You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya tambaye ta, zubura baki tayi tare da zunden Zaytoonah da idanunta suka kawo kwalla, juya fulatanci yayi ya ce mata, ""shiga mota ki tafi zan ji da ita."". ""Wallahi wuta balbal ko kabarin mutum yana ci da wuta ba zan yafe ba, da zagin da aka min."" Wuce ta Zaytoonah tayi ta shiga motar, kafin Nana ta fahimci abinda suke nufi motar ta bar gidan, kallon Aryan tayi ba™i sake. ""Idan baka yi haka ba ai ba zaka tabbata ka sha nonon Fulani ba, kuma zan kira Alhajin Allah na gaya mishi domin nayi alkawarin bani cin amanarshi."""

"Garin masifa har madubinta ya fadi, dauka tayi tana faWin. ""Allah ya isa Annabin Allah ya isa, kuma duk wanda ya"

"sake ya likawa jikana bazawara ban yafe ba, Allah bai yafe ba, Annabin Allah bai yafe ba."" Ta dauki madubin ta saka shi a juye. Wayarta ta lalluba ta shiga dankara kira. ""Halo Alhajin Allah "" ""bashi bane Haladu ne Nana."" Kashe kiran tayi ta kuma lallubar wani number. ""Halo Alhajin Allah."" ""Nana Halima ce fa!"""

"""Yau naga tijara Alhajin Allah nake nima."" Ta kuma kashe kiran, ta wuce gidanta, tana kiran Driventa""Salele!"" Da sauri ya iso. ""Kira min Alhajin Allah."""

"Tunda ta fadi Alhajin Allah yasan Majid ne, don haka.ya kira mata shi ya mika mata wayar. ""Gashi nan Nana."" Karba tayi wayar ma a juye ta saka a kunnenta. ""Halo Alhajin Allah, kasan ba zan cuce ba kuma ba zan ci amanarka ba."""

"""Eh Nana!"""

"""Tow ga wannan doguwar yarinyar nan, me kama da fatalwa tana kawo maka abinci. Ban san me ta kawo maka ba, na dai gaya maka gaskiya a tow ba zan iya cin amana ba."""

"""Na gode Nana!"""

".... A asibitin kuwa tun kafin su isa, Nana ta fesa mishi zuwan Zaytoonah, don haka ya shige Office Winshi yana shiryawa domin tana zuwa zasu fita. Bayan son wani ya san akwai wacce take bibiyar shi yanzu a fara yayata shi. Lokacin da Zaytoonah ta iso ne take raba idanu, tana nimanshi. ""Yan mata!"" Ya kira sunan, juyawa tayi tana tura baki, ""cutie cutie pie zaka ce."" ""Ok muje!"" Ya amshi basket din Hannunta, ya mata jagora har dakin da aka kwantar da Jamilah, ""Hamma ya cikinta?"""

"""Lafiya lau, baby girl ce kin ga yadda take, girma kuwa."" Ya nuna mata wani computer da yake kula da cikin Jamilah."

"""Allah ya bata lafiya!"" ""Amin Ya Allah."" Daga nan suka nufo wurin Amaan , anan suka sha hira"

"kamar ba gobe, sai dare ya sakata a mota ta dawo gida."

"Bayan wata biyu, an sallame Amaan har lokacin Jamilah bata farka ba,abin har ya fara kashe jikin kowa, shima Majid"

"ba karamin matsanancin damuwa ya shiga ba. Haka yasa suka fara tunanin ko a fita da ita waje ne. A bangaren Zaytoonah kuwa an nima sama mata Makarantar Jinya a nan Niamey, inda ta fara da taimakon Nabeeha."

"Tun faruwar Al'amarin su Amaan ba a kara jin motsin ko Hajiya Tani, amma kuma sai dai lokaci zuwa lokaci ana samu abu marasa dadi da suke faruwa, a tsakanin Kamfaninsu da kuma wasu abubuwan. Hakan yasa Majid ya Wan fara bibiyar kamfanin da taimakon Aryan wanda ya amshi matsayin Anisah, suka koma bakin aiki gadan-gadan. Ya ajiye aikin asibiti idan ya dawo da dare sai ya leka asibitin. Duk da bai cewa Hajiya ya koma kamfani ba, sai dai haka ya mata dad'i domin addu'a da ta dad'e tana yi ne Allah ya amsa mata. Lokacin da bata zata ba kuma abin daWin aiki biyu yake dubawa ko bai je kamfani ba, yana asibiti kuma da alamu aikin asibitin yana so ne har cikin ranshi, shi yasa ya ke lekawa idan ya samu lokaci. Amma bakiWaya aikin bai da lokacin na asibitin."

