You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can baya. Babu dad'i domin idan yarinya bata yi mishi ba, a gaban jama'a zai kunyatata, sannan yayi mata sanadin barin makarantar, ni idan na bar makarantar ina zan ni? Waye zai tsaya min. A hankali naji zuciyata tana gaya min Allah yana sane da lamarina ban da Allah waye ya raba ni da fitinar Addah? Ban da Allah waye zai min nisan kwana har yau na zo nan, nasan ko a mafarki ba xan tab'a kawo kaina nan ba, amma sai ga shi Allah ya kawo ni, ya saka min da wasu abubuwan da ban roka ba,"

"Tuna wannan abin da nayi yasa na fara niman agajin Allah, akan Abdullahi don bana son dalilin da zai saka a ce min nima wani abu mara dadi ya faru da ni a makaranta. Haka yasa na yawaita addua, ba dare ba rana, yawan addu'a yawan sab'ani da nisan da ke tsakanin mu, haka yasa kowa yake kallon kamar ya kasa min kome, ni nasan Allah ne ya shiga tsakanina da shi, ba iyawata ba ne kuma ba wai don nafi kowa ba ne, a'a Allah ne yaso haka."

"Haka lokaci yayi ta tafiya har muka kammala aji daya, muka shiga biyu abin ba wuya fa. Koda yake kana naka Allah yana na shi, na Allah shi ne gaskiya amma tabbas rayuwarmu karewa take, a lokacin Amira tana da shekaru biyu a duniya, ga ta da farin jini, haka yasa nake kara boye ta gudun kada bakin jama'a ya tasirantu akanta, don idan baki yayi yawa akan Yaro ana iya samu nakasu, sosai na ke boye ta."

"Nima Babba ban da ina saka Hijab da dogayen riguna dayawa cewa suke ni somalians ce, domin yanayin fata ta da jikina. Koda nace musu fulani ce ni ba yarda suke ba, na sha gaya musu ni Daga Nigeria nake amma sai su ce eh ai haka kowa ma yake boye Asalinsa. Haka yasa bakiWaya nake jan bakina nayi shiru ina kallon ikon Allah"

"

Somewhere in south Carolina.

"Babban gidan rawa ne, da yake tashin sautittuka. Dauke take da tire izuwa gaban wasu gungun matasa, maza da mata. Ajiye musu tiren tayi tana cire kofi nan glass din kan tiren. Sanye take da farin shirt da top akan rigar, sai skirt iya gwiwarta. Cikakkiyar bafulatana Zulaihah tsaye ta tufke kanta, da yake sanye da katon Black bam. Sannan ta Wauki tiren zata juya, wani matashi a cikin matasan ya mari mazaunanta, bata kula shi ba haka ta wuce inda suke Waukar kayan, ta tsaya. ""Zully ya dai?"" Murmushi tayi sannan ta ce mata. ""Ba kome Ra'if."" Ta faWa tana shafa bracelet din hannunta. ""Ko kin tuna da Baby da Zeehrah ne?"" Juyawa tayi tare da washe hakori, ""Eh kusan haka ne, amma a yanzu basu ne a tunani na ba, yadda zan bar wannan aikin nake."""

"Murmushi yayi ya karkad'a haWin da yake sannan ya ce mata. ""Dala talatin ake biyanki duk sati biyu, sannan kina sane da cewa Mr Williams ba zai kyale ki ba sai kin biya shi dukkan kuWin shi da ya saka akanki sannan zai barki ki tafi, bazan baki shawarar sabawa Allah ba, amma ki nemi yadda zaki yi, ki biya shi kudin shi in sha Allah akwai aikin da ya fi na shi."" Murmushi me ciwo tayi, tana wasa da bracelet din hannunta, kafin wasu gungun mata suka shigo, suka ce ayi musu hadi na musamman a kai musu, ita ta kai musu."

