saboda iskar da ake yi, nake tsaye a wurin. ""Ko wani hali Zuzu take ciki? Wani hali Munaisah take ciki ina suke yanzu?"""

"""Taya zan fara nimo su? Ina zan shiga ina zan fara nimansu?"" WaWannan sune manyan damuwata, ta ina zan nimo Yan uwana an samu shekara daya da wani abu kenan amma babu labarinsu. Jikina yaki amsar sun mutu yadda wani bangare na zuciyata take gayamin, nafi jin a jikina suna raye, a duk inda suke a fadin duniya sai na nimo su, ""Amma taya?"" Ajiye kofin hannuna nayi, kafin na cusa hannu a cikin sumar kaina. Taya zan nemo su? Ta ina zan fara? Babu shakka ina cikin damuwa. Allah ya kawo min mafita,. Amma dole na binciko yan uwana. *Mahaifiyarki fa?* Gabana ne ya fadi wanda yasa kofin hannuna faduwa niman wuri nayi na zauna, ina kallon duhun wajen. Mahaifiyata ya kamata na fara nemowa amma ta ina? Hawaye ne suka zubo min wanda ban san zan iya kukan ba, kuka nake sosai kamar raina zai fita domin ina cikin wani irin kewa, ina kewar Mahaifiyata sosai. Sai da nayi kuka me yawan gaske, sannan na mike zuwa ban daki nayi wanka nazo na kwanta a gefen Amirah."

*** Niamey

"Wannan sallah bata zo da alkhairi ba, lokacin da Majid ya saka bayanan da aka turo mishi akan Anisah, sai da jikinshi yayi sanyi. Duba agogon hannun shi yayi ya mike tare da Waukar keyn mota. Bai tsaya ba sai gidan Anisah, kiran mijinta yayi ya Wauka. ""Gani a kofar gidanka."""

"""Tow gani."" Can dai gashi ya zo ya buWe, cikin gidan suka shiga. ""Ina Anisah?"" ""Tana dakinta taki bude mana kofa da yara."""

"""Muje!"" Gaba mijinta yayi Majid yana bayanshi har kofar Wakinta. ""Anisah! Bude min kofar Abdul Majid Mamman Ba'are ne."""

"""Hammayo!"" Ta kira sunanshi da karfi, ""Na'am Autar Hajiya bude min na shigo."" Ya faWa da tausassshen murya. Kuka ta saka sosai, ""Ka tafi idan suka san kazo zasu cutar da kowa don Allah."" ""Babu wanda zasu cutar miki da shi, fito ina tare dake."" ""A'a Hamma!"" ""Bana ce ki yarda da ni ba, kin san halin da Amaan da Jamilah suke ciki kuwa? Tow kowani lokaci mutuwa zasu yi, Aryan ya farka dazun nan kin ga yanzu dare yayi. Bude min kofar don Allah."" Rufe bakinta tayi tana kuka kamar ranta zai fita."

"""Ki kunna wayarki, ki duba abin da yake faruwa. Idan har kika san baki da hannu a cikin wannan abin da ake fada tow ina jiranki A falonki."""

"Mikewa yayi ya bar kofar Wakinta ya dawo falon, a can dakin tayi kuka har ta godewa Allah, kunna wayar tayi tana ganin sakwannin mutane. *A yau muka samu labarin hatsarin da Yaran marigayi Mamman Ba'are suka yi, wanda aka ce daya daga cikin Yaran yake da hannu a cikinshi*"

"*An saki faife videon Amaan Mamman Ba'are wata majiya tace yar uwarshi tana da hannu wurin sakin faifen videon domin kada ya kalubalence ta akan mukamin shi da aka karba aka bata* sake wayar tayi da karfi, ta fito da gudu. ""Wallahi Hamma ban san kome ba, na rantse da Allah ban san kome ba."""

"""Nutsu ki gaya min me ya faru?"" Ya faWa yana kallon mijinta, da ya mike tare da nufar kitchen ya kawo mata ruwa. Amsa Majid yayi ya bude mata, domin ya lura a firgice take, sai da ya sha ruwan sannan ya mika mata, da sauri ta amsa ta sha dayawan gaske. Sannan ta sauke Ajiyar zuciya."

"""Mutuwar Babban sakataren kamfanin Alhaji Ahmed Ya'u, yana da nasaba da Sajjid Mamman Ba'are da Amaan, abin da ya faru a ranar da zai mutu. Amaan yaje Office din shi akan ya saka mishi hannu ya cire wani kudi ya turawa Sajjid yayi amfani da shi, amma Alhaji Ahmed Ya'u yaki, ya ce mishi ya je ya nimo amincewar hajiya ko Aryan ko kai."""