"A binciken da yayi na kamfanin yasa, aka shiga sallamar mutane musamman masu aikin bangaren tattalin arzikin kamfanin, don ya gano har dasu a cikin masu yi musu zagon kasa, sannan suna cikin masu yayyata wasu abubuwan, haka yasa bakiWaya ya™i yarda da kowa, aka sallame wasu aka kuma d'ebi wasu, a bangaren Jamilah kuwa sosai likitocin suka tsaya akanta, har Allah ya d'aga kafadarta bayan wata biyu tana sume, ba karamin farinciki Hajiya tayi ba, don su Yafendo sun koma da Maman Zaytoonah, aka barta a nan Nijar, sannan a bangaren Zaytoonah ba karamin haukar son Majid take ba, su kansu yan uwanshi, sun bata goyan baya, sannan haka yasa take shige mishi. Sai dai kamar yadda ya gayawa Hajiya gaskiya duk da bai fito ya ce yana da zabin ranshi ba, amma ya ce mata shi a kanwa ya dauke ta, ba a macen da zai aura ba. Shima din sai da a bakin Aryan da Amaan suka gayawa Hajiya, domin haka ya faru ne ranar babban sallah suna aikin Nama, ta kawo musu gasashen namar da ta gasa, don ana yankar ta tsaya akan Aryan ya diba mata, ta kawo kitchen tayi mishi denderu. Ta kai mishi koda ya amsa ce mata yayi. ""Ya Allah ya bawa Zaytoon miji na gari."" Hararanshi tayi tana tura baki, ta ce mishi. ""Mimi bata da dady sai kai."" ""Eh dama ai ni ne dadynta."" Murmushi tayi ta wuce, ""Hamma yarinyar nan tana sonka, me kake nufi da Allah ya bata miji na gari."""

"Tab'e baki yayi yana faWin. ""Ita dasu Anisah kallo daya nake musu, bana ajiyeta a tsarin matan da aka halitta daga hakarkarina."""

"""Abdul kana nufin cewa."" Lumshe idanunshi yayi ya bude akan wayarshi, da Umaima take kira, kashe kiran yayi ya kirata da kan shi. ""Barka da sallah ya kike?"" ""Abdul Majid Mamman Ba'are!"" Yarrr tsigar jikinshi ya mike, ya amsa a sanyayye. ""Na'am Umaima minjibir."" Ya amsa yana jiran yaji me zata ce. ""A gida a can na fitar da miji, ni kuma ban ga wanda ya dace da ni ba sai, please Majid kada ka yi rejected dina."" Iska ya ja yana jin shashekar kukanta. ""Kiyi hakuri, Allah ya ba™i wanda ya fini, amma babu aure a lissafina."""

"""Please Majid, kazo gidan mu ka gaya musu zai aure ni amma ba yanzu ba, wallahi zan jiraka."" Ta fada tana kuka,"

"""A'a ba zan yaudari kowa ba, ni namiji ne da zan amsa suna a ko ina namiji, ba zan yaudari yar kowa ba balle har akai Allah ya kama ni. Ni ba Basimpe ba ne Salle na yaudare ki, kiyi hakuri nasan akwai waWanda suke sonki baki basu fuska ba ne, kuma zasu fini sonki."""

"""Majid wallahi kai kaWai nake so, don Allah kada ka min haka, idan ma Zahra kake jira ta mutu."""

"""Zahrah!"" Ya ambata a hankali, kafin ya sake murmushi yana faWin. ""Ni ban santa ba, abin da na sani na gaya miki gaskiya babu shirin aure a tsarina. Idan zaki yi hakuri kiyi hakuri. Akwai wanda na san shi jiranki yake kuma zai rike ki da Amana da gaskiya amma ni idan na aure ki, zan miki rashin adalci."""

"""Majid ka gaya min baka sona."""

"""Idan na boye miki, ai babu armashi shi yasa nake gaya miki gaskiya kawai a wuce wurin."""