"Yau club Win yayi wani irin cikar da ba cika yi ba, saboda bikin auren jinsi da aka yi maza sun auri"

"maza mata sun auri mata , yayinda wasu masu jinsin biyu suka auri yan uwansu. Abin ba a cewa kome shi yasa club Win ya cika makil, babban burinta shine, ta fita kafin wani lokaci domin ana cika club Win xa a rufe kofar kuma haka yana nufin babu abinda ba zaa yi ba. Kallon agogon bangon club Win tayi, karfe biyu saura, kamar lokacin ake cin kasuwar rana, don haka ta cewa. ""Ra'if zan tafi, yau gidan nan babu masaka tsinke, kuma abin da zai biyo baya, babu kyau."" ""Ok ki shiga office din Mr Ardor Kiyi sign."" ""Na gode."" Da sauri ta wuce tana kallon agogon domin tasan Mr Williams yana can yana jiranta, idan ta kara koda minti Waya ne, sai ya ci mutuncinta, sannan ya wulakantata a gaban jama'a. Sauya kaya tayi zuwa doguwar riga, sannan ta yane kanta da mayafi, kafin ta wuce office din Mr Ardor tayi knocking, gurnanin shi ta ji haka yasa ta ce mishi. ""Sir nazo Sign ne."" ""Shigo kiyi zully "" shiga tayi zuciyarta na dukar uku uku. Kin kallon inda suke tayi ta wuce tayi sign, ta fita da sauri cikin d'aga murya ya ce ""crazy bitch."" Ita kan da gudu ta bar club Win, ta nufi wurin Bus stop. Tana tsaye har na wani lokaci kafin ta samu taxi zuwa gida, ina shiga na sauke ajiyar zuciya. ""Ke yar Afrika ce?"" ""Eh!"" Ta fada tana kallon gefen hanya, wani irin kewar Zahrah da Babynta"

"take, don ba karamin wahala ta sha ba. Don ma Allah ya taimaka, bata yi karuwanci ba amma kuma duk wani abinda"

"yake da alaka da assha a wurin take zaune, Mr Williams shine wanda ya saye ta a wurin wani dan kasar Japan, Hararu James. A wurin Hararu James ta fara aiki a bar din club Win. Mr Williams irin kazaman masu kudin nan ne, amma gurgu ne akan keke yake yawo, yana da yan mata kamar hauka, amma matsalar shi guda daya ne, a tsotse mishi taliyarshi. Tunda shi dai ba iya abin arziki zai yi ba, amma kuma zai mika musu ita kamar abin wasan Yara, sannan a duniya babu wanda yake addaba kamar Zuzu, domin ta fisu iya sarrafa abin. Idan ta makara kuwa haka zai rufeta a daki yasa Yaranshi yan mata su mata duka, tunda ta fahimci cewa akan haka suke dukanta yasa ta ™o™arin kiyayye abin da zai ja mata duka, kafin kace me har sun isa gidan, ta biya kudin motar ta nufi cikin gidan da sauri tana sauke ajiyar zuciya ko waya ba a bata damar rikewa ba, balle har ta nime wani nata, a farkon zuwanta har kula da aladu sai da tayi a wani gidan gona, tayi aiki na tsawon wata shida tunda aka fahimci ba zata iya aikin karuwanci ba, domin bayan haihuwarta take zubar da jini, babu namijin da ya isa ya kusanci inda take da sunan lalata, ba tare da zaren sadarwar shi ta tsaya ba, haka yasa suka camfeta da cewa yanayin kyanta da surarta ba mamaki tana daga cikin godness, haka yasa bakiWaya kowa yake tsoronta sai Mr Williams kawai da yake jin dadin ta tsotse shi."

"Kwabe kayanta tayi ta shiga dakinshi, yana kallon yadda ta shigo mishi murmushi yayi yana faWin. ""Good girl, tawo"

"nan."""

"Hawaye ne ya cika mata idanu, tana ji aranta Allah ya bi mata hakkinta kamar yadda Addah ta watsar mata da rayuwa."

"Sai da tayi mishi kamar yadda take mishi sannan ta fito ta wuce Wakinsu tayi wanka tare da alola tayi sallah,"

"

"Tunda ya dawo daga Poland bai kuma wani tafiya mai nisa ba, asalima Aryan yake wakiltawa akan kowani tafiya,"

"shi kuma da Amaan suna jikin kamfanin domin, sau daya suka hadu da Hajiya Tani a wata kwanciyar Nana asibiti,"

"wai ta shiga ban daki ta zame ta faWi, shine ta buge kugunta. Ai kuwa ta saka rikici kugunta ya Salle, aka yi aka yi ta nunawa mutane taki. Majid yana zuwa ta shiga nishi tana matsar kwalla. ""Alhajin Allah, ka shiga tsakanina da afiya ta fita daga gidana. Tunda ba tare Mamman ya bar mana gadon shi ba, kaga yadda na karya kuguna yarinyar nan zuba min ruwa tayi na zame gashi nan ko tafiya bana iyawa."""

"""Sannu Nana, ina ga zan sayo miki magani."" ""Wallahi ba zan yarda ba, ina wancan yarinya har daukarta kayi zuwa asibiti da bata da lafiya.""shiru yayi yana kallon yadda take kirkiro tashin hankali, saboda ya kula da Zaytoon da tayi fama da matsanancin rashin lafiya. ""Amma ita ai da kafarta ."""

"""Yo idan ba an shiga tsakaninmu ba, uban waye ya ce maka bani takawa da kafata?"" ""Amma Nana cewa kika yi kin karye?"""

"""Dalla can annamimi kwarin wake, na gaya maka bani zuwa ne ko kace na tashi na kasa ta shi ne? Ni fa bana son hada husuma na lura da kai Allah ya hore maka baiwar munafurci, Alhajin Allah muje asibitin ka ji."""

"""Nana idan muka je, ganinki za ayi kawai mu dawo amma ba zasu baki gado ba."" Inji Majid. Komawa tayi gefe tana matsar kwalla, hawayen gulma yana zubo mata. ""Ai shikenan sai ka tafi ka sayo min maganin ai nasan don ka kulla ce ni ne, sa'a ba zata tab'a barinka ka kula da ni ba, ai na sani don akan abinda ya faru ne shekarun baya ko Allah yana yafe mana balle kai Alhajin Allah """

"""Nana nifa bance ba zan Kai ki asibiti ba,tashi muje."" Ya faWa yana ™o™arin danne takaicin da yake cin shi idan Nana tana wannan borin, ya lura ko Yaranta bata yiwa wannan fi'ilin sai shi da ta gama renawa hankali. ""Yawwa dan albarka ai nasan sa'a bata yi haihuwar banza ba."" Haka ta mike, ya shiga gaba suka tafi asibiti. Tun kafin ya ga likitan kowa ta gani sai ta gaya mata ai jikanta ne ya kawo ta ganin likita don ta faWi, Yaron nan dan albarka ne, yadda ya damu da ita ai ba karamin abu ba ne, ita bata so zuwa ba amma shi ya matsa lallai dole sai tazo, gashi nan.dai tazo. Yana jinta haka ya share yaki yar da ya bata fuska kada ta disga shi ( Nana ikon Allah) da ya gaji da surutunta, wani daki aka kaita ya ce mata. ""Nana wallahi kiyi shiru ki zauna lafiya domin maganarki tayi yawa, kika kara magana wallahi zan saka su karya kugunki kowa ya huta."" Hannu ta kai bakinta ta rufe kamar yadda ake saka Yara su yi shiru."

"Haka tayi jinyar nan lafiya lau, don ma sai ta ga Majid zata fara narkewa, sannan duk wanda bai zo ya gaishe ta, in sha Allah kiranshi take awaya ta zungura mishi zagi me tsalle sa bakar magana, tare da cewa ko mutuwa tayi banda gayyatar su kan gawarta."

"Haka tasa Majid ya kira Aryan ta zage shi tas, sannan ta ce mishi. ""Kuma na gaya maka ko mutuwa nayi kada na ganka kan gawata, don bana bukatar almura irinka."""

"Dariya yayi yana faWin. ""kice kin kawo min kanki asibiti."" ""Alhajin Allah, sallame ni wannan bakin munafikin"

"yana zuwa ban san me yake nufi da ni ba."" ""Nana baki warke ba, gara kiyi jinyarki kada wani abu ya faru ace wani abu ya same ki."""

"""Kai babu abinda xai faru kawai ka sallame ni na gaya maka."""

"Haka ya sallame ta, suka.dawo gida sannan zaman asibitin jidali ne fa, duk wanda xai je gaida ta, da ledar shi na kunshin nama, ko cooler da farfesu. Wannan abin ya matukar takurawa rayuwar Nana, ga shi Zaytoonah itama duk zuwa da katon kular farfesu. Idan tazo Nana tayi ta watsa mata harara a fakaice, don tana ganin kamar da gayya take leka Majid."

"Wannan bibikon da Zaytoonah take yiwa Majid yasa aka fara kananun magana da cewa ai suna soyayya ne, shi kuma har ga Allah babu wannan batun, abin da yasa Ita Zaytoonah jin kamar ta mallaki Majid din, ta shiga wani kaf-kaf da shi."

"

Alhamdulillahi...

"Shekaru hudu, a wannan zangon karatun manyan kamfanoni da ma'aikatu sun turo takardun daukar Walibai masu hazaka. A cikin wannan yanayin daya daga cikin BA'ARE GOLDEN EMPIRES suka turo mataimakin Chairman dinsu Saura daya na gama Book one!"

300¦

0016341139 unity bank zahra'u yahaya Ali Katin MTN 400

#Mai_Dambu ce

"[4/22, 8:49 PM] Queen BeeBee: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

*040*

_Karshen littafi na Waya!_

"A ranar da kamfanin Ba'are suka zo, sun yi amfani da score din mu na kowace semester ne, haka yasa ina zaune aka"

"kira sunana, kamar wacce aka tsikarawa allura haka na mike ina zare idanu, ""Ni Zahra Abubakar?"" ""Eh ke."" Mikewa nayi tare da bin bayan masinjan Den, a hankali nake tafiya ina tattare hijab dina, har Office Winta."

"Lokacin da muka isa ni daya na shiga office din, manyan mutane ne a cikin office din idanuwansu ya dawo kaina,kunya kamar na nitse a kasa, ""Shigo ki zauna!"" Aka ce min, haka na samu wuri na zauna ina zare idanu. ""Zahra Abubakar."" Gyada kai nayi, kafin suka cigaba da tattaunawar su, ""Za'a a tura ki kamfanin Ba'are, kuma dama muna neman kwararru akan kasuwanci da kuma tattalin arziki, shin wacce gudummawar zaki bawa kamfanonin mu."""

"Zufa ce ta karyo min muryata na rawa na ce musu, ""Zan yi iya kokarina domin na bada iya gudummawar da zan iya, wannan shine kawai abin da zance."""

"""Bakya da wani fata ne ga cigaban Kamfanin?"" Murmushi nayi sannan nace musu, ""Fatana zai tsaya ne akan abinda ya kai ni, na gama lafiya na dawo makaranta lafiya"""

"Kallon juna suka yi kafin suka ce min. ""Kafin yau kin tab'a aiki da wani kamfani?"" ""A'a ban tab'a ba, wannan shi ne karon farko da zan fara."" Shiru suka yi sannan suka ce min. ""Idan har muka ga kwarewarki zamu dauke ki aikin dindindin."" ""Ina me farincikin jin haka, ni kuma xan yi iya kokarina akan aikin."""

"""Allah ya bada sa'a."""

"""Amin na gode!"" Na fada ina mikewa, bakiWaya sai naji babu wani shakka a raina, domin kuwa wani irin nauyi ne da aka sauke min nake ji, haka yasa na wuce aji. Fitowa ta na hadu da Kashim daya daga cikin abokan Abdullahi, kamar maye duk da ya gama makarantar amma ya mai da makarantar gidan Ubanshi, ""Kizo ga Sauban can mota ta buge shi."" Amadadin na wuce aji sai na tsinci kaina da faWin. ""Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, garin yaya yanzu na fita na barshi a aji fa."" ""Eh "" yayi gaba ina bin shi a baya, abin mamaki mu da zamu bi cikin mutane sai gashi ya kusa ta cikin lungun makaranta, ganin haka yasa na juya tare da cewa. ""Ba zan bi ka ba, idan ma turo ka aka yi."" Na juya tare da tattara hijab dina zan zuba gudu. Saka min kafa aka yi, ban san yaushe yazo wurin ba."

"""Kin zata zaki shigo tarkona ki gudu ne? Bayan na gama tsara yadda zan kamaki, shine zaki gudu."" Murmushin takaici nayi nace mishi. ""Sam babu tsoron zaka min kome, domin ba zaka iya ba. Kana tsammanin kai har zaka"

"razana ni na razana?"" Mikewa nayi tare da cigaba da cewa. ""Zan tafi kuma babu abinda zaka iya min, don ba xaka iya"

"dakatar da ni ba. Abdullahi ba tsoronka yasa nake gudunka ba, ko daya ni bana gudun sharrinka. Tunda Allah ya kare ni daga ta'addancin da aka yi mana, bana jin akwai wanda ya isa ya min wani abu. Sannan izuwa yanzu na koyi tsayawa kaina."" Takawa nayi gabanshi ina yar dariya na ce mishi. ""Gata tayi maka yawa, jin dadi sun lullube ka. Bani amsar waWannan tambayoyin nawa, ya zaka ji idan aka kashe mahaifinka akan idanunka? Ba ni amsar nan ya zuciyarka zata dauki ayiwa ahalinka fyade kana gani amma babu yadda ka iya?"" Hawaye ne ya zubo min, na haWiye kukana na ce mishi. ""Ya zaka ji idan wad'anda ka yarda dasu, suka ci amanarka ya zaka yi? Duk wannan ciwon da aka jiwa zuciyata bai saka na juya da baya don tsoro ba, shine kai akan yar kudirin da bai wuce kayi minti ashirin kai minti biyar ma, kai ji mana gaya min a wannan lokacin da na dawo daga mutuwar ce zaka razana ni har na razana? Gaya min? ni da har mutuwa nayi na dawo don na cimma abin da nake bukata baka san yadda rayuwa take ba shi yasa idan kaci ka koshi, baka da burin da ya wuce ka wulakanta mata irina masu kima da daraja, bana faWa kuma bana son faWa,amma abinda kake so ka gani a idanuna har abada babu kuma ba zaka tab'a samu ba, domin gata da jin dadi sun saka kullum lissafinka na dabbobi ne, da kana lissafi irin na zakuna mace ba ta gabanka sai abin da kasa a gaba ,don haka b'ace min a gaba, duk ranar da ka samu amsar tambayoyina ka zo ni zan baka damar yin yadda kaso da ni.."" daga haka na juya na barshi sake da baki, shi yasa aka ce ko wani mutum da fahimtar da yakewa kowa shi nashi fahimtar Mijinta ya watsar da ita, shi yasa zai maye gurbin shi duk yadda yaso ya b'ata mata lokaci da rayuwa, yanzu ya fahimci ashe bai san meye rayuwa karan kansa ba. Wauta da hauka yake domin da yasan darajar rayuwa ba zai tsaya bata lokaci haka ba,"

"A hankali ya juya yana bin bayanta da idanu,shin me rayuwarshi ta amfanar mishi? Me gatan da ya ke da ita tayi"

"mishi? Babu kodaya, a kodayaushe burinshi ya sami kintsatsiyar yarinyar ya lalata mata suna don basu cancanci shiga jami'a ba ko me? A rayuwarshi ko rashin kunya yaga mace take yi tsanarta yake domin yana ganin ta gama lalacewa babban burinshi ya lalata goben kamilalliyar mace, domin yasan dama wasunsu ba karatun ya kawo su ba, lalacewa ce ta kawo su makaranta. Da farko ganin Zahra ya kwadaitu da ita ne saboda wani irin dirin da take da shi, haka yasa shi matukar bukatar yayi nasara akanta. ""Boss ko muyi mata daukar amarya ne?"" ""Kai duk maganar da tayi bai shiga jikinka ba ne?"" Inji daya daga cikin abokan Abdullahi, ""Ya ne?"" ""A 'a tunda yake wata ta tab'a mishi irin wannan maganar? Don haka yarinyar nan ta tuna min da abinda na rasa, ban san hakkin yan matan da muka lalata ba, kaga tafiya ta Allah na tuba."" Haka ya tafi ya bar su, kafin kace me sauran biyun sun gudu sun bar Abdullahi a tsaye shi Waya kamar gunki."

"*Ni kan tunda na bar wurin, sai naji hawaye masu yawa suna zubo min,* nasan ba wayo na bane ko iyawata ba, kawai ikon Allah ne da buwayarshi. Aji na koma na dauki Jakata, na fita zuwa gida. Haka na wuni suku-suku. Sam na manta da batun zuwa aiki kamfani."

"

Niamey

"Cikin bala'i ta nufi cikin gidan Hajiya, tun daga bakin kofa take kwala mishi kira. ""Alhajin Allah, Alhajin Allah,!!"" Barci yake amma haka ya farka tare zuro kofar shi daga gado, ya gaji da fitinar Nana wallahi kamar ya gudu ya bar garin. ""Alhajin Allah!"" Ta kuma kwala mishi kira. ""Nana Barka da zuwa "" ""Yawwa ba wurinki nazo ba"" ta fadawa Hajiya tana baza hanci ita nan tazo wurin jikanta. Kasancewar yau Asabar yana hutun karshen mako, amma haka Hajiya Nana ta zo kawo mishi rigima. ""Sa'adatu ina Alhajin Allah."" ""Yana dakin shi."" ""Au sai na roke ki ne zaki kira min shi?"" Gyaran murya yayi daga bayanta. Washe baki tayi tana faWin. ""Dan arziki irin albarka, kun ga d'an da aka haifa tsiya tana barci, bata farka ba balle ta ganka. Alhajin Allah dan maliki me had'arin CFA, Hmmmm"" ta kuma ce cikin sigar gulma da ya kawo ta. Zama yayi yana fuskarta ta tare da hamma yana mika. ""Assalamu alaikum!"" Muryar Aryan da Zaytoonah ya ratsa falon, juyawa tayi ta wani turbune fuska irin bata yi maraba da zuwan su ba. ""Alhajin Allah, magana ce ta kawo ni. A tow ni dai tunda na ziyarci garin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, na dawo rakiyar munafukai da yan tsugudidi, sannan nayi alkawarin agaban Uban fatsima ba zan kara cin amanarka ba, tunda dai Umaran kai ne ka biya min ko?"""

"Gyada kai yayi yana kallon Zaytoonah da take narke mishi, salon fitina kala kala, Zaytoonah ta sani, duk da surutun da ake na cewa suna soyayya bai tab'a cewa kome ba, amma yana damuwa da ita, domin bai da abokiya na kusa kamarta, a lokacin zamanshi a kamaru, ita ce abokiyar hirarshi. ""Hamma!"" Bude shanyayyun idanunshi yayi akanta domin yadda take mishin nan, baya ya iya daukar abin, tausayin ya kasa koyawa kanshi sonta yake ji."

"""Ke bana son karuwanci, kin zo kin wani min bake-bake ke gaki nan yar bala'i. Wallahi gaban kika taras,ke har kin isa ki saka min jika a gaba? Haka kawai ban da karuwanci kin wani zo kina wani hamma a'a gatari ne, da ke da munafikin da yake zugaki wallahi sai na sha dammara mu doku. Kunji min munafukar yarinya wani"

"hammmmma, a'a gatari ne Sa'a zo ki dauke min wannan me shigen fatalwar a gaba, nazo ganawa da jikana kin wani"

"fito sai kace an daurawa cokali zani, wani hamma."""

"""Gaskiya Nana baki kyautawa."" ""Dalla can ka rufe min baki, ka wani zo da dogon wuya kamar autar amale, wallahi ahir dinka Ariyan na gaya maka ka fita idanuna domin nasan munafurcin da yake cin ka, algungumi da kai kamar tukunyar mayu."""

"Zuba tagumi Majid yayi yana kallon Nana tana faWa akanshi. ""Ina jinki Nana."" ""Raina ma ya b'aci duk na manta abin da nazo gaya maka, haba don Allah ayi duk gidan sa'a ba mutane na gari sai kai, duk mutanen banza aka haWa, alawadan naka ya lalace."""

"""Hmm! Muje na rakaki."" ""A'a zan tafi da kafata."" ""Tow muje na saya miki nama mana Nanata."" Washe baki tayi tana faWin, ""ke dai Sa'a kin iya farar haihuwa, kin ga d'a nagari, rabona da naci Nama tun bayan mutuwar Mamman."" (  Nana bata tsoron ilahi) ""Tun mutuwar Abba rabonki da nama kika ce fa?"" Inji Amaan da ya shigo gidan, ""Eh karya nayi Alhajin Allah?"" Share ta yayi ya wuce dakin shi ya dauko key, ""Nana kina jin tsoron Allah a cikin lamarinki, ban da tada husuma wai rabonta da cin nama tun mutuwar Abba."" Ai kuwa Nana tayi caraf ta fasa ihu, tare da zama a wurin dirshan tana kuka. Tsaki Majid yayi, ya lura sam idan akwai waWanda suka fi Nana fitina Aryan da Amaan ne, ""Wai meye haka ne Aryan, Amaan kai da kake babu."" Inji Hajiya,"

"""Hajiya kyale wannan tsohuwar bata da aiki sai fitina, wallahi duk ta saka Abdul a gaba sai kace danta, tayi kukan jini mana."" Saukowar Majid ne yasa ta sake karkace kai tana kuka. ""Tashi muje Nanata."" Mikewa tayi tana faWin. ""Kaji abinda suke gaya min.,"""

"""Allah ya shirya su."" Ya faWa suka fita, yawo yayi ta yi da ita tana bashi labarin gulmar shi da aka yi a dakin Hajiya Rabi, da kuma wani abin da bata fahimta ba, shine ta ce mishi. ""Mun gama da daya shima Ubanta mun hana shi magana."""

"""Inji waye Nanata?"""

"""Hmmm! Inji Balaraba yar gidan Rabi. Kasan

Please Login or Register in order to submit comment