"Haka yasa suka yi sa'in'sa, har ya kira Aryan bai same shi ba."" Shiru tayi tana share hawayen da suke zubo"

"mata. ""Bayan nan abin da ya faru shine aikin da ya sha kan Alhaji Ahmed yasa bai tafi gida da wuri ba, har aka shiga aka kashe shi ga abinda na samu lokacin da nake binciken Office Win shi."" Wani dan karamin recorder, ta mi™awa Majid, tun da naji haka na sake saka idanu akan Amaan domin tun da aka bani matsayin nan yake turo min sakon na ajiye mukamina ko ya min rashin mutuncin. Da ya ishe ni ne na kunna mishi recorder din yaji da kunnen shi, ashe na kai kaina ga halaka domin Sajjid yaji labarin ina da shaidar abin da suka aikata."

"Tun daga wannan ranar ban kuma barci ba, da fari turo min sakon waya ake na za a kashe ni idan ban sake bawa Amaan bayanan ba, na ki kula su daga baya sai aka fara min barazana da Rayuwar Yarana da Mijina. BakiWaya na rasa me ke min dad'i."

"Bansan ya aka yi ba Aryan ya san da zancen ba, sai gashi dukkansu sun tawo suka ce min zasu tawo har da kai, ashe kafin su tawo Aryan ya kira Sajjid sun yi faWa har da sa'in'sa Hammayo shine suka turo mota biyu suka buge su. Sannan suka sake faifen videon Amaan, bayan sun tilasta min na kira Hajiya na gaya mata kun mutu. Wallahi Hammayo ba da gangan nayi ba, Hammayo Yarana suka ce zasu kashe kamar yadda suka buge su Aryan."

"""Me yasa baki gaya min ba?"" Inji Mijinta."

"""Su'ad ba zaka iya kome a kai ba, babban al'amari ne da mu kan mu, dole muke yakin sunkuru, lokaci yayi da zan ajiye aikina na soja, na tsaya akan Dangina. Idan ba haka ba, ina can za a shafe min yan uwa da dangi"""

"""Amma Majid""!"

"""Akwai jami'an tsaro, sun zagaye gidan nan babu wanda ya isa ya kuma muku abin da zai d'aga muku hankali. Yaranki kuwa ki kyale su, ba zasu iya miki kome ba. Idan ya kuma kiranki kice ni Abdul Majid Mamman Ba'are idan ya cika namiji ya kira ni."" A razane ta kalle shi, share mata hawayen fuskarta yayi yana murmushi ya ce. ""Eh ni na gaya miki haka."" Sannan ya mike tare da barin falon. ""Su'ad ka saka idanu a kanta, ka tabbatar tayi barci."""

"Daga haka ya musu sai da safe, ya fito ya samu sojoji a harabar gidan, ""ku saka idanu akan ko tsintsu ne, idan ya zo giftawa ku sake mishi wuta."""

"""Sir!"""

Barin gidan yayi.

"Hajiya Tani tana tsaka da barci, hasken da ya cika dakin yasa ta bude idanunta. Majid ta gani zaune, a razane ta mike tare da cewa. ""Uban me ya kawo ka."""

"""Ba kome sai dai kashedi nazo nayi miki, domin nasan zaki fi dauka sama da yadda kowa zai dauka, d'anki yana wasa da wuta, amma bai san wuta yake wasa da shi ba."" Zama yayi a bakin gadon. ""Ki ja mishi kunne, idan ya sake aka kama.shi ko tow a gidan Yari zai mutu, domin laifuffukan shi da yawa, sannan idan ya fahimci cewa Raihana ce ta haife shi ba Tani ba, akwai ."" Da sauri ta sauka akan gadon ta zube a kasa, ""Don Allah ka gaya min me kake so?"" Ta tambaye shi jikinta yana rawa. Mikewa yayi yana zaga dakin. ""Me zance miki nake so, ai yaci ace kin gane me nake so."""

"""In sha Allah ba zan kuma barin shi ya shiga cikin al'amarinkaba, ba iya kai ba hatta yan uwanka."" ""Tani kina da lissafi"""

"BakiWaya ta girgiza domin abu ne da bata kawo wani mahaluki zai san wacece ita ba, sai gashi an canko wacece ita. ""Ki kula kowane yana......."

"*Barka da sallah, ina jiran goran sallah na * 300¦ "

0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400

+2347035133148 or 08130269641.....