"""Allah ya isa rejected dina da kayi, in sha Allah sai kasha wahalar so kamar yadda nake sha akanka, kuma ba zaka tab'a haduwa da Zahrah ba har abada."" Murmushi yayi yana kara rarrashinta, ita kuwa sai zaginshi take yi, amma shi murmushi yake yana bata hakuri, nuna mata muhimmancin hakurin dai da zata yi, ta samu wanda yake sonta ba wanda take so ba, ba karamin rigima tayi mishi ba, shi kuwa bai fasa rarrashinta ba. ""Majid me kake boye min? Yarinyar da ka kwanta da ita a asibiti kake tunanin zata dawo gare ka?"""

"""Umaima! Ina son ki gane cewa ni babu wani shauki a raina. Sannan bana jin akwai bukatar haka. Mace hmm ba a haifi matar Majid ba."" Wani uban ihu ta saka tana faWin. ""Karya ne Majid, karya kake wallahi yarinyar nan ita ce a ranka. Idan ita ce Majid ka kwallafa rai akanta, baka mana adalci ba wallahi."" Shafa yar kasumbar shi yayi yana faWin. ""Ko daya yarinyar da ban san yanayin fuskarta ya yake ba? Yarinyar da ko cikin dubu na ganta ba zan gane ta ba."""

"""Jininka ne a jikinta, zaka gane ta wata rana idan tana raye, amma yarinyar nan bata min adalci ba."""

"Dakyar ya rabu da ita, Amaan ya zuba mata idanu, shi kan Aryan bai yi mamaki ba domin kuwa ya sha jin yana waya tare da cewa. A bincika mishi sansanin gudun hijira, ko za a dace. Amma shiru sanin cewa baya son magana kuma.idan ka tambaye shi bai zama dole ya baka amsa ba, yasa shi jan bakinshi yayi shiru. ""Kai mata suna da matsala haka masu yan mata suke fama."""

"""Kai dai ka ji dadinka munafuki, kana da wacce take binka tana sonka amma dake kayi zubi da munafukai kayi shiru ka bar, Zaytoon tana wahala wacce me karfin ikon ce ta shammaci zuciyarka."""

"""Ba a haife ta ba."" Inji Aryan yana kunshe dariyarshi. ""Lokacin sai kuyi niman budurwa daya da Affan ko?"" Dan gidan Aryan inji Amaan. Mur yasha kamar bashi ba, domin bai cika son su tasa shi gaba da tsokana ba, don haka ya haWe rai ya cigaba da aiki, tun daga wannan ranar bai kuma ce musu kala ba, sai da Hajiya ta tuntube su akan lamarin Zaytoonah da Majid din ne suke gaya mata yadda suka yi da shi, karshe bata sare ba har daki ta same shi yana aiki a can kuryan dakinshi inda aka saka table da kome da kome, ta ja stool ta zauna tana kallon shi. Tunda yaga yadda take mishi kallon tuhuma yasan Hajiya yau no mercy. ""Umaimah Ashe ta kira ka akan ka aure ta kaki?"" ""Hajiya idan na ajiye mace zata bukaci abubuwa dayawa, babu wacce zata fahimci yadda nake ji idan ba wacce take da sanin yadda rayu take ba."""

"""Majid yaushe ka fara magana."" Shiru yayi bai ce mata kome ba, ""Majid ban yarda da kai ba, ka ajiye maganar baka da lafiya ni nasan lafiyarka lau, aure nake son naka yi """

"Shiru yayi bai ce mata cikanki ba, balle har ta yi tsammanin zai bata amsa. Ta cigaba da fada kamar zata mare shi. ""Na rantse da Allah, ka fitar da mace ko ni nayi nawa ikon akanka......."

300¦

0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400 07035133148

#Mai_Dambu ce

"[4/20, 9:07 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*038*

"* Kawayen Tani ina gaisuwa, Kawata Ambassador tare da Mamarsu Anam da Anum, da kanwata Labilah Lalan Mummy How market dole gayen nan yayi aure ko muyi mishi forcing marriage *"

"Yadda take ta fada har Amaan da yake falon kasa sai da ya hauro sama, ya ga yadda take fada Majid din bai ce"

"mata kome ba, amma ya kasa ci-gaba da aikinshi kanshi a sunkuye, haka yasa Amaan yayi maza ya riko hannunta"

"yana faWin. ""Me yasa ba zaki mishi addu'a ba? Me yasa kike wargaza aikinki akan mu? Me yasa ba zaki yi hakuri ki ta"

"nima mishi zabin alkhairi ba? Hajiya Maisarah cewa tayi tana son Majid aka kashe ta har lahira, gaya min yar waye zaki janyo cikin wannan tashin hankalin? Gaya min waye zai bawa Majid yar shi bayan ansan gidan nan akan mallakarka ma niman rayuwarka ake, Hajiya ya isa haka, idan Majid yana da lafiya lokaci ne zai gwada mana haka, idan bai da lafiya lokaci ne zai gwada mana, so kike su kashe shi da bakinciki idan aka san bai da lafiyar da zai rike mace, Haba Hajiya haba haba Hajiya. Gaggawar ta meye ne? Lokaci yana zuwa da Majid zai ajiye mace har da Yara don Allah ki shafawa ranki ruwan sanyi idan ba so kike zuciyarki ta samu matsala ba """

"A wannan lokacin ba karamar damuwa Majid ya shiga ba, shi yasa da ya samu damar kasuwanci a kasar Poland bai yi wasa da damar ba, haka ya dauki kome na shi ya tafi, da taimakon Amaan wanda suka tafi tare ya samu yaga likitan da ya daura shi akan Magani, domin Amaan ya mishi hanya, shege Amaan tunda ya ga ya kusan mutuwa, ya koma jikin yan uwanshi, sannan har kwanan gobe babu wanda ya ce mishi me ya faru a baya, domin sun san ™addara kuma zata iya fadawa kan kowa. Hajiya ba son shi ba ne don Allah ki sassauta mishi, Hajiya ni da nayi auren ba haduwa nayi da makirar mace ba, yaran da nake alfaharin nawa ne ba Yarana ba ne, Yaran Sajjid ne Hajiya me ya fi haka Muni? Hajiya Aure lokaci ne idan har Allah bai nufa zai yi yanzu ba, duk abinda zaki yi ba zai yi ba, don haka Hajiya ki kyale shi ya jira lokacinsa yayi."

"Kowane mutum da iyakar ™addarar shi, shi nashi ™addarar da sauran ta. """

"Mikewa Majid yayi ya dauki kayan zuwa asibitin shi ya bar dakin. ""Ka gani ba, wai yayi fushi."" ""Da bai tattara ya gudu ya bar kasar ba, shi ne zamu ce da sauki."" Zama tayi bakin gadon Majid Win. ""Kana nufin sai ya gudu?"" ""Tsaf sai ya gudu tunda kin ce auren dole zaki mishi."""

"""Kai Amaan ni sa'arka ce da xaka ce zai gudu don zan mishi auren dole."" ""Wallahi Hajiya idan da can baya ne tafiyar shi zai yi """

"Shiru tayi bata kuma magana ba, ta mike suka fita, ""Amaan ka saka idanu akan shi kaji don Allah kada ya gudu."" ""Bayan ya ajiye aikin sojan zai gudu ina? Babu inda zai je kawai ya tafi asibiti ne."" Hajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sauki a ranta ba ta kuma yarda tayi zancen auren ba, gudun kada ya fece."

"Ashe shi kan Majid ba asibiti ya wuce ba, gidan Nana ya wuce a can ya kwana. Domin baya jin zai ji dadi ranshi, shi yasa ya dawo gidan, yana shiga falon Nana ya hadu da Afiyyah. Sakin baki tayi don bata zaci zai zo gidan ba, sannan wani abin da ya kara rud'ata yadda take zaune daga ita sai bom short da yar shimi, haka mutumin nan ya wuce ta bai d'aga idanu ya kalli inda take ba, ya wuce dakin Nana kai tsaye. ""Ke bana ce ki tafi gidanku ba, sai ki tawo nan domin zuwa yawon darenki, ki hana ni barci ina zaman lafiya ta, ki fita kafin nazo na maka miki sanda."""

"""Ba ita ba ce"" ya faWa yana nufar daya daga cikin kujerun hutun Wakinta ya zauna, ya cire agogon hannun shi, ya kalle ta. ""Bani pillow dinki Waya."" Tashi tayi jikinta yana rawa ta mika mishi, sannan ta dawo ta dauki bargo, ta ajiye mishi tsantsar mamaki ya hana ta magana. bude botiran rigar shi yayi ya kwanta. Yana sauke ajiyar zuciya, don har zuwa lokacin zuciyarshi zafi take mishi."

"A nan ya bar Nana baki sake, bai yi barci da wuri ba, domin maganar da Nana take yi ita da Afiyyah da ta ce"

"ta bar mata gida ko ta gayawa Majid din yawon ta zubar take fita. Haka yasa ya fahimci yarinyar tana zuwa wurin Nana da sunan kwana amma yawonta take zuwa, yanzu haka file din yarinyar yana office Winshi akan za a dauke ta aiki, amma bai saka hannu ba, asuban fari Nana ta farka ta hango shi kan Abin sallah. ""Lallai Alhajin Allah da kokari kake, ahto wani shegen ya isa cutar ka, bayan Allah da Mala'ikun da suke tare da kai, yana idar da nafilla aka kira sallar asuba, ya tafi masallaci. Daga nan da aka idar da sallah, ya juya cikin gidansu, a falon kasa ya samu Hajiya tana zaune, ta kafe kofar gidan da idanu, tasan bai tafi asibiti ba tunda keyn Motarshi na falo, haka yasa hankalinta yaki kwanciya bata samu barci ba, idanuwanta sun yi jawur. Zama yayi a kujerar kusa da ita ya ce mata. ""Ina kwana Hajiya."" ""Sannu Majid. A ina ka kwana?"" Kafin yayi Magana Aryan ya ce mata. ""Hajiya don Allah me yasa kike haka ne? Tun jiya kin hana kowa barci Bayan kece kika fara tado abin da yasa shi barin gidan don Allah Hajiya ki yi hakuri mana."""

"""Ba zan yi ba, nace ba zan yi hakurin ba."""

"""Kyale ta, ai dama tunda naga Alhajin Allah yazo wurina ya kwana na kwana da sanin akwai dalili, yanzu ma na ga bai dawo ba nace bari na biyo sahu , ashe masifarki ce ta motsa kika hana shi barci, anya Sa'adatu? Wallahi kika sake wani abu ya same jikana kotun duniya ce zata raba bani da ke, haba don Allah duk abin da yaron nan yake bakya gani, tow kashe shi ki huta idan ya mutu kece da asara, ina cewa barin aikin shi yayi don ya tsayawa dan daudunki shine kike niman hallaka min jika wallahi baki isa ba, sai kotu ta raba ni dake Sa'adatu domin ba zan kara ganin wani gawar ba."""

"Ganin yadda Nana take shiga ba nan take fita ba, anan take gayamata . Ai ga abinda Alhaji"

"Haladu ya ce akan yarshi Afiyyah amma ita tana tare da Alhajin Allah duk abin da yake so shi take so, ba zata mishi"

"dole ba, duk son Hajiya da yayi aure, jin Afiyyah za a nemi haWasu tuni tayi saranda ta ce ita ta yafe auren Allah ya"

"bashi mace ta gari. Haka yasa Majid ya samu ™warya kwaryar zaman lafiya da Hajiya, don Nana tana tare da shi. Bai san me ya sauya Nana ba, amma a zahirin gaskiya baya tunanin bindigarshi ce tayi tasiri. Tashi yayi ya haura dakinshi ya shirya ya fito cikin wani American suit Navy colour, don yau ya tuna da bakin daga ne, ya fito sanye da farin glass, yayi mishi kyau, duba agogon falon yayi yaga karfe takwas saura, an kawo abin karyawa daga gidan Aryan, ga wanda Zaytoonah ta haWa musu, zama yayi ganin an bazawa Nana tana ci, ya zauna kusa da ita ya fara ci a cikin nata, dake Allah ya taimaka Nana tana da tsafta, idan ka cire abin da tayi mace ce me matukar tsafta da gyaran jiki,"

"Murmushi tayi tana ci da shi, ""Hamma kai zaka ajiye ni yau a makaranta don Allah."" Ta fada tana mi™ewa, ""Salele"

"zai kai ki, ni bana son gulma haba don Allah idan ba munafurci ba, taya za'ayi ki maida min jika direba, idan ba munafurci aka hada don a cuce min shi ba."" ""Nana kanwata ce fa."" ""Hmmm! Na dai ji wannan."" Da gangan Nana ta hana shi tashi, sai zai mike ta kawo mishi wani labari mara kan gado, ita nan don kada ya dauki Zaytoonah. Karshe Aryan yana shigowa Zaytoonah ta mike. ""Hamma Aryan muje ka ajiye ni school."" Ta fada fuskarta a had'e, ""oho dai sai dai ariyan din ya kai ki, amma ban da jikallena ba."" Don bakinciki sai da Zaytoon ta ji kwalla yana zubo mata, a gurguje Aryan ya sallami Hajiya da take kallon rigimar Nana da Zaytoonah. ""Nana me yasa kike mata haka?"" Ya tambayeta. ""Haka kawai zata mai da kai bawanta."" Ta fada tana zumburo baki , ""Nana ai duk namiji bawan mace ce, matukar ya san ciwon kanshi. Koda bai bautawa Matarshi ba, dole zai bautawa kanwarshi da Yarshi, Nana Zaytoonah marainiya ce, sannan ta baro Cameroon tazo nan domin mu, ina ga ita ai kamar jikarki ce."""

"""Ni ba jikata ba ce."" Ta faWa tana wani b'ata rai. ""Na ji ba jikarki ba ce, shi kenan ki daina ci mata fuska akan idanuna, na roke ki."""

"""Haba Alhajin Allah, sai ka roke ni ne? Kawai kace min Nana ki daina sai na daina, meye a cikin idanu banda ruwa."" Daga haka ya kashe bakin Nana, daga nan ya mike ya musu sai ya dawo."

"

"Hidimar kasuwancin ne ya kai su, har Poland don ba karamin ci-gaba za a samu ba, don haka sai yayi amfani da"

"wannan damar tare da ganin likita, wanda yayi nasarar gano matsalarshi, sannan ya Waura shi akan magani. Kwanakin shi goma sha daya, gobara ta kama wani part na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES."

"

Zahrah Buba.

"Karatun da ya sako ni gaba, yasa bani da lokacin kowa sai na kaina. Sai wani dan ajinmu me suna Sauban yana da matukar kirki. Yau ma daga dakin karatu muka fito, ya ce min. ""Fatimah zaki iya tafiya don ni zan shiga cikin makaranta, kuma kin ga yamma tayi."""

"""Haka ne, sai gobe kawai."" Anan muka yi sallama na wuce gida, a bakin get din makaranta na hadu da wasu yan department Winmu, dauke kai nayi domin daya daga cikinsu mai suna Abdullahi ya saka min idanu, Abdullahi yana masters ne amma irin yaran nan ne marasa jin magana, a bakin Sauban nake jin babanshi mai kudine kuma dan siyasa ne, haka yasa yake yadda yake so, duk da wannan abin bai taSa burge ni ba, domin ni karatu ya kawo ni ba shashancin ba, kodon na cikawa Yazid alkawarin shi,zan tsaya nayi karatu."

"Har na tsayar da abin hawa, iskanci da rainin hankali Abdullahi yake min, ina shiga na sauke ajiyar zuciya. Ina jin wani abu yana sauka a raina, don ba ™aramin abu ba ne, Abdullahi ya kunyata mace a gaban jama'a. Haka yasa Sauban ya gaya min nayi a hankali da shi. Sannan ganin yadda ake shakkarshi yasa shi jin shi wani jan wuya ne."

"Mun hadu ne ana sallah layya saura kwana biyar lokacin da aka bada hutu, ranar da mota na shiga makarantar,"

"nazo zan fita kawai ya tare hanya, kuma ya hana kowa fita, haka muka zauna a cikin makaranta har sai da Den na makarantar ta fito da kanta, shine ya bada hanya amma tabbas bamu ji da dadi ba, domin bai da mutunci. Haka yasa yana bada hanya muka fita, ina cikin waWanda suka fita da mugun gudu, tow ko me ya gani ya ke bibiyar rayuwata oho, ya dai turo min wani yaro na bawa Yaron hakuri akan cewa ni matar aure ce, mijina yana nan. Amma mutumin nan bai kyale ni ba, sai ma kara adabbar rayuwata yake, don ko da aka dawo hutun sallah, bai daina bibiyata ba. Zuwa yanzu kan sai hamdala kome yana zuwa min Cikin sauki da nasara. Bayan ya turo yaron sai da ya kuma tare Sauban da maganar banza, haka yasa Sauban ya gaya min abin da yake nufi, shi damuwar shi na zama budurwar shi na wucin gadi, sai kace wacce bata san ciwon kanta ba, don Allah ya zanyi?...."

*Kuyi hakuri muna fama da rashin wuta. *

300¦

"0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400, 07035133148"

#Mai_Dambu ce

"[4/21, 7:33 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*039*

*Wannan shafin domin ki Maman Husnah *

"Ban yarda nayi wani abun da zai janyo shi jikina ba, domin kuwa cikin shigar kamala da mutunci nake, sannan a"

"yadda nake jin labarin abin da ya faru a

Please Login or Register in order to submit comment