You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta surfa min, na dauka na wanke shi tass. Sannan na zuba ruwa na watsa gefen. Bude frij nayi, na dauko yogot na ciro na ajiye. Na gyara alala ta na Wora bisa wuta, sannan na koma daki nayi wanka. Na saka kayan shan iska, na fito nazo na dama kunun garin kunun da ruwan tsamiya na."

"Har kunun yayi min yadda nake so, na ajiye shi na daura shinkafa jallof, na cigaba da aiki. Ina haWawa na dawo na kunna tv, na fara kallon tafsirin Malam Awwal Albani Zaria. Gyara kwanciya nayi ina kallon, sai da naji kamshin alalen ya cika min hanci naje na sauke, kusan uku suka fashe. Haka na ajiye na gama haWa kome na fito dashi a faranti. Ina ajiyewa ana kiran sallah, komawa daki nayi na dauko jakata na tuna akwai fruit da na sayo. Haka na fito da dabino naci, na sha ruwa. Ban tashi a wurin ba, suka dawo min da Amirah, tayi barci kwantar da ita nayi na mika musu nasu abincin. Ina faWin, ""ku gaida min Mamanku."""

"""Mun gode sosai!"""

".... Bayan nayi sallar Magariba da Isha da su tarawee,, na kwanta a falon. Har na fara barci sama sama, naji kukan Amirah dakin nashiga na cire mata kayan jikinta, na mata wanka na sauya mata na barci. Sannan na dawo dakin bayan nayi wanka da alola, na kwanta barci me nauyi ya Wauke ni. Washe gari na tashi da wuri da yake Muna da test. Da wuri na wuce ban dawo ba, sai karfe biyu a gida nayi sallah."

"Haka aka azumi yayi ta tafiya, rayuwar da dadi babu dad'i, ban rasa ci ko sha ba. Amma sai nake ganin kamar daular tayi min yawa, ina matu™ar son da ko wani ne a cikin dangina na gansu, su dandani dadin da nake ciki sai dai.nasan kamar yadda Allah ya halicci wuta da ruwa basu gamuwa, haka nasan matukar muka hadu sai mun yi abin kunya, haka yasa ta wani bangaren nake ganin kamar nauyi aka sauke min akan Addah, gefe guda kuma ina jin kamar ban kyauta ba, ba dadi mutuwar mutanen da kasani. Amma kuma mutuwar Addah shine samun sukuni na da Amirah."

"Kwanciyar hankali da nutsuwa ya shige ni, sannan wani abin da ya kara bani mamaki ashe tun fil azal ina da kalar fata mai kyau, domin kuwa nayi fesh kamar bani ba. A makaranta ma gani na da Amirah yasa mutane dayawa sun shafa min lafiya, domin daga malamai har dalibai farkon zuwana sun fara matsa min da gaisuwa. Ni kuma na iya dauke kai bana kula kowa harkar gabana ta ishe ni."

"Saura kwanaki uku mu samu hutu, wani malami ba a department Winmu yake ba, amma bakiWaya idanunshi"

"yana kaina duk da bana son kula shi. Amma haka yake saka a kirani, Ni kuwa idan naje bana magana sai na tsaya mishi a kai."

"Yau ban shigo ba sai karfe goma, ina shiga department Winmu na ganshi dauke kai nayi kamar ban ganshi ba,"

"koda na kusan wucewa ya ce min. ""Zahra Buba!"" Juyawa nayi nace mishi.""Ni!"" Tasowa yayi daga inda yake zaune ya ce min.""Bayan ke akwai wata Zahra Buba ce?"" Share shi nayi naki magana. ""Ok! Dama akan yanayin gari ne ya kike?"" ""Bashi ya kawo ni ba."" Na fada ina karawa gaba. ""Ai naji labarin baki da miji zaman kanki kike."" ""Ina baka shawara da ka kiyaye kanka da bin rayuwar wasu, bin rayuwata kamar wasa da wuta ce."""

"""Ai na zata wasa da mutuwa ce."""

"Murmushi nayi na ce mishi. ""Ban yi wannan wayewar ba, amma ka tsaya a matsayinka."" ""Ok zaki gani, wallahi matukar kika yi wasa sai na baki mamaki."""

"""Ina mai baka shawara kada ka bani mamaki, kayi harkar gabanka nayi tawa."" ""Mtsew dani kike zancen."""

"Ban kula shi ba, na wuce aji abina na gama abinda nake muka fito. Bayan nan aka sanar da mu dawowa makaranta sallah da kwana biyar."

"Haka muka bar makarantar, zuciya ta tayi min dad'i. Ba karamin dadi ba fa. A wurin ajiye motoci na ganshi, sai da gabana ya fadi. Sai da na isa jikin motar ya wani fisgo ni. Fitowa Badar yayi ya zagayo ban san me yayi mishi ba, sai dai naga ya sake ni da sauri. ""Madame shiga gani nan zuwa."" Shiga motar nayi babu musu. ""Kayi hankali ba kowane abinci ake ci don koshi ba, akwai abincin da a madadin yayi maka dad'i, guba ce domin kashe ka zai yi. Nasan labarin kowa a cikin makarantar nan. Hmmm kace me?"""

"""Ban ce kome ba!"""

"""Yayi kyau, ko a hanya ka ganta ka kiyaye abin da zai saka ku had'a idanu. Ni nayi maka da sauki idan da wani ne tuni"

"ya tashi kanka."" Daga haka ya juya wurin motar ya shiga ya bar shi a nan tsaye, nima nayi mamakin me yasa yayi laushi lokaci guda, haka muka bar makarantar. Alhamdulillahi Yazid ya kare min mutuncina da kimata, yadda yayi al™awarin. Abin ya tab'a ni da yasani kuka ban sani ba, baya raye amma babu wanda ya isa ya min barazana a kyale shi. ""Meye alakarka da Yazid?"""

"Juyawa yayi ya kalle ni, kafin ya cigaba da tuki. ""Sultan zaki ce, idan ba Sultan ba. Ba zan iya baki amsar tambayarki ba."""

"Ya fada yana cigaba da tukin, ""Sultan kuma?"" Na kuma tambayarshi, bai bani amsar ba domin har mun iso gidan. ""Sultan! Waye Sultan Yazid?"" Murmushi yayi sannan ya ce. ""Mun iso gidanki....."

"```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available da saukin price"

"Huluna da Mayafai,na manya da na yara sai Wanda ranku yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shaddodi na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya mun tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au kafin kishiyarki tazo ta saya tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida atow kayanmu na Uwayen gida da Amare ne```"

*TUNTUBi WANNAN NUMBER 08130269641*

Leshi ATAMFOFI SHADDODI

Materials Kayan yara Veils Huluna. etc

#Mai_Dambu...

*BA˜IN HAURE *

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

Sorry Dearest yau babu editing .

*033*

"Jikina a matu™ar mace na fito daga motar, ""Waye shi?"" ""D'a ne ga sarki Hamir Julaibi na kasar Algeria!"" Bakina na rufe, jikina ya dauki wani irin rawa. ""Me?"" ""Na gaya miki gaskiya."" Juyawa nayi tare da barin motar, ina shiga falon na zube kamar wata matacciya, domin kuwa Yazid yana kashe ni da Mamaki,idan nace ban jijiga ba kayi karya. Ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, tashi nayi da gudu zuwa dakina na shiga banWaki na bude ruwa a kaina, zama nayi can gefen can banWaki. Yadda na ke kuka ni kaina ban san akan me yasa nake kuka ba? Kukan me nake yi? Kukan ya boye min waye shi? Ya cutar dani ta hanyar boye min kanshi. Ban iya tsinanawa kaina kome ba, har aka sha ruwa tea nasha, sai kunu da kosai da na sha, da dare yayi na ta fasa indomi da kwai, na koma gefe ina ci ina hawaye. Da asuba kuwa sahur nayi da tea kawai."

"Washi gari wuni nayi kamar mara lafiya, ban kara wani walwala ba domin na sha mamaki."

***

"Tunda aka kawo shi asibitin, suke ta fama da lafiyarshi. Domin hankalin kowa ya tashi yadda yake duhu da fama da rama. Shafa kanshi Aryan yayi cikin tausayi. ""Amaan"" bude ido yayi yana kallon Aryan Win da yake kara shafa kanshi. ""Me ke damunka?"" Yana son magana amma babu bakin magana, haka kawai aka same shi a tsakar dakinshi yashe kamar matacce, haka yasa suka kwaso shi zuwa asibiti sai dai ko da suka zo an bincikar lafiyarshi ne. Tunda Majid ya ganshi yasan bai da lafiya boyewa yake, a binciken da suke ne aka gano aikin da aka mishi na cikin, Jamilah ta fito daga Lab rike da wasu takardun tana faWin. ""Hamma babu aikin basir. Akwai abin da Amaan yake boye muku wallahi."" Amsar takardun Majid yayi suka wuce office dinta, shiru tayi tana kallon shi kafin ta bude baki zata yi"

"magana ya ce mata. ""Allah ya kyauta meye a cikin test din jininshi?"" ""Sakamakon bai fito ba"" ta faWa a hankali tana"

"wasa da pen din hannunta. A nutse yake kara kallon takardun hannunshi, yana jin kamar ya fasa ihu ne ko kuka. Mikewa yayi ya nufi dakin Amaan. Yana shiga ya samu Aryan yana rike da hannun Amaan din. Shi kanshi bai san irin kallon da yakewa Amaan din ba, shin tausayi ne ko takaici ne? Domin bai kawo lalacewar shi zata kawo har haka ba. Dakyar ya bude baki ya ce mishi. ""Tun yaushe ka fara. "" Turo kofar da aka yi yasa shi shiru ya zubawa Hajiya idanu,"

"""Majid meke damun Amaan din ne?"" ""Ciwon ciki ne, tare da borin jini!"""

"""Ban gane ba."" Hajiya ta fada a rikice, ""Hajiya zaki gane, bari a gama bincike."" Inji Aryan yana kallon Amaan, shigowar Jamilah yasa Majid suka kara fita, nan suka kara rikicewa kamar zasu tashi sama, domin ciwon sanyi ya shige shi sannan jikinshi zai iya daukar kowani mahaukacin ciwo matukar ba a kula ba. Haka yasa bakiWaya Majid ya shiga wani irin d'imuwa da tashin hankali."

"Duk Familyn Ba'are babu wanda zai zo ba, domin Amaan bai da wani matsala da su, dake wawa ne yana shiri"

"da kowa, haka yasa aka yi ta zuwa gaishe shi. BakiWaya ruwan kan Majid ya kone, taya zai gayawa Hajiya Amaan luwadi yake bai san da wata kalamai zai iya gaya mata ba, kallon Jamilah yayi yana faWin. ""Kada ki sake Hajiya ta ji labarin halin da yake ciki. Ki bari zan ji da kome."" Numfashi ta ja tana kallon shi kafin ta daure ta ce mishi. ""Hamma"" ""kada ki damu zamu yi magana da Aryan."" Ya furta tana lashe bakinshi da ta bushe. A hankali ya a nufi hanyar waje, yana nazarin abinda zai fadawa Aryan domin bakiWaya ya tattara damuwar ya azawa kanshi. Don yasan matu™ar Aryan da Hajiya taji sai zuciyarta ta kusan bugawa, ya kuma san idan aka gayawa Aryan kamar an gayawa Hajiya ce."

"Murmushi Hajiya Tani tayi tana kallon, videon Amaan tana faWin. ""Wannan lokacin ya dace na tashi kan Sa'ah."" Shan ruwa da yake gaban shi Sajid yayi yana faWin. ""Hajiya Sa'adatu ta kare mata, dole ta biya abin da ta saya."""

"Suka fada suna dariya, ""Meye tsakaninka da Afiyyah?"" Ware idanu yayi yana fadin. ""Ba wani abu fa, chill out muke da ita kuma nasan an dauke ta aiki a kamfanin Ba'are."""

"""Lallai kwanyarka bata ja Sajjid, taya zaka fara wannan aikin."" D'aga kwalba yayi yana faWin. ""Bana kuskuren harkalla, duk abin zan yi Hajiya da tsari a cikinshi. Yarinyar ita ce Bingo dina, tana sona ina bata abinda take so. Sannan zan san yadda zata matsa jikin Chairman din kamfanin yadda zan basu mamaki."""

"Murmushi Tani tayi tana faWin. ""Yaro yaro, ni na gama shirina saura ja jira tashin bom."""

"Ta fada tana dariya, tare da barin falon. Da sauri ya bi bayanta yana faWin. ""Hajiyata me kika shirya?"" ""Lokacin da zai faru zan gaya maka, domin ni kome nawa da tsari bana faWar tsarina kada a samu matsala. "" Hura iskar bakinshi yayi yana faWin. ""Ni dai ki gaya min shirinki, domin kuwa ba mamaki na tayaki."""

"Tsayawa tayi ta kalle ta kirashi da yatsu biyu, yana matsowa ta rike kunnenshi ta gaya mishi wata magana,"

"murmushi ya sake. ""Hajiya wacce irin Shaidaniyar tunani ne haka?"" jan kunnen shi tayi tana faWin. ""Ba zan tab'a yarda wani ya san wacece ni sannan, ya dawo ya soke ni a baya ba, sun wanda ya sake ya ci amanata sai na mai da rayuwarshi abin kwatance yadda kowa sai yaso yaji me mutum yayi min haka."""

"""A'a sam haka ba zai taba faruwa ba, ai kowa ya kwana lafiya shi yaso."""

"Hajiya kam hankalinta yana kan Amaan, bakiWayansu babu wanda yake zaune, azumin ma suna yi ne amma bakiWaya hankalinsu yana can. A ranar da ya cika sati daya a asibitin aka sallame shi, domin ya d'aga musu hankali lallai a sallame shi. Hakan ya faru ne wani zuwan da Sajjid yayi mishi cikin daren rana na biyar ya, yana kwance ya shigo mishi don a sanin Amaan dai Majid yake zaune da shi amma bai san ya aka yi Sajjd ya shigo dakin ba. ""Kana ta barci, ina can ina kewarka."" Cikin tsananin tsoro Amaan ya ce mishi. ""Sajjid wai ni daya ne kawai da ba zaka kyale ni ba? Ka kyale rayuwata kayi naka rayuwar."""

"Dariya ya saka mishi yana faWin. ""Amaan ba zan kyale ba, idan ka kuskura ka haura kwana goma a cikin asibitin nan, tabbas ward din mata nan zai zama wurin kwanciyar tsohuwarka. Domin ina ™ishirwanka, sannan ka duba wayarka zaka ga kayatattun hotunan da videon debe kewa"""

"Haka Sajjid ya saka kai ya bar dakin, sanadin haka yasa Amaan d'aga musu hankali sai an sallame shi. Sannan wani abin da ya kara tashin hankalinshi, yadda Sajjid ya tabbatar mishi matukar bai koma ruwa ba, sai kowa yasan abinda yake faruwa a tsakaninsu."

"Asalin rashin lafiyan Amaan yana da nasaba da Sajjid, domin kuwa lokacin da aka mishi aiki tsakani da Allah ya"

"daina wanna shashancin, ya mugun kame kanshi. Sai dai kuma gefe guda Sajjid ya haWe kai da matar Amaan, inda suke sharholiyansu. Ranar da aka kai na farko ya dawo gida, ya ga motar Sajjid cikin azama ya shiga cikin gidan. Koda ya shiga bai same kowa a falo ba, haka.yasa ya wuce dakin shi, abin takaici da bakinciki. Zuwa yayi ya samu Matarshi"

da Sajjid suna tsulla tsiyarsu. Kuma abin bakinciki babu tsoro ko dar a tare da ita. Shi idan yana son hakkinshi sai

"ya biya asalima sai tayi ta jan shi a kasa, ya zuba mata kudi ."

"Gashi a karon iska akan Idanunshi, Sajjid yana more ta. ""Na zata duk abin da kace nayi zan yi ba zaka wuce gona"

"da iri ba, ashe har matar aurena kake hakewa."" Basu fasa ba, karshe da bakinciki ya fita a dakin yana tari, tare da ciwon ciki tunda ya koma ruwa baya ganewa kanshi, gashi kullum idan suka yi akwai wani ruwa da Sajjid yake bashi ko yana so baya so sai ya sha ruwan tun daga wannan lokacin fatarshi ta fara duhu. Dalilin da yasa ya bar mata gidan kenan ya koma gidan Hajiya har ya fara rashin lafiya, tayi tayi ta same shi ya koma gida amma fir yaki da zata dame shi ya tura mata sakinta, haka yasa bakiWaya Sajjid ta shiga takaici, na farko yana amfani da Amaan yasan motsi Aryan. Na biyu yana da abin da yake son sani daga bakin Amaan."

"Sai akayi dace ranar da ya nemi ya ji dalilin sake, Matarshi. Suna haduwa ya saka mishi kwaya a ruwa ya bugar da"

"shi, anan ya ji labarin abinda ya faru a lokacin suna Kano, kofa ya farka abin da ya faru akan shi ya dawo mishi kai, rokon Sajjid yake amma ina Sajjd tsalleke shi yayi yana faWin. ""Kada na kuma ganinka, idan na ganka sai na gayawa duniya wacece Uwarka, anya kuwa kai dan halak? Idan har kai dan halak ne ba zan kuma ganin kazamar fuskarka ba."""

"Daga haka suka rabu wannan abin ya saka Amaan tsoro da faduwar gaba, sannan wani abin tashin hankali yadda"

"Hajiya zata ji yana luwadi, yayi kuka yayi kuka amma babu abinda ya sauya domin dai bayan kwana biyu Sajjid bai kyale shi ba, cigaba yayi da matsa masa lamba, tare da amsar kudin shi har a gadon asibitin da yazo, lallai Amaan ya kwaso takardun dukiyar Majid ne. Shi yasa ya zo mishi tare da bashi wasu zabin abubuwa uku."

"Na farko ko ya kawo mishi takardun Abdul Majid Mamman Ba'are. Na biyu ko ya turawa Hajiya videon nan, na"

"uku ko ya gayawa Duniya Tsohuwar Chairwoman na BA'ARE GOLDEN EMPIRES, karuwa ce da aka kamata har aka rufeta yana da shaidun da abin ya faru da su, kuma zai gayawa duniya cewa bakincikin haka yasa Mamman Ba'are mutuwa, karin tashin hankali shi ne yana kalubalantar Aryan da Jamilah da Aneesah ba jinin Mamman Ba'are. Sai ya zab'a a cikin wannan yanayin."

"Amaan sai a yayi fatar da mutuwa yayi da Rayuwar da ya jefa kanshi, yayi kuka yayi bakinciki a duniyar nan yaji"

"kamar ya mutu ma, amma yasan darajar rayuwa, yasan matu™ar Hajiya taji abin da yasa shi zama haka zata tsane shi, zata cire shi cikin Yaranta,. Hajiya zata yi alawadai da shi. Haka yasa bakiWaya yaki zama gidan Hajiya. Haka ya dawo gidanshi,"

"Ana gobe sallah Majid suka je gidan suka same shi, a daki kamar mayye. ""Wai lafiyarka zaka bar inda kake samun"

"kulawa ka dawo nan da zama?"" Kallo daya Majid yayi mishi ya fahimci yana cikin tashin hankali, daurewa kawai. ""Amaan Mamman Ba'are!"" Yaji muryan Majid ya ratsa kunnen shi."

"""Meke damunka? Kasan dai nasan abin da kake boyewa."""

"Kuka ya fashe da shi, har jikinshi yana rawa, a hankali wayarshi tayi kara. Yana dubawa ya dauka har jikin shi yana rawa ya ce mishi. ""Meye?"" ""Ina gargadinka da ka iya bakinka."""

"""Tow naji."""

"Kashe wayar yayi yana mikewa yana faWin. ""Muje babu abinda yake damuna."" ""Shi yasa daga waya zaka ware kamar babu wani abu?"" Inji Aryan."

"""Kyale shi, yana kara cilla kansa cikin tashin hankali."" Daga haka suka fita, sai mita Aryan ya™e, haka suka nufi gidan Hajiya. Anan suka yi shirin sallah."

***

"Tun ana jibi sallah, na dauki su Barakatu muka je saloon. Aka mana lalle da wanke kai. Sannan muka dawo, ana gobe sallah, kuwa munyi cin-cin da cake, donuts. Saboda gas Wina Babba ne."

"Ranar sallah muka shirya aka zo aka dauke mu zuwa masallacin idi. Bayan an sauko idi, muka dawo gida muka"

"cigaba da bikin sallah. Ni kan ina gida su Baraka da Amirah sun tafi, yawon sallah."

***

"Za a iya kiran yau da ranar sallah, amma a zahirin gaskiya ranar yau tana cikin wasu irin ranakun da Majid Mamman Ba'are ba zai manta ba, domin ana sauko sallah idi. Labarin rasuwar Maisarah ya karad'e cikin gidan bakiWaya, kafin a ce wani abu."

"Ana cikin wannan jimamin, aka sake videon Amaan Mamman Ba'are, a internet bakiWaya, Hajiya bata sani ba sai"

"da ta shiga gidan rasuwa taga yadda ake kallonta ana cewa. ""Eh danta ne na biyu.""bata ce kome ba, sai da ta isa dakin Maman Maisarah zata isa wurin gawarta, Hajiya Turai ta ce mata. ""Sa'a da alamu tarbiyyar Amaan ya sha bambam da na su Majid waye ya sani ko dukkansu daya ne."""

"""Ban gane ba? Wacce irin magana ne haka """

"""Sa'a ai kina da waya ki duba mana, waye ya sani, Yayanki dai bamu yarda Yayan Mamman Ba'are ba ne."" Zata yi magana Hajiya Tani ya ce mata. ""Duba wayarki da bada amsa karamar mara kunya."""

"A hankali ta duba wayarta dake datar a rufe take bata ga kome ba. ""Sa'adatun me make ji? Dama Mamman yasan kina bin maza a can Kanon ya dawo dake nan innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Wayyo Allah na."""

"BakiWaya maganganunsu ya kara gigita Hajiya, bata san me suke nufi ba. Sai da Anisah ta kirata tana faWin . ""Wayyo Allah na, Hajiya su Hammayo sun mutu....."

"********Barkan yan uwa masu kamshin furanya, ni dai anan xan tsaya sai Allah ya kai mu bayan sallah. Sannan ku saka ni cikin addu'arku Hajji nan ko Umara Ya hayyun Ya Kayyum ya kiramu duk me niyyar Alkhairi Assalamu alaikum da sauran free page's In sha Allah.... Kada ku manta 300N ne babu yawa Allah ya amshi ibadarmu Ramadan Kareem  "

#Mai_Dambujebuje 

"[4/13, 4:03 PM] Cutie cutie pie: *BA˜IN HAURE *"

{Greed for Money is the roots of all evils}

Arewabooks:maidambu41 Wattpad:Mai_Dambu Mallakar:Mai_Dambu

Appy sallah ina jiran goran sallah na

034

"Wani irin dauke wuta Hajiya tayi, bakiWaya kanta ya shiga juya mata, wani irin lumshe idanu tayi tana ganin duhu yana mamaye mata ilahirin ganinta, kamar daga sama ta tsinci bakinta da faWin.""Alhamdulillahi"

"innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, Alhamdulillahi."" Ta shiga faWa da sauri da sauri, amadadin gigita da tashin hankali sai Allah ya saukar mata nutsuwa. Kwalla ne suka cika mata idanu, kafin ta shanye su ta hanyar sakin murmushin da yafi kama da ya™e. Bata ce musu cikanku ba, ta nufi dakin Maman Maisarah ta ce mata. ""Allah ya ™ara miki hakuri, nima yanzu na samu labarin hatsarinsu Amaan."" Tana fadar haka ta juya ta bar kofar dakin, a falon kuwa ganin yadda lokaci guda nutsuwa ya dawo mata, ya b'ata ran Tani domin ita so take lallai sai ta ga kukan Sa'adatu, bata kaunar yadda take wani nunawa kamar babu abinda yake damunta. Bayan tasan cikin ranta tana cikin tashin hankali, cikin takaici da bakinciki ta ce mata. ""Ikon Allah, ko shima Amaan din ba d'an Mamman Ba'are ba ne?"" ""Tassss!"" Hajiya ta dauke ta da mari, wanda yasa kowa na wurin shiga hankalinshi hatta Nana da take zaune. ""Akul ki lalata min nasabar Yarana da Mamman Ba'are, nayi shiru tsawon shekaru talatin da wani abu, ba wai ban iya magana ba ne ko tsayawa kai na ne ba zan iya ba, na zab'i shiru shine mafi alkhairi. Tare da saka ran wata rana zaki gane kuskurenki."" Murmushi Hajiya tayi tana faWin. ""Kamar yadda kika san kome akan kowa, nima haka na hana idanuna barci domin nasan wacece ke."" Matsawa sosai Hajiya tayi tana mai kasa da murya ta ce mata. ""Idanun duniya yana kanki, domin na samu asalin waye Sajjid Mamman Ba'are, tare da labarin kawar da ta kashe kawar.."" dabas Tani tayi tana kallon Hajiya baki sake, murmushi Hajiya tayi tana me juyawa bata kuma magana ba, don dama karfin hali take kawai, don ita kaWai tasan yanayin da take ciki, zuciyarta tayi mata wani nauyi, ji take kamar zata mutu. Salati da taslimi take, tana fita a gigice ta faWa cikin motar da take jiranta, tana shiga ta dafe goshinta, ""wani asibiti suke?"" Ta fada da wata irin marayar murya, wanda yake gab da sakin kuka, haka suka nufi asibitin Ba'are hospital. Tunda Hajiya ta shiga asibitin, niman wuri tayi ta zauna tana kallon yadda mutane ke kaiwa da komowa, bakiWaya basirarta ta tsaya cak, a zahirin gaskiya inda suke ya dace ta nima, amma kuma sai gashi tana kallon kome da idanun zuci, lokaci guda jin ta da ganinta suka tsaya cak."

"A can emergency room kuwa, ana ta ™o™arin a ceto rayuwar Jamilah Mamman Ba'are, tare da Aryan"

"Mamman Ba'are. Wanda yake kansu kuwa Majid ne, aikin yake da zuciyarshi da rayuwarshi

Please Login or Register in order to submit comment