#Mai_Dambu ce

"[4/16, 8:16 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

"*Alhamdulillahi na gode sosai, marubuta da makaranta Allah ya saka da alkhairi, musamman yan grp din Fitilar"

"hikayar Dambuje, Allah ya bada lada naga kira da sakonnin ku. Allah ya karo dubun zumunci, Ubangiji ya jikan dukkan yan uwa musulmai da suke faWin duniya, tare da iyayenmu bakiWaya... Allahumma Amin*"

035

_Yau kan babu editing _

"Nad'e hannunshi yayi a kirji, yana kallonta yadda take gurfane a gabanshi. ""Ba xance kada ki hana shi ba, amma"

"tabbas nayi ido biyu da shi, sai dai Uwarshi ta kara haifar wani koda yake ina zao ganta. Amma ki saka idanu akan shi domin."" Sake hannunshi yayi ya nufi kofar fita yana faWin. ""Duk yadda kika so, kiyi amma inuwar Ba'are da al'ummar gidan kada na kuma ganinku."" Daga haka ya bar mata dakin da gidan bakidaya. Wani irin zufa ke karyo mata, yana fita da gudu ta mike ta Wauki goran ruwan da yake gefen gadonta, sai da ta shanye goran bakiWaya, sannan ta ajiye. Zirga zirga ta fara a cikin dakin tana jin kamar tayi ta kurma ihu, Hajiya Sa'a ta gaya mata magana akan haka, yanzu ma Majid ya kara gaya mata, haka yaná nufin sun san kome akanta, ita ce dai bata san kome akansu ba, wanda ta sani ma na bogi ne domin sune suka san wacece ita."

"Hannu ta saka a kai, kafin ta koma ta zauna tana jin kamar ta tattara yan abin da take da shi ta gudu,"

"domin zuwa yanzu da Majid yasan Sajjid ba dan Mamman ba'are ba ne, zai fi mata kyau tayi ta gudun hijira. Ai na Majid wasa ne akan na Sajjid don binne ta zai yi da ranta, matukar yaji wani labari mara daWi akan waye shi, cikinta ne yayi wani irin murdewa a daddafe ta shiga toilet. Bata san ya aka yi ba, sai g kashi shaaaa cikinta ya tsinke. Wato Majid bala'i ne, idan ta sake wani abu ya kara had'a su. Binne kanta zata yi da ranta kafin Majid ya zo gare ta, don na Majid me sauki."

"Koda ta fito daga ban dakin, a daddafe ta nime wuri ta zauna. Can cikin ya kuma murdeta, da sauri ta shiga banWakin ta zauna akan wurin kashin."

"A lokacin da ya bar gidan Tani, a hankali yake jin wani irin abu yana yawo a kanshi, har wani nutsuwa yake ji, Hajiya"

"Tani ba ita daya ba ce akwai wasu a bayanta. Bari ya ga iya gudun Tani domin idan akwai wani a bayanta dole zai fito, don haka ya tab'a spot point. Lokacin da ya isa asibitin Hajiya tana barci, zama yayi na wani lokaci kafin ya mike ya nufi Office Winshi, bude drowe office din yayi ya ciro abin sallah da jallabiya, murmushi yayi domin yasan aikin Jami'ah da Aryan ne, sune zasu nishi haka."

"Ban daki ya shiga yayi alola, ya fito ya shimfida abin sallah, tun ya fara sallah nan karfe uku bai tsaya ba sai da Masallacin asibitin aka kusan shiga sallah, ya sallame ya nufi masallaci. Bayan an idar da sallah ya zauna yana addu'a, sai da rana ta fito sannan ya wuce asibitin. Anan ya samu Anisah da Salamatu sun shigo. ""Hammayo!"" Ta kira sunanshi, bude mata gefen hannunshi yayi ta isa wurin tana kuka kamar ranta zai fita. ""Hamma kayi hakuri."" ""Shiiii!"" ""Duk laifina ne, da na fada maka haka da bai faru ba."" ""Ya isa haka, kin yi barci kuwa?"" Ya tambaye ta cikin kulawa, ""Nayi su'ad ya saka ni nayi barci."" Murmushi yayi ya ce mata. ""Good girl, muje ki bani abinci naci don naga basket a hannun Mama Salamatu."" Ya faWi haka don ya kwantar mata da hankali. Har dakin da Hajiya take suka shiga, ""ina zuwa ko"" ya faWa yana nufar dakinsu Aryan a can ya samu Matarshi tana ta kuka. ""Ya isa haka, ya farka fa bari na duba shi."" Ya faWa yana shiga dakin,duba shi yayi yaga lafiya lau barci yake, bai tashe shi ba ya nufi wurin Amaan, ya shafa kanshi tausayin shi ya masifar cika mishi zuciya, duk da rashin jituwa da yake tsakaninsu, haka bai tab'a damunshi ba, domin yasan wata rana zai gane gaskiya, duba karin wurin yayi yana me saka mishi wani ruwan. Sannan ya wuce kan Aryan da yake ta motsi. A hankali ya isa kanshi, ya cigaba da dube-dube har ya farka. ""Welcome back Mr Mamman Ba'are."" ""Anisah fa?"" Tab'e baki Majid yayi, sannan ya ce mishi.""Na zata matarka da Yaranka zaka tambaya."" ""Wani hali kanwata take ciki?"" ""Ina zan sani tunda ina tsaye akanku."" ""Hamma kasan bala'in da na gani jiya."" ""Ina zan sani ragon maza."" Ya faWa yana murmushi, d'ago shi yayi ya zauna. ""Hamma!"" ""Guduma!"" Ya faWa yana murmushi, don ya gaji da maganar Aryan. ""Hamma Abdul Majid."""

