You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isa domin ya sani, amma yaki faWa kuma yasan ana niman sajjid Win. Lokacin"

"da ya shiga cikin gidan, Sajjid yana tare da wasu mutane. Amma koda Amaan din ya isa zubewa yayi akan gwiwarshi, a gaban Sajjid din. Dariya suka saka tare da kallon yadda yake durkushe a gabansu. ""Don Allah ka rufa min asiri, ka gaya min duk abinda kake so."""

"Kallonshi Sajjid yayi yana juya kofin wine na hannun shi. ""Bana bukatar kome, ya cikin naka?"" Kamar ya fashe da kuka ya ce mishi. ""Da sauki."", ""Ka wuce zuwa asibiti duk abinda aka rubuta ka gaya min."""

"Kasa yayi da kai yana kallon kasa, kafin ya ce. ""Idan na tafi asibiti za a iya ganina, sannan mutane zasu ta yawo damu. Ina son fita Najeriya ne naga likita a can."" ""Shi kenan jeka!"" Girgza kai yayi yana faWin. ""Ba zan iya zuwa ba, sai da yardarka da izininka zan tafi."""

"Tashi Sajjid yayi ya nufi inda Amaan yake zaune, shima ya zauna yana kurbar wine din shi ya ce masa. ""Idan haka ne kafin ka tafi asibiti bakidayanmu sai mun more ka."" A razane Amaan ya zame zaune daga durkushen da yake, ya zubawa Sajjid idanu. ""Wallahi idan kuka min zan sha wahala, don Allah ka rufa min asiri."" Tab'e baki Sajjid yayi yana faWin. ""Idan kana tsammanin zaka sha ne, tashi ka je amma ka tanadi amsar da zaka bawa danginka da press!"" Ya fada yana d'aga kafadarshi. Wani abu ne ya tsayawa Amaan a rai, ya kasa cewa Uffan domin Sajjid ya kashe shi. ""Na gaya maka bani da lafiya, da ace ina da lafiya da zan maka yadda kake so, amma yanzu bani da lafiya."""

"""Tashi ka tafi dan uwarka, maza fita min a gida dan shegiya!"" Kasa motsawa yayi yana zaune a wurin, Sajjid ya cigaba da zagin shi, karshe da yaji haushi daukar kwalba yayi ya wurgawa Amaan a goshinsa sai da ya fasa mishi goshi, duk da haka Amaan bai motsa ba, yana durkushe a wurin, ""ka fita min a gida kafin na kashe dan iska irinka."" A hankali Amaan ya mike yana dafe da goshinsa ya fita, yana shiga motarshi ya saka tissues yana goge jinin. Haka ya gama ya fita sai da ya bar unguwar ya kifa kanshi a kan sitiyerin motar, ya saki wata irin ajiyar zuciya. Bai san makomarshi ba, matukar Sajjid ya saki videon da yake kokarin sakewa bai san yadda zai fuskanci Hajiya ba, ciwon cikin ne ya murde shi, taka motar yayi da gudun bala'i."

"Bayan fitar shi, daya daga cikin mutanen Sajjid ya ce mishi. ""Me yasa ka kyale shi."" Murmushi yayi yana me busa sigari hayaki na tashi sama. ""Ina da shiri ne, ka tab'a ganin yadda aka jefi tsuntsu uku da dutse daya?"" Girgiza kai suka yi, ya saki murmushi yadda yayi mishi, ""ina kan shiri na, kuma ina shirya abin da zai min kyau ne, idan har nayi nasara sauke da tsuntsaye uku lokaci guda bana jin duniya zata waiwaye ni, domin kuwa na shirya tsaf."" Ya fada yana kurbar wine din. ""Bamu fahimci abinda kake nufi ba."""

"""Zaku fahimta amma yanzu ku fara kai mana, mutanen mu ma'aikatan yadda suna shiga cikin aikinmu zai tafi daidai"

"da lissafinmu."""

"""Ban gane me kake nufi ba!"" Inji daya mutumin. Gyara zama Sajjid yayi sannan ya dauko abin"

"wasan chased ya saka yan statue din guda uku, sannan ya ce musu. ""Kamar haka nake nufi."" ""Au min fahimta yanzu."""

"""Bayan nan akwai abin da nake so ya gaya min. "" Ya fada yana murmushi, ""idan ya gaya min dole na saka kome akan inda ya dace, domin ina son bazata."""

"""Amma kai shege ne, yawwa ya batun dila ne? Kwaro ya kawo mana manyan kaya, kuma kayan nan har mun wuce da su. Scotland da France."""

"""Hmm! Haka Julie take gaya min, Kwaro bai tab'a kawo kaya masu kyan wanan kayan ba, musamman na bayan yafi kowanne kyau. Gaskiya labarin ya min dad'i."""

"Lashe baki daya mutumin yayi, yana faWin. ""kuma abin dad'i, irin wanda Mr Williams yake so, ya turo kuWin aka ce, naso da an bani kayan na gyara kaina kafin a saka kasuwa, karshe duniya ce zata fara morar kayan kafin kai ka samu ragowar yan iska."""

***

"Wasu takardun da Aryan ya kaiwa Hajiya take dubawa, hankalinta ya tafi sosai ga takardun aka yi sallama, sai da ya kara yi a karo na biyu Hajiya ta amsa tana faWin .""Barka da shigowa Alhaji kai ne da kanka?"" Zama Alhaji Haladu yayi yana kallon takardun gabanta, ya saki murmushi yana ce mata. ""Duk da kin sauka, har yanzu baki huta ba?"""

"""A'a ina duba abubuwa masu muhimmanci ne, sannan sauka nayi ba barin aikin nayi ba. A matsayin Uwa nake taya shi aiki sannan yana da damar ya bani aiki a kamfanin domin na kara taya shi da wasu abubuwan."""

"""Gaskiya ne amma kuma ai kin wuce lokacin da."" Kara kallonshi tayi kafin ta ce mishi. ""Na wuce lokacin me?"" Dariyar renin hankali yayi ya ce mata. ""haba yaushe zaki daina goya su?"""

"Zare medical glass Winta tayi tana murmushi. ""Idan ban goya su ba wa zan goya? Wa nake da shi da zan goya idan basu ba? Sune dole na, kuma karfina sune suka sani tsayawa da kafaffuna idan ban tsaya musu ba, gaya min waye zan tsayawa?"""

Gyad'a kai yayi yana faWin .

"""Tow Allah ya kyauta, tunda kin mai dasu rauninki."" Gyara zama tayi ta ce mishi. ""Su ba raunina ba ne, nice nan rauninsu domin tari kawai zan yi su dakatar da abinda yake ransu."" ""Au tow kice babu wanda ya isa ya tab'a ki, ba tare da sun matsa ba."" Ranta ne ya fara b'aci. ""Idan babu abin arzikin da ya kawo ka, zaka iya tafiya ina da abin yi."""

"""Tow Allah ya huci zuciyarki don naga ranki ya fara b'aci dama na kawo takardun Afiyyah ce."" Gyara zama tayi tana faWin. ""Au ashe bani Waya bace nake son Yaran? Kenan idan har haka ne tow wallahi ka sake gaya min sai na sab'a maka, ko dan uwanka aure ya bashi damar tozartani ba wai don ya isa ba, kuma ko yanzu ba za a sake maimaita abin da ya faru ba, don haka ka sami Amaan Mamman Ba'are, shine yake da alhakin daukar ma'aikata ba ni ko Aryan ko Aneesah ba."""

"Shiru yayi yana kallon yadda ta maida hankalinta kan aikin gabanta, ""tow babu yar wata alfarmar da zan samu ne?"" Juyawa tayi ta kalle shi, ""ok ajiye a can"" ta nuna mishi inda ya dace ya ajiye takardun, ta cigaba da aikinta. ""Mun gode Allah ya saka da alkhairi."" Ya fada mata, bata amsa ba illa aikin da yake gabanta da take yi, kuma ai tasan yana zaune."

"""Sa'adatu baki da burin aure ne? Da sauranki har yanzu idan har mutum ya nutsu zai dauka Majid da Amaan da yan uwansu kannenki ne, sannan a wannan lokacin da kike da sauran kuruciyarki aure ya dace dake ba wani abu ba."""

"""Idan ka gama bayaninka, zaka iya tafiya."" Ta ce mishi tana cigaba da aikinta. ""Ina dai kara tuna miki, zama haka ba naki ba ne idan da hali ki bawa wani dama ya goge miki tabon da Mamman ba'are ya miki."""

"Murmushin da bai kai zuci ba, tayi tana faWin. ""Kuma da yake an gaya maka namiji ne a gabana ko? Idan har wannan tunanin shine a ranka tow ka cire ni bana tunanin wani namiji, don Allah tashi ka fita."" Mikewa yayi yana murmushi. ""Nasan zaki so kiyi tunani ina jiran duk abinda kika yanke."""

"""Kana son naci mutincinka ne? Ka fita ka bar min gidana."" Ta fada a fusace, shigowar Amaan bai hana shi magana ba. ""Kina da sauran damarki, a matsayinki na mace mai lafiya da jini a jika don haka ina kara baki shawara ki yi tunani da kyau. A shirye nake na wanke miki zuciyarki."" Cikin wani irin fushi Amaan ya cakumi wuyarshi. ""Wallahi sai na karya wuyarka, kai na rantse ka kara cewa kana son Hajiya, sai na kashe ka."" Ya janyo shi kiiiiii kamar kayan wanki, ya watsa a waje yana faWin. ""Na rantse Hajiya ta fi ™arfinka na sake ganin, kiraren sawunka sai na ballaka."""

"Ya fada yana hayagaga, Amaan kishi yake taya Ubanshi. Domin baya kaunar Hajiya ta kebe da wani. Musamman lokacin da ta amshi kamfanin idan tayi ba™i masu saka hannun jari, tow bake-bake yake zuwa yayi yana kallon ko zata mika musu hannu su gaisa, duk da mugun halinshi yana matukar kishin Ubanshi sannan abinda ya faru a"

"kuruciyarsu da Hajiya yana nan a memory din shi bai manta ba, haka yasa baki daya yake kara jin haushin ganin"

"Hajiya da wani namiji, domin bayan faruwar lamarin abin da wasu suke ta faWa yasa shi cikin rud'ani haka yasa wani lokaci yake ganin, yunwa da wahala.yasa Hajiya aikata wancan abin. ""Kai meye haka?"" Hajiya ta tambaye shi tana watsa mishi harara. ""Hajiya cewa yayi fa."""

"""Sai me? Zama zan tayi? Ba zan yi aure ba kenan?"" Ware idanu yayi cike da takaici. ""Aure kamar ya? Fisabilillahi Hajiya da tsufarki, ki ce aure zaki yi? Ke Hajiya haka ya dace dake?"""

"Sakin baki tayi tana kallon shi cikin mamaki da takaici. ""Kasan ni ba mutum ba ce da zaka ce aure xan yi. Sannu isasshe jikan mallaka'u, aure zanyi kuma na gaya maka idan kaso kada na ™ara ganin kafarka a gidana."""

"""Wallahi kika yi aure sai na kashe shi, haka kawai don janyo mana abin kunya da magana kice aure zaki yi, Hajiya idan kin manta abinda ya faru wallahi ban manta ba, ba zaki tab'a aure ba, domin cin amana ne, taya zaki..."" Kura mishi idanu tayi tana son jin me zai ce. ""ban fahimce ka ba, meye na manta da ku baku manta ba?"" Hadiye yawu yayi ganin yadda ta kura mishi idanu. ""Babu kome."" ""Da kome mana, Amaan idan da babu kome mai zai kawo wancan maganar, shi yasa kake min rashin kunya da fitsara? Akan wancan abin da ya faru kake had'a kai da mutanen da suke bi na da sharri."""

"Murmushi tayi mai sauti tana kallon yadda yake zufa, ga goshinsa da ya sha bandegi. ""Kada ka damu, su din zasu maka abin da na kasa maka, amma ka sani duk lokacin da ta kwabe maka bana fatan haka , amma a lokacin zan iya barrata kaina da kai har abada. Ga takardu can ka dauka na Afiyyah zata yi aiki a kamfanin mu."""

"""Hmm!"" Ya fada yana jin wani irin ciwon ciki, da tsoron abin da zai je ya dawo tabbas idan hakan ta faru kwananshi ya ™are. Da sauri ya haura sama da gudu dakin Majid Mamman Ba'are ya wuce da sauri ya faWa ban daki, sai da ya katsiye abinda yake cikinshi, ga wani irin ciwon cikin da yake damunshi wanda ya saka shi kasa gane kanshi. Dakyar ya daure wandon shi ya fito yana nishi, koda ya sauko kasa, takardun ya dauka ya fita bai cewa Hajiya kome ba. Itama tana son yi mishi magana amma da yake ya bata haushi sai tayi banza da shi."

"Dakyar ya bar gidan Hajiya, don dole ya nufi wani kanti, ya sayi wasu bakaken kaya yasaka. Sannan ya nufi"

"wani asibiti. Dakyar yaga likitan, a lokacin wani sabon ciwon cikin ya kara turnike shi kamar zai mutu, haka likitan ya mishi scanning. Yana ganin yadda sperm ya dankare a cikin wurin kashinsa, shi yasa yake jin ciwon ciki."

"""Alhaji wannan abin da nake gani, matukar aka cigaba da yin shi zai haifar maka da Cancer cikin makasayarka, sannan idan ma baka yi fama da Cancer ba, karshe zai zama tsutsa ya cinye maka duburanka, idan da hali tunda Allah ya ce kada ayi shi haramun ne, tow a barshi wannan shine nasihar da zan maka."""

Idanunshi cike da kwalla ya ce mishi.

"""Likita ka raba ni da shi, don Allah nayi alkawarin ba zan kuma aikatawa ba."""

"""Tow zan daura ka akan magani, na tsawo kwanaki sannan idan muka tara shi wuri guda sai, a maka aiki a cire amma ka kula gaskiya domin zaka iya rasa lafiyarka sannan idan ka cigaba zaka iya kamuwa da wasu cututtukan da babu magani sai mutuwa."""

"Tashi zaune yayi ya rike hannun likitan, kamar yaro karami ya ce mishi. ""Likita na daina don Allah ka taimaka min bana iya rike kashi ma."""

"""Shiga ga ban daki, kayi."" Haka ya shiga da gudu, tausayin Amaan din ne ya kama shi. Can da Amaan din ya fito ya zauna yana dafe goshinsa ya ce mishi. ""ka kula sosai sannan idan mun yi aikin na cikinka zamu duba wurin muga ko zamu iya aikinshi."""

"""Ba zaku iya bane?"" Girgza kai likitan yayi yana cire handglove din hannun shi yana faWin. ""A'a ba haka ba ne, wurin yana da matukar hatsari ne matukar aka tab'a wurin ya samu matsala tow kai baka isa ka rayu lafiya ba, zamu duba yiwuwar dubaka ko mu turaka wani asibiti."""

"""Innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Allah na tuba don Allah likita kayi wani abu."""

"""Ban ce ba zamu iya ba, shi makasaya yana cikin wuri me matukar muhimmanci da hatsari da zarar an tab'a shi zai yi wuya mutum ya kara morar kanshi."""

"Cikin kaduwa Amaan ya kalli likitan. ""Ka min bayani yadda zan fahimta don Allah."""

"""Zan maka bayani ai, shi idan aka maka aikin matukar bai yi kyau ba tow ba kai babu rayuwa saida famfas zaka kare rayuwarka kamar yaro karami da ake goyo ne. Kullum duwawunka cikin kunzugu."""

"Wani azababben rawa jikin Amaan ya dauka. ""Likita babu wata hanya ce?"" ""Gaskiya babu tabbas, koda akwai kuwa."""

"Jikinshi ne ya dauki wani irin rawa, kamar zai saki fitsari a wandonshi. Kuma shima likitan yayi amfani da waWannan kalaman ne domin ya barranta shi daga wancan barnar domin idan ya mishi aikin zai iya komawa aikata abin da yake amma idan ya bashi tsoro dole ya hakura daga aikata shirmen domin wannan masifar da ta fad'o wannan zamanin ba karamar bala'i ba ce."

"Don haka ya cigaba da razana shi, har sai da yaji nadamar aikata haka yazo mishi, sannan likitan ya rubuta"

"mishi magani, ya tafi."

"Koda ya sayi maganin gida ya wuce, a falo ya samu Matarshi. ""Amaan ina son kudi?"" ""Ki kyale ni bani da lafiya don Allah."" Ya fada mata yana wucewa. ""Wallahi sai ka bani, kana board director ace baka da kudi uban me kake yi a kamfanin?"" Juyawa yayi ya kalleta kamar zai buWe baki yayi magana sai kuma yayi shiru, ya haura sama ya shiga dakinshi sai da ya rufe kofar ya nufi gefen gadon shi ya dauko kudi me yawan gaske ya fito. Kai mata yayi sannan ya juya zuwa dakinshi, kanshi kamar zai tsage haka yake ji. Lokacin da ya shiga dakin ya rufe kofar shi kwanciya yayi kafin ya tashi ya sha magani da fresh milki, kafin ya koma ya kwanta yana ji kamar ana tsatsagar zuciyarshi. Bai san dalilin fadawar shi wannan yanayin ba, amma tabbas bala'in da ya fada baya fatan wani ya kara faWawa, babban abin da yake kara tsorata shi ranar da Hajiya zata gane me yake aikatawa ranar kashin shi ya bushe, wani irin tsoro ne ya kara mamaye ilahirin lungu da sako, na cikin zuciyarshi. Tabbas ranar zai bukaci mutuwarshi da ganin wannan ranar."

Aryan.

"Har aka tashi aiki bai ga Amaan ba, don haka daga wurin aiki ko gida bai shiga ba, ya nufi wurin Hajiya haka ya zame musu al'ada tunda dama suna zuwa da safe sannan da rana suna zuwa wurin aikinta, yanzu da ta daina aikin wurinta suke fara zuwa kafin su tafi wurin matansu. Da sallama ya shiga falon tana lazimi. Zama yayi sannan ya jira ta gama, kafin ta kalle shi. ""Ya aiki?"" ""Alhamdulillahi!"" Ya faWa yana kallonta tv. ""Da magana ne?"" ""Matsayin Aneesah yayi mata nauyi, ita matar wani ce, mai zai hana a bawa wani wanda muka yarda da amanarshi da nagartar shi. """

"Kallonshi tayi kafin tayi shiru na wasu dakikai ta numfasa sannan ta ce mishi. ""Ina ga a bawa Abdul Majid dan Hadiza."""

"Murmushi yayi ya ce mata. ""Hajiya nayi tunanin haka, sannan idan kin lura sam ko cusa kanshi baya yi a cikin harkar gidan nan. Shi yake damun Hammayo amma shi Hammayo ko a jikinshi. Shi ya fi dacewa da xama CEO na kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES."""

"""Kuma idan aka bashi a bazata Uwarshi zata sha mamaki, duk makaman yakinta zata zubar, sannan rigimar da yake tashi akan kamfanin zai yi sauki "" inji Hajiya."

"""Tabbas nima na amince da haka, amma hajiya Amaan ya shigo kuwa?"" Tab'e baki tayi tana faWin. ""Ya shigo."" ""Tow shi kenan"" ya faWa yana me mikewa."

"""A gaida Nabeeha da takwara. Da dan Daada."""

*** Agadaz

OIM : Organisation International pour Les iMigrations

"office din yan gudun hijira suke kai takardun su ne domin a basu damar zama a cikin camp din oim yana under African countries ne, domin duk wasu ™asashen Afrika da suke makotaka da Nijar suna turo mutanensu, domin akwai hulWar zaman lafiya a tsakaninsu. Sannan akwai kyakkyawar fahimta idan har kasa ta turo dan gudun hijira Nijar zata mishi duk wani abin da ya dace har ta mai da shi zuwa ga gwamnatin ™asarshi sannan da abin yi me kyau, don haka *OIM* yana kasar Nijar a cikin jahohi biyu na ™asar, kusan kullum na duniya Addah da Ummi sai sun tafi office din amma kuma babu sa'a, domin yawan yan gudun hijirar da suke zuwa don niman a basu agaji."

"Yau ma kamar kullum bayan sun bi dogon layi, Adda da idanunta daya da ya samu matsala take ™are shi, wani jami'in wurin ya zo wucewa ya ganta ana ™o™arin ture ta a layin, ya ce musu. ""Sannu Inna muje ke daya ce?"" Ummi da take bayanta tayi maza ta ce mishi. ""A'a oga tare da ita muke ina mata jagora."""

"""Amma ai ke ya dace ki tsaya a bayanta ba a gaba ya dace ki tsaya bs."" Cikin gajiya da turereniyar da ake mata ta ce mishi. ""Shi kenan oga."" Ta faWa tana komawa gaban Addah. ""A'a muje a duba takardunku, domin ba a son me ciwon idanu yana tsayawa a rana."""

"""Mun gode fa "" suka bi bayanshi har cikin office din, mutane sai surutu suke, suna zuwa aka duba takardunsu, Asalima stamp na Hukumar tsaro ne a jikin takardar. Ba ajima ba aka sallame su aka tura su camp, wato OIM camp shine ake kiranshi da aljannar yan gudun hijira. Duk wani abu da zaka bukata na rayuwa a cikin camp din an tanadar maka, kulawar da ake bawa yan gudun hijiran ko yan kasar basu samu, domin babu abinda ba a musu. Ana kyautata musu, sannan kome nasu ana basu. Daga zuwan su aka wuce da Addah Clinic da yake cikin camp din aka fara duba matsalar idanuhta. Ita kan cewa take. ""Ku barshi zai tsiyaye da kanshi, ai idanun ya mutu."" Ta fada cike da takaici, duk ranar da ta haWu da Zahrah sai ta mata abinda ba zata manta ba, sai ta mata sanadin da ta sake komawa zero daga Add din da Yazid din ya sama mata, matukar tana numfashi sai ta saka mata Fargaba da tashin hankali a ranta, zata cigaba da zaman jiranta har ranar da zata bayyana."

"Ko a cikin Uwarta ya kaita sai ta zakulota ta rama abin da tayi mata, ba zata kyale ta ba. Haka tayi ta kintsa"

mugun nufin da yake ranta.

"Haka suka gama dubata, sannan suka sallame ta. Da magungunan masu yawan gaske."

*** Marad'i...........

#Mai_Dambulaaaaaaaaaaa

"[3/4, 9:14 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*029*

"Bahaushe yayi gaskiya da ya ce d'an uwa rigar k'aya, kabarshi a jikinka ya soke ka. Ka cire shi duniya ta zage ka. Ban fadi haka don kome ba, sai yadda nake cike da kewar Addah da Ummi, musamman Zuzu da ban san wata duniya take ba, ina matu™ar son ganin Zuzu ta gaya min meye nayi mata haka? Me yasa tayi min haka? Me yasa ta ha'ince ni? Kowacce rayuwa tafe take da kalubale. Sai dai a wannan lokacin na fahimci girma da muhimmancin nisantar su Addah. Sannan akwai wani abu daya da na kasa sabawa shi, wato tunanin Yazid, na kasa yarda ya mutu domin zuciya ta bata bani damar amsar labarin Mutuwarshi ba, sannan haka su Addah bana fatan ace suma sun mutu domin ciwon zai min yawwa."

"Yau ya kamata na fara zuwa makaranta, amma bani da karsashi da nutsuwar zuwa, zuciya ta a rufe take wani irin"

"yanayi nake ji mara daWi, haka yasa na cigaba da kwanciyar da nake har zuwa wani lokaci. Karfe tara na fada ban daki, na dad'e sosai sannan na fito daure da towel, a hankali idanuna ya sauka kan Baby da ta farka, gadon na nufa ina faWin. ""Kin tashi ne?"" Na d'auketa a kafadata, zuwa banWaki na mata wanka sannan na daurata akan karamin poo mikewa tayi tana ihu, ""yi hakuri zauna kiyi "" ai kamar na zage ta, haka yasa dole na.hakura muka fito na shirya ta cikin wata riga da wando, pink da purple. Sai farin hular Amnas, da nasaka mata, na shafe ta da turare mai daWi da sanyi, Yallabai Yazid ya koya min amfani da turare dan zaman da nayi da shi, ko wannan gidan haka ne domin gaban mirror akwai turaruka kala kala wasu ma ban taba jin sunansu ba. Hadiye yawu nayi ina jin kwalla na cika min idanu. Mikewa nayi na nufi sip dinmu na bude, karamin drowe din jikin siff din,bra ne da pants Winsu, a hankali na cire wasu farare kalkal, na saka a saman gadon na koma na bude asalin wurin kayana. Wata doguwar riga na ciro, da mayafinshi da hular da zata dace da shi."

"A hankali na saka bra din da pant, sannan na saka wani gajeran wando, iya gwiwa kafin na saka"

"gown din. Wanda aka rubuta Amnas collection, na saka a hankali, kallon kaina nayi a madubi fuskata tayi kyau, ba laifi sai dai kana kallon kwayar idanuna zaka fahimci ina cike da damuwa. Murmushi nayi na tattara gashin kaina,.na saka bam na daure shi tsaf, sannan na nufi inda mayafinshi yake na lullube, bugun kofar dakin aka yi na ce. ""Shigo."" Ina gyara jakar da zan fita da shi, ta shigo. ""Tante!"" Cikin kulawa na amsa mata. ""Na'am Barakatu?"" ""InJi Babanmu wai na gaya miki, mai kaiki makaranta ya jima da zuwa."""

"""Ok gani nan zuwa!"" Na mike ina.gyara zaman mayafina, tare da saka jaka a kafadar, na nufi wurin turare na shafa, sannan na fito ina dauke da baby, dake bata da rikici, mikawa Barakatu ita nayi na koma daki na d'aga towel din na shanya sannaan na dauki kudi a cikin drower gadon, na zuba a jakar ko da zan bukaci nayi wani abu, ina gamawa na dauko flat shoe na saka, sannan na fito bayan na rufe dakin, na dauki kayan abincin baby na kai musu, da wasu kayanta kala biyu da Pampers. ""Maman Barakatu zan tafi ga Baby Amirah sugrah!"""

"""Allah ya dawo dake lafiya, sai kin dawo."" ""Yawwa, Barakatu idan ban dawo ba, ki dafa mana shinkafa akwai sauran miyar nan ki zuba muku ku bar min sauran."""

"""Tow Tante!"" Ta fada, da sauri na fito daga wurinsu

Please Login or Register in order to submit comment