"""Anisah tana lafiya, wurin Hajiya matarka tana waje bari ta shigo."" Ajiyar zuciya ya sauke, ""Manyan mota biyu suka tasamu a gaba, Hamma dole na firgita."" ""Allah ya kiyayye na gaba."" Ya faWa yana ™ara duba shi. ""Ina ke maka ciwo yanzu?"" Ya tambaye. ""Hakarkarina ke ciwo."" Matsawa yayi ya d'aga mishi hannunshi, da sauri ya riko hannun Majid, ""Hamma bari kawai."" Sake hannun yayi yana dauki wani littafi yayi rubutu, sannan ya ce mishi. ""Motar ya doke ku ne?"" ""Tsakiyarsu suka saka mu, wallahi ban san yadda aka yi aka ciro mu a ciki ba."""

"""Anjima zaa zo a kaika x-ray, mu ga wurin "" inji Majid, juyawa Aryan yayi yana kallon Amaan, ""bai farka ba ko?"" Ya tambaye shi idanunshi cike da kwalla. ""Ba shi ne matsalata ba, Jamilah tana da ciki, kuma har yanzu bata farka ba."" Shiru ne ya gifta a dakin, dukkansu babu me kuzarin magana, fita yayi ya nufi ICU, inda aka kwantar da Jamilah. Yana shiga yaga yadda kome yake tafiya a cikin na'urar da aka saka mata, amma ya kasa tabuka kome dake ya samu wasu drs akanta, sai ya zama kamar dan kallo, haka ya juyo daga dakin ya gagara yin kome, a bakin kofar ya samu Mijinta, dasu Nanah."

"""Ya jikin nata?"" Kallon kayan jikinshi yayi kafin ya ce mata. ""Da sauki."" ""Kace anan kake zaune?"" ""Eh!"""

"""Ayya to dama ina babu wanda ya mutu?"" Banza ya bawa ajiyarta, ya cigaba da tafiya. ""Kai kurma ne ina magana kayi banza dani."" Uffan bai ce ba. "" Yau ga lalacewar duniya, kai yanzu ina magana kayi banza dani don kaga na tako inda kake? Yanzu don."""

"""Me kika ce ne?"" Ya juya yana me tambayarta da sigar renin hankali. ""Uwarka Sa'adatu da ta haifi Wan karuwi."" Murmushi yayi tare da cigaba da tafiya, tana kuwa bin shi, tana zagin shi. Sai kallonsu ake shi kuwa ko a jikinshi. Yana isa kofar office din shi ya ce mata. ""Idan kin gama jarabararki, na gode sai ko wuce gida domin na fito na same ki wallahi ni kaWai nasan me zan dirka miki a asibitin nan."" Ware idanu tayi tana faWin ""yanzu don baka da imani sai kayi min wani abu? Tambayarka nake sai kayi min wani abu!"""

"Hango wata nurse yayi ya ce mata. ""Ki kawo min babban sirinjin allura tare da maganin nan, yanzu."" ""Ke dan uwarki kika kawo wani abu, sai na saka an kore ki a asibitin nan, kafira me kama da fatalwa. Kai kuma zamu gamu da juna, mara mutunci dan banza me kama da gwaggon biri """

"Murmushi yayi ya rufe kofar shi, domin yasan Nana da dan banza tsoro, kuma bai zama dole ta kuma dawowa ba, murmushi yayi shi kaWai, har ya gama sauya kaya. Ya fito dakin Hajiya, ya samu ta farka sai kuka Anisah take Nana sai surutu take ta musu da sababi. Safar hannu ya saka tare da haWa kayan aikin ya cire ruwan daya kusan karewa, ya saka wani sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment